Buzu book 3 complete - Chapter 29
Buzu book 3 complete Chapter 29: Buzu book 3 complete Chapter 29. Nana ta girgiza kai ta ce "Ƙaisar kuka yake yi, an kashe babansa, ni ku bari zan yi…
3,920 words
Nana ta girgiza kai ta ce "Ƙaisar kuka yake yi, an kashe babansa, ni ku bari zan yi magana da shi, yana cikin jimami dan Allah kar ku kashe shi" Ta ƙarasa maganar har da haɗa hannayenta biyu alamar magiya. Hammad ya rungume ta, ganin yadda take neman ta fita daga hayyacinta, ga shi yana kyautata zaton tana ɗauke da juna biyu. Nana tana da matuƙar raunin zuciya, da tausayi banda haka ya za a yi abin da ya wahalar da ita, ta din ga wannan kukan ta ce ba za a raba ta da shi ba. 104
Sosai Nana ta rikice musu, take ta uban kuka, babu irin ban haƙuri da rarrashin da Hammad bai yi mata ba, amma ta ƙi saurararsa tana cewa ita ba za a kashe Ƙaisar ba. Malamin ya ce su rabu da ita, su koma masaukinsu su kwana biyu ta samu nutsuwa, sai su dawo da ita. Har suka koma masauki, Hammad bai kula Nana ba, gani yake yi kawai kamar ta fifita zama da Aljani a kansa, ban da haka ita da kullum cikin taka tsantsan take da imaninta da rayuwarta, me za ta yi da zama da aljani, aljanin da babu abin da ya yi face wahalarwa da muma azabtar da rayuwarta. Ita ma ba ta kula shin ba, ba ta bi ta kansa ba, Sultan ya ja masa kunne sosai a kan kar ya yi mata faɗa, ko kuma ya ce zai takura ta. Kamar wasa Nana abu har da rashin lafiya, zazzaɓi sosai da sosai, ta ƙi cin abinci. Da ta tuna yadda ta ga Ƙaisar yana kuka, sai jikinta ya yi sanyi, shi ma halittar Allah ne, cutar da shi ba zai kawo masalaha ba, wataƙila sai ma ta'azzara wasu abubuwan. Tun bayan tariyarsu, ba su taɓa yin faɗa ba sai a wannan lokacin. Da daddare ma a ƙasa ya kwanta, ba ta ko saurare shi ba, ta haye gado duk da rashin cin abinci da ta yi, ya tsaye masa amma ya dake ya ƙi kula ta. Gefe guda ta hango Ƙaisar, yana zaune ya saka wata hanya a gaba ya takure yana kallon hanyar. Jiki a sanyaye Nana ta ƙarasa gefensa ta zauna ta ce "Ƙaisar" Ya waiwayo a hankali ya kalli Nana ya ce "Na'am" Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ina matuƙar jin nauyinka, da kuma kunyarka, ban ma san me zan ce ba, ina mai baka haƙurin rashin mahaifinka da ka yi". Ya ɗan jinjina kai ya ce "Haƙiƙa mahaifina ya so ni, so mai tsanani, duk mai sonsa to ya so ni. Sai dai bayan mun raba gari babu yadda ban yi ba ya gane gaskiya, amma abu ya gagara. Ban ji baƙin cikin mutuwar mahaifina kamar mutuwar da ya yi a matsayin kafiri babu ta inda zan yi masa addu'a na roƙa masa Allah gafara. Tabbas Giyaz shi ya kashe kansa bayan malamin nan ya takura masa a kan ya musulunta ko ya ƙona kansa." Ya yi maganar cikin matsananciyar damuwa. Nana ta rasa abin yi, a hankali ta ce "Ka yi haƙuri, babu wanda ya isa ya shirya wani, idan ba Allah ba, wannan ita ce taka ƙaddarar" Ya jinjina mata kai, sannan ya ce "Me yasa ba kya son a kashe ni? Ko a raba mu?" Nana ta ja numfashi sannan ta ce "A tarayyata da kai, duk da akwai ƙalubale mai tarin gaske, amma na koyi darrussa daban-daban, kuma na fahimci abubuwa da dama. Tabbas yadda muke da mutanen kirki da kuma ɓata gari, kuma ku na da na kirki da ɓata gari a cikin ku. Kamar yadda nake yawan faɗa, idan ka na son ka zama mafi alkhairin mutane, ka rinjayar da alkhairi a kan sharri. Kuma bayin Allah ne, ku na taku da rayuwar Allah ya sanya mu rayu da mu da ku a Duniya ɗaya, duk da mu na da banbancin halitta, bai kamata ɗayanmu ya zamana yana cutar da ɗaya ba, ko amfani da ɗaya gurin fin ƙarfi da mugunta ba. Ni dai a yanzu zan iya bugun ƙirji na ce a cikin halittar aljanu akwai bayin Allah, sai dai su ma ajizai ne su na aikata laifuka kamar yadda ɗan Adam yake yi"
Ƙaisar ya jinjina kai kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce "Haƙiƙa nima tarayyata da ke na fuskanci abubuwa da dama game da rayuwa, kuma ina son baki wasu saƙonni da yakamata bil adam ku sani. Na ƙaru da abubuwa da dama ta ɓangarenki. Tabbas ba na cikin baƙaƙen aljanu, kuma ni musulmi ne, sai dai ban tsaya na fahimci addini yadda yakamata ba, gaba ɗaya na fi mayar da hankalina gurin burina, na sanin magunguna. Na ji daɗin samun ahalinki, gurin amfani da su, domin baje kolin baiwar da Allah ya yi mini, sai da kash, Duniya ɗaya muke rayuwa da ku, amma tsarin taku rayuwar ya banbanta da namu da cikin ƙiftawar idanu zamani yake canzawa. A lokacin da ki ka zo, nake farincikin samun cikakkiyar damar ci gaba da ayyukana, ashe lokacin ilimin addini ya daɗe da yawaita, duk da wasu sun rintse idanunsu daga kallon ilimin, su na aikata ɓarna fiye da ta sauran mutanen baya da suka rayu da jahilci. Rayuwa tare da ke, ya ƙara haska mini juriya a cikin ƙaddara, da taka tsantsan da tsananta imani da Allah. Duk tsanani da zafin ƙaddarar da ka ke ciki. Sannan kasancewaka mutumin kirki, ko mai tsoron Allah baya canza ɗabi'ar duniya ta zama mai adalci a gare ka, ko hakan ya hana Allah ya jarrabe ka. Wasu lokutan jarrabawa ta fi tsananta ma a lokacin da ka fi tsananta addu'a. Haka zalika idan Duniya za su taru domin su amfanar da kai wani abu, ba za su amfanar da kai komai ba, face abin da Allah ya rubuta maka, haka zalika idan za su taru domin su tauye ka da wani abu, ba za su tauye ka da komai ba face abin da Allah ya rubuta maka. Ban taɓa tsammanin tsakanin ke da mijinki wani ba zai mutu ba, saboda tasirin mugun tsafin da aka yi masa, ni kuma ga haushinki ina ji, ga burin Giyaz na ɗaukar fansa a kan ki. Haƙiƙa wanda ya dogara da Allah, Allah ya isar masa, ko ba a zo wannan gaɓar ba, ni da kaina zan tafi na bar ki, na yi nesa da ke da zuriyar ki. Zan yi ƙoƙarin shafe duk wani tarihin abin da ya faru a tsakaninmu da zuriyarku, kar a samu wani ya fito daga tsatsona ya nemi sake ɗaukar fansa. Ni kaina zan tafi inda ba a sanni ba, saboda kar wataran na ji na karaya na nemi sake dawowa gare ku, na kasa cika alƙawarin da na ɗauka. Zan ci gaba da neman ilimin addini, zan ci gaba da rubutu, da kuma bincike mai zurfi a kan ilimin sarrafa tsirrai. Sai dai na yi miki alƙawarin zan rubuta labarinki da girmamawa, da alfaharin kasancewarki uwar gijiyata, na fito da kyawawan halaye da kuma ɗabi'unki ababen koyi. Tauhidinki, juriya da kuma gudun Duniya. Zan yi iya yi na na kare wannan rubutu tsawon ƙarnuka, domin ya zama misali mai kyau ga duk wanda zai karanta. Domin zan yi ƙoƙarin nesanta kaina da duk wani abu da zai sanya na shiga harkar bil'adama. A ƙarshe ina fatan ki sanar da mutanenku, darussan da ki ka koya, a tsawon zaman da muka yi, sannan ki fahimtar da su aikata ayyukan jahilici da duk wani abu da kauce hanya, saboda kana iya shukar da ba za ta fito ba wataƙila sai shekaru masu yawa a gaba, a sanya wanda ba su ji ba, ba su gani ba girbe abin da ba su shuka ba, kamar dai yadda ya faru da ke. A ƙarshe ina yi miki kyakykywan fatan alkhairi, da fatan Ubangiji Allah ya sanya jarrabwoyin da ki ka shiga, su zame miki silar shiga aljanna, Allah ya raya miki yaronki da abin da za ki haifa a gaba ya shirya miki su. Ya baki zaman lafiya da kwanciyar hankali na har abada. Ina kuma fatan halittun Allah su gane cewa, jinkirin amsa addu'arsu a gurin Allah, baya nufin Allah ba ya son su, kuma zafin ƙaddara da jarrabawa baya nufin Ubangiji yana ƙin ka, sai ka yi duba ga rayuwar annabawa da salihan bayi. A ƙarshe ina roƙon dan Allah ki yafe mini, dan na san muddin ba ki yafe mini ba, sai Allah ya saka miki cutar da ke da na yi, ba tare da wata halattacciyar hujja a kan shari'a ba." Nana na kuka ta ce "Ƙaisar na yafe maka duniya da lahira Allah ya yafe mana gaba ɗaya, Ubangiji Allah ya albarkaci rayuwar ka ya sanya ka cikin salihan bayinsa. Ba zan taɓa mantawa da kai ba har abada" "Nima ba zan manta da ke ba Asma'u jikar Lanti. Ina fatan za ki yi ilimi mai zurfi ki karanci fannin ilimin magungunan musulunci da na gargajiya " Nana ta ce "Na yi maka alƙawarin haka. Amma daga nan ina zaka je?"
"Can nesa da Duniyarki, zan nemi ilimi sosai "
"Dan Allah ka tafi da Haula mana, tana matuƙar sonka da ƙaunar ka"
Ya miƙe tsaye yana murmushi, ta ga ya zama wani irin dogo mara misali. Ta ja da baya tana kallonsa. Ta din ga jin muryarsa a sama ya ce "Yi haƙuri, kar na tsorata ki, duk suffar da ki ke ganinmu a cikinta da ni da Giyaz, ba suffofinmu ne na halitta ba, idan muka fito muku a siffofinmu na halitta zaku iya rasa rayukan ku, ko ku zauce. Mu kan suffantu da abubuwa ne da idanunku za su iya kalla. Na gode sosai da sosai uwar gijiyata ina yi miki fatan alkhairi."
"Wayyo Allahana, shikenan ko ziyara ba zaka sake kawo mini ba. Tabbas a kan ka na yarda a sauran halittu akwai bayin Allah na ƙwarai, ba zan taɓa bari a raba ka da rayuwarka ba kai ma. Ina yi maka fatan alkhairi uban ɗakina, kuma ɗan uwana. Na san ba haka kurum Allah ya haɗa ni rayuwa da kai ba, duk da mu na da banbancin jinsi"
Kuka take yi iya ƙarfinta, Hammad yana riƙe da ita gam a jikinsa, sai mimmiƙewa take yi tana ci gaba da kiran Ƙaisar.
"Asmyna, ki yi haƙuri ki daina kukan nan haka" Ta buɗe idanunta a hankali ta kalli Sayyid, ta kalli dattijon malamin nan, ga su Sultan a gefe duk a cikin wani ɗaki. Ta fashe da kuka ta ce "Shi ma an kashe shi ko?"
Ya girgiza mata kai ya ce "A'a yarjejeniya kawai aka yi da shi, ya ce kun riga kun gama magana ma, ya yi miki alƙawarin ya tafi ya rabu da ke har abada"
"Shikenan ba zan sake ganin Ƙaisar ba? Ya cutar da ni, amma... Sai ta kasa magana ta ci gaba da kuka. "Na sani, na san komai Asmy ki yi haƙuri, mu na da banbancin da ba zai yiwu ki ci gaba da rayuwa da shi" Haka suka din ga rarrashin Nana. Shi kansa malamin ruƙiyyar cewa yayi bai taɓa samun case mai rikitarwa kamar na Nana ba, domin shi kansa Ƙaisar sai da ya yi kuka ba kaɗan ba, kafin ya ƙara tabattar wa malamin ruƙiyyar nan cewar ya bar ta har abada.
Kwana biyu suka ƙara a Egypt, Nana sam ba ta walwala kamar wadda aka raba da mahaifinta, gaba ɗaya memories ɗin abubuwan da suka din ga faruwa a rayuwarta a tsakaninta da Ƙaisar suka din ga dawo mata. Tabbas za ta kasance cikin biladama masu ban mamaki da suka yi rayuwa mai kusancin gaske tsakaninsu da Aljanu. Sai da suka ƙara kwana biyun. Haka Hammad ya haƙura ya din ga rarrashinta, saboda yadda duk ta danu, domin yana iya tuna wasu abubuwan da suka din ga faruwa tsakaninsa da Ƙaisar saboda Nana. Suka koma ta Nigeria, har da Sultan da Matawalle, suka gaisa da iyayen Nana, tare da sake jaddada musu godiyarsu, bisa ga abin da Nana ta yi wa yaransu na kulawa, tare da yi musu bangajiya na zuwa biki da suka yi Agadez. Tun da suka koma Agadez, hasashen Hammad ya tabatta, domin kuwa laulayi ne sosai ya kada Nana. Babban abin da yake damun Hammad, bai wuce duk yadda ya so, ya haɗa kan Nana da Asal ba, Nana ta ƙi yarda ta ce masa komai zai yi Asal ta riga ta furta mata ba ta ƙaunarta, kuma duk mutumin da zai nuna baya ƙaunarka ba ta ga abin mu'amala da shi ba. Sai dai ya ci gaba da matsa mata har ya yi fushi. Ta ce "Sayyid, bari na yi maka gwari-gwari tabbas ina jin zafin ƙiyayyar da Asal ta nuna mini, amma muddin za mu din ga haɗuwa, ko ka ce sai mun haɗa kai, ba zata taɓa sakewa ba, zan zame mata takura kasancewar na san sirrinta, za ta din ga ganina da abin. Bana fatan zame wa kowa matsala a rayuwata, ba na fatan Asal ta rayu a takure saboda ni. Dan haka ka yi haƙuri ka ƙyale ni" Ya gaji ya gaya wa Sultan halin da yake ciki da Nana, ya ce duk ya kai masa su can gida. Tun da Asal ta ga Nana, hankalinta ya ƙara tashi, ganin Nana da juna biyu a lokacin ya ɗago sosai, ga kuma Muhsin da tana ganinsa a wallpaper Hammad. Nana ta ƙara cika ta yi kyau sosai da sosai. Sultan ya yi musu nasiha sosai da sosai, tare da roƙonsu a kan komai ya wuce, idan ba haka ba muddin suka tafi a haka, to irin jahilcin da ya din ga faruwa a baya, na faɗan 'ya'yan sarakuna a baya, to kuma zai iya faruwa naku gidan, dan haka ku yi haƙuri ku tura komai baya. Nana sai da ta ɗan sha jinin jikinta, ko a lokacin yanayin yadda ta ga Asal kamar gaba ɗaya a tsorace take, duk ta kame jikinta babu izzar nan da jin kai da take yi a baya. Suka yi masa godiya, Nana ta tabattar masa da in Allah ya yarda komai zai canza. Asal ta lura da yadda shi kansa Sultan ta Nana yake yi, yanzu baya nuna mata kulawar da yake ba ta a baya. Ta lura Hammad ne kawai ya yafe mata yake yin ta. Duk yadda ta so share Muhsin, son da take yi wa Hammad, da kamanin da suke yi da Muhsin ɗin, sai da ya sanya ta tsaya kula shi. Babu inda ya bar Hammad a kamanni. Nana ba ta fasa jin kewar Ƙaisar ba, ita kanta har ƙoƙarin faɗa take yi wa kanta, amma sabo turken wawa, babu yadda ta iya, idan abin ya ishe ta har kuka take yi. Jamila ta riƙe istigfari da addu'a, da magungunan da Nana ta bata, cikin ikon Allah ta din ga samun afuwa, a kan lamarin larura da take fama. Lamarin Suwaiba ne dai ba arziki. A hankali tana juya kuɗin da Nana ta bata, idan jarin ya karye ta kira Nana, ta ƙara bata wani, gefe Nana tana lallaɓa Baba har ya haƙura yake shiga sabgar Jamila. Gaddafi ma ya yi aure, ya sha tagomashi daga gurin Nana. Nana ba iya gidansu ba, hatta maƙwabtansu sai da suka shiga rigar arzikinta. Tana samun kuɗi sosai a Agadez, ga allowance ɗin ta na sarautarta, ga na kasamcewarta matar Sardaunan Agadez. Ga shi Hammad yana sakar mata kuɗi sosai da sosai. Ban da tarin kyaututtuka da take samu. Nana ta ƙyale Hammad yake zuwar wa da Asal Muhsin, sai dai ta tsananta addu'a. Su Tafawa suka zama ba su da wata power ko ƙarfin faɗa a ji, dan hatta dogarai da jami'an tsaron da suke tare da su, sai da aka janye musu, aka yanke albashin da masarauta take biyansu. Hakazalika duk wani kasuwanci da masarauta ke gudanarwa, ake samun riba da Nana da Muhsin a ciki. Watan Nana tara da sati biyu cif ta sake haihuwa namiji. Hammad kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha, kasancewar kaf Agadez Nana ba ta da uwar da ta wuce Nene, ita ce tsaye a kanta a kan komai. Nana ta yi mamakin ganin Asal ta zo yi mata barka. Ahmad aka sanya wa jaririn, ake kiransa da Hamdan. Har da kyaututtuka Asal ta bayar a ba wa jaririn. Sosai take jin tausayin Asal, a zuwa ukun da ta yi ganin jaririn, duk lokacin da ta zo, daga gaisuwa babu abin da yake haɗa su da Nana, amma idan ta karɓi jaririn tana daɗewa sosai da sosai tana kallon yaron. Iya ƙoƙari Hammad yayi, a kan mantawa da duk wani abu da Asal ta aikata, amma bakin alƙalami ya riga ya bushe, lokuta da dama abubuwan da ta aikata masa su na dawowa zuciyarsa. Ita kanta a dole, take ƙoƙari take rintse idanunta ta kawar da kanta daga wasu abubuwan da yake aikatawa, Nana ke da miji Nana ne da 'ya'ya, kuma take da goyon bayan uban miji, da masaurauta ma baki ɗaya. Gimbiya Bilkisu ta din ga ziga ta, a kan lallai ta haƙura da auren nan, amma Asal ta ce ba za ta haƙura ba. Wataran Mahmoudu ya kawo musu ziyara, tare da matarsa, ana falo suna ta hira, yake bawa Mahmoudu labarin, darun da aka sha da Nana a kan raba ta da Ƙaisar. Mahmoudu ya hau dariya ya ce "Wasa-wasa fa, Gimbiya akwai daru, banda ita wa yake fatan tarayya da Aljani?" Hammad ya yi dariya ya ce "Mahmoudu sabo turken wawa, ita idan ka lura da ita ne, gaba ɗaya rayuwarta ba ta da damuwa, kuma tana da matsanancin tausayi amma Aljanin nan ya azabtar da ita, ni kuma ga mahaifinsa na gana mini azaba, wallahi yarinyar nan Allah ne yake kare ta, da wata ce tsaf zata haukace. Saboda azaba har a zahiri muke ganinsu, na zo da muka koma Buda hannuna na dama ya shanye, bakina ya koma gefe nikaɗai na san azabar da nake sha. Ga laulayi tana yi ga jinyata. Idan na fita daga hankalina na yi yinƙurin kashe ta, sai na dawo hayyacina sai na ga abin kamar a mafarki. Duk yadda zan kwatanta maka azabar da muka sha mutum sai dai ya ji kamar labari. Saboda jarabar Ƙaisar da babansa aka tashe mu daga wani gida da muka zauna aka ce mayya ce. Amma sau ɗaya Asmy ba ta taɓa nuna mini a fuskarta za ta rabu da ni ba, saboda ta yi imanin idan ta rabu da ni wa zai kula da ni. Amma yarinyar nan ina lallaɓata ina tuna mata abubuwan da Ƙaisar ya yi mata na cutarwa sai cewa ta yi ina ruwana, lokacin da na gudu na bar ta na san me ya yi mata? Kuma ai ta yafe masa tun da ya yi mata abin alkhairi. An sha daru kan su rabu. Tana nan tana gaya mini sai ta rubuta littafi guda, a kan Aljanu saboda Ƙaisar. Tun ina kishi da aljanin nan na haƙura da na gane dai duk abu ba jinsinmu ɗaya ba" Suka din ga dariya, Asal dai ta yi shiru, ita zancen ma tsoro ya hau bata. Fadila kuwa ta din ga yi masa tambayoyi, a kan yadda aka yi ya zamana Nana ɗauke da ɗa a jikinta shi kuma Uba. Babban abin da ya bata tsoro da mamaki, cewar da ya yi, har ciwon ɓarin jiki yayi, da irin wahalar jinya da Nana ta yi. Ya din ga misalta musu irin yadda yake ji, idan ciwon nan ya tayar masa yadda yake jin kamar ya kashe kansa saboda azaba.
Asal duk sai ta tsargu, ta kalli fuskarsa ta ga hirarsa kawai yake yi, hankali kwance, ba domin da alamar wata manufa a fuskarsa ba.
10YRS LATER Muhsin na da shekaru goma sha huɗu a Duniya, Nana ta kammala karatunta, na ilimin magungunan addinin musulunci. Hammad ya taimaka mata, ta gina katafariyar cibiyar koyar da addinin musulunci, wata a Agadez wata a Nigeria. A lokacin Nana yaranta huɗu duk maza, tana sanye da glass a fuskarta tana rubuce-rubuce, Hammad ya kira ta ya ce mata Asal ce ta kira shi ba ta da lafiya, ko za ta tura mata ko Yarima ne, idan da wani magani da za a bata kuma a bata. Nana ta ce "Ahh me Yarima zai iya yi, bari na je da kaina".
Ko da ta je gidan kuwa, tuni Muhsin yana can, Nana ta ce "Amma maimakon ku kira ni ku gaya mini, me Muhsin zai iya yi miki?"
Asal dai ta yi shiru, Muhsin yana kusa da ita ya ce "Kawai zuwa na yi nima, na tarar da ita bata da lafiya"
Nana ta ce "Ina ganin kawai mu tafi Asibiti" Nana ta taimaka mata ta canza kaya, suka tafi Asibiti.
Likitoci suka ce tiyata za a yi mata a cire abin da yake cikinta. Nana ta kira Hammad ta ce masa lallai ya dawo, tiyata za a yi wa Asal ana buƙatar a saka hannu. Ya ce "Ki saka, ba zan iya dawowa a yau ba, sai zuwa gobe in Allah ya kaimu"
Nana ta ce "To ai ba zai yiwu ni na saka ba, ko a kira mahaifinta a waya?"
Da sauri ya ce "A'a bari na kira Sultan, kuma ki tsaya ki bayar da order, kar wani ya zo a ba shi ɗana, idan ba ke ko Sultan ba, babu yadda zan yi na dawo ne"
Haka aka yi, Sultan ya je Asibiti da kansa ba wakilici ba, ya sanya hannu aka ciro wa Asal jaririyarta. Nana aka fara ba wa yarinyar, ta yi wata irin ajiyar zuciya tare da gode wa Allah, sannan ta kai wa Sultan ita.
Ya rungume yarinyar yana kallonta cike da ƙauna, ya ce "Kin ga ikon Allah, bayan shekaru kusan ashirin da aure, sai yanzu Allah ya yi ikonsa"
Nana ta ce "Tabbas Allah abin godiya, Abin da na yi ta gaya wa Sayyid kenan, ba a cire rai da rahamar Allah. Asal na kwance a post up room, ta buɗe idanunta a hankali, ta kalli Nana da take ta shafa kan jaririyar. Tsawon wannan shekarun, babu wata jituwar arziki a tsakaninsu, sai dai tun kiran da Sultan ya yi musu, ya yi musu nasiha Nana ta daina hana yaranta zuwa inda Asal take. Aka sanar da haihuwar Asal, amma aka hana kowa zuwa Asibitin da take. 'ya'yan Nana haka suka kewaye Asal da jaririyar nan, wannan ya ɗauka wannan ya ɗauka. Da kyar suka tafi gida, saboda makaranta. Ƙarfe sha biyu da rabi Hammad ya iso Asibitin. Ya tarar da Nana tana shirya jaririyar a cikin kaya. Bakinsa ya kasa rufuwa, ya miƙa mata hannu ta bashi, Nana ta ce "Ba tukuici babu komai" "Zan baki idan muka haɗu" Tana murmushi ta miƙa masa jaririyar, ta tashi ta basu guri. Ya ƙarasa kusa da Asal yana murmushi ys rungumota ya sumbaci goshinta. Ya ce "Kin ga ikon Allah ko Cherié?" Ta yi murmushi ta ce "Na gani, kalli kamar ta ɗaya da Yarima, duk kamar ka suke yi" Ya yi dariya ya ce "Ba dole su yi kama da ni ba, ni ɗin na wasa ne. Alhamdillah bayan samari da Allah ya bamu ga 'yar budurwa."
Asal ta ce "A saka mata Asma'u" da sauri ya waiwayo ya kalle ta, ya ce "Ba na son wasa"
"Da gaske nake, na ga kana sonta da yawa, ko ita ma za ta ci albarkacin son da ka ke yi wa rayuwarta, ka so ta sosai"
Hammad ya ce "Kin ga ni ba na son rigima daga haihuwar ki, ke cewa na yi ba na sonki ne?"