Buzu book 2 complete - Chapter 26
Buzu book 2 complete Chapter 26: Buzu book 2 complete Chapter 26. Nana ta koma gurin girkin, ta fara ƙoƙarin dafa shayin girfa, saboda babu shi, Adama ta…
3,314 words
Nana ta koma gurin girkin, ta fara ƙoƙarin dafa shayin girfa, saboda babu shi, Adama ta saka ta wani aikin. Wasu lokutan har rasa yadda za ta yi take yi, sai dai ta kan jure dan kar ta gaza ta sare, dan jikinta yana bata zamanta a gurin nan ka iya sanyawa ta yi nasara. Sai dai abinka da ɗan Adam, wasu lokutan ta kan bujire. Ta kammala ta tambayi ofishin Hasna, aka nuna mata ta kai mata shayin har can. Tana tare da Al Hussain ta tarar da ita, da wasu manyan mutane guda uku a office ɗin. Cikin girmamawa Nana ta gaishe su, cikin gurɓatacciyar hausa suka amsawa Nana. Hasna ta sake mayar da Nana, wai ta kawowa baƙinsu shayi. Haka Nana ta koma, ta sake kai musu wani shayin, duk da hakan ba aikinta ba ne ba.
Ta fito daga ofishin, Al Hussain ya biyo ta yana kiran sunanta. Ta tsaya ta waiwayo ta jira ya ƙaraso.
"Nana ko haryanzu jikin ne ba ki warke ba?"
Cikin ƙarfin hali ta girgiza kai ta ce "A'a jiki na warke"
"A'a idan ba ki warke ba, na saka a kai ki Asibiti, sai a baki hutu"
Ta girgiza kai cike da ƙwarin gwiwa ta ce "A'a na ji sauƙi fa, zan ci gaba da aiki in sha Allah, na gode sosai da sosai" Ta juya ta ci gaba da tafiya. Shi dai haka kurum Nana tana ba shi tausayi, sai dai babu wata dama da ta bari, da za a iya zama da ita a ji matsalar ta, ko za a iya taimaka mata. Ya lura ko a cikin ma'aikatan ba ta da sukuni, ba ta sakin jiki da su. Kuma yanayin ta ƙarara yake bayyanar da damuwa duk da tana da ƙoƙarin dakiya.
*****
Alhaji Zailani ya din ga kiran lambar Hajiya Amina. Gaba ɗaya ya rikice hankalinsa ya yi mummunan tashi, ya rasa abin da yake yi masa daɗi, yana tsoron kar ta aikata wani abin da zai kawo matsala. Ga jirginsa sai washegari zai koma Kano, ga shi yana da manyan uzururrukan da yake son yi a Abuja, da ba zai iya tsallakewa ya bar su ba.
Shukura ta je har gida, ta sake samun Hajiya Amina ta lallaɓa ta a kan ta amince su je gurin Doctor Sabo, amma ta ce babu inda za ta je. Da ƙyar ta amince ta ce ba za ta je a ranar ba sai washegari.
Shukura ta ɗan numfasa ta ce "Mami ba na son yi miki maganar nan ki na cikin damuwa, sai dai nima ba a son raina ba, na rasa abin da yake yi mini daɗi"
Cikin damuwa Hajiya Amina ta ce "Dan Allah ki kwantar da hankalinki, kar wannan cikin ma ya sake samun matsala mene ne?"
Ta numfasa ta ce "Sagir ne fa yake ta ƙoƙarin dawo da tsohuwar matarsa"
Hajiya Amina ta ce "To shi ne ki ka damu haka? Dan Allah ki rabu da shi ya ƙarata, ki lallaɓa ki haihu lafiya kalau, kin ga ga hawan jini ki na fama fa"
"Wallahi Mami zuba masa idon na yi, takaicina bai gaya mini ba, su na ta ƙwarbai da Hajiya, ta ce ba zai dawo da ita, a bakin ƙannensa nake ji".
"To babu ruwanki, su sha'anin dangin mijin nan ba a zaƙalƙale musu, idan ta dawo ɗin ma wataƙila su tattara su haɗe kai, babu ruwan ki ki kula da kan ki, ki sauka lafiya"
Shukura ta jinjina kai ta ce "In sha Allah, sannan dan Allah Mami ke ma ki kwantar da hankalinki, nutsuwarki ita ce ta wa, dan Allah Mami ki kwantar da hankalinki kema"
"Wallahi Shukura ƙarfin addu'a ya sanya mini nutsuwa da tawakalli, yadda ku ke yi mini biyayya da ke da Yusuf ko ni na haife ku, Alhamdillah na san iya abin da za ku yi mini kenan. Kuma na san ko yau na bar Duniya za ku tuna da ni ku yi mini addu'a"
Idon Shukura fal hawaye ta ce "Mami ke uwa ce abar alfahari, har Duniya ta naɗe ke uwa ce a gare mu, kuma muna alfahari da samun ki" Suka rungume juna da ita da Shukura, Hajiya Amina ta ci gaba da gode wa Allah, tana jin da natan ta haifa wataƙila ma ba lallai su yi mata biyayya haka ba.
Sai bayan tafiyar Shukura, sannan ta shiga ɗaki, ta tarar da kiran wayar Alhaji Zailani rututu.
Yana ganin kiranta ya ɗaga, bai tsaya amsa gaisuwar ta ba, ya hau tambayarta abin da ya hana ta tafiya.
Ta ce "Matsala aka samu, kuma na yi ta kiran ka a waya, ba ka ɗaga wa"
"Matsalar me?"
"Ba komai, idan ka dawo ma yi magana"
Ya ce "Yanzu nake son ki gaya mini koma mene ne, meye dalilinki na kiran Sharif kina tambayarsa ana haifar mace babu mahaifa?"
Ta ce "Amma laifin me na yi haka? Na tsaya a Egypt su duba lafiyata ne, tun ina can nake neman ka, ban same ka ba, sakamakon gwajinsu ne ya tabattar da ba na ɗauke da mahaifa"
"To uban waye ya ce ki je? Ba sai da na ce miki ki bar batun yawon neman haihuwar nan ba, da yake ban isa na saka miki doka ki bi ba, kin raina ni bani da mutunci a idonki?" Duk bayanin da ta so ta yi masa, yaƙi saurararta, ya din ga zazzaga mata bala'i. Ranta ya ɓaci, ta ga Sharif bai kyauta mata ba, ya za a yi daga tambayarsa abu ya ɗau waya ya kira shi ya gaya masa, ai gara ta gaya masa da kanta, duk da ba wani abin ta ce masa ba, tambaya ce kawai ta yi masa.
*****
Ɓamgaren Alhaji Fatuhu, Hajiya Suwaiba kamar ta yi bindiga, ganin ya amince ana yi masa maganin gargajiya, a ganinta dan Fadila ta saka baki ne, ta lallaɓa shi yake yi. Yanzun ma Fadila tana ta ƙoƙarin kunna garwashin da za ta yi masa turare, gefe ta kunna mp sautin ayoyin ruƙiyya su na tashi a hankali.
Ya kalli Fadila ya ce "Baby, ina fatan dai magungunan nan, babu wani abu na kauce hanya a cikin su?"
Ta girgiza kai ta ce "Haba Daddy, kai ma ka san ba zan yi duk wani abu da zai taɓa imaninmu ba in sha Allah, Kawu ne duk ya bayar da su, kuma ka san shi ma masanin Addini ne sosai. Babu wani na shirka a ciki."
Ya ce "To ki yi haƙuri, kawai da na tambaya ne, kin san yanayin abin, kar garin magani mu kauce hanya na je na mutu a mummunan tafarki, ya zamana na kasa jure ƙaddarata na kauce hanya"
Fadila ta ce "In sha Allah ba zaka mutu yanzu ba, za ka samu lafiya"
"To ki yi haƙuri, na ga kin ji haushix
Ta girgiza kai ta na ɗan murmushi ta ce "A'a ban ji ba"
"Kin ji mana, kin tura baki gaban ne ba ki ji haushi ba?" Sai kuma suka yi dariya a tare.
Ya ce "Ki yi haƙuri, in sha Allah ba zan sake magana ba, na yarda da ke, ba zaki cutar da mu ba"
Hajiya Suwaiba ta shigo ɗakin, tana basarwa jin yadda ɗakin ya ɗume da ƙamshin jan almiski, da ƙaurin hayaƙi. Ta ɗan taɓa baki a ranta ta ce watakila ma a cikin wannan tsiyatakun take mallake ka.
Ta ajiye masa kwanukan Abinci, ta juya za ta fice.
Ya ce "Ba magana ne?"
"Sannu ya jiki?" Ta faɗa a daƙile.
"Jiki Alhamdillah, a hankali ji nake jikina ya yi daɗi, na ɗan samu sassauci daga abin da nake ji kamar an ɗaure ni, ba na iya motsi sai da ƙyar da dabara, da ƙirjina da yake yi mini nauyi nake jin kamar an toshe mini baki da hanci da kokowa nake numfashi" Duk da tana jin haushinsa sai kuma ta saki fuska ta ce "Alhamdillah, sauƙi yana samuwa kenan? Ubangiji Allah ya ɗorar da sauƙi, dama komai nufi ne na Allah"
Ta kalli Muhsin da yake ta tattaɓa kwanon abincin da ta kawo. Ta ce "Kai ɗan lukuti acici, ka zubar mini da Abinci sai ka biya ni. Ki zuba masa abincin ko ci zai yi" Ta yi maganar sama-sama tana ɗan kallon Fadila. Duk da matsanancin kishin da Hajiya Suwaiba take yi da ita, yanayin yadda take yi wa Muhsin wasu lokutan ya sanya Fadila ba ta fiye jin haushinta ba.
***** Hasna kuwa ta sako Nana a gaba, bayan aikin da take yi, ta din ga sanya ta wasu ayyukan daban da ba sa cikin jadawalin wanda aka ɗauke ta yi. Wasu lokutan sai ta gama aiki, ta koma ɗakinsu, sai ta saka a taso ta, ta saka ta aiki. Abin ya ishi Nana amma ta danne. A wannan karon ma, har ta yi shirin kwanciyar, aka zo aka kira ta. Kawai ta ji a ranta, ko Hasna za ta kashe ta yau, sai dai ta kashe ta, dan ba za ta yi mata kowane aiki ba, sai dai ta kore ta.
Ƙarafe goma sha ɗaya na dare, amma tana ofishinta ba ta tashi ba. Ko da Nana ta je, tsayawa ta yi ƙyam tana jiran ta ji me Hasnan za ta ce. Sai dai ta ci gaba da aikin gabanta, sai da Nana ta fara ƙosawa, sannan ta kalle ta ta ce "Amma an ce 'yar Nigeria ce ke ko?"
"Eh" Nana ta amsa a ƙufule.
Ta ɗan ƙura wa Nana ido sannan ta ce "Ina da wasu baƙi ne gobe in Allah ya kaimu " Nana ta ɗago tana kallonta, ta ji ina ne ƙarshen zancen, dan kullum cikin baƙi suke kamar gurin boka.
"Dan haka ba aikin gurin cin abincin nan za ki yi ba gobe in Allah ya kaimu, aikina za ki yi. Zan saka a sanar musu ma. Ina son ki yi Abinci mai kyau da daɗi na Nigeria. Ina son na sauke su da shi. Wajen la'asar za su zo, dan haka za ki dafa abin karayawa, da abincin rana da na dare, za a zo a ɗauka" Nana ta yi ajiyar zuciya jin ba wani aikin rainin hankalin Hasna ta saka ta ba.
"Allah ya kaimu, zan iya tafiya?"
Hasna ta ce "Saurin me ki ke yi ne?"
"Na gaji ne sosai, bacci nake ji ina son na samu na tashi da wuri"
Ta jinjina kai ta ce "Ya yi je ki" Nana ta fice ta tafi ɗakinsu.
Sai dai duk gajiyar da ta yi, bacci ya gagari idanunta.
Tun bayan sallar Asuba, ta tafi kitchen ɗin ta fara aikin da Hasna ta saka ta. Sai bayan Azahar ta kammala komai, Hasna ta aiko aka ta ɗauki Abincin. Nana ta fara shirin tafiya ta je ta yi wanka ta huta.
Adama ta ce "Ina za ki je kuma ga ayyukan kitchen fal?"
Nana ta numfasa ta ce "Ki yi haƙuri, Hasna ce ta saka ni aiki, ta ce idan na gama, na je na huta"
"A'a ba zai yiwu ba, ni ce mini a aka yi kawai za ki yi mata aiki, dan hakan idan kin gama ki saka hannu ku ci gaba da aikinmu, wa za ki bar wa wannan aikin?"
"To ki yi haƙuri, na gaji gaskiya ba na jin daɗi" kawai ta fice, tattaunawa suka shiga yi a tsakanin su, yadda za su kawo ƙarshen Nana a gurin baki ɗaya. A ƙarshe suka yanke shawarar, su ƙara ƙaimi su ɓata ta a gurin Hasna, ganin yadda ita ma ta sako Nana a gaba da tsangwama.
Bayan sallar isha'i, Nana ta daɗe a zaune tana tasbihi, tunanin gidansu da 'yan uwanta ya addabi zuciyarta, ga shi abin da ta fito neman har yau babu labari. Ta daɗe tana addu'a kafin ta nemi guri ta kwanta.
Washegari ma su na ta aiki tun safe har Yamma, sai ga Hasna ta shigo.
Duk yadda Hasna take da kyau, ita da Al Hussain, wannan da suka shigo ta fita kyau, tamkar balarabiya, jawur da doguwa sai dai siririya ce sosai. Fuskarta ta sha make up, sai zuba ƙamshi take yi. Ta yafa ɗan siririn mayafin abayarta a kanta. Sai kallonsu take ɗaya bayan ɗaya tana yatsuna fuska su na yare ita da Hasna. Duk suka gaishe su, Nana kuma ta yi burus. Hasna ta nuna mata Nana ta ce "Kin ganta nan"
Asal ta yamutsa fuska ta ce "Ya na ganta baƙa ƙirin haka, ina fatan ba na ƙazanta ba ne?" Nana ta yi mamakin jin Hausa raɗau a bakinta.
"Ke ina ruwanki da baƙinta, ba dai Abinci ya yi ba?"
"Eh kin san ba na son ƙazanta ne"
Hasna ta ce "Sauran ma'aikatan namu ma ai akwai baƙaƙe, kuma kema kin san da ba ta da tsafta, ba zan saka ta yi miki girki ba.Ke Nana ba ki ganni da baƙuwa ba ne?" Nana ta ɗaga kai ta kalle su, ta yi shiru tana wasa da wuƙar hannunta, saboda ciwon da maganganun da suke yi ya yi mata, na cin zarafin baƙar fatarta da danganta ta da ƙazanta, duk ba wai duhu ne da ita sosai ba.
Shiru Hasna ta yi ta kamo wata hirar, ganin alamun idan ta matsa Nana za ta yarfa ta ne a gaban baƙuwarta. Ba a taɓa ma'aikacin da ba ya shakkar ta ba sai Nana. Duk abin da ta saka ta na aiki za ta yi, amma ba ta son rainin hankali.
Bayan sun fito Asal ta tsaya ta kalli Hasna ta ce "Hasna"
"Na'am"
"Ina ga yarinyar nan ta yi dai-dai da abin da nake nema"
"Wace yarinyar?"
Asal ta ce "Wannan 'yar Nigeriar, ina buƙatar za ki ba ni ita"
Ayshercool 08081012143
70
Sai da Nene ta tabattar Nana ta ɗan nutsu, sannan suka kwanta.
Washegari Nene ta fita, ta bar Nana a gidan tare da Muhsin. Bayan ta dawo daga gurin sama'arta ta cewa Nana, yakamata ta je ta ɗan sai abubuwan da za ta buƙata saboda tafiyar da za ta yi da nisa, kuma ba su san yaya tsarin aikin can ɗin yake ba. Nana ta ce "Ni babu abin da nake buƙata, ki bani wani abin na riƙe a hannuna, sauran kuɗin kuma ki riƙe saboda kula da Muhsin na s...
"Biyana za ki yi kenan dan na riƙe miki Muhsin?" Nene ta katse ta.
"Allah ya baki haƙuri, ba haka nake nufi na, na ga dole ɗan abubuwan buƙatunsa duk ke ki ke yi masa Nene, tun da ga kuɗi sun"
"Kuɗinki ba su isa su saka na riƙe miki ɗa ba ko?"
Nana ta ce "Na sani, ai shi ya sanya na ce ki yi haƙuri.
Nene ta ce "Ba zan yi haƙurin ba sai na gama, kin iya kunna ni da na fara faɗa ki hau bani haƙuri, wato in ci kaina to sai na idar" Nana ta yi mata shiru ta yi faɗanta ta gama. Washegari Nene ta saka Nana a gaba suka je kasuwa, ta sata ta yi sayayyar kayan sakawa da na ɗan shafe-shafe, ta yi wa Muhsin sayayyar kayan sakawa da pampers. Babu yadda ba ta yi da Nene ba ta ɗauki wani abin ta ce ba za ta ɗauka na. Nana ta haɗe rai ta ce "Eh dama ba ki ɗauke ni 'yarki ba, shi ya sanya duk abin da zan yi miki ba kya karɓa"
"Ni za ki yi wa wayo, na ji ban ɗauke ki 'yar ba, ni ga ɗana nan" tayi maganar tana shafo Muhsin da ke bayanta. Da ƙyar sai da suka kai ruwan rana Sannan Nene ta karɓi abin da Nana ta saya mata. Sai dai kan su bar kasuwar har sun shirya. Nana ta ce "Nene kin ce mini ki na da ɗa, amma ban taɓa ganinsa ya zo ba, ba ya zuwa ya gan ki ne?"
Nene ta ce "Kamar ban damu da shi ba ko?"
"A'a kawai dai tambaya na yi "
"Yana can Nigeria"
"To me yake yi a Nigeria ba ya zuwa inda ki ke?"
"Sana'a yake yi, ai ya zo ki na can gurin aiki" Duk da Nana ba ta gamsu da amsoshin da Nene ta ba ta ba, amma ta basar ta ce "Allah sarki, Allah bai yi zamu haɗu ba".
Haka suka ci gaba da hira suka koma gida, Nana ji take yi tamkar ta ɗauke ɗanta ta tafi da shi.
Gidansu Ashura Nana ta je, ta samu keke ta ɗiɗɗinka kayan da ta sayo, ta sake haɗa jakarta ta ɗauki muhimman abubuwa a kayanta. Duk da a ɗaki Nene take rufe mata su, ba ta taɓa ganin alamar Nenen tana yi bincike a cikin kayan ba.
***** Ko da Jamila suka dawo Kano, fakar ido ta yi ta jefar da wannan tarkacen da aka ba ta aka ce da su za ta kai jini. Gaba ɗaya da ta tuna abin tsigar jikinta take tashi, ta ji ciwon kanta da zazzaɓi ya ƙaru. Gefe guda kuma hankalinta yana kan yadda ta ji Hajiya Sa'a tana faɗin za ta sake bayar da ɗan Alhaji Fatuhu. Ta jinjina rashin imaninta mutumin da yake fama da karayar arziki ga ciwo, ya rasa wancan ɗan kuma a sake bayar da wannan kamar ba a yi masa adalci ba. Sai dai gaba ɗaya ba ta san ta ina za ta fara ba, tana jin a ranta kamar yakamata ta tseratar da yaron. A gida ta tarar da Gaddafi, ta sha jinin jikinta da irin mugun kallon da ya yi mata, amma bai ce mata uffan ba. Suwaiba ma ƙura mata ido ta yi tana bin ta da kallo. Ta tsuke fuska ta harsri Suwaiba, sai dai Suwaiba ta tuntsure da dariya, kamar za ta shiɗe. Jamila ta yi tsaki ta shige ɗakinsu. Ba ta tarar da Mama a gida ba, haka ma Baba.
*****
Shiru Alhaji Zailani ya yi yana kallon Doctor Sharif yana sauraren shi, har ya gama karanta masa abin da Shukura ta je ta same shi ta yi masa. Ya ja numfashi ya ce "Shikenan, aikinka ya yi kyau Sharif, na kuma gode sosai da sosai da ka ke sanar da ni wannan abubuwan, Allah ya saka maka da mafificin alkhairi. Ka je za ka ga saƙo" Sharif ya yinƙura ya tashi ya tafi.
Alhaji Zailani ya numfasa a fili ya ce "Duk da kasancewar ki 'ya mafi soyuwa a cikin zuciyata, an zo gaɓar da ki ka ƙetare layin da bai kamata ki ƙetare ba, kina ƙoƙarin tono abin da zai wargaza zaman lafiya da kwanciyar hankali, dan haka ki yi haƙuri da duk matakin da zan ɗauka a kan ki.
***** Nana ta jingina da jikin gilashin motar, tana kallon tulin yashin saharar da ya mamaye gurin. Fili fetal hagu da dama duk yashi ne. Cikin yanayi mai kama da bacci take ganin abubuwan da ta din ga gani a bacci cikin saharar. Ko a yanzun ma su na tafe Sayyid kawai take gani a kan raƙumi yana biye da su a cikin saharar. Kamar an taɓa ta ta ɗan yi firgigit ta kalli gurin, haryanzu a titin da ya ratsa saharar suke tafiya, zuciyarta ta yi wani irin bugu da sai da ta dafe ƙirjinta. Sanyi ta fara yana ratsa ta har cikin ƙashinta, ta ɗaga ido tana ɗan waige-waige ta ga ta ina za ta gano Ƙaisar ko wata baƙuwar halittar da ba jinsin mutane ba, sai dai ba ta ga komai ba. Ta sake jingina da jikin motar tana ta karanto duk addu'ar da ta zo bakinta. A haka har suka shigo cikin gari sosai da sosai. Nana na son karanta Symbols ɗin da take gani, amma ba komai take iya fahimta ba saboda rubutun French. Babbar hanya mai ɗauke da ƙaton gate ta ciki suka wuce. Ba ƙaramar gajiya Nana ta yi ba, saboda azabar nisan tafiyar da suka shawo ba, ba su ƙarasa ba sai bayan magariba. Kewar ɗan ta ta addabi zuciyarta, tunaninta yadda za ta din ga sintirin tsakanin Agadez da Maraɗi a wannan uwar tafiyar kamar ta ya da shege.