Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 17
Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 17: Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 17. "Sayyid" ta kira sunansa da ɗan ƙarfi, amma ta ji shiru.
3,359 words
"Sayyid" ta kira sunansa da ɗan ƙarfi, amma ta ji shiru.
Ta yi mamakin dalilin da yasa ya rufe ko ina haka. Ta shiga banɗaki ta yi alwala, saboda an idar da sallar azahar ma.
Da ya shigo ɗakin ya tarar da ita ta idar da salla, bai ce mata komai ba, ta ɗora girki tana yi masa hira, saboda ba ta iya tuna komai ba. Jin ya yi shiru ba ya tanka mata, ya sanya ta yin shiru.
*
Yaya Atine ce ta zo gida duba Baba, ta ga yadda yake tafiya da ƙyar saboda ciwon ƙafa.
Ta jinjina kai ta ce "Wai Isa wannan ƙafar taka, ka je asibiti kuwa?"
"Atine da wani kuɗin? Kin san auren 'ya na yi kwanan nan ai, mai nasara nake saya da aboniki sai a ji garau da nake haɗiya, shi ne nake samun afuwa na yi bacci"
Ta kwaɓe baki ta ce "Yanzu kana nufin duk kuɗaɗen da ka samu, da auren Nanan babu wanda za ka je Asibiti, ni fa zuwa na yi idan zan samu wani abu ma ka ɗan bani, gidana ko ƙwayar shinkafa babu"
"Haba Yaya Atine, ina su Nazifin da za ki zauna babu abinci?"
"Kai ina Gaddafi, ka ke zaune a haka?"
Baba ya ce "Gaddafi tun auren Nana ya tafi Ikko"
"Ka ga kawai ka fito da kuɗi, idan kuma matarka ta saka ka a gaba, ta tatse ka shikenan dama ka saba abin kunya"
Caraf Mama ta ce "Ina zunubin yake balle romonsa? Ina abin yake ni kar a yi mini sharri, ban ci komai ba"
"Idan ma kin cin ai ba za ki ce kin ci ba, ni Wallahi kamata ya yi ka mayar da hankali su ma su Jamila ka aurar da su, ko ka samu ka huta. Ni ina suke nema tun da na shigo ban gan su ba"
"Su na nan sun je gidanmu" Mama ta ba ta amsa tana tsuke fuska, saboda kar ma ta ja zancen.
Ta gama surutanta, ta tashi ta tafi" Ayshacool **** Nana kuwa haka su ka ƙarasa wunin su, ba tare da wani yana kula wani ba, ya koma mata buzunsa. Sai dai hakan bai damu Nana sosai ba, saboda ya yi mata bayani. Duk da shirun bai yi mata daɗi ba, ɗan kulatan da yake yi, ba ƙaramin daɗi take ji ba.
Sai dai tana zaune, tana addu'ar kwanciya bacci, ya shigo ya gama abin da zai yi ya ɗane kan katifa. Ya zauna ta ƙarasa addu'a ta shafa shi ma ya shafa.
Yana shirin ya ga ta kwanta, amma ta ƙi kwanciya.
Ya ce "Mu kwanta"
Ta murguɗa baki ta ce "Ni ba bacci zan yi ba"
"To mu zauna"
"Ni kawai sai ka wani din ga yi mini shiru, ni ka daina irin haka ba na so" Zuciyarsa na azalzalarsa ya tambaye ta abin da yake cikin zuciyarta, saboda har wani irin zafi yake ji a ƙirjinsa, amma ya kasa furta komai. Ya rasa me ma zai yi gaba ɗaya.
"Ba zaka kula ni ba ko?"
"Husnahhh" ya furta a kunenta. Zirrr tsigar jikin Nana ta tashi.
"Ki amsa ni"
"Na'am" ta furta a tsorace. "Ni mahaukaci ne, nima ba na gane rayuwar da nake yi, rayuwata ta banbanta da yadda sauran mutane suke ta su. Ni baƙo ne a duniyar nan taku. Ke kaɗai ce Ahalina, da ke kaɗai nake gane kan wannan rayuwar. Ba zan iya zama yadda ku ke ba gaba ɗaya, duk da ke ma wasu lokutan kin bambanta da rayuwar sauran mutane. Amma ki yi haƙuri da yadda ki ka same ni"
"Sayyid"
Ya amsa mata da "Ma vie"
"Dan Allah ka gaya mini gaskiya, zan karɓe ta a duk yadda take, dan Allah kai wane jinsi ne? Ka na tsorata ni wasu lokutan"
Hannunsa bai daina yawo a jikinta ba ya ce "Na fi yadda ni halitta ne kamar ke, mutum ne ni, amma ban san ya ake yi... Sai kuma ya yi shiru, kuma ya hana Nana sake cewa uffan, ta hanyar jan su zuwa duniyar ma'aurata, mai cike da al'amura masu tsayawa a zukata da wahalar mantawa.
Duk da, da faransanci yake gaya mata wasu kalamai, da ba ta san ma'anarsu ba, amma kai tsaye maganganun nasa suke shiga zuciyarta, tare da haifar mata da wata irin nutsuwa, duk da wahalar da ya bata.
Ta ƙara narkewa a jikinsa, ga bacci na son ɗaukar ta, amma zuciyarta da ƙwaƙwalwarta, na kan kalaman da ko fassarar su ba ta sani ba, sai dai tsananin daɗin da suke yi mata, ya sanya ta ci gaba da sauran su.
Sun shafe lokaci a haka, sannan da ƙyar ta tashi ta fara yin wanka, sannan shi ma ya tashi, sai dai kan ya dawo tuni bacci ya yi awon gaba da ita.
* Tamkar Nana ta taka rawa yau, saboda murnar za su fita yau, ya ce mata tare za su je dubiyar.
"Amma babu matsala ba za su buƙace ka ba mutanen gidan? Kar mu yi laifi"
"Na gaya musu"
Da wuri ta gama komai, suka shirya suka fita tare.
Ta ɗaukko dubu goma a kuɗin hannunta, ta tsaya ta yi sayayya a hanya, sannan suka tafi.
Asibitin da aka kwantar da Shukura suka fara zuwa.
Haidar ne ya fara gano ta, ya zabura daga jikin mahafinsa ya nufo Nana da wani irin gudu, cikin matsanancin farin ciki.
Caraf Nana ta ɗaga shi, ta rungume tana juyi da shi a gurin. Kawai ya ƙara ƙanƙame ta ya saka kuka.
Ita kanta Nana hawaye ne ya cika mata ido, cikin sanyin murya ta ce "Is ok sweetheart, ya isa haka" ta yi maganar tana shafa kansa cike da ƙaunar sa. Yanayin kamaninsu da ta gani da Sagir, ya sanya ta gane shi ne mahaifin sa.
Ta ƙarasa suka gaisa, ta ce masa "Dan Allah a wane ɗakin suke?"
"Su na ciki room 2 VIP, sai dai ba sa bari a shiga"
Ta ce "Subhnallah jikin har ya yi tsanani haka, Ubangiji Allah ya ba ta lafiya, Hajiyan na ciki ne?" A fusace Sayyid ya ja hannunta, zuwa cikin asibitin. Sagir ya miƙe da sauri ya bi bayan su, saboda ga Haidar a gurin Nana, shi kuma ya ja Nana sun yi ciki ba sallama ba komai.
A ƙofar ɗakin suka tsaya, Sagir ya ƙaraso ya ce "Bari na yi wa Mummyn magana" ya shiga cikin ɗakin, Nana ta dubi Sayyid ta ce "Daga tsayawa tambaya, sai ka ja hannuna mu tafi ai ba zai ji daɗi ba"
Wani mugun kallo ya yi mata, da ya tilasta mata yin shiru da bakin ta.
Hajiya Amina ce ta fito fuskarta ɗauke da fara'a tana faɗin "Ga 'ya ta, ga 'ya ta" ta rungume Nana. Nana ta durƙusa har ƙasa tana gaida Hajiya Amina.
"Lafiya ƙalau Nana, kin ga yadda ki ka yi kyau tubarkallah? Haidar yau ga Nana" Ya yi murmushi yana sake riƙe hannun Nana. Ayshacool Hajiya Amina ta ce "Allah sarki, tare da mai gidan ku ke ashe, mu na ta ƙin abin nan da ganin an zalunce ki, Allah dai ya ƙulla lamarin. Sannu ka ji ya gidan?" Hannu ya ɗaga wa Hajjya Amina tare da risunar da kansa ƙasa cikin girmamawa, ba tare da ya yi magana ba.
Nana za ta yi magana, mijin Shukura ya leƙo ya kalli Nana ya ce "Ta ce ki shigo" mamaki ya kama Nana, amma ta ɓoye hakan. Ya karɓi Haidar saboda kar ta shiga da shi, ya damu Shukura. Nana ta shiga ɗakin da sallama, babu haske sosai a ɗakin, amma ana iya ganin komai da yake ɗakin. Nana ta ƙarasa gaban gadon da Shukura take. Sai dai ta ɗan tsorata ganin Shukura duk a kumbure.
"Sannu Maman Haidar, ya ƙarfin jiki?"
Ta yinƙura da kyar, Nana ta taimaka mata ta jingina da jikin gadon ta ce "Jiki da sauƙi Nana, dama za ki zo duba ni?"
"Haba Maman Haidar, me zai hana? Ni ban za ci za ki kawo yanzu ba ki haihu ba ma. Sannu" Ta jinjina kai ta dudduba ɗakin ta ga daga ita sai Nana a ɗakin. Ta kama hannun Nana ta ce "Na san a zamana da ke, wataƙila na yi miki abubuwa marasa daɗi, duk da ina yaba ɗawainiyar da ki ke yi da Yarona. Sai dai kowane mutum akwai irin baiwar da Allah ya yi masa, komai kallon ƙasƙancin da ka ke yi masa. Wannan maganganun nawa, ba sa rasa nasaba, da yawan miyagun mafarkin da nake yi da ke"
Gaban Nana ya yi wata irin mummunar faɗuwa, ta kalli Shukura ta ce "Da ni kuma?"
Sai kuma Shukura ta rikice, ba ta san ta ina za ta fara yi wa Nana wannan bayanin ba, amma ta dake ta ce "Mafarkai nake yi marasa daɗi, kuma ina yawan ganinki kin zo za ki taimaka mini. Ni dai kawai ki saka ni a addu'a a tsorace nake, ji nake yi tamkar zan bar duniya, ba zan rayu ba".
"A'a maman Haidar, kamar ba wayayyi ba, mafarki fa ba gaske ba ne ba, duk da wasu lokutan ishara ne, amma mafarkin annabawa ne yake ɗari bisa ɗari gaskiya. Sai kuma wasu bayin Allah da a kan yi wa ishara a mafarki. Wasu lokutan shaiɗan ne kawai yake wasa da hankulanmu, amma ki kwantar da hankalinki ki saka a ranki babu wani mai yi sai Allah, kuma babu wanda ya isa ya yi miki abin da Allah bai yi miki ba. Sannan in sha Allah zan saka ki a cikin addu'a ba dan ki yarda cewa ganina da ki ke a mafarki a zahiri nice zan taimake ki ba, Ubangiji za mu nufa da buƙatunmu baki ɗaya, shi zai magance koma mene ne, ki kwantar da hankalinki dan Allah"
Shukura ta jinjina kai ta ce "Haka ne, na gode sosai da sosai Nana, na gode"
"Ba komai Allah ya ƙara afuwa, bari na je, na ji an ce ba a bari a shigo a gan ki"
"To shikenan na gode" ta ji daɗin kalaman Nana, mussaman da ta yi ta nanata mata, mafarki ba gaskiya ba ne, wasu lokutan sharrin shaiɗan ne kawai.
Nana ta fito daga ɗakin, jikinta duk a sanyaye.
Hajiya Amina ta taso tana faɗin "Nana kin fito?"
"Eh Hajiya, Ubangiji Allah ya bata ingantacciyar lafiya, Ubangiji Allah ya raba ta da cikin nan lafiya"
"Amin ya Allah Nana"
"A'a Hajiya ina Haidar ɗin?"
"Babansa ne ya tafi da shi yanzun nan"
Jiki a sanyaye Nana ta ce "Kash, ban gama ganinsa ba Hajiya"
"Ki yi haƙuri, jiransa ake yi, yana tafiya da Haidar ne gurin kakarsa ake kai shi, ni kin ga ga jinya, abin zai yi mini yawa ne. Amma in sha Allah zan saka a kawo miki shi har gida."
"To shikenan, ga wannan a bawa yarona, wannan kuma a saya wa Maman Haidar wani abin, ban san me take so ba"
Hajiya Amina ta ce "Nana har da ɗawainiya har haka, dan Allah ki bari kar ki takura kan ki, zuwan ma da ki ka yi na ji daɗi sosai da sosai "
Nana ta ce "A'a Hajiya, idan ba ki karɓa ba ba zan ji daɗi ba, dan Allah ki karɓa"
Hajiya Amina fuskarta ɗauke da murmushi ta karɓa ta ce "To Allah ya saka da alkhairi, ki yi wa mijinki godiya ma ya ba wa Haidar kuɗi, Allah ya saka da alkhairi. Na ga haryanzu ba ya magana"
Nana ta ɗan saci kallonsa, ta yi murmushi ta ce "Ba komai Hajiya"
Ganin hirar ta ssu ba zata ƙare ba, ya sanya shi yin gaba, Nana na ganin ya yi gaba, ta yi wa Hajiya Amina sallama a gurguje, ta nufi hanyar da ya bi.
"Shi ne za ka yi gaba ka bar ni?" Ya waiwayo ya kalle ta ya ci gaba da tafiya. Ayshacool Ta tsaya tana yi wa Nurses ɗin gurin sallama, ya ja ya tsaya tare da waiwayowa yana hararar Nana. Ta yo gaba tana murmushi, tare da mamakin yadda yake so ta ƙarfin tsiya sai ya mayar da ita irin sa, na rashin kula mutane.
Yana zuwa bakin ƙofar fita, ya ja ya tsaya, Nana ta ƙaraso tana ƙoƙarin duba, abin da ya hana shi fita amma ya tare ta, shi bai shiga ba, kuma ba dawo ba. Ta leƙa ta gefensa, ta ga mene ne ya hana shi wucewa, kawai ta ga Alhaji Zailani, tare da Doctor Sharif, a take gabanta ya yi wata irin mummunar faɗuwa, ta ja ta tsaya cike da razani da fargaba.
Ayshercool 08081012143 Ayshacool Alhaji Zailani ma gabansa ne ya faɗin, cikin fargaba yake bin ƙwayar idon Buzun da kallo, tare da mamakin ganinsa a gurin a dai-dai wannan lokacin.
A hankali Sayyid ya ja da baya, taku biyu, ya sanya hannunsa ya riƙo Nana ta bayansa, ya ba su hanya.
Alhaji Zailani ji yayi tamkar an zare masa lakar jikinsa, jikin nasa ya yi wani irin sanyi, wani abu mai kama da tsoro ya shige shi. A hankali ya taka ya shigo, yana ƙoƙarin kallon Nana da ke tsaye a bayan Sayyid, amma Sayyid ɗin ya hana hakan, saboda yadda ya ƙare babbakewa ya kare ta. Ita kanta Nana ji ta yi yanayin ta na ƙoƙarin canzawa, ta saka hannu ta riƙe na Sayyid, tana addu'a a cikin zuciyarta. Wani irin baƙin ciki ya mamaye zuciyar Alhaji Zailani, ganin yanzu wannan Buzun ne mijinta, da ya aure ta ya san da yanzu buƙatar sa ta biya, wani abin yake hari ba wannan ba, amma Mahaifinta ya yi masa sagegeduwa. Doctor Sharif ya ce "Alhaji lafiya kuwa?"
"Eh lafiya ƙalau" Har Alhaji Zailani ya yi gaba, ya tsaya ya sake waiwayowa, amma ya sake ido huɗu da Sayyid, ya kange Nana, ya kare ta babu yadda za a yi ya iya hango Nana yadda yakamata. Sai da Sayyid ya tabattar Alhaji Zailani ya bar gurin, sannan ya waiwayo ya kalli Nana, yadda duk jikinta ya yi sanyi, ya kamo hannunta suka fita waje.
Bai dai ce mata komai ba, ta tare musu abin hawa, ta gaya masa inda zai kai su.
Gaba ɗaya Nana ta rasa abin da yake yi mata daɗi, ta rasa dalilin da ya sanya, gaba ɗaya ta rasa abin da yake yi mata daɗi. Duk da tana zaton hakan baya rasa nasaba da mugun nufin da Alhaji Zailani ya taɓa nuna mata, amma ta rasa dalilin da ya sanya gaba ɗaya take nema ta rikice, ta fita daga hayyacinta.
A hankali ta kwanta a jikin Sayyid. Cikin damuwa ya dube ta, ya dafa ta ya ce "Ba lafiya ne?"
Ta ce "A'a"
"To Meyafaru?"
"Ba komai" ta furta a hankali kamar mara lafiya.
"Ko mu koma gida ne?" Ta girgiza masa kai alamar a'a.
"Sannu" ta jinjina masa kai.
Sai da suka je daf da titin unguwar su, sannan ta tashi daga jikinsa, tana kallon titin nasu.
Suka je gurin da za su sauka, ya ciro kuɗi a aljihunsa ya miƙa wa mai Napep ɗin su ka tafi.
"Sayyid"
Ya waiwayo ya kalle ta.
Sai kuma ta yi shiru, dan rasa me za ta ce masa ta yi.
Tsayawa ya yi yana ƙare wa ƙofar gidan su Nana kallo. Ko ina faci ga uwar kwata a layin.
"Bari na shiga na yi musu magana, sai ka shigo"
Ya jinjina mata kai ya ce "Zan je masallaci " Ta ce "To shikenan, a yi mini addu'a" Ya ɗaga mata hannu, tare da jinjina mata kai, ita kuma ta shiga cikin gidan.
Sallama ta yi, Nasiru yana tsakar gida yana goge takalminsa, yana ganin Nana ya tashi da gudu ya nufe ta.
Nana ta rungume shi tana murmushi, "Nasiru ya garin?"
"Lafiya ƙalau"
"Ina mutanen gidan ne?"
"Mama ta ɗan fita, Baba kuma ya je masallaci"
Nana ta ce "Samo mini tabarma na zauna a nan, ina su Jamila?"
"Jamila daga warkewarta ta tafi yawo, Suwaiba ma ba ta nan"
"Ohh ya jikinta kuwa, mu ka yi waya da Ummi, ta ce mini tun da ku ka dawo ba ta da lafiya "
Nasiru ya ce "Eh, amma ta warke, Mama ta ce wai me magani ya ce Aljani suka yi wa laifi. Aka yi sadakar ƙosai, aka dafa zakara aka bin...
"Ammm ya jikin Baba kuma" Nana ta katse maganar Nasiru.
"To ga shi nan dai, yanzu zai shigo ai ki gan shi"
Nana ta ɗaukko wayarta ta ce "Nasiru ga wayata, ga kuɗi ka yo mini turin fina-finai dan Allah" ya karɓa ya miƙe tsaye tare da faɗin an gama yanzu kuwa.
Nana ta tashi ta fara tattare tsakar gidan, saboda yadda aka bar shi kaca-kaca. Ta gama sharewa Baba ya yi sallama, ta ɗago ta kalle shi. Da ƙyar yake taka ƙafarsa yana bin bango. Ya tsaya sororo ya ce "Ke me ki ke yi a gida kuma?" Duk da Nana ba ta ji dadin tambayar da ya yi ba, saboda ta san yana tunanin ko auren ya samu matsala ne, amma ta yi murmushi ta ce "Baba duba ku na zo yi" Ta yi maganar tana gyara masa tabarma a tsakar gida.
Ya ƙarasa ya zauna da ƙyar, Nana ta koma gefensa ita ma ta zauna ta ce "Sannu ya jikin naka?"
"Jiki ga shi nan mu na lallaɓawa abu ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa"
Ta kalli ƙafafuwan nasa ta ce "Wacce ce take ciwon a ciki?" Ayshacool Ya ce "Duka, sai dai wannan ta fi ciwon" ya yi maganar yana nuna mata ƙafarsa ta hagu.
"To Baba ka je Asibiti?"
"Da wane kuɗin zan je Asibitin? Na gargajiya zan koma, ina fatan dai ba wata matsalar ba ce ta dawo da ke gidan nan?"
Nana ta yi murmushi mai ciwo tana buɗe jakarta, ta fito da leda tana faɗin "Baba idan matsala ta dawo da ni, ba zaka karɓe ni ba ko? Ai ka yi mini addu'a ka ce Allah ya bani zaman lafiya, in sha Allah matsala ba za ta kawo ni ba sai alkhairi" ta yi maganar tana ɓare dafaffen ƙwan da ta fito da shi daga leda.
Ta gama ɓare ƙwan, ta miƙa wa Baba, ya saka hannu ya amshe, yawun bakinsa na tsinkewa.
"Baba na san ni mai laifi ce a gurinka, na ɓata maka rai a kan abubuwa da dama, mussaman na bijirewa auren waɗanda ka so na aura, amma ina son mu saka a ranmu cewa, dukkanin su Allah bai ƙaddara akwai mijina a cikin su ba. Ni yanzu babban fatana ka daina yi mini kallon mutuniyar banza, na san dole na fuskanci tuhuma na abin da ya kai ni ɗakin su magadi, amma ba abin da ka ke tunani ba ne Baba, da zan lalace da ban kawo wannan lokacin ban lalace tun a baya ba." Tuni hawaye ya wanke mata fuska, zuciyarta na wani irin tafasa da raɗaɗi. Baba bai ce mata komai ba, sai karɓe ƙwan da yake yi yana lamushewa. Ta goge hawayen ta, sai da ta ɓare masa dafaffen ƙwan nan guda biyar, ta ɗebo ruwan randa ta kawo masa ya karɓa yana sha.
Ta ɗaura alwala ta yi sallar azahar, bayan ta idar, Nasiru ya shigo gidan yana faɗin "Nana ga wayar ki, an ciko miki ita da fina-finai fal"
Ta yi murmushi ta ce "Na gode yaron kirki"
Mama ta yi sallama ita da Suwaiba, sai da suka ɗan yi turus ganin Nana a gidan babu tsammani.
"Lafiya dai na ganki a gida? Ba dai auren ne ya samu matsala ba"
Nana ta waiwaya ta kalle ta, ta yi murmushi ta ce "A'a ganin ku na zo yi, na gaishe ku, aurena bai samu matsala ba" Mama ta kwaɓe baki tana rataye mayafinta a kan igiya.
Nana har kallon Mama take yi, tana mamakin wai ita ba ta san ƙarara a fili take nuna ƙiyayyar da take yi mata ba.
Nana ta ce "Suwaiba ya ku ka zo gida?"
"Lafiya ƙalau wallahi, mu na dawowa Jamila ta kwanta rashin lafiya"
"Haka Ummi take gaya mini, shi yasa yau na yinƙuro na fito. Nasiru duba idan ya idar da salla, ya shigo ya duba Baban mu tafi, ban yi girki ba"
Nasiru ya ce to.
Suwaiba ta ce "Nana wai waye yake ba ku Abinci? Gidan da ku ke aikin ne suke ba ku?"