Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 14
Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 14: Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 14. Cikin mamaki yake bin ta da kallo, yana tunanin me ya yi mata take wannan…
3,363 words
Cikin mamaki yake bin ta da kallo, yana tunanin me ya yi mata take wannan kururwar.
Ya taka ya ƙara matsawa kusa da ita, amma ta din ga ja da baya, tana maimaita "kar ka matso kusa da ni, ba na buƙatar ka, kar ka zo inda nake".
"Kalli ni mutum ne ba abin tsoro ba, babu abin da na yi miki, le regard kalli" ya yi maganar yana nuna mata hannunsa domin ta taɓa ta tabattar.
Cikin fita hayyaci Nana ta ce "Ka fita ba na son ganinka, ba za ka haukata ni a banza ba, ka fita ba na son ganin ka" ta yi maganar jikinta na tsuma da karkarwa. Cikin sauri ya nufi ƙofar fita yana waiwayen ta.
Yana fita ta silale ta faɗi a gurin.
Fitar sa ke da wuya, ruwan sama mai ƙarfin gaske ya sauka.
****
Dare ya tsala, Fadila na zaune bacci ya gagari idonta, ta kalli kusa da ita, mijinta Sagir yana ta baccinsa hankali a kwance, ita kuwa duk dare fargabar kwanciya bacci take yi, saboda miyagun mafarke-mafarken da take yi. Tun Sagir na damuwa har ya gaji ya rabu da ita. Ta yi niyyar yin alwala ta yi nafila ko raka'a biyu ce, amma kasala ta danne ta, ga wani irin tsoro da take ji. Dama ko normal sallar farilla a zaune take yin ta, saboda yadda cikin ya tsufa sosai da sosai ga shi da girma. Ga exams tana facing, ba ta iya karatun sam. Ta dafe goshinta tana wani irin gumi, duk da sanyin A.C da ya sanyaya ɗakin.
Tana jiyo surutan Haidar a cikin bacci, yana ta kiran sunan Nana.
Kawai ta zuba uban tagumi hannu bibbiyu ba tare da sanin abin yi ba.
****
Ko da Nana ta buɗe idanunta, da hasken fitilar ƙwan ɗakin, ta fara karo.
Ta juyo da kanta, da ya yi mata nauyi tamkar zai tarwatse, kawai ta hange shi a bakin ƙofar banɗaki, yana ta sanɗa yana cire kayan jikinsa a hankali, da suke ta ɗigar da ruwa, jikinsa yana ta wata irin karkarwa. Aka yi walƙiya ta hangi yadda ruwa yake zuba ta taga. A take ta tuna abin da ya faru, da azama ta tashi zaune, ta yinƙura ta tashi, ta nufe shi. Sai a lokacin ya farga da ta tashi. Sai da ya tsorata ya tsaya cak, yana tsoron kar ta sake rikicewa ta ce ba ta son ganinsa.
"Me yasa ka fita ruwa ya dake ka har haka? Subhanallah" ta yi maganar tana karɓar rigar hannunsa. Babban abin da ya tsorata ta, bai wuce yadda jikinsa yake karkarwa ba, haƙoransa suke haɗuwa da juna, su na bayar da wani irin sauti. Ta buɗe wardrobe ta ɗaukko zaninta, ta fara goge masa ruwan jikinsa. Cikin damuwa ta ce "Me yasa ka tsaya ruwa ya dake ka haka?" Kawai ya kalle ta.
Ta ajiye zanin, ta ɗaukko flask ɗin da ta zuba ruwan zafi, ta shiga banɗakin ta zuba a bokiti, ta haɗa masa ruwa mai zafi.
"Ka shiga ka yi wanka da shi, za ka rage jin sanyin" bai musa ba ya shiga banɗakin, ta ɗauko wando ta rataye masa a jikin ƙofar, ta rufe masa ƙofar.
Ta ɗaukko bargonta, ta ajiye a kan katifar, ta duba kayanta, ta samo man zafi ta ajiye. Ta tsaya tana jiransa. Ba a jima ba ya fito, sai dai jikinsa na ta ci gaba da tsuma, yana karkarwa.
Mamaki take yi, yadda dukan ruwa ya saka shi haka, ita ba ta san adadin dukan da ruwa ya yi mata ba, ko ciwon kai bai taɓa saka ta ba.
Ta ɗaukko riga, ta miƙa masa, amma ya ture ta, ya nufi gurin da yake kwanciya.
Ta riƙo hannunsa ta ce "Zauna a nan" ta nuna masa gefen katifar. Ya zauna a hankali yana rintse idanunsa.
Ta ɗauki man zafi tana shafa masa a jikinsa, sai dai jikinsa ya ɗauki zafi rauuu.
"In baka rigar ka saka?" Ya girgiza mata kai alamar a'a.
Ta gyara masa fulo ta ce "To kwanta" ya ja jikinsa a hankali ya kwanta, ta lulluɓe shi da bargo. Ayshacool Ta yi shiru cikin matsananciyar damuwa, ita kanta ba ta san ya aka yi yau ta gigice har haka ba. Ba ta san yadda aka yi ta rasa nutsuwar ta har hankalinta ya gushe ba, duk da abubuwa irin haka na faruwa da ita, wasu lokutan kuma ta na iya sarrafa kanta.
Ji ta yi yana wani irin nishi, jikinsa tamkar ana girgiza shi. Ta ɗaga bargon cikin damuwa, ta ga yana jijjiga.
Ta rikice ta fashe da kuka ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, tsoro ka ke bani ne, ba ina nufin ka fita ruwa ya dake ba ne ba."
Tana kuka ta ɗaukko ɗan kwalinta, ta jiƙo shi da ruwa, ta ci gaba shafa masa. Amma ta ga leɓensa har ya fashe saboda karkarwa. Ta kalli gari yadda ake ta lafta ruwa, balle ta ce a taimaka mata a kai shi asibiti.
Ya yi mata alama da hannunsa ta matsa kusa da shi, ta matsa sosai a hankali ya ce "Zafi, ana ƙona ni, ƙonewa nake yi"
Cikin kuka ta ce "A'a babu wanda yake ƙona ka, zazzaɓi ne ka yi haƙuri"
"A'a, ƙona ni ake yi, sanyi nake so"
Cikin rashin fahimta ta ce "Sanyi kuma?"
"Eh, saboda ƙonewa nake yi yanzu" yayi maganar haƙoransa na ƙara karo da juna.
Cikin damuwa ta ce "To mu koma bakin ƙofar ɗakin?"
Ya girgiza kai ya ce "Sanyin da ki ke ji nake so"
"Sanyin da nake ji kuma? Ai ba na jin sanyi"
"A'a ki na ji, ki taimaka mini dan Allah, sanyin da ki ke ji nake so"
"To ta yaya zan baka?"
"Jikinki za ki bani, shi nake buƙata ko zan daina jin zafin wutar nan" duk da jikinsa yana rawa, amma tana fahimtar abin da yake faɗa.
"To ai ni ban san ta yaya zan baka ba" Ta yi maganar a sanyaye dan ba ta san ya yake nufi ba.
"Kin yarda za ki bani?" Ya yi maganar yana buɗe idonsa da suka kaɗa su ka yi jawur ya kalle ta.
Ta jinjina masa kai alamar eh, cikin tsoro dan ba ta san ya yake nufi ba.
Ya buɗe mata cikin bargon, ya saka hannunsa ɗaya ya janyo ta, ya mayar da bargon ya rufe., ya mirgina ta gefensa ya saka hannayensa ya ƙanƙame ta.
"Wash Allah! Zafi zan ƙone" ta yi maganar a gigice, saboda wani irin zafi da yake fitowa daga jikinsa, yana ratsa fatarta, duk da akwai rigar bacci a jikinta.
Ta yinƙura za ta tashi, sai dai ta kasa, saboda ya danne ta, ta kowane ɓangare.
"Yi hakuri, ba za ki ƙone ba, za ki daina ji"
Nana ta fashe da kuka tana girgiza kanta, shi da zafin yake fitowa daga jikinsa ya yake ji kenan?.
A hankali yake shafa gashin kanta, zuwa bayanta, yana sauke numfashi a wahale. Cike da ƙarfin hali yake cewa "Yi haƙuri, na san ba zaki ƙone ba, nikaɗai nake ƙonewa" ya din ga hura mata iska a kunnenta. A hankali ta daina jin zafin, temperature jikinsa, ta fara komawa normal, ta ji ya daina wannan tsumar, numfashin ma da yake ta saukewa ya daina. Sai ta ɗan zabura a rikice ta ɗago, ta kai hannu hancinsa. Bai buɗe idonsa ba ya ce "Ban mutu ba, ina numfashi" ajiyar zuciya ta sauke tare da gode wa Allah ganin yana raye ya kuma dawo daidai.
"Sannu ka daina jin zafi?" Ya jinjina kai alamar eh.
"Dan Allah ka yi haƙuri ka yafe mini, tsorata ni ka ke yi ne, ba ina sane na yi maka ba"
"Ni ma ki na tsorata ni wasu lokutan"
Cikin mamaki ta ce "Ta yaya?"
"An gama ruwan ko?" Ya yi maganar yana basar da wadda ya yi.
"Eh an daina, amma dama ka na doguwar magana haka sosai?"
"Eh"
"Amma na yi ta magana ɗazu ka ƙyale ni" ta yi maganar da shagwaɓar da ita kanta ba ta san ta iya ta ba.
Dariya ta ji yana yi, ya ƙara riƙe ta gam.
"Yanzu wai da gaske ba ka iya tuna komai game da kan ka?"
Ya ɗan yi shiru sannan ya numfasa ya ce "Haka ne, ina iya tuna abubuwa na yau da kullum, wasu lokutan kuma ba na iya tuna komai ma. Tun da farka a cikin wannan duniyar da nake jin ta tamkar mafarki, nake iya ƙoƙarina na tuna waye ni, saboda na fuskanci babu wanda yake rayuwa shikaɗai kowa yana da ahali. Amma a duk lokacin da na yi ƙoƙarin hakan, na takura ƙwaƙwalwata, sai na ji wani duhu ya ƙara ninkuwa a cikin kaina, na ji kamar kan zai tarwatse. Kuma a ƙarshe sai na yi rashin lafiya, ko dai na ji wannan zafin tamkar ana babbaka mini wuta, ko kuma na sake manta wasu muhimman abubuwan. Amma yanzu ke ce ahalina"
"Kenan ba dalilin dukan ruwan nan ne ya saka jijjiga ba?"
"Ba zan iya ganewa ba, abubuwan suke saka ni hakan da yawa" Ayshacool 35
Nana ta motsa, ta ji taushin katifar da suke kai, ta fi ta ɗakinsu. Ga ƙamshin turaren da ya sauya, ya sanya Nana sakankancewa a kan a wannan karon ma, irin wancan mafarkin ne. Gaba ɗaya jikinta rawa yake yi, a wannan karon ma ta kasa sarrafa kanta da nutsuwar ta.
Sai dai a wannan karon al'amarin ya banbanta da na farko.
"Kai ka rabu da ni" Ta faɗa da ƙarfi, tana ƙoƙarin ture shi.
"A'a" ya faɗa ƙasa-ƙasa.
Tabbas ba mafarki ba ne ba, bayan Buzun mijin nata ya dangana da ita, wani bugire mai girman gaske, bugiren da ba ta taɓa kawo faruwar sa a tsakanin su ba. Ita a tunaninta tun da ba shi da cikakkiyar lafiyar ƙwaƙwalwa ba ya jin komai, hakan ne ya sanya take yawonta ma babu hijjabi a ɗakin, sai ta ga ya dame ta da kallo, ta rufe jikinta.
Cikin kuka ta ce "Dan Allah ka ƙyale ni"
"je suis désolé (ki yi haƙuri)" ya yi maganar muryarsa ƙasa-ƙasa.
Bayan wani lokaci da Nana ba ta iya tantance adadinsa ba, domin ta daɗe da daina gane komai.
"Ma femme. (Matata)" Ya yi maganar yana ɗan murza ya tsunta. Ta buɗe idonta da ya yi jawur, da ƙyar tana kallon sa.
A wannan karon fitilar ɗakin a kunne take. Sai dai fatarsa ta yi jawur.
Ta sunkuyar da kanta daga kallonsa.
Ya saka hannu ya share hawayen da ke fuskarta, sai dai kuma ya kasa magana.
Ya kai bakinsa ya sumbaci goshinta, ya kamo hannunta ma ya sumbata. Ta lumshe idanunta tana numfashi a hankali.
"Merci (Na gode)" shiru ta yi tana ƙara sunkuyar da kanta.
Ya saka hannunsa ya ɗago fuskarta, amma ta lumshe idanunta, ta ƙi buɗewa.
"Kalle ni mana"
Kwaɓe baki ta yi, ta ci gaba da kuka. Ya saki murmushi yana goge mata hawayen fuskarta ya ce "A yi haƙuri"
Ya ci gaba da wasa da yatsun hannunta, daga baya ya tashi a hankali yana kallonta, sai dai ya rasa abin gaba ɗaya.
Nana ta yinƙura da ƙyar, ta tashi zaune, ta ja bargon ta rufe jikinta.
Su na haɗa ido ta sunkuyar da kai ƙasa, fuskarta a haɗe, hawaye na biyo fuskarta.
"Yi haƙuri" ya yi maganar yana kallon ta.
Kawai ta sake fashewa da kuka, har da sheshsheƙa.
Shafa bayanta ya ci gaba da yi, cikin sigar rarrashi, amma ta maze ta din ga kuka.
Ya ce "Ki yi shiru"
Ba ta kula shi ba, ta janyo rigarta, ta saka ta yinƙura ta tashi da ƙyar, ta nufi gas ɗin ta.
Ta dafa ruwa ta shiga banɗaki, ta jima sannan ta fito, a ƙofar banɗakin ta tarar da shi a tsaye.
Sai da ta ɗan tsorata, ta na ƙoƙarin raɓa shi ta wuce, ya ce "Ni fa?" Ta kalle shi.
Ya ce "Zan yi wanka"
Ta ba shi hanyar shiga banɗakin, ya kalli hanyar ya ce "Ruwan sanyi? A a ina jin sanyi"
"Bari na dafa" ya koma gefe ya zauna, ta ɗora masa ruwan, ta kalli agogon ɗakin, huɗu da rabi, ta san idan ta kwanta yanzu ba bu lallai ta samu sallar asuba.
Ta shimfiɗa sallaya, ta ajiye wayarta a kai, ta ajiye hijjabinta.
Yana gefenta, sai bin ta yake yi da ido.
Ta kai ruwan banɗaki, ta na haɗa masa, sai a yanzu ta tuna lokacin da ya ce mata zai yi wanka, ashe ruwan sanyi ne ba ya so.
Ta kashe famfon kenan, ta yinƙura ya shigo banɗakin. Ta tashi tsaye tsam tana rarraba ido.
Ya mayar da ƙofar ya rufe, ta ɗago da sauri ta ce "Amm ga ruwan nan, idan zafin bai yi ba, sai ka kunna famfo ka ƙara sirkawa".
"Na kasa tuna yadda ake wankan, sai kin tuna mini"
"A'a wallahi nima ban iya ba" ta yi maganar idanunta a waje dan tsoro.
"Amma ke ki ka yi? Ko wankan kwanciya bacci ki ka yi?"
Gaba ɗaya mamaki ya cika Nana, mutumin da magana take yi masa wahala, shi ne ya ritsa ta da wannan maganganun kamar ana karanta masa.
"Dan Allah ka yi haƙuri, ni ban iya ba"
"Astagfirullah ba kyau ƙarya" ya yi maganar yana taɓa ruwan.
*
Doctor Sharif ne da wani likita a kan Shukura, su na gwada bp ɗin ta. Duk ta kumbura sosai da sosai.
Jininta ya hau sosai da sosai, ba zai yiwu a yi mata tiyata a wannan ƙadamin a cire jaririn ba, saboda hawan da jininta ya yi. Ga shi lokacin haihuwar ta bai yi ba.
Sakamakon da ya fito daga lab kuma, still ya nuna jininta ya yi ƙasa. Ayshacool Doctor Sharif ya fito cikin damuwa, ya dubi Hajiya Amina da Yusuf, da kuma mijinta Sagir ya ce "Wai me yake damun Shukura har haka. Normal teses ɗin suke tuk daga farkon cikin nata, amma lokaci ɗaya a ce jininta ya yi wannan mugun hawan ta kumbura har haka?"
Sagir ya ce "Wallahi doctor na rasa gane kan ta, tun bai fi kwana uku da dawowa ta ba, duk ta canza. Ba ta cin abinci, bacci ma ba ta iya yi. Kullum na farka cikin dare tana zaune, na yi, na yi na tambaye ta mene ne,ta ce mini ba komai, Mummy ai har ke na gaya wa ko za ki tambayeta abin da yake damun ta.
Hajiya Amina ta ce "Rigima ce kawai irin ta Shukura, duk ta ɗaga hankalinta, wai tana ji a jikinta wannan cikin mutuwa za ta yi. Ina ta rarrashinta ina ba ta haƙuri, amma ta addabi kanta kuma wallahi farkon cikin duk ba haka ta yi ba."
Cikin damuwa Yusuf ya ce "Yanzu doctor mene ne abin yi?"
"Zamu ajiye ta a nan, a samu jinin ya sauka, idan babu matsala za a iya barin cikin ya cika watannin haihuwar fine, idan kuma akwai matsala za a tiyata a cire cikin"
Hajiya Amina ta ce "Allah ya zaɓa abin da ya fi alkhairi"
Doctor ya amsa da "Amin, dan Allah a kula, hajiya ke kaɗai za ki zauna a gurin ta, babu 'yan dubiya Please, kar a bari kowa ya je inda take, yanzu dai ta samu bacci Alhamdilillah"
"To shikenan in sha Allah, za a kiyaye"
Kiran Alhaji Zailani ne ya shigo wayarsa, dan haka ya bar gurin ya yi gaba ya ɗaga.
"Sharif"
"Na'am ranka ya daɗe"
"Yaya ake ciki, Amina ta gaya mini su na asibitin ku Shukura babu lafiya, haihuwar ce ko yaya?"
"A'a tukuna dai ranka ya daɗe, jininta ya yi hawan da ba zai yiwu mu yi tiyata yanzu ba, mu na dai ƙoƙarin dai-daita jinin nata ne".
"To ko ma dai mene ne, kar ka manta da maganar mu"
"Ban manta ba, ina sane ranka ya daɗe"
"Yauwwa ya yi" ya katse wayar.
*
Jamila ce zaune fuskarta duk hawaye, a gaban Hajiya Sa'a. Hajiya sa'a ta riƙo hannunta ta ce "Kar ki damu Jamila, na san kin yi iya ƙoƙarin ki, za mu canza fasalin aikin namu, Sannan za ki samu lafiya za ki warke gaba ɗaya ma"
Jamila ta jinjina kai ba tare da ta ce komai ba.
"Akwai wata tafiya da nake son na yi Abuja, idan babu damuwa ina son za ki raka ni, amma sammako za mu yi, mu je mu dawo?"
Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Mama za ta bar ni, Baba ne babu lallai ya yadda, amma na san za ta saka baki ya bar ni, zan ma iya tahowa bai sani ba"
"Yauwwa Jamsy, kar ki damu ki kwantar da hankalinki, in dai mu na tare, kuma za ki din ga yi mini biyayya babu abin da ba zan yi miki ba, kin ji yarinyar kirki?" Jamila ta jinjina kai tana ɗan sakin fuskarta.
Ta numfasa ta ce "Hajiya bari na je gida"
"Ban ce ki daina ce mini Hajiya ba?"
"Yi haƙuri Mummy"
"Good, sai kin dawo yarinyar kirki, ki gaida gida, zan saka miki kuɗin, kayan kwalliya a account ɗin ki"
Ta saki murmushi ta ce "Tom Na gode sosai da sosai, Allah ya saka da alkhairi"
Ta juya ta bar falon, tana jin wani irin nishaɗi, duk da wata irin fargaba na ratsa ta, daga ƙarƙashin zuciyarta, da ba ta san ta mece ce ba.
Karo ta yi da wani matashin saurayi, yana ƙoƙarin shiga gidan.
"Sannu ina wuni?"
"Lafiya ƙalau ya ki ke?"
"Lafiya ƙalau" ta amsa tana niyyar raɓa shi ta wuce.
"Gurin Mummy ki ka zo ne?"
Jamila ta ce "Eh gurinta na zo"
Ya ce "Ok shikenan, ki gaida gida"
"Gida zai ji na gode sosai da sosai" ta nufi gate ɗin ta fice.
****
Da ƙyar Nana ta iya sallar asuba, saboda gajiya ga bacci da take ji, da ta idar da sallar ma, a kan sallaya ta jingina tana gyangyaɗi ta kasa azkar ɗin.
Hannunta ya ɗan shafa, ta buɗe idonta da kyar ta kalle shi.
"Bacci ne?" Ta ɗaga masa tana lumshe idonta.
Ya kama hannunta, ya ɗaga ta tsaye, ya ja ta zuwa kan katifa. Ta tsaya tana ƙoƙarin cire hijjabin, ya ƙarasa cire mata ta kwanta. Ta hau katifa ta buɗe bargo ta kwanta, kawai ta ji shi ma ya bankaɗo bargon ya shigo. Zumbur ta tashi zaune tana kallon sa. A ranta ta ce "Lallai ji mutum da samun guri" za ta yi magana ta fasa ta tsaya tana kallon sa. Ayshacool Shi kuwa ya yi kwanciyarsa, ya lumshe idanunsa, ya bar ta a zaune tana hamma. Sai da bacci ya ci ƙarfinta sannan ta kwanta. Sai da ya ji ta kwanta sannan ya buɗe idonsa. Ya juya sosai yana kallonta.
Zai iya cewa tun da ya tsinci kansa a cikin wannan duniyar da yake a yanzu, wadda yake kamantawa da duniyar mafarki, bai taɓa tsintar kansa cikin nishaɗi da farincikin yau ba.
Ya kasance cikin damuwa, da tsananin ɓacin ran rashin sanin waye shi, daga ina yake? Ina zai dosa? Rashin sanin amsoshin nan, na dugunzuma hankalinsa da haifar da wani irin nauyi a ƙirjinsa, wani irin duhu ya mamaye shi, bai taɓa jin daɗin komai, ko farinciki da komai ba. Duk da dai-dai gwargwado Habu da sauran wanda suke tare su na ƙoƙari a kansa, amma sam babu abin da yake raguwa na duhu da damuwa a tare da shi. Sai bayan da ya fara kasancewa da Nana a ɗaki guda.
Ganin gilmawarta kawai, yana kallon ta, yana jin daɗi. Ya kan ji kamar ya yi mata magana amma sai ya kasa, ya rasa mai zai ce mata. A wannan duniyar da ya yi wa laƙabi da duniyar mafarki, ya ga mutane na bawa ahali muhimmanci, amma shi ba shi da su, kuma ba a duba rashin ahalin nasa ba, aka aura mata shi, hakan ya kan saka ya ji tausayinta.
Yanzu a wannan duniyar yana kallon Nana a matsayin ahalinsa. Duk da ba ya son hayaniya, amma muryarta mai sanyi da daɗin sauraro, ba kamar su Habu ba, sai yana cikin damuwa ko rashin lafiya, ya din ga jin muryoyin su a sama kamar kwarankwatsa ba. Ya kan ji babu daɗi idan ya ji ta shiru, yana matuƙar son ya ga tana kallon sa, idan su ka haɗa ido ta murguɗa baki tana magana ƙasa-ƙasa, komai na ta a sanyaye.