Buzu book 3 complete - Chapter 11
Buzu book 3 complete Chapter 11: Buzu book 3 complete Chapter 11. "To shikenan, idan akwai wani abu, ki sanar da Mahmoudu ya gaya mini. An je za a taho da…
3,323 words
"To shikenan, idan akwai wani abu, ki sanar da Mahmoudu ya gaya mini. An je za a taho da mai magani ya zo ya duba shi, idan kuma abin ba zai yiwu ba zamu kai shi Asibiti" Nana ta jinjina masa kai kawai.
Inda Allah ya taimaki Nana, akwai pad a cikin kayanta, sai dai yanayin gurin babu gurin discarding pad ɗin. Cikin ikon Allah kuma ba ta zubar da jinin sosai.
**** Sultan na zaune a sashensa, ya gama ganin wasu baƙinsa, aka yi wa Asal iso, ta shiga gurinsa. Bayan sun gaisa ta ce "Abie dama na zo ne ina son duba jikin Imam"
Sultan ya gyara zamansa ya ce "Yarinyar kirki, Imam Hammad yana cikin yanayin da ba zai so a cika kawo masa ziyara ba. Dan haka mu na son ya samu hutu ne, kafin lokacin da za a samo mai maganin da zai duba shi"
Cikin damuwa Asal ta ce "Ko sau ɗaya ne Sultan, jiya kwana na yi ina mafarkinsa, ina cikin damuwa ne"
Ya ce "Na ga alamun hakan a tattare da ke, amma ki yi haƙuri ba za ki samu ganinsa ba, zuwa lokacin da zai samu afuwa sai ki gan shi har ma ku koma gida ma"
Ba dan Asal ta so ba, haka ta haƙura ta tashi ta tafi. Tana kan hanya kiran Tafawa ya shigo wayarta.
"Yaya ake ciki?" Ya tambayeta ba tare da amsa gaisuwar da ta yi masa ba.
Ta ce "Yau ba a bani damar ganinsa ba, Sultan ya ce mini jikinsa ya yi zafi, dan haka ba zan samu ganinsa ba. Dole na jira zuwa lokacin da za a samo mai magani ya duba shi"
"Ya dai tabatta haukan yake yi ko? Lokaci ya yi da zan bankaɗa abin nan, yadda Sultan zai kunyata daga shi har ɗan nasa"
Asal ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, ba hauka yake yi ba, rashin lafiya...
"Ke yi mini shiru, abin da na yanke dole haka za a yi, kar ki sake ki sake yi mini musu" Ya katse ta yana yi mata tsawa da dole ta sanya ta yin shiru.
***** Alhaji Fatuhu ne ya kira wani abokinsa, ya ce ya zo ya kai shi gidan Yayarsa Hajiya Sa'a a motarsa, saboda yadda baya samun ta kwana biyu a waya.
Ko da yaje gidan, mai aikinta ta sanar da shi cewa ta ce ko waye ya zo, kar a sake a dame ta.
Ya kalli mai aikin ya ce "Ko wannan dokar za ta yi aiki a kan kowa, ba za ta yi a kaina ba, dan haka yi mini magana da ita"
Mai aikin ta shiga ta fito, ta ce "Na yi mata magana ba ta kula ni ba"
Ba shi da zaɓin da ya wuce ya shiga ɗakin nata da kansa. Ya tarar da ita a zaune, daga mutuwar Abba zuwa yanzu ta yi wani irin tsufa, jikinta duk ya saki. Fuskarta duk ta yi wani iri kamar ba ita ba.
A hankali ya taka da sandarsa, sai ta ƙura masa ido tama fara tunanin a ina ma ta san shi? Gaba ɗaya sai kanta ya toshe ta kasa tuna waye shi.
Sai da ya ce "Yaya Sa'a, lafiya kuwa?" Yana yin maganar, sai kuma ta tuna shi. Ta yi zuru tana tunanin ya aka yi ya samu lafiya haka har yake iya takawa?
"Yaya Sa'a me yake damunki?" Ya yi maganar cikin damuwar halin da ya tarar da ita. Kawai ta fashe da kuka.
Cikin damuwa ya ce "Haba ke kuwa, kamar ba musulma ba, yanzu da ke Allah ya jarabta da halin da nake ciki yaya za ki yi? Dan Allah ki yi haƙuri mu ci gaba da yi wa Abba addu'a, amma wannan hanyar da ki ka ɗaukko, ba mai ɓullewa ba ce ba" Ya yi ta rarrashinta da lafuzzan ƙwarin gwiwa. Ya sanya mai aikinta ta kawo Abinci, ya tabbatar ta ci sannan ya yi mata sallama ya tafi. Sai dai bayan tafiyarsa sai ta hau tunanin abin da ya faru gaske ne ya faru, ko kuwa dai mafarki ne. Gaba ɗaya. Haka ta zauna tana ta lissafin yanayin.
*****
Bayan majalisar Sultan ta cika, domin ci gaba da gudanar da sha'anin mulki na Agadez. Akwai takardu da a kan turo domin gabatar da su a tattauna.
Mai karanto takardun ya warwareta, ya zuba wa takardar ido sannan ya numfasa ya ce "Zuwa ga Sultan da 'yan Majalisar sa baki ɗaya. Sanin duk wanda ya kwana ya tashi a Agadez ne, babu wani abu da muke martabawa, bayan addininmu kamar al'adarmu. Mu na kira ga Sultan da 'yan majalissar sa, su gaggauta duba ga al'amarin Imam Hammad. Babu yadda za a yi ya ci gaba da jagorantar majalissar Imam, ba tare da zoben tambari ba, wanda kawo yanzu babu wani cikakken bayani a kan inda zoben nasa yake. Sannan ya yi iƙirarin yana da ɗa, wanda haryanzu ba mu ji matsayar binciken da aka ce za a gudanar ba. A dan haka muke kira ga sauran 'yan uwanmu na majalissar Sultan, a gaggauta sanar da mutane sakamakon binciken da aka gudanar, sannan Imam Hammad ya fito gaban majalisar sarki, ya kare kansa, ko kuma ya sauka daga kan muƙaminsa na shugaban majalisar Imam, har zuwa lokacin da sakamakon binciken iƙirarin da ya yi na yana da ɗa zai fito. Idan kuma shaci faɗi ne abin da ya faɗa ta tabatta yana da matsalar ƙwaƙwalwa, kamar yadda jita-jita ta yi yawa.
86 A SAUKE HAKKI, A BIYA KUƊIN KARATU 0069685771 AISHA ADAM STANBIC 08081012143 Gaba ɗaya tsit majalissar ta yi, aka rasa wanda zai sake cewa wani abu. Wani abu mai ɗaci ya tsirga wa Sultan a zuciyarsa, yana takaicin kasancewar Tafawa ɗan uwansa, yadda yake nuna son ganin bayan jininsa wato Hammad duk saboda mulki. Ya san ko ba a gaya masa ba, da saninsa aka rubuta wannan takardar aka kawo. Surutu 'yan majalissar suka fara yi ƙasa-ƙasa. Sardauna ya numfasa ya yi gyaran murya, duk aka yi shiru Sannan ya ce "Ina ga wannan maganar mun riga mun yi ta a baya. Ban ga amfanin sake dawo da ita ba, mu na nan ana kan bincike a kan al'amuran kuma za a zo da sakamakon binciken, sake dawo da maganar ba abu ne da zai taimake mu ba, duba da yadda muke da tarin abubu a gabamu, da yakamata a ce an mayar da hankali a kai" Ɗaya daga cikin mutanen majalisar ya ce "A'a Sardauna, ba na tunanin wannan ba maganar da za a tattauna ba ce ba. Kar ka manta goben Agadez ta ta'alaƙƙa da waɗannan Imam da aka naɗa, su ma suke jagorantar wasu al'amuran na sha'anin sarauta, muddin aka ce da tangarɗa kuma ba a ɗauki wani mataki ba, to yana nufin goben ƙasar nan yana cikin hakin da ba a sani ba"
Matawalle ya ce "Turaki ai dama sanin gobe sai Allah. Mu muna bulayinmu ne kawai. Amma kamar yadda mai girma Sardauna ya ce, a jira sakamakon binciken ya fito tukuna. Sannan wani batun taɓin hankali da ake danganta Imam Hammad da shi, batu ne mara tushe balle makama, sannan duk wanda muka samu da yaɗa wannan zancen, za a ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki a kansa." Haka aka so tayar da hatsaniya, sai da Sultan ya tsawatar, haka aka watse daga zaman babu wata ƙwaƙwƙwarar magana. Sultan ya san tabbas tun da Tafawa ya samu magoya baya a Majalisa, al'amura za su sake dagulewa ne, kuma za su ci gaba da bibiya su ji ƙwal uwar daka.
*****
Shukura ce a kwance a ƙasa, sai burgima take yi, wani irin matsanancin ciwo yana ratsa ta. Sai jujjuya kanta take yi a galabaice. Kamar kullum mai ba ta abinci ya buɗe ƙofar ya ziro abincin ya ajiye mata ya tafi. Sai dai a duk lokacin da aka kawo mata abincin, idan aka rufe ɗakin duhu ne yake gauraye ko ina, amma sai ga yau da sauran haske. Ta ɗaga kanta a mugun galabaice ta kalli ƙofar ta ga kamar ƙofar ce ba ta rufu ba. Ta lumshe idanunta cike da azabar ciwo, wata zuciyar na azalzalarta ta je ta buɗe ƙofar ko a buɗe take, wata zuciyar kuma ta ce mata wahalar ciwo ne kawai amma ƙofar a rufe take. Ta ji ciwon na ƙara tsananta, yayin da wani abu mai ɗumi da ba za ta iya tantance ko na mene ne ba, yake bin ƙafarta. Ta din ga jan jikinta a hankali, ta lalubi bango ta dafa, a durƙushe ta ƙarasa gaban ƙofar ta saka hannu ta ja, kawai ta ga ƙofar ta buɗe. Ta zura kanta ta lelleƙa ta ga babu kowa a harabar gurin, daji ne sosai aka yi ɗakin a cikinsa. Tana faɗin "La'ila ha illa Anta Subhanaka Inni Kuntu mina Zalumin" Ta ci gaba da jan ƙafafuwanta tana takawa a hankali. Ko da ta duba jikinta sai ta ga alamun faya ce ta fashe, ga ruwanan mai haɗe da jini a jikin ƙafafuwanta da rigarta. Ba ta damu da yadda take gani dishi-dishi ba, saboda azabar galabaitar da ta yi, da kuma haske da ya cika mata ido, kawai ta saɓi hanyar da ba ta san ina ne ba, ta hau tafiya. Duk da duk taku ji take yi tamkar ɗan cikinta zai faɗo saboda nauyin cikin da azabar ciwo. Tafe take tana addu'a Allah ya kuɓutar da ita.
Alhaji Fatuhu kuwa bayan komawarsa gida su na hira da Fadila ya ce "Fadila yakamata ku je ku duba Yaya Sa'a, saboda tana jin jiki nesa ba kusa ba, duk ta rame ta fita daga hayyacinta. Ta bani tausayi sosai da sosai haryanzu tana jin raɗaɗin mutuwar nan"
Fadila ta ce "Allah sarki, har na tuna lokacin da na rasa Muhsin ɗina, da ta ce ba ni da tawakalli kamar a kaina a ka fara haihuwa, Allah sarki yanzu ta ji abin da na ji"
Ya tsuke fuska ya ce "A taƙaice dai, gaya mini magana ki ke yi"
Ta girgiza kai ta ce "Wace ni? Ai ban isa ba, kawai dai na tuna abin ne, kuma ya daɗe yana yi mini zafi"
"To koma dai mene ne yanzu ya wuce, zan gaya wa Suwaiba, yakamata ku shirya ku je ku duba ta, a yi mata sannu, idan babu hali ma ina ga gara ta dawo gidan nan da zama, wataƙila kai komonmu zai rage mata damuwa da kaɗaici" Cikin sanyin ta ce "Ka manta ne? Ka manta mu ma a under notice muke, daga yanzu ko wani lokaci an ce mu fita mu bar gidan nan?"
Ya yi shiru ya tafi zancen zuci. Ta ce "Dan Allah kar ka ɗaga hankalinka, mun samu Allah ya sanya ka farfaɗo da kyar. Ni da Maman su Janna za ta yarda da ɗan abin hannuna da nata, mu samu ko karamin gida ne a saya, ni ba na son hayar nan ko ɗaki uku ne mu koma"
Ya waro ido ya ce "Ɗaki kuma? Ina ɗaki uku zai ishe mu rayuwa? Ko sashenki ɗakuna huɗu ne da falo biyu, ya yi mana kaɗan"
Fadila ta ce "Daddy ka manta wacece Fadilan taka ne? Sai dai ku ya yi muku wahalar rayuwa ai ni na riga na saba, gidanmu ma na da daka auro ni ai ɗaki biyu ne ni da Umma"
Ya ce "Ki daina tuna abin da ya wuce mana, ni ba ga shi kin zamo mana alkhairi ba. Da na tsaya duba wani shrime da ƙyale-ƙyale da daga ke har Suwaiba ba na tunanin za ku kasance da ni, duk da halin da muka tsinci kanmu. Ina ƙara yi muku godiya sosai da sosai"
Fadila ta ce "Haba Daddy, ka cancanci fiye da haka daga gare mu, lokacin da ka ke da wadata ba mu ba, na kusa da mu ma ka yi musu, ka gatantamu ka kula da mu, sai Allah ya kawo mana jarrabawa kuma mu juya maka baya, da Allah bai barmu ba kuwa"
Ya ce "Ke dai a yi sha'ani masoyiyya, idan Allah yana ƙaunar bawa, idan ya jarrabe shi ta nan, sai ya sassauta masa ta can, da yawa idan larura ta same su, iyalan nasu barin su suke yi. Kin san wani abu kuwa?" Ta ce "A'a sai ka faɗa Angona" Ya tuntsure da dariya ya ce "Ango ko?" Ta ɗaga masa gira tana murmushi. Ya ɗan ja kumatunta yana murmushi. Ya ce "Wannan rahar ma da nake yi da ke, ba tare da kin sauya mini ba saboda ba ni da lafiya, kuma ba ni da abin hannun yanzu ba, wallahi ba ƙaramin daɗi nake ji ba. Haƙiƙa larurar nan ta ƙara mini tsoron Allah da imani, ya ƙara kusantar da ni da Ubangijina, a duk lokacin da na motsa ambaton Allah kawai nake yi, gani nake rayuwata ce ta zo ƙarshe. Saɓanin lokacin da nake da dukiya da lafiya, ina ambaton Allah amma ba can sosai ba, ba kamar yadda na ƙara samun kusanci da Ubangiji ba lokacin da na rasa komai. Kuma a jikina nake jin wani tagomashin alkhairi yana kusanto mu in sha Allah"
Ta ce "Haka ake so Daddy, ina fatan kuma ka canza tunaninka a kan magungunan gargajiya da na addini yanzu"
Ya yi dariya ya ce "Na canza tuni, ke dai madalla da ke matar aljanna" Suka ci gaba da hira cike da nishaɗi.
*****
Kwanakin Nana uku tare da Hammad, jikinsa ya yi ƙalau abin sa, sai dai magana ce babu. Nana ta yi iya ƙoƙarinta gurin tana kauce wa duk wani abu da zai sanya faruwar wata mu'amala tsakaninsu. A ƙasa suke kwana, ba ta taɓa kwanciya sai ya yi bacci, sai dai wasu lokutan ta ji ya ƙanƙameta idan ciwon ya motsa Sai dai tun da ya warware sosai, take ganin kamar ya canza mata, wani irin kwarjini yake yi mata yanzu, mussaman idan ya saka ta a gaba da kallo duk sai ta rikice. Ta kasa gane take-taken sa. Sai dai ta riƙi karatun Alkur'ani sosai da sosai. Sai dai tun wannan ganin na ƙarshe da ta yi wa Ƙaisar, ba ta sake ganinsa ba, ko a farke ko a cikin bacci ba. Duk ta damu shi ma ta na son sanin halin da yake ciki. Ga shi gaba ɗaya ta rikice, a kwana ɗayan da ta ga jinin nan, ba ta iya tantance wane jinin ta yi ba. Ɓari ko na haila. Tuni aka ƙara ƙawata ɗakin da kayan alatu, da kayan wanka da shafe-shafe na Imam Hammad, da duk wani abu da za su buƙata. Yana banɗaki yana wanka, ta gama cika cikinta da kayan marmari, dan ba ta fiye cin abincin da Mahmoudu yake kawowa ba, fruit take samu ta ci ta ƙoshi ta ci nama. Sai da ta fara tsorata kanta da tunanin anya ba cikin ne da gaske ba. Ta yi zurfi sosai da sosai a cikin tunani. Razana ta yi jin yadda ba ta ji alamun fitowarsa daga banɗakin ba, sai ji ta yi ya zagaya hannayensa a cikinta. Duk da ɗakin ƙato ne sosai da sosai amma duk ƙanƙantar motsi tana iya jinsa, amma sam ba ta ji motsinsa ba. Tsigar jikinta ta hau tashi, ta ji jikinta ya fara tsuma, tana neman ta rasa nutsuwarta. Ya ɗan yi murmushi ya cika ta, ya nuna mata gadon da yake ɗakin, alamar ta hau ta kwanta. Amma ta yi mursisi ta ƙame a gurin. Ya kama hannunta zai ja ta, amma ta ƙwace hannunta ta ja ta tsaya. Sai ya rabu da ita, yaje ya haye gadon ya kwanta. Ta tsaya a gurin tana rarraba ido, sai da ta ga ya jima da hawa gadon, ta lallaɓa ta ɗauki fulo ta ajiye a ƙasa ta kwanta. Kwanciyarta ke da wuya, ta fara jin sukuwar wasu halittu da ba ta san ko na mene ne ba, a cikin ɗakin. Hayaniyar halittum ya ci gaba da yin amsa kuwwa a cikin kunnuwanta tamkar a filin yaƙi. Wani mutum ta gani ya shigo ta wata ƙofa, ba a iya tantance jinsinsa, ya rufe ko ina na jikinsa, yana shigowa ya nufi gadon da Sayyid yake kwance, ya ajiye wannan takardar, ya nufi wata ƙofa. Da azama Nana ta bi bayansa duk da yadda yake wani irin gudu kamar iska na kaɗa shi. Sai dai wannan sautin ƙarar ya hana ta ci gaba da bin sa. Rungume ta ya yi a jikinsa, jikinta na ta rawa, duk ta toshe kunnenta da hannayenta biyu. Saboda yadda take jin hayaniyar kamar zata tarwatsa mata kai. Ta ɗaga kai ta kalli Sayyid, ta kalli ƙofar ta ce "Akwai wani abu a nan?" Ya ɗan yi shiru, sai kuma ya yi gaba, ya buɗe ƙofar. Ya riƙo hannunta suka ratsa hanyar da take baƙiƙirin mai ɗauke da duhu, kai ba ka ce a cikin wannan katafaren ɗakin mai ɗauke da hasken fitilu hanyar take ba. Babu tsammanni ta ga sun ɓullo wani guri kamar corridor. Shimfaɗaɗɗen yashin sahara ne a gurin, gurin ya bayar da wani ni'imtaccen sanyi, ga tsilla-tsillar bishiyu da suke a bushe a gurin hasken farin wata ya haske saharar. Ta waiwaya ɗaya gefen, ta hango wani irin gini, mai kama da tsaunin dutse, hasken wuta na ci na tashi ta wata kafa mai kama da taga a jikin ginin Dutsen. Bakinta na rawa ta kalle shi ta ce "Sayyid na san gurin nan, tun kafin na sanka nake mafarkin saharar nan, har na zo na sanka, ina mafarkinka a cikin saharar nan. Kuma a nan nake yawan ganin ka tare da Giyaz. A waccan bishiyar ku ke zama da su Habu ku sha shayi da wasu mutane ma da ban san su ba. Ina ne nan, kuma meyasa abubuwan da nake gani a bacci suke dawo mini a zahiri, haryanzu ina da ayoyin tambaya da dama a kanka"
"Yanzu kin yarda da nake gaya miki ruhinmu a haɗe yake? Ɗaya ba zai iya rayuwa babu ɗaya ba"
"Ba wannan nake son ji ba, haryanzu akwai wasu abubuwa ɓoyayyu da ban gama fahimta game da kai ba"
"Komai zai warware a hankali, za ki fuskanci komai rayuwata, amma ba na nufin cutar da ke ta kowace fuska, amma sannu a hankali za ki fahimci abin da ki ke kokwanto a kai."
Ta buɗe idanunta tana ƙarasa jin sautin muryarsa a cikin kunnuwanta. A kan gadon ta gansu tare, fuskarsa na kallon ta ta, yana ta yi mata numfashi a fuska a hankali, wanda hakan ya ƙara dagula mata lissafi dan kuwa ita ta san a zahiri abin ya faru, amma ya rikiɗe ya juye ya koma kamar mafarki. Ga shi yanzu Ƙaisar ba cikakkiyar lafiya ce da shi ba, balle ta ce ko shi ne yake wujijjigata, hakan ya ƙara hargitsa mata tunaninta. Ta tsura masa ido, kamar a fuskarsa za ta gano gaskiyar abin da take fata.
"Meyafaru?" Sautin muryarsa ya doki dodon kunnuwanta. Ba ta ce masa komai ba, ta zame jikinta ta juya masa baya, tana ta tufka da warwara a zuciyarta. Sake matsawa ya yi kusa da ita, sai dai wannan karon bai yi magana ba, sai dai jin manufarsa, ya sanya ta zabura da sauri tana ƙanƙame jikinta.
AREWABOOKS
Ƙanƙance idanun ya yi, kasancewar fitilar ɗakin a kunne take, ya din ga bin Nana da kallo, yadda ta tsuke fuska ta sanya hannayenta tana kare jikinta.
"Nana" Ya kira sunanta kamar yadda ake kiranta. Sai ta ji wani iri gaba ɗaya babu daɗi, ta kalle shi a tsorace.
"Me yasa?" Ya furta a hankali. Ba ta ce komai ba ta sunkuyar da kanta, tana ƙoƙarin matsawa kaɗan.
"Matata ce fa ke? Da gaske kin daina so na ko?"
Ta ce "Ko ina sonka, ba zai yi mini wani amfani ba. Kuma a da ne nake da cikakken 'yanci a matsayin matarka, a Duniyar da nikaɗai ka ke kallo. Wannan duniyar kuma ka yi mini nisa, a yanzu ma na san da na gama amfani za a sallame ni, sake yadda da kai shi ne ganganci mafi muni da zan sake aikatawa"