Buzu book 3 complete - Chapter 4
Buzu book 3 complete Chapter 4: Buzu book 3 complete Chapter 4. Hawaye sharkaf a kan fuskarta, ya ce "Kar ki wahal da rayukanmu, ni da ke abu guda ne Asmy,…
4,491 words
Hawaye sharkaf a kan fuskarta, ya ce "Kar ki wahal da rayukanmu, ni da ke abu guda ne Asmy, ko kin tafi kin bar ni, ba za ki taɓa samun nutuswa da kwanciyar hankali ba. Kamar yadda tun da muka rabu nawa ruhin ma bai samu nutsuwa ba. Ina ƙaunarki rayuwata" Duk yadda Nana ta so yi masa rashin kunya, ta gaggaya masa maganganu masu zafin gaske, amma ta kasa tamkar ya saka wani abu a cikin idanunsa da ya yi tasirin da ya hana ta maganar. "Ki yi mana addu'a rayuwata, akwai kaya a ɗakin da muka je jiya, idan kin yi wanka akwai kayan sakawa. Sai akwai kitchen shi ma, duk za ki iya shiga ki dafa mana duk abin da ki ke so. Sai na dawo" Ko tari Nana ba ta kuma yi ba, har ya tashi ya bar ɗakin, ta bi bayansa da harara.
Nene ce rungume da Muhsin, ya sha ado cikin kayan buzaye, kayansa iri ɗaya da na jikin babansa, sai ƙoƙarin cire mayafin da aka rufe masa gashinsa da shi yake yi, sai ƙamshin turare yake yi. Hammad ya saka hannu ya karɓe shi fuskarsa ɗauke da murmushi har da wata irin ɓoyayyiyar ajiyar zuciya.
Hammad ya ce "Mu je ko?"
Nene jiki a sanyaye ta ce "Ina mai neman afuwarka, ni tsoron zuwa gidan nan nake yi. Kuma a wane hali Nana take ciki yanzu, na kasa nutsuwa gaba ɗaya, ina jin ban kyauta ba gaba ɗaya"
"Ki kwantar da hankalinki, Nana tana tare da ni, kuma babu wanda zai yi miki komai a cikin gidan, ki taimaka mini dan Allah"
AREWABOOKS
Nene ta numfasa ta ce "Alfamarka ce kawai za ta sanya na yi maka abin da ka nema, dan na yi alƙawarin babu abin da zai sake haɗa ni da wannan gidan naku, saboda mummunan tabon da yake binne a zuciyata. Kuma da ko me za ka yi mini ba zan ba da ɗan nan ba, saboda ya saɓa alƙawarin da muka yi da Nana, ban kyauta mata ba za ta yi mini kallon mutuniyar banza mara alƙawari. Amma kai ma ɗa ne a gurina, ban da dalilin haka gaskiya ba zan iya ba"
"Na sani, kuma na gode sosai da sosai, da wannan alfarma da ki ka yi mini"
Ta risunar da kanta cikin girmamawa. Ya miƙa mata Muhsin ta karɓe shi, suka shiga mota.
***** A tsanake Tafawa ya kalli Asad ya ce "Asad, wai waye ka ce ya karɓi ayabar nan ya ci?"
"Wata yarinya ce, ni ban santa ma a gidan nan ba gaba ɗaya"
"Dole a nemo ko wacece, saboda an tabattar mini, da cin ayabar da ta yi, da gayya ta karɓa ta ci, dan aikin da aka yi ya ɓaci ya lalace."
Asad ya yi shiru, ya ce "Gaskiya ban san ko wace ce ba, sai dai ko a tambayi Asal, ko ta santa abinci dai ya kawo mana. Ina kyautata zaton ko kuku ce ko dai makamancin hakan. Ban ma san yadda aka yi ta zo inda muke ba, dan kamar ba buzuwa ba ce gaskiya"
Tafawa ya yi shiru yana nazari, ya ce "Babu yadda za a yi wadda ba buzuwa ba, ta tsallako ta shigo gidan sarautar Agadez, ta yi wannan abin, lallai zuwanta na manufa ne, dole a binciko wace ce." Asad ya jinjina kai cike da gamsuwa.
Asal duk ta rasa nutsuwarta da kwanciyar hankali, mussaman da Imam ya kwana uku ba ta san inda ya shiga ba, hakan ya sanya ta fara jin kamar akwai ƙamshin gaskiya a maganar da Tafawa ya gaya mata. Ta kasa jurewa ta je ta samu Sultan, tana yi masa kuka.
Cikin damuwa ya ce "Yarinyar kirki lafiya kuwa?"
"Sultan ji na yi an ce wai Imam yana da ɗa, dama aure ya yi ban sani ba? Kuma tun shekaranjiya ban sake ganinsa ba, kuma ba na samun sa a waya"
Sultan ya ce "Waye ya gaya miki?"
Ta yi shiru ta sunkuyar da kai. Ya numfasa ya ce "Shikenan na fahimta, amma ki kwantar da hankalinki, na tabattar da Hammad ba zai aikata abin da zai zubar da kima da mutuncin gidan nan ba, dan haka ki yi haƙuri ki bani lokaci, ina kan bincike ne"
"Amma Abie, to ina ya tafi, haryanzu ban san inda yake ba, kuma wayarsa ba ta shiga"
Sultan ya ce "Na sani, ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki. Zai dawo in sha Allah" Asal ta jinjina kai, ta tashi ta tafi, sai dai zuciyarta ta gaza haƙuri da samun nutsuwa.
Washegari, Sultan na tare da Sardauna da kuma Matawalle su na tattaunawa, aka zo neman iso cewar Imam Hammad yana neman izinin shigowa. Cikin takunsa mai burgewa, ya shiga. Gaba ɗaya suka zuba masa ido suna kallonsa. Hammad ya nemi guri ya zauna a ƙasa tare da gaishe su. Matawalle ya amasa masa. Sultan kuwa rasa abin cewa ma ya yi sai daga bisani ya numfasa ya ce "Ina ka tafi tsawon kwanaki uku haka, ka kashe wayoyinka ka tayar mana da hankali?"
Hammad ya numfasa ya ce "Ina mai bayar da haƙuri, na laifin da na aikata, na yi hakan ne, domin tabattar muku da abin da na faɗa. Ina cikin hayyacina na faɗi abin da na faɗa, kuma da shaida a kan abin da na faɗa". Sardauna ya ce "Ka na da hankali kuwa? Ka na nufin da gaske ka haihu da matar da ba mu sani ba?" Ya jinjina kai daidai lokacin da Mahmoudu ya shigo ɗakin shima."
Matawalle ya ce "Ga munafukin nan, ya san komai"
Sardauna ya ce "Ni kun sani a duhu, shi kuma wannan waye ya kawo shi cikin wannan mas'alar?"
Sultan ya ce "Bari mu ji ta bakinsa"
Mahmoudu ya zauna ya gaishe su. Sannan ya numfasa ya ce "Da fari ina neman afuwar mai girma Sultan, da ahalinsa da 'yan majalissar sa, da ma duk wani wanda abin ya shafa. Na san na aikata laifin da na cancanci hukunci, kuma a shirye nake na karɓi hukuncin laifina, na aikata abin da ya saɓa wa dokar masarauta duk da girman matsayin Imam Hammad a ƙasar nan"
Sardauna ya ce "Mu na jin ka, ka yi mana bayani, me ka aikata, kuma me a sani a kan lamarin?"
Sultan ya numfasa ya ce "Wato Sardauna mun ɓoye wa mutane abubuwa da dama da suka faru. Magana ta gaskiya Imam Hammad ya samu matsala ya bar ƙasar nan bamu sani ba. Mun yi ta bibiyar inda zamu samo shi. Muka rufe muka ce yana faransa babu lafiya. Da muka rasa shi, aka rasa hadiminsa Mahmoudu, shi ne muka koma binciken Mahmoudu ta ƙarƙashin ƙasa, aka yi nasarar gano su a Nigeria. Sai dai da aka dawo da shi Agadez tamkar ya manta da mu baki ɗaya, baya cikin hayyacinsa. Bamu san haƙiƙanin abin da ya faru a Nigeria ba, sai dai idan sun yi mana bayani yanzu.
Abin ya ɗaurewa Sardauna kai, gaba ɗaya bai san lamarin nan ba sai a yanzu, jin abin yake tamkar almara.
Mahmoudu ya ce "Bayan na tafi da Shugabana Imam Hammad Nigeria, nema masa magani, bayan da na fuskanci ya manta duk wani abu da ya shafe shi. A can muka haɗu da yarinyar a gidan da muka zauna, mahaifinta ya ba shi aurenta. Shi da kansa ya ce a biya sadakin aurensa da ita. Tun da shugabana ne ba ni da 'yancin yi masa musu. Na yi ƙoƙarin tunatar da shi, amma ko na tuna masa, ba zai iya tuna komai da ya shafe shi ba"
Matawalle ya ce "Wai wannan wace irin shiririta ce ku ke karanta mana? Wane irin abu ne haka? Ta yaya mutumin da ya manta komai ya san ya ce a biya masa sadaki ya yi aure?"
Mahmoudu ya ce "Imam waye shi, da duk abin da ya shafi Agadez ya manta, amma duk wani abu na rayuwa na yau da kullum ya sani. Kuma ga shi a tambaye shi, tun da yanzu yana iya tuna abubuwan da suka faru a Nigeria"
Sardauna ya ce "Shi tunanin nasa network ne kenan, ko zamani da idan wannan ya zo wannan zai wuce?"
Kafin Mahmoudu ya bayar da amsa, Matawalle ya ce "Wato Mahmoudu ba ka ji kashedin da na yi maka ba a kan sanar da shi wani abu ba"
Mahmoudu ya ce "Ba laifina ba ne ranka ya daɗe, shugabana ne duk abin da ya umarce ni, dole na yi ba ni da zaɓi"
Hammad ya miƙe ya ce "Ina zuwa" Ko da Hammad ya fita, Mahmoudu suka ci gaba da yi wa tambayoyi, yana ta ƙoƙarin basu amsa da rufa wasu abubuwan.
Tsit suka yi da suka ga Hammad ya dawo, Nene na bin sa a baya da ɗa a hannunta.
Matawalle ya ce "Imam me ya kawo wannan matar gidan nan kuma?" Nene ta yi turus tana haɗe rai ta sunkuyar da kai. Kafin su ƙara magana, Muhsin ya jefo mayafin kansa ƙasa, tare da waiwayowa yana kallon mutanen gurin. A sukwane Sultan ya miƙe tsaye. Imam Hammad ya karɓi Muhsin daga hannun Nene, ya nufo Sultan da shi. Jikin Sultan ya hau tsuma, yana kallon yaron da ya jiye tamkar Hammad ɗin sa yana ƙarami. Shi kuwa Muhsin kallon babansa ya din ga yi yana kallon Sultan, ganinsu iri ɗaya. Ya miƙa hannu ya ɗauki Muhsin yana faɗin "La haula wala ƙuwwata illa billah"
Su kan su Sardauna da Matawalle, ƙura wa yaron ido suka yi, duk sharrin mai sharri ƙarya ne ya ce wannan ɗan ba na Hammad ba ne ba.
Matawalle ya ce "Ikon Allah, da gaske dai Hammad yana da ɗa"
Sultan ji yake yi tamkar ya haɗiye Muhsin, da a yake son ya sauke shi ya koma gurin Nene. Ya juya yana miƙawa Hammad hannu ya ɗauke shi.
Sardauna ya miƙe ya ce "Yanzu ina uwar yaron take" "Tana nan" Imam ya faɗa yana sunkuyar da kansa ƙasa.
Sardauna ya ce "Akwai rikita-rikita a lamarin nan. Dole a san yadda za a yi. Mu na buƙatar ka zo mana da uwar yaron nan, gobe in Allah ya kaimu. Ku kuma zamu tsare ku har sai komai ya daidaita mun gano komai."
Nene ta ce "Ranka ya daɗe me zai sanya a tsare ni? Mahmoudu ne naku dama, ku ci gaba da tsare shi da duk abin da za ku yi masa, amma ni ina roƙon alfarma a ƙyale ni na tafi"
Matawalle ya ce "Jayayya za ki yi da abin da muka ce kenan?"
Nene ta sunkuyar da kai ta yi shiru. Hammad ya ce "Zan cika miki alƙawarin da na ɗauka, babu abin da zai faru in sha Allah, ki yi haƙuri gobe in Allah ya kaimu zan zo da ita" Nene ta yi shiru cikin sanyin jiki.
Duk yadda Sultan ya so ƙanƙame Muhsin ya ƙi yadda, ya zamo ya sauka daga jikinsa, ya koma jikin Nene ya kwanta, ya saka hannunsa a baki. Gaba ɗaya Sultan ya kasa zaune ya kasa tsaye, saboda ganin Muhsin, bayan shafe lokaci yana fatan ɗan nasa ya samu haihuwa.
Sardauna ya ce "To ita matar Mamman me ya kawo ta cikin wannan lamarin ne? Na ga kamar yaron ma ya santa?x
Hammad ya ce "Eh, a gurinta yake ne" Haka aka killace Nene da Mahmoudu, aka hana su zuwa ko ina.
*****
Ko da ya shiga sashensa babu kowa, Asal ba ta nan, ya yi mamakin inda ta tafi. Ya tafi kitchen ɗin da Nana take girki, ya shiga ya buɗe fridge ya samu sassanyar madarar raƙuma, ya tsiyaya ya fita. A ƙalla ya kai awanni biyu a zaune, sai ga Asal ta dawo, babu tsammani ta gan shi a falo a zaune. Ɗan turus ta yi tana kallon sa. Ya ce "Ƙaraso mana" Jiki a sanyaye ta ƙarasa ta zauna a kusa da shi.
"Ina ki ka je haka?"
"Nemanka na je yi" ta furta jiki babu ƙwari.
"To zan gudu ne? Ai gani na dawo"
"Wancan karon ma ai ka tafi ka bar ni"
Ya yi murmushi ya ce "Wannan na larura ne ai Cherié" Ya yi maganar yana miƙewa, har ya nufi bedroom ta ce "Hammad" tsayawa ya yi cak, jin ta kira shi da gundarin sunansa na yanka. "Da gaske ka haihu da wata a waje ban sani ba?"
"Waye ya gaya miki?"
Asal ta kalle shi ta ce "Kar ka amsa tambayata da tambaya, ka bani amsa ko na samu nutsuwar zuciya, babu abin da yake yi mini daɗi. An ce ka kira ni da juya, kuma ka ce ka na da ɗa, da gaske haka ne?" Ta yi maganar hawaye na cika mata ido.
Sai ya fasa shiga ɗakin, ya nufi inda take zaune, ya tsura mata ido sannan ya ce "Ni da ke na taɓa gaya miki haka? Ta girgiza kai jiki a sanyaye.
"Wanda ya gaya miki ya so cin mutuncinki ne, amma da bakina na taɓa faɗa?" Ta girgiza kai jikinta a sanyaye.
"To ki toshe kunneki daga jin abin da za a zo a gaya miki wai wai, ki jira abin da zai fito daga bakina zuwa kunnuwanki"
Ta yi ajiyar zuciya ta ce "To, amma ba ka gaya mini inda ka je ba"
"Wani aiki nake yi wa Sultan, ki kwantar da hankalinki" Ya miƙe ya tafi ya bar ta a gurin. Da magariba ta ga yana ta shiri, ta ce "Amour ina zaka je ne?" Ya ce "Eh yanzu zan yi miki bayani, zan je wani aiki da Sultan da ya saka ni ne, sai gobe in Allah ya kaimu zan dawo"
"Aiki kuma sai da daddare?"
Ya kalle ta ya ce "Asal, wai ki na zargina ne, yau na fara fita yin aiki da daddare, me yasa za ki tsare ni da tambayoyi kamar ba ki yarda da ni ba, shirya mu tafi tare" Yayi maganar yana haɗe rai. Ta risunar da kai cikin girmamawa ta ce "Tuba nake yi, zuciyata ce ta cika fargaba, amma ka yi haƙuri" Ya miƙe ya nufi hanyar fita, haka nan zuciyarta ta tsananta bugawa.
Bayan fitarsa ya tsaya a harabar gidan, ya ɗauki wayarsa ya kira Tafawa. Tafawa ya ɗaga tare da yin sallama. Hammad ya amsa tare da cewa "Barka da dare ranka ya daɗe"
"Barka dai" Ya amsa a taƙaice.
"Yauwwa, dama na kira ka ne na sanar da kai, ka san abin da za ka din ga sanar da Asal, ka daina shiga cikin batun iyalina, idan ba haka ba za ka iya saka wa ta rasa ranta ko lafiyarta"
"Hammad, ni ka ke gaya wa haka?"
"Kai ka bani damar na gaya maka hakan ai. Abin da ba ka sani ba shi ne, Asal ta riga ta fara so na, tsawon lokacin da ya gabata, ci gaba da gaya mata magana kowace iri a kaina, ka iya haifar mata da matsala. Amma 'yarka ce duk abin da ka ke ganin shi ne daidai ka yi ba wani abu" Ya kashe wayarsa gaba ɗaya, ya shiga mota da kansa ya ja motar ya bar gidan.
A zaune ya tarar da Nana a ɗakin da kayanta suke, ta sanya atamfa riga da skirt, kanta babu ɗan kwali. Ta yi parking ɗin black natural hair ɗin ta, da siririn band na yi wa yara kitso. Dan zabura ta yi, da ta ji motsinsa. Hannunsa riƙe da ledoji, ya ƙarasa ya zauna ya ajiye ledojin ya ce "Sannu da gida, na bar ki ke kaɗai ko?"
"Dama can ai nikaɗai ɗin nake rayuwata"
Ya yi murmushi ya ce "Haka ne, amma dai kin rayu da ni ɗin ko?" Ta yi masa shiru tana kai hannunta ta ɗauki ɗan kwalin kayan, za ga ɗaure kanta. Ya janye ɗan kwalin ya ce "A haka nake son ganinki, kin yi mini kyau sosai da sosai"
"Sayyid, duk wannan abubuwan da ka ke yi, ba za su taɓa tasiri a kaina ba, ka bani ɗana kawai na kama gabana"
"Gaskiya ne maganganuna ba za su yi tasiri a kan ki ba, ciki har da kirana da Sayyid. Ga abinci na kawo miki, ki ci"
Ta kalle shi cikin damuwa ta ce "Ai na ci Abincin kamar yadda ka ce, yaushe za ka ba ni ɗa na?"
"Kin ci, amma ba kamar yadda nake buƙata ba, sonake ki ƙara ƙiba, alamu sun nuna ba kya nutsuwa ki ci abinci ki ƙoshi" Ta kawar da kanta gefe, dan kar ma ya ci gaba da jan hirar. Dan ba ta son duk wani abu da zai sanya a ranta ta ji za ta iya ci gaba da rayuwa da shi."
Ya kwance rawaninsa, ya rage kayan jikinsa, ta kawar da kanta gefe, ƙirjinta na bugawa da sauri da sauri. Ya zauna a kusa da ita ta ɗago ta kalle shi, gashin nan a kwance ya sha gyara. Ya ɗago mata yatsunsa ya ce "Ina zobena ne? Kin saka an addabe ni a kan zoben nan da yawa" Yana nuna mata yatsunsa.
Ta yamutsa fuska ta ce "Na yar da shi"
"Kin yar da zobena, kin ajiye turarrukana da mayukan gashina, ki na kallo ki na jin daɗi. Soyayyar gaskiya mara algus. Gobe in Allah ya kaimu za mu je gaban Sultan, mu ji hukuncin da za a yanke mana. Saboda na aikata laifi mai girman da babu wanda ya taɓa aikata shi sai ni."
Ayshercool. 08081012143 81 Nana ta taɓe baki ta ce "Wanda za a yanke maka dai, ni babu abin da ya haɗa ni da masarautarku, kawai a bani ɗa na na tafi"
Ya zura mata ido, ya jinjina kai ya ce "Kin daina so na dai kenan ko?"
"Eh" ta faɗa tana kawar da kanta gefe.
"Shikenan, zan ƙara miki lokaci, zuwa lokacin da ki ka ga ya dace ki saurare ni, amma ki sani, ni shugaba ne, kuma wasu lokutan idan aka tashi kawo gyara, toshe kunne muke yi, mu farantawa wani mu ɓatawa wani, domin samar da gayar. Dan haka duk abin da ya kama zan banƙara na aikata, domin ganin ba ki suɓuce mini ba, ko da kuwa abin da zan aikata ɗin na nufin ƙara miki ƙiyayyata. Yanzu dai ga abinci ki samu ki ci, sai ki kwanta ki huta da wuri zamu tafi" Ta murguɗa baki ta sake kawar da kanta gefe. Duk wannan abubuwan da take yi masa, ko sau ɗaya bai ji haushinta ba, shi dai fatansa da roƙonsa ta saurare shi cikin nutsuwa, ya warware mata zare da abawa, saboda ya san ko shi ne haka ta faru a kansa, zai ce wulaƙanci ne aka yi masa. Ganin ya ƙi tashi ya bata guri, ya sanya ta ɗago ta kalle shi, ta ga ya zuba mata ido, kamar zai lashe ta. Ta sake kai hannu ta ɗauki ɗankwalinta, amma ya jefa shi bayansa. Wannan kallon da yake ƙanƙance ido ya fara yi mata, ta ƙara tsuke fuska tana tattara nutsuwarta, amma ya kai hannunsa kan gashinta, ya fara shafawa a hankali. Bai sani ba ko dan ya saba ganin irin gashinsu Asal na buzaye nai laushi da santsi ya sanya na Nana yake burge shi. Baƙi ƙirin da shi natural, mai cika sosai da sosai. Ta hau ture hannunsa, amma yaƙi barin abin da yake yi, sai ma lumshe mata ido da ya hau yi. Duk wani abu da Nana za ta yi ta baƙanta masa rai, tana aikatawa domin gujewa barin nusarar zuciyarta ta sake yarda da shi, ta ba shi wata damar ya cutar da ita.
Sai da ya bar ɗakin ta samu ta ci abinci, ta tura ƙofar ɗakin, sai dai babu mukulli yadda za ta datse ƙofar dan kar ya shigo mata. Tana kwanciya bacci, nannauyan bacci ya sake yin awon gaba da ita.
***** Doctor Sharif ne ya tashi a razane, bayan mummunan mafarkin da ya yi da Shukura, ta biyo shi tana kuka jikinta duk jinin haihuwa, da wata sharɓeɓiyar wuƙa tana, ya ba ta jaririnta. Ya din ga gudu yana ihu, ya ɗan tsaya ya waiwaya kawai ya ganta a tsaye a kan matarsa, da wannan wuƙar a hannunta, tana kallon cikin tana kallonsa tana faɗin "Ka zo ka bani jaririna, ko na farka cikin matarka na ɗauke nata, ka ji abin da na ji" A daidai nan ya tashi cikin razani, ya haɗa uban gumi. Ya kalli agogon ɗakinsa ya ga ƙarfe biyu da kwata na dare, kawai ya ji zuciyarsa ta kasa nutsuwa, so yake ya je ya ga halin da matarsa take ciki, amma ya tuna wa zai fita ya bar wa yaransa mata su biyu da suke bacci. Doctor Sharif bai samu haihuwa da wuri ba bayan ya yi aure, sai da suka shekara goma sannan ta haifi yara mata biyu, yanzu za ta yi na uku ciki yana ta wahalar da ita. Tun da ya haɗa kai da Alhaji Zailani ya ba shi jaririn Shukura abin yake damunsa, amma tun da Alhaji Zailani ya shaƙa masa kuɗi, sai ya manta sai kuma yau da ya yi wannan mummunan mafarkin.
**** Yau ma Nana a kan gadon rannan ta hango Ƙaisar, lulluɓe da mayafi, hannunsa kawai ya ziro ta ƙasan mayafin yana rubutu a kan wani littafi.
Ya ɗago kai ya kalle ta, ya ci gaba da rubutunsa.
"Ƙaisar"
"Na'am" ya amsa ba tare da ya kalle ta ba. "Wai dan Allah me ya same ka?"
"A ina?"
"Na ga yanzu kullum ka na kan gadon nan, kuma a lulluɓe. Giyaz ne ya yi maka wani abin ne?"
Ya girgiza kai ya ce "A'a me ki ka gani?"
"Na san shikaɗai ne yake iya cutar da kai" Ta yi maganar a sanyaye.
"In ji wa? Akwai Aljanu masu ƙarfi da suka fi ni ƙarfi da za su iya cutar da ni. Kawai ni ba na shiga harkar kowa ne, ina gefe ina jin daɗin rayuwar kaɗaicina da litattafaina da haɗa magunguna na"
Nana ta yi murmushi ta ce "Yaushe za ka yi aure ne kai?"
"Sai na girma"
"Au yanzu baka girma ba? Ina Haula ne?"
Tsuke fuska ya yi ya ce "Je ki ɗakin magungunana, akwai wata kwalba taswirarta kamar zanen Duniya, ki ɗaukko ki kawo mini" Nana ta ce "To" Ta nufi ɗakin da yake ajiye-ajiyen kayan maganinsa. Ta tsaya tana ta kallon kwalaben, da yadda wasu magungunan suke yawo a cikin kwalaben, tamkar abubuwa masu rai. Ta ga wanda ya ce ta ɗaukko ta waiwayo kawai ta ga Giyaz a tsaye a bayanta.
"A'uzubikalimatillahi tammat" Ta furta cike da tsoro, a suffarsa ta tsoho tukuf ya bayyana a gabanta.
Ya buɗe baki ya ce "Ban taɓa ganin halittar da na tsana a doron ƙasa ba sama da ke, sai na sabauta rayuwarki, sai na kashe ki na ƙarar da zuriyarku na huta da wannan bala'in. Ya ja da baya ya nuna ta da sandarsa, da take ci da wata irin wuta mai tartsatsi. Nana ta ja da baya, ta saka hannayenta ta rufe fuskarta, tana jiran jin wutar ta fara ƙona ta, amma ta ji shiru. Ta buɗe idanunta a hankali ta ga Ƙaisar ya shiga tsakiyarsu, tartsatsin wutar ya ƙona shi, ya faɗi a gefe jikinsa yana hayaƙi. Nana ta saki kwalbar ta nufe shi da gudu. Cikin tashin hankali da tsoro ta ce "Ƙaisar, me ya same ka?" Sai a lokacin ta ga tarin raunukan da suke jikinsa, ga ƙonewar da ya yi yanzu. Giyaz ya ƙaraso kan Ƙaisar da sauri, ya saka hannunsa ya ɗago shi, amma ya ga jikinsa ya saki.
"Wallahi muddin ɗa na ya mutu sai na kashe ki har lahira"
Cikin dakiya da kawar da tsoro ta ce "Me ka yi masa? Kai wane irin azzalumar halitta ne wai, kowane abu yana alfahari da ɗansa da ƙoƙarin ba shi kariya, amma kai kullum cikin ƙoƙarin cutar da shi ka ke. Ƙaisar ka tashi dan Allah. Ta yi maganar cikin kuka tana ƙoƙarin taɓa shi, amma wani irin matsanancin sanyi ya ratsa ta. Ta buɗe idanunta a hankali cikin sheshsheƙar kuka, har da majina kawai ta ganta a jikin Sayyid ya riƙe ta gam yana kallonta cikin tausayawa. Ta yinƙura za ta tashi amma ya hana ta, ya ce "Ki bari ki ɗan nutsu. Me ya same shi ki ke wannan uban kukan haka? Idan komai ya lafa mini, dole na ɗauki mataki a kansa, dan ba zai yiwu ya din ga bibiyar matata ba, ina baƙin ciki da hakan"
"Ba za ka yi masa komai ba, babu ruwanka da shi, tun da dai duk da tsana da abubuwan da nake yi masa, shi bai gudu ya bar ni ba, kamar yadda ka yi mini ba"
Ya ɗan zura mata ido har zai yi magana sai kuma ya fasa. Ta zame daga jikinsa ta kwanta, zuciyarta cike da damuwa da tashin hankali, tare da fatan Allah ya sanya ba wata mummunar illar Giyaz ya yi masa ba. Ya tashi ya bar mata ɗakin, dama kukanta da sheshsheƙarta ya jiyo, shi yasa ya fito ya je ɗakin nata. Washegari da safe, ya kawo mata kayan da za ta saka su tafi. Ya kalle ta cikin magiya ya ce "Ma vie, na san ni mai laifi ne a gurinki, amma dan Allah ki tattara nutsuwarki guri guda, domin mu samu mafita. Duk abin da za su tambaye ki, ki sanar musu da komai, kar ki ɓoye musu komai saboda makomarmu"
"Ni ba wata makomarmu, kawai ɗa na za a bani na tafi"
Ya ce "To na ji, ga riga da za ki saka, ki je ki yi wanka ki shirya, ina jiran ki" Ta kalli rigar kamar ba zata karɓa ba, sai kuma ta karɓa ta ce "Na gode"
Ya yi murmushi ya ce "Ko mu je ki yi wankan a ɗakina, akwai mayukan shafawa"
"A'a ina da man da zan shafa"
"To su ma nawan ne dai ki ke shafawa, saboda tsabar ƙauna" Ta murguɗa baki ta juya ta ajiye kayan, murmushi ya gaza barin fuskar sa. Ya ce "Kin san me na tuna? Lokacin da ki ke yi mini wanka mu na Nigeria, sauran ki yi mini wanka a Agadez".
"Sai ka je gurin Gimbiya hamshaƙiya, farar fata da take biladama ta yi maka" Ta yi maganar ba tare da ta juyo ba. Ko da ta yi yinƙurin juyowa, sai jikinsu ya haɗu, sam ba ta san ya ƙaraso bayanta ba, saboda cikin takunsa mai kama da hawainiya ya ƙaraso. Dan sam ba shi da hayaniya ko karakaina. Ya saka hannunsa ya zagaye ƙugunta, ƙirjinta ya tsananta bugawa tsoro ya bayyana ƙarara a fuskarta.
"Ma viee banda dalilin soyayyarki, ta sarƙe ni ta ko ina ta hana ni motsi, da sai na saka an sa bulala an zane mini ke. Imam Hammad ki ke yi wa magana a haka? Ki yi mini magana cikin girmamawa, ki daina ɗaga mini murya" Ya yi maganar yana sunkuyo da fuskarsa daidai ta ta har su na jin numfashin juna. Yana murmushi ya ce "Na taɓa yi miki wannan kashedin, kin tuna?" Ya yi maganar yana kashe mata ido. "Dan haka ke za ki yi mini wanka a Agadez da ma"