Kenza eBookz

Buzu book 3 complete - Chapter 40

Buzu book 3 complete - Chapter 40

Buzu book 3 complete Chapter 40: Buzu book 3 complete Chapter 40. Ko da aka nemi Asal ta tofa wani abu a gurin taron, Nana ba ta zaci za ta yi magana ba,…

1,090 words

Ko da aka nemi Asal ta tofa wani abu a gurin taron, Nana ba ta zaci za ta yi magana ba, amma ta karɓa ta taya ta murna, tare da shaidawa duniya, a kanta Nana ta fara gwajin maganin haihuwa kuma Allah ya amsa. Nene ta taimakawa Nana sosai a ɓangaren magungunan, haka Sarkin baka ya halarci taron, Hammad ne da kansa ya gayyace shi. Ya din ga yi wa Nana dariyar ba a guje wa ƙaddara. Nana ta yi murmushi ta ce "Na karɓe ta ta hanyar da ta dace ne" Nana ta yi shiru tana kallon gurin nata. A hankali ta furta "Na cika maka alƙawarinka uban ɗakina" "Nima na cika wanda na yi miki uwar gijiyata, na rubuta tarihinki da alƙalamin zinare a cikin kundi na mussaman da ba zai ɓace ba" Ta ji tamkar muryar Ƙaisar a gurin. Idonta ya sauka a kan award da ta yi da sunansa ta ajiye a gefe guda.

Shukura wannan rashin lafiya da ta yi ta fama, da damuwar da take ciki ne yayi ajalinta, Yusra ta shiga damuwa da tashin hankali sosai, sai dai ta rungumi yaran Shukura da waɗanda ta haifa. Jamila ta samu wani jami'in ɗan sanda mai mata biyu ta aura, Allah ya taimake ta, ya ware mata gidanta sai dai tana shan azabar kishiyoyin duk da haka. Ta rungumi sana'arta sosai da sosai. Suwaiba kam ƙwaƙwalwa ta riga ta taɓu haka Mama ta ci gaba da wahala da ita.

Allah Al-musawwiru, shekarar Husna ɗaya a duniya, ta sake samun juna biyu, a dole Nana ta ɗauke ta, ta yaye ta. Ta haifi yara biyu mace da namiji. Nana kuma sai a haihuwa ta ƙarshe, ta haifi 'ya mace, duk da ba wani shiri suke yi ba, amma kan yaransu a haɗe yake sosai da sosai. Nana tsaye take a kan tarbiyya da kuma ilimin yaran mussaman na addini.

Hatta garin Buda sai da suka amfana da Nana, dan ta sai filin da kukar Lanti take, filin da kukar da aka yi wa Lanti girka, aka buɗe islamiyya. Sannan duk shekara suna samun abin alkhairi na kayan masarufi mussaman da azumi.

Ummanta duk ta aurar da ƙannenta mata, Imrana bayan ya kammala karatunsa, ya yi zamansa a faransa, sai da Nana ta matsa masa da batun aure, sannan ya ce ta samo masa duk wadda ta yi mata zai aura.

Suka rayu cikin kwanciyar hankali, da son juna. Ta samu kulawa da tsantsar soyayya daga miji, yaransu gaba ɗaya suna matuƙar sonta da ƙaunarta. Husna kuwa tamkar babbar 'yar Nana. Yayin da Yarima yake ɗan gurin Asal. Ta shiga cikin mata da aka sanya sunansu a kundin tarihin Agadez. Ta rayu cikin aminci da nutsuwa, a rayuwar da sai ta so ta yanke tsammani saboda gwagwarmaya. Sai ɗan sauran ƙalubale da faɗi tashin rayuwa da ba a rasa bawa da shi.

A hankali ya yi ajiyar zuciya, ya kalli matashin da yake zaune yana saurarensa, ya ce "Ka ji labarin Gimbiya Asma'u, to kai ma shigen abin da ya faru da su ne yake shirin faruwa da kai"

Ɗaya matashin ya ce "Allah ya yi mini tsari, idan kuma ni ban taki irin wannan sa'ar da Nana ta taka ba fa? Lallaɓawa zan yi na bi dare na gudu na bar garin nan, sai ta koma bin wani. Haka kurum mahaukaciya ta liƙe mini ta din ga bi na"

Ɗayan ya kwashe da dariya, ya ce "Dan Allah kar ka yi haka. Yau wuni ta yi a ƙofar gidan ku, an bata abinci ta ƙi ci, Yaya kawai take faɗa, dan Allah ka je ka bata Abinci kamar ma ba ta da lafiya"

"Kai wallahi ba zan koma ba hauka ake yi, idan ta gaji ta ƙara gaba ta nemi wands za ta bi"

*Tofa, ko su kuma wannan matasan suwaye? Waye wannan aka ba wa labarin BUZU da Nana, shi kuma wace mahaukaciyar ce take bin sa. Sai mu tara a gaba a cikin jerin littattafan da za su zo muku daga alƙalamina nan kusa ko a gaba*

(Waɗanda suka gaza juriya, a farkon littafin da ganin na matsa rayuwar Nana a farko, ina fatan a ƙarshe kun fahimci abin da nake son ku fahimta. Ba kowace Addu'a Allah yake karɓa a take ba, ya kan jinkirtawa bawa, ya amsa masa lokacin da ya fi dacewa. Annabawan Allah misali ne a kanmu. Har kullum ina fatan zamu din ga kamanta wasu darussan da muke karantawa a littafi, da rayuwarmu ta zahiri, hakan ne zai sanya a ɗauki gyararrakin da yakamata.)

TAMMAT BI HAMDILLAH. KOMAI NISAN DARE GARI ZAI WAYE. ALLAH YA KAWO MU ƘARSHEN WANNAN LITTAFIN LAFIYA. DUKKAN YABO DA GODIYA DA JINJINA DA KIRARI SU TABATTA GA BUWAYIN SARKI GAGARA MISALI DA YA BANI ARON RAI DA LAFIYA, NA KAWO WANNAN LITTAFIN BAYAN SHAFE TSAWON SHEKARU BIYU INA BINCIKE A KANSA. INA ROƘON ALLAH ABIN DA NA YI NA KUSKURE YA YAFE MINI. GODIYA TA MUSAMMAN GA TEAM ƊIN BRIGHT PENS Aisha Adam Ayshercool Zainab shehu kumurya Na'ima Suleiman Nazeefa sabo Nashe.

Ƙungiyar YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA.

Godiya ta mussaman taki kekaɗai Amanar Cool

Sai kuma gaisuwa ta mussaman da godiya, bisa taimakawa bincikena da ku ka yi. Maryam Muhammad Mum amnash Dr. Salihu Nura Adam (Salihan nur) Fatima A abdou Nijar Da ma kafatanin marubuta baki ɗaya. Hakazalika ina godiya, ga masu gyara, sharhi da shawara Ubangiji Allah ya saka muku da alkhairi ya fi ni yabawa.

Na gode sosai da sosai, da jimirin bibiyata, ina roƙon Allah duk wanda ya karanta littafin nan, ko ya ƙaru da wani abu, ko bai ƙaru ba Ubangiji Allah ya tabattar da zukatanmu ni da ku a kan Imani.

Ina miƙa godiya sosai da sosai, ga waɗanda suka kasance tare da ni a tafiyar nan, tun daga telegram har AREWABOOKS. Waɗanda na yi wa kuskure, ina mai baku haƙuri, saboda ɗan Adam ce ni, mai ajizanci.

Wanda ku ka sarrafa mini littafi, ta wasu hanyoyi ba da izinina ba, ba a yafiya ranar lahira.

Wanda kuka karanta mini baku saya ba, ga account number na zan saka, ku bani hakkin wahalata na wata shida, akasin haka ina muku tuni da duk mai son ci gaba a nasa neman, baya yi wa wani mugunta. Kuma hakkin wani komai ƙanƙantarsa na iya kawo maka naƙasu a naka neman. A saka mini hakkina dan Allah, ko na bar mutum da Ubangijin Musa da Harun, ubangina ubangijinku. 0069685771 Aisha Adam stanbic bank.

Sai mun haɗu a littafi na gaba, idan Allah ya bamu aron rai da lafiya.

08081012143 💃💃💃💃

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull