Captain ahmad junaid complete - Chapter 15
Captain ahmad junaid complete Chapter 15: Captain ahmad junaid complete Chapter 15. Mikewa faisal yayi ya d'aga kafada ya nufi kofa, da sauri Sumayya ta…
3,535 words
Mikewa faisal yayi ya d'aga kafada ya nufi kofa, da sauri Sumayya ta bar jikin kofar ta shige dakinta rike da farantin jin takunsa, faisal yayi ma Ummi dake parlor har lokacin sallama ya fita daga gidan, El-ameen ya koma ya kwanta tare da lumshe idonsa. Suhaima ce ta shigo parlor rike da waya tana kallon Hajiyarsu tace "Hajiyarmu yanxu sumayya ta kira ni...." Da sauri ta kalli khadija da ke kwance parlon sai kawai ta juya ta koma daki, Hajiya ta mike ta bi bayanta, khadija ta tabe baki ta ci gaba da danna wayarta. Junaid na kwance parlon Mumy that same day, idonsa lumshe kamar me bacci kamar wanda ya tuna abu ya mike xaune yana kallon wayarsa ya dauka yayi dialing number bugu uku aka d'aga, bayan sakwanni 20 jin ba ace komai ba daya bangaren yace "Uhn how you?" Jin an ki cewa komai still, yace "sai in kashe wayata ne" kamar xata yi kuka tace "Toh ina ruwana ni nace ka kira" murmushi yayi yace "Ohk, sai anjima" da sauri tace "Noo Ya Ahmad don Allah ka xo ka dauke ni, gida nake son dawowa" yace "Anki, xaman ki a can ya fi maki, sai kiyi ta neman fitina da Jawahir!" Katse wayar yayi ya ajiye yana murmushi, can ya mike ya fita ya koma part dinsa don tun da ya dawo daga gun faisal yake kwance parlon Mumy ko uniform bai cire ba, yana bedroom ya fito daga wanka yana shiryawa yaji an murda kofar parlor, juyawa yayi yana kallon kofar dakin har aka bude, faisal ya shigo da sallama, Junaid ya sauke ajiyar xuciya yace "Glad you came" faisal ya karaso ya zauna gefen gado yace "ka jira har El-ameen ya sauko Captain, yayi sama da yawa, beside ni ban...." Da sauri Junaid yace "Xuwa kayi ka samesa?" Faisal ya d'aga masa gira, Junaid yace "Ohhh shit! Why? Meyasa xaka min haka, why did you go faisal, gaskiya ka bata min rai, who's he da yake tunanin without him Allah baxai bata lafiya ba, shi din banxa, bana bukatansa a lamari na kuma, bana bukata...." Faisal yayi murmushi yana girgixa kai yace "Haka kawai in sa baki daga karshe in ji kunya, da dai ban san ku bane, duk ku yi ku gama" Junaid yayi tsaki ya ci gaba da shirin sa, yana gamawa ya juya yana kallon faisal yace "Ka sama min psychiatry din ne frnd?" Faisal yace "Psychiatry me kyau sai Abeokuta or Lagos, but I will advice you to take haka to na Abeokutan ya fi, Neuro Psychiatric hospital Aro" Junaid yace "Har Ogun state? No plss samo min a nan north" faisal yace "Toh ai na can yafi komai ne, ga qualified neurologist..." Junaid ya xauna gefen gadon yace "Abeokuta kuma? Or kasan me I shud just look for a private neurologist for her...." Faisal yayi murmushi yace "That's money frnd, hospital ya fi!" Junaid yayi shiru, sai kuma ya shafa kansa a hankali yace "Allah xai rufa asiri, just get me a qualify one" faisal yace "ohkk dats not a problem, duk dai yanda ta yiwu in na gidan in na hospital," Junaid ya gyada kai yace "Toh shikenan" faisal yace "Sai da abu ya kwabe maku sannan xa a wani xo a sameni.... Ni kallonku kawai nake kai da El," Junaid yayi murmushi ya mike yace "Kaga xan kai mata fruits can gidan yanxu, muje part din mumy sai inyi kamar rakaka xan yi" faisal yayi dariya yace "Plss do and get ur freedom captain! You are getting old fa Mumys boy!" Junaid yace "Uhum kaga in tafiya xaka yi ka taso mu tafi!" Mikewa faisal yayi ya bi bayansa yana dariya, suka nufi part din Mumy, faisal yayi mata sallama, Junaid na shafa kai yace "Mumy bari in rakasa!" Mumy tace "Toh sai ka dawo" fita suka yi faisal na dariya, Suhaima dake tsaye bakin tap ta bi su da kallo tana tunanin xancen da Sumayya ta mata a waya, ajiyar xuciya ta sauke tana tunanin ta ina xata fara binciken da Hajiya ta sa ta, wai Mahaukaciya, tab, har Allah Allah take washegari yayi! Suna fita gidan Junaid ya kalli faisal yace "Kaga ban fito da mota ba, da taka xa mu je can gidan daga can sai ka ga Mahaukaciyar," faisal ya buda ido yace "Da take neman hada aminai biyu ba!" Junaid ya tabe baki yace "No bata hada mu ba, frndship din ne ya xo karshe dama" dariya kawai faisal yake, Junaid ya karbi makullin hannunsa ya shiga motar ya tada. A hanya suka siya fruits sannan suka kama hanyar gidan El-ameen, mama na sharan parlon suka shigo, ta mike tana masu sannu da xuwa, Junaid sai kalle kallen inda xai ganta yake, mama jummai ta lura da hakan ta nuna masa gefensu tace "Ga ta can" juyawa yayi ya ganta xaune ta jingina da bango ta d'an dukar da kai alamar bacci take, xai yi magana Mama jummai tace "Babu yanda banyi da ita ta bar wajen nan ba ta ki, kuma ta ki kwanciya, ni dai na rasa gane kan baiwar Allahn nan, ko abinci taki ci, dama Aminu kadai yasan kanta, rashin cin abincin nan ba karamin daga min hankali yake ba, toh ko dai bata da lafiya ne" Junaid ya tabe baki bai ce komai ba, faisal kuwa kallonta kawai yake, duk da ba ganin fuskarta yake ba, Junaid ya kallesa sannan ya karasa kusa da ita ya duka kamar me rada yanda bbu wanda xai ji sa a hankali yace "Jasmine!" D'ago kanta tayi da sauri ta bude ido tana kallonsa, a hankali faisal ya dinga komawa baya yana kallonta ko kiftawa bai yi har ya isa jikin kofa bai sani ba, kalle kalle kawai take sai kuma ta mike tana kallon kofar jin alamar mutum, da sauri ta nufi kofar Junaid ya bi ta da kallo, tana isa bakin kofar ta tsaya tana kallon faisal, still yayi a wajen ko kwakkwaran motsi bai yi, har lokacin idonsa na cikin nata, juyawa tayi a hankali ta dawo kusa da Junaid ta xube gabansa ta xauna, kallo daya xaka mata ka ga ramar da tayi, mama jummai ta fara dariya tace "Wayyo, ca take Aminu ne baiwar Allah, to ko don bata ganinsa yasa taki sakin jiki ne? Kasan fa ko mara hankali dole ya gane me kyautata masa" Junaid ya lumshe ido ya bude ya ajiye mata ledan fruits din hannunsa ya bude, kallon fruits din kawai take, a hankali ya 6alli ayaba guda daya a bunch dinsa ya mika mata, karba tayi tana ta kallon ayabar kamar me son gano abu, can dai ta sa hannu a hankali ta shiga cire peel din yanda ta ga El-ameen na mata, Junaid dai kallonta kawai yake, tana gama cirewa ta mika masa, ya karba ya kai mata baki ta ki ci, duk yanda yayi da ita kin ci tayi ta kwanta nan wajen, Mama jummai tace "Wai yaushe Ahmad din xai dawo ne, ina jin fa yarinyar nan sabon da tayi da shi yasa ta ki sake jiki rashin ganinsa, tausayi take ban wallahi" mikewa Junaid yayi bai ce komai ba, ya nufi kofa, faisal dake wajen har lokacin yana kallonta ya basa hanya ya fice, sannan shi ma ya juya ya bi bayansa, xama Junaid yayi a balcony ya fito da wayarsa yana jujjuyawa, faisal ya sauke ajiyar xuciya yace "Me ka fahimta game da reaction din yarinyar...." Tsaki Junaid yayi yace "kaga Kawai na yanke shawarar tafiya da ita Abeokutan, xai fi! Maganar ta saba da wannan ta saba da wancan bai taso ba yanxu" faisal dai kallonsa kawai yake, Mikewa yayi yace "Xan koma gida kafin....." Faisal ya katse sa yace "Haba Captain kana jin ance tun safe bata ci komai ba sai kace xaka tafi, ko da milk ne ka siyo a gwada bata mana" Junaid yace "Yea! But I don't want my mum to start calling me, bayan bakin gate kadai nace xan raka ka, do me a favour by buying the milk and bringing it to them, ga Atm card dina" kallonsa kawai faisal ke yi, har ya fiddo card din ya mika masa, can ya girgixa kai yace "Nima yanxu Mumyna xata kira ni" Junaid yace "Ohk then! Let me send the gate keeper!" Daga haka ya nufi gun mai gadi, faisal ya girgixa Kai ya koma parlon, ai tana jin an tura kofa ta mike da sauri, faisal ya rungume hannayensa yace "Poor you!" Komawa tayi a hankali ta xauna. Ya juya ya fita daga parlon wani tausayinta na shigarsa, anya ba asiri bane wannan, ban da haka me yayi mata xafi haka har ya kai ta ga hauka at her young age!" Ko da ya fita har Junaid yayi masa gaba da motarsa, tsaki kawai yayi ya nufi titi don hawa tricycle, ko waye bai son uwarsa???
Washegari Junaid na office ya kira faisal, bayan sun gaisa yace "Plss frnd make arrangement for me ko xuwa gobe ko jibi sai a tafi da ita can din, ta flight" faisal yace "Who's going der with her?" Junaid yace "Yea xan ce ma Mumy an min transfer din sati daya xuwa lag, kaga kafin sati dayan duk xa ayi abubuwan da ya kamata, bari dai xan xo idan na bar gun aiki sai muyi magana" faisal ya tabe baki yace "Ohk," sannan ya katse wayar. El-ameen ne xaune office ya hade kai da table, ya ji an bude kofar office din, dagowa yayi da sauri don ganin waye, sanin ya gaya ma nurses din ya gama attending ma patients for that day, ganin faisal ne ya kalli agogo yaga uku ya gota, faisal ya karaso yace "What's the problem El?" El-ameen ya shafa kansa tare da lumshe ido yace "Bacci!"
✍🏻 *Haske Writers Association*💡
Thanks all for the prayer Allah bar xumunci. ⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓
_Khaleesat Haiydar_✍🏻
27.....
Faisal yace "Uhn wai bacci!" Kallonsa kawai El-Ameen yake da lumsassun idonsa, faisal ya xauna kan table yace "Ya aikin?" El-ameen yace "Alhmdllh" faisal yayi murmushi yace "Abokin ka xai tafi da patient din ku Abeokuta soon..." El-ameen ya d'aga kafada yace "Dat's nyc, Allah ya bada sa'a, ita kuma ya bata lafiya," faisal yace "Ameen, and you know what?" El-ameen ya girgixa kai, faisal yace "Ta ki cin komai yarinyar, from all indication, she is missing you" El-ameen ya girgixa kai yace "No! Idan aka takurata kuma aka tsoratata xata ci" faisal yayi shiru, sai kuma yace "Don Allah ku bar wannan childishness din kai da Junaid ku hada kai ku taimaki baiwar Allah, ni banga abun xuciya a nan ba, ga yarinyar 'yar karama da ita...." El-ameen ya hade rai yana kallonsa yace "Look nace banyi kuma, ba gashi xai kaita asibiti ba, don Allah ka bar ni in ji da abinda ke damuna" shiru faisal yayi kafin yace "But ni ina tunanin anya ba asiri aka mata ba, banda haka me xai ja mata brain disorder at her young age...." El-ameen ya girgixa kai yace "Na fa yi diagnosing dinta, brain disorder ne, she's suffering from post-traumatic stress disorder!" Faisal ya d'an bude ido yace "And what's the cause?" El-ameen ya lumshe ido ya bude yace "Serious accident, sudden demise of love one, terrorist incident, a lot of them..." Faisal ya sauke ajiyar xuciya yace "Allah sarki, Allah ubangiji ya bata lafiya" El-ameen yace "Ameen!"
Kusan a tare Junaid ya shigo compound da Suhaima da tayi kamar bata san mota ce bakin gate din ba sai tafiyarta take, ya kusa bugeta da motar ya nufi parking lot abun sa, bude baki tayi bayan tayi tsalle ta bar wajen ta bi motar tasa da kallo, ya fito ya rufe motar ya nufi part din Mumy, tsaki tayi ta shige part din Hajiyarsu tun daga parlor ta dinga kwala mata kira ta fito da sauri, Suhaima tace "Uhn in gaya maki haka maganan take Hajiya, Mahaukaciya Ahmad ya tsinta yanxu haka tana gidan El-ameen ana kula da ita wai, don ma Sumayyar bata san gidan bane da mun je" Hajiya tana tafe hannu baki bude tace "Ikon Allah, mahaukaciya kuma? xan ko je in samu uwar Aminun yanxu ba sai gobe ba" Suhaima tace "Amma fa Hajiya xai ma iya yiwuwa Khadija ta san komai" Hajiya tace "Ae baxa tayi magana ba shegiyar, bari ina zuwa in je gun balki mu san abun yi" dankwali ta dauka ta fice tayi bangaren Umma. Junaid na bude kofar Mumy Humainah dake labe jikin kofar tayi masa k'ara a fuska, turata yayi har sai da ta kusa faduwa ya hade rai yace "baki da hankali ne" kallonsa ta tsaya yi kamar xata yi kuka, ya galla mata harara ya juya ya fita daga parlon, parlon sa ya tafi ya kwanta, duk ya rasa me ke masa dadi, bayan isha yana xaune parlor Fatima ta tace Abba na kiransa, bai tanka ta ba har ta fita sannan ya mike ya fita ya tafi part din Abban, Mumy ce parlon tana yanka masa watermelon sai Umma da ita ma shigowarta kenan, ya xauna kasan rug din tsakar parlon yana kallon Abban nasa yace " Sannu da dawowa Abba" Abba yace "Yauwa, ya maganar mu ta ranan ban ji ka sake cewa komai ba" Junaid ya d'ago da kyar yana kallonsa, a hankali yace "ina sane Abba..." Abba xai yi magana Umma ta riga sa tana murmushi tace "Toh ko dai har yanxu baka samo mana surkar bace Ahmad" ko kallonta bai yi ba bare ya tanka ta, Mumy dai bata ko kallesu ba tana ta yankar kankanar gabanta, Abba yace "Toh ina sauraranka, don kwanakin da na dibar maka ya kusa" kai kawai Junaid ya iya kada masa ya mike ya fita daga parlon jikin sa a sanyaye, part dinsa ya koma ya kwanta duk jikinsa ba kwari, shi yanxu a ina xai samo mata ana xaune kalau gashi sati daya da 'yan kwanaki kadai ya rage a kwanakin da Abba ya dibar masa, gaba daya daren ranan kasa baccin kirki yayi, ya mike ya dauro alwala ya fito ya hau sallahn nafila a dakin, washegari da safe haka ya shirya cikin rashin kuzari ya tafi gun aiki, da ka gansa kasan akwai damu tattare da shi sosai, after Asr ya nufi gidan El-ameen, driving kawai yake amma gaba daya hankalinsa bai jikinsa ga wani mugun sara masa da kansa yake, ya rasa wanda xai gaya ma damuwarsa a lokacin, da da ne da yanxu ya kira El-ameen ya sanar da shi, yana isa gidan yayi xaman sa cikin mota bai fito ba har bayan kusan rabin awa, can ya fiddo wayarsa yayi dialing number faisal, bugu biyu faisal ya d'aga, Junaid ya lumshe ido yace "Plss faisal ka taho gidan El-ameen if you are less busy" faisal yace "Ohk" katse wayar Junaid yayi, sai ya ji kamar ya kira El-ameen sai ya fasa, yana nan xaune har faisal ya iso layin bayan kusan minti ashirin, Yana gama parking ya fito Junaid ya danna masa horn don ya gane yana cikin motar, faisal ya nufi motar ya bude yana kallonsa yace "Mummy's boy...." Shiru yayi ganin yanayinsa, can ya shiga motar yace "Ya aka yi Captain" Junaid ya lumshe ido ya bude kamar baxai ce komai ba, faisal ya tabe baki yace "Haka fa, ni ba El-ameen ba ina kai ina gaya min, but kiran me ka min?" Junaid yayi murmushi yace "Mu shiga ciki" daga haka ya bude motar ya fita, faisal ma ya fito suka shiga gidan a tare, mama ce xaune parlor ita kuma tana kwance jikinta tana gyara mata gashinta, suka gaida Mama ta amsa da murmushi tana masu sannu da xuwa, Junaid ya xauna idonsa a kan jasmine, haka ma faisal, a hankali ta bude ido tana kallonsu don dama ba bacci take ba, Junaid yace "Ta fara cin abincin mama?" Mama jummai tace "A'a daxu dai na bata kunu ta sha ba laifi, sai dai jikinta da dumi" Junaid bai kuma cewa komai ba, faisal yace "Toh ta sha madarar jiya?" Mama ta girgixa kai tace "A'a" Junaid dai sai kallonta yake, faisal ya mike ya isa gabansu ya duka a hankali ya daura hannunsa kan forehead dinta, tayi wani kara da ya sa shi mikewa da sauri ya koma baya, mama jummai tayi dariya tace "Toh bata sanka ba" faisal yace "Uhun na ga alama" murmushi Junaid yayi ya mike ya nufi kofa, mama tace "Kai dai Ahmad ka iya tafiya ba sallama" juyawa yayi yace "A'a ban tafi ba mama ina waje " mama tace "Toh yaushe Aminu xai dawo, ka ga maganinta ya tsaya yanxu" yace "Xai dawo, amma ba yanxu ba shi yasa ma yanxu nake shirin kai ta asibiti a ci gaba da dubata a can kafin ya dawo" daga haka ya nufi kofa ba tare da ya jira cewarta ba, ta bi sa da ido lkci daya jikinta yayi sanyi jin abinda yace, faisal ya juya ya bi bayansa, hawaye ne ya cika idon mama jummai ta dago jasmine tana kallonta tace "Yanxu raba mu xa ayi?" Junaid na fita balcony ya xauna, faisal ya xauna gefensa yace "Nayi kadan in ji damuwar ka ko Junaid" Junaid ya kallesa yayi murmushi yana girgixa masa kai, bayan kusan minti biyu cikin sanyin murya ya soma gaya ma faisal matsalar da yake ciki, faisal yayi shiru yana kallonsa cike da tausayinsa, can yace "Toh kai yanxu baka da budurwar da ta maka ne" Junaid ya girgixa masa kai yace "I don't have!" faisal ya sauke ajiyar xuciya yana kallonsa, bayan kusan minti daya murya can kasa yace "You know what Capt?" Junaid ya kallesa bai ce komai ba, faisal yace "ka auri yarinyar nan kawae...." Junaid yace "Wacce yarinya?" A hankali faisal yace "Baiwar Allahn nan da kake kokarin ganin an sama ma lafiya, I assure you ba karamin lada xaka samu ba, sannan yarinyar bata yi kama da 'yar kananun mutane ba, ina da yakinin 'yar babban gida ce, you won't regret it frnd....." Kallonsa kawai Junaid yake da mugun mamaki, faisal ya girgixa kai yace "Its for ur good, for her good Capt, yanxu misali kayi aure dole baxa ta ke samun attention gun ka ba as before and ba ko wace mace bace xata yarda da taimakon ta da kake, kaga wannan shine anyi ba ayi ba don gidan jiya yarinyar xata koma, but idan ka daure ka aureta kaga ka rufe bakin parent dinka, ita kuma sai ka ji dadin kula da ita sosai tunda you now have ur freedom har Allah ya bata lafiya, then sai ka sauwake mata idan baka da ra'ayin xama da ita ta tafi ta nemi 'yan uwanta, in ka mata haka ka mata komai na rayuwa, kai kadai ne gatan yarinyar nan Junaid, ka ajiye batun mahaukaciya ce ka aureta, I assure you dat you won't regret helping her...." Katse sa Junaid yyi yace "What the hell are you saying faisal, a haukacen xan gabatar da ita gun su Abba? Sai ince ina danginta da 'yan uwanta suke, kuma kasan dai dole sai na kai ta gida gun Mumy, this is totally out of it...." faisal yace "Uhmm! Toh nemo wani solution din" Junaid ya sauke ajiyar xuciya yace "Don nayi aure baxai sa in ki ci gaba da taimakonta ba, ni nayi niyyar nema mata lafiya, babu kuma macen da ta isa don na aureta tayi controlling dina, da aurena ko ba aurena I will help her kamar yanda nayi niyya, yanxu dai xuwa gobe nake son gama arrangement din tafiya da ita" faisal ya d'aga kafada yace "Ohk Allah ya shige mana gaba, yanxu mu je in siya drugs ka kawo mata don akwai xaxxabi jikinta" El-ameen ne kwance dakinsa bayan magrib, Ummi ta shigo dakin tana kallonsa tace "What's ur problem Ahmad, are you ohkay?" Mikewa xaune yayi a hankali yace "Slight headache ne Ummi" tace "Toh ka fito ka ci abinci ka sha magani mana ko kwanciyar ne xai sama maka relieve" daga haka ta juya ta fita tana naxarin maganan da Hajiya fati ta xo mata da shi daxu, wai sun ajiye mace can gidansa shi da Junaid, she trust her son, ta kuma san abinda xai yi da wanda baxai yi ba, ganin condition dinsa tun da ya dawo daga gun aiki yasa bata yi masa magana ba, ta kuma yanke shawarar ba ma sai ta masa ba kawai sawa xata yi aje a gano mata kuma idan har hakan ne ta tanadi abinda xata yi masa don she's a no nonsense ita, bayan minti kusan goma da fitan Ummi dakin Faisal ya xo, yayi mamakin ganin El-ameen din kwance yana bacci, ya tada sa yace "Lafiyarka kuwa El kai da baka bacci da wuri" El-ameen ya kuma lumshe ido yace "ina jin xaxxabi ne ke son kama ni, am not feeling OK" faisal yace "Toh ka sha magani?" Girgixa masa kai El-ameen yayi, faisal yace "Saboda me? patient dinku ma na can ita ma xaxxabin take, na dai siya mata drugs Junaid ya kai mata..." Mikewa xaune El-ameen yayi da sauri yace "Xaxxabi kuma, tun yaushe? Wani drugs din ka siya mata?"
✍🏻 *Haske Writers Association*💡 ⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
28.....