Kenza eBookz

Buzu book 3 complete - Chapter 4

Buzu book 3 complete - Chapter 4

Buzu book 3 complete Chapter 4: Buzu book 3 complete Chapter 4. "Ki nutsu ki kwantar da hankalinki, haryanzu ban tabattar ba tukuna, ina ga faɗa kawai ya…

3,358 words

"Ki nutsu ki kwantar da hankalinki, haryanzu ban tabattar ba tukuna, ina ga faɗa kawai ya yi dan ya huce takaicinsa, kuma saboda tsagwaron munafunci aka sallami kowa daga zaman, ba a bari na ji ƙarshen zancen ba, amma zan bincika na tabattar da gaskiyar maganar?" Ba ta iya tantance sauran abin da yake faɗa ba, ta kashe wayar jikinta yana rawa, ta hau kiran lambar Hammad, sai dai shiru wayarsa ba ta shiga, ta kira ya kusa sau hamsin, amma shiru ba ta shiga. Ta yi jifa da wayar tana huci. "Wallahi Hammad, zancen nan ko ba gaskiya ba ne ba, sai ka fuskanci mummunan tashin hankali da abin da ba ka taɓa zato ba. Wallahi ta tabatta ka haihu da wata mace, sai an mutu har Liman." Ta zauna Jikinta yana wata irin tsuma ta tashin hankali. Sultan kansa ya kasa zaune ya kasa tsaye, dan babu yadda ba su yi da shi ya yi magana ba, bayan tafiyar Nana ba amma ya ƙi.

Hankalin Sultan ya yi mummunan tashi, Abduou matawalle ne ya din ga rarrashin sa yana kwantar masa da hankalin a kan su bi komai a hankali, har su samu Hammad ya yi musu bayani dalla-dalla.

Sultan ya ce "Matawalle, a tsorace nake, Tafawa ya yi nasara, ya yi nasarar tabattar wa da Duniya cewar Hammad mahaukaci ne, idan ba haka ba ta yaya zai zo ya ce yana da ɗa, ɗan ma ba da buzuwa ba, 'yar wata ƙasar bayan ya san me hakan yake nufi. Tafawa ya ce "Kar ka yi mamaki, yanzu dole mu jira ya yi magana, mu ɗan ba shi lokaci ya nutsu, dan mu tabattar jikin ne, ko kuma da gaske yake. Kar ka manta tsawon lokacin da ya shafe ba tare da mu ba, bamu san me da me ya faru ba, kuma kar ka manta a Nigeria a ka gano mana shi"

Sultan ya goge gumin da yake tsatstsafo masa ya ce "Matawalle, akwai gagarumar matsala, babu buƙatar mu ba shi wani lokaci na daban, dole ya warware mana zare da abawa mu ji yadda aka haihu a ragaya. Kira mini wayarsa, duk inda yake a nemo shi, kuma a kira mini yarinyar ma"

Matawalle ya ce "Haka ne, kuma a nemo wannan munufukin yaron Mahmoudu, domin tabbas ya san komai, ya san duk abin da ya faru"

"Wai ni ita yarinyar ma, ni kamar na taɓa ganinta, a ina aka samo ta ne?"

Matawalle ya ce "Eh, lokacin da Hammad ya dawo, tana cikin waɗanda suka yi girki, wai Gimbiya Asal ce ta kawo ta"

"Asal kuma?" Sultan ya yi maganar yana nazari.

Sai dai duk tarin kiran wayar da aka yi wa Imam Hammad, ko sau ɗaya wayar ba ta shiga ba. Hakan ya ƙara jefa su a tashin hankali.

A hankali Nana ta yi miƙa, dan tamkar ta ci wani abu, haka ta yi wani irin nannauyan bacci. Cikinta ne yake wata irin ƙara, saboda azabar yunwar da take ji. Ta yinƙura da ƙyar, za ta tashi zaune, ta yi tozali da kyakykywar fuskarsa, yana kallonta. Ja da baya ta yi tamkar ta yi tozali da wanda ba muharraminta ba. Ta kalli jikinta babu hijjabi, rigar jikinta ma an canza mata wata.

"Kin tashi?"

"Ina ɗa na yake? Kuma waye ya ce ka taɓa ni ka canza mini riga, waye ya baka wannan damar?"

"Sadakina" ya ba ta amsa kai tsaye. Ita tsantsar mamakin halayyarsa take yi ma a yanzu, gaba ɗaya ya canza mata.

"Na haɗa ka da girman Allah, ka bani ɗa na, ka bani ɗa na, ni ban sanka ba, ɗana kuma ba ɗan ka ba ne, dan Allah ka bani yarona na tafi, dan Allah ka taimaka mini, na karɓi yarona na koma ƙasata" Ta yi maganar hawaye na bin fuskarta.

Ya wani lumshe ido yana murmushi ya ce "To ni kuma ina za ki kai ni idan ki ka tafi?"

"Ni ban sanka ba"

"Haba?" Yayi maganar yana ƙanƙance idanunsa. Wani marurun takaici ne ya ƙule Nana.

"Ki tsaya ki saurare ni, na yi miki bayani"

"Ni ba zan ji wani bayaninka ba, duk abin da zai fito daga bakinka, ba zan taɓa yarda da shi ba. Ka bani ɗa na na tafi"

Sayyid ya yi ajiyar zuciya ya ce "To ki bari ki haifa mini abin da yake cikinki, ki bani abina, sai mu san abin yi"

Daina ganewa Nana ta yi na wani ɗan lokaci, ta yi shiru ta tuna ya ce mata tana ɗauke da juna biyu ma ɗazu. Ta kalli cikinta, ta ɗago ta kalle shi, ya ɗage mata girarsa ɗaya.

Ayshercool 08081012143 80 Gaba ɗaya kanta ya kulle, ta zuba masa idanunta da suka yi jawur.

A mugun kasanlance ta ce "Ciki kuma?"

Ya jinjina mata kai, ta rasa abin da za ta yi gaba ɗaya. Ciki yaushe? Yaushe wani abu ya shiga tsakaninsu da har za ta ɗauki ciki? Ta tambayi kanta, sai dai ta kasa tambayarsa. Sai tsare shi da ta yi da idanunta.

Ya gyara zamansa sosai ya ce "Kina ji na?"

"Babu abin da zan ji? Kar ka gaya mini komai, ba zan ji ba kuma ba na fatan ji. Abin da ka yi mini haka ma ya isa, ka bar ni na ji da kaina". Ta yi maganar a matuƙar zafafe.

Ya ce "Shikenan na ji. Na rabu da ke. Amma ina so ki sani, muddin ba ki saki jikinki ba, ki din ga cin abinci ki rage wa kanki wannan damuwar ba, to fa ba zan ba ki Muhsin ba. Gwargwadon sakin jikinki, da cin abinci da zaki yi, shi zai sanya ki gan shi. Akasin haka kuma zan ci gaba da tsare ki a nan, na kai wa Asal shi ta riƙe shi, tun da dama ita Allah bai ba ta haihuwa ba. Wannan ma idan ki ka haifa ki bani abina tun da ba za ki saurare ni ba" Kallon ba ka da hankali ta yi masa. Ya yinƙura da kyar, jikinsa babu ƙwari, ya ɗauki hiraminsa ya rufe kansa ya fice ya bar ɗakin. A ɗaya falon ya tarar da Mahmoudu, cikin zaƙuwa ya ce masa "Yaya ta saurare ka kuwa?"

Jiki a sanyaye ya girgiza kai tare da zama ya ce "Fafur ta ƙi saurar ta, duk wani rarrashi da ban baki da zan yi, taƙi saurarta kawai na ba ta ɗan ta na sake ta ta nanata mini, na rasa yadda zan yi ko na minti ɗaya ta saurare ni. Babban abin da yake ɗaga mini hankali gani nake kamar da gaske Husna ta daina so na"

Mahmoudu ya girgiza kai ya ce "Ka yi haƙuri, ɓacin rai ne kawai ya sanya ta faɗar haka, amma a irin so da sadaukarwar da ta yi maka ba zai yiwu a ce ta daina sonka ba" Ya tashi zaune sosai yana kallon Mahmoudu ya ce "Kana ganin idan ta huce, za ta ci gaba da so na kuwa?"

"Sosai ma, yanzun ma ɓacin rai ne kawai. Amma za ta ci gaba da sonka da zarar ta huce"

Ya koma ya kashingiɗa yana kaɗa ƙafafuwansa.

Mahmoudu ya numfasa ya ce "Yanzu Imam mene ne abin yi, na san fa yanzu ana can ana nemanmu, ta ina zaka fara Fuskantar wannan balahirar? Ta ina za a fahimce mu, akwai gagarumar matsala fa"

Ya ɗan kwaɓe baki ya ce "Wannan balahairar ba ta kai fushin da Asmy take yi da ni ba. Ni duk yadda za su yi da ni sai dai su yi. Ko su bar ni a raye ko ma su yanka ni, burina da fatana na ga ta haƙura ta yafe mini ta saurare ni."

"Yanzu soyayyarka gaba take da gagarumin tashin hankalin da yake gabanmu?"

"Nesa ba kusa ba kuwa, idan aka kamanata shi da zunzurutun soyayya mara algus ɗin da na samu. Ko ka manta abu ne da nake nema ido rufe"

Mahmoudu ya ce "Turƙashi, to yaya za ka yi da Gimbiya Asal?"

Kawai ya saki murmushi, ya shafa sajensa.

"Au dariya ma na baka?"

"Eh mana, ni fa duk wannan masu sauƙi ne, ban ɗauke su matsaloli ba, zan gaya wa kowa gaskiya ko me za a yi mini sai dai a yi mini, ni fatana Asma'u ta yafe mini" Ya ƙarasa maganar cikin damuwa.

"Ka kwantar da hankalinka, in sha Allah za ta saurare ka, ta ɗauki zafi ne, amma tana hucewa za ta saurare ka"

*****

Doctor Sharif ne yake kallon matarsa cikin tausayawa, cikinta ya tsufa, amma sai fama take da rashin lafiya, duk da haihuwa ta biyar za ta yi. A dole ya ba ta gado a Asibitin, cikin wata bakwai da sati ɗaya, amma tana ta zubar da ruwa, ga matsalar numfashi da suga da yake hawa yana sauka. Ta kalle shi cikin damuwa ta ce "Gida zaka tafi ka bar ni?"

Ya ce "Eh mana, ba ga Yaya za ta kwana tare da ke ba? Kin ga yara su na gida, ga shi gobe in Allah ya kaimu akwai makaranta, dole na koma gida. Da na kai su school zan taho nan, duk wani abu da za a yi miki, na yi shi a rubuce duk za a yi miki" Ta numfasa ta jinjina kai ta ce "To shikenan, sai da safe" "Yauwwa Madam, ki samu isasshen bacci dan Allah"

"Idan na kwanta ne, baccin ko na fara sai na ji numfashina yana yi mini sama, kwanciyar babu daɗi sam"

"Na sani, ki yi haƙuri sai ki kwanta a side ɗin hannunki na hagu ko na dama"

Ta ce "To, sai da safe" Suka yi sallama ya tafi cike da tausayinta, wannan cikin tun yana ƙarami ya zo da tangarɗa yake wahalar da ita, ga shi ya tsufa ma amma ba ta daina wahala ba.

Hankalin Alhaji Zailani ya yi mummunan tashi, ganin sauƙi sosai da sosai a tattare da Alhaji Fatuhu. Ga 'yan kasuwa sun yi masa caaa a ka, a kan lallai ba sa son shugabancinsa, sai dai ya sauka a canza wani. Ya tattara nutsuwarsa ya yi burusu da su, domin ba ya son ya rarraba hankalinsa, wani abin ya ƙwace masa.

****

Nana kuwa ji ta yi da gaske yunwa na ƙoƙarin hana ta sukuni. Tashi ta yi ta fito, ta fara dube-dube. Yana daga inda yake tsaye yana kallon ta. "Me ki ke nema ne?"

Firgita ta yi ta juyo tana kallon inda yake, ganin yadda yake ƙare mata kallo ne, ya sanya ta haɗe rai. "Ina fatan ba wani gurin ki ke shirin tafiya ba, babu hanyar da za ki bi ki je ko ina"

"Ni ba guduwa zan yi ba, idan na ci Abincin yau za ka bari na gan shi?"

Ya yi murmushi ya ce "Ki ci ɗin tukuna, Bismillah biyo ni" Jiki a sanyaye ta bi bayansa, cikin matsanancin tsoro, dan ganin shi take yi kamar wani mutum na daban.

Haɗaɗen bedroom ya kai ta, ta tsaya saroro tana kallon ɗakin, ta ɗaga kai ta kalli agogon ɗakin, ƙarfe ɗaya da rabi na dare.

"Zauna ki jira ni a nan" Ta tsaya tana kallon sa.

"Ki zauna mana" Ya yi maganar yana nuna mata bakin gado. Ta yi ƙyam tana kallonsa. Bai sake ce mata komai ba, ya fita ta tsaya tana zazzare ido, tana ƙara ƙarewa ɗakin kallo. Ta gaji da tsayuwa, ta samu guri ta jingina da jikin bango, sanyin AC da yake ɗakin ya fara damunta. Falon ta koma, tana nan zaune sai ga shi ya shigo da leda a hannunsa.

"Me yasa ki ka fito?"

"Sanyi nake ji" Ta ba shi amsa a taƙaice.

"Ohh yi haƙuri, mu je sai na kashe miki A.C" Ta girgiza masa kai tana sake haɗe rai.

"Shikenan, zauna ga abincin na samo" Ya yi maganar yana riga ta zaman.

Ta zuba wa ledar ido, bayan da ya fito da gasassun zabi guda biyu, babu abin da ya faɗo ranta, sai zaman su a gidan Hajiya Halima, lokacin da ya saka Habu ya kawo mata zabbi gasassu.

Ya kalle ta ya ce "Ko na dafo miki shayi?"

Ta girgiza kai ta tashi tsaye. "ina za ki je?"

"Ɗakin da nake zan koma,a can zan ci" Ta ba shi amsa ciki-ciki.

"To mu je can ɗin, nima ban ci komai ba, wataƙila idan muka ci tare, zan iya sakin jiki na ci Abincin"

Nana ta ƙara haɗe rai ta ce "Ni fa ba zan ci wani abinci tare da kai ba, bana buƙatar duk wani abu da zai ƙara kusanta ni da kai. Ni a yanzu neman maraba nake yi da kai".

"Neman maraba ki ke yi da ni?" Ya yi maganar yana murmushi mai ciwo, daga bisani ya ce "Shikenan, ɗauki abincin ki je ki ci, sai ki kwanta ki huta" Ya tashi ya bar mata falon. Ta tattare kan kayan abincin, ta tafi ɗakin da aka ajiye ta. Sosai ta fara ƙoƙarin cin abincin, saboda azabar yunwar da take ji, sai kuma ta tuna da gaske idan ba ta yi girki ba, ba ya cin abincin. Kenan tun da ta tafi bai ci cikakken abinci ba kenan ko yaya? Wata zuciyar ta tambaye ta. Har za ta yinƙura ta tashi, sai ta tuno batun cikin da ya ce tana da shi. A take wani malolon takaici ya ƙule ta, ta ƙuduri aniyar sai ta yi dalilin zubewar cikin nan. To tayaya ma za a yi a ce ina da ciki? Yaushe kuma ta yaya?" Ta tambayi kanta. Gaba ɗaya ta ji kanta yana juya mata, dan haka ta haƙura da tunanin, ta je ta wanke hannunta ta ta rufe abin da ta rage ta kwanta.

Sai dai ta ƙi yadda ta yi bacci, saboda gudun kar ya biyo dare ya zo ya yi yinƙurin yi mata wani abin.

Sai dai ko mintuna goma ba a yi ba, ta tsinci kanta a cikin Libraryn Ƙaisar.

Ta gan shi a kwance a kan wani gado, ya lulluɓa da wani baƙin mayafi.

Ya kalli fuskarta da ke ɗauke da damuwa ya ce "Ya dai?"

Ta Numfasa ta ce "Ya na gan ka a kwance a nan?"

"Eh to zan yi ta zama ba zan kwanta ba ne?"

Ta ce "A'a, amma galibi sai ba ka da lafiya ka ke kwanciya a nan gurin"

"Lafiyata ƙalau. Na ɗauka zan gan ki cikin murna da farin ciki, tun da mijinki ya dawo hayyacinsa ya gane ki, sai kuma na gan ki cikin damuwa?" Ta nemi guri ta zaune a gefen Ƙaisar ta ce "Ni fa ba na ƙaunar mutumin nan, fatana kawai ya bani ɗa na, na koma Nigeria Ubangiji Allah ya sanya su Baba su yafe mini, ina kyautata zaton alhakinsu ne ya kama ni"

Ƙaisar ya ce "Waye ba kya ƙaunar yanzu?"

"Sayyid"

"Ƙarya ki ke yi" ta ce "Ƙarya kuma?"

"Da dai ban san halinki ba ne"

Cikin sanyin jiki ta ce "Da gaske nake, ba wasa nake yi maka ba. Ba na ko ƙaunar jin sunansa, ya yaudare ni, sun cutar da ni. Gaba ɗaya kimarsa da son da nake yi masa sun zube a idanuna"

Ƙaisar ya yinƙura ya tashi zaune, yana ƙara rufe jikinsa ya ce "Tun da ya ce ki saurare shi, ki tsaya ki ji mai zai ce miki mana. Kar zuciyar da ki ka yi ta sanya ki yanke hukuncin da ba zai ɓulle muku ba"

"Ni fa babu abin da zan ji daga bakinsa, ba na buƙatar sa a rayuwata gaba ɗaya" Ƙaisar ya yi murmushi yana gyara zamansa a hankali. Idon Nana ya sauka a kan Jakar Sarkin baka da ke gefen gadon da yake. "Ƙaisar, me ka ke yi da jakar Sarkin baka?" Ya yi mata shiru kamar bai ji ta ba. Miƙewa ta yi da sauri ta ce "Wani abu ya faru tsakaninka da Giyaz ko?"

"A'a aron jakar na yi, wani aiki na yi da ita".

Nana ta saka hannu ta ɗan ja mayafin da ya rufe jikinsa da shi, wani irin haske ne ya haske mata ido, daga bisani hasken ya ragu a hankali. Jikinsa ya yi wani irin kore-kore, wani gurin kuma ya yi baƙi ƙirin tamkar an ƙona shi. Nana ta ce "Meyafaru? Me ya same ka haka? Giyaz ya yi maka wani abu ne?"

"Babu abin da ya faru, zan dawo miki da jakar ki kuma, ki je sai na sake neman ki" Nana ta farka daga baccin da take yi, fuskarta duk hawaye. Gaba ɗaya jikinta a sanyaye ta tashi ta yi alwala, ta yi nafilfili, sannan ta gabatar da sallar asuba. Har gari ya yi haske, tana zaune a ƙasa. Shiru ta yi tana tuna yadda ta ga jikin Ƙaisar, sai ta ji abin ya dame ta sosai da sosai.

"Mene ne makomar wannan sakankancewar da nake yi da Ƙaisar yanzu? Me yasa kuma yake taimakona a wasu guraren? Anya ba wani tarkon na yaudara ya yi mini ba, yake son na afka ya yi amfani da damar ba? Ko ma dai yaya ne, Ubangiji Allah ka tsare ni daga sharrin duk wani abin ƙi." Sosai take son mantawa da tunanin Ƙaisar, ta koma tunanin Muhsin, da wannan balahirar ta gabanta, amma abu ya ci tura, a jikinta take jin Ƙaisar, take jin ta damu da halin da ta gan shi a ciki.

Sallamarsa ce ta katse mata tunani, ta amsa masa ciki-ciki. Ya je gabanta ya ajiye tray. Ya ɗan tsura mata ido ya ce "Barka da safiya Rayuwata" Wani mugun kallo ta yi masa, haɗi da uwar harara.

Ya yi murmushi ya ce "Ga abin karyawa nan, kar ki manta sakin jikinki, da cin abincinki ne zai sanya ki ga ɗana"

"Ka daina danganta mini ɗana da kanka, ba shi wata alaƙa da kai" Ta yi maganar cikin tsiwa.

"Ba shi da alaƙa da ni, sai da Ƙaisar?" Ya yi maganar ya kallonta yana murmushi. Bai ba ta damar ba shi amsa ba ya ce "Yau zan koma gida, zan je na ji yadda za mu yi da su Sultan, amma ki nutsu ki kwantar da hankalinki dan Allah"

"Ba ni da wata nutsuwa ko kwanciyar hankali, idan ba ɗa na na gani ya zo hannuna ba". Ya yi shiru yana tsare ta da idanunsa. Ta ɗaga kai ta kalle shi, ta ji gabanta ya faɗi, ta rasa gane wane irin kallo ne yake yi mata haka. Ta sunkuyar da kanta tana haɗe rai. Ta sake ɗaga ido ta suka haɗa ido, ya yi mata murmushi, ya ce "Ma vie, ban san daga ina nake jin ƙaunarki ba a rayuwata, kar ki hukunta ni da abin da ki ka gani kawai a zahiri. Ina sake roƙonki, ki bani dama ki ji ta bakina"

"Ni babu abin da zan ji, na ce maka ɗana kawai nake buƙata"

Ya shafi sajensa ya ce "Muhsin ai nawa ne ni da Asal. Idan ki ka haihu kuma nawa ni da ke, shi ma idan ba kya so sai ki bani abina"

Wata irin ɗagowa ta yi, cike da takaici, ya shammace ta ya rungume ta ya haɗe bakinsu. Nana ta tattara nutsuwarta, da duk wata jarumta dan ganin ba ta biye wa Sayyid. Ta din ga ture shi iya ƙarfinta tana kai masa duka, amma tamkar dutse ba jikin ɗan Adam take duka ba. Sai da ta gaji ta ƙyale shi. A hankali ya zare bakinsa daga nata ya ɗago fuskarta yana kallonta.

Hawaye sharkaf a kan fuskarta, ya ce "Kar ki wahal da rayukanmu, ni da ke abu guda ne Asmy, ko kin tafi kin bar ni, ba za ki taɓa samun nutuswa da kwanciyar hankali ba. Kamar yadda tun da muka rabu nawa ruhin ma bai samu nutsuwa ba. Ina ƙaunarki rayuwata" Duk yadda Nana ta so yi masa rashin kunya, ta gaggaya masa maganganu masu zafin gaske, amma ta kasa tamkar ya saka wani abu a cikin idanunsa da ya yi tasirin da ya hana ta maganar. "Ki yi mana addu'a rayuwata, akwai kaya a ɗakin da muka je jiya, idan kin yi wanka akwai kayan sakawa. Sai akwai kitchen shi ma, duk za ki iya shiga ki dafa mana duk abin da ki ke so. Sai na dawo" Ko tari Nana ba ta kuma yi ba, har ya tashi ya bar ɗakin, ta bi bayansa da harara.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull