Kenza eBookz

Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 34

Buzu complete by ayshacool 1 - Chapter 34

Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 34: Buzu complete by ayshacool 1 Chapter 34. Ko da ya shiga ɗakinsa, babbar rigarsa ya cire saboda azabar gumin da…

3,340 words

Ko da ya shiga ɗakinsa, babbar rigarsa ya cire saboda azabar gumin da yake yi. Dan tun da Doctor Sharif ya gaya masa ga yadda suka yi da Shukura hankalinsa ya yi mummunan tashi. Ya kuma sake jaddada wa Sharif, muddin wani abu ya fita to babu hannunsa a ciki. Kuma likitan ya yi masa bayanin process ɗin da ya bi, abu ne mai wahala a gano. Ya yakice gumi ya nemi guri ya zauna.

Hajiya Amina ta ce "Me yasa ba ki ba shi haƙuri ba, kina kallon yadda ya yi fushi?"

"Mummy, duk wannan abubuwan kamata ya yi a tsaya a saurare ni, a kuma fahimce ni. Da hankalina fa ta yaya zan din ga iƙirarin an kashe mini ɗa haka kurum. Ayshacool Mummy ranar da za a yi mini aiki, kina bacci cikin dare, na kasa bacci saboda damuwar da nake ciki, aka buɗe ƙofar ɗakin, aka zo aka kama hannuna aka laluba cannula, aka yi mini wata allura a cikin duhun nan. Tun da aka yi mini allurar nan. Na ji kaina ya fara juyawa, ina neman na fita hayyacina, duk iya ƙoƙarina na kasa, na ji jikina na ƙamewa kamar zan yi jijjiga. Saɓanin da da idan za a yi mini allura cikin dare, za a ƙwanƙwasa ɗakin, sai kin tashi kin ce a shigo tukuna, a kunna ftila a yi mini" Mummy ta ɗan yi shiru, cike da mamakin me yasa tuntuni ba ta faɗa ba, amma domin kawo ƙarshen maganar, sai kawai ta kawo gigin ciwo ne ya sanya ta ga haka a lokacin. Dan haka ta ce "Duk da haka wannan ma ba hujja ba ce, ke da ki ke fama da ciwo ina za ki tantance wani abu ma. Dan Allah ki bar zancen nan" Shukura ta yi murmushi ta ce "Shikenan, na bar shi"

Sai kuma ta sake cewa "Mummy, Nana shiru, ni yakamata ki kwatanta mini gidan da suke na kai mata Haidar"

"Gidan Alhaji Garba giwa ne fa, kuma fafur babanku ya hana ni zuwa ban san dalili ba" Dummm! Ƙirjin Shukura ya buga, ta ce "Saboda ne ya hana ki zuwan?"

"Ban san dalili ba, za ki je ne? Sabon gidansa nan Kano"

Shukura ta ce "Wace matar ce a gidan?"

"Halima ce, uwar gidan sa"

Shukura ta girgiza kai ta ce "Ba zani ba, gidansu tsohuwar matar Sagir ce"

Mummy ta waro ido ta ce "Ke haba? Dama 'yar Halima ce matar Sagir ɗin?"

"Eh mana"

"Ikon Allah, da na ce wa Daddy, ya taimaka musu, a samo wa mijin Nana, gurin da zai yi gadi, su samu su zauna, shi ne aka samo gidan"

Shukura ta ce "wai canza masu gadi ku ka yi ne?"

"Ina fa, ina nan cikin gida, daga baya ma Yusuf yake gaya mini. Wai zuwa aka yi da motoci da alama daga ƙasar su ne ma, motocin duk rubutun fransanci aka kwashe su kaf, kuma babu wanda aka yi wa bayanin me yasa"

"Ikon Allah, kuma ba laifi suka yi ba?"

"To ina zan sani, ina nan cikin gida?" Suka ci gaba da tattaunawa da jajanta lamarin. Har wayar Nana suka jarraba kira, su ji ko ita nata mijin yana nan, ba a kama shi ba amma wayarta ba ta shiga sam.

**** Da safe Nana ta tashi, ta fara alwala sannan ta zuba wa Sayyid ruwan da yara suka ɗebo musu jiya, dan gidan babu ruwa. Ya yi alwala a ƙofar ɗakin, sannan suka koma ciki ya yi salla. Sai dai bai ga alamun ta san abin da ta yi cikin daren jiya ba. Ƙarfe tara da rabi, Uwani ta aiko yara da kunu da 'yar tsala aka kawo wa su Nana. 'yar aiken ta ce "Uwani ta ce idan kin gama karayawa, wai ki je"

Nana ta ce "To, zan zo a ce mata mun gode sosai da sosai, Allah ya biya ta"

Ta koma ta zauna a gaban Sayyid ta ce "Sayyid, ka ga kunu ne da 'yar tsala za ka iya ci, ko na nemo maka wani abin?" Ya girgiza kai.

"To za ka iya cin wannan ɗin?" Ya gyaɗa mata kai.

Kunun tsamiya ne, na daka ba niƙa ba, ya sha kayan ƙamshi, sai dai babu suga ko kaɗan a ciki, ga tsamiyar nan cau har ka. Ƙuli-ƙulin 'yar tsalan, ya sha barkono, ta zuba masa a kofi ta ba shi. Ya saka hannu ya karɓa. Tun da ya yi kurɓa ɗaya, ya yi shiru. Nana ta ce "Za ka iya sha kuwa?" Ya jinjina kai ya ci gaba da sha, saboda Nana. Ya haɗa da 'yar tsalan nan, duk da ba son Abincin yake yi ba. "Sayyid, idan ba zaka iya cin Abincin nan ba, ka bari na nemo maka wani"

Ya ɗaga kai ya kalle ta, sai dai ba baki, dan haka ya harare ta, ya ci gaba da cin abincin. Ta yi murmushi ta ce "Ni ka ke harara ko, aishikenan"

Ya gama karyawa, ta saka ɗankwalinta, ta goge masa bakinsa da hannunsa. Ta ce "Bari na je kiran da Uwani take yi mini, daga nan na saka a raka ni, na ɗan yi mana sayayya, dan na san dole za ta daina bamu Abinci yau da gobe sai Allah" Bai ba ta amsa ba, ya jingina da bango, saboda yadda yake jin daɗin hakan, yana lumshe ido.

"In je?" Ya yi mata shiru, kuma yaƙi yi mata wata alamar, da za ta gane ya amince ko a'a.

Cikin shagwaɓa ta ce "Sayyid" ya kawar da kansa gefe, ya ƙi buɗe ido.

"Duk da maganar nan ɗaukewa take yi, amma dai tun asalinka miskili ne, ina ta magana ka ƙi kula ni, ni ce fa rayuwartaka guda ka ke wa haka?"

Murmushi ya yi, tare da saka hannunsa a cikinta, yana shafawa a hankali. Ayshacool "Wai ba za ka kalle ni ba?" Ta yi maganar tana juyo da fuskarsa. Ya ƙara rintse idanunsa, wai ba zai kalle ta ba. Nana ta din ga dariya.

Ya ja jikinsa a hankali, ya kwanta a kan cinyarta, ya zuba wa cikinta ido, tamkar zai gano abin da yake cikin.

"Idan na haihu na ga yadda za a yi, da kai da jaririn wa zai bar wa wani cinyar nan" Ta yi maganar tana shafa gashin sa.

*

Hajiya Sa'a ce take cin abinci, tana kallon Jamila, da take ta cakala kaɗan-kaɗan.

"Jamila ya ne? Ki saki jiki ki ci abinci mana" Jamila ta jinjina kai ba tare da ta ce komai ba.

"Ko dai haryanzu abin da ya faru ɗin ne yake damun ki? Tun wuri ki ajiye wannan abin, ki ci gaba da rayuwar ki cikin kwanciyar hankali. Ɗan ƙaramin abu ne fa, ranar da aka ce ki bayar da jini kuma ya zaki yi? Ki na gani Safiyya ta tafi Dubai ma sarin kaya, kuma duk harka ce ta ƙungiya ta ɗaukakata haka. Har gara ke ma da ba ki da aure, Safiyya da aurenta, amma kalli yadda ta kama ƙasa, mijin ma ita yake yi wa biyayya, ki saki jikinki dan Allah ki daina wannan damuwar. Ki ƙarasa cin abincin, Talatu ta gyara gidan, idan an zo ana son kaya, kin san gurin da suke, zan je sake duba Fatuhu ne, daga nan na je a gyara mini kaina"

"To Mummy a dawo lafiya"

"Yauwwa Daughter Allah ya sa"

Ta gama abin da take yi ta fita, bayan fitar ta, Jamila ta tashi ta nufi harabar gidan, tana kallon flowers ɗin da aka ƙawata harabar da su. Jibga-jibgan motocin Hajiya Sa'a uku na hawa. Ga na ɗanta Abba biyu. Iya harabar gidan abar burgewa ce, ta yadda duk mai rai zai yi fatan ya samu wannan wadatar. Sai dai kash, hanyar da aka bi gurin tara dukiyar, duk wanda ya ji muddin yana da imani, sai ya gudu da ƙafafuwansa.

Ji ta yi kamar wani abu yana bin wuyanta, ta juya a hankali ta ga Abba ne a tsaye, yana saka abin fulawa a wuya. Ta yi guntun murmushi ta ce "Yaya Abba"

"Na'am ƙanwar Abba. Ya na ganki nan lafiya dai ko?"

"Lafiya ƙalau, ba ka fita ba?"

"Yau ba zan fita ba, ba na jin daɗi ne gaba ɗaya, dan da zazzaɓi ma na kwana wallahi"

Cikin tausayawa ta ce "Kash, sannu Allah ya ba ka lafiya. Ka je Asibiti mana"

Abba ya ɗan numfasa ya ce "Na sha magani already, dan haka ba sai na je ba, zo mu je mu zauna ki yi mini hira, na san zazzaɓin zai sauka gaba ɗaya" Dariya ta ɗan yi ta ce "Ai ni ban iya hira ba"

"Ba wani nan, amma ki na yi da Mummy ai, gaskiya mu je sai kin yi mini" Tana dariya ya wuce gaba ta bi bayan sa. Sanyin halin Abba ya fara tasiri a zuciyar Jamila.

* Alhaji Fatuhu na zaune, Hajiya Suwaiba ta gama gyara jikinsa, fuskarsa ɗauke da damuwa, ya kalli uwar 'ya'yan nasa ya ce "Haryanzu Fadilan ba ta haihu ba?" Ta taɓe baki ta ce "Tana can ba ta haihun ba tukuna."

"Allah ya sauke ta lafiya" ta yi shiru ba ta amsa ba.

"Yakamata a sallame ni na koma gida haka, na gaji da zaman Asibitin nan gaba ɗaya"

A hasale ta ce "To mu koma gida mu yi yaya ne? Nan ɗin ba dai magani ake baka ba ana kula da kai, komai sai ka nuna kai ba a kyauta maka ba, ba a iya ba haba dan Allah"

Jiki a sanyaye ya ce "Yi haƙuri, Allah ya baki haƙuri" daga haka ya sunkuyar da kansa. Sai kuma jikinta ya yi sanyi, ta zauna a kusa da shi, tana tunanin ta yi magana. Ta ga yana share hawaye.

Cikin damuwa ta ce "Alhaji kuka ka ke yi? Dan Allah ka yi haƙuri raina ne a ɓace, amma dan Allah ka yi haƙuri"

Ya yi mata shiru, gaba ɗaya ta rikice ta rasa abin da za ta ce. Raudah ce ta turo ƙofa hannunta da towel ta ce "Daddy guess what?" Ta miƙa masa narkeken jaririn da Fadila ta haifa.

Hannunsa na karkarwa ya riƙe jaririn ya ce "Another Muhsin" ya yi maganar yana murmushi.

Ya din ga yi wa jaririn kiss, yana shafa shi kamar ba a taɓa yi masa haihuwa ba.

****

Fafur Sayyid ya hana Nana zuwa ko nan da can, har aka yi azahar.Uwani ta sake aiko musu da dambu, ta ce a cewa Nana ba za ta zo ba, sai ta zo da kanta.

Cikin damuwa ta ce "Sayyid dan Allah ka bari na je, na ji kiran me take yi mini" fafur ya sha kunu ya tsuke fuska. Ayshacool Babu yadda Nana ta iya, ta zauna ta ƙi fita. Ta zazzage kayansu, tana ƙara gyara musu, ta fito da kayan wankin gashinsa, da turarrukansa da duk wata sai su Habu sun sayo sun kawo. Ta ɗaga kai ta ga ita yake kallo, ta ɗan yi murmushi ta haɗe su a guri ɗaya da combs ɗin sa na taje gashi.

Sai yamma bayan sallar la'asar, ta yayyafawa tsakar gidan ruwa, ta share shi. Ta yi shimfiɗar tabarma a tsakar gidan, ta saka wa Sayyi fululluka ta kamo hannunsa zuwa waje. Ya zauna, ta ɗaukko mayafin rawaninsa ta yafa masa a kansa.

Babu jimawa sai ga Uwani ta zo, tana faɗin "Tun da ba za ki zo ba, ni ga ni na zo da kaina"

Nana ta ce "Ba ƙin zuwa na yi ba Uwani, yanayin jikinsa ne sai a hankali, shi yasa ban fito ba"

"Koma dai mene ne gani na zo ai" Ta kalli Sayyid ta ce "Sannu ko" ya jinjina mata kawai.

"Dama kiran ki nake yi, na ji idan akwai wani abu da ku ke buƙata?"

"Eh, ina son yin sayayya ba mu da fitila sai ta waya, da kuma 'yan kayan buƙatu"

"To da kin sanar, ai da na saka yara sun raka ki, dama zan ce miki kuma idan an kwana biyu, yakamata ki zo a ɗan zagaya da ke cikin dangi, su san kina garin nan, tun da dama ba zuwa ku ke yi ba, dui ba sanin ku aka yi ba"

Nana ta jinjina kai ta ce "To in sha Allah"

"Wai ni Nana ina Mai jidda kuwa?"

"Tana can Bauchi inda take aure"

Uwani ta ce "Kuma tana zuwa?" Jiki a sanyaye Nana ta girgiza kai.

"Ai dama na san babu lallai ta zo, ko dan saboda baƙin halin Isa. Ai ya bamu mamaki. Ita ma tun da suka rabu ba ta sake zuwa garin nan ba. Kuma yakamata mu je na zagaya da ke, har inda danginta suke a nan"

Cikin mamaki ta kalli Uwani ta ce "Danginta kuma?"

"Ƙwarai da gaske, tushen Maijidda garin Buda ne. Kakanninta 'yan nan garin ne, can wajen unguwar Wanzamai, ƙarewa ma a nan garin suka haɗu da babanku. Ai kakarta aka raina a Bauchi, aka haifi babarta da ita a can. Har an saka mata rana, suka zo garin nan, ke ma Babanki ya zo gida, suka haɗu a dandali. Aka yi ta ɗauki ba daɗi suka ƙulla soyayya. Ga shi can garinsu an saka mata rana da wani, ina ga shi ne mijinta na yanzu da take aure. Asali tun kan ta auri babanku da shi aka fara saka mata rana. Kakarta ta ce sai an warware wancan baikon ta auri babanku, ko ba komai sa din ga zuwa gida a kai kai. Haka aka mayarwa da wancan kuɗinsa ta auri babanku. Ya Babanku ya so ta sosai da sosai, kuma aka ƙulla auren nasu da tunanin hakan ya ƙara kawo zaman lafiya a tsakanin zuriyarmu da zuriyar wanzamai kin san a tarihin garin nan ba zaman lafiya ake ba. Kuma dai cikin ikon Allah sun fara zamansu lafiya gwanin sha'awa, amma Allah ya ƙaddara rabuwar su."

Nana ta yi shiru tana tunanin, kamar ta san wani abu mai kama da wannan labarin da Uwani take ba ta, amma sam ta kasa tunawa. Gaba ɗaya hirar ta Uwani ta gundure ta, saboda ta san shi kansa Sayyid a takure yake, ba ya son mutane ko kaɗan, balle uwa uba dogon surutu. Ita kuwa Uwani tamkar an ƙona ta a ka ko gajiya ba ta yi. Babu wanda ya taɓa ba ta wannan labarin, sai yanzu babu wanda ya taɓa gaya mata cewar mahaifiyarsu tushenta a garin Buda yake, sai dai kamar ta san labarin da Uwanin ta bata.

"Ga wata 'yar rama na zo muku da ita, sai ku ci kafin Abincin dare ya sauka. Wai shi mijin naki kurma ne?"

"A'a ai kin ga ba shi da lafiya ne"

"Eh gaskiya ne, Allah ya ba shi lafiya, amma a ina ki ka samo Buzu haka? Ni wai anya ma labarin da Rabi ta din ga bayar wa ranar bikinki nan gaskiya ne? Abin dai da mamaki. Allah ya ba shi lafiya bari na tafi, dan Allah idan ki ka samu lokaci kya zo a je a gaggaisa.

"To in sha Allah zan zo"

"Yauwwa, zan din ga turo miki yara, idan da aike kya din ga ba su, duk 'yan uwanki ne, 'ya'yan 'yan uwa ne. Kuma ki kwantar da hankalinki duk abin da ku ke buƙata ku sanar mini, da yardar Allah ba zai gagara ba"

Nana ta ce "In sha Allah, mun gode sosai da sosai"

"Ba komai, ki yi haƙuri ki riƙe mijinki ki kula da shi, sai ki ga kaf ayyukan ki, Allah bai karɓa ba, silar wannan jinyar ta sa ki shiga aljanna, a yi ta haƙuri yayata"

Nana ta tashi ta raka ta, ta ce "In sha Allah" Ayshacool Ta yi ƙasa da murya ta cewa Nana "Dan ubanki, ki din ga ɓoye mijinki, kar ki bari 'yan mata su din ga zuwa su na kallon sa." Uwani ita iya rage muryarta kenan, amma Sayyid na jin ta. Nana ta ɗaga kai suka yi ido huɗu, ya yi murmushi yana sunkuyar da kai.

*

Alhaji Fatuhu, farin cikinsa ya kasa ɓuya, duk da halin rashin lafiya da yake ciki, idan aka zo duba shi, sai ya yashe haƙoransa da sukaɗai suka rage farare a jikinsa. Alhaji Zailani ya ƙura wa jaririn ido, ya kalli Alhaji Fatuhu da yake ta yashe baki.

Hajiya Sa'a ta ce "Kai Fatuhu. Sai ka ce ba a taɓa yi maka haihuwa ba, ji yadda ka ke washe baki, kana fama da kan ka"

Hajiya Suwaiba ta kwaɓe baki ta ce "Abin da na gani kenan"

Alhaji Zailani ya ce "A'a ku bar shi ya yi, ɗan mutum fa, kyauta ce Allah ya ba shi, da duk Duniya babu mai ba shi. Ni ba gani ba 'ya'yan duk babu sai biyu ne suka tsaya." Ya yi maganar yana zuba wa jaririn ido, yana tuna na Shukura. Tun da yake harkar ƙungiya, bai taɓa bayar da jinin da ya tsaya masa ya kasa mantawa ba, sai na Shukura. Mussaman idan yana tuna irin baƙar wahalar da ta sha. Ya kalli Fadila, da take ɗakin a zaune, ga jego tana yi, amma ta tare a Asibiti da ɗanyen jaririn da ko suna ba a yi ba.

Ya yi ajiyar zuciya ya ce "Wane sunan za ka saka masa?"

"Muhsin ɗina zan mayar" ya yi maganar muryarsa ɗauke da rauni.

Hajiya Sa'a ta ce "Wai an din ga saka Muhsin ɗin kenan?"

"Sunan mahaifin Fadila ne, shi za a mayar mu ci gaba da kiransa Muhsin, ni na yi mata alƙawari shi yasa. Na so Muhsin ɗina da ya rasu sosai da sosai. Na ji zafin rashin sa, sai dai ina tausayawa wannan Muhsin ɗin. Ya zo lokacin da mahaifinsa ba shi da komai, ba zan iya ɗaukar nauyinsa na kula da shi ba. Wataƙila ma kafin ya yi wayon sani na na rasu. Ga shi ko hakika ba zan iya yi masa ba" ya yi maganar hawaye na zubowa daga idanunsa.

"Haba Fatuhu, ya haka? Dan dai Hakikar da za ayi wa jaririn nan, ka san ba za ta gagara ba, amma ya za ka zauna kana kuka kamar ƙaramin yaro, a gaban iyalinka da 'yan uwanka hakan bai kyautu ba ai".

Alhaji Fatuhu ya ɗago idanunsa da suka yi jawur ya ce "Zailani. Ka san me nake ji kuwa? Gidaje da motocin hawa nake da, ina kyautar maƙudan kuɗaɗe ba tare da na ji komai ba, da abu ya dame ni, zan sai ticket na tafi umara. Ina da shaguna dukiya Allah ya yarje mini, bayan gwagwarmaya da na sha ta rayuwa. Astagfirillah ba ƙarar Allah nake kawowa ba, ko rashin imani da ƙaddara ba, ina jinjina girman lamarin Ubangiji, kuma ina jin babu daɗi ɗa na na cikina, ba zan iya saya masa ko wando ba"

Fadila ta ce "Dan Allah Daddy ka yi haƙuri. Mu na murna sauƙi yana samuwa, ga shi ka na ta magana sosai da sosai, kukan nan karya mana zuciya yake yi. Kuma da ka yi mana a baya, yanzu kuma da Allah ya kawo jarrabawa shikenan sai a yi haƙuri"

Su na nan zaune, sai ga ƙanin Baban Fadila, ya zo duba Alhaji Fatuhu ya kuma jaririn Fadila, wanda shi ne waliyyin Fadila. Sai dai shi ma ya tsorata da ganin Alhaji Fatuhu.

"Alhaji haka jiki ya zama? Subhanallah Allah ya baka lafiya"

"Amin kawu, amma jiki ya yi kyau Alhamdillah, tun da ina ta magana"

"Haka ne, amma menene takamaiman abin da aka ce ya same ka ne?"

Fadila ta ce "Haryanzu ba a gano takamaiman mene ne ba, yau a ce ƙodarsa ta kumbura, gobe a ce ko cancer ce, an yi gwaji ba ita ba ce. An yi gwajin zuciya shi ma lafiya ƙalau"

Cikin damuwa ya ce "Amma Fatuhu ana haɗa maka da na addini kuwa? Ka san muna da ido ne ba na ganin gari ba. Mussaman ku da ku ke shahararrun mutane da Allah ya ba wa wadata. Yakamata a yi na sihiri da shaiɗanu"

Alhaji Zailani ya ce "A'a ga likitoci su na kula da shi, ya za a yi a ce kuma a kawo wani abu daban? Magungunan gargajiyar nan kashe mutane suke yi ai, tun da ba auna su ake yi ba".

Readers Also Read