Buzu book 2 complete - Chapter 37
Buzu book 2 complete Chapter 37: Buzu book 2 complete Chapter 37. Babu tsammani ta ji an buɗe ƙofar ɗakin, hakan ya sanya ta kalli ƙofar da sauri. Sai dai…
3,371 words
Babu tsammani ta ji an buɗe ƙofar ɗakin, hakan ya sanya ta kalli ƙofar da sauri. Sai dai hasken fitilar mai wayarya haske mata ido, ba ta iya gane waye ba. Sannu a hankali ya jingine wayar hannunsa ya zura mata ido. Duk da ta ɗan razana amma abin bai wani ba ta mamaki sosai ba.
Ya zuba mata ido sannan ya ce "Kin yi mamaki ko?"
Ta girgiza kai ta ce "Ba sosai ba"
"Ko me yasa?"
"Saboda jikina ya daɗe da bani hakan"
"Ta yaya kenan?"
"Na daɗe ina zarginka ne, sai dai ana ta dankwafe ni, an hanani"
"Gaskiya ne, ban so ki zurfafa ki takura da son sanin abin da bai kamata ki yi ta bibiya sai kin gano ba, amma ban san me ki ka gani ki ka dage kina bin diddigina ba"
"Zarginka nake yi da kai da doctor Sharif na kasa yadda ɗa na mutuwa ya yi, saboda har yau ina ji a jikina, mafarkin da na yi gaskiya ne"
Alhaji Zailani ya ce "Haka ne, lokuta da dama mafarki ishara ne, duk da ban san abin da ki ka gani ba, amma zarginki gaskiya ne duk da na yi iya yi na a kan na ɓoye komai, sai dai kashi kin zaƙe Shukura, soyayyar da nake yi miki ba za ta hana ni ɗaukar matakin da ya dace a kan ki ba"
Shukura ta yi ajiyar zuciya ta ce "Da gaske ka na da masaniya a kan batun mahaifar Mami?"
"Ina da ita, haka zalika ina da masaniya a kan jaririnki ma da ki ke ta zargina da Sharif a kai, duk da ban san me ki ka gani a mafarkin ba" Shukura ta yi masa wani irin kallo, zuciyarta na bugawa da sauri da sauri.
"Tabbas mafarkinki ishara ne. Amma kafin na yi miki wannan bayanin ina son ki sani, talauci bala'i ne Shukura, babu yadda ban yi a kan na yi yaƙi da shi ba, amma abu ya gagara. Na faɗi na tashi na yi iya yi na amma na kasa nasara a rayuwata. Burina ya gaza cika na mallakar manyan motoci da gidaje da tara manyan kuɗaɗe yadda zan yi nesa da talauci. 'yar makarantar da nake taƙama da ita, abubuwa suka nemi ƙwace mini, bayan faɗuwa a jarrabbawa. A taƙaice dai a makaranta na samu ƙungiyar asiri na shiga, cike da burin na gama makaranta cikin sa'a da fatan cikar burikana na yin arziki mai yawan gaske ta hanya mai matuƙar sauƙi. Bayan na auri mahaifiyarku, ta haifi Sadik, ƙungiya ta fara neman jini a gurina. Na bayar da babban ɗa na Sadik, na kaɗu na shiga tashin hankali, sai dai hakan ne zai ba ni damar taka babban matsayi a ƙungiyar, duk da na bayar da waɗanda ba jinina ba a ƙungiyar amma na ji zafin bayar da Sadik. Aka haifi Yusuf, aka haife ki, ba a sake neman kowa ba, sai da wata buƙata ta sake taso mini, wadda biyan buƙatar na buƙatar na ƙara taka wani matsayi a ƙungiyar. Haka na bayar da matata ta fari, Hafsat da tsohon ciki, na saka mata ƙyallen jini a ƙasan shimfiɗarta ta tashi da ciwon naƙuda ta mutu a gurin haihuwa. Hakan ya sanya dukiyata ƙara haɓaka, na yi kuɗi na yi suna. Duk fafutukar kasuwanci da muke yi tare da Fatuhu, shikaɗai yake abin sa, ni fakewa kawai nake yi da kasuwanci amma ta ƙungiyar asiri nake samun kuɗina. Duk da ina samu ta kasuwancin ma, amma ga mamakina Fatuhu da baya ƙungiyar asiri, ya fi ni samun kuɗi, kuma duk inda muka je an fi son sa. Bayan na auri Amina, aka buƙaci duk wani ɗa da za ta haifa, zan din ga ba wa dodon ƙungiya. Lamarin ya yi mini nauyi, saboda ina jin ɗacin rabuwa da iyalina. Na nemi sassauci, sai aka dasa wa Amina wani jaririn aljani a cikin mahaifarta, duk cikin da ta samu ba ma ta sani yake cinyewa. Sai dai kawai ta wayi gari tana zubar da jini, babu ƙaƙƙautawa. Karo shida na shidan saura ƙiris ta rasa ranta, saboda jini take zubarwa ba kaɗan ba, sai dai a yi ta saka mata jini. Ba a taɓa gane ɓari take yi ba, an zata larura ce kawai, Asibiti aka kasa gane abin da yake damunta, na kuma hana a yi mata na hausa, tana zaune lafiya kawai sai ta hau zubar da jini babu ƙaƙƙautawa. Ta damu ta damu da matsalar rashin haihuwa, amma na hana ta zuwa Asibiti ta ci gaba da bibiyar lafiyarta. Ni kaina na damu da wahalar da take sha, sai aka nemi na sadaukar da mahaifarta gaba ɗaya ga wannan jaririn aljani, yadda ba sai ta ci gaba da samun ciki ba, cinyewar da yake tana azabtar da ita ba. Haka na amince, cikin dare ta farka tana ihu da buge-bige, ina kunna fitila na haska, na ganmu a cikin jini male-male. Na rirriƙe ta, amma ta fita daga hayyacinta, ihu kawai take tana riƙe mararta, a dole na ɗauke ta muka yi Asibiti, ganin za ta rasa ranta saboda zubar jinin nan. Ta fi kwana uku ba ta hayyacinta, jini kawai ake saka mata. Aka tura mu scanic, domin a gano musababbin zubar jinin. Na takurawa mai scanic ɗin ya gaya mini me ya gani. Ya sanar da ni babu mahaifa ma a jikinta gaba ɗaya, dan haka bai ma gano daga inda bleeding ɗin yake ba a scanic ɗin, sai dai a ci gaba da bincike. Abin ya bani mamaki, duk da a cikin ƙungiyar asiri nake, ban taɓa tunanin za a ga abin a zahiri a yi scan a ga babu mahaifa ba. Na biya mai scannnic kuɗi, ya rubuta sakamakon da ba daidai ba. Muka koma gurin likita, aka din ga bincike ba a gane komai ba. Ita kuwa sai da ta shafe kwana goma ba ta tantance wanda yake kanta, har an fitar da rai da ita sai kuma ta warke. Na daɗe ina tunanin abin da na yi mata saboda son da nake yi mata. Muka tattauna da malamina, da mamakin yadda a scanic ɗin aka gane bata da mahaifa ma zata a zahiri bs a za a gane ba. Sai ya ce mini idan na ce haka na ƙaryata kungiyar asiri gaskiya ce kenan, amma ya aka yi na yadda da kuɗin da nake samu a cikinta, har nake kashe su a zahiri? Ya ce mini dole na san duk yadda zan yi na ci gaba da rufe mata ba ta da mahaifa, dan kar ta ce za ta bi diddigi duk da ko ta bi diddigin babu abin da za ta iya ganowa. Wannan aljani haryanzu yana rayuwa a cikin Amina, gurbin da mahaifarta take, kan addabe ta da ciwo wasu lokutan, sannan wannan aljani shi ne yake saka ta zubar da jini lokaci zuwa lokaci da take tunanin Al'ada take yi. Wasu lokutan ta zubar da jini fiye da kima wanda take tunanin duk su ne dalilin rashin haihuwarta."
Cikin matuƙar tsoro da matsanancin mamakin yadda ya zauna ya wassafa mata wannan mummunan labarin da tun da ta buɗe ido a duniya ba ta taɓa jin labari mai razanarwa da tashin hankali ba.
Cikin matuƙar tsoro da matsanancin mamakin yadda ya zauna ya wassafa mata wannan mummunan labarin da tun da ta buɗe ido a duniya ba ta taɓa jin labari mai razanarwa da tashin hankali ba. Da ƙyar ta harhaɗo kalmomin da ta ce "Kai ka kashe Mummy, kuma ka bayar da mahaifar Mami? Da..da.dama aljani duk zai iya yin irin wannan abin?"
Yayi dariya ya ce "Ki na mamaki ne? Kodayake mutane duk abin da ba a kanmu ya faru ba, bamu fiye yarda ba, nima da fari kasa yarda na yi, abin ya ɗaure mini kai. Sai dai idan ki ka duba, ba a taɓa yi wa Amina aiki ba, kuma babu alamar tabo na tiyata a jikinta, dan haka ta yaya za ta rasa mahaifarta? Aljani muddin za ka yi masa biyayya, ka yi abin da yake so, to zai zama mai biya maka dukkanin buƙatunka. Da su ake sihiri, da su ake jifa, neman shugabanci, ɗaukaka kungiyoyin asiri da makamantansu. Duk wani siddabaru da za a ce miki sun yi ba abin mamaki ba ne ba" Ya yi maganar yana wata 'yar guntuwar dariya. Shukura ta ƙara rikicewa ta kiɗime. Ta ce "Yanzu Daddy, duk son da mahaifiyarmu ta yi maka kai ka kashe ta? Ga amanarmu da Mami ta riƙe ta kula da mu, ashe dama rashin haihuwarta da ciwon nan na zubar da jini da take yi babu gaira babu dalili, kai ne sila? Kai ka haddassa mata? Yanzu tayaya zaka nemi yafiyar su? Ka rasa imaninka saboda abin Duniya? Kai fa ka kashe su"
Ya ce "No in ji wa? Ai ban rasa imanina ba, ai annabi ya ce duk wanda ya ce La'ila ha illalahu zai shiga aljanna"
Cikin kuka ta ce "La'ila ha illalahu ba ta fatar baki ba Daddy, tayaya za ka shiga aljanna bayan ka kai buƙatarka gurin wanin Allah da ya buƙaci ka saɓa wa mahaliccinka dan ya biya maka buƙata. Me yasa ka ga buƙatar ka ta yi girman da ta gagari Ubangijinka ka dangana ga waninsa"
"Wannan wa'azin naki kin riga kin makara Shukura. Ina da yaƙinin zan tuba kan na mutu, kuma Allah zai yafe mini"
"Wa ya baka garantin ganin nan da awa ɗaya ma?" Ta yi maganar tana kuka mai tsuma zuciya.
"Ina da shi, dan ko ciwon kai sai na shekara ban yi ba" Ya miƙe tsaye yana faɗin "Ki mayar da hankali ki din ga cin abinci, saboda ke da abin cikinki nake sanya ran ku zama sadsukarwar ƙarshe da zan yi a ƙungiya. Sai dai kafin nan, ina roƙon afuwarki ko ba komai ke ma kin ci albarkacin dukiyata. Ɗanki da ki ka rasa ni na yi amfani da shi" Daga nan ya ɗauki wayarsa ya yi gaba abin sa hankalinsa a kwance, kamar bai aikata komai ba. Wani irin gunji Shukura ta din ga yi tana kuka mai tsuma zuciya, ta din ga fatan ina ma mafarki ne ba gaske ba. Tabbas wannan babbar jarrabawa ce, a ce mutum irin mahaifinta shi ne mahaifinka, gara a ce an haife ka ba ta hanyar aure ba, ko makamancin haka. Amma uba irin Alhaji Zailani ba shi da wani amfani. Duk wata gwagwarmayar sa da faɗi tashinsa a kan iyalinsa ya zama na banza, a dalilin wannan mummunar hanyar mara ɓullewa. Abubuwan da ya gaya mata sun shallake tunaninta, yanzu yadda ya tafi haka zai je ya ci gaba da rayuwa da Hajiya Amina duk da zaluncin da ya yi mata. Ta ji dama ta ba wa Sagir damar kai ta Asibiti wataƙila da ba a samu damar sace ta ba. Cikin kuka take roƙon Ubangiji Allah ya tona wa mahaifinta asiri, saboda a yadda zuciyarsa ta ƙeƙashe ɗin nan, babu wani abu na rashin imani da zalunci da ba zai iya aikatawa ba.
Can gida Sagir ko abinci ba ya iya ci. Yusra kuwa abin ka da ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba, sai ta kwanta rashin lafiya, saboda yadda ta addabi kanta da ɗorawa kanta alhakin ɓatan Shukura, dan cewa take saboda ta dawo gidan Sagir Shukura ta tafi. Haka Hajiya Amina ma, Addu'a kawai take yi a kan Ubangiji Allah ya bayyana Shukura a duk inda take. Sosai take jin tamkar 'yar cikinta ce ta ɓata, tun tana daurewa har ta kasa ta fara zubar da hawaye, kasancewar babu wani labari mai daɗin ji da zai nuna an kusa gano inda Shukura take.
****
Asal ta na tsaye a banɗakin cikin ɗakinta, bayan tabattar da Imam baya ɗakin, ta danna wata lamba ta kira. Can aka ɗauka mutumin ya ce "Na'am ina jin ki"
"Ina da labari ne"
"Ina sauraren ki"
Ta numfasa ta ce "Hannun Imam babu zobensa na tambari, na tambaye shi ya ce mini karyewa ya yi ya kai gyara, daga bisani kuma ya ce mini bai san inda yake ba" "Kin tabattar da hakan, ba kuma ɓoye shi ya yi a wani gurin ba?" Asal ta ce "Eh na tabattar ai zobe ne da ba ya cire shi, tun da ya dawo babu zoben a tare da shi" Mutumin ya numfasa ya ce "Madalla, ki ci gaba da sanya ido da sanar da ni duk wani abu da yakamata na sani" Ta jinjina kai tamkar yana ganinta ta kashe wayar ta fita. Jikin Nana tamkar an yi mata duka, saboda azabar gajiya da ta yi. Ta kammala aikinta tana ta gyaran kitchen, sai ga Balaraba ta shigo da ƙatuwar jarka. Ta ajiye ta ta ce "Gashi nan madarar raƙumi ce da Imam yake sha"
"To sannu da ƙoƙari Mama Balaraba"
Ta ce "Yauwwa kukun Imam, Allah ya taimake ki"
Nana ta yi murmushi ta ce "Kar ki ba ni kunya mana"
"Ba kunya zan ba ki ba, ai ke yanzu duk wata kuku a gidan nan a ƙarƙashinki take, ke kaɗai ki ke dafa abincin da zai ci, dole mu girmama ki saboda kema shugabarmu ce"
"A'a ni ba shugabarku ba ce ba, ni da nake bare ma a cikinku. Amma dan Allah Mama Balaraba wai su wa ake cewa Imam ɗin nan ne? Dan na ga wanda ake kira da hakan da yawa"
"Eh su Biyar ne, galibinsu jikoki ne na gidan sarauta, su na cikin jerin waɗanda za su iya gadon kujerar Sultan. Shi Imam Hammad a gidansu su biyu ne da shi da Imam Abdallah, sai Imam Zahradeen shi ma jikan marigayi Sultan ne, akwai Imam Asadullah yayan Asal, sai Imam Omar, waɗannan su ne jerin waɗanda ake sanya ran za su gaji kujerar Sultan. Duk da su na ganin cewa Sultan na yanzu nuna son kai ƙarara na son Imam Hammad ya gaje shi a cikin yaransa. Imam Hammad yana da 'yan uwa da suke uba ɗaya amma su biyu ne suka cika ƙa'idojin zama Imam. A ƙasar nan ana girmama duk wani Imam fiye da zatonki, mu na ƙasa mu na son Imam Hammad sosai mussaman baƙaƙen buzaye da fararen ke yi mana kallon kamar ba 'yan uwansu ne mu ba, bayinsu ne kawai. Idan kin lura galibi hadiman gidan nan baƙaƙen buzaye ne, fararen kaɗan ne ƙarara yake ƙoƙarin yaƙi da kyamar da fararen buzaye suke yi mana, yana ta fafutukar nema mana 'yanci, da ƙoƙarin mu ma a din ga bamu dama a cikin shugabanci, bai kamata iyayenmu sun ƙare a bauta mu ma mu ƙare a haka ba. Amma manyan nan ba sa son shi sam, gani suke yana ƙoƙarin hana su rawar gaban hantsi. Ni tun da ya dawo ma duk ya canza mutum ne mai sanyin hali, amma kaifi ɗaya ne, ba sani babu sabo. Shi ne shugaban majalisar duk Imam ɗin ƙasar nan. Duk da a cikin su akwai wanda suka girme masa, amma a haka dole su girmama shi kamar yadda yake a dokar ƙasar nan. Tarihin masarautar Agadez yana da yawa da kuma faɗi Nana, bari na tafi na je na ci gaba da aikina. Nana ta jinjina kai ta ce "To shikenan na gode sosai da sosai" Bayan fitar Balaraba Nana ta naɗe hannunta a ƙirjinta, tana nazari da tunani.
Jiki a sanyaye ta koma ɗakinta, ta duba kayanta ta lalubo takardar nan da aka kawo saƙon aka ce a ba wa Sayyid. Ta ƙare wa takardar kallo. "Ko a cikin Imams ɗin nan ne wani ya aiko da wannan takardar?" Ta yi maganar tana tuna maganganun da ta ji suna yi ranar da aka kai su yin girki a gidan Sultan. Ta koma ta lalubo zoben gurin Sayyid ta din ga jujjuya zoben ta ce "Ko kai a ke nema ne? Idan kai ne ta yaya zan ba shi abin sa, tun da ban san iya adadin muhimmancin sa a gare ka ba, idan na baka ka manta ni ta yaya zan yi bayani a yarda da ni?" Ta din ga surutai ita kaɗai ta gaji ta nannaɗe kayan ta buɗe jakar sarkin baka ta watsa takardar da zoben ta rufe ta ajiye a cikin kayanta. Bayan sallar magariba aka sanar mata baƙin Imam sun iso, su na can sashin karɓar baƙin sa wanda ɗaki ne a can wajen lambun gidan. A kwanduna ta shirya kulolin Abincin, ɗaya daga ma'aikatan gidan, ta taya ta kai wa. Su na zazzaune a ɗakin, gaban su shaƙe da kayan marmari da uban soyayyen nama. Duk wannan Imam Imam ɗin ne, gaba ɗaya zaune a gurin. Ayabar hannun Sayyid ta kalla, da ya kai bakinsa ya gutsura fuskarsa ɗauke da murmushi. A take ta ga jini yana bin bakinsa, ayabar ta koma baƙa ƙirin, wasu abubuwa masu tsini tamkar ƙayoyi suka tsiro a jikinta.
Ayshercool 08081012143 77
Rikicewa ta yi, amma ta fara ƙoƙarin daidaita nutsuwarta dan ta san idan ta yi wani gangancin a gurin, babu lallai ta sha ta daɗin rai duba da girman mutanen da suke gurin a zaune. Ganin ta tsaya ta zuba masa ido, ya sanya ya sauke hannunsa a hankali yana kallon ta shi ma. Ta ƙarasa shigowa a hankali ta ajiye musu kwanukan abincin.
Zuba mata ido suka yi, gaba ɗaya suka yi shiru daga hirar da suke yi. Ta ce "Shugabana, ga abincin ko zan jira ku duba idan da abin da bai yi ba?" Ya girgiza kai ya ce "Za ki iya tafiya" Sai dai ta kasa tashi, ta ci gaba da rarraba ido. Ya sake cewa "Za ki iya tafiya" "Dan Allah ka taimaka mini da ayabar hannunka, yunwa nake ji"
Imam Omar ya ce "Imam Hammad, wai wace ce wannan ɗin? Ta san waye kai kuwa abin hannunka za ka ba ta?" Ya kalli ayabar ya kalle ta, bai kai ga yin magana ba, ta saka hannayenta biyu ta miƙa masa. Tamkar soko haka ya miƙa mata ayabar, ba tare da musun komai ba. Ya ce "Ga wata nan ki ɗauki yadda za ta ishe ki" Ta girgiza kai ta ce "Wannan kawai ta ishe ni, na gode sosai da sosai" Duk su ka bi Nana da ido, wasu cike da takaici, wasu kuma mamakin tsaurin idonta, duk da ba abin mamaki ba ne sosai, tun da ba ta san irin girmansu da matsayinsu ba, kasancewarta bare ba ƙabilarsu ba, kuma ba 'yar ƙasarsu ba.
A hankali ta saci kallon hannayensu, sai ta gan su sanye da zobunan nan irin na hannun Sayyid da ya ɗauka ya bata. A take ta koma gefe ta cinye ayabar, sannan ta yinƙura ta tashi. Imam Asad ya fara masifar wace mahaukaciyar haka, da za ta zo ta yi musu wannan rashin hankalin, su zuba ido su na kallonta. Hammad ya ce "Ina mai baku haƙuri, baƙuwa ce a cikin lamarin gidan mulki, ku yi mata afuwa" Nana tuni ta fice daga ɗakin, aikuwa fitarta ke da wuya, jiri ya fara ɗibanta, bango ta dafa tana bi a hankali, sai dai kan ta kai inda take so ta yanke jiki ta faɗi. Faɗan Ƙaisar ne ya sanya ta buɗe ido, a matuƙar galabaice. "Waye ya ce da ki ka karɓa ki ci? Kin san abin da aka yi a jikin ayabar? Ban da na riga na buɗe miki ido ki na ganin abubuwa, da ba zan sake bari ki ga komai a kansa. Sai kin kashe kan ki a banza a kan mutumin nan, gaba ɗaya kin ƙarar da ƙarfinsa a kan ki, wanda ko tabbacin idan ya tuna ki zai miki irin wannan son ba ki da shi" Nana dai kasa magana ta yi, saboda yadda jikinta yake a mace, duniyar take juya mata. Ɗaga bakinta ya yi ya zuba mata wani abu mai kama da turiri, ta yi wani yinƙuri ta hau amai ta hanci da bakinta. Ba ƙaramin galabaita ta yi ba, jin yadda ƙayoyin da suka tsiro a jikin ayabar su na sukar ƙirjinta gurin yinƙurin aman da ta yi.
Cikin fusata mutumin yake magana, "Wane irin wawanci ne haka da shirme da rashin hankali, ta yaya zamu shirya abu ka je ka bari ya ɓaci?"
Cikin damuwa matashin ya ce "Wallahi Tafawa ba laifina ba ne ba, dan har ya fara ci wata yarinya ce ta hana shi ci, wai ya ba ta yunwa take ji"