Buzu book 2 complete - Chapter 4
Buzu book 2 complete Chapter 4: Buzu book 2 complete Chapter 4. Sai da aka bar 'yan sanda biyu, gudun abin da ka iya faruwa, saboda matan da abun ya faru a…
3,285 words
Sai da aka bar 'yan sanda biyu, gudun abin da ka iya faruwa, saboda matan da abun ya faru a gaban su, su na ta ƙara balbalawa wutar fetur. Tare da mayar da abin da aka yi da wanda ma ba a yi ba. Gaba ɗaya zancen ya zagaya unguwa. Har sha ɗayan dare case bai ƙare ba, Nana ta farfaɗo ta ga Ummi a ɗakin su, ga duhun dare ya fara yi.
"Ummi lafiya kuwa?"
"Ina fa lafiya Nana, meya haɗa ki da mutanen gidan nan, ga shi ana cewa ke mayya ce".
"Mayya kuma?"
"Eh mana, yanzu case na hannun 'yan sanda, Baba yana can tare da su, ana jiran likitoci su faɗi sakamakon binciken su."
Nana ta gaya wa Ummi iya abun da ta iya tunawa. Sai dai ta sha mamaki, ta ji wai Baba ya zo kan matsalar ta. Ta kalli Sayyid da yake kwance lamo, abin Duniya duk ya dame shi. Sajida ta haɗa kayanta, ta gudu ta ce ba za ta iya kwana da Nana a gidan ba.
Sai zuwa da safe, Likitoci suka tabattar da anemic shock ne ta samu, bayan binciken ƙwaƙwaf da suka yi, suka gano ta yi ɓari sati biyu baya, ta kuma zubar da jini sosai ba ta je Asibiti ba. Ta zo ta yi zazzafan zazzaɓi na typhoid amma suka alaƙanta hakan da mayu, nan ma ba a je Asibiti ba. Hakan ne ya haddasa faɗuwar ta. Bayan fito da sakamakon, mijinta da 'yan uwanta suka ce ba su yarda ba, sakamakon ƙarya ne kawai aka gaya musu. Ga Barira ta farfaɗo, tun a cikin daren ma, har ta ci Abinci, amma suka ci gaba da surutu a kan Nana mayya ce.
Ummi tare da su Nana ta kwana, saboda tsananin tsoro. Dan da gidanta akwai guri can za su tafi ma. Sai dai tashin hankalin abin da ya faru, ya sanya jikin Sayyid rikicewa gaba ɗaya, ya zamana kamar ma ba ya gane wanda yake kansa.
Hankalin Nana ya yi mummunan tashi, ga shi babu isasshen kuɗin tafiya Asibiti. Ta kuma san tashin hankali, da damuwar abin da ya faru ne, ya sanya jikin nasa ƙara rikicewa.
Nana ta rasa abin da yake yi mata daɗi, ga matan gidan kowacce ta koma gidansu, sun ƙi dawowa gidan wai tsoro suke ji. Ummi ce ta yi sallama, Nana ta amsa ta yi mata izini ta shiga ɗakin. Hannunta riƙe kular Abinci. Ta kalli inda Sayyid ke bacci a wahale, numfashinsa na fita sama-sama. Cikin damuwa Ummi ta ce "Yanzu Nana haka jikin nasa ya koma?"
"Wallahi Ummi, gaba ɗaya hankalina a tashe yake"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ana wata ga wata"
Cikin damuwa da rashin fahimta ta ce "Me ya faru?"
Cike da karaya, da matsanancin tausayin ƙanwarta ta ce "Mai gidan nan ne, ya je ya same ni, ya bani dubu goma sha biyu, wai ga sauran kuɗin ku nan, ku tashi. Ba ya son tashin hankali, kuma ga sauran 'yan hayar sun ce ko ku tashi, ko ya mayar musu da kuɗinsu su tashi. Nayi-Nayi ya ƙara wani abu, tun da ko wata ba ku yi ba, amma ya ƙi wai wannan ɗin ma da ƙyar ya samo su ya kawo."
Nana ta jingina da jikin bango tana maimaita "Innalillahi wa Innalillahi raji'un"
"Nana mene ne abin yi yanzu?"
Nana ta girgiza kai, jiki a sanyaye ta ce "Ban sani ba Ummi"
"To ko wani gidan za a nemo? Sai na koma na neme shi, na roƙi alfarmarsa?"
Ta girgiza kai ta ce "A'a Ummi, an riga an yi mini mummunan tambari a unguwar nan, abu ne mai wahala ma mu sake samun wani gidan a unguwar nan"
"Bari na kira Baba na ji me zai ce"
Nana ta ce "A'a Ummi, kin san halin Baba, kar ranki ya ɓaci"
"To Nana ya zamu yi, dole a kira shi mu ji me zai ce" Ummi ta kira lambar Baba, yana ɗaga wayar muryarsa a sama ya ce "Ya kuma aka yi, ba an kashe case ɗin a gurin 'yan sanda ba?"
Ummi sai da ranta ya sosu, amma ta maze ta ce "Baba ba wannan ba ne. An kori su Nana daga gidan da suke ne, mai gidan da suke ya ce sai sun tashi"
"To sai kuma aka yi yaya? Ni zan nemo musu wani gidan? Ko kuma mijinta ne yakamata ya nemo musu wani?"
"Baba ka fa zo gidan nan, ka ga halin da mijin nata yake ciki na rashin lafiya, saboda haka aka kore shi daga gurin aikin gadi. Dan Allah Baba ka yi wani abu a kan yarinyar nan. Nana yarinya ce ƙarama pressure ta yi mata yawa."
"To Ummi ya ki ke so na yi? Ni dai nan gidan babu gurin da zan ajiye ta, ita da mijin nata, idan kuma ke ki na da guri ki taimaka ki ba su. Idan ba haka ba ta nemo 'yan uwansa su ɗauke shi, su rakata inda danginsa suke. Kin san dai nan gidan idan ta dawo, abin da za ta ci ma aiki ne. Nima yanzu sai abun da aka samo aka bani"
Hawaye ya cika idon Ummi, cike da takaicin yadda Baba bai fiye damuwa da damuwarsu ba. Ta ce "Baba da ina da inda zan ajiye Nana da mijinta, wallahi ba zan kira ka ba"
Nana ta ce "Ummi, dan Allah ki katse kiran nan, nima ba zan koma can gidan ba."
Tarin Sayyid ta ji, ta mayar da hankalinta kan sa, ta nufe shi tana faɗin "Sannu Sayyid"
"Ki ba ni ruwa" ta amsa da to. Ta ɗaukko ruwan leda, ta buɗe masa ya tashi zaune ta fara bashi.
"Sannu Sayyid" Ummi ta faɗa cikin tausayawa, kallo ɗaya ta yi masa ta gane yana jin jiki. Da da ne, kome za a yi,ba zai bar gashin nan a buɗe ba. Amma yanzu ba ta gashin yake yi ba, ga fuskarsa duk ta kumbura. A zuciya irin ta Nana, ta san ko a titi ta tsince shi a wannan yanayin, ba za ta iya tafiya ta rabu da shi ba, balle mijinta.
Ƙarar da wayarta ta yi ne, ya sanya ta dawo hayyacinta. Ta ɗaga wayar tare da yin sallama.
"Ke Hansai, ina ta kiran wayar ki, amma ki ka ƙi ɗagawa?"
Ummi ta ce "Eyya, ba haka ba ne Uwani,ba na kusa ne, ya gida ya mutanen garin?"
"Lafiya ƙalau, ya na ji muryar ki ƙasa-ƙasa, laulayi ko rashin lafiya"
Ummi ta yi yaƙe ta ce "Ba gara a ce laulayi nake ina kwance ba, da abin da yake faruwa"
"Subhanallah, meyafaru?" Kasancewar Uwani kaka ce a gurin su Nana, ƙanwar kakarsu ce, da kakarsu wadda Nana ta ci sunanta da Uwani, uwa ɗaya uba ɗaya suke. Sai dai ita tana can Garko da iyalinta. Ummi ba ta ɓoye mata komai ba, ta gaya mata. Uwani ta rafka salati. Ta ce "Sai an yi magana ku nuna ku mutanen birni, kun fi mutanen karkara wayewa. Ina wayewar take. Aikuwa sai na kira Isa na ci ubansa mara mutunci. Tuntuni nake ganin take-takensa kamar har da ƙiyayyar uwar su, take shafar su a gurinsa. Ai Imrana yana zuwar mini nan. Ya hana kowa riƙe su kuma shi yana yi musu riƙon sakainar kashi. Yanzu ina duk sauran 'yan uwanki Ummi, ina 'ya'yan Atine, ina su Gaddafi da ba za ku iya taruwa ku rufa wa 'yar uwakku asiri ba?"
AREWABOOKS "Wallahi Uwani mun yi iya yinmu ne.."
"Rufe mini baki, ina wani iya yinku, kuma duk wanda ya ce mana mayu Allah ya isa bamu yafe ba. Mu bamu gaji maita ba, balle a saka yarinya a gaba a tsangwame ta. Na san babu lallai ta iya zaman ƙauye, amma mu nan akwai ɗakuna, har ma da gida da babu kowa, idan za su iya zama ta yi jinyarsa. Babu mai damun ta, kuma babu mai cewa ta tashi. Amma tabbas kun ji kunya, idan har ku ka bari Asma'u ta wulaƙanta, a ce an rasa inda za ta zauna, ta yi jinyar mijinta, yawan ku kun zama taron tsintsiya babu shara." Ummi ta yi shiru, Uwani akwai kirki da karamci, amma idan ta botsare tana faɗa, to duk gaskiyar ka, sai dai ka yi haƙuri. Ta gama faɗan ta, Ummi ta kashe wayar.
Ta kalli Nana, ta ga yadda ta tattara hankalinta a kan mijinta, tana ba shi Abincin da ta kawo musu, sai lallaɓa shi take, da alamu abincin ma ba ya so.
"Nana, kin ji abin da Uwani ta ce?"
Nana ta girgiza kai ta ce "A'a.
"Cewa ta yi idan za ki iya zama, ku tafi can Buda ki kula da shi, akwai inda za ku zauna. Kin ga nan tun Baba ya san maganar maitar nan, kamar Mama ta ji ne. Ita kuma kin san gishiri za ta ƙarawa abin ta yi ta bayar da labari. Amma ban sani ba ko ki na da wata shawarar?"
"Ummi wace shawara? wanda yake ruwa ko takobi aka miƙa masa, ai karɓa zai yi. Sai dai shi nake tausayawa, amma ba ni da wata mafita da ta wuce wannan ɗin. Ni in dai zan samu inda zamu zaune na kula da shi, ba komai zan zauna ko a cikin dutse ne ba ƙauye ba"
"Kin tabattar Nana? Da wayonki fa sau ɗaya Baba ya taɓa bari, muka je muka kwana biyu"
Nana ta ce "Ba komai, zan zauna"
Sayyid ya sanya hannunsa biyu, ya damƙe na Nana. Nana ta kalle shi ta ce "Sayyid, mene ne?"
Idanunsa sun kaɗa sun yi jawur, wata jijiya a saman goshinsa ta ɗaga ta kumbura, fuskarsa ta yi jawur. Laɓɓansa sauka din ga karkarwa yana son ya yi magana, Nana ta girgiza kai ta ce "Ba sai ka yi magana ba Sayyid. In sha Allah duk rintsi ina tare da kai, har Allah Ubangiji ya baka lafiya" Ummi ta kasa jurewa ta fashe da kuka.
Nana ta ce "Ummi idan ki ka yi kuka,ni ya zan yi? Kun saka ni a tsakiya, nama fi ku juriya, har da kai ma" ta yi maganar tana murmushi bayan saka idanunta cikin na Sayyid, duk da idon nata a cike da hawaye.
"Ummi ki gaya wa Uwani na amince"
Ummi ta share hawayenta ta ce "To shikenan, ya za a yi tafiyar to?"
"Ina ga a sayar da kayan ɗakin nan, katifar ta ishemu, sai a sai ledar ɗaki, sai kayan sawarmu"
"Nana, kina amarya amma a ce ɗakin ki babu kayan ɗaki, haka za ki je ki zauna? Kin san mutanen ƙauye ba sa raina abin surutu dai"
"Ummi ai ba ado da kwalliya zan je ba. Kuɗin kayan ma riƙe saboda ɗawainiyar abinci da kuma magani"
Ummi ta ɗan yi shiru ta ce "Kuma haka ne, yanzu zuwa gobe in Allah ya kaimu, zan samo dillalai su saya"
Cikin sauri Nana ta ce "A'a Ummi, ba na son ci gaba da zama a unguwar nan, ban san me za su yi mana ba. Idan da hali a nemo su yau kawai. Su saya gobe in Allah ya kaimu mu tafi"
"To shikenan, bari na fita na gani"
*****
Yana zaune a cikin office ɗin sa, ya ɗora ƙafafuwansa a kan tebur, yana juyi, ya din ga kiran lambar cike da fatan a ɗauka. Har ya yanke tsammani, kawai ya ji ta ɗauka, sai dai ta yi shiru.
Da sauri ya sauke ƙafafuwansa ya ce "Hello" ta yi shiru ba ta amsa ba.
"Hello ki na ji na?"
"Eh" ta amsa a raunane.
"To ba za ki yi mini magana ba?"
"Ba cewa ka yi ba ka gane ni ba, ranar da na kira ka?" Ya ɗan yi guntun murmushi ya ce "Ki yi haƙuri, sai daga baya na ɗauki muryar ne. Ya ki ke ina fatan kina lafiya?"
"Ai baka damu da ina lafiya ba, tun da ka sake ni baka ƙara nema na ba, saboda ka yi aure matarka ta haihu, dama ni haushina ka ke ji, ba na haihuwa" "A'a Yusra, kar mu fara haka da ke. Kin san ko bayan mun rabu, na yi ta neman lambarki, amma ba ta shiga har na haƙura. Ya jikin ki?"
"Da sauƙi, amma ni ba mahaukaciya ba ce"
Sagir ya ce "Ai dama ban ce ba"
"Lokacin da muna tare ai ka ce" ya yi murmushi ya ce "Wannan ba ya wuce ba? Amma Mami ba ta san kin kira ni ba ko?"
"Eh, ina gidan Mummy Zahra, da wata na haɗu sunanta Nana, ita ma ta san irin rashin lafiyata. Ita ma tana yi"
Ya ce "Haba dai?"
"Wallahi. Ita ta din ga ba ni shawara, ita ce ma ta ce na kira ka fa, na ma zata ba zaka ɗauka ba, ka ɗauka amma ka nuna ba ka gane ni ba" dariya ya yi ya sakankance sosai, yana sauraren Yusra. A yanayin surutun da take yi, ya fuskanci jikinta da saura, ba ta warke ba, amma ya tattara hankalinsa yana sauraren ta. Hirar ta din ga tuna masa da yadda suka zuba soyayya a baya kafin aure. Yana kallon kiran Shukura amma ya ƙi ɗagawa ya ba wa Yusra lokacin sa.
"Ki na ji na"
"Eh"
"Yanzu ina gurin aiki, kuma lokacin salla ya yi, zan sake kiran ki, in sha Allah"
"Tom sai anjima"
"To 'yar farata, bye-bye"
Kamar tana gabansa ta saki murmushi, cike da sanyin jiki, saboda ta yi kewar jin sunan.
Shi ma murmushin ya yi, yana tuna wasu abubuwa da suka wuce.
Ya kira Shukura, sai da ta kusa katsewa sannan ta ɗaga. "Madam ya aka yi ne?"
"Ina ta kiran ka, kana waya, har da rejecting kirana"
"Sarkin ƙorafi, kin san da wa nake wayar ne?"
"Ai ba sai ka gaya mini ba, na san 'yan matanka ne"
"Ni ba da 'yan mata nake waya ba. Ya aka yi?"
Shukura ta ce "Ba komai"
"Madam Shukura, bakomai ɗin ki, na nufin akwai komai. Yanzu dai a yi mini afuwa da ni da 'yan matan nawa."
"Ni shikenan kawai" ta kashe wayar. Ya girgiza kansa tare da ɗan lumshe idonsa.
****
A ranar dillalai, suka saye wardrobe da mudubin Nana, da sauran kayan da take ganin za su zame musu shirgi. Ta tattare musu kayan su cikin bagcco, duk wani kayan amfaninsu ta tattare. Da safe ƙarfe goma, ita da Ummi suka je suka samo taxi. Har fargaba take yi kar mijin Ummi ya yi ƙorafi a kan yawon da take yi saboda ita. Duk da ba mazauni ba ne. Suka yi cinikin a nawa zai kai su Garko cikin ƙauyen Buda. Aka ɗaure katifa a saman taxi, aka loda kayan su a ciki. Ummi ta shiga gaban motar, ita da babbar 'yar ta Islam. Nana kuma suka shiga bayan motar, tare da Sayyid. Ya kwanta a jikin Nana ya yi shiru, ita kuma ta riƙe hannunsa tana matsa masa a hankali cike da kulawa.
Awa ɗaya da rabi, suka isa har cikin garin Buda. Sai dai shigar su garin ke da wuya, Nana ta fara jin sanyi yana ratsa ta. Addu'a ta din ga yi, a kan Ubangiji Allah ya rufa mata asiri, ya kawo musu ɗauki, ya shiga tsakaninsu da su Ƙaisar.
"Ma vie" ta ji ya yi magana.
"Na'am Sayyid" Sai kuma ya yi shiru, bai sake cewa komai ba. Yara suka firfito suka tatstsaya bayan ganin mota ta tsaya a ƙofar gidan Uwani.
Uwani da kanta ta fito tana tafa hannu, tana "Maraba da mutan birni. Ina yayar tawa take?" Nana ta buɗe motar ta fito tana murmushi.
Ummi ta sallami mai motar, Uwani ta ce "Ina mai gidan?"
Nana ta buɗe taxi ɗin, ya fito a hankali, kansa rufe da mayafi.
Uwani bakinta fal magana, amma ta haɗiye ta yi musu maraba, zuwa cikin gidan. Babban gida ne mai ɗauke da ɓangarori. Ta kai su sashen ta, aka yi shimfiɗa Sayyid ya zauna ya jingina da bango. Abin da dai ba ya ƙauna, ya sake tararwa a garin, kallo. Ba ya son a zura masa ido, amma ya lura da yadda ake ta kallon sa.
Uwani ta karrama su da ruwan pure water, da abinci shinkafa da wake.
Ummi ta ce "Kafin cin abinci, Uwani a ina za su zauna, a gyara musu?"
Sai da Uwani ta sake yi wa Ummi ta tas, tamkar ita ce Baban, sannan ta kalli Nana ta ce "Yayata, kin ga cikin gidan nan, akwai ɗakuna, idan ma ba zaku zauna a nan ba, nan baya tafiyar babu nisa, akwai gida da ɗakuna biyu da tsakar gida. Babu kowa a gidan idan za ku zauna".
Nana ta ce "Gara su zauna a inda babu kowa"
Ummi ta ce "Maimakon ku zauna a cikin mutane, yadda ko wani abin ne, a taimaka muku"
Nana ta ce "Akwai dalili gara mu zauna inda babu kowan" Nana kuwa ta yi hakan ne, domin samun rufin asiri na larurar da suke fama daga ita har Sayyid. Ga uwa uba takura da Sayyid ba ya so.
Uwani ta saka yara, su ka je su ka share gidan tas, aka wanke.
Nana ta ce "Sayyid, bari mu je da Ummi, a gyara gidan, sai mu zo mu tafi da kai" Ya saka hannu ya riƙe nata, tare da girgiza mata kai alamar a'a.
"Mu tafi tare za ka iya tafiya?" Ya jinjina mata kai alamar eh.
"To ta so" Ya yinƙura a hankali ya tashi tsaye.
Uwani ta ce "Nana, ku bar shi a nan mana, tun da ba shi da lafiya, ke ku je, ku gyara gidan"
Nana ta ce "Ai ba zai zauna ba, ya ce bin mu zai yi"
"Ikon Allah, ni da bita zai-zai, to Allah ya taimaka" Nana ta yi murmushi kawai, tare da jin nauyin abin da Sayyid ɗin ya yi.
Sauran yaran gidan Uwani, suka bi su Nana, su taya su shirya kaya. Wanda galibi Nana ba ta ma san su ba, saboda ba zuwa garin suke yi ba, domin ita rabonta da garin ma, har ta manta. Gidan ƙasa ne tsura, da zunzurutun turɓaya Ɗaki ɗaya ne gyararrre, sai aka yi masa siminti, da plasta, aka shafa farar ƙasa, da ƙofar langa-langa. Sai wani ɗakin kuma, si kuma ko rufi babu, sai banɗaki. Duk lalacewar gidan su Nana ya fi nan nesa ba kusa ba, Ummi jarumta kawai take yi, zuciyarta a cunkushe babu daɗi, biyo bayan tuna cewar a nan Nana za ta rayu. Sai dai ta ga tsantsar tawakkalli a fuskar Nana. Su ka gyara ɗakin aka shimfiɗa leda, sai katifar su. Sai kuma tarin kayan su, na girki sai na sakawa a cikin bagco. Uwani ta aiko musu da Abinci. Da la'asar bayan Ummi ta yi salla, ta ba wa Nana kuɗin barkononta da aka sayar, ta yi ta mata nasiha da kwantar mata da hankali, sannan ta yi musu sallama. Ɗan gidan Uwani ya ɗauke ta a kan babur, ya tafi da ita.
Nana ta ƙarasa gaban Sayyid, da ya zuba mata idanu tamkar bai taɓa ganinta ba.
Ta riƙo hannayen sa ta ce "Sayyid, duk da ban san wace irin rayuwa ka yi a baya ba. Amma wadda muka yi, mun yi ta ƙarƙashin kulawar su Habu, ba mu taɓa neman abu mun rasa ba. Amma Allah shi ne abin godiya. Wannan yanayin da muke ciki, ba zai dauwama ba in sha Allah. Ina fatan Allah ya baka lafiya, ya kuma baka haƙuri da juriyar a yanayin da muka tsinci kanmu a ciki".
Ya sanya tafukan hannayen sa biyu, a fuskarta laɓɓansa na rawa, amma magana ta gagara.
Ta girgiza masa kai tana murmushi, ta ce "Ruhinka yana cikin jikina, kar ka damu kanka lallai sai ka yi magana. A jikina ina jin abin da ka ke son faɗa" ɗan guntun murmushi ya yi, duk da yadda yake matuƙar son ya furta wani abu.