Buzu book 3 complete - Chapter 23
Buzu book 3 complete Chapter 23: Buzu book 3 complete Chapter 23. "Shhh, Babu abin da ki ka yi mini na ba dai-dai ba Nana. Sai dai tashin hankali da…
4,333 words
"Shhh, Babu abin da ki ka yi mini na ba dai-dai ba Nana. Sai dai tashin hankali da fargaba na shige shi, na rashin sanin inda ki ke, da kuma wani hali ki ke ciki, ga tsohon ciki kin tafi kin bar gida. Amma Imrana ya zo inda nake, tare da Yayan mijinki, sun yi mini bayanin komai. Nana na yi sujuda na gode wa Allah, ba wai domin daular da ki ke ciki ba, ko kina auren wani ba, sai domin murnar kina cikin ƙoshin lafiya tare da ke da yaronki. Sun ce kar na gaya wa kowa, babu wanda ya sani, amma sun zo sun yi mini alkhairi Imrana ya zama babban mutum ya nutsu, kema hankalinki yana kwance. Ni dai fatana su yi su kawo mini ke, ko na wanko ƙafata na taho,amma sun ce na yi haƙuri kaɗan"
Cikin kuka Nana ta ce "Ni dai ki yafe mini dan Allah, tashin hankalin da na sanya ku a ciki, dan Allah ku yi haƙuri Umma" Imrana ya karɓe wayar ya ce "Umma sai anjima, da na sani ban haɗa ku ba, nema take ta rikice"
**** Hajiya Amina tana zaune tare da Alhaji Zailani, tana ta lallaɓa shi a kan ya ci abinci, amma ya ƙi ci, saboda shikaɗai ya san bala'in da yake ciki. Tun da ya yi mafarkin an huda saitin zuciyarsa, dodon ƙungiya yana sha masa jini, ya farka ya ji saitin zuciyarsa ya yi masa wani irin nauyi. Ga jikinsa sai yi masa wani irin raɗaɗi yake yi, kamar ya yi wanka da yaji. Yana jin yadda wayarsa take ta ringing amma ya ƙi ɗagawa. Daga ƙarshe, Hajiya Amina ta saka hannu ta ɗauki wayar, ta saka a kunnenta tana sallama. Jin ta yi shiru ya sanya Alhaji Zailani ɗagowa ya kalle ta, sai dai ta tsare shi da idanunta ba ta ce masa uffan ba.
Jiran Hajiya Amina yake yi ta yi magana, amma ta yi shiru ba ta yi magana ba. Jiki babu ƙwari ya ce "Ya dai? Meyafaru?" Jiki a sanyaye ta ce "Daga makarantar su Yusuf ne, wai yana kwance a Asibiti babu lafiya, yau kwana uku kenan" Ya waro ido ya ce "Yusuf ɗin?" Ta jinjina masa kai. "Ki kira su ki gaya musu, ni ba ni da lafiya, babu lallai na iya driving su dawo mini da ɗana gida" Hajiya Amin ta jinjina kai tare da mayar da hankalinta kan wayar.
*****
Gidan Baba ya zama tamkar maƙabarta, babu walwala ko kaɗan, ko ƙaunar tunkarar gidan baya son ya yi. Saboda matsananciyar damuwa, da takaicin abubuwan da suke faruwa a gidan. Jamila kuwa kullum tana ɗaki, dan ta sha baƙar azaba, sai da ta kwana tara a Asibiti, da kyar aka samo kanta kamar ba zata rayu ba. Ya daina shiga harkar Mama da yaranta gaba ɗaya, ko abincin gidan ya daina ci. Ga damuwa da kewar yaransa Nana da Imrana da suka addabi zuciyarsa. Ya fito daga cikin gida da buta a hannunsa, ya yi alwalar sallar Azahar sai ga wata danƙareriyar mota irin ta matafiya, sabuwa gal sai ƙyalli take yi ta shigo layin. Bai damu ba, ya idar da alwalarsa ya ɗaukko wayarsa, yana son kiran can Buda, saboda yaga kiran wayarsu, bai samu ya ɗaga ba. Sai ya ga motar nan an tsaya da ita a ƙofar gidan. Sai ya yi tsuru yana kallon motar. Sulei ne tare da Mahmoudu suka fito, suka nufo Baba. Ya tsaya saroro har suka ƙaraso inda yake. Suka durƙusa har ƙasa suka gaishe shi, ya amsa musu yana bin su da kallo, kasancewar sun rufe fuskokinsu da takunkumi. Bayan sun gaisa, Mahmoudu ya ce "Baba mu na tare da baƙi ne daga Agadez" Baba ya ɗan yi shiru, shi dai ya san babu wanda ya sani a Agadez, amma ya miƙe ya ce "To bari na kawo muku abin zama" Ya tashi ya shiga cikin gidan, ya ɗaukko tabarma ya shimfiɗa musu, ya koma ya aiki Nasiru ya sayo ruwa. Ya zata iya su Mahmoudu ne baƙin, kawai ya ga Sulei ya je ya buɗe motar, wani dogon mutum mai jiki ya fito da wani matashi, shi ma sanye da rawani suka fito, suka nufo shimfiɗar. Shi dai Baba duk abin ya ɗaure masa kai, tsoro ya shige shi. Ya yi musu barka da zuwa, suka zazzauna, Mahmoudu ya sauke rawanin fuskarsa ya ce "Baba baka gane ni ba?" Baba ya yi shiru ya ce "Kamar dai na sanka, amma ban gane ka ba" Imam Zahradeen ya sauke rawaninsa shi ma, shi ma dai Baban ya yi masa kallon sani. Mahmoudu ya ce "Baba kamar baka gane mu ba ko?" Baba ya ce "Gaskiya dai" "Baƙi ka yi daga Agadez"
"To bawan Allah, ni wa nake da shi Agadez, kuma ba ɓatan kai ku ka yi ba?"
Mahmoudu ya ce "Ba mu yi ɓatan kai ba, na yi mamaki da ka ce ba ka gane ni ba, amma ai ka tuna buzun da ka aura wa 'yarka shekarun da suka gabata" A razane Baba ya ɗago ya kalli Mahmoudu, sai kuma ya riƙe rigarsa, ya ce "Dama ku ne? Ba ku yi mini adalci ba, ku ka tattara ku ka gudu, ku ka bar mini 'ya da jinyar ɗan uwanku, shi ma daga ƙarshe ya gudu ya bar ta, saboda wauta da rashin hankali wai ta tafi Niger neman shi, haryanzu shekara ta uku kenan, babu wanda ya san inda take, baku kyauta mini ba" Baba yayi maganar yana kuka kamar ƙaramin yaro.
Imam Zahradeen ya ce "Baba, ka yi haƙuri abubuwan da suka faru ba a kyauta maka ba. Amma mu na da kyakyawan albishir ne"
Baba ya ce "Kai ba kai ne mijin nata ba?" Yayi maganar yana nuna Imam Zahradeen. Zahradeen ya ce "Baba ai na fi wancan tsufa, shi ya fi ni ƙuruciya, ya kuma fi ni kyau, ni yayansa ne. Zancen da nake yi maka, a kowane lokaci mahaifinmu zai iya aiko da mutanensa daga Agadez da kayan auren Nana za a sake gagarumin bikin aurensu"
Baba ya ce "Ashsha! Yarinyar da nake gaya muku shekara uku babu wanda ya san inda take, kuma babu wanda ya waiwaye ta tunda ku ka gudu kuka bar ta. Kuma ni mene ne haɗina da Sarkin Agadez da zai kawo kayan aure? Ni dai na yi nadamar abin da na aikata na aurar da 'yata ga mutumin da ban san daga inda yake ba" Imam Zahradeen ya lura ran Baba a ɓace yake. Ya sassauta murya ya ce "Baba sunana Imam Zahradeen Jalaludeen Agadez, ni Yaya ne ga Imam Hammad Jalaludeen Agadez. Kuma 'ya'ya ga Sultan Jalaludeen Agadez, wato Sarkin Agadez na yanzu. Buzun da ka aura wa 'yarka, ɗan uwana ne, kuma ɗa ne ga Sultan na Agadez."
Baba ya kalli Imam Zahradeen kamar yana raina masa hankali. Ya ce "Ɗan sarki ne zai zo baro ƙasarsa ya zo Nigeria yana aikin gadi?"
Mahmoudu ya ce "Baba, idan baka manta ba, ko lokacin da aka yi aurensu, a yanayi na rashin lafiya yake, rashin lafiya ce ta kama shi"
"To yaya za a yi a ce ɗan sarki ya zo Nigeria gadi, ni abin ya bani mamaki ne. Kuma na kasa yarda, ni kar ku sake dugunzuma mini hankali bayan halin da nake cikix
Zahradeen ya ce "Baba ba dunguzuma maka hankali za mu yi ba. Mun zo mu sanar da kai batun zuwan baƙinka ne daga Agadez, kafin su zo ɗin."
"To wai su zo, su yi mini me?"
" 'yarka Nana, tana gurinmu tare da ɗanta Muhsin" Baba bai san ya aka yi ya tashi tsaye ba, yana zazzaro ido ya ce "Nana Asma'u dai 'ya ta? Yaya aka yi ku ka same ta? Tana ina? Kun taho mini da ita?"
Mahmoudu ya miƙe tsaye ya ce "Baba shi ne bayanin da muke yi maka, Nana tana tare da mu, za a kawo dukiyar aurenta Nigeria za kuma a yi bikin aurensu sosai da sosai. Duk abin da za mu gaya maka yanzu ba za ka fahimce mu ba, saboda a cikin damuwa ka ke, kuma abubuwan da suka faru su na da tsawo da sarƙaƙiya akwai buƙatar a yi maka bayani daki-daki. Ba Nana ba hatta Imrana yana tare da mu a Agadez, akwai tarin bayanai da sai ka nutsu, an yi maka bayani zaka fahimce su"
"Amm bawan Allah, ni ko yanzu a shirye nake, mu tafi Agadez ɗin na karɓi 'ya'yana. Bayan Nana kuma me ya haɗa ku da Imrana"
Imam Zahradeen ya ce "Alkhairi ne, a cikin satin nan, zuwa mai kamawa in sha Allah; za a sake turo maka baƙi daga can. Kuma za a yi bikin su al'ada saɓanin yadda ya gudana, kuma za a yi maka bayani kamar yadda nake nanata maka. Amma kafin nan mu na son za a gyara maka gidan nan, ko kuma a canza maka wani"
Baba ya girgiza kai ya ce "Ba na buƙatar haka, muddin Nana yake so, babu amfani a raina inda ta fito, ni dai fatana na gansu cikin ƙoshin lafiya"
Zahradeen ya ce "Ba raina maka aka yi ba, matsayinka da girmanka ne ya sanya za a yi maka." Fafur Baba ya ƙi yarda da hakan, da kyar suka rarrashe shi suka tafi, dan cewa ya yi ba za su bar ƙofar gidansa ba, ba tare da ya ga yaransa ba. Kasancewar duniya makarantar da ko babu malami, ta biya maka darasi dole ka ɗauka ce, ta karanta wa Baba darasin da duk son abin Duniyarsa, yanzu tsoro yake ji. Zuwansu Imam Zahradeen babu wanda ya sanarwa, saboda gani yake yi tamkar ƙarya Buzayen nan suka zo suka sharara masa. Ya kasa gaya wa kowa, sai Uwani ya kira ya sanar mata. Sai dai a ƙarshen maganar Baba ya ce "Amma Uwani ni ban ji na yarda ba, ji nake kamar ƙarya kawai suke yi ban ji na yarda ba" Uwani ta ce "Alhamdillah, ni dai na ji na yarda har cikin zuciyata. Ko ba hakan ba ne, ina fatan Allah ya tabattar da shi ya zama gaske. Wallahi zuciyata ta daɗe tana bani, mijin Nana ba ƙaramin mutum ba ne, to ita Nanan da gaske tana gurinsu, kuma har da Imrana sun haɗa ku ko a waya ne?"
Ya ce "A'a, shiyasa na kasa yarda ma gaba ɗaya"
"Isa, yarda ni dai na gama ta, zamu duƙufa mu ci gaba da addu'a in sha Allah Nana suna cikin kwanciyar hankali tare da ɗan uwanta" Kalaman Uwani suka ɗan ƙwarara wa Baba gwiwa. Bayan sallar isha'i ya shiga gida, yana zaune yana jin radio, Mama tana cikin ɗaki tare da Jamila da ta koma so silent, ko magana ba ta iya yi. Ihun da Jamila ta yi ne, ya sany Baba jifa da radio ya tashi tsaye yana rarraba ido. "Mama! Mama!! Dan Allah ki taimake ni, dodon ƙungiya zai shanye mini jini. Hajiya Sa'a kin cuce ni, kin cuci rayuwata, na kasa samun aminci da salama. Na baku Abba me kuma ku ke nama a gurina?" Cikin rashin fahimta duk suke kallon Jamila, Baba ya ce "Me yarinyar nan take faɗa ne haka?" Mama ta ce "Nima ban sani ba wallahi, ina ga jikin ne ya motsa." Baba ya ce "Jikinta ya motsa kuma take irin wannan maganganun?" Ba ta ko saurare su ba, ta ci gaba da surutanta. "Ni ban so shiga kungiyar nan ba, dole ki ka yi mini, ga shi kin sanya ni a bala'i, na rasa mutuncina, kin saka nayi kisan kai, yanzu kuma na kasa samun kwanciyar hankali, sai tsorata ni ake yi, nima ana nema na a kashe ni, kin cuce ni" Baba ya ce "Jamila, meyafaru ne? Me ki ke faɗa wai?"
"Baba riƙe hannuna, Baba ku taimake ni"
Ya ƙarasa ya riƙe hannun Jamila, cikin kuka ta ce "Baba na shiga uku, na aikata mummunar ɓarna, Baba hakki ne zai yi ajalina"
Baba ya ce "Jamila, ki gaya mini, me ki ka aikata?"
"Ƙungiyar asiri, Baba ƙungiyar asiri aka shigar da ni, saboda na kai jinin Nana"
Kamar ta watsa wa Baba wuta, haka ya fizge hannunsa ya ja da baya, yana kallon Jamila da take ta uban kuka. Mama ta ce "A'a baban su Jamila, dan Allah kar ka yarda da abin da ta faɗa, ka san ba ta da cikakkiyar lafiya, wataƙila zafin ciwo ne, amma wace irin magana ce wannan, a ina Jamila za ta ga wata kungiyar asiri ta shiga"
Alhaji Zailani ne a durƙushe a gaban gawar ɗansa Yusuf, bayan an dawo da shi daga makaranta, dama babu rai aka dawo da shi. Ba shi ne abin da ya ɗaga masa hankali ba, sama da ganin busashshen jini a baki da kuma hancin Yusuf. Ba dan ya yi iya ƙoƙarinsa ba, da tuni ya aikata abin da zai fallasa kansa. Wani irin raɗaɗi da zafi ya din ga ji a zuciyarsa ya kasa magana, ya kasa ko ƙwaƙwƙwaran motsi. Ba a jima ba, gidansa ya cika da jama'a, Hajiya Amina sai kuka take, ga Shukura ta ɓata, ga kuma mutuwar Yusuf. Ya hau neman lambobin yaransa, da ya sanya su kashe Shukura, a kan kar su kuskura su kashe ta, amma ya kasa samun su. Duk da daɗewar da yayi yana aikata zalunci kala-kala, mutuwar Yusuf ta dake shi, ta tsaya masa. Ya din ga jin tamkar ya yi ta kururuwa yana burgima, ko zai ji daɗi. Ko da aka yi jana'izar Yusuf, Alhaji Zailani tafiya ya yi ya kulle kansa a ɗaki. Kaf yaransa babu kowa sai Shukura yanzu, Shukuran ma ba a san inda take ba. Kuma ita ma baya tsammanin za ga tsallake sharrin dodon ƙungiya, tun da ya gaza bashi jinin shekara.
Sosai ake ta shirye-shiryen gudanar da bikin auren Imam Hammad, da matarsa 'yar Nigeria. Ita Nana abin har mamaki yake bata. Tun da Sultan ya amince da auren Nana da Sultan, Nene take sintiri kawo wa Nana kayan gyaran jiki. Ban da matar da ake ware mussaman Nene take zuwa da ita, take yi wa Nana wani irin gyaran jiki na mussaman. Nana ta ce "Nene duk wannan abin fa ihu ne bayan hari" Nene ta ce "Ke, gyaran ne ba kya so?" "To Nene ya riga ya sanni a yadda nake, me kuma zan gyara?"
Nene ta ce "To kar ki gyara, komai yana buƙatar gyara ai" Aka ajiye wa Nana kayan sakawa, da na ado irin na Buzaye. Nana ta ƙudurce a ranta, bayan ta tare, kayanta na 'yan Nigeria za ta saka Hammad ya ajiye mata, saboda ita ma tana son tata al'adar. Shi kansa Hammad ya so a ƙyale masa ita a haka, dan shi komai nata ya yi masa. Sai dai gyaran jikin da ake yi matan ba ƙaramin kyau take yi ba. Ga shi tare da Muhsin suke kwana da Nene, hakan ya ƙara sanya ta farin ciki. Hammad ya ce ta fita ta ɗan zagaya, amma ta sanya takunkumi ta rufe fuskarta. Har mamaki Nana take yi, yadda idan Muhsin ya ga raƙuma ko shayi, kamar zai tashi sama saboda murna. Sarkin baka ta hango, suka nufe inda yake. Cikin jinjina ya ce "Barka da tattaki uwar gijiyata" Nana ta yi dariya ta ce "Dan Allah ka daina kunya ka ke bani" Shi ma yana murmushin ya ɗago ya kalli Nene, ya ce "Ni kuwa dama ina ta son na yi miki magana, Allah bai yi ba"
Nene ta ce "Ni ɗin ko? Ka sanni ne?"
Ya ce "Eh, ai duk inda muka ga juna, muna gane kanmu"
Ta yi dariya ta ce "Na ji, ai ban yi zaton haryanzu akawai abin da tattare da ni ba"
Sarkin baka ya ce "Ni na ji na gane ai. Kuma ni ɗalibin marigayi Sa'adu Aska ne"
Nene ta waro ido ta ce "Kana nufin Babana?"
Sarkin baka ya ce "Ƙwarai da gaske, ya sanar da ni magunguna, sai muka kwana casa'in tare da shi, a mabanbantan dazuzzuka, daga bisani muka rabu, ban sake ganinsa ba. Mahaifinki mutumin kirki ne, ba zan manta da shi ba har abada"
Nene ta ce "Ikon Allah"
Nana ta ce "Sarki kai komai ma ka sani ne? Kuma kowa ya sa ka"
Yayi murmushi ya ce "Na san dai abin da Allah ya sanar da ni, kowa ya sanni kuma na sha yawon duniya ne" Yayi maganar yana ɗaukar Muhsin.
Nana ta ce "Sarki ka ga Nene ta daina harkar bayar da magani, kaima ina fatan zaka daina?"
Ya ce "Meyasa zan daina? Ba a daɗe ba ni ba, ke kanki ki ka bayar da magani zan ce, ko ba ke ki ka tono inda aka yi wa mijinki asiri, meyasa Allah ya zaɓe ki ya nuna miki, duk yawan jama'ar da ke ƙasar nan. Abin da ki ke ta gudun sai da ya faru"
Jiki a sanyaye Nana ta ce "Ba ina nufin ka daina bayar da magani ba, ka daina aiki da aljanu, shi ne ɓarnar. Sannan ka yi ilimi na zamani, cikakke domin ka inganta harkar maganin naka. Ya zamana maganunnanka da awo kar ka bayar da abin da zai cutar maimakon a samu lafiya"
Yayi dariya, Nene ma ta yi, Ya ce "Yaro yaro ne. Nana a dalilinki wallahi na daina surkullen haɗa ayoyin Alkur'ani da wasu abubuwan na yi sihiri. Saboda uban gidana ma, Allah ya ja zamaninsa uban duƙusa ko in ce Ƙaisar, shi ma ya ce na daina wannan, na kuma daina. Na daina surkulle da sihiri na tuba, amma ba zan iya daina aiki da aljanu ba"
Nana ta ce "Amma saboda me?"
"Saboda ɗebo mini magani, wasu ayyukan kuma dole su ne nake aikawa su yi wani aikin."
"Sarki, ta'amalli da aljanu da ka ke yi ba shi da wani alkhairi shirka ne, dan Allah ka daina. Kana cikin mutanen da nake son mu tsira Duniya da lahira."
"Ni ba ni na nemi aljanu na fara aiki da su ba, aljanu su suka takura ni, kamar dai ke da kuma wannan baiwar Allah. Bana ta'amalli da aljanu, na bayar da kuɗi, ko na yi wa wasu sihiri, ko wani abu makamancin haka, ai kin je gurin maganin nawa kin gani"
Nana ta ce "Sarki, kar mu shiga wani bugire da bai kamata mu shiga ba, mu kalli gaskiya kai tsaye kar mu yi mata wata kwaskwarima saboda son zuciyarmu"
"Asma'u babu kwaskwarima domin ba wa ƙarya kariya a maganganuna. Su turawan da ku ke taƙama da su, su na amfani da ku, da daƙile magungunnku ne, saboda gina nasu kasuwancin. Kuma Nana magunguna na da awo nake bahar da su. Ban ƙi ba akwai masu bayar da magani, saboda neman abinci. Amma wanda ya sani ya sani, wanda bai sani ba, bai sani ba kawai. Kuma banda abin ki tun a zamanin baya magungunan 8su na da awo, wani a ce ka auna da ɓawon gyaɗa,ko farce, wani a ce ka sha safe da yamma, duk sharri ne wasu abubuwan da ake faɗa, da ƙoƙarin kashe mana magungunanmu. Sai a ce ku daina shan magungunan gargajiya saboda ɗaci, hanta ba ta son ɗaci, amma Allah ya halicci maɗaciya a tsakiyar hanta. Idan hanta ba ta son ɗaci, Allah ba zai sanya matsarmama a cikin hanta ba. Kuma su magungunan baturen, ba ɗaci ne a cikin su ba. Ba zan kushe wa kowa ba, amma kar a kuskura a kushe mini nawa. Yakamata mu daina wannan musun haka,kowa ya riƙe abin da yake ganin shi ne dai-dai " Nana ta ɗan yi jimm tana tunani, daga bisani ta ce "Wasu maganganun naka na kan dai-dai, amma kowa ya riƙe abin da yake ganin shi ne dai-dai!"
"To ki daina takura mini a kan lallai sai na yarda da abin da ki ke kai"
99
1k ne via 0069685771 Aisha Adam stanbic 08081012143
Har Nana za ta sake magana, Nene ta riƙo hannunta, ta ce "Nana mu koma ciki, ai kin ɗan tattaka, kin san baya son a ganki, ko a gane ki a yanzu. Ɗan uwa idan muka kuma haɗuwa zamu tattauna sosai mu gaisa.
Sosai shirye-shirye suka yi nisa, hankalin Sultan gaba ɗaya ya koma kan shirin zuwa Nigeria da bikin da za a gudanar. Sai dai yana ta fuskantar ƙalubalanta a kan hukuncin da ya zartar. Gimbiya Bilkisu ta rasa inda zata sanya kanta, ta tuntuɓi Tafawa ta sanar masa da matakin da Sultan ya ɗauka a kanta, amma ya ce mata shi ma ta kansa yake yi, hankalinsa a tashe yake. Duk yadda ta kai ga ƙoƙarin yin dabarun da Sultan zai saurare ta, fafur ya ƙi ko kallo ba ta ishe shi ba. Ranar ƙarshe ma da ta je ɗakinsa kamar zai dake ta ya ce "Bilkisu bana ƙaunarki bana ƙaunar ganinki, tun da har za ki yinƙurin sabauta mini rayuwar ɗa, idan ki ka sake zuwa inda nake, sai na yi miki abin da baki taɓa tsammani ba, fice ki bar mini ɗaki kafin na yi miki illa" Abin ya ɗaure mata kai, bata taɓa tunanin zai yi irin wannan fushin har haka ba.
Jamila ta koma gata nan gata nan, ita ba mahaukaciya ba, ita ba mai hankali ba, kuma ita ba mara lafiya ba. Shi Baba gaba ɗaya ma yanzu tsoro suke ba shi. Ya riƙe istigfari ba dare babu rana, gaba ɗaya yaransa sun watse babu wani na kamawa. Gaddafi ya zo gida, ya tarar da gidan nasu duk wani iri. Yayi mamakin ganin yadda Jamila ta wani rakwakwkwaɓe, jiki babu ƙwari, ta yi wata irin muguwar rama ta fita daga hayyacinta kamar ba ita ba. Sun dawo daga sallar Asuba, tare da Baba, Baba ya numfasa ya ce "Gaddafi ka ga yadda Allah ya yi da gidanmu ko? Gaba ɗaya babu wani mai ɗan dama-dama" Gaddafi ya ce "Na gani Baba, ina son na yi magana dai na fasa, na ga Suwaiba ta daina magana gaba ɗaya, har da dalalen yawu take yi. Jamila kuma na kasa gane abin da yake damunta" Baba bai ɓoye masa komai ba, jikin Gaddafi ya din ga tsuma, ya dubi Baba ya ce "Baba, Jamila ta yi ciki, kuma tana maganar ƙungiyar asiri? Innalillahi wa Innalillahi raji'un"
Cikin matsananciyar damuwa Bab ya ce "Babarta ta ce zafin ciwo ne, amma na kasa yarda nima" Ya yi maganar yana zubar da hawaye. Gaddafi ya ce "Shiyasa Baba na din ga maganar kuɗin da ta din ga ta'amalli da su, amma mahaifiyarta ta nuna ba ta so, ta nuna baƙin ciki nake yi, da ci gaban Jamila ka ga irin abin ko? Shikenan sun lalata mana gida" Baba ya yi kuka ya ce "Ina kyautata zaton hakkin yaran nan ne, su Nana, dan sai daga bayan nan, nake duba wasu abubuwan da na aikata musu na ga sam babu adalci a cikinsa. Amma wasu mutane sun zo wai daga Agadez sun ce mini tana gurinsu" Nana Baba ya gaya wa Gaddafi abin da su Mahmoudu suka zo masa da shi. Gaddafi ya rikice ya ce "Baba kuma baka karɓi lambar wayarsu ba ko ka bi su ba?" Baba ya girgiza kai ya ce "Ban karɓa ba, ni tsoro ma na ji, ji nake kamar ƙarya suke yi. Na bar wa Allah ikonsa" "Amma Baba akwai mamaki a cikin abubuwan da suka faɗa, masu sarƙaƙiyar gaske" Baba ya ce "To ai shiyasa ban ma gazgata ba, sai abin da hali yayi" Gaddafi ya ce "Ba wani abu, in sha Allah mu tsammaci alkhairi" Baba ya jinjina kai cike da gamsuwa.
**** Nana ce a tsaye, tana kallon Ƙaisar, yana zuba wa wata tsuntsuwa abinci a cikin keji. Nana ta kalli tsuntuwar ta ce "Ƙaisar ita kuma wannan fa, a ina ka samo ta?" Ba tare da ya kalli Nana ba ya ce tsinto ta na yi a daji, za ta mutu, ban zaci ma zata rayu ba, sai kuma na ga ta farfaɗo yanzu ta ware ma" Nana ta ƙarasa gaban kejin ta zauna, sannan ta ce "To kuma tsuntsuwa ce ita, ko kuma aljana ce?" Ya kalli Nana ya ce "Dama akwai tsuntsu mutum da aljan ne?" Nana ta ɗan yi shiru tana kallon tsuntsuwar. Ya ce "Mutum jinsinsa daban, aljani daban, haka ma tsuntsu daban. Babu Aljani tsuntsu sai dai Aljani ya shiga jikin tsuntsun, ina fatan kin gane?" Ta gyaɗa kai, ta ce "Haka ne, wai ni kuwa Ƙaisar ina Haulat? Ka fara son nata?"
"Ban sani ba" Ya yi maganar yana hararta.
Nana ta yi murmushi ta ce "To shikenan kai ba zaka yi aure ba kenan? To sonta ne baka yi ko kuma me ta yi maka?" Yayi mata shiru, yana rufe kejin tsuntsuwar nan. Nana ta numfasa ta ce "Ƙaisar ina kewar gida fiye da tunani, zuciyata kuma ta cika da fargabar rashin sanin abin da zan je na tarar. Ina jin kunyarsu ban san da wani idon zan kalle su ba. Duk da Imrana ya haɗa ni da Mama, ta yi mini Addu'a ta ce na kwantar da hankalina, amma kunyarsu nake ji ban kyauta ba abubuwan da na yi" Ya ce "Za ki tarar da alkhari in sha Allah, da abun da zai yi miki daɗi da wanda ba zai yi miki ba. Ni na din ga shagaltar da ke daga tunaninsu, da tunaninsu ya yi tasiri a zuciyarki, da ba ki cimma wannan nasarar ba, da kin rushe komai, dan idan ki ka koma gidan babu abin da zai canza"
Cikin mamaki Nana ta kalle shi ta ce "Ban gane ba, kai ne ka sanya na daina jin damuwar da na din ga ji a baya, da son komawa gida?"
"Sosai, saboda ruhi ne mu, mu na iya shiga ko ina a jikin ku, kuma muna iya hargitsa tunani da sanya muku rashin nutsuwa"
Ta yi shiru tana nazari, ta sake cewa "Ƙaisar ka sanya ni a fargaba, abin da zan tarar a gida da gaske mara daɗi ne? Kodayake ko ka gaya mini ma idan na tashi na san mantawa zan yi sai abin da na je na tarar kawai"
"Kin yi zaton da mugunta kawai nake nuna miki abu na mantar da ke ko?" Nana ta jinjina kai.