Buzu book 1 complete - Chapter 6
Buzu book 1 complete Chapter 6: Buzu book 1 complete Chapter 6. YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA 002)
4,469 words
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA 002)
P8
Kallon farko da Nana ta yi wa mai maganin, takaici ya kama ta duƙun-duƙun da shi kamar wakilin sarkin dauɗa. Yana zaune a cikin wasu tarin shirgi da ta rasa ko na uban mene ne. Ɗakin sai azabar ƙauri yake yi, da tsamin wasu abubuwa da ta kasa tantance ko na mene ne. Jikin bangon ɗakin, an zana wasu irin hatimai, kuma an saƙale ƙahunhuna da layoyi. A take zuciyar Nana ta bata wannan mutumin boka ne, ba malami ba, ko kuma malun malun.
Ya ƙare wa Nana kallo, ta kawar da kai ta ƙi kallonsa, Yaya Atine ta gyara zama za ta fara yi masa bayani, ya dakatar da ita, ya ce "Ɗan saurara tukuna Hajiya. Ba ki ga ta kasa haɗa idanu da ni ba? Ai sun zo shegun sun ƙaraso, tare ku ka shigo da su ai, ku na tafe su na biye da ita runduna guda, manya da yara tsofaffi da matasa, yanzu haka kusa da ke ma duk su ne a zazzaune makaran nata, sun cika gurin nan" Yaya Atine ta zabura ta tattare ƙafafuwanta ta ce "Innalillahi. A nan ɗin malam?"
"Eh fa, yi a hankali kar ki hau kan wani"
Nana kuwa waiwaya ta yi, domin ƙara tabattar da a kan wa yake maganar ne?.
Ya gyara zama, ya juya ya ɗaukko wani ruwa, a wata tasa ruwan duk yayi gansa kuka, baƙi ƙirin da shi, ya ɗebo a hannunsa ya watsowa Nana. Take Nana ta ɗan ja da baya, saboda idan wannan ruwan dauɗar ya zuba a hijjabinta jirwaye zai yi.
Ya ce "Kin gani ko, ga su nan za su yi magana, sun ji ruwan azaba, wane su dan uban su. Waye ya zo kanta za ka yi magana ko kuwa?"
Nana ta ɗago kai baki buɗe tana kallon ikon Allah, tana tsoron ta yi wani abin, ya ce Aljanun ne suka zo, kar ta je ya zane ta. Sai dai ta ga idan ba ta yi da gaske ba, sai ya yi mata wanka da ruwan dattin nan, aikuwa ta tashi tsaye ta ja da baya. Yaya Atine ta miƙe da sauri, ta yi baya cike da tsoro da fargaba.
"Ba za ku yi magana ba?" Yayi maganar yana zare mata ido, tare da miƙewa.
Nana ta ce "Wai suwaye za su yi maganar ni ce fa"
Ya ce "Da alama wannan makaran nata, su na da azabar taurin kai, sai an yi aiki tuƙuru a kansu. Yanzu zan yi mata wani ƙaramin aiki, somin taɓi idan kuma da kuɗi a hannunki ki bayar da dubu goma sha biyar, za a sayo turarukan da za ayi mata aikin da su. Ranar Litinin kafin hudowar alfijir, ake yin aikin, za ki kawo mana namijin goro guda bakwai, da zuma farar saƙa, kuma da wuya idan ba sai an yi yanka ba, kin ga sun ƙi magana". Yayi maganar yana ƙarasa sheƙa wa Nana ruwan hannunsa, hakan ya sanya hijjabin Nana, kwanciya a jikinta ya fito da surar da Allah yayi mata. Takaici ya isheta, tun da suka zo, mutumin nan bai ambaci Allah ba, ko ayar Alqur'ani sai shirme da soki burutsu. Warin ruwan da ya zuba mata duk ya cika mata hanci. Kawai ta nufi hanyar fita ta bar ɗakin. Yayi wuf ya riƙo hijjabinta.
A fusace Nana ta juyo ta ce "Meye haka, ka sakar mini hijjabina ba na son haka"
Mutumin ya dubi Yaya Atine da ke zare ido ya ce "Hajiya za su yi magana yanzu, ba ita ba ce ba" Nana ta saka ƙarfinta za ta fizge hijjabinta, ya saka ƙarfinsa ya hankaɗata take ta faɗa kan shirgin da ke cikin ɗakin, wani azababben wari, kamar na ruɓewar wani abu, ya daki hancin Nana, ga ƙume ƙeya da ta yi, wanda gudun kar ta yi ihu, ya sake fakewa da haka ya yi mata wani abun, ya tilasta ta yin shiru. Tana ƙoƙarin ɗagowa, ya shaƙa mata wani abu a hancinta, ta kawar da kanta ba ta sheƙa da yawa ba, amma ta ji wata irin gigitacciyar azaba ta ratsa hancinta zuwa kanta. Ba ta san lokacin da ta kurma ihu ba, jin azabar ta danne mata hanyar fitar numfashi.
Ya kalli Yaya Atine ya ce "Hajiya jeki waje zan yi aikina"
Yaya Atine ta ce "Ka na ganin ba wani abu na je?"
"Eh mana, idan ma kin tsaya babu abin da za ki iya yi, idan ba haka ba idan suka zo fita su shige jikinki" ai cikin azama ta bar ɗakin. Sai da ya leƙa ya tabattar ta bar wurin, sannan ya dawo kan Nana, da take ta layi a ƙasa.
Kan Nana ya yi, yana ƙoƙarin kai hannayensa ƙirjinta duk biyun, ta yinƙura ta juya tana takaicin yadda Yaya Atine ta iya tafiya ta bar ta, daga ita sai wannan zindiƙin mara tsoron Allah.
Ƙoƙarin juyo da ita yayi, yana laluben yadda zai saka hannu a cikin jikinta, tayi wani kyakyawan yinƙuri, ta fizgo wani ƙaho da ke rataye daf da ita, ta raɗa masa a daidai tsakiyar kansa.
Afujajan ya tashi tsaye, yana zazzaro ido, ya gigice saboda yadda ta yi masa dukan a bazata, dan a zatonsa hankalinta ya gushe.
Ya kasa tsayuwa, ya nemi wuri ya zauna, saboda azabar raɗaɗi.
Ta tashi da ƙyar, tana tangaɗi, ya yinƙura ya yi kanta domin hanata fita, kar ta tona masa asiri. Amma ta sake ɗaukan wata ƙwarya wadda take cike da ruwa, yayi baƙi ƙirin saboda tarkacen da yake ciki, ta sheƙa masa a fuska, sannan ta tattara ɗan kuzarin jikinta, ta yi masa ɓarin makauniya da ƙwaryar a fuska sai da ƙwaryar ta ragargaje.
Ganin Nana ta fito tana tangaɗi, ya sanya Yaya Atine tashi ta nufe ta, mutanen wurin na ta yi mata sannu.
"Ke Nana lafiya, ke ce ko aljanun naki ne? Wani mugun kallo ta yi wa Yaya Atine, ta ɗauki takalmanta a hannu ta riƙe.
Yaya Atine ta koma ɗakin mai maganin, ta tarar da shi hanci na zubar da jini. Cikin tashin hankali ta ce "Malam lafiya kuwa?"
"Artabu muka yi da aljanun nata, ba aljanu ne a kanta ba, baƙaƙen iblisai ne, shaiɗan ne da zuriyar sa" ya yi maganar yana shafo jinin da yake fita daga hancinsa.
Sai hankalinta ya rabu biyu, tana ƙoƙarin ta tambaye shi, abin yi, kuma ga hankalinta a kan Nana. Ta koma in da ta bar Nana a tsaye, wanda suke zaune suka ce mata ai ta fita.
Ta fita da sauri, amma ko alamar Nana ba ta gani ba, ta bi hanya tana salati da fatan ba wani wurin ta yi ba. Sai da ta ƙarasa titi, ta hangota zaune a gefen hanya, takalmanta a hanunta tana ta layi.
Su na yin ido huɗu, kafin Atine ta tsallaka, Nana ta tashi ta shige wani adaidaita sahu, ya ja sun tafi.
Salallami da salati, Atine ta hau yi, ta tari wani adaidaita sahun, ta tafi gidansu Nana.
Baba na ganinta a rikice ya ce "Atine yaya dai? Lafiya kuwa?"
"Ina fa lafiya Isa, mu na wurin mai magani, sun yi karambatta da aljanun nata, kawai ta fita ta haye adaidaita sahu, ai na za ta nan ta yo"
Gaddafi da yake wanki, ya ja tsaki ya ce "Wallahi lamarin yarinyar nan har da iskanci, kuma da gangan take ƙin yin auren nan, a kaita gidan mutumin nan da na gaya maka Baba, idan ba gaske ne, idan ma ƙarya take yi duk zai faɗa babu wani aljani da ya gagare shi"
"To yanzu a ina za a ganota?"
Baba ya ce "To wa ya sani, kwanaki fa kwananta biyu ba ta nan, sai daga baya suka zo da Ummi, wai kawai ganinta ta yi a gidanta, idan ma da gaske take, idan ma ƙarya suke yi oho musu. Ni wallahi na gaji da sabgar yarinyar nan shi yasa nake Alla-Alla a samu mai so ya aura na huta. Kuma ga wannan ƙanin mijin Ummi ta tsaya tana iyayi"
Babu tsammani, sai ga Nana ta shigo, Jamila ta riƙota tana ta tangaɗi, da takalmanta a hannu.
Gaba ɗaya suka yi kan Jamila da tambaya "A ina ki ka ganta?"
"Gidan maman khairat zan je, kawai na hangota tana ta tangaɗi kamar ma ta kasa gane hanyar gida ne"
Mama da take ɗaki, tana jin su, sai yanzu ta yi but ta fito ta ce "Jamila, ban hana ki naniƙar yarinyar nan ba, sai kin kwashi masifa da bala'i"
Atine ta ce "To 'yar nema, da ki na jin duk abin da ake yi, ki ka ƙule a ɗaki?"
Mama ta ce "Ya shafe ni ne da zan fito, ba zaki cikata ba?"
"Mama faɗuwa za ta yi fa idan na cikata"
"Dan ubanki ki rabu da ita aka ce, duk ranar da ta ji miki rauni, ta sabauta ki ai kya shiga hankalinki" Gaddafi ya yi maganar cikin ɗaga murya.
Duk da abin da mai maganin nan, ya shaƙa wa Nana, bai gama sakinta ba, amma tana jin duk abin da suke faɗa. Ta zame hannunta daga jikin Jamila, ta dafa bango ta nufi ɗakinsu. Tana jin Baba yana tambayar ta, dan me ta baro wurin mai magani, tayi masa shiru dan ko buɗe baki, wahala yake yi mata balle doguwar magana. Tana jin yadda Yaya Atine ta cafe, take yi masa bayanin, bataliyar aljanun da ke kan Nana, har da ƙara abin da ba a yi ba, kamar yadda mai maganin yayi mata bayani.
Tun tana jin su sama, har wani abu mai kama da bacci ya ɗauketa. Kamar a zahiri ta daina jin komai a duniyar da take ciki, ya zauna a gabanta yana kallonta, kafin ya ƙyaƙyace da dariya wani irin baƙin hayaƙi yana fita daga bakinsa. Sam dariyar babu daɗin ji, ta saka hannu ta toshe kunnuwanta, amma ba ta fasa jin dariyar ba.
"Igiyar ƙaddara, ta ɗaure ki ta ko ina, kuma kina da damar kwanceta, amma azabar baƙin taurin kanki, ya hana ki saduda ki karɓi ƙaddararki"
Nana ta numfasa ta ce "Shirka ba ta cikin ƙaddarata, komai za ka yi mini, ba zan karɓi abin da ka ke buƙata na yi ba" Ya ɗago dogwayen yatsunsa, ya kai fuskarta ya lakuto gumin da take ta yi, ya kalli gumin a hannunsa ya ce "Ki daina cika baki, lokaci zai fayyace komai" Daga haka ya ɓacewa ganin Nana.
Bayan farkawar Nana, ta tashi da wata azababbiyar yunwa, ga sallolin da ake bin ta. Ta tarar da Ummi ta zo, ta gaisheta amma ta amsa mata sama-sama. Ba a damu ba, ta yi sallolinta ta koma tsakar gida ta ce "Mama akwai abinci kuwa?"
"Babu" ta bata amsa kai tsaye.
Ummi ta ce "Mhmm Nana kenan, ai in dai irin wannan abubuwan ne, yanzu ki ka fara gani, tun da zaman gidan bai ishe ki ba, shi wancan na farkon Allah bai ƙaddara an yi da shi ba. Shi malamin naku an ce ya fito yaƙi, amma duk da larurarki, Saleh ya ce yana sonki amma sai wulaƙanci ki ke yi masa. Ya je ai ya gaya mini duk abin da ki ka yi masa"
Nana ta yi kunnen uwar shegu da Ummi, kamar ba da ita take ba.
"Mun yi magana da Baba, aure babu fashi, ya ce a gaya masa iyayensa su turo"
Nana ta kalli Ummi ta ce "Yanzu za ki so hafsa ta auri mutum irin Saleh? Kin san fa ɗan shaye-shaye ne, kuma a Lagos ɗin kin san ina ne wurin sana'arsa da suwa yake tare? Duk ba kwa duba mini wannan?"
"Nana ke ma fa kina da aibun nan, amma ya runtse ido ya ce ya ji ya gani, ita fa rayuwa yanzu idan ki ka samu mai sonki, duk wani tone-tone ba naki ba ne ba" ba ta sake kula Ummi ba, har ta gama abin da za ta yi ta bar gidan.
Tunanin yadda Allah ya ƙwaceta daga hannun mai maganin ɗazu take yi, da tuni ya cuceta ya cuci rayuwarta, ita kanta ta san Allah ne kawai ya ƙwaceta, amma ya riga ya bugar da ita. 'wataƙila ga in da addu'oinki suke yi miki amfani, amma ki ke garaje da ɓacin rai' wata zuciyar ta tunatar da ita, a take ta yi ta istigfari.
Sosai Baba ya ɗauki maganar Saleh da muhimmanci, Nana kuma ta na ta kai kukanta ga Allah, duk da neman lafiya da take roƙa ya rinjayi duk sauran adduo'in da take yi.
Gashi duk da shirun da take yi wa Saleh idan ya zo, ba ya zuciya sai ya kuma dawowa, dan babban abin da yake saka shi zuwa ba yau ba gobe, bai wuce tozali da ƙirar jikin Nana ba, da yake jin kamar zai ɗimauce, idan bai kai hannunsa jikinta ba. Ta kan ƙare masa kallo, tana mamakin yadda Baba ya rintse ido, daga ganin aibun Saleh, kama daga kan askin banzar da yake kansa, zuwa suturar da yake sakawa da sunan gayu. Kodayake dama gayu idan ya haɗu da jahilci hauka ne tuburan, duk soki burutsun da zai yi mata babu maganar Allah a ciki sai shirmensa.
Gefe guda ga kewar malam Auwal da ta dameta, tabbas ba dan mutunci da kamewarta, na ɗiya mace ba da babu abin da zai hanata zuwa gidansu ta tuntuɓi ko lafiyarsa ƙalau. Sai dai duk da haka sai da ta tambayi abokinsa malam Nura, ya tabbatar mata da lafiyarsa ƙalau ayyuka ne su ka yi masa yawa kawai.
Kimanin makwanni biyu kenan, ba ta ga malam Auwal ba, zuciyarta na raya mata, karɓar lambarsa a wurin malam Nura, ta ari waya ta kira shi, amma ta kasa. Kwatsam su na cikin karatu a aji, ta jiyo muryarsa a waje. Ta kasa riƙe kanta, ta tashi ta fita.
Kafin ta isa, har ya shiga cikin ofishinsa, yana cikin tattara litattafansa, kawai ya waiwayo ya ga Nana.
"Yaya Auwal meyasa ka ke guduna? Ina ta son mu haɗu na yi maka bayani, amma ka daina zuwa ma gaba ɗaya"
"Babu malami a ajinku ne?"
"Eh, tilawa muke yi"
"Ki koma aji" ya bata amsa ba tare da ya kalle ta ba.
Ta marairaice ta ce "Amma Yaya Auwal, magana nake son mu yi, dan Allah ka fahimce ni ba abin da ka gani, ba abin da ka ke tunani ba ne...
"Ki tafi aji na ce Nana, ba sai kin yi mini bayanin komai ba" yayi maganar cikin tsawa.
Tsayawa ta yi tana kallonsa, bayan tayi nasara sun haɗa ido.
A hankali ta sauke ajiyar zuciya, ba ta tafi ba kuma ba ta ce komai ba, sai dai idonta ya cika da hawaye.
Sai ya tausasa murya ya ce "Ki je aji Nana, ba na son gardama"
Ta girgiza kai ta ce "Koma me ka ke ɓoye mini ka gaya mini. Kai malamina ne, kuma abin koyi na, ka karantar da ni nagartattun halayen fiyayyen halitta Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam. Wanda ya haɗa da gaskiya, da kuma haƙuri. Ka gaya mini ko ma mene ne a ranka dan Allah"
Jiki a sanyaye ya ɗan sunkuyar da kansa, sannan ya kalle ta ya ce "Nana kin san komai nufi ne na Allah, maganar aure tsakanina da ke, ba zai yiwu ba yanzu haka Qatar zan tafi da wani ɗan ƙanƙanin lokaci"
Murmushi ta yi, duk da hawayen da ya cika mata ido, ta ce "Ko kai fa, ka ga yanzu da ka gaya mini gaskiya zan fi samun nutsuwa sosai da sosai. Ina yi maka fatan alkhairi amma dan Allah ka ci gaba da yi mini addu'a, na san larurata ce ta saka ka fasa aurena, ka yi mini addu'a Allah ya bani wanda zai iya aurena da larurata a haka"
"A'a Nana, idan baki manta ba, tausayinki da halin da ki ke ciki, ya sanya na ce zan aure ki, ban ƙi auren ki saboda larurar ki ba"
Ta share hawayenta ta ce "Eh, da fari tausayina, daga baya ka koma so na, dama na san zaka rabu da ni, dama na fi so na ji daga bakin ka ne, tun lokacin da aka ce ba zaka iya riƙe aure ba, na ga komai a bacci, har rabuwar nan tamu na yi mafarki na gani, ba zaka aure ni ba. Hakan ba ya nufin zan manta tarin alkhairin ka a gare ni, Ubangiji Allah ya baka mace ta gari lafiyayyiya"
Zai yi magana ta girgiza kai, ta fice daga ofishin, zuciyarta na zafi hawayen da take ƙoƙarin dannewa, su ka ƙi dannuwa.
Auwal bai taɓa tunanin yana son Nana har haka ba, sai da Umma ta hana shi aurenta, kuma abin bai tsaya a nan ba, sai da Umma suka tura shi Qatar.
Nana ta tafi rijiya, ta ɗebi ruwa ta wanke fuskarta, sannan ta koma ajinsu aka ci gaba da tilawa da ita.
Sosai rabuwa da Auwal ya shigi Nana, duk da ta yi mafarkin hakan, amma ba ta bari ta gasgata hakan ba.
Har aka tashi daga makaranta, hankalinta ba ya kan abin da aka ƙara musu sam.
Da daddare, bacci ya gagari idanun Nana, sai tunani da zancen zuci, ya din ga ziyartar zuciyarta, har ta rasa wane tunani ya kamata ta yi.
Jamila ce ta zo da abinci daga gidan maman khairat, ta cewa Nana ta tashi ta ci, amma ta ƙi. Sai da ta takura mata, sannan ta ci kaɗan, ta sha lemon ta kwanta, sai dai abincin ya tsaya mata yaƙi wucewa.
Tana daga kwance, tiryan-tiryan, yadda aka fasa aurenta na farko ya dawo mata, yadda take samari, su na tafiya, duk da galibi mutanen banza ne suke bibiyarta. Amma Suleiman ya zo da gaske zai aure ta. Sai dai Baba ya din ga zubar mata da mutunci a idonsa, ta hanyar roƙe-roƙen kuɗi, kuma wani abin mama ce take ziga shi yake yi, har ita ma wasu lokutan sai ta tura ta ce ya bata kuɗi, sun wuni ba su ci abinci ba. Tun yana bayarwa da marmari, har ya gaji ya fara mita. Ya san da Nana ba ta da cikakkiyar lafiya, duk da a lokacin abin ya lafa, amma mama ta zaunar da shi, ta din ga karanta masa Nana aljanu har sun fara haukata ta. Matarsa ta zo har gida ta ci mutuncin Nana, har da an gaya musu babarta ce take biye-biyen bokaye, abin ya koma kanta take fama da aljanu. Duk da dama Mama ta saba faɗar wannan maganar, idan ta so cin mutuncinta, amma abin yayi mata zafi ya mata ciwo. Wuni ta yi tana kuka, Suleiman da kansa ya je gida ya ba wa Nana haƙuri, bayan ya samu labarin abin da matarsa ta zo ta yi mata, sai dai tun da matar ta koma gida, ya aka rasa gane kanta, ta kwanta rashin lafiya. Ta din ga fama da matsanancin ciwon kai, idan ta fara sai ta fita hayyacinta ko gani ba ta iya yi, suka je asibiti ba a ga komai ba. Ya koma gidansu Nana, ya ce idan ta san wani abu ta yi wa matarsa, ta bari uwar 'ya'yansa ce, ba zai so lafiyarta ta taɓu ba, tun da ai ya zo ya bata haƙuri. Nana ta din ga rantse-rantsen ita babu abin da ta yi mata, ƙarshe dai matar kamar za ta haukace, ya zo ya ce a dawo masa da kayan aurensa, tun a waje Nana ta cutar da iyalinsa, ina ga idan ya aureta, dama kuma an ce masa mahaifiyarta na biye-biye. Duk yadda Nana take son ta yi aure, ko dan saboda tarin ƙalubalen da take fuskanta, amma fasa aurenta da Suleiman bai wani dame ta ba, domin tana fargaba mussaman yadda aka gama zubar mata da mutunci a wurinsa. Ajiyar zuciya ta sauke da ta zo nan a tunaninta, sai da kanta ya sara, ta sauke ajiyar zuciya. Ga abubuwa da dama su na cin zuciyarta, tana buƙatar abokin shawara da tattaunawa, amma rashin yardarta bai sanya ta bawa wani damar, hakan a rayuwarta ba. Mutanen da suka cancanci hakan a rayuwarta duk ba ta ita suke yi ba. Babbar damuwarta a yanzu, bai wuce yadda ta san ko ba ta so, Baba sai ya ƙaƙaba mata Saleh ba, dan ta fuskanci zamanta ne kawai ba a so cikin gidan, duk ga su Suwaiba da Jamila, su babu wanda yake takura musu a kan aure sai ita. Sosai take jin zafin rashin Auwal, ko ba komai mutum ne ma'abocin Alqur'ani da kuma riƙo da addini, ta san abu ne mawuyaci a iya cutar da shi, ta sanya ran idan tana tare da shi, za ta samu sauƙin wasu abubuwan.
"Ke baiwar Allah" ta ji an kirata. Ta ɗaga kai, ta hangi wata mata bararoji a tsaye, ta yi kwalliya da tarin tsummokara, da wasu irin tarin sarƙoƙi na zare a wuyanta, da ƙullin kaya a hannunta, ta burtso da gashin ta gaban goshin ta. Nana ta ɗaga kai ta ganta a wani wuri, da ba ta san ina ne ba.
Matar ta ce "Zo na baki magani"
Nana ta ce "magani kuma, na me?"
Matar ta sauke mayafin da ta rufe fuskarta, ko ina tsagu ne a fuskarta, har baka iya tantance kamaninta, saboda azabar billayen da ke fuskarta.
Matar ta ciro wani magani a cikin, ƙullin kayanta ta ce "Ki zuba a tafin hannunki, ki lashe"
Nana ta ce "To ai ba ki gaya mini na mene ne ba?"
"Idan ka sha, ba zaki ganin Ƙaisar ba, zai daina bibiyar ki yana takura wa rayuwarki, zai rabu da ke har gaban abada. Dukkanin damuwar ki za ta kau, babu wanda zai sake zuwa auren ki, yayi nasarar korarsa ko ya saka miki wani ciwo. Dan yan daf da fara kashe mutane, domin wata ƙungiyar asiri ce suke nemansa ido rufe yayi musu aiki. Idan suka sadaukar masa da jini, zai fara kisan mutane ne, kuma zai fara da mutane mafi soyuwa a gare ki"
Jiki na rawa Nana ta miƙa mata hannu, domin karɓar maganin.
Matar ta yi murmushi, haƙoranta suka bayyana baƙaƙe ƙirin da su, ta kama tafin hannun Nana, ta zuba mata maganin, da yawa. Tana kama hannunta, Nana, ta ji tamkar an zare mata lakar jikinta, jikinta yayi wani irin sanyi, da ta kasa ko ƙwaƙwƙwaran motsi. Ta kai garin maganin bakinta ta fara sha...
Ayshercool 08081012143
BUZU
AISHA ADAM AYSHERCOOL
YOTA/002
P9
Ko da Nana ta sake lasar maganin, sai ta ga fuskar matar tana komawa baƙa ƙirin, tana ta fito da dogon harshe, tamkar na macijiya, wani abu mara kyan gani na futa daga bakin nata. Iya ƙarfinta Nana take son ta yi addu'a, idan mafarki take ta farka, amma ta ji tamkar an saka dutse an tokare maƙogwaronta zuwa huhunta.
Babu tsammani, ta ga wata irin guguwa ta haɗu, Ƙaisar ya bayyana a tsakaninsu yayi wani irin mugun cilli da matar a gefe. Yayo kan Nana, ya zubar da sauran maganin hannunta, ya shaƙe mata wuya. Wani irin kakari ta din ga yi, ta na amai dunƙunlen jini yana fitowa ta hancinta da bakinta. Ji ta yi numfashinta na neman ɗaukewa.
Ita ma Nanan, ya yi jifa da ita gefe, ta riƙe wuyanta tana numfashi da ƙyar.
Ya kalle ta a zafafe ya ce "Idan ki ka ci gaba da irin wannan gangancin, za a kashe ki a haka, babu wani mahaluki da zai iya raba ni da ke. Guba ta baki za ta kai jininki ayi tsafi da ke saboda tasirin taurarinki. babu wanda zai iya baki wani magani ya raba ki da ni, idan ki ka ci gaba da yinƙurin rabuwa da ni, za ki kashe kan ki da kan ki" yana maganar tartsatsin wuta na fitowa daga jikinsa, yana ƙona Nana.
A hankali ta buɗe idonta, ta ganta a kan shimfiɗarta, ta takure jikinta yana ta rawa, numfashinta yana fita da kyar. Wuyanta sai raɗaɗi yake yi mata, haka ma jikinta.
Ta kai hannu ta ɗauki fitilarta ta kunna, tana haska ɗakin, ba kowa a ɗakin sai ita kaɗai. Jikinta ya ba ta wani abin tayi, su Jamila suka gudu suka bar ta a ɗakin.
Ta yinƙura da azama ta tashi tsaye, amma jikinta sai raɗaɗi yake mata, kafaɗunta kamar ba a jikinta suke ba.
Ayatul kursiyyu ta din ga karantawa, ta fita ta ɗauki buta, ta shiga banɗaki. Tana fara fitsari ta ji ƙarnin jini, tana dubawa ta ga fitsarin jawur, jini a maimakon fitsari. Gashi ko kwana bakwai ba ta yi da gama al'ada ba. Ta wanke jikinta tayi alwala, ta koma ɗaki, gaba ɗaya ta kasa yadda har yanzu ba a cikin mafarki take ba.
Da safe ta fito ta yi aikace-aikace da za ta yi, Jamila ta ce "Nana me ya same ki haka?"
"A ina?"
"Jiya da daddare ki na ta kakarin amai, ki na kuka a bacci, yanzu kuma kalli jikinki, kamar an zane ki da bulala" Baba da ya fito daga banɗaki, shi ma ya kalli Nana.
Jikinta duk kwanciyar bulala, gashi ta ɗashe ta yi haske, kamar mara jini a jiki.
Nana ta kalli jikinta, ta ɗan taɓe baki ba ta ce komai ba, ta ɗebi ruwa ta shiga banɗaki domin yin wanka. Sai dai wannan karon ma, fitsarinta jini ne kawai yake zuba. Kawai ta jingina da jikin banɗakin, ta fashe da kuka, sai da ta yi mai isarta sannan ta ta fara yin wankan. Sai dai tana zuba ruwan a jikinta, ta ji kamar fatarta za ta zazzago, jikinta ya hau kyarma. Duk da a cikin banɗaki ta yi, haka ta furta a'uzubillah, ta cigaba da zuba ruwan a jikinta tana wanka, har ta kammala ta fito. Ta yi alwala, ta shiga ɗaki ta shirya, tana kallon Baba yana kallonta, amma ba ta gaishe shi ba, haka kurum ta tashi da matsanancin ɓacin rai, ko ganin Baban ba ta son yi.
Ba ta kula kowa ba, ta fice ta tafi makaranta.
Gaba ɗaya jikinta ciwo yake yi mata, ga jiri tana fama, dan haka a cikin aji ta yi zamanta, ta kifa kanta a kan tebur, tana ta kewar rashin Auwal.
***** "Safiyya"
"Na'am Hajjaju"
"Yaya kin yi magana da Jamila kuwa?"
"A'a yanzu dai nake saka ran zuwanta"
"Dan Allah, ki ɗan bugi cikinta ki ji, yarinyar nan ta sha lemon kuwa?"
Maman khairat ta ce "In sha Allah, zan bugi cikinta zamu yi magana da ita"
"Amma ina fatan, ba ki gaya mata ko na mene ne ba"
"A'a haba Hajiya, ya ma za ayi na gaya mata, ai kin ce ko wani ma ya ci ba komai, ita ɗin dai ake so ta ci, zan tambaye ta idan ta zo"
"To shikenan, na gode sai na ji ki"
*****
Ƙamshin turare ne ya cika wa Nana hanci, sai dai ba ta motsa ba ko ta buɗe idanunta ba. Teburin da take kai, ya ɗan bubbuga, sai a lokacin ta buɗe idonta a hankali. Dishi-dishi ta fara gani.
A hankali idonta ya washe, ta ɗaga kai ta kalle shi.