Captain ahmad junaid complete - Chapter 28
Captain ahmad junaid complete Chapter 28: Captain ahmad junaid complete Chapter 28. _Tnx all for the prayers sisters Allah ya kara ma duk musulmai lafiya…
5,271 words
_Tnx all for the prayers sisters Allah ya kara ma duk musulmai lafiya Ameen_ Sorry for keeping you all waiting sisters. [3/19, 9:22 PM] El-hajj💥: *Captain Ahmad Junaid* _By Khaleesat Haiydar_ 57..... Junaid na fita gidan ya kira wayar Faisal, yana dagawa yace "Ya? ku na ina yanxu?" Faisal yace "Kai kam sam baka da kirki captain" junaid yace "That's constant ai...." Faisal yace "Toh yayi kyau muna shirin kai ango..." Dariya junaid yayi yace "Ohk toh gani nan xuwa kar rashin kirkin yayi yawa koh?" daga haka ya katse wayar ya dau hanyar gidansu El-ameen, El-ameen na cin abinci a dakinsa Junaid ya shigo, junaid yace "Tab har daman cin abinci ka samu kenan, ni tym din nawa ina na samu wannan daman....." Ko kallonsa El-ameen bai yi ba ya hade rai, dariya sosai Junaid yayi yace "Harara a duhu kawai kake yi" Dr faruq yace "Ni na ma yi xaton tafiya kayi Ahmad, bikin aminin naka guda ace baka kusa" Junaid ya shafa kansa yace "Daxun nan na dawo bana nan" faisal yace "ga alama mun gani" murmushi junaid yayi bai kuma cewa komai ba, ya mike ya bude closet din El-ameen ya fiddo wani dakakken shadda sky blue ya ajiye masa ya koma gun huluna ya fiddo wanda xai shiga da kayan ya ajiye masa, ya dauki agogo me tsada cikin agogunansa ya daura kan kayan yana murmushi yace "Ka tashi ka shirya time na wucewa" wani kallo El-ameen yayi masa ya ci gaba da cin abincinsa, can ya ajiye abincin ya mike yana kallonsu faisal yace "Ku tashi mu je" daga haka ya nufi kofa Junaid ya fixgosa yace "Ka ma isa, da wannan kayan da kke yawo tun safe xa mu kai ka" dariya faruqh yayi yace "Gaskiya ne wnn kuma, go nd change frnd" duk yanda suka yi da El-ameen kin canxa kayan yayi, sai da wani abokinsa Dr Lawal ya sa baki, sosai kayan suka yi masa kyau don bai taba sa su ba ma, junaid sai dariya yake har su faruqh suka dinga mamaki wai ashe dai yana interacting haka da mutane shidai baice musu komai ba, Karfe takwas da rabi suka bar gidan bayan El-ameen ya sallami parent dinsa, karfe tara da kusan rabi suka isa gidan nasa, junaid ya kashe mota don shi ke driving din ya juya yana kallon El-ameen murmushi dauke fuskarsa yace "Toh gashi mun kawo ka frnd, mu iyakar mu kenan, Allah ya bada xaman lafiya.." Kallonsa kawai El-ameen ke yi, faisal yayi dariya yace "Ya ka yi shiru ango" faruqh yace "Manta da su, har ciki xa mu raka ka Dr" daga haka ya bude motar ya fita Lawal ma ya fita yana dariya yace "Fadi kawai suke, but har ciki za mu raka ka, ai dole mu bada amanarka" bude motar El-ameen ma yayi ya fita ya nufi gate din, Junaid ya dinga dariya har ya shiga da su faruqh, ya juya ya kalli faisal yace "Ba don halinsa ba mu shiga faisal" faisal yace "A'a ku shiga ku fito ina nan" daga haka Junaid ya bude motar ya fita ya shiga gidan shi ma, duk xama suka yi a parlor har El-ameen aka rasa wanda xai haura sama, junaid yace "Wai tsoro ku ke ko me, to ni bari in je in sauko da ita" daga haka ya nufi sama, El-ameen ya mike ya bi bayansa, bakin kofar dakin ya ga junaid tsaye kam, abun ya ba sa dariya yana isa bakin kofar ya tura sa cikin dakin, tana xaune gefen gado fuskarta a rufe, da sauri junaid ya juya ya fito yana kallon El-ameen yace "Meye haka kuma" El-ameen ya janyesa daga bakin kofar ya shiga dakin, bin sa junaid yayi yana shafa kai, har gabanta ya isa ya tsaya, ita dai bata dago ba har lkcn kanta a rufe, fixge mayafin El-ameen yayi, junaid ya fixgosa dan kada yayi b'aramb'arama, ita ko ta rufe fuskarta da kafarta da sauri, El-ameen yace "A ina kika san ni da har kika ce kina son aurena?" Mikewa tayi tsaye tace "I shud be asking you your silly ques.....!" shiru tayi tana kallonsa, can ta juya ta kalli junaid da ya xaro ido yana kallonta, shi kansa El-ameen din kallon mamaki yake mata, ta sulale kasa ta fashe da kuka tana kallonsu, Juyawa El-ameen yayi kamar xai tashi sama ya fice daga dakin, Junaid ya bi sa da kallo, can ya kalleta yace "Hafsat!" Ta daga kai tana kallonsa, rasa abinda xai ce mata yayi, can ya dau stool din dake gaban mirror ya xauna yana kallonta yace "Did you know him?" Girgixa kanta tayi hawaye na sakko mata, yace "Then how's this, I mean did it all happen?!" Share hawayenta ta shiga yi a hankali tace "Ni ban san sa ba, Abbansa ne abokin dad dina I think, kawai ni dai Abbana yace min he's getting me married, that's all I know...." Junaid yayi shiru kafin yace "But kinsan yan gidansu?" Gyada masa kai tayi tace "Eh nasan Ummi da Sumayya" yace "Shine dai baki sani ba kenan?" Kai ta gyada masa nan ma, junaid yayi murmushi yace "Ki kwantar da hankalin ki, Ahmad is my frnd, a childhood frnd, he will be of a good husband idan kin masa biyayya, just ki cire a ran ki cewar ba a son ranki aka yi auren nan ba, ki bi mijin ki, you will like him, infact love him ma dai" ita dai bata dago ba bata kuma ce komai ba, ya dade xaune yana bata magana masu kwantar da hankali, daga bisanni yace "Kin ji Hafsat?" Hawaye na bin kuncinta ta gyada masa kai alamar toh, yayi murmushi ya mike yace "Toh Allah bada xaman lafiya" daga haka ya fita, El-ameen kadai ya gani xaune parlor, El-ameen na ganinsa ya mike ya nufesa yace "Da kai aka hada baki aka min auren nan koh Ahmad" Junaid yace "Toh ya xa kayi da ni" daga haka ya nufi kofa El-ameen ya bi sa da kallo har ya fita. Ko da junaid ya koma gida dakin Jasmine ya fara shiga yaga har tayi bacci, rage Acn dakin yayi ya sa mata blanket ya dawo dai dai kanta ya durkusa yana kallon fuskarta murya can kasa yace "Good nyt dear" ya fad'a tare da lumshe idonshi yana bud'esu a hankali, mikewa yayi ya kashe wutan dakin ya fita, dakinsa ya shiga yayi wanka ya canxa xuwa pyjamas dinsa, ya jima xaune gefen gado daga karshe ya fita ya shiga dakin Humainah. Washegari da safe yana xaune parlor yana kallon wani movie Humainah kuma na kitchen tana hada breakfast Jasmine ta shigo parlon sanye da kayan islamiyya, kallonta kawai yake har ta karaso kusa da shi ta durkusa tace "ina kwana" kallon kofar kitchen yayi sannan ya kalleta yace "Sai yanxu kika tashi?" Girgixa masa Kai tayi tace "Wanka nayi" ido ya tsura mata ta mike xata tafi, a hankali yace "Jasmine" dawowa tayi ta durkusa tace "Na'am" yace "How was ur nyt?" Tace "Alhmdllh" yace "baxa ki islamiyya ba yau!" Ta kallesa da sauri tace "fashi?" Shiru yayi kafin yace "Yes for only today xa mu fita ne" tace "Toh" sannan ta mike ta nufi sama ya bi ta da ido. Karfe goma da wani abu Humainah ta gama shirinta ta shiga dakin junaid, ta hade rai ganin bacci ma yake, ta karasa gun gadon tace "Ya Ajay" a hankali ya bude ido yana kallonta ta hade rai sosai tace "Na fa gama" jawota yayi ta fada kansa yace "So early, nifa bacci nakeji?" ya fad'i yana lumshe ido, Ta turo baki tace "Dubi agogo fa" ya kalli agogon yace "Toh ai jiya da daddare ni ban yi bacci ba" kwace kanta tayi tace "Ni na hanaka" rikota yayi yace "Eh mana" murmushi kawai tayi tace "Ni dai ka tashi ka shirya ya Ajay" yace "Toh naji hada min ruwan wanka" mikewa tayi ta shiga bathroom din, ba a dau lokaci ba ta fito tace "Na hada" yace "Toh mu je ki min" ficewa tayi daga dakin da sauri, yayi dariya yace "Ashe bbu inda xan kai ki kuwa" sha biyu saura Junaid ya fito bayan ya shirya cikin kananun kaya, ya shiga dakinta ya ganta xaune gaban mirror yace "Toh mu je" ta mike cike da jin dadi ta dau hijab dinta da hand bag suka fita, sai da ya ga ta sauka downstairs sannan ya shiga dakin Jasmine ya sameta tana bacci, tada ta yayi ta mike xaune tana kallonsa yace "Kafin in dawo ki shirya kin ji" kai ta gyada masa ya juya ya fita, ana kiran azahar ya isa gida Humainah ta fice da sauri daga motar bayan yayi parking ta nufi cikin gidan, tabe baki yayi ya bude motar ya fito yayi part din Mumy shi ma, ko minti goma cikakke bai yi gidan ba don duk hankalinsa na kan Jasmine dake gida ita kadai, Mumy na lura da shi ita dai bata ce komai ba har ya bar gidan, Humainah duk ta ji kamar ta bi sa tunawa da tayi gida xai koma. Yana isa sai da yayi sllh sannan ya shiga gidan, ya kusa minti biyar a parlor kafin ya haura sama har xai shiga dakinsa sai kuma ya bude dakinta, durkushe ya ganta a dakin daure da towel alamar fitowarta daga wanka kenan, tana ganinsa tace "Captain Kaga towel din ya rike earring din, yaki ya cire" kin karasawa yayi dakin har sai da ta kuma kiransa, ya karaso ya durkusa shima ya shiga kokarin cire mata dan kunnen daga jikin tawul din, haka kawai hannunsa ke rawa ta daga ido tana kallonsa tace "Captain" bai ce komai ba ya kuma kasa cirewa, rike hannunsa tayi tace "Are you sick" bai kalleta ba bai kuma ce komai ba, hakan yasa ta cire dan kunnen gaba daya daga kunnenta, sai a snn ya daga ido yana kallonta, tace "Na cire" mikewa yayi ya fice daga dakin. Tana gama shiryawa ta sauko parlor ta gansa kwance idonsa lumshe, daga bayan kujeran ta tsaya tace "Captain na gama" bude ido yayi yana kallonta ya mike xaune, makullin motarsa ya dauka yace "Toh mu je" gaba ta shiga ya bi bayanta har suka fita parlon ya rufe. Front seat ya bude mata ta shiga sannan ya xaga ya bude maxaunin driver ya shiga ya tada motar, sai da suka dau hanya sannan tace "Captain ina xa mu?" Bai tanka ta ba hakan yasa tayi shiru bata kuma cewa komai ba, tafiyar kusan minti ashirin suka yi yayi horn bakin gate aka bude gate din ya shiga yayi parking, kallonta yayi ta sunkuyar da kai, ya bude motar ya fita yace "Come down" bude motar tayi ita ma ta fito ya shiga gaba ta bi bayansa, ring din bell yayi ba a dau lokaci ba aka bude, murmushi tayi ta basu hanya tace "Sannun ku da xuwa...." Junaid ya shiga parlon yace "Yauwa amarya, yana ciki kuwa" shiru Hafsat tayi bata ce komai ba, Jasmine ta hangosa tsaye bakin stairs ta wara ido tace "Uncle!" Da gudu ta karasa cikin parlon daga Junaid har Hafsat suka bi ta da kallo, tana isa gun stairs din ta rungume sa, murmushi El-ameen yayi ya janyeta jikinsa, Hafsat ta kalli junaid da ya dauke kai, ita ma ta sunkuyar da kai, kama hannunts El-ameen yayi suka dawo parlon tace "Uncle ban san nan captain xai kawo ni ba" junaid ya fiddo waya kamar xai yi kira ya juya ya fice daga parlon, Jasmine tace "kuma Uncle yace min kayi aure da gaske ne?" Wara ido yayi yace "uhn! He's lying" ta langwabar da kai tace "Ohh captain! Why him" Juyawa tayi ta kalli Hafsat dake tsaye har lkcn bakin kofa ta matsa kusa da shi a hankali tace "Who's she?" Satan kallon Hafsat yayi yace "My sister" mikewa tayi tace "Ohk let me greet her" kafin yace komai har ta isa gun Hafsat tace "Anty ina yini?" Hafsat ta d'an yi murmushi tace "Lafiya lau, sannu da xuwa" Jasmine na murmushi tace "Ke sistern uncle ce koh?" Kai Hafsat ta gyada mata, El-ameen ya mike yace "Xo ki xauna in kawo maki drink ko baki so" dawowa parlon tayi tace "Ina so uncle" fridge ya nufa Hafsat kuma ta nufi kitchen, hollandia drink ya dauko mata da goran ruwa daya sai glass cup ya dawo kusa da ita ya xauna ya bude drink din ya xuba mata ya sha kadan ya bata ta wara ido ta karba tace "Thank you uncle" Hafsat ta fito daga kitchen rike da food warmers da plate a tray ta shigo parlon ta durkusa nan kusa da su tace "Ga abinci!" Jasmine ta kalli El-ameen, bude abincin Hafsat tayi ta dibar mata ta sa spoon ta mika mata, karba Jasmine tayi tace "Na gode Anty" murmushi Hafsat tayi mata ta mike ta bar wajen, Jasmine ta sauko kasa tana kallon El-ameen tace "I like her!" Murmushi yayi ya shafa kai bai ce komai ba, spoon din ta dauka ta fara cin abincin tace "Uhnn akwai dadi" El-ameen ya karbi spoon din ya debi abincin shi ma ya ci, mikewa Jasmine tayi da sauri ya kalleta yace "What?" Ta xaro ido tace "Ina captain toh?" Kofa ta nufa da sauri El-ameen ya bi ta da kallo, tana fita ta gansa xaune waje, tace "Baka shigo ba captain" mikewa yayi yana mata wani kallo yace "ina takalmin ki?" Kallon parlor tayi yace "Tafi ki dauko...." Ta marairaice tace "Are we going?" Wani mugun kallo yake mata xai yi magana El-ameen ya fito, kamar xata yi kuka tace "Uncle wai tafiya xa mu yi" El-ameen yace "A'a mu je ki ci abincin ki" juyawa tayi ta koma parlon, El-ameen ya d'aga ma junaid hannu yana murmushi yace "In xaka shigo ka shigo malam" daga haka ya koma parlon, xaunawa Junaid yayi ya dafe kansa, can ya mike ya sauka daga balcony din ya nufi motarsa ya shiga ya danna horn mai gadi ya bude masa gate ya fice daga gidan, Jasmine tace "Uncle ya tafi" El-ameen yace "Ci abincin ki" a hankali tace "Toh" ta ci gaba da cin abincin ta, yana nan xaune har ta gama ta mike tace "Na gama uncle ka tafi da ni gida" shiru yayi yana kallonta, ta koma ta xauna ta marairaice tace "Ka ji?" Yace "Nan ba gida bane?" Bin parlon tayi da kallo a hankali tace "Gidan Captain xaka kai ni" hade rai yayi yace "ina aiki a sama sai na gama" daga haka ya haura sama ya bar ta wajen, mikewa tayi ta bi sa da kallo kamar xata yi kuka, ko minti biyar ba ayi da tafiyarsa sama ba, Hafsat ta sauko tace "Har kin gama" gyada mata kai tayi, Hafsat tace "Toh taho mu je sama" ba musu Jasmine ta nufi stairs suka haura sama a tare Hafsat ta shiga da ita dakinta ta nuna mata gado ta xauna, sannan ta kunna mata kallo. Har bayan la'asar Jasmine na dakin tayi rub da ciki kan gado tana kallo, Hafsat kuma na ta danne danne a laptop aka bude kofar dakin duk suka juya kallonsa, karasowa cikin dakin yayi yana kallon Jasmine yace "Kin yi sllh" gyada mata kai yayi, ya d'an saci kallon Hafsat suka hada ido ya dauke kai da sauri, Jasmine tace "Anty ce kawai ya rage tayi sallah" [3/19, 9:25 PM] El-hajj💥: ⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
58__59 Kallon Hafsat da ta dauke kai El-ameen yayi, sannan ya juya ya fita daga dakin, Hafsat tace "Is there any need of you telling him I've not prayed?" Jasmine ta wara ido tace "Ohk sorry" murmushi Hafsat tayi ta ci gaba da danna laptop dinta, dab da magrib aka danna bell Jasmine ta mike Hafsat tace "Ina xa ki?" Jasmine tace "To open the door" Hafsat tace "No! Ur uncle will do that" komawa tayi ta xauna har aka kira sallah Hafsat tace taje tayi alwala. Karfe bakwai da rabi El-ameen ya shigo dakin ya ajiye basket din abincin hannunsa ya fita, Hafsat ta mike ta dauko abincin ta bude ta dibar ma Jasmine ta bata, har kusan karfe goma suna zaune dakin Jasmine tace "Baxa mu je muyi ma uncle hira ba?" Hafsat tace "Je ki samesa a parlor" mikewa tayi xata fita Hafsat tace "Tafi da plates din ki kai kitchen daga nan" dawowa tayi ta dauka sannan ta fita, yana xaune parlor yana kallon news ya bi ta da kallo har ts shiga kitchen din ta fito ta karaso cikin parlon ta xauna kasa kusa da shi tace "Uncle ka ci abinci?" Girgixa mata kai yayi tace "Why?" Yace "Ba a bani ba ai" mikewa tayi yace "Ina xa ki?" Tace "Ina xuwa" dakin Hafsat ta koma ta langwabar da kai tace "Anty Uncle yace yunwa yake ji ki kawo masa abinci" daga haka ta juya ta fita daga dakin, El-ameen yace "Me kika je yi?" Tace "Nace Anty ta kawo maka abinci?" Ya hade rai yace "Did I send you?" Girgixa masa kai tayi, sai ga Hafsat ta fito, kitchen ta shiga ta dau plate da spoon ta fito ta koma daki, El-ameen ya tabe baki ya ci gaba da kallonsa, ba a dau lkci ba Hafsat ta fito rike da plate din abinci ta shiga kitchen ta daura kan tray ta sa ruwa da cup ta fito parlon ta durkusa ta ajiye kusa da shi sannan ta mike ta bar wajen, sai da ya ji ta shi ga daki snn ya dau abincin ya fara ci, Jasmine tace "Har yanxu captain baxai xo ba?" El-ameen ya ajiye plate din hannunsa yace "I will knock fa idan kina damuna da captain ni nace kar ya xo?" Shiru tayi tana kallonsa, a hankali tace "Sorry!" Daukar abincin sa yayi ya ci gaba da ci. Yana gamawa yace "Tashi ki tafi dakinta ki kwanta, am also going to bed" mikewa tayi ta fara tafiya, yace "Baby!" Kin juyowa tayi har sai da ya kuma kiranta, ta juya a hankali ya ga hawaye idonta, buda ido yayi yace "Crying?" Ta girgixa masa kai, ya kwantar da murya yace "toh gaya min kukan da kike?" Shiru tayi yace "Am waiting fah!" A hankali tace "Captain ya...." Mikewa yayi yace "Get away!" Ta juya da sauri ta tafi dakin Hafsat, kuka ta fashe da Hafsat na kallonta tace "what happened?" Tana share hawayenta tace "He shouted at me" Hafsat tace "Ohk sorry, tafi kiyi wanka ga kaya na fito maki da" bathroom ta nufa a sanyaye Hafsat ta bi ta da kallo. Tana fitowa ta saka rigar da Hafsat ta fito mata da tayi kwanciyarta. Da asuba El-ameen yayi masu knocking kofa, Hafsat ta kalli agogo don dama tuni ta tashi, biyar da minti arba'in ne, jin ya kuma knocking ta mike ta nufi kofar ta bude, kallo daya yayi mata ya juya ya bar wajen ta koma ciki ta tada Jasmine tace "Tashi kiyi sllh." Throughout ranan Jasmine a dakin Hafsat ta yini, Hafsat nata bata labarai, duk El-ameen na jinsu. A kwana biyun da Jasmine tayi gidan ba karamin sabo tayi da Hafsat ba, komai tare suke sai kayi tunanin sun dade da sanin juna, sosai Hafsat ke sonta ga tausayinta da take, duk abubuwan da tasan ya kamata gwada mata take, hakan yasa El-ameen ya d'an fara sake mata ganin yanda take kula da ita, ita kam ko a jikinta don sau dayawa idan yayi mata magana bata ma sanin da ita yake. Ran thursday da yamma suna kitchen su biyu suna girki shi kuma yana parlor aka danna bell, mikewa yayi ya isa gun kofar ya bude, Junaid ya gani tsaye, El-ameen ya shafa kai yana murmushi yace "Sai yau" Junaid bai ce komai ba ya shigo parlon, sai dai bai xauna ba yace "Tana ina?" El-ameen yace "Wa?" Junaid yace "Warce na kawo!" El-ameen xai yi magana sai ga ta ta fito daga kitchen, ta wara ido ganin junaid tace "Captain!" Karasowa tayi inda suke ta nufesa da fara'arta sai kuma ta ja ta tsaya ta fara dariya tana rufe baki tace "I missed you!" Ba yabo ba fallasa yace "Tafi ki dauko Hijab din ki" kallon El-ameen tayi sai kuma ta marairaice tace "Noo! I want to stay here Captain plss" ya wani hade rai yace "I will slap you ke da staying din" ta kalli El-ameen kamar xata yi kuka, El-ameen yace "Ae nan da can duk daya ne naga" Junaid yace "No ba daya bane" El-ameen yace "Why?" Yace "Coz a can tana xuwa makaranta...." Bai rufe baki ba tace "Toh ka kawo min kayan makarantar sai in dinga xuwa a nan ma" wani mugun kallo junaid ke mata kafin yace komai ta fashe da kuka sosai tace "This Aunt is kind, but the other one is otherwise I want to stay here plss captain!" Me El-ameen xai yi ban da dariya, cikin kuka tace "Uncle its not funny, I don't like her, I prefer staying here plss" sakin baki junaid yayi yana kallonta, El-ameen na dariya yace "Gud nd fyn tafi gun kind aunt din ki" juyawa tayi da sauri ta nufi kitchen, El-ameen ya kalli Junaid ya d'aga kafada yace "Ka kawo mata kayan makarantar ta" wani kallo Junaid yyi masa ya juya ya fice daga parlon. Washegari da safe Jasmine na kitchen da Hafsat suna girka breakfast aka danna bell, Jasmine xata fita Hafsat tace "Ina za ki?" Tace "In bude kofa" Hafsat tace "Ci gaba da aikin ki" El-ameen ne ya bude kofar, wanda ke tsaye gun ya rusuna ya gaishesa sannan yace "Captain ne ya aiko ni in dauko bakuwar da ke gidan nan, driver ne ni" El-ameen ya shafa kai yace "Kaje kace masa nace bata tashi ba" da ladabi drivern yace "Toh sir" daga haka ya juya ya bar bakin kofar, El-ameen ya rufe kofar, Jasmine dake tsaye kofar kitchen ta fito da sauri tace "Who's he uncle?" Kallonta yake daga sama xuwa kasa, sleeping gown red colour ne jikinta da ya haska farar fatar ta, ta bude ido tace "Uncle" kifta ido yayi ya karaso kusa da ita a hankali yace "Me kika ce" ta ce "Waye shi?" Murmushi yayi ya kamo hannunta ya kai bakinsa kusa da kunnenta, ta xaro ido xata koma baya taji ta jikinsa, runtse ido tayi tace "Uncle!" Ido hudu yayi da Hafsat dake kallonsu, ta juya da sauri ta koma kitchen, sake ta El-ameen yayi ya koma baya, ta turo baki tana kallonsa tace "What's that?" shafa kansa yayi ya juya ya koma daki. ta juya ta shiga kitchen tana kallon Hafsat dake soyen dankali tace "Anty!" Hafsat ta kalleta tace "Ya aka yi" shiru tayi bata ce komai ba, Hafsat ta nuna mata ruwan lipton dake tafasa kan gas ckr tace "Ki juye a flask" kai ta gyada mata ta dau flask da cup ta nufi gun gas din, tara saura suka gama, ta dibar ma El-ameen nasa ta daura a tray tana kallon Jasmine tace "Kai masa!" Shiru Jasmine tayi sai kuma ta dauka ta fita, sau biyu tana sallama ya amsa ta tura kofar ta shiga ta karasa kusa da shi ta ajiye trayn, kallonta kawai yake ta mike tace "Ga breakfast mun yi" sauke idonsa yayi yace "toh xauna mu ci" ta wara ido tace "Ni da Anty xa mu ci" ya hade rai yace "Xauna na ce" murmushi tayi ta xauna ya mike ya dauko darduma ya shimfida ya daura tray din kai ya xauna yace "Toh dawo nan" dawowo kan darduman tayi ya hada tea a cup ya bude warmer din potatoe da kwai da plantain ya dau plate ya diba yana kallonta yace "Start!" Langwabar da kai tayi tace "Toh Anty fah?" Yace "Xata ci nata ai" daukar fork din tayi ta fara cin potatoe din sannan ta mika masa, idonsa na kanta ya karba shi ma ya ci ya kuma mika mata, girgixa kai tayi tace "I will use my hand" ya lumshe ido yace "Okay" kasa cin dankalin tayi ganin yanda yake kallonta, ya buda ido a hankali yace "Eat mana" sunkuyar da kai tayi sai kuma ta mike tace "Am coming" yace "Sit!" Kamar xata yi kuka tace "Uncle am coming" yace "Ina xa ki?" Ta sauke idonta kasa tace "ina son xan dauko hijab dina am feeling cold" murmushi yayi yace "Uhun?" Ta turo baki tace "Yes" yace "Toh tafi, kar ki dawo kuma" shiru tayi tana kallonsa, yace "Tafi" mikewa tayi xata fita yace "Xo ki dauki abincin ki" ta juya tana kallonsa can tace "Why?" Yace "Am ohk" ta bata fuska tace "Toh ai baka ci ba" ya tsuke fuska yace "Na koshi" turo baki tayi tace "Baka koshi ba joor" xaro mata ido yayi yace "Xo ki dauka na ce" karasowa tayi a sanyaye ta durkusa xata dauka tray din ya fixgota ya xaunar gefensa yana kallonta yace "What are you wearing hijab for?" Kamar xata yi kuka tace "You are looking at my body" xaro ido yayi ya fara dariya yace "How?" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "What's there idan na kalle ki?" Gyara xama tayi tana kallonsa tace "But you are not my muharram!" Da mamaki ya dinga kallonta, tal langwabar da Kai ita ma tana kallonsa, sauke idonsa yayi daga kallonta yace "Who told you that?" Shiru tayi sai kuma tace "Mu'allim!" Tabe baki yayi yace "Shi kuma captain muharramin ki ne kenan?" Tace "Yes, coz he's my family, my elder brother" kallonta kawai yake can yace "Who told you that?" Tace "I know!" Yace "Then who am I to you?" Ta kallesa tace "you are captain's frnd, nd... You are our family frnd" wani kallo yake mata kafin yace "Toh tashi ki tafi" ta mike ta nufi kofa ya bi ta da ido, tsaki yayi ya mike ya shiga bathroom. Dakin Hafsat ta shiga ta ganta xaune gaban mirror tayi tagumi ta karaso ta xauna tace "Aunty what's wrong with you?" Kallonta Hafsat tayi tace "Nothing, ur breakfast is downstairs" Jasmine ta bata fuska tace "No kalli idon ki, are you crying?" Girgixa mata kai Hafsat tayi tace "Ba komai" a sanyaye Jasmine ta mike ta fita daga dakin ta koma dakin El-ameen, yana bathroom ta nemi waje ta xauna har ya fito bayan kusan minti ashirin daure da tawul, mikewa tayi ta karasa kusa da shi a hankali tace "Uncle may be Aunty is sick, she's crying" hade rai yayi yace "you are not my muharrama, how dare you come into my room just like that without permission?" Ta buda ido tace "Ohh, I....." Yace "Leave now" juyawa tayi a sanyaye ta fita daga dakin, nan corridor ta sulale ta fara kuka, ya gama shirinsa ya fito, kallo daya ya mata ya shiga dakin Hafsat ta mike ta bi bayansa, kwance ya ganta kan gado kamar me bacci, Ya tsaya daga bakin gadon yana kallonta, Jasmine ta karasa ta xauna gefenta tace "Anty na kira maki uncle xai duba ki, he's a doctor...." Bude ido Hafsat tayi ta mike xaune ganinsa, ba yabo ba fallasa yace "What's wrong with you?" Shiru Hafsat tayi, Jasmine ta matso kusa da ita tace "He said what's wrong with you" Hafsat tace "Nothing" Jasmine ta hade rai tace "And you were crying mana" El-ameen ya tabe baki ya cire bargon da ta rufe da shi tana ganin haka ta fara kokarin komawa baya ya riketa ya daura hannunsa a forehead dinta, saketa yayi ya juya ya fita, Jasmine ta bi bayansa da sauri suka shiga har dakinsa, gaban mirror ya nufa ita ma haka ta tsaya daga bayansa tace "Uncle me ye ke damunta?" Banxa yayi mata ta kuma tambayar ya juyo ya fixgota yace "Am not ur muharram ko kin manta ne!" Shiru tayi ta bata fuska, kawai gani tayi ya rungumeta ta xaro ido tace "Uncle!" Bakinsa ya kai kunnenta yace "And Captain isn't ur muharram also...." Jikinta ya dau rawa ya saketa ya fice daga dakin. Fitowa ita ma tayi ta shige wani daki ta fara kuka, har rana bata fito ba, karfe uku tayi wanka ta sa hijab dinta ta fita ta nufi gate, tafiya kawai take har ta iso main road, tsaye tayi tana kalle kallen ababen hawa dake wucewa, ko sanin yanda xata ce su tsaya bata yi ba, can dai tayi deciding ta jira motar captain, ta kusa minti sha biyar tsaye sai wasa da hijab take wani mota yayi parking gefenta ta bi motar da ido, wani ne ya fito ya kusa minti uki tsaye kafin ya karaso kusa da ita yana kallonta ya rungume hannu yace "Good afternoon!" Dauke kai tayi ta turo baki, ya karyar da kai yace "naga alamar kina jiran driver ne koh?" Kallonsa tayi tace "No motar captain nake jira in gani" ya dan wara manyan idonsa yace "Kike jira ki gani?" Tace "Eh" yace "Ohk yace maki yana xuwa ne?" Girgixa masa kai tayi, ya d'an yi shiru kafin yace "Toh ki kirasa" tace "Bana da waya" yace "Toh ga ta wa" tace "Bana da number" murmushi yayi yana kallonta yace "Ohh dat's good, to in yi dropping din ki?" Kallonsa tayi tace "Toh" sannan ta nufi gaban motar, bin ta yayi da kallo har ta bude ta shiga, ya xaga shi ma ya shiga, sai da ya hau kan titi sannan yace "Ina ne gidan ku" buda hannu tayi tace "Nima ban sani ba" kallonta yayi da sauri yace "Baki sani ba?" Kamar xata yi kuka tace "Ehh amma kamar ta can captain ya biyo, sai yayi corner" waje ya samu yayi parking don kansa ya fara rikicewa yana kallonta yace "Ya sunan ki!" Langwabar da kai tayi ta wara ido tace "Jasmine, jewel baby!" Kallonta yake ko kiftawa bai yi, can yace "Daga ina kike yanxu?" Kamar xata yi kuka tace "Uncle ne yayi min ihu ya koreni, shine xan je gidan Captain" jinginar da kansa yayi jikin kujerar motar yace "Toh fah! Amma ba garin nan kike ba koh?" Tace "Ehh Mami na ta tafi UK in ji uncle a can muke sai muka xo nan yace min?" Xaro ido yayi yace "Toh yanxu ina xan kai ki?" Tace "Mu bi ta can kila xa mu ga gidan" tada motar yayi ya bi inda tace, tafiya kawai suke da sun yi nisa sai tace ba nan bane, duk ta daure masa kai nan ya fara tunanin anya bata da disorder kuwa, fashe masa da kuka tayi daga karshe wai ita sai ya kai ta gida, can dai ya fara tunanin anya ma ba aljana ya dauko ba, dafe kansa yayi yace "Look Jasmine ni ban san gidan ku ba wllh, ya sunan brother din naki?" Tace "Sunansa captain!" Yace "Real name dinsa fa nace?" Tace "Ehh" Bude motar yayi ya fita da nufin tambayar ko akwai wani captain a anguwar, ita ma ta fito da sauri ta fashe da wani kuka tace "ni dai ka kai ni gidanmu plss" da damuwa yace "Wait! idan na maida ki inda na dauko ki xa ki gane gidan?" Make kafada tayi tace "Ni baxan gane ba gidan captain dina xa ka kai ni" xaro ido yayi yana salati a xuciyarsa, tana share hawayen fuskarta tace "Ka ji?" Hannunta ta ji an kama ta juya da sauri lokaci daya ta warce hannun, wata mata ta gani tsaye tana kallonta baki bude, a d'an tsorace ta koma kusa da shi, matar ta saki salati tace 'yar nan! Ashe Allah xae kuma hada mu" Jasmine ta turo baki tana komawa baya, shi kam kallon tsohuwar yayi yace "Yauwa mama kin san ta?" Washe baki tayi tace "Wllh na santa, kwarai kuwa na santa"