Buzu book 2 complete - Chapter 24
Buzu book 2 complete Chapter 24: Buzu book 2 complete Chapter 24. "Amin, a hakan ma gaskiya kina da sa'a sosai da sosai, sai da muka kawo musu mata uku, da…
3,338 words
"Amin, a hakan ma gaskiya kina da sa'a sosai da sosai, sai da muka kawo musu mata uku, da ƙyar suka ɗauki ɗaya, wai duk ba su yi musu ba, wasu kuma sai an zo yi musu gwaji sai su faɗi. Amma ke ya ce ba zai yi miki ma gwaji ba, kawai an ɗauke ki aikin. Abin da zan gaya miki kawai shi ne ki kula, ki kula da kanki sosai da sosai, banda ƙazanta banda son jiki. Sannan kar ki ga kin tsallake wannan matakin, ya ɗauke ki aiki a haka cikin sauƙi, ki zata miƙe ƙafa za ki yi, mace ce mai gurin nan, kuskure kaɗan za ki ta ci mutuncinki ta kore ki. Su kan su ma'aikatan kwantar da kai suke yi, su na yi mata biyayya, duk wata tijara da bala'inta kawai ki toshe kunnenki ki yi haƙuri." Nana ta yi shiru, sai da Hansatu ta gama gaba ɗaya sannan ta numfasa ta ce "To Ubangiji Allah ya iya mana"
Hansatu ta amsa da "Yauwwa Amin"
Hakanan Nana ta ji a jikinta, ba za ta ɗauki wulaƙanci da cin zarafi ba, duk da kuwa abin da take son cimma. Ko Nene da ake kambama faɗanta da masifarta, ba ta cin mutunci, kuma duk abin da za ta yi faɗa a kai, to a kan gaskiya ne. Amm yanayin yadda Hansatu take yi mata bayanin mai gurin nan, a kaikaice dai ba ta san darajar mutane ba.
Ɗakin da Nana take, ita da wasu Zabarmawa ne guda biyu. Ta yi alwala ta yi sallar Azahar. Ta daɗe a kan abin salla, tana gaya wa Allah, cikin magiya a kan ya sanya ta samu abin da ta fito nema, ya kuma raba ta da duk wani sharri da abin ƙi. Bayan ta idar, ɗaya daga cikin 'yan ɗakin, ta ce mata ta zo su je ta zagaya da ita. Can ɓangaren da ake girke-girken ta kai Nana, suka zagaya daga nan ta kaita cikin gurin da ake sayar da abincin. Nana ta yi mamakin girman gurin, da yadda gurin Abincin yake da tarin kwastomomi. Sai dai da gani ka san na manya ne, dan duk waɗanda suke zuwa gurin cin abinci akwai alamun abin hannu a tattare da su.
*****
Ɓangaren su Shukura cikin jikinta ya tsufa sosai, sai dai a wannan karon ta dage fafur ta ƙi yin awo a Asibitin su Doctor Sharif. Gefe Sagir ya jewa mahaifiyarsa, da maganar son dawo da Yusra, amma ta ce ba ta lamunta ba, ba ta buƙatar ya sake rayuwa da Yusra, gara yaje ya auro wata can daban, amma ba Yusra ba. Gaba ɗaya ya shiga damuwa, saboda mugun sabo da shaƙuwar da ya kuma yi da Yusra. Ita ma Hajiya Halima tun da ta samu labarin, Sagir ne tsohon mijin Yusra yake zuwa gurinta, ta din ga bala'i ta ce ko shi ne autan maza, Yusra ba za ta koma hannunsa ba, balle a sake ci mata mutunci a sako ta. Ga shi daga shi har ita su na son junansu. Dan haka ya yanke shawarar tafiya gurin ƙanin mahaifinsa ya yi masa magana. Shi kuma ya kira Hajiya Halima ya din ga yi mata faɗan dan me za ta hana shi mayar da matarsa alhalin sulhu alkhairi ne, wancan karon da auren ya mutu ma, gutsuri tsomarsu ce ta kashe Auren. Mussaman ta kira Sagir gida, ds ya je ya same ta, ta dirarar masa da bala'i. "Wato ƙarata ka je ka kai wa ƙanin ubanka saboda mace ko Sagir?"
Ya girgiza kai ya ce "A'a Hajiya ba ƙararki na kai ba"
"Rufen baki ko na make ka, ba ƙarata ka kai ba ya kira ni yana faɗa? Tun da abin da ka zaɓa kenan, ka je ka yi duk abin da ka ga dama" Kalaman na Hajiya, tamkar ɗsure shi ne da jijiyoyin jikinsa, gaba ɗaya ya rasa abin da yake yi masa daɗi ba ya son ya yi abin da daga baya zai zo yana dana sani, saboda rashin amincewar Hajiyarsa.
**** Daren yau sam Nana ba ta samu isasshen bacci ba, da yake sai washegari aka ce za ta fara aikin, ba ta yi aikin komai ba ranar. Raba dare ta yi tana nafilfili addu'oi, saboda a jikinta tana jin wani abu game da gurin, wanda ta kasa tantance ko mene ne. Washegari da safe, suka shirya ita da 'yan ɗakinsu, suka tafi gurin aikin Abincin. Kayan girki ne ga su nan a zube, kamar abin banza, yanayin yadda aka jibge kayan a gurin, Nana ta sha jinin jikinta, ta san aiki ne tuƙuru za a yi shi gurin. Aka ba su jadawalin abinccicikan da za a girka a ranar, Nana ta san wasu, wasu kuma ba ta san su ba. Su na nan tsaye shugabar ɓangaren na ƙara yi wa Nana bayani, da gurɓatacciyar hausarta, sai ga mutumin jiya shigo. Gaba ɗaya suka wani ruɗe, masu gyara tsayuwa na yi, masu kama aiki suna yi, Nana dai ta ƙame a gurin da take. Ba yabo ba fallasa ya din ga amsa gaisuwar da ake yi masa, sai da ya zo kan Nana ya saki murmushi ya ce "Baƙuwarmu, ya ki ka ga gurin namu, ba dai wata matsala ko?" Nana ta girgiza kai ta ce "Babu matsala"
Ya ce "Yauwwa, ki saki jiki ki yi aikinki da mu, kamar kina Nigeria, duk abin da ba ki gane ba, ga shugabar sashin nan, idan kuma ba haka ba ni ki zo ki same ni ki yi mini magana" Ta jinjina kai ta ce "To in sha Allah, na gode sosai da sosai"
Ya kalli matar ya ce "Dan Allah kar a ce za a sakar mata aiki lokaci ɗaya, a koya mata abin da ta sani ba a hankali, kafin a sakar mata aiki"
Matar ta risuna ta ce "In sha Allah, amma za a yi mata gwajin ne ita ma?"
"Kin ji na ambaci hakan ne, a maganata?"
Ta girgiza kai ta ce "Tuba nake"
Ya ce "'Yar Nigeria, a yi aiki lafiya"
"Na gode sosai" Nana ta yi maganar cikin girmamawa. Ya wuce ya fita. Bayan ya fita suka juya yare, suka ɗan yi maganganu, sai dai duk da Nana ba ta jin yaren nasu, ta san gulmarta suke yi. Suna aiki amma gaba ɗaya hankalin Nana ba a kan aikin yake ba, yana kan halin da Sabir yake ciki. Tana ta tunani yaya yake? Yana rigima ko kuwa bai damu ba ya kwantar hankalinsa, haka ta yi ta wasi-wasi a zuciyarta.
***** Hajiya Amina ce ta yi shirin tafiya Umara, ta tsaya a Egypt za ta kwana biyu, ta tsaya a ɗan binciki lafiyarta. Sai dai ta din ga ji a ranta, yakamata a ƙara bincika mata matsalarta ta rashin haihuwa, mussaman da take tuna maganganun Nana. Sai dai gefe guda tana tuna yadda Alhaji Zailani yake gargaɗinta a kan shi ya fauwwala wa Allah, bai damu lallai sai ta haihu ba, tun da an nemi magani ba a dace ba. Sai dai a wannan karon, ta sake jin tana son jarraba da bibiyar lafiyarta, da ganin likita, ko za a dace, tun da ba ta daina al'ada ba ma. Da harshen turanci suka tattauna da Likitan, ta yi masa bayani, ya rubuta mata gwaje-gwaje ya ce ta je ta yi, ciki har da hoto. Kasancewar komai na su ba kamar na ƙasarmu ba, cikin ƙanƙanin lokaci aka yi duk gwaje-gwajen, aka tura wa Likitan sakamakon. Bayan ta koma gurin Likitan ya duba na'ura mai ƙwaƙwalwarsa, ya kalli Hajiya Halima ya ce mata "Sakamakon hoton da aka yi mata, ya nuna babu mahaifa a jikinta gaba ɗaya" wata irin ƙara cikinta yayi, zuciyarta ta buga a jejjere da ƙarfin gaske, sai ta hau kame-kame tana tunanin, ko kunnuwanta ba su ji daidai ba? Ko kuma turancin nata ne ya ƙwace.
Cikin rawar murya ta ce "Ka tabattar da abin da ka gaya mini, ko kuma nice ban fahimta ba?"
Ya ce "Na tabattar, shi ne sakamakon gwajin da aka turo mini, amma idan ba ki yadda da sakamakon ba, kina iya zuwa wani Asibitin a sake duba ki!.
Yammm ta ji kanta yana yi, ta daina gane komai, hankalinta ya rarrabu kashi-kashi, tana son yi wa likitan tarin tambayoyi amma kanta ya kulle. Shin da gaske ana iya samun mace babu mahaifa, ko kuma wani abin ne daban? Ya aka yi duk tsawon lokacin da ta ɗauka tana bulayin neman haihuwa ba a taɓa gaya mata ba ta da mahaifa ba sai yanzu?.
Gaba ɗaya Hajiya Amina, ta rasa kalmomin da za ta tattaro ta sake furta wani abu. Jikinta rawa kawai yake yi, wani irin gumi yana tsatstsafowa ta kowace kafa ta gashin jikinta. Likitan ya ci gaba da yi mata bayani, amma ta kasa fahimta. Ba ta san ma da ya aka yi ta bar Asibitin ba, ta koma masaukinta saboda tsabar ɗimuwa. Ta kuma rasa wa za ta kira ta sanarwa wannan maganar. Gaba ɗaya kanta ya juye, dan ba ta ma iya tuna yadda su ka ƙarƙare da Likitan ba. Tana so ta zubar da hawaye, ta ji sanyi a ranta, amma abu ya gagara idanunta suka bushe zuciyarta ta yi nauyi. Babbar tambayarta ita ce, dama ana iya samun macen da ba ta da mahaifa? Ko kuwa ta ta ce ta yi ɓatan dabo?. Tambayar da ta rasa wa za ta yi wa, balle a ba ta amsa.
*****
Nana kuwa gurin nan aiki ake yi tamkar babu gobe, duk da ba ta da son jiki, amma aikin yana da yawa ga babu isasshen hutu, sai aikin ɗorawa da saukewa. Ga shi ta kasa sakin jiki da ma'aikatan gurin, saboda yadda suke tsangwamarta, da nuna mata ƙabilanci, saboda ita ba 'yar ƙasar su ba ce ba. Sam ba sa gaban Nana, duk da tana ɗan saka ido ta ga, ko akwai wata mai hankali da za ta ji ta yarda da ita, a kaikaice ta ɗan fara ƙwanƙwasa cigiyar Sayyid. Sai dai gaba ɗaya ba su yi mata ba ma'aikatan gurin, gaba ɗaya ba ta ji ta aminta da ko mutum ɗaya daga cikin su ba. Kullum da safe Al hussain, mutumin da ya ɗauke ta aiki, sai ya zagaya su ya ga yadda suke gudanar da aikin safe da yamma. Da ya zo ma'aikatan suke nutsuwa, kowa ce ta kame kanta, marasa kamun kai kuma su fara ɗan karairaya. Shi kuma ya tsuke fuska yana basarwa. Sai dai da ya ga Nana sai ya saki fuska, ko ba ta kula shi ba, shi sai ya yi mata magana.
"'yar Nigeria ya alƙawarinmu ne?"
Nana ta ɗan saki fuska ta ce "Wanne?"
"Au har kin manta?"
Ta yi murmushi ta ce "Duk lokacin da ka shirya, sai mu fara"
Ya ce "Kin san akwai wani abokina, sonake kafin na haɗu da shi, ko gaisuwa na iya da turanci, saboda ya iya turanci ni ban iya ba, ya juya yare ya yi ta magana ba na gane me yake cewa, to kin ga yakamata na ba shi mamaki nima"
Nana ta ce "Gaskiya ne, shi ma Buzu ne kamar ka?"
Al Hussain ya ce "Ya aka yi ki ka san ni Buzu ne?"
"Ga rawani nan ka na yi" ya yi dariya ya ce "Kash, to shikenan tun da kin gane, shi ma buzu ne, mun kwana biyu ma bamu haɗu ba, ban je Agadez ba"
"Duk Buzaye a Agadez ku ke?"
Ya girgiza kai ya ce "A'a, sai dai mun fi yawa a can, ko kina son zuwa ne? Mu na da wani gurin Abincin ma a can, babban wannan sai a mayar da ke can" Nana ta girgiza kai ta ce "A'a tamabaya dai kawai na yi"
Ya jinjina kan ya ce "To yaya aikin?"
"Alhamdillah"
"To ma sha Allah, Allah ya taimaka"
Tun da suka fara hirar nan, Nana ta lura da irin kallon da ake yi mata, saboda ya tsaya sun yi hira. Sai dai ita ba kallon ne ya dame ta ba, a jikinta take jin sam ba ta kyauta ba, tsayawa da ta yi tana magana da Al Hussain har take yi masa murmushi ba, saboda ta san da Sayyid yana gurin, ko da makamancin wasa ba za ta taɓa aikata hakan ba, saboda yadda yake tsananin kishinta. A hankali ta ce "Ka yi haƙuri Sayyid, babu yadda na iya ne, duk a ƙoƙarina na son zuwa gare ka ne, ka yi mini afuwa" ta furta a hankali kamar mai raɗa.
"Nana wai a ina ki ka san Al Hussain ne?"
Nana ta ɗaga kai ta kalli Shugabar gurin nasu, da take yi mata tamabaya cike da tuhuma. Kamar Nana ba za ta yi magana ba, sai kuma ta ce "Waye hakan?"
Matar ta ce "Kamar yaya?"
Nana ta ce "Wanda ki ke tambayata"
Gaba ɗaya suka kalli Nana, jin yadda take bawa Adama, shugabar ɗakin girki. Ita kuwa Nana ko a jikinta da irin amsar da ta bawa Adaman.
Cike da takaici Adama ta ce"Mutumin da ya fita yanzu"
Nana ta ce "Au sunansa kenan dama? A nan Nijar na san shi, meyafaru?" Ta yi maganar tana tsare Adama da ido, tana jiran abin da za ta sake cewa. Sai dai ta yi shiru ba ta kuma magana ba, su kuma suka hau mamakin irin amsar da Nana ta bata, kuma ba ta iya ce mata komai ba. Gaba ɗaya Nana hankalinta ya koma kan sauran kwanaki nawa ta koma gida, duk da kullum sai ta yi waya da Nene. Amma ta ga kamar kwanakin ba sa matsawa sam.
**** Hajiya Amina revers ta yi, ta dawo gida Nigeria, saboda kiɗima da tashin hankali da take ciki, ta rasa wanda za ta fara tunkara da maganar. Ta so samun mijin Alhaji Zailani a waya, ta fara yi masa bayani, amma ba ta same shi a waya ba. Ta koma gida a kiɗime, amma ta tarar da saƙon ya yi balaguro zuwa Abuja.
Jikinta na rawa ta kira Doctor Sharif, ya ɗaga yana faɗin "Hajjaju barka da yamma"
"Sharif abu zan tambaye ka dan Allah"
Gabansa ya faɗi, saboda yadda ya ji muryarta cike da tsoro da kuma damuwa.
"Hajiya lafiya dai?"
"Lafiya ƙalau, tambaya zan yi maka dan Allah"
"To Allah ya sa na sani"
"Dan Allah Sharif ana iya samun matar da ba ta da mahaifa dama?"
Ya yi shiru sanann ya ce "Me yasa ki ka tamabaya?"
"Ka bani amsa kawai"
Nutsuwa ya yi ya tattara hankalinsa, kar ya ba ta amsar da zai fallasa wani ɓoyayyen abin da bai kamata ba. Duk da bai san dalilin da ya sanya ta yi tambayar ba.
"Eh ana samu Hajiya, sosai ana samu wani abu ne ya faru?"
"A'a shikenan na gode sosai" ta kashe wayar, sai a lokacin hawaye ya fara gangaro mata, da ta ƙara tabattar da har abada ba za ta samu haihuwa ba. "Amina butulci za ki yi wa Ubangiji? Sauran ni'imomin da ya yi miki fa?" Wata zuciyar ta tunatar da ita. Sai dai kasancewarta biladama mai ɗauke da zuciya irin ta ɗan adam, sai ta kasa jurewa ta bi nasihar da zuciyarta take yi mata, ta fashe da matsanancin kuka mai taɓa zuciya. Duk da ta daɗe tana yin sa a ɓoye, amma ba ta yanke tsammani ba ta ci gaba da addu'a, amma a wannan karon da ta san ba ta da rabo baki ɗaya, sai ta sare.
***** Shirye-shiryen bikin Abba yayi nisa, dan bai fi saura sati biyu bikin ba, ta ƙara saka masa ido da shi da Jamila. Jamila sam ba ta nuna mata cewar ta san abin da take yi ba, ta rabu da ita. Ya kasance taronsu na ƙungiya lokaci yayi, dan haka suka shirya tafiya a wannan karon har da maman Khairat. Da suka je masaukinsu ma a garin Abuja, Jamila ba ta shiga sabgarsu ba, harkokinta kawai take yi.
Maman Khairat ta ce "Wai Jamsy ya ne? Duk kin zama so silenta, babu wannan rawar kan" Jamila ta ɗan taɓe baki kawai. Hajiya Sa'a ta ce "Jamila haushina take ji, ban san me na yi mata ba"
Jamila ta ce "Mummy kenan"
"A'a ba wani Mummy kenan, magana za ki yi"
"To Mummy, ki na ta daughter daughter, amma ƙarara ki ka nuna ba kya ƙaunata, daga ganina tare da Abba, ki ka haɗe rai ki ka yi kicin-kicin, ki ka tashi nema masa aure. Abin ya bani mamaki"
Hajiya Sa'a suka haɗa idi da maman Khairat, ta ce "Haba daughter, ya za a yi na ƙi ki da Abba, ke me ma za ki yi da aure? Na daɗe ina gaya miki za ki iya rayuwa ki da kuɗinki, ba tare da kin yi aure ba. Za ki huta ki yi duk abin da ki ke so."
"Amma Abba ma ai yana da kuɗi, shi me yasa ba ki ce ya yi rayuwa da kuɗi kawai ba, ki ke shirin yi masa aure? Duk wata ƙasaita, kuɗi da wadatar mace, inuwar aure ginshiƙi ce kuma sutura ce ga 'ya mace. Amma na san saboda ni rayuwata ta gama lalacewa, ke kuma kina son ɗan ki ya yi kyakykywar rayuwa, ki ka yi ƙoƙarin raba ni da shi. Sai dai tun ran gini tun ran zane. Ban ji haushinki ba ko kaɗan Mummy, abin da ki ka yi shi kowacce uwa za ta yi. Ina yi mana fatan dacewa da ƙarshe mai kyau" Tana gama maganar ta yinƙura ta tashi, ta bar ɗakin.
Safiyya ta ce "Kin ga Hajiya, ki bi yarinyar nan a hankali, alamu sun nuna hankali ya fara shigarta, ta san ciwon kanta, kuma abin da aka yi mata duk da ta samu kuɗi ya yi mata ciwo. Kar ki bi ta da ƙarfin tsiya ta yi tawaye"
Hajiya Sa'a ta numfasa ta ce "Na ga alama, amma ba zan taɓa rainon ɗan kwiykwiyo, ya girma ya fara yi mini haushi ba. Ina son samun jinin 'yar uwatta na riga Zailani samu ko ta halin ƙaƙa, daga nan zan yi maganinta"
Safiyya ta jinjina kai.
Doctor Sharif ya din ga kiran Alhaji Zailani, ya sanar da shi kiran da Hajiya Amina ta yi masa, amma ya kasa samunsa a waya, saboda su shinga taron manyan ƙungiya da suke yi, wanda sai sun kwana uku suke fitowa, sannan ayi babban taro na kowa da kowa da ke cikin ƙungiya.
Ganin kiran Hajiya Amina ya bawa Shukura mamaki, dan idan tana Saudiyya sai dai su yi video call. Ta ɗaga ta ce "Mami, yaya ba ki samu tafiyar ba ne?"
"Shukura za ki iya zuwa gida, ban takura miki ba"
Cikin tashin hankali Shukura ta ce "Lafiya kuwa, ya na ji muryarki a haka?"
"Dan Allah idan da hali ki zo gida"
"Shikenan, gani nan zan kira baban Haidar na gaya masa, gani nan Allah ya sa lafiya"
Hankali a tashe, ga tsohon ciki haka ta ɗauki mota ta tafi gida. Tana matuƙar jin Hajiya Amina a zuciyarta, saboda bayan rasuwar mahaifiyarsu, tun su na ƙanana babu yadda ba ta so cuzguna mata ba, amma Hajiya Amina babu ruwanta. Ba ta damu da abin da mutane za su ce ba, ta riƙe ta da halin ta, sai da ta ƙara wayo sannan ta gane ba ta da wata uwa da ta wuce ta. Shi yasa take matuƙar jin damuwarta a ranta tamkar uwar da ta haife ta. A bedroom ta tarar da ita, idanunta jawur sun kumbura. Cikin tashin hankali ta ƙarasa ta zauna ta ce "Lafiya kuwa? Ko ba ki da lafiya ne?"
Ta girgiza kai ta ce "Yi haƙuri Shukura, na taso ki ga tsohon ciki, na rasa da wanda zan yi zancen nan na ji daɗi a raina."
Cikin damuwa ta ce "To meyafaru?"
"Shukura wai ba ni da mahaifa"
Shukura ta yi saroro, ta ce "Kamar yaya?"
Ta share hawayenta ta gaya mata duk abin da ya faru. A ƙarshe ta ce "Na kira Doctor Sharif ya ce mini eh ana iya samun mata da basu da mahaifa, amma na yi mamakin yadda duk yawon Asibiti da na yi a nan, ba a taɓa gaya mini ba"