Buzu book 1 complete - Chapter 4
Buzu book 1 complete Chapter 4: Buzu book 1 complete Chapter 4. Sai dai ba ta san yana yi ba, iya ƙarfinta take ƙoƙarin karanta addu'a a cikin baccin, amma…
4,480 words
Sai dai ba ta san yana yi ba, iya ƙarfinta take ƙoƙarin karanta addu'a a cikin baccin, amma ta kasa.
Gaddafi ya danƙo ta, ya fito da ita tsakar gida, ya watsar da ita a wurin, ya ce "Ku wuce ku kwanta, idan ta gama iskancin ta tashi, ba wani aljanu iya shege ne kawai, kowa ya koma ɗaki ya yi kwanciyar sa".
Jikin Baba ya yi sanyi ganin halin da Nana ke ciki, ya ce "Ba iya shege bane, na kira ma an yi mata karatu fa, kalli yadda jikinta yake yi" yayi maganar yana tsugunawa a kanta, duk da wannan abun na Nana shi kansa ya ishe shi. Wasu lokutan, sai yayi tunanin ko ƙarya take yi, amma idan ya yi la'akari da wasu abubuwan, sai ya ga normally mutum ba zai iya haka ba.
Sanyin Asuba, da zafin cizon cinnaku ne, ya sanya Nana farkawa, daga nannauyan baccin da take yi, da babu komai a cikinsa ban da azaba da wahala. Ba ta damu da yadda ta ganta a tsakar gida ba, a tunaninta ita ta fito da kanta ta kwanta a gurin, dan yanzu ba ta mamakin yadda wasu abubuwan suke faruwa da ita.
Alwala tayi ta shiga ɗakinsu, ta yi salla, sannan ta tashi su Suwaiba.
Cike da farin ciki ta tashi, dan yau ɗin ta kama litinin ce, za a koma hutun makarantar boko. Domin tana koyarwa a wata private school, da Nanny ta nema a makarantar, sai malamar da take koyar da 'yan kindergarten ta koma garinsu, aka bata riƙon ajin, kasancewar tana da kwalin sakandare, sai dai ƙoƙarinta da sabon da tayi da yaran, ya sanya suka ƙyale ta, suke ba ta dubu bakwai a wata. Tana matuƙar jin daɗin, yadda take shiga cikin ƙananan yaran, su yi ta tsalle-tsalle da wasa tana koyar da su. Sai dai ta tsananta addu'a, Allah ya rufa mata asiri, kar ciwonta ya tashi a makarantar, ta cutar da 'yan yaran.
Tana ta hanzari, ta gama abin da zata yi, ta shirya ta fita, Gaddafi ya shigo da buta a hannunsa, da alama sai a lokacin zai yi sallar asuba.
Yana ganin Nana ya tsaya ya ce "Yauwwa ke Nana, dan abu ta kaza kazanki, idan ki ka kuma tashi cikin dare, ki ka hana mutane bacci kina yi mana ihu, sai na yi miki shegen duka, dan wallahi sai na karya ki na gaya miki. Mahaukaciyar banza maƙaryaciya" Duk da ba wannan ne karon farko, da ake kallon ƙaryar ciwon take yi ba, amma tana mamakin yadda za ace, tana wulaƙanta kanta a gaban mutane, ta hanyar yin wasu abubuwa tamkar mahaukaciya. Ba ta fatan ko maƙiyinta, Allah ya jarrabe shi da irin larurarta, ba dan haka ba da ta roƙi Allah ya jarrabi Gaddafi da jarrabawar da ya daɗe yana ƙaryata ta, a kai.
Ba ta ce masa komai ba, ta ci gaba da gudanar da aikinta, ba ta damu da rashin samun abin da za ta karya ba, duk ta ga an yi abin karin kumallon, ta kammala shirinta ta fice.
Nana akwai ƙoƙarin sammako, dan haka kusan hatta malaman, duk a makarantar suka tarar da ita, ta ji daɗin ganin yaran sosai, kamar yadda su ma suka ji daɗin ganinta, suke ta murna tamkar sun ga mahaifiyarsu.
*****
Ƙurii ta yi masa da idanu, yadda yake ta jujjuya kofin kokon hannunsa, ya kalli yarinyar da take kwance a kan katifa ya ce "Ita wannan ba ta tashi rashin lafiya ba, sai da aka koma makaranta?"
Babbar macen da take gefe tana karyawa ta ce "Dama rashin lafiya ana saka masa lokaci ne? Larura ce Allah ya kawo mata" ya jinjina kai ya ci gaba da cakalar abincin.
"Wai Auwwalu me yake damunka ne?"
Auwal ya numfasa ya ce "A ina?"
"Ka ƙi cin abinci, sai jujjuya kofin kawai ka ke yi" ya jinjina kai ya ce "Mama magana na ke son yi, amma ban san yaya za ki kalli abin ba"
Ta ajiye kofin hannunta, ta ce "Ko ma a yaya zan kalle shi, gaya mini ina sauraron ka"
Ya tattara hankalinsa, cikin nutsuwarsa da kamala ya ce "Mama dama akwai wata yarinya ne, da nake zuwa wurinta, to shi ne mahaifinta ya ce in tura magabatana ayi magana"
Tayi masa ƙuri da ido, sai da ya kammala, sannan ta ce "Me ka taka haka ne Auwwal, da zaka ɗaukko maganar aure? Fili ne fa kawai da kai a ƙasa, babu muhalli ba wata uwar da ka ke yi tun da ka kammala makaranta, bayan koyarwar nan sai 'yan kame-kame, abin da ka ke samu mu kanmu bai ishe mu ba, balle ka yayimo mana wata a bar maganar nan, kar ka sake tayar da ita yanzu maganar aure, ba nan ba ce"
Auwwal yayi shiru, ya rasa abin da yake yi masa daɗi, ba ya son mutuncinsa ya zube a idon Nana, da mahaifinta. Har cikin ransa yake son ya taimaketa, mussaman da ya fuskanci ita sam ba ta da buri, kamar na sauran 'yan matan zamani.
****
A wannan karon ma, Alhaji zailani ne a zaune a gaban Malam, fuskarsa ɗauke da damuwa ya ce "Wanda aka samu ka ce duk ba su yi ba, abin ba zai yiwu da su ba, na rasa abin yi gaba ɗaya"
"Alhajin Allah, ai ci gaba da duddubawa za ayi, za a samu dai ba za a sare ba, sai kuma ɗaya aikin da na baka, yaya ake ciki yau kwana ashirin da huɗu da fara shi ko?"
Alhaji zailani ya ce "Eh, na kusa kammala shi wannan, kuma na fara ganin alamun nasara"
Mutumin yayi dariya ya ce "In dai zaka yi biyayya, to za ka samu duniya yadda ka ke so, shi wanda ka ke maganar a kansa, shi ma ba a zaune yake bane ba, wani shu'umin aljani nake so ya yi mana aikin nan, zai iya dan yana da juriya da baƙin naci, amma fafur yaƙi"
Alhaji zailani ya tattare babbar rigarsa ya ce "Dan Allah ka tambaye shi, ko me yake so zan yi masa, ba ni da burin da ya wuce, na ga bayan fatuhu, gaba ɗaya shi ya hana arzikina haɓaka, ba a faɗar sunan kowa sai nasa"
"Ai duk wani tayi, da mu kan yi wa aljani, domin mu saka shi aiki yayi, na yi masa ya ce ba zai yi ba, akwai aikin da yake yi. Makirin aljani ne, idan na matsa masa zai iya ɓata mini wasu ayyukan, amma ka ci gaba da waɗanda na baka, sallar asuba da la'asar sai kwanakin da na ɗibar maka sun cika, sannan za ka ci gaba. Zan so ace kafin lokacin a samo yarinyar nan, aikin zai fi tafiya dai-dai "
"In sha Allah, zan ci gaba da ƙoƙarin hakan, za a samo yarinyar duk in da take"
"To shikkenan, kai nake sauraro" yayi maganar yana ci gaba da zazzana ƙasar gabansa.
*****
Shigar Nana gida babu daɗewa, Baba ya ce mata, taje gidan da Jamila take zuwa, ta kira masa ita. Nana ta ji daɗin hakan, domin a zatonta Baba zai tsawatar wa Jamila ne, saboda yadda take zuwa ta shantake a gidan, ta wuni kamar a gidan ubanta.
A ƙalla Nana tayi sallama ya kai sau huɗu, sannan aka amsa aka ce ta shiga.
Jamila ta tarar a zaune a falo, tare da matar gidan maman khairat, sai kuma wata hamshaƙiyar mata a gefe, su na ta hira. Rashin dacewar hakan Nana ta gani, bai kamata ace Jamila tana tsakiyar su, su na ta uwar hira har tana sallama ba sa jin ta ba.
Nana ta kalli maman khairat ta ce "Ina wuni?"
Cikin sakin fuska ta ce "Lafiya ƙalau Nana, ke ba kya zuwa gidana, Jamila ce kawai 'yar ɗakina" Nana tayi murmushi, ta kalli matar da tun da ta shigo, ta ƙure ta da ido. Haka kurum gaban Nana ya faɗi, amma ta dake ta gaishe ta.
Cikin ƙasaita ta amsa mata "Lafiya ƙalau 'yan mata ya ki ke?" Nana ba ta iya amsawa ba, jikinta ya hau rawa har bakinta ya nuna ta ce "Ja.jam..jamila Baba yana kiranki" tana faɗar haka kawai ta juya ta fice.
Maman khairat ta ce "Jamsy, meya samu yayarki ne?"
Cikin ko in kula ta ce "Wallahi ban sani ba, kin san tana da aljanu ba wuya ta burkice, kamar sun taɓa mata ƙwaƙwalwa ma"
Maman khairat ta ce "Subhnallah, ƙwaƙwalwa kuma?"
Jamila da ta tashi tana ɗaukar mayafinta ta ce "Wallahi Anty, to sai ta tashi cikin dare tana kurma ihu, ranan fa kwananta biyu ba ta gida, babu ma wanda ya san in da take ba, kullum cikin ciwo take"
Matar da take gefe ta ce "Allah sarki, har ta bani tausayi, amma ta burge ni a nutse take masha Allah. Masu irin larurarta na buƙatar tausayawa da ja a jiki, kar ku ƙyamace ta, abin zai yi mata yawa"
Jamila ta ce "Ai ko ba ka ƙyamace ta, ka yi gudun ceton ranka, duk da ba ta duka, amma idan ta fara ihu cikin dare da gurnani, layin nan ba wanda zai rintsa. Yanzu hatta ƙawayenta sun daina zuwa wurinta, saboda tsoron kar su kwasa" Jamila ta daɗe tana ba su labarin Nana, sannan ta tafi gida.
Nana kuwa tun da ta baro gidan, jikinta yake wata irin tsuma, zuciyarta take bugawa, haka kurum jikinta ya din ga bata akwai wani abu na ba daidai ba, a tattare da gidan, ko kuma matar da ta tarar a gidan. "Hasbunallah wa ni'imal wakil. Wa hifzan min kulli shaɗanin marid " ta din ga maimaitawa cike da fatan Allah ya daidaita mata nutsuwarta.
Gaza cigaba da addu'a ta yi, bayan da ta jiyo Baba yana tambayar Jamila, wai gidan uwar ɗakin nata, ba su gama abinci ba, yunwa yake ji, Gaddafi ya bayar da kuɗin cefane, amma an yi girki an hana shi.
Wani malulun takaici, ya turnuƙe Nana, duk wani salo na zubar da kai, Baba ya iya shi, kuma hakan shi sam baya damunsa ko kaɗan.
Tun da Gaddafi ya dawo, Nana take iya ƙoƙarinta, wurin ta kaucewa yin duk wani abu da zai haɗa su, amma hakan ba ya sanya wa, ta tsira daga zagi da cin mutuncinsa. Wannan bai dame ta ba, kamar yadda malam Auwal ya rage shiga harkar ta, zuwan ma ya daina yi gaba ɗaya, sosai abin yake damunta, zuciyarta na ta son gazgata cewar Aljanin da yake bibiyarta ne, ya shiga tsakaninsu amma wata zuciyar ta hana ta yadda da hakan, domin malam Auwal mutum ne mai addini, kuma ta yadda duk abin da ya samu bawa muƙaddari ne daga Allah, Aljani bai isa ya hana Ubangiji ikonsa ba.
Duk da ya hanata yin kwalliya a lokacin zuwa makaranta, ko da kuwa man leɓe ne, dan haka yau ta saka jam baki, ko zata samu ya kula ta.
Ta riga kowa zuwa a ajinsu, ta ɗauki tsintsiya, ta fara share ajin, ta shimfiɗa musu tabarma, ta fito harabar makarantar ta share iya in da za ta iya.
Tana shirin komawa ajinsu, Auwal ya shigo makarantar, jinkirta tafiya aji tayi, ta tsaya ya zo zai gifta ta, ta ce "Yaya Auwal ina wuni" wani zirr ya ji a jikinsa, yanayin yadda ta gaishe shin, ya ce "Lafiya ƙalau" ya wuce ta zuciyarsa cike da damuwa, kamar ya waiwayo ya kalleta, sai jikinsa ya ba shi: shi take kallo, dan haka ya fasa waiwayowa. Tana ɗan jima a wurin a tsaye, daga bisani ta nufi ajinsu, gwiwa a sanyaye tana tunanin meyafaru Auwwal ya canza lokaci guda.
Tana ta kallon Alqur'aninta, tana son ta yi tilawa, amma zuciyarta na ta gargaɗinta, da tunatar da ita, halin da za ta iya shiga, muddin ta ce za ta karanta.
Tana nan zaune, 'yan ajinsu, suka taru suka fara tilawa.
Malam Auwal ne ya shigo yayi musu ƙarin Alqur'ani, sai dai da ta ɗaga kai, sai su yi ido huɗu da shi yana kallonta.
Sai dai kafin ya kammala ƙarin, ƙafafuwanta sun riƙe gam, su na yi mata wani irin zugi kamar ana karyata. Gwargwadon ɗaga muryarsu a karatun, gwargwadon raɗaɗi da zugin da ƙafafun nata suke yi mata. Ba a tashi ba, ta ɗauki jakarta ta bar makarantar, da ƙyar ta nufi gida, tana taka ƙafafuwan nata da kyar.
Ummi ta tarar a gidan, tare da Baba a tsakar gida.
Amsa sallamar Nana suka yi, suka tattara hankalinsu a kanta.
Ummi ta ce "Ummi ya dai na ga kina bin bango, kina tafiya a hankali?"
Ummi ta kalli ƙafafuwanta ta ce "Ƙafafuwana ne suke yi mini ciwo, ba a tashi ba ma na taho gida"
Baba yayi caraf ya ce "Haka dai, kullum cikin ciwo ki ke Nana, yau ƙafa in anjima ciwon kai, gobe kuma ciwon ciki, idan ki ka ƙoshi kuma sai ihu da kururuwa, ni wannan lamarin ciwon naki ya ishe ni wallahi. Can a dangin babarki ki ka kwaso wannan jarabar, ni dangina babu irin wannan"
Ummi ta ce "Baba aka ce mahaifiyar Inna 'yar bori ce "
"In ji uban wa? Ƙarya ne bayar da magani kawai tayi"
Ummi ta yi murmushi, ta ce "Nana ƙaraso magana zamu yi"
Nana ta so wucewa ɗaki, ta kwanta, duk da ta yi murnar zuwan Ummi gidan, amma soki burutsun da Baba ya fara ya sanya duk ta ji komai yayi mata zafi. To idan ubanta mahaifi ya gaza da larurarta ina ga miji, da za su haɗu rana tsaka su yi aure?" Ta zauna a hankali, tana jin yadda ƙafafuwan nata suke yi mata zugi.
"Yaya magungunan da muka karɓo a wurin mutumin nan, kin yi su kuwa?"
Nana ta jinjina kai alamar eh.
"To yaya ki ka ji, akwai sauƙi?"
Da ƙyar Nana ta ce "Eh akwai"
Baba ya ce "Ina fa wani sauƙi, babu sauƙi ko kaɗan sai wurin Allah. Nan na ɗaukko malamin nan na almajiran gangare, yayi mata ruƙiyya wai aljanun suka ƙi magana, ba ki ga dukan da ta ci ba, sai da ta ba ni tausayi amma jiya i yau. Shiyasa duk na damu na aurar da ita, ko na huta. Ai ni wannan zancen da ki ka zo mini da shi, ba ƙaramin daɗi yayi mini ba, Allah ya tabattar da alkhairi tun da shi wancan yaƙi cewa komai".
Cikin mamaki da rashin fahimta, Nana ta ce "Wane zancen ne?"
Ayshercool 08081012143 BUZU AISHA ADAM (Ayshercool) Arewabooks Ayshercool7724 Watpad Ayshercool7724
YOTA 002
BRIGHT PENS 3rd batch
P6
Ummi ta yi murmushi, ta tura wa Nana wata leda gabanta. Nana ta kalli ledar, daga saman ledar take iya hango sabulun wanka da man shafawa.
"Saleh ne ya aiko ni, tun ranar da ki ka je gidana, yake bibiyata shi fa son ki yake yi, auren ki zai yi" take Nana gabanta ya faɗi, damuwa ta bayyana ƙarara a fuskarta ta ce "Anty Ummi, Saleh kuma?"
Baba ya ce "Shi fa, ƙanin mijin Ummi ba yaron kirki"
Jiki a sanyaye Nana ta ce "To Baba Auwwal ɗin fa, da ka ce masa ya turo?"
Sai Baba ya hau faɗa ya ce "To ina na ganshi? Tun da na ce ya fito ɗin ya fito? Da a bawa bare ke, ba gara shi ba, tun da ya san larurar ki, idan aka yi auren ba ruwanmu da kayan ɗaki, ya ɗauke ki ya tafi da ke can Ikkon, wurin neman kuɗinsa ba, ɗaki ɗaya ya ishe ku kafin Allah ya yassare masa ku tara zuriya ba. Nana wannan iskokan duk aure ki ke buƙata da kin yi shikenan za su daina damun ki".
Har Nana za ta yi shiru, amma ta kasa ta ce "Baba to idan iyayen malam Auwal ɗin suka turo fa?"
Ummi ta ce "Nana wai ƙanin mijin nawa ne ba kya so ko kuwa?"
Gaddafi da yake gefe, tun da ake maganar bai ce uffan ba, ya na ta faman gyara wata radio ya ce "Ai dama ke Ummi ke ce ki ke tausayin yarinyar nan, ita ba tausayin kanta take yi ba" Nana ta yi shiru ta rasa abin da yake yi mata daɗi, ya ma za ayi Ummi ta yi mata haka, ta ce zata haɗa ta da wani Saleh, mutumin da ba nutsuwa ce da shi ba, ga shaye-shaye da yake yi, askin da yake kansa kaɗai ya isa ya bayyana maka, abin da yake aikatawa a Lagos ɗin.
Ummi ta taɓa ta ta ce "Nana kin yi shiru"
"To me zan ce, Allah ya zaɓa mana abin da ya fi alkhairi"
Baba ya amsa da Amin.
Nana ta miƙe ta nufi ɗakinsu, zuciyarta babu daɗi, addu'a take yi da fatan, Ubangiji Allah ya sa Auwal ya fito, amma Saleh kam, ba ta tunanin ko me za ayi mata, zata iya aurensa. Dan ko Suleiman da aka fasa aurensu ya fi dama dama a kan Saleh.
Ji tayi jiri yana ɗibar ta, dan haka ta samu wuri ta kwanta, ta din ga yi wa Allah kirari, tana magiyar Allah ya daidaita ta da Auwwal ya fito ya turo iyayensa. Ummi ta leƙo tayi mata sallama, amma ta ganta a kwance, ta ce "Nana bacci da yammacin nan, ni dai na tafi, in sha Allah zai zo ku gaisa". Nana na jin Ummi, amma tayi banza da ita. Shikenan dan ana so ka yi aure, sai a ace ka auri mutumin banza.
Ranar dai haka ta ƙarasa wunin ranar sukuku, dare ma yayi bacci ya ƙaurace wa idanunta, sai wani azababben ciwon kai da ya kama ta. A hankali ta din ga juyi a kan shimfiɗarta, amma babu bacci babu alamarsa, sai wannan ciwon kan, da take jin tamkar ana sara mata kan da gatari. A hankali kuma ta din ga jin, tamkar ana ɗaɗɗaureta da sarƙa, ambaton Allah take ƙoƙarin yi, amma ta kasa sai a zuciyarta. Ta saka hannun tana laluben hularta, domin ta saka a bakinta ta toshe, kar ta yi ihu cikin dare, ta hana mutane bacci. Ji ta yi an kira sunanta a tsakar gida, duk da ba ta san muryar ba, amma ta amsa a wahale. Jin an ci gaba da kiran sunanta, ya sanya ta yinƙura da ƙyar ta tashi, kanta babu ɗankwali, ta fito tsakar gida neman mai kiranta. Kallon tsakar gidan tayi, taga duhun ya ninka na dare, ba ta iya gane komai a tsakar gidan. Ta juya don ta koma cikin ɗaki, amma ta rasa hanya, saboda duhu ba ta ganin komai. Ji ta yi an ci gaba da kiran sunan ta, kawai ta hau tinkarar wurin da take jin ana kiranta.
Gaddafi yana shagonsa a ƙofar gida, ya ji an buɗe gida, ya duba agogon wayarsa, ƙarfe biyu saura mintuna tara na dare. Tashi yayi ya leƙo, ya ga Nana ta fito, daga ita sai zani da vest kanta ko ɗan kwali babu. Sai da ya bari ta yi nisa, sannan ya fito ya bi bayanta, a zaton sa ko wani yawon banzan take, sai dai ga mamakinsa kawai tafiya take yi.
Ganin tafiyar ta ƙi ƙarewa ya sanya ya ce "Ke dan ubanki ina za ki je a tsohon daren nan?" can kamar a wata duniyar, haka take jiyo muryarsa. Ba ta tsaya ba, kuma ba ta yi magana ba, ta cigaba da tafiya.
Danƙo hannunta yayi, ya din ga jan ta har zuwa gida, sai dai ba ta yi masa musu ba, bin sa kawai take yi, dan ta kasa tantance bacci take yi, ko kuma a zahiri ne.
A tsakar gida ya hankaɗa ta, ta faɗi ƙasa, cikin ɗaga murya, yake tambayarta gidan uban wa za ta a wannan daren.
Shiru tayi, ta ci gaba da laluben hanya tana ƙoƙarin tashi. Ya saka ƙafa ya hankaɗa ta ta sake bajewa a wurin. Wata 'yar ƙaramar ƙara ta saki, ta sake yinƙurawa za ta fita, wannan karon da azama ta yinƙura, sai dai tamkar ya samu namiji ɗan uwansa ya sake janyota yayi jifa da ita.
A wannan karon, ba ta ji muryar komai, sai dai zafin buguwar da take yi.
Baba ne ya fito daga ɗaki, yana tambayar Gaddafi ko lafiya.
"Wannan mahaukaciyar yarinyar ce, ta buɗe gida ta fita a haka, na bi bayanta na kamo ta".
Baba ya ce "Innalillahi wa innalillahi raji'un, ni Wallahi lamarin nan na Nana ya ishe ni, kula Gaddafi za ta sake fita". Baba yayi maganar yana nuna masa Nana, da ta kwaso da gudu za ta nufi hanyar fita. Ƙafa Gaddafi ya saka mata, ta faɗi a wurin, amma cikin ƙarfin hali, ta sake tashi. Fizgo ta ya sake yi, ya wanka mata mari har sau biyu. Amma ko gezau ba ta yi ba.
Baba ya ce "Gaddafi daina dukanta, ba fa ta hayyacinta, ba ta san me ka ke yi ba"
"Wallahi ƙarya take yi, iskanci ne kawai, buɗe idonki ki kalle ni" dan sai a lokacin ya lura duk abin nan idanunta a rufe suke.
"Gaddafi tofa mata abin da ya sauwwaƙa, ni tsorona kar ta fita tayi wani wurin ba a sani ba"
"Ni me na iya da zan tofa mata?"
Baba ya ce "Jeka kawai, bari na zauna na ga jikinta ya saki, kar ta sake fita. Dan Allah ko da bacci zai ɗauke ni, idan ka ji motsinta ta buɗe gidan, ka riƙota"
"A'a wallahi ban yi alkawari ba, bacci zan yi"
Baba ya ciro zanin mama da yake kan igiya, ya rufawa Nana da take baje a wurin kamar abin banza.
***** Washegari da safe, Nana sai haƙura ta yi da zuwa makaranta, saboda yadda jikinta yake yi mata ciwo, dan har targaɗe ta yi a hannu. Da safe Jamila take gaya mata abin da ya faru.
Shiru Nana tayi ba ta iya cewa komai ba, ita kanta dan babu yadda za ta yi da ƙaddararta ne. Ƙugin da cikinta yake yi na yunwa bai dameta ba, ta nemi wuri kawai ta kwanta tana goge hawaye a ɓoye.
***** Fuskarta babu annuri take kallon mutumin, kamar ta fasa ihu ta ce "Wai kana nufin babu abin da ya sauya kenan?"
"Ƙwarai kuwa, komai yana nan yadda yake"
Ta sake tsuke fuska ta ce "Kuma kai babu wani abu da zaka iya yi a kai, gaskiya ba zan iya zuba ido, duk aikin da na yi tuƙuru, kuma ace ba zan mori wahalata ba, ba fa zai yiwu na zama a ƙarƙashin maƙiyana ba"
Yayi murmushi ya ce "Bar ganin mu na kauce hanya, akwai abin da bamu isa mu yi wani abu a kai ba, ko kuma mu canza ba, ke za ki yi duk iya ƙoƙarin da za ki yi, sai mu ga ta ɓangarenmu me za mu iya yi. Amma taurarinta su na da haske sosai, duk wanda ya raɓe ta, za ta iya haska na su tauraron"
Guntun tsaki matar ta ja, ta ce "Ka ga duba mini wani abun, ka bar maganar nan kawai"
Can gida babu wanda ya matsa Nana ta fito ta yi aikin gida, ita ma kuma ba ta yi ba. Sai dai abin da ya ɗaga mata hankali, bai wuce yadda ta ji Baba su na magana da Mama da Gaddafi ba, wai akwai wani mai magani a tsanyawa, idan aljanu suka gagara, har kwantar da mutane yake yi, a tafi a bar shi, sai ya warke ya sallame shi. Babu tunanin komai ta ji Baba ya amince, za a kaita. Rasa abin yi ya sanyata fashewa da kuka.
Sallamar Jamila ce ta sanya ta goge hawayenta.
"Nana ya jikin?"
"Da sauƙi" ta amsa a hankali.
"Ungo wannan naki ne" tayi maganar tana miƙa mata leda.
Ba ta karɓa ba ta ce "Mene ne wannan?"
Jamila ta gyara zama ta ce "Kin tuna ranar da ki ka je kira na, a gidan maman khairat" Nana ta jinjina kai, ba tare da ta yi magana ba.
"Kin tuna matar nan da ki ka gaisar a falo"
"Na tuna"
"To ita ce ta ce a baki, atamfa ce da turaruka, kin san 'yar kasuwa ce"
"Meyasa za ta bani, ta sanni ne?"
Jamila ta ce "A'a ranar da ki ka je ne, ta ga duk kin rikice da kuka gaisa, bayan kin tafi ta tambaye ni ko ta yi miki wani abin ne; na ce mata a'a baki da lafiya ne, shi ne ki ka bata tausayi".
Ita dai Nana ta yi ƙuri da ido, tana kallon Jamila. "Nana ki karɓa mana, ba a mayar da hannun kyauta baya" ta saka hannu ta karɓa ta ce "To na gode sosai" ba dan ta so ta karɓa ɗin ba, ita abubuwan da suka dame ta a yanzu, sun hanata jin daɗin komai na duniya yanzu. Ji take yi tamkar ta kashe kanta ta huta kawai. Kullum cikin addu'a take, babu dare, babu rana, akan Ubangiji Allah ya bata lafiya, sai dai haryanzu Allah bai karɓa mata ba. Wasu lokutan har shagala take da roƙo lahirarta, saboda yadda take fatan lafiya ido rufe, sai dai idan ta tuna ta yi ta istigfari.
*****
Ranar laraba, ta shirya ta tafi makarantar da take koyarwa, sai dai zuwanta ke da wuya, aka sanar mata da director yana son ganinta. Ta san a rina, dan haka ta tsananta addu'a, ta nufi ofishin nasa. Ta tarar da shi tare da wani babban mutum, zaune kirim a kan kujera. Ta gaida mutumin ba tare da ta kalle shi ba, ba kuma ta jira ya amsa ba, ta gaida director. Ɗan ƙaramin yaron da yake zaune a jikin mutumin, ya saukko daga jikinsa, cikin gwarancin yara, ya nufo Nana yana faɗin "Anti Nana" ɗagowa ta yi tana murmushi, dan gaba ɗaya da ta shigo, hankalinta ba a jikinta yake ba, dan haka ba ta lura da yaron ba ma. Ta buɗe hannayenta ta rungume shi.
Director ya ce "Kin ga wannan shaƙuwar taki, da yaran nan ne, ya sanya haryanzu ban sallame ki ba daga makarantar nan. Babu wadda take iya ɗaukar rigimarsu kamar ki, amma ki na ta wasa da damarki. Kwata-kwata yaushe aka dawo makarantar da har za ki yi fashin kwana biyu, ba tare da kin sanar da hukumar makaranta ba?"
Cikin nutsuwarta da kamala ta ce "Dan Allah sir ka yi haƙuri, ba ni da lafiya ne, ba a son raina na yi fashi ba"
A ƙule ya ce "Wai wace irin rashin lafiya ce haka, da kullum ba ki da lafiya, idan ba zaki iya ba, ki ajiye aikin mana dole ne?"
Mutumin da yake zaune ya ce "A'a ba za ayi haka ba, ayi mata uzuri musamman duba da yaranmu suke ƙaunarta. Ka ga ba zuwa makarantar nan nake yi ba, na fi shekara rabon da na zo, amma na san Anty Nana a bakin Muhsin, duk abin da yake yi, idan aka ce za a gaya mata sai ya daina. Ina nema mata afuwa dan Allah"
Director ya ce "Alhaji ba zaka gane ciwon kan da yarinyar nan take bamu ba. She's very hardworking lady, yarinya ce mai ƙoƙari da juriya, amma wannan fashin nata, kullum cikin ciwo shi ne yake ɓata mini rai wallahi"