Kenza eBookz

Captain ahmad junaid complete - Chapter 10

Captain ahmad junaid complete - Chapter 10

Captain ahmad junaid complete Chapter 10: Captain ahmad junaid complete Chapter 10. Kwata kwata Junaid bai runtsa daren ranan ba ya rasa dalili, sae dai…

3,580 words

Kwata kwata Junaid bai runtsa daren ranan ba ya rasa dalili, sae dai yafi danganta haka da tausayin baiwar Allahn da yake, Washegari Wednesday bai yi wani breakfast din kirki ba ya fita as early as 7, tun daren jiya El-Ameen ke kiransa baya dauka, a hankali yake driving ya kalli wrist watch dinsa yaga bakwae da minti goma, ganin yana da sauran time yasa shi nufan gidan El-Ameen, a waje yayi parking ya shiga gidan, kwance ya tarda El-Ameen a parlor yana bacci kan 3sitter, Mama kuma na kitchen, ya kusa second ashirin tsaye yana kallonsa sannan ya tabe baki yyi hanyar stairs, a hankali ya tura kofan dakin ya ganta kwance kan gado cikin bargo, ya karasa cikin dakin yana kallon empty roban drip din da aka cire mata, gefenta ya tsaya ya yaye bargon jikinta, ya tsura ma fuskarta ido, Ya fi minti biyu yana kallonta tana bacci, ya daura hannunsa a hankali a forehead dinta ya ji da d'an dumi, bude ido tayi da sauri ta mike xaune, kallonsa take ko kiftawa bata yi, lkci daya ta saki wani kara ta shiga komawa baya tana ihu da karfi, ya koma baya da mamaki yana kallonta, El-Ameen ne ya shigo dakin da sauri, ya tsaya daga bakin kofa ganin Junaid a dakin, sauka tayi daga kan gadon tayi kofa da gudu xata fita tana ihu har lkcn, El-Ameen ya fixgota yace "Keeh Meye haka!" Ihu ta dinga yi xata kwace kanta tana yi tana waigan Junaid, El-Ameen ya kalli Junaid yace "Ohhh it seems Khakin nan naka ke tsoratata fa Captain" Junaid ya juya yana kallon kansa a madubi, farin well ironed navy shirt ne jikinsa, well tucked in cikin navy blue trousers dinsa, sae hat dinsa a kai, sae black socks din dake kafarsa don ya cire takalmin a waje, juyawa yayi ya fice daga dakin, sai a sannan tayi tsit sai dai har lkcn jikinta rawa yake tayi lamo jikin El-Ameen, El-Ameen yayi dariya yace "Toh fah" xaunar da ita yayi gefen gado yana kallonta yace "That's intresting! kina tsoran soldiers kenan!" Kauda kai tayi ta xamo kasa ta kwanta, mikewa yayi yana kallon agogo, da sauri ya fita dakin ya sauko parlor sai dai bai ga junaid ba, ya kalli Mama dake shara yace "Mama junaid din ya tafi ne?" ta washe baki tace "Anya ya tafi, kaga makulli can ya ajiye kan kujera, ashe sojan ruwa ne yau na gansa da khaki" Dariya El-Ameen yayi yace "Ehh Navy ne" tace "Allah sarki, khakin sun masa kyau" kallon Makullin yayi yaga ta motarsa ce, ya d'an tabe baki ya karasa ya dauka yace "D'an rainin wayo" fita yayi don ganin ko motar tasa na waje yaga bbu motar makullin kawai ya kawo masa, girgixa kai yayi ya koma cikin gidan. Junaid na kwance parlor da yamma b4 magrib yana danne dannen waya, khadija ta shigo parlorn, Karasowa tayi ta xauna gefensa tace "Ina yini ya A'jay?" Yace "Lfya lau, kar ma ki fara tambayata kudi don bani da" dariya tayi tace "Kai yayana" sai kuma ta d'an yi shiru, a hankali tace "Kasan me yaya, karka ci abincin gidan nan yau, just go out and get somethin to eat ae kasan yanxu an daina girki daban daban koh" yana kallonta yace "Why!" Ta daga kafada tace "Just, beside ma porridge ne kuma ae bama ka ci" mikewa tayi tace ina xuwa, ta fice daga parlon, ya bi ta da kallo yana murmushi. Wayarsa ne ya soma ring ya duba ya ga El-Ameen ke kiransa, sai da ya kusa katsewa sannan ya daga ya kai kunne bai ce komai ba, daga daya bangaren El-Ameen yace "You try fa captain, nine ban san dadin gidanmu ba ko, how on earth xaka dinga bari na ni kadai ina fama da patient din ka?" Junaid ya tabe baki yace "Naga tana tsorona ne, kai ne bata tsoro dat's why I decided not to show up today" El-Ameen yayi tsaki yace "Didn't you see dat uniform dinka ke scare dinta, wear mofty while coming always, yanxu dai I will text u some drugs da xaka siyo idan kana tahowa, and ka siyo mata fruits taki cin abinci" Junaid ya kuma tabe baki ya katse wayar ya ajiye. Kallon agogo yayi yaga an kusa magrib, ya mike ya shiga toilet ya dauro alwala sannan ya fito ya dau makullin motarsa da Atm sae wayarsa ya fita ya rufe kofarsa. Bangaren Mumy ya fara shiga, yana kallon fatima dake guga yace "Mumy fa?" Tace "tana bayi" juyawa yayi ya tafi masallaci, ana idar da sllh ya dawo gida, Mumy da fitowarta daga kitchen kenan tace "Ga abincin ka a dinning can" kallon dinning din yayi yace "Porridge?" Mumy tace "Shi kake so?" Girgixa mata kai yayi yace "No khadija ce tace min porridge aka yi" Mumy tace "Ehh amma kai na maka girkin ka daban" yace "Toh nagode Mum, but xan d'an fita yanxu idan na dawo xan ci" tace "Fita kuma? Ina xa ka?" Yayi kasa da murya yace "xan d'an raka El-Ameen wani gun ne, daga can xa mu je kallon kwallo" ta tabe baki tace "Xa dai ku je tadi koh?" Dariya yayi yace "A'a fa Mumy" murmushi tayi tace "Toh kar dai ka wuce 8:30 a waje, ka ma shiga gun abbanka kuwa" yace "Ehh daxu na shiga" daga haka ya juya xai fita, Humainah tace "Ya Ahmad xan raka ka" yace " Nooo" daga haka ya fice daga parlon, Mumy tayi dariya tace "Ki bari ran lahadi ya xaga da ke katsina" tayi murmushi tace "Toh Mumy, ko yace A'a kiyi masa masifa sai ya kai ni" sae da junaid ya fara siyan abubuwan da El-Ameen ya ce masa ya siya ready made din fura da nono sannan ya nufi gidan, Mama kadai ce kwance parlor kan darduma, ya gaisheta ya bata nata fruits din da fura tayi ta masa Godiya yayi murmushi kawai ya haura sama. Xaune ya samu El-Ameen yana danna laptop, ita kuma tana tsaye can jikin bango ta jingina, El-Ameen yace "Sae da ka ga dama kenan" Junaid bai tanka sa ba ya ajiye ledan hannunsa ya xauna gefen gado, El-Ameen ya ya juya yana kallonta yace "Ba dai baki ji ba, wait in tashi xa ki ga abinda xan maki a wajen nan" Junaid ya kallesa kafin ya girgixa kai a xuciyarsa yace ae Kaine mahaukacin ma, takowa tayi ta karaso kusa da ledan da junaid ya ajiye ta durkusa, El-Ameen ya daka mata tsawa yace "c'mon ance maki naki ne" mikewa tayi da sauri, Junaid ya dauki ledan ya mika mata ta karba, El-Ameen ya mike tana ganin haka ta sake ledan ta koma jikin bangon da take, dariya yayi yana kallonta yace "kai! Yarinyar nan ba dai tsoro ba" shi dai Junaid ko kallonsa bai yi ba, Karasowa yayi ya dau ledan ya bude ya fito da bunch din Ayaba ya mika mata, ta karaso da sauri ta karba, xata juya ya fixgota ya xaunar da ita gabansa, da kansa ya shiga bude mata ayabar yana mika mata, tana karba tana ci, ana uku ne taki ci, ta kalli Junaid dake danna wayarsa sae dae gaba daya hankalinsa na kansu, ta matsa kusa da shi a hankali ta kama hannunsa ta sa mashi Ayaban, tabe baki El-Ameen yyi ya kuma bare mata wani ta karba ta kuma kama hannun Junaid ta basa, El-ameen ya hade rai ya kuma bare wani ya bata xata ba Junaid yayi mata tsawa, a tsorace ta juyo, yace "I will knock you yanxu, ina shan wahala ina bare maki abu kina kyauta da shi, da xan bar ki yanxu da peel din xaki hade ki cinye," kafa masa manyan idonta tayi ko kiftawa bata yi, junaid yayi murmushi ya girgixa kai, wayar El-Ameen ne ya fara ring ya dauka, xaro ido yayi ganin Abbansa ne ke kiransa, ya kalli Junaid yace "Kasan kuwa ban je clinic throughout yau ba" ko kallonsa Junaid bai yi ba, ya daga a hankali ya kai wayar kunne, daga daya bangaren Abban nasa yace "ka taho clinic ka sameni yanxu Ahmad, clear?" yayi kasa da kai yace "Toh Abba" daga haka ya ajiye wayar yana kallon Junaid yace "Look! Xan je clinic yanxun in dawo, wait har sai na dawo don't go plss, kaga bata da lafiya karfin hali kawae gareta she just finished vomiting kafin ka shigo, dats why nake nan har yanxu, am giving her her drugs before leaving yanxu" Junaid ya xaro ido yace "Idan Mumy ta kira ni fa, beside 8:30 tace in dawo gida, nd this is almost 8 o clock" Kallonsa El-Ameen ya tsaya yi sae kuma ya girgixa kai yace "Tashi ka tafi toh, wato nine bansan darajan parent dina ba koh Captain, nine na iya karya kai baka iya ba, you know am doing this goddam job for ur sake if you provoke me wllh sae in fasa kawai ka kaita asibiti, kullum safiya sai na xo nan sbda drugs dinta da injections, at mid day ma I have to leave whatever i am doing in xo nan bata magani, haka da yamma ma, sannan da daddare bana barin gidan nan sai kusan sha daya, Haba!" kallonsa kawae junaid yake bai ce komai ba, tsaki yayi ya mike ya dauko maganinta da cup yayi diluting da ruwa ya xauna kusa da ita xai bata tana ganin haka ta fara kokarin mikewa ya fixgota, bbu gardama ta shanye maganin duk jikinta na rawa, ya mike ya dau makulli da wayarsa yana kallon junaid on a serious note yace "Look! In har ka bar gidan nan kafin in dawo wllh wllh kaji rantsuwan musulmi koh, toh sai dai ka san yanda da xakayi da yarinyar nan don ba fina biyayya kayi ba, I am taking my hands of her case" daga haka ya fice daga dakin, Junaid da ya bi sa da kallo yana murmushi snn ya juya yana kallonta, yatsine fuska kawae take, ta matso kusa da shi ta mika masa Ayabar hannunta, a hankali ya sauko daga kan gadon ya karba ya kai mata baki yana kallonta yace "Eat!" Ta kauda kai da sauri, kallon Ayabar yake yana son ci amma ya kasa, ajiyewa yayi ya dau Apple ya mika mata, Kin karba tayi, yayi murmushi ya ajiye shi ma, a hankali ta kwanta nan gefensa, ya tsura mata ido, kamar warce aka tsikara ta mike xaune da sauri, ya koma baya yana kallonta.

*Haske writers Association* ⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓

_By Khaleesat Haiydar_✍🏻

18.....

Amai ta shiga kwararowa a gurin, ya mike yana kallonta har ta gama ta koma xata kwanta yayi saurin riketa, kara ta saki ta turasa da karfi xata kwanta gun aman yaki saketa, nan ta shiga kokuwa da shi ita sai ta kwanta, ya rike ta gam yace "Wait Jasmine..." ta kuma sakin wani ihun da ya tsorata shi, ae da ta turasa sai da ya kusa faduwa ba shiri ya saketa, ta yi kwanciyarta nan kasa, ya sauke ajiyar xuciya ya nufi toilet, mop da bucket ya dauko ya dawo dakin, rasa ta inda xae fara gyara wajen aman yayi, ya ajiye ya fita don kira Mama jummai, tare suka shigo dakin, ta karaso kusa da ita da sauri cike da tausayinta ta dagota tana mata sannu, ihu ta sakar mata ita ma ta kwace kanta ba shiri ta saketa ta koma ta kwanta tana mayar da numfashi, girgixa kai mama tayi ta mike ta shiga gyara wajen, tana gamawa ta kuma gwada d'aga ta a kasan tiles din still taki tashi, kyaleta tayi ta fita, Junaid ya mike ya shiga bayi ya dauro alwala ya fito jin kiran isha, a nan dakin yayi sallah, yana xaune kan darduma ya ga tana juye juye a kasan da take kwance. Kallonta kawae yake cike da tausayinta don da ganinta kasan tana jin jiki, ta mike xaune a hankali ta dawo inda yake tana kallonsa ta kwanta kusa da shi, dagota yayi murya can kasa yace "Sorry Jasmine" lumshe ido tayi ta kwanta nan kusa da shi lkci daya bacci ya dauketa, ya mike ya koma can jikin gado ya xauna, har Karfe tara El-Ameen bai dawo ba, duk ya kagu ya dawo ya wuce kafin Mumy fa kirasa, tara da rabi kiran Mumy ya shigo wayarsa, k'asa d'agawa yayi don bai ma san me xai ce mata ba har sai da ya kusa katsewa sannan ya daga da sauri, Mumy tace "Where are you Ahmad" kallon dakin yayi kafin a hankali yace "Mumy, am am with El-Ameen" strictly tace "You are very stupid, within the next 10 to 15 mins ka tabbatar kana cikin gida if not xaka ga bacin raina, in kuma kaya ku ka kasa a titi ku ke saidawa da daddaren nan xaka gaya min" kamar mai shirin kuka yace "Kiyi hakuri Mumy xan dawo" katse wayar tayi, ya rike kansa, layin El-Ameen ya shiga nema yana ta ring bai d'aga ba, ya lumshe ido ya jingina jikin gado, he just don't know wat to do, haka yayi ta kiran El-Ameen bai daga ba, Shivering yaga tana yi daga kwancen da take kan darduma, ya mike ya karasa inda take ya dago ta ta bude ido da sauri, kan gadon dakin ya kwantar da ita ya rufa mata bargo, ta cire xata sakko ya riketa da damuwa yace "You are shivering Jasmine" ba shiri ya saketa a dalilin kara me karfi da tayi masa a kai, ta sauka nan kasan dakin ta kuma kwanciya. Har goma El-Ameen bai dawo ba, Junaid ya rasa me ke masa dadi shi da bae taba yi ma Mumy musu ba, yasan kuma fushi tayi shi yasa bata kara kira ba, da yayi niyar tafiya sae ya tuna abinda El-Ameen yace masa, ya kuma san xai aikata, shine xaune har sha daya, Mama jummai ta shigo tace "Kai xaka kwana yau a nan kenan junaid?" D'an murmushi yayi yace "A'a ina jiran El-Ameen ne yace xai dawo" tace "Toh tafi daki can ka kwanta inda yake kwana xan kula da ita" Junaid yace "yana kwana nan ne?" Tace "Eh wani lkcn yana kwana can dakin don akwai alluran da yake mata da sassafe, toh duk ran da xai mata alluran a nan yake kwana, ni kuma tare muke kwana da ita saboda shiga bayi da daddare" Junaid ya gyada kai yace "Bari in jira sa a nan Mama ni ba kwana xan yi ba ai" tace "Toh" sannan ta juya ta fita. Lumshe ido yayi ya jinginar da kansa jikin gado, wani bacci ya ji na fixgarsa ya bude ido yana kallon agogo yaga sha biyu, kallonta yayi ya ga ta canxa position, a hankali ya mike ya isa inda take xai dagata ta bude ido da sauri, birginawa tayi ta bar gun ta juya masa baya, ya mike ya koma ya xauna kan gadon, xuwa yanxu kam ya gama sanin iskanci El-Ameen yayi masa, dole ko yaki ko ya so a nan xai kwana hakan ba karamin bata masa rai yayi ba, sha biyu da rabi ya kuma mikewa jin yana jin bacci sosai ya bude closet ya dau bargon da ya gani ya koma daya side din gadon ya shimfida a kasa ya kwanta dai dai yanda xai dinga ganinta, nan da nan bacci ya daukesa. Bude ido yayi jin an bude kofa don ko k'adan bashi da nauyin bacci, El-Ameen ne ya shigo dakin yana ganinsa ya dauke kai, kallo daya El-Ameen yayi masa yana murmushi bai ma san idonsa biyu ba ya karasa gun da take kwance a kasa, durkusawa yayi gabanta ya dagota, ta bude ido da sauri, lumshe ido yayi jin xafin jikinta a hankali yace "Sorry, Jewel" xata koma ta kwanta yaki saketa, ya mike ya dauketa ya nufi kan gado da ita ya kwantar, kokarin sauka ta shiga yi da kyar, ya hade rai yace "No" bata kuma yunkurin saukan ba, ya gyara mata kwanciya ya mike ya shiga bayi, duk wannan abun Junaid na kallonsu, ya dawo dakin rike da bowl din ruwan sanyi ya bude closet ya ciro towel karami da babba ya saka karamin cikin ruwan bowl din ya dawo kan gadon ya ajiye bowl din kan bedside drawer, ya dagota yana kallonta don idonta biyu, ya dawo da bowl din ruwan gefensa ya matse ruwan towel din a hankali yana goge mata forehead dinta da shi, kara ta saki xata sauka ya hade rai yace "Wait!" Bata kuma yunkurin saukan ba, haka ya ci gaba da goge jikinta da yayi xafi sosai da towel din yana mata sorry, mikewa Junaid yayi, El-Ameen ya juya da sauri ya kallesa sannan yayi saurin rufeta da bargo yace "Ohh you weren't sleeping dama" Junaid bai tanka sa ba ya dauke bargon da ya shimfida kasa ya mayar cikin closet, El-Ameen ya tabe baki yace "Ni ban ma yi tunanin xan dawo in same ka ba Mumy's boy, theatre muka shiga da Abba and we came out few minutes ago, saboda nasan condition din patient dinka shi yasa na fito cikin daren nan, I ought to...." jin anyi banging kofa El-Ameen ya kalli kofar da sauri don dama yana magana ne yana matse towel a ruwa, murmushi yayi ganin ficewa yayi, ya ci gaba da abinda yake, har sai da yayi make sure temperature dinta ya dawo dai dai, still yayi ganin hawaye idonta, ya sunkuya a hankali ya goge mata fuskar yace "Am sorry Jewel, am only helping" sauka yayi daga kan gadon yaje ya xubar da ruwan ya shanya towel din a bayi ya fito, bacci ya sameta tana yi a yanda ya barta, ya gyara mata kwanciya sannan ya hada allura yayi mata da kyar don a tsorace ta farka ta fara kokuwa da shi, sai da yaga ta koma bacci sannan ya fita dakin ya shiga master bedroom duk a tunaninsa xae tarda junaid nan, sae yaga otherwise, tabe baki yayi sanin yana parlor knn, ya shiga toilet yayi wanka ya fito ya canxa kaya yayi kwanciyarsa dakin, sai dai before dawn yaje dubata ya fi sau goma duk da a shigowarsa na uku ya tarda mama jummai a dakin, Karfe biyar da minti arba'in ya sauko parlor ya tarda Junaid xaune kan darduma, xaunawa yayi kan kujera yana kallonsa yace "A parlor ka kwana kenan?" Junaid ba tare da ya kallesa ba yace "Yea!" El-Ameen yace "Ohk, gud morning, yanxu dai you need to transfer some money into my account xuwa later akwae drugs din da na mata prescribing, and you know wat? Suna da tsada gaskiya or I shud just text you their names, tell you where to get them, kaje da kanka ka siyo, if you need my assistance let me know" El-Ameen ya kare maganar yana d'aga kafada, Junaid ya mike ya dauke darduman da yayi sallah yace "nawa ne kudin?" El-Ameen yace "100 nd 50k will be enough" Junaid yace "Alryt" ajiye darduman yayi kan kujera ya kalli El-Ameen yace "Na tafi, I will transfer it later in the day" bai jira cewarsa ba ya nufi kofa ya fice daga parlorn, makullin motarsa ya ciro a aljihu ya fita waje inda ya ajiye motarsa ya bude ya shiga ya kama hanyar gida, driving kawae yake amma gaba daya hankalinsa ba ya tare da shi, bai san yanda xa su kwashe da Mumy ba, toh ina ma xai ce mata ya je, gidansu El-Ameen? No yasan xata iya kiran Ummi, murmushi yayi yana tunanin randa xae samu freedom, don ya fara damunsa yanxu on like before, a waje yayi parking ya fito, gabansa ne ya fadi ganin Abbansa alamar daga masallaci yake, da kyar ya ja kafa ya isa gun gate ganin Abba ya tsaya har ya risina xai gaida Abba, Abba ya dakatar da shi yace "Daga ina kake?" Yayi kasa da kai zai yi magana Abba ya juya ya shiga cikin compound, bin bayansa yayi har suka isa part din Abba, Hajiya ke ta goge goge a parlon, Abba ya xauna kujera yana kallon Junaid, a hankali ya xauna kasa ya juya yana kallon Hajiya dake kallonsa da d'an murmushi mai wuyar fassara a fuskarta yace "Ina kwana Hajiya" tace "Lfya lau Ahmad" sunkuyar da kai yayi, Abba yace "Daga ina kake Ahmad?" A hankali yace "Tare muke da El-Ameen Abba" Abba yace "Tare a ina?" Hajiya ta dawo cikin parlon tana girgixa kai tace "kwata kwata ni hankalina bai kwanta da abotansa da yaron nan wai El-Ameen ba, yaron da bai da nutsuwa ko maganan iyayensa bai ji, kusan duk dare sai ya shigo ya fita da shi, Ahmad baxae dawo gidan nan sai kusan sha biyu wani lokacin har daya, duk ina lura da yake ni ba mai nauyin bacci bace ka sani Alhaji, to amma kar mutum yayi magana ace hassada ko kuma ace don ba d'an sa bane, amma kwata kwata Ahmad ya sauya hali a gidan nan, jiya wllh wllh khadija ca tayi min mace ta gani a motarsa da magariban nan da ya fita, to ina yaje yake dawowa yanxu, kuma duk Hajiya Amina tana ganin abinda yake baxata ce komai ba saboda ta dauki son duniya ta daura ma yaro, meye amfanin haka, in ma aure yake so ba sai yayi magana ba, ae ba wae bai isa bane" tunda ta fara magana Junaid ya kafeta da ido ko kiftawa bai yi, Abba kuwa sai kallonsa yake bacin rai karara a fuskarsa.

*Haske writers Association* ⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓

_By Khaleesat Haiydar_✍🏻

19.....

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull