Cutarwa Book 1 complete - Chapter 18
Cutarwa Book 1 complete Chapter 18: Cutarwa Book 1 complete Chapter 18. Ummi ta ji daɗin mutuntawar da malaman da take wa kallon iyaye suka yi mata, da…
4,460 words
Ummi ta ji daɗin mutuntawar da malaman da take wa kallon iyaye suka yi mata, da nuna damuwarta kamar ta su, nasihohin su, sun shige ta sosai da sosai.
HOD yaje ajin su ummi, ya yi musu jirwaye mai kamar wanka, ta hanyar gugar zana a kan wulaƙanta ɗan Adam, da muhimmancin girmama ɗan Adam.
Ta samu sassauci daga jin wani abu mai nauyi da yake damun zuciyar ta.
Sai dai ta kasa manta kalmar gorilla, noor da Abdul suna falo suna kallon film ɗin king Kong, ummi har ta wuce ta dawo, ta ce "Yaya Abdul"
Ya ɗaga kai ya ce "Na'am yaya ummi"
"Dan Allah wai ina kama da gorilla?"
Wani irin banzan kallo yayi mata ya ce "Wace irin magana ce wannan?"
Cikin son ɓoye abun da ya faru ta ce "Amm, dama kawai na tambaya ne, dan na ji ana cewa ni mummuna ce"
"Kuma sai ki haɗa kanki da biri, haba ummi, ke tsakani da Allah idan aka ce ke mummuna ce sai ki yarda? Ki ƙarewa kanki kallo, a kan me zaki yadda ke mummuna ce? A halittar Allah babu mummuna, duk wanda ya ce miki mummuna ki ce ubansa ya sassaƙo kamar ki"
Noor ta ce "Maama kenan za a gayawa, itama tana cewa yaya ummi mummuna, kuma fa yaya ummi gashinta har nan, tafi fa maama gashi"
"Tashi ki bar nan wurin kan na tatsileki, baba suda" yayi maganar yana kallon noor.
Ummi kuma ta ce "To shikenan yaya Abdul, na gode sosai "
"Dan Allah kar ki kuma faɗar haka "
"Ba zan sake ba in sha Allah" sai dai a ranta tana jin har ta mutu ba zata manta da Nura ba, ya shiga cikin jerin mutanen da take yi wa wani irin kallo a zuciyarta.
Ƴan ajinsu ummi ba su tashi mamaki ba, sai da result ya fito na first semester, ummi ta ja magana, GPA ɗin ta 4, wanda kaf ajin babu mai wannan grade ɗin.
Kasancewar ɗabi'a ce ta ɗan adam, mu'amala domin cikar muradi, ya sanya suka fara lallaɓowa, domin shiga jikin ummi, amma fafur taƙi ta cigaba da rayuwar kaɗaici.
***
Gidan Idris kuwa, kamar masu zaman bariki, saboda faɗa zagi yana zagin hindu tana ramawa, tana kiran sunan uwarsa da ubansa tana zagi, idan yayi gangancin dukanta kuwa, ta dinga wawurar abubuwa tana kwaɗa masa kenan, dambe da zage-zage har ƙofar gida kamar dabbobi, maƙwabta suna raba su. Sulhu kuwa an yi musu shi babu adadi, amma abu ya ci tura. Sam ba ta ganinsa da mutunci, shi ma kuma haka, taje gidansu ta gaida Iyayensa kuwa ba ta wannan, saboda ta ce ba zata je gaida tsohuwar banza ba, ta ji labarin zaman da yayi da matarsa ƴar uwassa, ita ba zata lamunci cin zarafi ba.
Ya gaji da iskancinta, ya kamata yayi mata tulus da duka, ashe tana da juna biyu, ta yanke jiki ta faɗi, ƙarshe dai sai da iyayenta suka rufe Idris a police station, aka wulaƙanta shi aka kai ruwa rana kafin a sake shi, banda kuɗin magani da aka saka ya biya.
Kwana biyu da dawowar sa daga hannun ƴan sanda, ya je ya samu hashim a kan ya bashi shawara, so yake a lallaɓa kawu yahaya da ummi, a dawo da auren su.
Hashim ya ce "Haba Idris, lokacin da na din ga ankarar da kai ai kasa ganewa kayi, ummi tafi ƙarfin ka yanzu, wace irin azaba ce ba ka yi mata ba, tun tana ƙaramar yarinya. Yanzu ta sauke Alqur'ani har sau biyu, ta shiga jami'a tana karatu, ka ce ta dawo, to tayi maka me? Kai da ko kwalin sakandare baka da shi".
Idris ya waro ido ya ce "Ummin ce a jami'a, kai waye ya gaya maka?".
Hashim ya ce "Muna waya da ita, bautar ƙasa nake son na gama, idan Allah ya sa na samu aiki, zan nemi auren ummi".
Idiris yayi masa wani mugun kallo ya ce "Amma dai ka ci kai, matar da na saki zaka aura? Bazawara ce fa kai kuma baka taɓa aure ba. Haryanzu bana son ummi, ban taɓa jin ƙaunarta a raina ba, amma ina da muradi a kanta, idan har ba ta dawo mini ba, idan ina raye baka isa ka aureta ba".
Hashim ya yi murmushi ya ce "Zamu gani ai" Idris ya tashi fuuuu ya tafi.
Idris yayi shiru yana tunani, tun da mahaifinsu ya takura masa da maganar aure, ya gaya masa ga ƙudurinsa, Iya ta ce bai isa ba, ba zai auri bazawar da ƙaninsa ya saki ba, kuma ta riga ta cire ummi daga jikokinta tun da ta ƙi yarda a rufawa Idiris asiri!.
Babansa kuma ya ce Idan ya sake ɗaga maganar nan, zai yi masa abun da bai taɓa tsammani ba.
Duk son ummi da islamiyya, haka ta haƙura, saboda yanayin makaranta, ta samu wata makarantar, a nan unguwarsu, take zuwa asabar da lahadi ɗaukar karatu.
Sai dai ganin ummi tana da ilimin addini dai-dai gwargwado, idan aka yi mata ƙarin nata karatun, sai a haɗata da aji tayi musu ƙarin Alqur'ani da wasu litatafan.
Duk da ayyuka sun ƙara yi mata yawa, hakan yayi mata, saboda tana zama busy sosai, tana hana zuciyarta tunane-tunane da sukan jefata cikin damuwa.
Ga bikin Intee ya matso kusa, sai gori take sha a gidan nan, wai ta zama guzuma, babu mashinshini a haka za ta dauwwama wanke-wanke da shara.
Kawu yahaya yayi rawar gani, ya yi wa inteesar kaya na kece raini, ya so ace ta fara makaranta kan yayi mata aure, amma ta dage soyayya ta rufe mata ido, ta ce ita fa aure take so, dan haka ba yadda ya iya ya ƙyale ta.
Sagir ya danƙaro mata uban kayan lefe, kaya ba na wasa ba, ya ciko akwatuna da kaya, sai iyayi take tana rawar kai.
Albarkacin auren inteesar, a wannan karon da kawu yahaya ya yi mata ɗinki, farida ba ta ƙwace ba, har da sabon takalmi, farida kuma ta bata tsohon mayafi, kalar kayan.
Ranar party, farida ta ce ta zauna a gida, ta kula da baƙi masu shige da fice, kuma ta tsaya a kan girke-girken da za ayi.
Ummi ta zage ana can ana party, tana gida suna aikin girki, dan ita ta jagoranci aikin abincin bikin.
Ranar wuni ya kama ranar da za'ayi ɗaurin aure, dan haka da wuri motoci suka kawo ƴan gagarawa. Su Idris da babarsa, su magaji kafatanin ahalin Iya.
Lokacin ummi ba ta gidan, suna can tana ta hidima da ƙawayen inteesar, ana yi wa inteesar kwalliya.
Ummi ta yi wanka, ta yi wa noor, ta saka kayan ankonta da ita da noor.
Sai da inteesar ta kalli ummi ganinta babu mayafi, dan zata iya ƙirga rabonta da ta ga ummi babu hijjabi.
Tayi ture ka ga tsiya, ta kanannaɗe gashinta a ƙeyarta, ɗaurin ya zauna cas a kanta, ga ɗinkin ma dai-dai jikinta.
Ta shafa man leɓe, ta yafa mayafinta a kanta, ta rufe jikinta sosai, ta kama hannun noor, suka fice.
Wani irin farinciki ya kama ummi, ganin ƴan gida gaba ɗaya sun zo, dan rabonta da su tun da ta baro gagarawa.
Duk bin ummi suka yi da kallo, yadda ta girma ta zama budurwa.
Cikin su ummi ta shiga tana gaishe su, Iya sai wani hura hanci take yi.
Ta ce "Ina yaya magaji?"
Sa'adatu ta ce "Sun tafi wurin ɗaurin aure".
Ummi ta karrama su da abinci, dan matar gidan ba ta ta su take yi ba, ta kai su ɗakinta, ta yi ta ɗawainiya da su. Bayan azahar su Hashim suka dawo daga wurin ɗaurin aure, ummi baki yaƙi rufuwa saboda duk ƴan uwan mahaifinta sun zo. Ɗaya bayan ɗaya ta din ga gaishe su, suna mamakin yadda ta girma, ta zama cikakkiyar mace, sai dai ko kusa bata kalli in da Idris yake ba.
Farida sai bin ummi take yi da kallo, dan ba ta taɓa tsayawa ta kalli ummi sosai cikakken kallo ba sai yau, rashin gyara ne ke ƙara munanta ummi, idan ka kalleta sau ɗaya sai ka sake kallonta, mussaman yadda take kokowa da mayafin, kasancewar ita ba ma'abociyar ta'amalli da shi ba ne ba.
kasancewar hashim shi ne mutumin ummi, can harabar gidan suka koma, suna ta hira.
Ya dubeta ya ce "Ummi, kawu yayi miki magana kuwa a kan batun nemo mamanki?"
Cikin sauri ta ce "A'a, ya ake ciki?"
"Subhanallah, ya ce dai kar na kuskura na gaya miki saboda wani dalilinsa, amma dai idan bai ganta ba yana daf".
"Ya salam, bai gaya mini ba, ko maganar zan yi masa?"
"A'a, dan ya yi mini kashedin kar na gaya miki, ki kwantar da hankalinki duk abu zai haɗaku".
Cikin karaya ta ce "Yaushe hankalina zai kwanta, tana raye amma rabona da ita kusan shekara goma sha, ina son ganinta".
Idiris kuwa wani abu ne ya din ga yi masa zillo a maƙogwaronsa, ganin ummi tare da Hashim, gashi ta gayar da kowa, amma ko sashin in da yake ba ta kalla ba, balle ta gaishe shi. Kasa daurewa yayi, ya nufi in da suke zaune.
Sai dai ummi na hango shi, ta miƙe tsaye ba tare da ta gama maganar da take yi da Hashim ba.
Cikin zafin nama ya sha gabanta, ya kalleta ya ce "Ina zaki je? Saboda wulaƙanci ki ka gaida kowa baki iya gaisheni ba, kuma na taho da ki ka ga nan zan zo, shine ki ka tashi".
Cikin ƙwayar idon Idris ta kalla, wani abu mai kama da wuta yana zafi a ƙirjinta.
Tuni idanunta suka tara hawaye ta ce "Cikin abun da bana ƙaunar sake gani a nan duniya har da lahira, har da fuskarka, ka matsa ka bani hanya, ko kuma in yi maka abun da baka taɓa zato ba!"
Whats app only please 🙏 Ayshercool. 08081012143 *CUTARWA!*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
P21
FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK.
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu Abduljalal Wata kissar sai mata Wuta a masaƙa Cutarwa Ƙanwar maza Gaba da gabanta Aƙidata Ruɗin ƙuruciya
Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata. 08081012143.
And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link. https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Ayshercool.
PAID ADVERT!.
Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku
Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi Man garan gashi Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921
*TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*
BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.
21
Mamaki ne ya cika shi, har sai da ya bayyana a kan fuskarsa, bai taɓa tunanin ummi za ta iya furta abun da ta gaya masa ba, saboda tun fil azal tamkar sokuwa take ba ta da wani karsashi balle ta yi faɗa.
Bai gama nazarin ba, ta angije shi tayi wucewarta tana tsaki, abubuwan da suka faru a baya, suna sake dawo mata tamkar yanzu suke faruwa.
Ƙarshen cin mutunci da tozarci yayi mata a garin nan, wanda yana daga dalilan da ya sanya ba ta ƙaunar sake zuwa gagarawa, haryanzu baƙin ciki da mugun tabon da take da shi a garin, yana damunta.
Dan har cikin zuciyarta tana fatan a gidan duniya, Allah ya yi wa Idiris abun da ya yi mata kafin ya koma ga Allah, ba ta sani ba ko a gaba ta iya yafe masa, amma har zuwa wannan lokacin, ba ta ji alamar manta abun da yayi mata ba, balle ta yafe masa.
Ranar da ya fara kwana a ɗakinta, ya korota waje, ta kwana cir a tsaye ruwa yana dukanta, saboda mugunta da zalunci.
Tayi iya ƙoƙarin ta wurin danne hawayen da ke ta ƙoƙarin zubo mata, ana ta hotuna, angon inteesar sagir, da kansa ya ce ummi ta zo ayi musu hotuna.
Idiris ya jinjina kai, tare da tabattarwa da kansa zaman birni, da kuma zuwa jami'a ne ya sanya ummi lalacewa, domin kuwa an ce dama ƴan matan jami'a ba su da mutunci lalacewa suke yi.
Duk in da ummi tayi sai ya bita da kallo, tamkar wani shashasha, hindu da yake yi wa kallon wayayyiya kyakykyawa, yanzu duk ta tararraɓe, haihuwa uku tayi, har da waccan mai sunan Iyan, ƙirjints da yake ɗaukar hankalinsa, duk sun zube, kullum daga ciki sai shayarwa.
Amma yanzu ummi komai nata a tsaye kyam, dai-dai da jikinta, duk da tana ta rufe jikin nata da mayafi.
Bayan la'asar suka ce zasu yafi, dan ba su zo da niyyar kwana ba dama, saboda sanin halin farida.
Duk lalacewar naka naka ne, ummi ta ji daɗin zuwansu sosai da sosai, tayi ta yi musu fatan alkhairi har suka tafi.
Idiris kuwa kamar maye, saboda azabar kallo, har suka ɗauki hanya suka tafi.
Kallo ɗaya zaka yi wa rahama da yaronta, ka san ba a kwanciyar hankali take ba, ga dai kuɗi miji yana da shi, amma yarkace-yarkace hak take, dan hatta kayan sawa wasu lokutan farida ke bata ko ta sayawa ɗan, duk wannan ƙafafar da ikon babu shi, duk ta zama so silent.
Taro ya watse, aka kai amarya, ummi kuma ta sake cin uban aikin gyaran gida, ranar monday kuma ta tafi makaranta.
Gaba ɗaya jikinta a mace yake, da ƙyar take tafiya ma duk jikinta ciwo, saboda azabar aikin da ta sha, ba ta samu damar hutawa ba, a haka a tafe har gajiyar ta ware.
Karatun ummi yayi nisa, kuma haryanzu ba a samu wanda ya doke point ɗin ta ba, duk da ba ta fasa fuskantar ƙalubale ba.
Dan haryanzu farida da kausar ke cin ƙaniyarta.
*** Tana zaune ta duƙufa tana ta aikin shirin dutse, ɗanlami yayi masa jagora har cikin ɗakin da take zaune. Ɗakin tsaf da shi, sai ƙamshin turare yake yi, kai ba ka ce mara lafiya ce a ɗakin ba. Ta ɗaga kai ta kalleshi, ta sunkuyar da kanta ta cigaba da aikin gabanta.
Ya ɗan ƙare mata kallo, shekaru sun ɗan ja, ta girma yanzu, amma tsaf da ita, tana samun kyakywar kulawa.
Ya dubi ɗanlami ya ce "Ɗan uwa, kuma a haka ba ta da lafiya?"
Yaya ɗanlami ya ce "Babu lafiya, wasu lokutan dai hankakin yana dawowa, wasu lokutan kuma sai ciwon ya dawo tayi ta shirme. Amma a hakan nan da take, za ta yi wanka, tayi shara tayi kwalliya ga shirin dutse nan ma gashi ka ganta tana yi, likita ne ya ce a samo mata abun da zai din ga ɗebe mata kewa. Ka ga yanzu tafi sati ba ta yi magana ba, ba ta duka ba ta zagi, kaga daga mutuwar mijinta, ga rabata da ummi, ta zo ta haihu ɗan ba rai, tayi jijjiga depression yakamata sai kuma dai ta samu matsala gaba ɗaya. Ban taɓa tunanin wani daga dangin baban ummi zai biyomu ba, dan mun yi alƙawarin ba zamu sake zuwa ba, irin jafa'i da mugun bakin da mahaifiyar ku tayi wa ƴar uwarmu, ya sanya muka ce gara mu yanke alaƙa da ku kawai".
Dr. Yayi ajiyar zuciya ya ce "Tun da na ɗauki yarinyar nan, nake fafutukar neman ina ku ke, ni ban san garin nan ba, ainihin in da kuka zauna aka aureta, mun je aka ce ba kwa nan, abubuwa dai duk ba su yi daɗi ba, sai fatan Allah ya kyauta".
Mama da yaya maryam da suke gefe suka amsa da amin, dan maryam ta zo gida yau, babu tsammani suka ga kawu yahaya.
Maryam ta ce "To ya ummin take? Ba ka zo mana da ita ba?"
Ya girgiza kai ya ce "Ba yanzu ba, ummi na nan a jami'a".
Yaya maryam ta ce "Dan girman Allah, ummin?"
Yayi murmushi ya tashi ya ƙarasa gaban ta ya zauna yana kallonta, ba tare da ta ɗago ba tayi murmushi ta ce "Baban ummi"
Ya ce "Na'am".
"Jigidata da ka tsinka mini nake gyarawa"
Sunkuyar da kai suka yi cike da jin kunyar abun da ta faɗa, dan tafi sati ma ba magana.
Yayi murmushi ya ɗebi dutsen da take ta shiryawa ya ce "Gaskiya ban kyauta ba, ki haɗa wata maza".
Ta sake yin murmushi ta ce "Da na san zaka dawo, ai da na yi kitso, an yi mini lalle, kaina ba kitso, bana son kitso tun da ka tafi bana son kitso" tayi maganar tana cire hular kanta, gashin kanta baƙi wuluk ya bayyana.
Yaya maryam zata yi magana, ya ɗaga mata hannu tare da girgiza mata kai, ya ce "To tun da na dawo yanzu sai ayi ko?".
"Ba zan yi ba, tun da ka tafi ka bar ni, ka ƙi ka dawo, Iya ta ƙwace mini ummi, ɗa na ya mutu ka ƙi ka zo ka ganni kuma bani da lafiya" tayi maganar tana kuka wiwi.
Ya ce "To ki yi haƙuri, ki yi haƙuri ba zan sake tafiya naƙi dawowa ba"
Ta riƙo hannunsa ta na cigaba da kuka ta kwantar da kanta a hannunsa ta ce "Baban ummi"
Ya amsa mata da "Na'am"
Ta ɗaga kanta ta kalleshi ta ce "Ka je ka karɓo mini ummina, Iya ba zata din ga yi mata wanka ba, ko idan yamma ta yi ta saka mata kayan sanyi, ba ta son ummi, dan Allah baban ummi ka karɓo mini ummi, kaga katifata ta ishemu ni da ita, idan ka sai mana gida sai in dawo gagarawa ko?"
Ƙura mata ido yayi, cike da matsanancin tausayinta, lallai yana daga horon da za ka yi wa uwa, ka rabata da ɗan ta, duk da tana cikin hauka, amma ba ta manta da ƴar ta ba.
Yayi ajiyar zuciya ya ce "To shikenan, ki daina kukan ya isa haka, mayar da hularki, kiyi haƙuri" ta ɗauki hularta ta saka.
Ta ja bakinta ta sake yin shiru.
"Zan kawo miki ummi in sha Allah, amma ba yanzu ba".
Yaya maryam ta ce "Saboda me? Abun da ta daɗe tana jira kenan, ka taimaka".
Ya ce "Ina da dalilina, kuyi haƙuri dan Allah"
"To amma mu ai ka bari muje in da take".
Kawu yahaya ya ce "Da ina da ƙudurin rabaku da ummi, da ba zan neme ku ba, ina da hujja mai ƙarfi sosai. Zan cigaba da shiga lamarin nemawa mariya magani in sha Allah, komai zai daidaita kuma zai wuce".
Ba haka suka so ba, amma ba su san takamaimai menene dalilinsa na ƙin haɗa su da ummi ba.
*** Hangen dala ba shiga birni ba, domin kuwa inteesar tayi zaton soyayyar da suka sha da sagir a waje, ita za aje a cigaba da yi a gidan, sai abun da take so shi zai din ga yi mata, amma ina. Ya nuna mata shi namiji ne, mage mai kwanciyar ɗaukar rai, a gida ta saba ba abun da take yi, ummi ce take komai. Yanzu kuma ya ce shi ba zai ɗauki ƴar aiki ba. Dan haka sai komai ya din ga bata wahala, asubar fari zata tashi ta haɗa masa breakfast, gashi su yi ta faɗa dan abincin nata ba daɗi, ga almubazzaranci kamar ba mace ba. Ga rashin kunya da rashin iya magana, gashi ɗan uwan mata, yana da tarin yayye da ƙanne mata, ga uwarsa mai shegen sanya ido. Sai ƙannensa su zo gidan su fi sati, gasu manya duk sun girmeta, su yi ta yi mata rashin mutunci, idan tayi magana su ce za su yi mata dukan tsiya.
Abun duniya ya damu inteesar, ta dawo gida tana kuka, ta gayawa mamanta.
Farida a zatonta zata iya maganin abun, ta kira Sagir tana masifar dan me ba zai tsawatarwa ƙannensa ba? Ya ce mata ba zai iya ba, baya son ya saɓawa mahaifiyarsa.
Abu kamar wasa aka fara jamb, kawu yahaya ya turawa inteesar kuɗi, ya ce taje tayi jamb, a nema mata admission. Amma sagir ya ce ba yanzu ba, sai ta haihu, domin kuwa a lokacin ma laulayi take yi.
Kawu yahaya bai matsa ba, farida ta din ga masifar dan me ba zai dage sai inteesar ta fara makarantar yanzu ba?
Ya bata amsa da "Yanzu ya fi ni iko da ita, shiyasa tun tana ƙarƙashin ikona, na so ta fara makarantar, yadda bai isa ya hana ba, amma ku ka dage, dan haka ni ba abun da zan ce".
*** BAYAN WANI LOKACI!.
Kasancewar tsakiyar damuna ne, an ɗan kwana biyu ba a yi ruwan sama ba, dan haka ana tafka zafi, ga uwar rana da ake ƙwalawa.
Tamkar ba ita ranar ke duka ba, haka take tafiya sannu a hankali, tana ratsa layukan unguwar, sannu a hankali take tafiyar, tamkar tana tausayin ƙasa, kamar mai rangji haka take tafiyar kamar tana tausayin ƙasa.
Ta cikin niƙabinta take kallon dogon layin, tare da lissafa sauran tafiyar da ta rage mata, ta isa in take fatan zuwan.
Layin shiru, sai lokaci lokaci, ababen hawa ke giftawa, manyan gidajen layin ko ina a rufe.
Ƙarar babur ta ji, kasancewar gefen hanya take bi, ya sanya ko a jikinta, dan ko waiwaya wa ba ta yi ba, ashe layin da yake gabanta yake ƙoƙarin shiga.
A ɗan fusace ya ce "Ke, kurma ce ne? Sai mutum ya tureku, ace bai kyauta ba, ba ki ji ina horn bane?"
Ta tsaya cak, ta ɗan ja wasu seconds, sannan ta juyo ta kalleshi ta cikin niƙab, sai dai ba ta ce komai ba.
Maimakon ya wuce ya tsaya ya ji me za ta ce, idan rashin kunya za ta yi masa, ya ƙare mata ta tas.
A hankali ta ce "Sorry, ga hanya wuce" tayi maganar tana ɗan ja baya ta bashi hanya.
Fuskar ta a rufe da niƙabi, amma muryarta ce ta saka shi ƙara kallonta.
"Malama idan zaki ware murya ki ware, da na bugeki ai ba zaki maƙale murya ba".
Ta ce "Ikon Allah, me muryata kuma tayi maka, ai na ce ka yi haƙuri ka wuce"
Tsaki yayi ya ja babur ɗin sa ƙirar lifan, ya yi gaba.
Ita kuma ta yi ajiyar zuciya, ta cigaba da tafiya.
A ƙofar ƙaton gate ɗin gidan ta tsaya, mutum biyu ta tarar sanye da uniform na security, suka dubeta suka ce "Gurin wa zaki je?"
Ta ce "Habu baka gane ni ba?"
Jin muryarta ya sanya shi cewa "Ahha wata sabon gani, ke dama kina duniyar nan?"
Ta ce "Ina nan mana, ya aiki ya kwana biyu?".
"Alhamdilillah, gaba ɗaya tun da ƙawarki ta bar gidan nan muka daina ganinki"
"To ai gashi na zo wanke laifina yau, ina fatan mami na nan?".
Ya ce "Eh tana ciki" Ta ce "Yauwwa na gode" ya buɗe mata ƙaramar ƙofar gate ɗin, ta shiga ciki.
Ɗayan ya kalleshi ya ce "Ka barta ta shiga? Baka kira hajiya bilkin ba, kuma ba ta ɗaga niƙabinta ba".
Habu ya ce "Ai ƴar gida ce, ƙawar maryam ce, tun da tayi aure ne ta daina zuwa".
Ya ce "Ok, na so ta ɗaga niƙabin naga fuskarta, muryarta tayi mini daɗi".
"Ji ɗan wahala, ka sani ko yanzu tayi aure, ka shiga hankalinka".
Ummi kuwa sashin mami ta nufa, fasalin gidan yana nan yadda yake, amma yanayin fentin da aka sassauya masa da wasu abubuwan zaka san arziki ya fi na da.
A falo ta tarar da mai aiki, duk da ƴar bata san ƴar aikin ba, suka gaisa sannan ta tanbayeta ko mami tana nan.
Mai aikin ta ce "Eh, tana falon sama"
"Ki ce mata ummi ce ta zo" mai aikin ta jinjina kai ta nufi ƙafar benen ummi kuma ta zauna.
Bai kai mintuna biyar ba, mai aikin ta saukko, ta ce wa ummi ta shiga.
Ummi ta tashi ta bi bayan ƴar aikin.
Da sallama ummi ta shiga, mami ta waiwayo tana cewa "muryar wa nake ji ne haka? Gaskiya koma nayi fushi"
"Tuba nake mami"
Sai dai tana zagayowa, ta tarar da na kan babur da ya kusa tureta da lifan, yana zaune ya barbaje ƙafa a kan centre table, sai yanzu ta gane a in da san shi. Sai da ya ɗan sake ɗaga kai ya kalleta shi ma.
Nan suka gaisa da mami, mami nata mitar ummi ta ɗauke ƙafa ta daina zuwa tunda maryam ta bar gidan.
Ummi ta kalleshi ta ce "Ina wuni?"
Ya basar ya ce "Lafiya ƙalau"
Mami ta ce "Laaa ka amsa kuwa? Kema meyasa ki ka gaishe shi? Ƙaninku ne fa, ƙanin maryam ne Raihan ne. Kai kuma ka amsa kamata yayi fa ka gaisheta" ya wani basar.
Ummi ta ce "Ƙyaleshi mami, ai dama su Allah ya bawa girman" tayi maganar tana ɗaga niƙabin fuskarta.
Sai yanzu shima ya ganeta, ranar saukarsu da maryam a makaranta.
Mami ta ce "Ya wani je ya tara gemu, yafi kowa girma kai ka ce wani babba ne, ni wannan gemun ina tantama idan ba mai ya shafa ya fito ba, dan ga gemun nan dai, amma hankali da saura".
Ummi ta yi murmushi ta ce "Girma ya riga hankali kenan" sai da ya ɗan buɗe baki jin abun da ummin ta faɗa.
Mami ta ce "Eh mana, ya makaranta ummi?".
Ummi ta ce "Mami makaranta muna jiran result"
"Masha Allah, lokaci ba wahala har kin gama ummi, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi, to ya batun aure kuma? Ko invitation ki ka kawo mini?".
Ummi ta sunkuyar da kai, tayi murmushin yaƙe ta ce "Tukuna dai mami"
Mami ta ce "Ya salam, Allah ya kawo nagari ummi, yanzu fa maryam kusan shekarar ta bakwai da aure, ke kuma shiru duk ƴan islamiyyar ku sun yi aure, saura ke, amma kar ki damu komai lokaci ne"
Ummi ta ce "To mami, bari na yi alwala dan Allah"
Mami ta ce "To shikenan ba damuwa, je ki yi"