Buzu book 2 complete - Chapter 39
Buzu book 2 complete Chapter 39: Buzu book 2 complete Chapter 39. Misalin ƙarfe ɗaya da rabi na dare, Nana ta gabatar da sallolinta na dare. Ta zauna tana…
1,424 words
Misalin ƙarfe ɗaya da rabi na dare, Nana ta gabatar da sallolinta na dare. Ta zauna tana karanta Alqur'ani, a hankali sai ta daina ganewa. Ziiiiiiiiii ta fara jin ƙarar guguwar iskar sahara tana tasowa. Ta rufe Alqur'anin a hankali ta ajiye, sannu a hankali sanyi ya fara ratsa ta. Ji ta yi tamkar an buga wani abu da ƙarfi, ta zabura ta miƙe tsaye. Cikin hanzari ta buɗe ƙofar ɗakin da take ciki ta fito corridor da ɗakinta yake ta tsaya. "Imam mene ne haka? Meye haka ka ke yi wai?" Sautin kakarinsa ya daki kunnuwan Nana. Gaba ɗaya ta kasa zaune ta kasa tsaye. Asal ta gani ta fito da gudu daga ɗakin, ta yi waje ta fice daga falon, ta ja ƙofar falon da karfi ta rufe. Gaba ɗaya sai kan Nana ya kulle ta rasa abin yi, ta bi bayan Asal, amma ta ji ƙofar a rufe gam. Ta juya a hankali ta kalli hanyar bedroom ɗin da sautin kakarinsa yake ta fitowa. A hankali ta fara takawa tana tunkarar hanyar ɗakin, duk da ba ta taɓa zuwa ko daf da gurin ba. Zuciyarta na bugawa cike da tsoro ta buɗe ƙofar ɗakin. Wani irin sanyin na'urar sanyaya ɗaki ta dake ta, hakan ya ƙara ninka sanyin da take ji. Wani ni'imtaccen ƙamshi ya ziyarci hancinta. Girman ɗakin baccin har tsoro ya ba wa Nana, ita dai tana mamakin yadda suke abubuwan su kamar babu lissafi, ɗakin kwana kawai an yi shi gari guda. Idanunta ya sauka a kan Sayyid da yake shirin faɗowa daga kan gadon yana jijjiga. Ta ƙarasa da sauri daidai lokacin ya faɗo ƙasa. Ta ɗaukko pillow za ta saka masa, kawai ta ga wannan hoton a ƙasan fulonsa. Cikin mamaki take kallon hoton, tare da mamakin yaya aka yi ya zo kan shimfiɗarsa. Ta durƙusa a kansa, ta kalli jikinsa duk wata jijiya da take jikinsa ta miƙe ta kumbura. Ƙwayar idonsa ta koma fara ƙal, gashin kansa ya hargitse, gaba ɗaya ya koma abin tsoro tamkar wani dodo. Ta yi Bismillah ta zauna, tare da jin sai dai komai zai faru ya faru, ko a mutu ko a yi rai, ko da za a zo a kama ta gara balli ya tashi ko za su ƙaryatata gara duk abin da zai faru ya faru, da bar shi a wannan yanayin da bayan shi kansa babu wanda ya kai ta sanin mawuyacin halin da yake shiga. Tamkar mayen ƙarfe haka ya riƙe ta gam, bakinsa yana karkarwa yana furta "Wuta! Zafi!" Ya danneta a ƙasa ya ƙanƙameta, bakinsa na fitar za kumfa. A hankali ta fara karanto suratul Saffat, ta sanya hannunta a cikin gashin kansa tana shafawa a hankali. Sannu a hankali ya daina wannan gurnanin da yake yi ya yi shiru, sanyin jikinta ya fara ɗibarsa. Ya yin da ita kuma take jin tamkar ana gasa ta a tukuba saboda zafin Jikinsa. Sosai Nana ta ƙanƙame shi ita ma, cike da matsananciyar kewarsa, wasu hawaye da ita kanta ba ta san na mene ne ba, suka din ga sintiri a kan fuskarta.
"Sai ki tashi ki tafi tun da ya samu bacci, tun da ke dai a rayuwarki ba kya tsoron matsala, tarar aradu kawai ki ke yi da ka. Maimakon ki bari mutumin nan ya gane ki, a yi duk wadda za a yi, amma sai ƙoƙarin kunno wa kan ki matsala ki ke yi" Ƙaisar ya yi maganar cike da takaici yana harar ta.
Nana ta ce "Wasu lokutan nasara ns buƙatar sadsukarwa, da kuma tarar aradu da ka. Mu da ku ba irin zubin halittarmu ɗaya ba, ba zan iya jure ganinsa a wannan mawuyacin halin ba. Ina tausaya masa a yanzu fiye da a lokacin da na san shi bai kan sa ba, yake ce mini yana ji a jikinsa rayuwar da yake da ni ya fi wadda ya manta aminci da kwanciyar hankali, ga shi kuma yanzu ina gani. Sai na ƙyale shi a haka?"
Ƙaisar ya yi tsaki ya ce "Allah ya sa shi zai iya yin abin da ki ke yi a kan sa"
Nana ta numfasa ta ce "Dama ba dan ya rama mini nake yi ba"
Sai gefen asuba jikinsa ya saki, ya ci gaba da nannauyan bacci. Ta saka masa filo ta tashi, sai dai jikinta tamkar ana karyata haka take ji, saboda azabar riƙon da ya yi mata. Bayan ta idar da sallar asuba, ta yi adduo'inta ta shiga kitchen. Kafin ƙarfe tara har ta kammala komai, ciki har da gyaran katafaren falon Imam Hammad. Tana son sanin halin da yake ciki, ya farfaɗo ko kuwa bai farfaɗo ba. Tana can tana tunani, shi kuwa tuni ya fito ras da shi, ya hau buɗe-buɗen kwanuka. Har wani murmushi ya yi ganin ƙosai a cikin kayan karyawarsa. Shiru ya yi yana kallon kofin madarar raƙumin da ke gabansa, bayan da ya buɗe ya ga 'ya'yan habbatussauda a kan madarar. Ya ciro wayarsa ya daddana, ya kara a kunnensa.
"Al Hussain"
"Allah ya taimaki Imam Hammad adalin shugaba abin koyi"
"Barka da wannan lokaci ya aiki?"
"Alhamdillah, ina nan tafe cikin Agadez a wannan satin, tun da an ce mini yanzu ana ganin ka"
Imam ya ce "Eh, ammm tambayarka nake son yi"
"Ok Imam, Allah ya sanya ba wani abun aka ce na yi ba"
"Akwai yarinya da Asal ta zo da ita, ta ce a nan gurin cin abinci na Maraɗi ta ɗaukko ta, wata 'yar Nigeria"
Al Hussain ya ce "Haka ne, sai dai ba na nan suka tursasata Gimbiya Asal ta tafi da ita, na ɗauka ma nan gidan cin abinci na Agadez za ta dawo da ita"
"A ina ku ka samo ta?"
Al Hussain ya ji gabansa ya faɗi cike da tsoron, ko wani abin ne ya faru.
"Wani kamfani ne suka kawo ta, da muke neman ma'aikata masu ƙwarewa a fannin girki"
"A nemo kamfanin, da shugaban kamfanin"
"To in sha Allah, amma ina fatan ba wani abin ne ya faru ba?"
Imam ya ce "Sarkin ruɗewa, babu abin da ya faru, ina sauraren ka" Daga haka ya ajiye wayar daidai lokacin da Asal ta shigo.
Ya ɗaga kai ya kalle ta ya ce "Ke ina ki ka tafi ne? Na yi zaton ma ko ki na sashenki ne?"
Ba ta ba shi amsa ba, Sultan ya shigo a rikice. Da mamaki yake kallon su.
Sultan ya ƙaraso cikin hanzari ya ce "Hammad ka na lafiya ya jikin naka?"
Imam ya ce "Ai ni lafiyata ƙalau, tun ranar da na faɗo fa babu abin da ya same ni"
Sultan ya kalli Asal, a rikice ta ce "Wallahi Sultan ba shi da lafiya, ba ka ga riƙon da ya yi mini jiya ba, wasu abubuwa ya din ga yi masu ban tsoro".
Imam ya ɗaga kai ya yi mata wani irin kallo, da sai da hantar cikinta ta kaɗa. Ya gyaɗa kai ya ce "Ni ban san me take magana a kai ba, lafiya ƙalau na kwanta kawai dai ba na jin daɗi kaina yana yi mini ciwo, ban sani ba ko ciwon haukan ne ya motsa mini ba"
Sultan ya ce "A'a ba ka da wani ciwon hauka, kawai dai rashin fahimta ne, ka san ba ka da cikakkiyar lafiya"
Hammad ya miƙe riƙe da kofin madararsa, yana sha a hankali ya ce "Abie zan je na shirya, zan ɗan fita ne"
Ya nufi ɗakin sa.
Asal ta kalli Sultan ta ce "Wallahi Sultan ba ƙarya nake yi ba"
"Na sani, na san ba ƙarya ki ke yi ba, ki yi haƙuri. Dan Allah ki yi shiru da bakinki kar ki gaya wa kowa. Zan san abin da zan yi a kai"
Nana kuwa burgima ta din ga yi a ɗaki, saboda azabar ciwon da jikinta yake yi mata, kamar ta saka ihu haka take ji. Tun da ta jiyo muryar sa sama-sama a falo, hankalinta ya kwanta ta san jikinsa da sauƙi.
Sai dai wunin yau ma ba su haɗu ba, Asal ta ce mata ta ajiye masa Abincin, za a ɗauka a kai masa inda yake.
Ruwan zafi Nana ta dafa, ta shiga ta ya wanka da shi, ko za ta samu afuwa, ta gyara jikinta ta fita. Gidan ya yi shiru saboda dare ne, kowa ya kwanta. Ta shiga kitchen ɗin ta tabbatar komai lafiya ƙalau, sannan ta koma ɗakinta.
Tana shiga ɗakin ta ga duhu an kashe fitila, ta nufi gurin kunna fitilar ta ji an mayar da ƙofar ɗakin an rufe.
Ayshercool 08081012143 1K NE VIA 0069685771 Aisha Adam stanbic bank 💃💃💃