Canjin rayuwa Book 3 - Chapter 7
Canjin rayuwa Book 3 Chapter 7: Canjin rayuwa Book 3 Chapter 7. 8⃣9⃣Hajiya Nana tace, Nafisa in har zaki fitar da kudi gurin shawo kan yaronnan, ba zai…
4,343 words
8⃣9⃣Hajiya Nana tace, Nafisa in har zaki fitar da kudi gurin shawo kan yaronnan, ba zai zama matsala ba. Nafisa tace, haba Nana kamar baki sanni ba, in ta samu kan yaronnan koni sai na qara haskawa a idon babansu bare ita. Kin sani ban tausayin kudi a gurin kashewa, ynxun dai fada min me za'a yi? Hajiya Nana tace, tsabar katan qamshi za'a hada masu fizgar hankali. Sai yabi ta ko ba don Allah ba. Ba sai ta shafa wani man bilicin ba. Tashi muje gidan Hajiya Hauwa. Naje naga kayan, daga kaduna aka turo mata su jiya, lokacin ina gidan nata. Dandano ta bani na shafa, amma Alhaji, yadda kk san ya zauce. Surutai kuwa daya dinga zubowa, wane yayi kaza, wacce ma tayi kaza. Momy Nafisa ta sheqe da dariya. "kai Nana! Allah ya shiryeki. Tace, kin zata qarya ne? Zomuje in mun dawo kidan ta6a ki gani. Momy tace, ni mijina da bashi da lfy, yaushe zan sake zauta shi. Har suka kai gidan Hajiya Hauwa, Hajiya Nana tana bawa momy Nafisa labarin kyawun kayan. Da ido kurum momy nafisa ta kalli kayan, ta gamsu da batun Hajiya Hauwa. Ta basu kayan, inda daganan suka nufi gidan Na'ima. Cikin sauri ta bude falon lokacin da taji qaran alarm. Domin tana tsoron kar ta sake yin laifi. Rungume momy tayi tana kuka. Kayanta ta soma hadawa bayan sun zauna a bakin gadon Na'imar. Tana fadin momy qafata qafarki. Ba zan sake zama a gidannan ba. Hajiya Nana tace, "ke da Allah natsu! Na'ima ta tsaya tana share hawaye don tasan Hajiya Nana bata daukar raini, tace zonan ki zauna in karanta miki.9⃣0⃣Nan ta soma shiryo abinda suka zo dashi, tace kin zauna kinata faman wasu koke-koke. Duk matar da kk ganta gidan auren ta, karki tsaya tona irin qalubalen da take fuskanta, ko kuma wanda ta fuskanta a baya. Mu kanmu nan da kk gani munsha gwagwarmaya kafin mu kafu a cikin gidajenmu. Ta ciro mata wata kwalba, wannan ki lura dashi da kyau, don duk yafisu tsada kuma ya fisu aiki. Natsu sosai kiji yadda zakiyi amfani da ko wanne. Nan suka karanta mata, tare da bata shawarar yadda zata shanye duk wani wulaqncin da zai mata. Momy tace, kar in sake jin batun tafiya a bakinki, du-du-du, yaushe akayi auren da zakice kin gaji. Salon kija mana dariyar 'yan baqin ciki. Da ma gashi jikin dadynku yaqi, ki jure kawai, kuma kiyi aiki da abinda aka fada miki. Nan dai suka dan kwantar mata da hankali, suka fita, suka tafi. Sha biyu da kusan minti arba'in na dare lokacin ne Abokan Abbas suka sauke shi a gida a buge. Daga bugun qofar falon, zaka san baya cikin hayyacinsa. Na'ima, wadda ta soma barci sbd gajiya da tayi da jiranshi, ta miqe a tsorace ta nufi qofar inda yaketa kiranta. "Na'ima in na shigo sai na ci miki mutunci. Ba zaki budemin qofar ba? Tana budewa yabi ta da kallo tun daga qasa zuwa sama. 'yar mitsilar rigar varci ce a jikinta mai shara-shara. Yana kai idanunsa fuskarta, sai yaga ta rikide masa ta koma mimi. Cikin wata kidima ya rungume Na'ima a zaton ta abubuwan da tayi amfani dasu ne suka fizgeshi. Amma shi mayensa da yake ciki shine ya suranta mashi haka. Sai kurum taji yana cewa, Mimi kin dawo gurina ko? Dama nasan zaki dawo gareni. Samansa sukayi yanata ririta ta, tare da nuna qaunarsa tamkar zai cinyeta. Na'ima tana kukan takaicin yana tare da ita, amma yana ambatar sunan mimi, har lokacin da yayi buqatarsa da ita ya fadi gefe, yana sheqa varcinsa. Canjin rayuwa
8⃣9⃣Hajiya Nana tace, Nafisa in har zaki fitar da kudi gurin shawo kan yaronnan, ba zai zama matsala ba. Nafisa tace, haba Nana kamar baki sanni ba, in ta samu kan yaronnan koni sai na qara haskawa a idon babansu bare ita. Kin sani ban tausayin kudi a gurin kashewa, ynxun dai fada min me za'a yi? Hajiya Nana tace, tsabar katan qamshi za'a hada masu fizgar hankali. Sai yabi ta ko ba don Allah ba. Ba sai ta shafa wani man bilicin ba. Tashi muje gidan Hajiya Hauwa. Naje naga kayan, daga kaduna aka turo mata su jiya, lokacin ina gidan nata. Dandano ta bani na shafa, amma Alhaji, yadda kk san ya zauce. Surutai kuwa daya dinga zubowa, wane yayi kaza, wacce ma tayi kaza. Momy Nafisa ta sheqe da dariya. "kai Nana! Allah ya shiryeki. Tace, kin zata qarya ne? Zomuje in mun dawo kidan ta6a ki gani. Momy tace, ni mijina da bashi da lfy, yaushe zan sake zauta shi. Har suka kai gidan Hajiya Hauwa, Hajiya Nana tana bawa momy Nafisa labarin kyawun kayan. Da ido kurum momy nafisa ta kalli kayan, ta gamsu da batun Hajiya Hauwa. Ta basu kayan, inda daganan suka nufi gidan Na'ima. Cikin sauri ta bude falon lokacin da taji qaran alarm. Domin tana tsoron kar ta sake yin laifi. Rungume momy tayi tana kuka. Kayanta ta soma hadawa bayan sun zauna a bakin gadon Na'imar. Tana fadin momy qafata qafarki. Ba zan sake zama a gidannan ba. Hajiya Nana tace, "ke da Allah natsu! Na'ima ta tsaya tana share hawaye don tasan Hajiya Nana bata daukar raini, tace zonan ki zauna in karanta miki.9⃣0⃣Nan ta soma shiryo abinda suka zo dashi, tace kin zauna kinata faman wasu koke-koke. Duk matar da kk ganta gidan auren ta, karki tsaya tona irin qalubalen da take fuskanta, ko kuma wanda ta fuskanta a baya. Mu kanmu nan da kk gani munsha gwagwarmaya kafin mu kafu a cikin gidajenmu. Ta ciro mata wata kwalba, wannan ki lura dashi da kyau, don duk yafisu tsada kuma ya fisu aiki. Natsu sosai kiji yadda zakiyi amfani da ko wanne. Nan suka karanta mata, tare da bata shawarar yadda zata shanye duk wani wulaqncin da zai mata. Momy tace, kar in sake jin batun tafiya a bakinki, du-du-du, yaushe akayi auren da zakice kin gaji. Salon kija mana dariyar 'yan baqin ciki. Da ma gashi jikin dadynku yaqi, ki jure kawai, kuma kiyi aiki da abinda aka fada miki. Nan dai suka dan kwantar mata da hankali, suka fita, suka tafi. Sha biyu da kusan minti arba'in na dare lokacin ne Abokan Abbas suka sauke shi a gida a buge. Daga bugun qofar falon, zaka san baya cikin hayyacinsa. Na'ima, wadda ta soma barci sbd gajiya da tayi da jiranshi, ta miqe a tsorace ta nufi qofar inda yaketa kiranta. "Na'ima in na shigo sai na ci miki mutunci. Ba zaki budemin qofar ba? Tana budewa yabi ta da kallo tun daga qasa zuwa sama. 'yar mitsilar rigar varci ce a jikinta mai shara-shara. Yana kai idanunsa fuskarta, sai yaga ta rikide masa ta koma mimi. Cikin wata kidima ya rungume Na'ima a zaton ta abubuwan da tayi amfani dasu ne suka fizgeshi. Amma shi mayensa da yake ciki shine ya suranta mashi haka. Sai kurum taji yana cewa, Mimi kin dawo gurina ko? Dama nasan zaki dawo gareni. Samansa sukayi yanata ririta ta, tare da nuna qaunarsa tamkar zai cinyeta. Na'ima tana kukan takaicin yana tare da ita, amma yana ambatar sunan mimi, har lokacin da yayi buqatarsa da ita ya fadi gefe, yana sheqa varcinsa. , amma yana ambatar sunan mimi, har lokacin da yayi buqatarsa da ita ya fadi gefe, yana sheqa varcinsa. Canjin rayuwa 9⃣1⃣Na'ima tayi kuka, iya kuka cikin daren kafin varci yayi gaba da ita. Qarfe takwas ya farka. Halin daya ganshi ciki ya sashi kallon gefensa. Na'ima ya gani kwance cikin irin yanayin daya samu kansa. Ya soma tunanin da yaushe har tazo masa daki akai hakan? Ya dai iya tuno jiya sun samu matsala da Jennifer. Yarinyar daya kawo ta Abuja da kansa ya kama mata gida tana zamansa, ynxun kuma sai ta dinga munafuntarsa. Jiya yaje mata zuwan bazata sai ya sameta ta kawo wani gidan. Yayi mata magana tana fada masa cewa, itafa ba matarsa bace bare ya dinga yi mata dokoki. Yayi mata duka kafin ya baro gurin ta ya nufi club dinsu inda suke hadewa da abokansa suna shaye-shayensu. Ya fada musu halin da yake ciki, nan suka bashi shawarar cewa, yasha mayensa ya manta da ita, ya daina zuwa ta gani in akwai wanda zai mata kwatankwacin abinda yake mata. Sha yayi sosai, don bai ta6a sha irin haka ba. Ko iyayensa basu san yana sha ba, domin baya sha da yawa. Ya kasa komai don haka suka kawoshi gida. Tuna hakan yasa shi gane cewa, maye ne ya suranta masa Na'ima a matsayin Mimi. Tsaki yaja sannan yasa hannu ya daddaka mata duka. Firgigit ta farka tana kallonsa, fuskarsa daure. Yace, tashi ki fita! Tace dama kai ka kawoni bani nazo ba. Ta soma kuka, yace ban tambayeki wani dogon zance ba. Nace dai ki fita. Na'ima ta saka rigar varcinta ta fita da kuka. Ya jima shiru yana takaicin faruwar hakan Tsakanin su, don bai tsara zaiyi hakan da ita ba. Amma sai ya miqe ya nufi bandakinsa.9⃣2⃣Na'ima ma bayan tayi wanka da sallah, ta koma ta zauna tanata tunanin yadda mijinta yake mutuwar son mimi. Kai ita da ta sani, da bata kawo kanta gurin son maso wani ba. Can ta miqe ta nufi kicin, yauma da kanta ta girka abinda zataci kifi ta gasa, irin gashin da Mimi kansa ayi mata. Na'ima ta dan iya girki, domin ko a gidansu tana shiga kicin gurin masu yi musu girki jefi-jefi. Ta gasa bread dinta, zata fito shi kuma zai shigo kicin din, ya kalli tiren hannunta, "bani kiyi wani! Bata musa ba, ta miqa masa don tanason su riqa 'yar hulda ko yaya. Ta koma ta hado wani abin karin. Bayan ta karya ne ta shiga turare gidan da turarukan da aka kawo mata. "Yayi qamshi. Ya fada, duk da ba cikin walwala yayi maganar ba. Taji dadi, kuma taji mamaki. Don haka bayan fitarsa, sai ta dauko sauran abubuwan ta kama amfani dasu. A waya Abbas ya kira Usman, yana bashi labarin abinda ya faru a jiya. Usman yace, kai sakarai me nace maka? Ai na fada maka kawai ka more quruciyar Yarinyar kace a'a, to ynxun don ja nuna ma Jennifer kurenta kawai, ka share ta kaci amarcinka. Abbas yace, banason Yarinyar tayi tunanin cewa, ina sonta ne. Usman yace, ai ba wai zaka sakar mata fuska bane sosai. Ka gane? Abbas yace, shikenan zan kwatanta. Tun daga ranar Na'ima tadan samu sauqin mijinta. Zai sata ta dafa masa abinci, kuma zai kirata shimfidarsa. Amma ba wata soyayya, ko kulawa, ko hira ko sakin fuska. Abin da ta lura amfaninta kenan tayi masa girki, sannan yayi buqatarsa. Wani dare ya kirata a waya taje samansa. Ta sameshi a falo tace gani. Yace ki shiga mana. Kin tsayamin akai, sai kace wani sa'anki. Ranta ya sosu, tace, wai kai kana bani mamaki. Kana nema a gurina amma kayi ta dauremin fuska, kana fadamin abinda kk so. Yace kar ki kawomin raini. Ki wuce muje. Tace, ni varci nakeji, ta juya. Nan take ya kamota, saida ya mammareta, sannan yayi abinda yake so anan falon, ya kuma koreta zuwa dakinta. Zahiri baya sonta, amma abubuwan da take sha, da wanda take qamsasa jikinta suke fizgarsa gareta. Irin Rayuwar da Na'ima ke ciki kenan. Gashi danginsa sun tsane ta, musamman uwarsa wadda tace, Na'ima ta bada ita a gaban Qawayen ta. 9⃣3⃣Zainabu kuwa tana can gidansu, saiga Alhaji ya diro da la'asar sakaliya. Yayi sallama dz innar su Zainabu. Yau kam fuska daure ta fita, da nufin bala'i tare da ita. Sai dai shima tana kallon sa tasan cewa da hakan yazo, kuma in ba sa'a bama shi ya dama ta ya shanye. Kafin tayi magana ya riga ta. Nazo daukar Zainabu ne. Ta lailayo ashar ta maka, sannan tace, Zainabu ba zata koma ba, sai ya sauke dubu ashirin da hudu na asibiti. Yace, tunda dai banyi muku qorafin cikina da kuka zubar ba, to ku bani matata kawai mu tafi. Inna tace, au tanan ka biyo? To ai inason ka sani, tuni muka samu labarin baka son haihuwa, bare kayi wata barazanar banza. Ba zata koma ko ina ba, sai ka canke kudin mutane. Yace, haka kk ce? To kuwa ku shirya cin wani bashin don zaku amsa sammaci, kotu zamu shiga. Ya ciro wayarsa, iroro dake gefe yace, Alhaji ai sai ka kira lauyannan naka tukun, domin duk wanda baisan mutunci ba, gara ayi masa abinda yafi sani. Wato rashin mutuncin ba. Inna tace, ku kira alqali, ba lauya ba. Kai kuma dan kanzagi makwadaici kabi a sannu. Kaje ka nemi sana'a ba maula ba. Iroro yace, ai indai wannan ne sunanmu daya dake, wato 'yan maula. Kwadayinki kuwa ya ninka nawa. Tunda kk miqa 'yarki ga wanda bashi ta za6a ba. Alhaji yace, ko ba haka bama Iroro, ai baka kaita roqo ba, kullum dan aike yana hanya. Tace, kodai me zaku fada, ku fada...... Canjin rayuwa
9⃣4⃣Lokacin ne layin ya shiga wanda yake nema. Alhaji yace, yauwa Barista audu kaji ko? Daga can suka ji murya tace, eh ina jinka Alhaji lawal. Iroro yace, Yauwa Alhaji ai gara kasashi a speaker taji. Alhaji game da zancen da mukayi ne na matata. Ynxun haka ina gidan uwarta ta hanani matata, don haka zanzo mu shigar da qara. Daga can sukaji muryar barista yace, qarar kisan kai zamu shigar, tunda basu da mutunci. Ina ga ko dan gidan da suka mallaka, sai sun daida ba tare da kuma sun kare kansu ba. Don haka kar ka damu. Alhaji yace, shikenan nagode. Ya kalli inna yayi murmushin mugunta, sai mun hadu a kotu. Iroro ya sheqe da dariya. Dana sani tanata bibiyarki. Har sun juya tace, Alhaji ya tsaya. Sannan ya waiwayo. Lafiya? Tace, bari in turo ta ku tafi. Kudin mutane dana aro kuma idan nayi maka Allah ya isa fa? Tare suka sheqe da dariya, Iroro da Alhaji. Iroro yace, shegiya wuya! Alhaji yace, inna ai dama Allah ishasshe ne. Cikin jin haushi, inna tace, ni ba innarka bace don na tabbata ni kaina ka girmeni. Ta juya cikin takaici, suna tayi mata dariya. Zainabu tana kuka, tana komai, ta fito tabi Alhaji, tabar innarta cikin takaici. Wani qarin abin haushi a lokacin suna isa gida, saida yayi buqatarsa ya fita, ya barta tana kuka. Kishiyoyin suka shigo sunayi mata sannu tare da bata haqurin rashin zuwansu. Ko kawo mata abinci sunce Alhaji ne ya hana. Haka Zainabu taci gaba da Rayuwar gidan Alhaji mai cike da matsi da takura, gami da wahala, duk ta qara kodewa, ta fige ta lalace. Kuma ya hana innarta zuwa, kamar yadda itama yace ta daina zuwa gidansu. Innar Zainabu tasha kuka tare da takaici da kuma da na sanin hada Zainabu da Alhaji lawal. 9⃣5⃣Alhaji bashir ya dauki wayarsa ya soma neman layin Abba. A ringing na biyu Abba ya dauka, ya kara a kunne yana fadin dad ina kwana? Bayan sun gaisa Alhajin yace, inason kazo yau ka tafi dani katsina. Abba yace, amma lfy dai ko dad? Alhaji yace, lfy lau, inason ganin mahaifiyarku ne, gashi har ynxun bana jin dadin jikina. Abba yace, shikenan daddy, sai nazo. Qarfe biyu Abba ya sauka garin Abuja. Tuni daddy ya turo direba yana jiransa. Suka nufi maitama. Momy Nafisa batasan da batun ba, saidai taga Abba. Ya gaisheta tare da tambayar jikin daddyn, tace da sauqi. Lokacin data shiga don sanarda Alhajin zuwan Abba, sai yace ta hada masa wasu kayansa na ciki da kuma wasu takardunsa. Tace, ina zaka Alhaji? Yace katsina, nine nace wa Abba yazo ya tafi dani. Tace, ba zaka bari kadan qara samun sauqi ba? Yace, karki damu, can ma zanci gaba da ganin likita. Shida daidai suka sauka a filin jirgin sama. Sun samu direba na jiransu, domin kafin su taso daga Abuja, Alhaji yasa Abba ya kira direban hajiya sauda, batasan da zuwan Alhajin ba tana zaune a falo tana ba Zainab magani, don yau kwananta uku babu lfy, kullum suna hanyar asibiti. Sai kurum taji Sallamar su. Bata zaci Alhaji bane, don muryar Abba irin ta Alhajin ce. Saida taji yaran suna Oyoyo daddy. Da sauri dago tace, sannu da zuwa Alhaji. Ta miqe cikin sauri bayan ta kwantar da Zainab, tace, Alhaji baka sanar dani cewa kana tafe ba. Yace karki damu tu tunda mun iso lfy. Sun gaisa da Abba sannan ya nufi gidansa. Canjin rayuwa
9⃣6⃣Hajiya kuwa ta dauki jakarsa kuma ya bita zuwa daki. Sannan ta dawo kusa dashi. Ya kamata kayi wanka ko? Ya kalleta, zan yi wankannan kuwa? Barci nakeji kuma inajin sanyi, sai inga kamar in nayi wankannan zazza6i zai iya rufeni. Ta cire masa riga, sai singileti. Ya kwanta akan gado, ta zauna bakin gadon. Kasha magungunan ka kuwa? Yace, nasha, sai dai akwai na ynxun qarfe shida, amma sai zan kwanta sannan zan sha. Tace, a'a nidai kasha ynxun, yana da kyau kabi dokar likita. Ynxun tashi zakayi in taimaka maka kayi wanka, kasha magani kayi sallah don kaga magriba ta kusa. Ya tsura mata ido, "sauda nayi miki laifi ko? Ta kama hannunsa, ni baka min laifi ba, to muje kayi? Yace, to sauda muje. Kafin yayi sallah har ta shiga kicin da kanta tayi masa tuwon alkama miyar alayyaho. Yana zaune kan sallayarsa yana istigfari. Can qasan zuciyarsa kuwa tunanin mimi takeyi. Zuwa ynxun ya gama tabbatar ma kansa cewa, son da yake wa mimi ya zarta tunaninsa, kuma ba zai ta6a son wani cikin 'ya'yansa kamarta ba. Amma dole ya jure sbd ya samu ya ida nufinsa don ta samu canjin rayuwa. Wasu hawaye suka soma zubo masa. Sam baiji Sallamar Hajiya sauda ba, har saida ta dafa shi, sannan ta tsugunna tare da aje abincin dake hannunta dayan. Duk da saurin da yayi ya share hawayen sa, saida tace "na shiga ukuna! Alhaji kukan me kkyi? Cikin sarqaqqiyar murya yace, ba kuka nake ba. Sauda ta zauna dirshan akan sallayar, cikin tashin hankali tace, haba Alhaji. Shekarunmu nawa ban ta6a ganin hawayen ka ba sai yau. Dole akwai wani babban al'amari.9⃣7⃣Ta kama hannunsa. "Na roqeka karka 6oyemin komai. Idanunta suka cika da hawaye yadan matsa hannunta, "sauda karki tada hankalinki ba wani abu bane. Sannan inason don Allah ki yafe min nasan cewa, na sa6a miki da yawa. "qara firgita tayi, gani takeyi tamkar Alhajin mutuwa zaiyi ya barta. Sai ta soma kuka. Jikinsa ya janyo ta. Haba sauda, mene ne na kuka kuma? Tace Alhaji don Allah karka tafi ka barni. In kuma wata matsala ce tasa zubar hawayen, don Allah ka fadamin. Yace, sauda bazan 6oye miki ba, ina kuka ne sbd mimi. Saida na rabu da mimi nasan cewa, inayi mata mugun son da bansan adadinsa ba. Tunanin ta ne ya hana sugar na sauka, na sani. Ya dago fuskarta mai dauke da mamaki. Ta kalleshi cikin ido, "sbd mimi kk cikin wannan tashin hankali? Yace, eh sauda. Tace to me zai hana ka tashi muje gurinta ynxun a asibiti? Yace, lokaci baiyi ba. Sauda ynxun zan sanar dake dalilina na aura wa mimi talaka. In kince ban kyauta ba, to zanje gurinta ynxun, in kuma raba auren ta, sannan in fita da ita wajen qasarnan don nema mata lfy. Hajiya sauda tace, kafin nan bari in baka abinci da kuma magani. Tunda munyi sallar isha'i, sai inje in sallami yara na inzo in saurareka har zuwa asubahi. Yayi guntun murmushi. Ta janyo tiren, ta zuba tuwon a cikin plate, tasa a gabansa. "in baka a baki?" yadan karkatar da kai, "bana tuna shekaru na matsawar ina gabanki. Ki bani zanci da hannayenki masu albarka.9⃣8⃣Ta soma bashi tuwon, bayan yayi bissimillah. Bai iya tuna lokacin da yaci abinci kamar na yau ba sam. Tana bashi tana masa hira har yayi qat. Ta bashi magani, sannan ta jashi da wata hirar, tunda ta gano maganar Mimi ce damuwarsa. Batun 'yan uwanta ta dauko masa na auren 'ya'yan sa'ade 'yar uwarta, da irin gudummuwar da ta basu. Yace, nima zan bada tawa. Kullum inason in nazo inje in gaida ya Dikko sai abubuwa susha min kai. "sauda tace, har na gaji dayi mata qaryar cewa, kana gaida ta. Kwanaki tazo tayi sati hudu. Har yaya jabiru yazo suka tafi baka zo ba. Yace, wannan karan zan huta a gurinki sauda, zanje in ganta jabiru dai ya hanamu ita, da ynxun tana nan. Sauda tace, ai bazai yarda ba shiyasa na haqura. Ya qura mata ido na 'yan kakwanni. Ta shafi kumatunsa, "wai wannan kallon fa? Yace, karki tsorata sauda. Nasan tsoranki, kar in mutu in barki ko? Ta matsa hannunsa dake cikin nata. "wlh tsoron kenan Alhaji. Ko tuna hakan nayi ina zubar da Hawaye bare ace ta kasance. Ya sauke ajiyar zuciya. "sauda ni kaina banason in mutu ba tare da na cika burina ba. Burina in saku cikin farin ciki bayan mutuwa. Tace, wace irin mutuwa zakayi inyi farin ciki in ba ni na riga ka ba? Burina in rigaka. Yace, a'a sauda, ni ya dace in tafi in barki, domin 'ya'yanki su samu tarbiyyar ki. Ko mimi inayi mata takaicin rashin samun tarbiyyarki. Ma'anar in na mutu kuyi farin ciki shine, in daidaita tsakani na da Allah da kuma tsakani na da iyalina da sauran mutane. Canjin rayuwa