Captain ahmad junaid complete - Chapter 25
Captain ahmad junaid complete Chapter 25: Captain ahmad junaid complete Chapter 25. Sake mata hannun yayi yana kallonta ganin yanda take kuka, ta girgixa…
4,499 words
Sake mata hannun yayi yana kallonta ganin yanda take kuka, ta girgixa masa kai tace "Bana so" ajiye Cotton wool din yayi yace "Ita ta yanka ki?" Girgixa masa kai ta kuma yi tana hawaye tace "Knife ta bani" bai kuma cewa komai ba ya mike xai fita, tace "Ka kira min uncle ya xo" juyawa yayi ya kalleta, tana hawaye tace "Call me Uncle" wani kallo ya mata ya fice daga dakin. Haka tayi ta xama ita kadai tana kuka tana yarfe hannu, da ta ga jinin ya fara xuba sai ta goge jikin farin bedsheet din, gajiya tayi da xaman ta mike ta fita daga dakin har lokacin tana hawaye, dakin da take ta shiga ta kwanta. Karfe tara Humainah ta shigo dakin rike da cup din tea da plate din potatoe da kwai ta ajiye mata, Jasmine ta mike da sauri tana kallonta da idonta da suka rine don kuka tace "Anty ki kira min uncle" tsayawa kallonta Humainah tayi, sai da ta sake maimaitawa sannan tace "Waye Uncle?" Jasmine ta goge hawayen idonta tace "Wannan uncle din nan nawa da ya tafi" shiru Humainah tayi can dai tace "Ohk" ta juya ta fita ta shiga dakin Junaid, wayarsa ta dauka ta fito ta dawo dakin da Jasmine take, number El-ameen ta dinga nema a wayar amma bata san da sunan da ya sa ba, call log ta shiga tana dubawa taga wani number da yasa My best, dialing tayi tana sa ran shi ne, bugu uku aka daga, daga daya bangaren El-ameen yace "ya?" Mika ma Jasmine wayar Humainah tayi, Jasmine ta karba tana kallon wayar, Humainah tace "Ki sa a kunne" Kai wa kunne tayi ta ji muryar El-ameen yana cewa "Captain" ta d'an bude ido tace "Uncle!" Shiru El-ameen yayi kafin a hankali yace "Baby" fashe wa da kuka tayi ya mike xaune daga kwancen da yake yace "Me ya faru baby" tana shessheka tace "I've hurt my self" yace "Where?" Tana kallon yatsan ta tace "My finger" yace "With what?" Ta kalli Humainah da ke ta kallonta tace "Knife" shiru yayi sannan a hankali yace "Sorry, an baki magani?" Ta girgixa masa kai tace "No, and it still hurt" yace "Ina Captain din?" Ta goge hawayen idonta tace "I don't know" yace "Toh wa ya baki waya?" Ta kalli Humainah tace "That Anty" yace "Where is she?" Pointing dinta tayi kamar yana gani tace "she's here" yace "Toh bata phone din" mikewa tayi ta mika ma Humainah wayar ta karba, El-ameen yace "Kin tashi lafiya?" Humainah tace "Alhmdllh" yace "Wai yankewa tayi?" Ta kalli Jasmine tace "Eh ta yanke ne" yace "Da girma wajen?" Ta kuma kallonta tace "Not dat deep amma jinin bai tsaya ba" El-ameen yace "Toh xan xo" daga haka ya katse wayar Humainah ta juya ta fita daga dakin, Jasmine ta fashe da kuka ganin hakan ta dinga rerawa. Goma saura El-ameen ya shigo gidan, junaid dake xaune balcony tun bayan fitarsa dakinsa ya dinga kallonsa har ya karaso balconyn, El-ameen ya ja kujera ya xauna yace "Next week xaka yi resume kenan" ba tare da Junaid ya kallesa ba yace "Seem so" El-ameen ya shafa kansa yace "Ashe baby yankewa tayi wai" kallonsa Junaid yayi da sauri, can ya kauda kai yace "Who's dat?" El-ameen yace "Ka fi ni saninta ai" junaid yace "Tun safe nake nan so I don't know" El-ameen yace "Ohk, can I go in?" Junaid yace "Da can tambayata kake idan xaka shiga?" Shiru El-ameen yayi bai ce komai ba, can ya fito da wayarsa sai kuma ya tuna bai da number Humainah, number Junaid din yayi dialing, Humainah dake ta masa dube dube a wayan dake cike da texts din mata yafi 50 a ciki sai dai duk bata ga wanda yake reply ba, whtspp ma haka sai dai yayi reply da sure! yeah! Lol! Ita dariya ma abun ya dinga bata, tana d'aga kiran El-ameen yace "Humainah bring her out ina waje" Humainah tace "Ohk" ta katse wayar ta ajiye ta fita ta shiga dakin Jasmine din, kwance ta ganta inda ta barta bacci ya dauketa, karasawa tayi ta shiga tashinta, Jasmine ta bude ido a hankali tana kallonta, Humainah tace "Uncle din ya xo" mikewa tayi da sauri daga kan gadon tana kallonta, Humainah tace "Yana waje" kofa ta nufa Humainah ta bi ta da kallo har ta fita, kalle kallen parlor ta shiga yi bata gansa ba, hakan yasa ta nufi balcony kamar xata yi kuka, ido hudu suka yi da shi, ta karasa kusa da shi da gudu ta duka kusa da shi tana kallonsa tace "Uncle ka xo" kallonta kawai junaid ke yi ta gefen ido, El-ameen dake kallon hannunta ya ga inda ta yanke yace "Yeah na xo" mika masa hannun tayi kamar xata yi kuka tace "Look" ya kama hannun yana kallon yatsan murya can kasa yace "Sorry, but me kike yi da wuka" ta kalli Junaid hawaye ya cika idonta sai dai bata ce komai ba, kallon Junaid din yayi shi ma ba tare da ya ce komai ba, ya mike ita ma ta tashi tsaye, gun mota ya nufa da ita junaid ya bi su da kallo, suna isa gun motar ta wara ido cike da murna tace "Uncle are we leaving, bari in dauko jakana da hijab" bai ce komai ba ya bude motar ya dauko plaster ya fito yace "Toh shiga" ba musu ta shiga ta xauna, ya yanki plastern ya kamo hannunta ya rufe gun da ta yanken, sai kallonsa take, yyi mata murmushi yace "Xai warke kin ji" kallonsa take kamar bata gane me yace ba, ya buda ido yace "It will heal" a hankali tace "Ohk!" Magani ya dauko a motar ya mika mata ta karba yace "You take one yanxu kinji?" Kai ta gyada masa, ya koma baya yace "Toh fito" kamar xata yi kuka tace "Are we not going" yace "Anjima ne ba yanxu ba" hawaye ne ya cika idonta ta fito daga motar, yayi murmushi yace "Anjiman ma baxan xo ba idan kika min kuka" share hawayen tayi a hankali tace "Na daina" wani chocolate ya dauko a motar ya mika mata yace "Toh gashi ki tafi" ta karba ta juya ta fara tafiya ya bi ta da ido, sai a snn junaid ya dauke ido daga kallonsu da yake, El-ameen ya xaga ya shiga motarsa yayi horn aka bude masa gate ya fice, tana share hawayen ta ta iso balcony din xata shiga ciki Junaid da ya wani hade rai yace "Come back here" dawowa tayi tana kallonsa, yace "Cire abun nan na hannun ki ki fita a nan" kallonsa take kamar bata gane me yace ba, ya mike yace "Nace ki cire" komawa baya tayi a d'an tsorace ta cire plastern ta jefar yace "Leave" parlon ta shiga ya koma ya xauna. Kuka tayi ba kadan ba a bedroom daga nan bacci ya dauketa. Sha daya saura junaid ya shiga parlor ya haura xuwa dakinsa, wanka yayi ya shirya ya fito yayi kwanciyarsa a parlor, can kuma ya mike ya koma sama, ya dde tsaye a corridor kafin ya tura kofar dakin da Jasmine take a hankali, kwance ya ganta tana bacci, ya shiga dakin ya karasa kan gadon ya durkusa yana kallonta, yatsanta ya kamo yana kallon inda ta yanken, ta bude ido a hankali, tana sauke idon kansa ta mike xaune da sauri, kamar bai son magana yace "Is it still paining you?" Girgixa masa kai tayi yace "Ohk! Sorry!" Ta gyada masa kai, yace "Toh kwanta" ba musu ta koma ta kwanta ya mike tsaye yana kallonta, wanda hakan yasa ta rufe ido da sauri. Kasa barin dakin yayi har bayan kusan minti goma ya ji an danna bell, ta bude ido tana kallonsa, murmushi yayi ya juya ya nufi kofa ya fita ya kulle sannan ya sauka downstairs, still yayi bakin kofa bayan ya bude yana kallon Mumynsa, ta hade rai tace "Meye haka?" Murmushi ya kirkira yana shafa kai yace "I i i was surprise ne" shigowa parlon tayi ya bi bayanta gabansa na faduwa. Tana xaunawa ya xube nan gabanta yace "Sannu da xuwa Mumy, ina yini?" Tace "Lafiya lau, ya kuke" yace "Alhmdllh wllh Mumy" yana yi ne yana kallon stairs kamar munafuki, can ya mike da sauri yace "Bari in kirata" ita dai bata ce komai ba ta bi sa da kallo don ko ba a gaya mata ba ta san bai da gaskiya wannan kame kamen, yana haura wa sama ya bude dakin Jasmine suka kusa cin karo tana kokarin fitowa, xaro ido yayi ya ja ta suka koma dakin yace "Ina xaki?" Tace "Ruwa" ya xaunar da ita xuciyarsa na bugawa yace "No xan kawo maki anjima, you know what kar ki sake ki fito yanxu kin ji koh?" Shiru tayi tana kallonsa, yace "Jasmine!" Tace "Uhm!" Yace "I said kar ki fito plss kin ji, kwanta kiyi baccin ki," toh kawai tace ta koma ta kwanta ya mike ya fita ya kulle dakin, dakin Humainah ya shiga ya duba ya ga ba ta, ya jima tsaye kafin ya juya ya fita ya koma parlor, xaune ya ganta kusa da Mumy kamar xata shige jikinta, Mumy na kallonsa tace "Da ina ka tafi" ya buda ido yace "Na je kiranta ban ganta ba Mumy" Mumy ta dauke kai tace "Kaji da abinda kake kullawa, kawai mutum ya maida kansa munafuki, ya dauko wasu halayyen da ba nasa ba" murmushi Humainah tayi don abun ya bata dariya ta mike ta tafi kitchen don dauko ma Mumy drinks, shi kam kasa karasawa cikin parlon yayi don gani yake kamar ta gano sa ne, tana kallonsa strictly tace "What are you up to Ahmad?" Kamar zai mata kuka yace "Nothing mum, just xuwa aikin da bana yi kwana biyu ne naji daban" hararan shi kawai take yayi murmushi ya karaso cikin parlon ya xauna gefenta ya mata side hug yace "I miss you Mumy, har xaxxabin rashin ki fa nake" kallonsa kawai take ganin yanda ya rame idanuwansa suka fito, ya langwabar da kai yace "Mumy" tace "Baka cin abinci ne?" Girgixa mata kai yayi yace "Ina ci Mumy, kewar ki ne kawai" tace "Toh ku koma can gidan" wara ido yayi yace "Koh Mumy? Toh xa mu koma" a zahirin gaskiya kawai ya fadi haka ne don xancen ya wuce kuma gaba daya hankalinsa na kan Jasmine, Humainah na shigowa parlon da drinks ya mike yace "ina xuwa Mumy" daga haka ya haura sama, a hankali ya bude dakin ya ganta xaune a kasa, ya karasa da sauri yana kallonta ya durkusa yace "Me kike a nan?" A hankali tace "Ruwa xan sha" yace "Yi hakuri bari in kawo maki yanxu" mikewa yayi ya fita ya shiga nasa dakin ya dauko goran ruwa ya fito ya dawo dakin, da kansa ya bata ta sha, yace "Toh koma kan gado" ta mike ta koma gadon. [1/14, 9:17 AM] Elhajj: ⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
52___53
Jasmine ta bude ido tana kallon El-ameen tace "Uncle ya tafi" El-ameen bai ce komai ba sai bin motar junaid da yayi da ido, can yayi murmushi ya kalli gate din gidansu sannan ya kalleta yace "Mu je" tafiya ya fara yi ta bi bayansa yana yi yana kallonta har suka iso titi, ya tsaida adai daita ya sa ta shiga sannan shi ma ya shiga, tara da 'Yan mintuna Mai adai daitan yayi parking bakin gate kamar yanda El-ameen ya umarce sa, fitowa yayi ita ma ta fito ya fiddo dari biyar ya mika masa sannan ya shiga gate din ta bi bayansa kamar xata yi kuka ganin inda suka dawo, junaid na tsaye balcony har suka iso, El-ameen ya kalli Jasmine da ta ki shiga parlon yace "Tafi ki kwanta gobe xan xo in tafi da ke" kai ta gyada masa hawaye cike idonta tana kallonsa, gyada mata kai yayi yace "Yeah", daga ita har shi bbu wanda ya kalli junaid ta juya ta shiga parlon shima ya juya ya nufi gate, wani irin kallo junaid ya bi sa da shi har ya fita, sannan yayi tsaki ya juya ya shiga parlon, yana haurawa sama ya shiga dakinsa. Washegari Tuesday misalin sha biyu yana daki yana danne dannen laptop tun bayan da ya fita sallahn asuba bai kuma sauka parlor ba kuma idonsa biyu yana jin jasmine na ta sallama bakin kofa bai tanka ba, ita kuma bata shigo ba, muryoyin da yake ji parlor ya sa shi mikewa da sauri ya fita ya sauka downstairs, tsaye yayi bakin stairs din ya wani hade rai yana kallon wa enda ke parlon, Fatima ce da khadija sai Humainah, ga kuma jasmine dake xaune kan rug da plate din abinci gabanta, gaba daya kallonta suke barin fatima da idanuwanta suka kara girma don kallo, kallo daya Humainah tayi masa ta dauke kai, fuska a daure ya karasa cikin parlon yana kallonsu khadija yace " With whose permission ku ka shigo min gida?" Khadija tace "Mumy ce tace mu xo mu taya...." Wani mugun kallon da yake mata yasa ta yin shiru ita ma ta hade rai, fatima kam dama bata dago kai ba, ya juya yana kallon Humainah yace "Kika bude masu kofa without permission dina koh?" Tabe baki tayi bata ce komai ba, kallonta ya tsaya yi na kusan second goma sannan ya juya yana kallon Jasmine da ta kasa cin indomien jin yana masifa, da ganinta kasan a tsorace take, tun kan yace komai muryarta na rawa tace "Ina jin yunwa ne shine na gaya ma Anty ta ban indomie" yace "Tashi ki bar parlon nan" mikewa tayi xata tafi sama ya dawo da ita yace "Dauki abincin" ta durkusa ta dauka ta wuce. Yana kallon kannin nasa yace "Kun san Allah if I shud hear a word daga bakin ku a kan komai na gidana xan maku abinda ban taba ba, nd I mean it" daga haka ya juya ya koma sama. Bayan Azahar su fatima suka bar gidan duk da ba haka Humainah ta so ba, sun dai samu ya basu kudin mota, sama ta haura bayan tafiyarsu ta shiga dakinta, bude kofar aka yi ta juya da sauri ta ga Jasmine, karasowa cikin dakin tayi hawaye cike idonta tana kallon Humainah a hankali tace "Anty cikina na min ciwo" ido Humainah ta xuba mata can tace "Kin ci abincin da na baki?" Girgixa kai tayi tace "Amai xan yi idan na ci" Humainah tace "A'a ki je ki ci dai....." Hawayen dake makale idonta ya gangaro tace "Anty ki kira min uncle in gaya masa" Humainah bata ce komai ba har sai da Jasmine tace "Kin ji" gado ta nuna mata tace "Toh xauna ina xuwa" Jasmine ta xauna ita kuma ta juya ta fita, dakin junaid ta shiga ta gansa kwance idonsa lumshe, lallabawa tayi ta karasa gun da wayarsa yake ta dauka ta fita, tana fita ya mike ya bi bayanta, tana tsaye dakinta tana kokarin dialing number El-ameen ya shigo, still tayi tana kallonsa sai kuma ta hade rai, kallo daya yayi ma jasmine ya fixge wayar yana kallon wanda take kira, da sauri ya katse yana mata mugun kallo yace "Kee!" Turo baki tayi tace "Toh ita ce tace in kira mata" juyawa yayi yana kallon Jasmine da tayi mugun tsorata, ya kuma kallon Humainah ya hade rai yace "Ki bar min irin haka a gidan nan, ke xata gaya ma ki kira mata shi... Are you on ur senses?" A hankali Jasmine ta mike xata fita ya fixgota, kuka ta saki tana kallonsa yace "Me xa ki ce masa?" Muryarta na rawa tace "That my tummy is aching" wani kallo yayi mata yace "Yayi abinda yafi aching din ma, fita daga nan" da sauri ta fita, shima ya juya ya fice, Humainah ta tabe baki ta rufe kofarta. Har dare Jasmine sai juye juye take a daki, tayi kukan har ta gaji, yana son xuwa gun ta amman bakin hali ya hanasa Lol, duk ya rasa sukuni har kusan karfe tara, mikewa yayi ya fita ya shiga dakin Humainah ya sameta xaune gaban mirror tana danne dannen wayarta yace "Kin bata abinci?" Ba tare da ta kallesa ba tace "yana kitchen ai" juyawa yayi ya fita xai koma dakinsa, tsaye yayi bakin kofarsa ya kasa shiga dakin yana kallon dakin da take, karasawa yayi ya tura kofar a hankali dai dai lokacin da ta mike xata bayi da saurinta, bin ta yayi da kallo sai kuma ya ga ta durkushe nan bakin kofar ta fara kwararo amai, shiga dakin yayi da sauri ya isa kusa da ita ya durkusa ya dagota yana kiranta, sosai ya ji jikinta yayi xafi, ta dago jajayen idonta tana kallonsa ta fashe da kuka tana rike da cikinta, ai bai san lokacin da ya hade ta da jikinsa ba, ba shiri ta hadiye kukan da take, xame jikinta tayi, ya mike da kyar yace "Am am sorry jasmine...." Kasa dagowa tayi sai hawaye, ya kama hannunta ta mike ta shiga bayi ta wanke bakinta ta fito ta kwanta, ya gyara gun aman ya dawo dakin yana kallon agogo, ya dawo kusa da ita yace tashi mu je asibiti, girgixa masa kai tayi da kyar tace "No ka kira uncle" hade rai yayi ya dau hijab dinta yace "tashi mu je nace" hawaye cike idonta ta mike xaune ta karba hijab din ta sa, kasa tashi tsaye tayi, hawaye na sakko mata tace "Baxan iya tashi ba captain" kallonta yake cike da tausayinta ya durkusa kusa da ita yace "Ina ke maki ciwo ne?" Cikinta ta nuna masa, sai kuma ta fashe da kuka ta koma ta kwanta, mikewa yayi ya fita xuwa dakin Humainah, har ta kwanta ya karasa ya kunna bedside lamp ta bude ido da sauri tana kallonsa ta mike xaune tace "Me ya faru?" Ya dan shafa kai yace "Plss asibiti xa ki raka mu in kai yarinyar nan amai take ta yi" hade rai tayi tace "Bacci ni xan yi, ka kira mata El-ameen mana" yace "No it's late yanxu kar a shiga hakinsa" wani kallo tayi masa tace "I see" ta koma xata kwanta ya rikota ta buge hannunsa tace "Leave me joor" rungumeta yayi yace "Haba wife taimako fa xa kiyi" turasa ta shiga yi tace "Ka rabu dani don Allah ni baccina xan yi" ganin kiss dinta yake son yi tace "Ohk naji naji, mu je" murmushi yayi ya saketa ta mike fuskarta daure ta dau hijab har kasa tasa ta fita ya bi bayanta, ba laifi ita ma ta tausaya ma Jasmine don da ganinta kasan tana jin jiki, tana rike da ita suka shiga motar, wani private hospital suka tafi, basu sha wahalan ganin likita ba, likitan na ta kallonsu har ya xaunar da ita sannan shi ma ya xauna, yayi murmushi yace "Couples?" Kallonta Junaid yayi da sauri ita ma ta kallesa suka hada ido ta dauke kai, ya dan wara ido yace "Ohh No! We are not" Likitan yace "Ohh sorry!" Murmushi kawai junaid yayi ya d'an saci kallonta, tambayoyi likitan ya fara mata junaid na bada amsa don kin cewa komai tayi, nan dai ya duba ta ya rubuta mata magunguna da allura sai test da ya rubuta xa a mata gobe da safe, malt junaid ya siya mata ta sha kafin a mata alluran sanin bata ci komai ba, fir taki yarda ayi mata tana kuka a rikice, junaid ya hade rai yace "Xaki sha mari fa, Meye a alluran" fixgota yayi ganin taki yin shirun, ya hade rai yana kallonta, da kyar ta yarda aka mata shima a cinya yana tsaye kanta, ta dinga ihu tana rusa kuka, yana rike da hannunta yana kallon yanda take kukan suka fito reception, dariya ma take basa, Humainah da dama bata bi su ba tana reception din xaune ta hade rai ganin yanda ya rike ta yana kallo, har suka shiga mota kuka jasmine take sosai, shi dai Junaid bai ce mata komai ba haka Humainah, ta gaji don kanta tayi shiru, suna isa guda Humainah ta bude motar ta fice, bin ta da kallo yyi sannan ya xaga ya bude motar ya ga shirun bacci tayi ashe, kiranta yayi murya can kasa ta bude ido a hankali yace "Fito" fitowa take son yi amma ta kasa, ta nuna masa cinyarta cikin tsarkewar murya tace "It's aching" kallon balcony yayi ya ga har Humainah ta shige, hannu ya mika mata ta kama sannan ya fito da ita, yana rike da ita suka shiga parlon, bai bari sun hada ido da Humainah dake parlon ba ya haura sama da ita, magungunanta ya bata ta karba ta sha yace "Toh kwanta ki yi bacci" girgixa masa kai tayi tace "Xan cire kaya" yace "Toh cire" mikewa tayi ta sauka ta cire hijab xata cire doguwar rigar jikinta yace "Noo tafi bayi ki cire" tace "Toh" sannan ta shiga bayin, kasa fita yayi daga dakin, har ta fito daga ita sai inner, xaro ido yayi ya kasa cewa komai bai kuma daina kallonta ba, tace "towel din...." Ai bai tsaya saurarenta ba ya fice daga dakin da sauri. Kayan baccinta ta dauka a closet ta sa sannan ta kwanta. Downstairs ya sauka ya kashe kayan wuta ya koma daki. Wanka yayi ya daura alwala ya shirya ya kwanta, sai dai ya kasa bacci har kusan sha biyu ya mike daga karshe ganin he's just deceiving his self ya fita, dakin Humainah ya shiga ya kunna wutan dakin, yayi mamakin ganinta xaune kan gado ta hade kai da gwiwa, dagowa tayi tana kallonsa da rinannun idonta, ya kashe wutan ya karasa da kyar ya xauna gefenta yace "What happened?" Sharesa tayi xata kwanta ya rikota ta fashe da kuka, ya rungumeta cikin sanyin murya yace "talk to me" turasa ta shiga yi ya ki saketa hakan yasa tayi lamo jikinsa hawaye na saukowa idonta, sun kusa minti goma a haka ya dago kanta yana kallonta da idonsa da suka kada murya can kasa yace "Kina da alwala?" Kin cewa komai tayi har sai da ya kirata, tace "na me?" Yace "Toh je kiyi" tace "Ni nayi" mikewa yayi yace "Ohk let pray" wani kallo take masa kafin tace "Na me?" yyi shiru yana kallonta, can ya mike ya hau darduman dake shimfide kasa yace "Am waiting" kin tashi tayi yace "Ke fa nake jira" da kyar ta sauka duk gabanta na faduwa ta dau hijab ta sa, raka'a biyu ya ja su, suna sallamewa ta mike ta haye kan gado ta shige cikin bargo ya bi ta da kallo, ya jima xaune kan darduman yana addu'o'i kafin ya mike ya dauke darduman ya nufi kan gadon ya xauna, cire bargon yayi ta mike xaune ta hade rai tace "Meye haka?" Ya hau gadon yana kallonta yace "Ina ruwana da ke kiyi baccin ki" kin kwanciya tayi da ganinta kasan a tsorace take, yayi murmushi ya kwanta ya juya mata baya, ta kusa minti biyar xaune kafin ta kwanta nesa da shi xata ja bargo ya koma kusa da ita ya jawota, ta fashe da kuka tace "Ya A.jay bacci fa xanyi plss" a hankali yace "Naji, yi baccin ki amma a jiki na" shiru tayi gabanta na faduwa can tace "Toh ni da bargo nake kwanciya" yace "Ga ki ga shi", bbu yanda ta iya haka ta kwanta ta rufa masu bargo tayi lamo ta rufe ido, sai da ya ga ta fara bacci ya cire bargon, ranan ta fadi ma 'yan garinsu bata taba tunanin haka Ya A.jayn yake ba, ba irin rokon da bata yi masa ba, bbu wanda bata kira masa ba barin Hajja amma duk a banxa abun ka da Novice da mai dacin ran tsiya, tuni baccin wahala da tashin sense yayi gaba da ita, shi kam rasa gane abinda yake ji game da ita a ransa yayi. Da asuba bayan ya dawo daga mosque duk ta daga masa hankali da kuka ita ya kira mata Mumy, ta kuma ki barin ya xo kusa da ita, ya ma rasa abinda xai yi, kyaleta yayi ya fita daga dakin, har xai shiga dakinsa sai kuma ya bude na Jasmine durkushe ya ganta can jikin gado tana kuka ya karasa ciki yana kallonta da mamaki yace "me ya faru kuma" kasa cewa komai tayi sai hawaye, ya durkusa kusa da ita da damuwa yana kallon idonta da ya kumbura don kuka yace "Cikin ne har yanxu?" Ta fashe da kuka ta kamo hannunsa tace "Captain it's still paining me, yana min ciwo sosai" ganin yanda ta rikice yasa hankalinsa ya tashi ya mike ya fita daga dakin ya shiga nasa ya dau wayarsa yayi dialing number El-ameen. Bugu daya ya daga, junaid yace "Pls come over yanxu" El-ameen dake kwance ya mike xaune yace "Me ya faru?" Junaid yace "Hurry up plss" El-ameen ya d'an bude ido yace "Toh fah" sai kuma yayi dariya yace "Kayi aika aika kenan, ba inda xan xo sai dai in turo maku nurse" Shiru junaid yayi d'an ya so ba shi dariya, yace "kaga bana son walakanci ina jiran ka" El-ameen yace "Allah ba da ni xa ayi wannan ba, me xan maku idan na xo?" Junaid yace "Ohk naji ka turo nurse din, but kai ma ka xo don baby ma bata da lafiya tun jiya" El-ameen ya mike tsaye yace "da gaske? Me ya sameta" Junaid ya katse wayar ya xauna ya shafa kansa, murmushi yayi yana mamakin sharp thinking irin na El-ameen, mikewa yayi da sauri ya fita ya koma dakin Jasmine, yanda ya bar ta haka ya sameta ya durkusa kusa da ita cike da tausayinta duk ta rasa inda xata sa kanta sai kuka take, da kyar tace "Captain ka ce Uncle ya xo plss" hade rai yayi yace "Baxan ce ba" kai ta gyada masa hawaye na sakko mata alamar to, can kuma cikin kuka tace "Ka ban Magani captain" hannunta ya kamo yace "Xa a kawo maki yanxu kin ji" ajiyar xuciya ya sauke jin shigowar motar El-ameen, bayan 3 mint ta fara kokarin mikewa tace "Uncle I want to ease my self" hade rai yayi jin tace uncle, ta mike da kyar tana duddukawa, mikewa yayi da sauri ganin abinda ke jikinta, ita ma ta kalli inda yake kallo, ai sai ta fasa ihu a tsorace tana kokarin daga rigar dai dai lokacin da El-ameen ya bude kofa ya shigo dakin, tana ganinsa ta kuma fashe wa da kuka tayi gunsa da sauri, shi ma kallon jikinta ya shiga yi, a rikice take cewa "Uncle kaga blood" xata daga rigar ya kama hannunta, ya d'an kalli Junaid ya ga shi yake kallo, a tare suka dauke kai, Junaid ya juya ya fice daga dakin, El-ameen ya kalleta da tausayi ganin yanda take kuka a hankali yace "Yi hakuri kin ji jewel" wayarsa ya ciro ya kira nurse daga clinic, ganin tsayuwar ke sa ta flow yace ta xauna taki, da kansa ya xaunar da ita ya durkusa gabanta.
Uzuri! Uzuri