Cutarwa Book 1 complete - Chapter 48
Cutarwa Book 1 complete Chapter 48: Cutarwa Book 1 complete Chapter 48. Babansu ya kalli Idris ya ce "Ka ga illar bujirewa iyaye ko? Matar da aka aura…
4,476 words
Babansu ya kalli Idris ya ce "Ka ga illar bujirewa iyaye ko? Matar da aka aura maka, ka wulaƙanta ta bayan ka yi abun kunya, ga wadda ka ke so ɗin abun da take faɗa a kan kakarka, mun gode amma in Allah ya yarda zaka gani, kuɗin nan da ka cinye sai sun hanaka kwanciyar hankali " aka din ga bashi haƙuri, a kan kar ya yi wa Idris baki.
Ummi ta ƙara tsorata da lamarin rayuwa, da yadda take tsoron Iya da Idris, abun ba a cewa komai, amma kallesu yanzu abun tausayi, da gari banza ne da iya tana nan tana ta zagin jikokinta tana tsine musu da sun motsa, ga tsinuwar nan tana ta tasiri a tsakanin su yanzu.
Ummi ta tashi ta fita tana amsa wayar raihan, a ƙalla ta kai mintuna arba'in, sai ga ta dawo da receipts a hannunta.
Ta miƙawa ƙanwar iya ta ce "Gasu nan, na biya duk abun da yakamata ayi mata, za su yi mata".
Ta waiwaya ta kalli Idris ta ce "Kai kuma, daga nan zan je in kai ƙararka wurin ƴan sanda, duk in da kuɗin nan suke ka dawo da su, dan ba wanda za a ƙara tursasawa shan wata dauɗar gora, da ake shanye ta wasu a ƙi shan ta wasu, shi ma auwwalun duk in da yake sai an nemo shi"
Kamar su shige cikin ummi, suka din ga zambaɗa mata godiya, Iya kuwa ta ƙure ummi da ido.
Ummi ta zauna a kusa da ita, ta ciro kuɗi, ta saka mata a cikin hannunta ta ce "Na san da magana a bakinki iya, amma ki sani ban yi miki wannan abun, dan na burgeki ba, ko ki so ni, bana fatan ko da ƙiftawar ido na yi abun da zai saka ki so ni ko na burgeki, tun da wanda na yi a baya ma babu riba. Na yi miki ne kawai saboda zatin Allah, kuma saboda kin haifi mahafina, mutumin da ki ka azabtar kamar ba ke ki ka haife shi ba, saboda abun duniya, saboda waɗan nan" tayi maganar tana nunawa Iya kuɗin hannunta.
"Yanzu dai ba ya duniyar, mummunar ƴar sa da baki tabattar ko daga tsatsonki take ba, cikin hukuncin Allah ya rufa mata asiri. In sha Allah ba zan bari ki yi wulaƙantcciyar jinya ba, saboda babana bai wulaƙanta mini uwa ba, ke ma ba zan wulaƙanta ki ba, amma ki sani hakkin zuriyarki da ki ka raba kansu da kanki ne, ki ka gama tsine musu yake bibiyar ki. Allah ya baki lafiya, duk abun da Allah ya yassare mini, zan din ga turawa yaya magaji"
Kamar munafukai haka duk suka duƙar da kai, ta gama maganganun ta, ta tashi ta ce wa su Abdul su tafi.
Idiris hankalinsa ya tashi da ya ji ta ce ƴan sanda, dan ya tsorata da lamarin ummi, tun da ta saye gidansu na gado.
Abdul suna tafe a hanya, suna tattaunawa a kan yadda familynsu yake ƙara rushewa, saboda jahilci da rashin background mai kyau.
Can uganda dr. Ya cigba da karatunsa, idan baya nan yaran abokinsa suna shiga su taya mariya zama. Duniyarsa kawai yake ci da tsinke, yana samun duk abun da yake so daga gareta, ba tare da fargabar tashin hankali ko abun da za a buƙata daga gare shi ba.
Sai dai ƙasan zuciyarsa babu daɗi, yadda kausar da inteesar suka haɗe kai da babarsu, suka daina shiga sabgarsa, ko gaishe shi da suke yi a waya suka daina, daga noor sai Abdul sune suke ta tasa, sai kuma ummi.
Dan ƙarewa ma farida blocking ɗin sa ta yi a what's app.
Tun abun yana damunsa har ya watsar, ya cigaba da addu'a tare da rungumar amaryarsa hannu bibbiyu, ya ji hakam kamar samun salama ne daga rashin mutuncin farida.
Ga mariya da tsantsar ladabi, dan haryanzu wasu lokutan abubuwan ta irin na da take yin su.
Bayan tafiyar ummi, a ka yi wa Iya hoton ƙwaƙwalwa, cikin kanta lafiya ƙalau, sai dai tsananin damuwar abubuwan suke faruwa ya sanya jininta yin mummunan hawa.
Likitoci suka yi iya bakin ƙoƙarin su, aka sallamota a kan magunguna.
Bayan sun koma gida, aka kwantar da ita aka shiga jinya, saboda ba ta iya yi wa kanta komai, ita ma jinyar tun da aka yi mata ta marmari, aka fara ƙosawa.
Idris kuwa ya din ga bin ƙannen babansa yana roƙonsu a kira ummi, a bata haƙuri kar ta kai shi wurin ƴan sanda.
A ranar da ya koma gida daga asibiti, ya samu hindu ya din ga zaginta da ci mata mutunci, a kan maganganun da ɗahara ta ce ta faɗa a kan Iya.
Hindu ta ce "Duk tsohon dai bai ji kunyar hawa jaki ba, jaki ba zai ji kunyar kayar da shi ba, tun da ba uwata ba ce ta je ta mutu ba abun da yayi mini zafi, matar da ba ta da mutunci. Wai kai har ka na da bakin magana ma, tun kan ka dawo har gida aka zo aka bani labarin ka cinye kuɗin maganinta, kai ba ka ga laifinta ba sai nawa, sai ka fara yi wa kan ka masifar ai"
Kamar yadda suka saba, haka suka yi ta faɗa su na cece ku ce.
*** Anty rakiya kuwa, ta samu mami ta din ga surfa mata bala'i, ta in da ta shiga ba ta nan take fita ba, wai ta biyewa tsoron dangin miji, za a raba musu zumunci.
Ta ɗauki gaba da ita, gaba ɗaya ta rasa abun da yake yi mata daɗi, ta na ji tana gani raihan yanzu ya koma mata kamar wani baƙo, sam ba ya sakewa da ita, saboda kar ta yi wata magana a kan ummi, kusan abun da take gudu shi yake shirin faruwa, ummi ta mallake mata ɗa.
Dan labari yana isheta cewar, kullum raihan status ɗin sa, yabon ummi ne tare da koɗata, dan ita ya riga ya rufeta daga gani.
Ta fuskanci sam fushinta da shi ba ya tasiri a kan sa yanzu, dan ya fi zuwa wurin hajiya ma yayi al'amuransa, ga wata irin muguwar shaƙuwa tsakaninsa da Salim yanzu har ma da Sagir.
Hakan ya ƙara mata tsananin tsanar ummi, da duk da abun da take yi wa ummin, ta kan kira waya ta gaisheta, tayi girki ko ta bayar da abu ta ce a bata, ta wulaƙanta amma tun da abun nan ya faru, ummi ba ta ƙara shishshigin raɓar in da take ba.
Aka gama gyaran gidan dr. Da idan sun dawo za su tare da mariya, daga can ƙasar ya turowa ummi kuɗi, a kan ta yi mata sayayya ta haɗa da kuɗaɗen hannunta, ta din ga yi mata sayayya. Dan ba ƙarya hannun raihan a sake yake, kuma yana sakar mata yadda yakamata, kuma ita ma na ta hannun a sake yake.
Tun da aka yi scanic aka tabattar wa su ummi, yara biyu ne a cikinta, raihan yake murna, kuma ya gargaɗe ta a kan kar ta kuskura ta gaya wa kowa. Suka yi ta shiri, tare da sayen kayan jarirai.
Sai dai cikin yana wata bakwai, kamar ummi za ta durƙusa ta haihu, saboda girma, kullum cikin lissafin kwanakin da suka rage take yi, saboda yadda nauyin cikin yake damunta, idan ta zauna sai an ɗagota saboda girman cikin.
Gefe guda kamar yadda ta yi alƙawari, tana tura wa yaya magaji kuɗi lokaci zuwa lokaci, saboda kula da Iya.
Farida ba ta haƙura ba, wurin bin bokaye da malamai, a kan lallai sai an raba auren dr. Da mariya, kuma a sake mallake mata shi ta juya shi fiye da yadda take yi a baya.
Sai dai abun da ba ta sani ba shi ne, duk da kallon mahaukaciya tuburan take yi wa mariya, a hakan ba ta wasa da addu'a, mace mai son addini sosai da sosai, dan yana ɗaya daga abun da ya sanya ta ƙara shiga ran dr. Sosai da sosai.
Hajiya ita ta maye wa ummi gurbin sirika, dan kusan har role ɗin uwa take yi mata playing, kusan kullum tana tafe zuwa duba ummi, ko yi mata aike take, tana tausayin ummi sosai da sosai, saboda abu ne na fari ba ta san ya yake ba, tana yawan cewa ummi "Anya ummi ba zaki likitoci su ƙara caje cikin nan ba, girmansa yayi yawa tubarkallah" sai dai tayi murmushi, ba tare da gaya mata haƙiƙanin abun da yake cikin ba.
Ummi ta daina fita ko ina, gashi ta ƙara zama mafaɗaciya, saboda damuwar ciki. Kasancewar Hajiya na gaya wa raihan sai yayi haƙuri da ummi, a wannan stage ɗin mata masu ciki na fuskantar saurin fushi, dan haka sam baya damunsa, shi tausayi ma take bashi.
Duk tsaftar ummi, sai da zamana dogon gashin nan sai ya kwana uku babu taza, kusan kullum sai dai ta saka kaya masu sauƙin nauyi yadda iska za ta wadace ta, takalmi kuma idan ba over size ba duk haushin takalman take ji.
Da safe ta fito, tana ta mita noor ba ta ɗumamata shinkafa ba, wai ita ba ta cin abun da ta dafa.
Noor ta ce "Ke fa ki ka ce ba kya son warin shinkafa"
Kamar tayi kuka ta ce "Haba noor, amma tun jiya na ce miki zan ci, yunwa nake ji, ina magana kina kallo kin yi mini banza"
Noor ta ce "Ai Yaya ummi ban san yaya zan yi miki na burgeki ba, MD ne kawai yake iya miki, ni ba ni na ɗora miki nauyin cikin nan ba, amma ki yi ta yi mini faɗa. Kuma sai na koma gida tun da faɗa ki ke yi mini"
Ummi ta marairaice ta ce "Haba noor, to ki yi haƙuri dan Allah kar ki tafi, wai ni ya ku ke so in yi?"
Raihan da yake bayanta ba ta sani ba, ya kama dariya, ba wuya ta bayar da haƙuri, ba wuya kuma ta fara kuka.
Ciki duk ya mayar da ita wata iri, sai dai bai sanya ta daina kyau a idonsa ba.
Yayi gyaran murya ya ce "Ya aka yi ne yau ke da noor ɗin taki ku ke faɗa"
A shagwaɓe ta ce "Wai tafiya za ta yi"
Ya ce "Haba nooriya, uwa guda ki tafi ki bar ƴar ta ki?"
Noor ta tura baki ta ce "Faɗa take yi mini, kai ma fa shaida ne ta ce ba ta son shinkafa, wai yau kuma shinkafa za ta ci, wai ta gaya mini jiya da daddare, ni ina na ganta jiya da daddaren?"
Ummi ta ce "Ni duk kun tsane ni, baku san me nake ji ba, ko tausayina ba kwa ji"
Raihan ya ce "Mu mun isa, mu kuwa muke ƙaunar ki, jeki ki yi wanka ki shirya, har noor tare zamu tafi office yau, kya ji daɗin jikinki"
Ta juya tana hararar noor, noor ta kama dariya ta ce "Na fasa tafiyar yaya ummi"
"Ki yi ta tafiyar ma, ina ruwana" suna lallaɓata suna yi mata dariya. Aka ba ta ɗunamen shinkafa ta ci hankalinta ya kwanta.
Tare suka tafi wurin aiki, fitowar ta yi mata daɗi tana kallon titi.
A can wurin aikin, suna zuwa a parking space noor ta ga motar Salim.
Sun shiga take tuna masa wulaƙancin da ya yi mata, ta zo ganinsa.
Yau bai biye mata ba, ya ce "Allah ya baki haƙuri, kar na tanka cibi ya zama ƙari"
Ma'aikata na ta gaishe shi, yana amsa musu cikin mutuntawa.
Wani mutum ya taso, ya tare su ya durƙusa a gaban raihan yana dan Allah maigida ka taimaka mini da aikin sharar nan ko masinja, nafi wata ina zuwa an hana ni ganinka, ina cikin mummunan yanayi na babu da fama da rayuwa, dan Allah ka taimaka mini.
Ummi ta zubawa mutumin ido, raihan ya kalli ummi ya ce "ya dai? Kin san shi ne?"
"Ishaq Abdulkarim magashi" ta faɗa jiki a sanyaye, mutumin ya ɗaga kai yana kallonta.
A rikice cikin tashin hankali mutumin ya ce "Salma Muhammad Bashir, ke ce da ma ke ce? Kina nan dama" ya fara maganar cikin kame-kame.
"A ina ki ka san shi?"
Ummi ta ce "Ɗan ajinmu ne a University"
Raihan ya ce "Ɗan ajinku? Amma yake neman shara?"
"Wallahi yallaɓai korata aka yi daga makaranta, dan Allah ka taimaka mini"
Raihan ya ƙare masa kallo ya ce "Kana cikin wanda ku ka din ga muzanta mini mata kuna makaranta ko?"
"Dan Allah ka yi mini rai yallaɓai, lamarin Allah kenan, gashi yau ina neman alfarma a wurinta, na yi nadama dan Allah ki yi haƙuri ki yafe mini"
Gwiwoyi a ƙasa yake yi musu magiya, ummi ta ce "Kar ka damu, ba ni nake ɗaukar aiki ba, ni abun da ya faru ya wuce a wurina, wannan wurin kuma ba ni da hurumin ɗaukar ka aiki, idan ya baka haka nake fata, idan bai ba ka ba ka yi masa uzuri wataƙila babu vacancy ne" daga haka ta ja jikinta ta yi gaba zuwa office ɗin raihan.
Ba ta san yadda suka ƙare ba, shima da ya zo office ɗin bai gaya mata yadda suka yi ba, noor ta ce "MD a ina yaya Abdul yake?"
Raihan ya ce "Ai ba a nan branch ɗin yake ba, yana sharaɗa shi".
"To ina first born?"
Ya kalleta ya ce "Wa kenan?"
"Yaya Salim mana, ba ka san last born yake ce mini ba, shi kuma first born?"
Raihan ya yi dariya ya ce "Ni ina zan sani, baya nan"
Noor ta ce "Na ga motarsa fa"
Ummi ta ce "Kai noor, me zaki yi masa an ce miki baya nan"
Raihan ya ce "Da gaske kin ga motarsa?"
"Wallahi na ganta"
Raihan yayi murmushi ya ce "Yaya hukuma sai da rarrashi, office fa na bashi, nake ta bin sa ina yi masa magiya, ofishin kula da ma'aikata da ladabtar da au na bashi, ya ce ba ya so ba zai yi ba wai wata sana'ar zai yi. Na ce Alhaji ya saka baki, amma ya ƙi shi ne yau ya zo ban sani ba, ko ma ya neme ni, bari na je office ɗin nasa na duba"
Noor ta bi raihan har office ɗin da Salim yake, sai haɗe rai yake yi.
Ya kalli raihan zai yi mita, sai ya ga noor a bayansa, sai kuma ya saki fuska.
Raihan ya ce "Yaya ashe ka zo ɗin ban sani ba".
"Eh da ka je ka haɗa ni da hajiyan Bauchi ko?"
Raihan ya sosa kai ya ce "Tuba nake babban yaya, with due respect kuma kai ne mataimaki na zan ɗebo sauran ayyukan da nake gabatarwa, na kawo maka zuwa next few months kuma, i will step down ka yi taking over"
Salim ya yi masa wani mugun kallo ya ce "Raihan ba ka da hankali ko? Tayaya makakke zai jagoranci wannan abun, kai da ka ke a nutse ma kana fama"
Noor ta ce "Ahh ba ka daina ba? Ka ce mini ka rage sosai ai" Raihan yana ja da baya yana dariya ya ce "Yauwwa noor gaya masa dai"
Kwanaki suka cigaba da tafiya, wasu rayuwarsu na daidaituwa, wasu kuma suna girbar abun da suka shuka.
Ummi ta shiga watan haihuwa, dr. Suka dawo ya kammala karatun da zai ba shi damar zama professor.
Duk wanda ya kalli mariya ya san ta samu kwanciyar hankali, shi kamaa dr. Ya canza.
Bai sauka a ko ina ba sai tsohon gidansa, in da za su zauna da mariya, gida yayi kyau ummi ta gyara komai.
Abdul ne ya ɗaukko su daga airport ma, farida sam ba ta san ma sun dawo ba.
Ummi ta yi wa Allah godiya, ganin mama cikin ƙoshin lafiya da kwanciyar hankali.
Dr. Ya ce noor ta kwana tare da mariya, duk da jikinta yayi sauƙi sosai da sosai, shi kuma ya tafi can gidansa, sai dai ko kallon kirki bai samu daga farida ba, balle karɓa mai kyau.
Tana saka ran asirin da ta yi ya ci shi, ya biyo ta yana lallaɓata, amma ta ga ko ta kanta bai bi ba shi ma, yayi wanka ya shiga ɗakinsa ya hau bacci.
Tsananin takaici da baƙin ciki ya sanya ta je ta tashe shi da masifa, har da iƙirarin sai ta kashe mariya, bayan ta gama ci mata mutunci da kiranta mahaukaciya.
"Wallahi farida ban taɓa gaya miki ba, amma yau zan faɗa na yi dana sanin aurenki farida, baki da tarbiyya ko kaɗan. Suffar da ki ka mu'amalance ni daban kan na aureki, wadda ki ka nuna mini bayan auren daban. Wallahi na yi dana sanin rashin auren mahaukaciyar da ki ke faɗa tuntuni ta fiki sanin darajata. Wallahi ki ka kuskura ki ka yi mata wani abu, a shirye nake da kowa ya kama gabansa da ni da ke, ba zaki kashe ni ba wallahi" ta dafe ƙirji tana zazzaro ido "Da can ba ka san bani da tarbiyya ba sai da ka auri mahaukaciya?"
"Na sani mana, kara nake yi miki ina yi miki kawaici, ke kuma ba kya gani, gara na fito miki a mutum, ina kuma jaddada miki, idan ki ka kuskura ki ka taɓa mariya kin taɓa igiyar aurenki, dan ba zaki cutar da abun da nake samun farinciki daga gare shi ba".
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, na shiga uku wallahi yahaya kai butulu ne, azzalumi ni ka ke gaya wa haka?"
Dr. Ya ce "Ke ki ka so, ai ni ban san tuntuni kamar a kurku nake ba, sai yanzu na yi ƴanci ai. Ke ki ka janyo duk abun da na yi miki, ke ma kin san na yi haƙuri da ke, kuma bani da niyyar cutar da ke, amma halinki ya fara kaini bango"
Gaba ɗaya farida ta ji duniyar tayi mata zafi, komai ne naman ƙwace mata.
Washegari dr. Ya shirya ya tafi gagarawa duba iya, babu yadda bai yi da mariya ba, ta ce masa ita fa ko rasuwa iya ta yi ba za ta je ba. Sam mariya ba ta da zafi, amma tun da ta faɗi haka ya san abubuwan da iya tayi mata suna cigaba da ƙona mata zuciya ne, dan haka ya ƙyaleta.
Ya je ya tarar an mayar da iya asibiti, babu wata kulawar kirki, babu jinya mai kyau tana iya magana amma ba sosai ba, sai ta yi zawo har ya fara bushewa a jikinta ba a ɗagata an gyara ta ba.
A wannan karon mariya ta matsa sosai a kan lallai sai ta je sun gaisa da maman raihan.
Raihan ya sanar da Alhaji, Alhaji ya ja wa mami kunne sosai a kan kar ta kuskura ta wulaƙantawa ummi uwa.
Mai hali baya fasa halinsa, dan sai da tayi abun da mariya ta fuskanci akwai wani abu a ƙasa, Hajiya kuwa ta karramata sosai da sosai.
Sai dai mami ta yi mamakin ganin maman ummi, sam ba baƙa ba ce ba ga dogon hanci har baka.
Sati biyu da dawowar su dr., Ƴan maiduguri suka zo ganin gidan mariya, suka din ga murna ganin yadda ta yi ƙalau da ita.
Bayan ummi ta koma gida daga gidan mariya, cikin dare naƙuda ta tayar mata.
A cikin daren ita da raihan suka tafi asibiti, dan noor ta gudu wurin mariya, wia sai ummi ta haihu za ta dawo, yanzu ta zama masifaffiya.
Da safe raihan ya kira waya ya sanar suna asibiti, sai dai haihuwa ta gagari ummi, ga ciwo amma labor baya gaba, duk ta galabaita, likita ya ce sai dai ayi mata aiki.
Alhaji ya ce lallai sai mami ta je asibiti ita ma, ayi komai da ita ai matar ɗanta ce.
Ummi ta tayat da hankalinta, ta din ga kuka tana cewa tsoro take ji, duk aka kewayeta ana rarrashinta.
Noor kuma tana gefen ta tana tayata kukan.
Ummi ta kalli mariya, ga mama matar kakanta, ga Anty maryam, ga hajiyar su raihan, ga Abdul ga raihan kansa har da Salim, ga Nihal ƙanwar raihan, ana rarrashinta. Duk da mami ita sai yatsuna fuska take yi.
A ranta ta ce "Allah sarki, haka family suke dama? Kowa ya damu da kai" wani irin farinciki ya cika mata zuciya.
Ta ce sai dai a shiga aikin har da raihan, idan mutuwa za ta yi ya riƙe hannunta.
Mami ta ja wani uban tsaki, raihan kuwa ya riƙe hannunta yana ta kwantar mata da hankali.
Raihan ya kasa zaune ya kasa tsaye, aka shiga da ummi, awa guda da wani abu, aka fara fito da jarirai, mace da namiji.
Sai dai hankalinsa ba a kansu yake ba, Ummi yake jira a fito da ita.
Yana nan tsaye aka turo ta a kan gado idonta a rufe, an rufeta da green ɗin yadi.
"Salma" ya kira sunanta da ɗan ƙarfi.
Ta buɗe ido tare da riƙe hannunsa ta ce "Ka yi magana a hankali mana, ban mutu ba" yayi dariya ya durƙusa ya sumbaci goshinta ya ce "Thank you very much sweetheart, Allah ya baki lafiya"
Can waje kuwa ana ta murna an fito da jarirai, mami ta kallesu ta ce "Taɓ, wannan wane irin yara ne, mu kaf danginmu babu wannan kalar, meye wannan?"
Ayshercool 08081012143.
CUTARWA!
AYSHERCOOL
(BRIGHT PENS)
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
49
PAID ADVERT
*Hajiya ina zaki? Saurin me ki ke yi haka? Ɗan bani aron mintuna biyu kacal, na gaya miki albishir ɗin da na zo miki da shi. Shin ko kin san sirrin sheƙin fatar ummi, da ya sanya ta kama zuciyar MD raihan ta hana shi sukuni? Kai ba ma skin care ba, har da sirrin gyaran gashi, ina masu fama da amosani, karyewar gashi ko kuma sanƙo, jan gashi ne da ke? Ko taurin gashi kamar soson ƙarfe. Idan matsalar ki budurwar fata, tare da rashin glowing, Annur skin scrub da hair bliss sun shirya tsaf domin magance muku kukanku, me ku ke jira ku tuntuɓe su a kan lambar wayar su dan ƙarin bayani 07045971194 ko 08140450950*
49
Tsit kowa ya yi ya zuba wa mami ido, tana wani yatsune fuska.
Hajiya ta ce "Amma meyasa zaki ce haka? Wannan ai ba magana ba ce ba"
"Eh na faɗa, ko a dangina kin taɓa ganin irin wannan?, kalli kalar uwarsu ki kalli raihan ki kalli yaran".
Jajawur yaran, haskensu ya wuce ace hasken raihan kawai suka ɗaukko, gasu manya sosai, kuma kansu ƙwal babu gashi, kuma ba su da gashin gira ko kaɗan sai alamarta.
Mariya cikin jin kunya ta ce wa Hajiya "Bari na gansu"
Aka miƙa mata yaran, ta zuba musu ido tana murmushi sannan ta kalli mami ta ce "Hajiya, ai yaran nan da babansu su ke kama, haka na haifi ummi, Iya ta din ga ce mata aljana, sai dai kwana biyu kanta ya cika da gashi ko anty maryam, sai dai ummi tun tana jaririya baƙa ce".
Wani mugun kallo ta yi wa mariya ta ce "To ni danginmu babu irin wannan abubuwan, ni ban taɓa ganin jarirai a haka ba, danginmu dai kaf babu mai wannan farin"
Nan da nan Maryam ta harzuƙa ta ce "To mu namu akwai, duk tsiya dai ai na ɗanki ne ba wani ba"
"Ba ni da tabbas, ni ɗa na ma ba shi da cikakkiyar lafiya"
Hajiya da ta fara fusata ta ce "Ke dai ya rainawa hankali, dan ya tsallake son zuciyarki"
Mariya ce ta din ga basu haƙuri.
Raihan kuwa yana can ɗakin da aka kai ummi, sai zuba yake yi yana yi mata kalamai masu kwantar da hankali da ƙwarin gwiwa.
Likitan da yake yi mata allura ya ce "Maman twins ai ba Kya buƙatar maganinmu, wannan kalaman sun ishe ki warkewa" suka din ga dariya, sai da bacci ya ɗauke ta sannan ya tafi ɗakin da su Hajiya suke.
Noor ji take kamar ta kwaɗawa mamin raihan mari, ko karar ganin idon mariya bai saka ta yi alkunya ba.
Abdul da yake ɗakin ya tashi ya fita, Salim ma surutun ya ishe shi, ransa ya fara ɓaci.
Mariya ta kalli Salim ta ce "Salim, dan Allah jariran nan ba da babansu suke kama ba, dan Allah kar ki saka zargi a kansu tun suna jarirai, su sha wahala kamar ummi, idan ta tashi ta ji, ba za ta ji daɗi ba".
Salim ya ce "Mama, muna murna muna fatan Allah ya bawa ummi lafiya, mun gode wa Allah kyautar da ya bamu" ya ƙarasa maganar yana yi wa mami mugun kallo.
Kamar daga sama raihan ya shigo ya ce "Hajiya ba ni su na gansu"
Hajiya ta maze kamar babu abun da yake faruwa ta ce "Tun yanzu ka fara nuna wariya, ka tafi wurin matarka ko ɗaukar su ba ka yi ba" cikin washe baki ya ce "Tuba nake, dole in fara zuwa kanta, saboda su an yanka mini mata" yayi maganar ko a jikinsa yana ɗaukar su, wanda hakan ya sake ƙular da mami.
Ya ce "Tubarkallah, Hajiya irin idon ummi ne da su, brown masu kyau masha Allah, yaya ka ga namijin kallesu duk farare. Alhamdilillah" yayi maganar yana kallon Salim.
Farincikin da mariya ta gani a fuskar raihan, sai ya mantar da ita takaicin abun da mami ta yi musu.
Sauran mutanen maiduguri da suka zo ganin gidan mariya, suka cika asibitin. Ana jimawa ma sai ga dr. Ga Alhaji.
Raihan ya din ga sanar da ƴan uwa batun haihuwar.
Tsabar takaicin yadda raihan yake rawar ƙafa, ya sanya ta tashi ta bar asibitin.
Sai da ummi ta yi awa shida tana bacci, sannan nurses suka tasheta, suka ɗagata aka wanke ta, sannan aka bata abinci. Ta saka kaya tayi kyau, kamar ba ita ba, sannan aka turo ta a kan gado aka mayar da ita main ɗakin da take.
Suka din ga murna ganin an fito da ummi ras da ita.
Sai jerawa ummi sannu ake yi, aka miƙo mata yaran dan ta shayar da su, amma ta kasa saboda yadda ido ya yi yawa.
Hajiya tare da Salim suka koma gida, ta yi wanka ta yo girki, suka dawo da Alhaji.
Shi ma Alhaji baki buɗe yake ta murna, yana yi wa jariran addu'a, duk da babu wanda ya gaya masa abun da matarsa ta yi.
Sai dai noor ta gaya wa ummi, abun da mamin ta ce, wanda ba ƙaramin ciwo yayi mata ba, sai dai ta basar saboda tana cikin murnar kyautar da Allah ya bata.
Ummi ta ce "Mama, jikin yaran nan kamar jariran mage, basu da gashi kwata-kwata".
"Me ki ke ci na baka na zuba? Zai fito in sha Allah"
Dr. Ma da daddare ya zo ganin jariran, tare da yi mata sannu.
Kusan kwanaki uku, ana ta shigowa ana fita duba ummi, a kwanaki ukun nan gashi ya cika kan yaran nan fal.
Kwanan ummi biyar, aka sallame su daga asibiti, raihan ya ce bai yadda a ɗauki hoton yaransa ba a saka a waya. Saboda masha Allah kai ba zaka ce ummi ce ta haife su ba, dan sun fi kama da larabawa sosai.