Cutarwa Book 1 complete - Chapter 8
Cutarwa Book 1 complete Chapter 8: Cutarwa Book 1 complete Chapter 8. An doshi shekaru huɗu, da rasuwar Bashir, ummi ta cigaba da rayuwa ba tare da ta sake…
4,496 words
An doshi shekaru huɗu, da rasuwar Bashir, ummi ta cigaba da rayuwa ba tare da ta sake sanya idonta ana mahaifiyarta ba, tamkar baiwa a cikin gidan nan haka take rayuwa, babu gata babu kulawa, wahala ta yau daban ta gobe daban, ga Iya ta tsiri yi mata kunu ranar asabar da lahadi ta kai kasuwar garin, ta sayar mata, har ma wasu su yi abun sayarwar su a gidan su haɗa mata. Babu yadda Hashim bai yi da iya ba, a kan ta daina ɗorawa ummi tallar nan, azabar da take sha tayi yawa, amma iya ta zage shi tsab, ta ce idan ya cigaba da yi mata katsalandan, za ta ci mutuncinsa ta tsine masa.
Babu kunya ba tsoron Allah, Iya ta saka aka ɓalle ƙofar ɗakin mariya, aka kwashe kayanta aka sayar, ta karɓe kuɗin, wai da su zata tarawa ummi kayan ɗaki, ɗakin ya zama wurin tara itace, hatsi da sauran shirgi.
Ummi ta dawo daga makarantar boko, takalminta ya kusa rabewa biyu saboda tsufa ƙasansa kuwa ya huje, malaman su, sun gaji sun ƙyaleta, ƙafarta futu-futu. Ta tarar da Iya a tsaye tana jiran isowarta.
Jiki a sanyaye ta ƙarasa in da Iya take, ta ce "Iya laifi na yi ne?"
"Au tambayata ma ki ke yi, saboda tsabar kin shahara, nan gaba makami zaki fara nuna mini, ki yi mini ƙwace, kuɗina zaki bani da saminu ya zo jiya da daddare, ban gan su ba, kuma daga ni sai ke a ɗakin"
Gaban Ummi ya faɗi, ta girgiza kai ta ce "Wallahi iya ban ɗauka ba, ki sake dubawa".
"Ni ki ke gaya wa na sake dubawa? Ƙarya zan yi miki kenan? Ki zo ki bani kuɗina kan jikinki ya gaya miki"
Ummi kawai tayi shiru tana kallon iya, dan ta rasa me za ta ce mata ma, ta san kawu saminu ya bata kuɗi jiya, amma ba ta san ma a ina ta ajiye su ba.
"Au saboda kin mayar da ni ƴar iska ki ka tsaya kina kallona, ba zaki bani kuɗina ba?"
Ummi ta sunkuyar da kai, dan gaba ɗaya kanta ya kulle.
Iya ta saɓa mayafi ta fice, jiki a sanyaye ummi ta ƙarasa cikin ɗakin iya, ta hau duddubawa, ko za ta ga in da Iya ta ajiye kuɗin.
Maganar Iya ta jiyo da idris ta ce "Ka tambayeta ina ta kai mini kuɗi, ka yi ta dukanta, har sai ta faɗa" kan ummi ta ankara sai ganin idiris ta yi a kan ta, hannunsa riƙe da manyan reshen bishiyar darbejiya.
Kafin ta yi magana, ya shiga shimfiɗa mata tsumagiyar nan a jikinta, gashi ya tare duk wata hanya da zata bi ta fita. Kasancewar dama haushinta yake ji, ya sanya ya zage duk wani ƙarfin sa, ya dinga jibgarta, har da taka ta da ƙafa.
"Fito mini da ita daga ɗaki, ɓarauniyar banza da ta wofi, kuma daga yau kin bar kwanar mini a ɗaki" a ƙasa haka ya din ga jan ummi, ya fito da ita tsakar gida.
"Ga ɗakin uwarta can da ake tara itace yanzu, rufe mini ita a ciki, ko abinci kin daina ci, sai kin bani kuɗina"
Haka kuwa aka yi, idris ya rufe ummi a ɗakin mariya, da yanzu ake tara itace da hatsi a ciki, ya rufe ɗakin bisa umarnin iya.
Ummi ta kwanta a ƙasa, jikinta sai zafi yake yi, hannunta da Idris ya din ga hauri da ƙafarsa, tamkar ba a jikinta yake ba, hannun yayi sanyi ga ciwo yana yi nata.
Sai da ummi ta kwana ta wuni a cikin ɗakin nan, shima magaji ne ya ga baya ganinta, ya matsa da tambaya, su Alhassan suka ce masa ai Iya ta sacewa kuɗi dubu goma sha biyu, ta saka idiris ya zane ta, aka kulle ta a ɗaki.
Hashim ya ji kamar ya ɗora hannu a ka yayi ihu, ya buge kwaɗon, ya tarar da ummi a zaune a takure wuri ɗaya, saman idonta ya kumbura, ko ina jikinta rauni ne. Dogon gashin nan duk ya kwashi datti da karare.
"Ummi" ya kira sunanta, ta ɗago ta kalleshi ta sunkuyar da kai.
"Da gaske kin ɗaukar wa iya kuɗi"
Ta girgiza masa kai, ya ce "Na san ba zaki ɗauka ba ummi, yi haƙuri taso ki fito"
Ta girgiza masa kai ta ce "Dan Allah yaya magaji ka ce Allah ya sa na mutu, bana son zama da iya, dan Allah ka kai ni wurin mama, wallahi zan mutu" tayi maganar tana sheshsheƙar kuka.
Ya kalleta yarinya shakaf, amma tana iƙirarin ta mutu, "Ba zaki mutu ba, wuya bata kisa ummi, tashi kar wani abun ya cije ki" Da ƙyar ya fito da ita daga ɗakin.
Iya kuwa duk ta gama barbaɗawa mutanen gidan ummi ta sace mata kuɗi.
Ko kallonsu Iyan ba ta yi ba, ya nemo abinci ya bata, ya ce tayi wanka.
Tana banɗaki, Hashim ya samu Iya ya ce "Iya dan Allah meyasa ba kya ƙaunar ummi ne?"
"Kamar yaya, in haifi ubanta ka ce bana son ta? Tarbiyya nake bata, uwarta na tsana ne, bana ƙaunar uwarta ne, kuma alamu sun nuna halin uwarta ta yi"
"Ba wannan ba, Iya kin duba ɗakin nan da kyau baki ga kuɗin ba? Ummi bata taɓa yi miki sata ba fa?"
"In ji uban wa? Faɗa ne kawai ba na yi, amma sata kam ba yau ta fara ba, kamar ta sha nonon ɓeranya"
Zai yi magana ummi ta fito daga wankan, tana ɗingisa ƙafarta.
Bai cewa iya komai ba, ya tashi ya bata kujera ta zauna, ya kamo hannunta da ya kumbura, ya fara matsawa a hankali. Nan ta din ga yarfe hannu tana kuka.
Fatar ummi duk wannan wahalar da take sha, jikinta tamkar auduga saboda taushi.
Iya ta watso mata ƙullin kayanta, ta ce sai dai ta koma ɗakin itace ta cigaba da zama.
Babu magiyar da magaji bai yi mata ba, amma ta ce bata san zancen ba.
Da kansa ya share wa ummi ɗakin, ya samo buhu ya shimfiɗa mata, ya kawo tabarma ya shimfiɗa mata, ya din ga rarrashin ta, yana bata haƙuri, ji yake kamar ya zauna ya yi wa ummi kuka.
Iya ta aika a kirawo mata Alhassan zata aike shi, ta ce ya duba ƙasan katifarta ya ɗaukko ɗari biyu, Alhassan ya fito da wata leda a hannunsa ya ce "Iya ba wannan kuɗin ki ke nema ba?"
A razane ta karɓa tana ƙifta masa ido, gaba ɗaya ta manta ina ta ajiye su.
Hashim yayi kamar bai ji me ta ce ba, haka ummi, sarai ummi ta ji Alhassan yana gaya mata kuɗinta, duk wasu kalaman rarrashi, sai da Hashim yayi amfani da su, wurin ba wa ummi haƙuri, saboda ƙarfin hali, har da Murmushin ta, tare da ƙoƙarin nuna bakomai.
Da daddare ya sayo gyaɗa da rake, ya kai wa ummi, duk cikin son ya ƙara rarrashin ta, ya daɗe yana sake kallon ɗakin da zata kwana a ciki, babu ko fitila a ɗakin, kuma ba za a rasa ƙwari masu cizo a ciki ba.
Ya kalli ummi ya ce "In sha Allah zan sayo miki fitila, sai ki din ga haskawa, sannan tun yamma ki din ga karkaɗe ko ina, ki tabattar babu wani abu a ɗakin kan ki kwanta".
"To yaya na gode" ya jinjina mata kai ya fice.
Iya tana kallonsa daga tagar ɗakin ta, yanayin yadda yake shishshigewa ummi, abun ya fara ƙular da ita, dan haka tayi ƙwafa, tare da aniyar ɗaukar mataki a kansa.
Sai dai can ƙasan ranta, ta ji babu daɗi ganin kuɗin da aka yi, gashi ta riga ta saka an zane ummin, an rufeta a ɗaki kwana da wuni, ba tare da hakkinta ba. Haka nan abun ya din ga damunta, da safe ummi ta je har ɗaki ta gaisheta, da uniform za ta tafi makaranta.
"Kin karya ne zaki tafi makaranta?"
Ummi ta ce "A'a"
"Ki je wurin sa'adatu ta zuba miki kunu idan ta dama" ummi ta ɗan yi shiru ta tuna yadda sa'adatun ke haɗe rai idan ta je karɓar kunun.
Ummi ta ce "Na san idan na je ya ƙare"
Iya ta bankaɗa ɗan tofinta, ta ciro naira ɗari, ta ajiye wa ummi ta ce "Gashi nan ki sai waina a hanya ki ci"
Ummi ta kalli kuɗin, tana wani irin murmushi da ita kaɗai ta san ma'anarsa, ta miƙe tsaye idonta fal hawaye ta ce "Ki bar shi iya, idan na dawo na ci abincin" tayi waje.
Tana jin Iya na zazzaga mata masifa, tana zaginta, amma tayi waje tana share hawaye.
"Ƴar ƙanƙanuwarki da ke, kin san munafunci, to kin yi wa kanki, halin uwar taki da nake ta gudu sai da ki ka kwaso shi? To ki ci kanki, da ke da mugun halin naki" Haka iya ta cigaba da sababi da kame-kamen borin kunya.
Ummi na tafe a hanya tana kuka, haka ta ƙarasa makaranta, suna ta shirye-shiryen shiga sakandare, sun kusa zana jarrabawar common entrance, shi ma kuɗin jarrabawar da ƙyar, ta biya, shi ma Naima ce ta zo gida, ta sa aka kirawo ta, take ta yi mata tambayoyi da ƙyar ta gaya mata batun kuɗin jarrabawar.
*** Manema na ta zuwar wa mariya, duk da ba fita take yi ba, amma mariya tayi burus, mahaifinta ya kaɗa ya raya, amma taƙi tsayar da kowa, da yayi mata zancen auren ma sai ta hau koke-koke. Yayi ta rarrashin ta, a tunanin sa ko saboda tsohon mijinta ya sanya take jin ba zata sake yin aure ba, yayi nasihar, yayi rarrashin saboda kusan shekaru huɗu kenan rabonta da aure. Kuma shekarun nan huɗu cif, ita ba mai lafiya ba ita ba mara lafiya ba. Takura mata da maganar aure, ya sanya ta daina cin abinci ma, ta ƙara tsananta kaɗaice kanta, ga rashin barcci da ya sarƙafe ta, ta wuni ciwon kai dare yayi ta kasa bacci.
Tsananin ciwon kai ya sakata a gaba, gashi tayi shiru ba wanda ta gayawa, abu kamar wasa tun tana daurewa har ta kasa, ta din ga burgima a ƙasa tana wayyo kanta.
Sai a lokacin suka san ba ta da lafiya, aka kaita asibiti, sai dai babu cigaba, idan an kaita asibitin sai an tursasata shan magani, idan ta sha ɗin ma babu cigaba, wasu lokutan haka zata riƙe kanta tana ihu, tana kuka saboda rashin iya bacci, idan aka kaita asibiti sai dai su yi ta yi mata allurai.
Ƙarshe aka tura su ganin likitan ƙwaƙwalwa, hankalin mahaifin mariya ya tashi da ƴan uwanta, jin an tura su ɓangaren likitan ƙwaƙwalwa.
Likita ya duba ta sosai da sosai, ya basu shawarar a kula da ita sosai, saboda depression ne ya kamata, idam ba a kula da ita sosai ba, za a rasa hankalinta gaba ɗaya.
Karo na farko da iyalan su mariya suka ji mahaifinsu yayi wa wani ɗan adam Allah ya isa, wanda sai da ya zubar da hawaye, yana matuƙar tausaya wa mariya, dan haka bai gaza ba, ya sake tashin yaya magaji, tare da Maryam, ya ce su je su bawa uwar mijin mariya haƙuri, ko sau ɗaya ta bayar da ummi, ta zo ta kwana biyu tare da mariya, ko a samu hankalinta ya kwanta.
Yaya magaji ya ce "Baba, ka san matar nan ba zata bayar da yarinyar nan ba, sai dai a tafi da mariyar, ta je ta ganta mu dawo"
Maryam ta ce "A hakan zamu tafi da ita? Ba zai yiwu ba ai, kana kallon abun da take yi, ai salon ta sake jin daɗi ne, dan matar nan ba mutunci ne da ita ba, kuma muddin aka bawa mariya ummi, ba zata bari a sake rabata da ita ba, a ganina kawai mu mayar da hankali a kan nema mata lafiya"
Yaya magaji ya ce "Duk da haka, zan jarraba zuwa, duk da na san ba zamu wanyeta ƙalau ba, amma zan jarraba zuwa na ga yarinyar ma daga nan, Allah sarki ummi, na san yanzu ta yi wayo sosai.
"Zata shekara goma zuwa sha ɗaya fa yanzu, ai ta zama budurwa"
Suka bar maganar a kan cewa, yaya magaji zai je ya gano ummi, idan ya ga fuska ya sako zancen tahowa da ummi.
Ummi ta daina zuwa ɗakin iya idan ba dole ba, saboda gudun kar ace ta yi wani abun, kullum cikin itace nan da buhhunan hatsi take kwana. Tsabar daka kuwa hannunta duk yayi kanta, yayi ta ɗurar ruwa yana fashewa, saboda tana da taushin fata sosai.
Tana tafe tana yada hannu, saboda gajiya ga rana, yunwa da ƙishirwa duk sun addabeta, mutumin da ta hango a ƙofar gidan su ne tare da kawu Ilyasu, ya sanya ta tafiya a hankali, ta ƙarasa ƙofar gidan.
Shi ma ƙuri yayi da ido, yana kallonta, ta ƙarasa ta durƙusa ta ce masa "Ina wuni?"
Jiki a sanyaye ya amsa ya ce "Ummi kin gane ni?" Ta jinjina masa kai alamar eh.
"To waye ni?"
Maimakon ta bashi amsa sai ta ce "Ina mama?"
"Haryanzu baki manta da ita ba?"
Da sauri Ummi ta sake kallonsa ta ce "Da ita ku ka zo?"
"A'a, na zo dai neman alfarmar na tafi da ke na kai ki wurinta, amma sun ƙi yarda"
Kawu Ilyasu ya wani haɗa rai, cikin haushi kamar tsohon kare ya ce "Ke! Tashi ki wuce ki shiga cikin gida"
Ƙafafuwanta suka yi mata sanyi, ta ji tamkar ba zasu iya ɗaukarta ba"
"Ba zaki tashi ba?" Ya sake yi mata tsawa. Cikin rawar jiki ta tashi, yaya magaji ya kamo hannunta ya danƙa mata kuɗi, yana riƙe da hannunta ya kalli Kawu Ilyasu ya ce "Da ku da mahaifiyarku, ku shirya amsar da zaku bawa Allah, kalli wai wannan ƴar ɗan uwanku ce dan abun kunya, kalli kayan makarantar da suke jikinta, kalli ƙafafuwanta. Kun ce idan na tafi da ita babu ku babu ita, ku ba dangin mahaifinta bane ba, duk in da aka je aka dawo, da dangin uba ake ado, kuma ba zan cigaba da jayayya da ku ba, muna raba abun faɗa, Allah zai zama gatan marainiya"
"Ummi ki kula da kanki kin ji ko? Ki yi ta yi wa mamanki addu'a, hankalinta yana kan ki, Allah ya yi miki albarka".
"Wai ba zan sake ganinta ba?"
"Zaki sake in sha Allah, Allah ya shiga lamarin ki"
Rirriƙe hannunsa tayi tana kuka, tana yi masa magiyar ya tafi da ita.
Da ƙarfin tsiya kawu Ilyasu, ya fizgi hannunta, ya angizata zuwa cikin gida.
Tana kuka suka ƙarasa shashinsu, sai dai da munanan kalaman iya ta fara cin karo, tana ɗaga murya tana cewa "Ni dai azo a nema mini magani, a rabani da wannan dangin maitar da jaraba, sun kashe mini ɗa suna bibiyata saboda ƴar su na hannuna, ba dole mariya ta haukace ba, ai kaɗan ta gani, hauka bata ma fara shi ba, tun shekarun baya da na karɓi ƴar ba ta yi haukan ba sai yanzu, Allah ya ƙara tuburata, yadda ta rabani da ɗa na babu ita babu sukunin duniya!!".
Bright pens fans group, da sauran masoya ummin Iya, ina ganin sharhinku, ina godiya sosai da sosai 🙏🙏🙏
Ayshercool 08081012143 *CUTARWA!*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
BRIGHT PENS (FREE BATCH)
P9
Gaba ɗaya Ummi ta ji ƙafafuwan ta sun yi mata sanyi, har suna neman gaza ɗaukarta, tayi ta maza ta ja jikinta ta shiga, kai tsaye ɗakin da take ta wuce, ba ta tsaya a in da Iya ke banbaminta ba.
Wucewar ta bai sanya Iya jan baki tayi shiru ba, sai ma haƙiƙancewa da tayi, tana cigaba da masifa "Ni dai na gaji da wannan maitar da masifar, dole in miƙe in nemi tsari da bala'i da tashin hankalin wannan mutanen su daina yi mini sintiri da bibiyata, ba dole mariya ta haukace ba, hakkin ɗa na ba zai taɓa barinta ba, daga haka ma in Allah ya yarda sai ta fara yawo tsirara, ni bai dame ni ba, hakkina da na ɗa na ba zai bar ta ji daɗin rayuwa ba, hauka ma yanzu ta fara ba ta ga komai ba tukuna".
Ummi ta ja ta tsaya a cikin ɗakin, tana ƙare masa kallo, kasancewar haddar yaro ƙarami, ba abu ne da yake gogewa cikin sauƙi ba, ya sanya take ummi ta shiga hasaso abubuwa da dama da suka faru a ɗakin nan.
Yanayin jeren ɗakin, ƙamshin turaren wuta ɗan tsinke da mamanta ke yawan kunnawa, yadda take zama a kan cinyar mahaifinta ta ci abinci, yadda daren da aka yi mata fyaɗe ya kasance, ko ba komai ummi ke iya tunawa ba, ba ta manta yadda mamanta take iya ƙoƙarin ta wurin yi wa Iya biyayya, ta kalli yadda ɗakin ya zame mata a yanzu baƙi ƙirin, tamkar dajin da wuta ta cinye bishiyun da suke ƙawata shi.
Durƙusawa tayi ta fashe da kuka tana sheshsheƙar kuka, tana jin Iya na cigaba da ci wa mahaifiyarta mutunci, tare da yi mata fatan masifa kala-kala da aibantata da sharruka.
Ummi ba ta samu fitowa daga ɗakin nan ba, sai daf da la'asar, dan ma Allah ya taimake ta zuwa makarantar allo da take yi, ana horasu a kan kula da ibada, wanda dama ta samu wannan horon daga mahaifiyarta, amma dan ta Iya, ko za ta shekara ba ta yi salla ba, babu ruwanta da ita.
Ta yo alwala ta dawo ɗakin tayi azahar da la'sar, ko tunanin zuwa makarantar allon ba ta yi.
Tana jiyo yadda duk wanda ya shigo sai Iya ta gaya masa ai Mariya ta haukace, tana can an sakata a turu, hakkin rai yana bibiyar ta, ta fara bi bola-bola tana tsince-tsince.
Ummi ta sha kuka, sai da idanunta suka kumbura, dan duk kukan da za ta yi idonta baya ja, sai dai ya ɗan sirka, kuma su kumbura.
Ta kalli kuɗin da yaya ɗanlami ya bata, ta watsar da su a tsakar ɗakin, ta ƙanƙame jikinta, tana sauke numfashi hawaye na tsiyaya daga idonta.
Ba tsammani ta ga magaji a kanta.
"Ummi" ya kira sunanta a hankali.
Ta ɗaga kai tana kallonsa. "Kukan me ki ke yi?"
"Yaya magaji"
"Na'am ummi".
"Wai mamana ta haukace?" Tayi maganar wasu hawayen na gangarowa saman kumatunta.
"Subhanallah waye ya gaya miki haka?"
"Wanda ya tafi da ita ne yazo, shi ya bani wannan kuɗin"
Hashim ya ce "Kar ki sake cewa ta haukace, bata da lafiya dai, tana ganin likitan ƙwaƙwalwa aka ce"
"Likitan ƙwaƙwalwa? An ce sai mutum ya haukace fa ake kai shi wurin likitan ƙwaƙwalwa"
"Ba haka bane ba"
"To meyasa Iya take cewa mama ce ta kashe baba, ba hatsari yayi ba?".
"Ki daina damuwa da maganar Iya, ki kwantar da hankalinki, ki ta yi wa mamanki addu'a Allah ya bata lafiya"
"Dan Allah yaya magaji ka kai ni wurinta, ina son in ganta dan Allah" tayi maganar tana haɗe hannayenta alamar magiya, tana kuka.
Cikin matsanancin tausayinta ya ce "Ummi Maiduguri ba nan ba ce akwai nisa, kuma ban san a ina mahaifiyarki take a Maiduguri ba, lokacin da aka aureta muna yara, kuma kin ga ba taɓa zuwa muka yi ba. Amma ki yi haƙuri ki daina kuka, zan bincika miki in sha Allah"
"Gidan uwarka zaka bincika mata, munafukin Allah ta'ala, to kar ka fasa, wallahi magaji idan ba ka kiyaye ni ba, sai na hau kujerar tsiya na ci ubanka la'ada waje a kanta, kar ka fasa kai ta inda uwarta take, zaka ga cin mutuncin da zan yi maka, dai-dai nake da kai. Kema tsohuwar munafuka, halin uwarki haka halinki yake, duk wannan ƙoƙarin da nake yi a kanki ba kya gani, da ki ke hannunmu mutuwa ki ka yi? Kowa yazo sai ki ɓare baki, ke a kai ki wurinta, tun da namanki nake gutsura in ci, to ki cigaba kar ki fasa, amma ki sani nayi alwashin yadda mariya ta rabani da ɗa na, ke da ita har abada, sai ta ɗanɗani abun da ta ƙunsa mini, wannan kuɗin na meye?" Tayi maganar tana nuna kuɗin da ummi ta watsar a wurin.
Hashim ya ce "Yayan babarta ne ya bata"
"Tattaro mini su ki miƙo mini" ummi ta tarkata kuɗin ta miƙa mata.
Ta karɓe ta kalli Hashim ta ce "Zaka tashi ka fita ko sai na ɓata maka rai, kuma daga yau na yi maka tsakani da ita, tun da kai ne ka ke zigata, shashashai kawai"
Hashim ya tashi zuciyarsa na yi masa zafi, muddin ya buɗe bakinsa, zai iya ɗurawa Iya ashar, dan haka yayi shiru ya bar ɗakin.
"Tashi ki fice ki auni dawa ki surfa mini, tun da baki je makarantar allon ba"
Haka Ummi ta ja jiki ta fito, ta fara ƙoƙarin aikin da Iya ta saka ta, ƙasan zuciyarta tana fatan, ina ma Maiduguri babu nisa da guduwa za ta yi, ta tafi wurin mamanta.
Kayan da yaya ɗanlami ya kawowa Ummi kuwa, Iya ta tsince wanda zata tsince ta ce a fita da sauran, ba ta ƙaunar duk wani abu da ya shafi Mariya.
Duk salla sai ummi ta yi addu'ar Allah ya jiƙan babanta, ya bawa mamanta lafiya, ya sa ta dawo ta ɗauke ta.
Tun wannan tafiya da yaya ɗanlami yayi, wani daga danginsu, bai sake waiwayo in da Ummi take ba, suka mayar da hankalinsu a kan lafiyar ƴar uwar su. Dan abun na mariya gaba ya din ga yi, babu sauƙi ko sassauci, yanzu tana zaune lafiya idan aka jima, sai ta hau kuka tana burgima tare da surutai, irin na masu taɓin hankali.
Ummi kuma ta cigaba da karɓar gashi a gidansu, tsangwama da kyara a cikin yara a makaranta ko kuma a gida.
Iya ta sanya ido sosai a kan magaji, ɗan taimakon da yake yi wa ummi, ta tasaya tsyin daka ta hana shi.
BAYAN SHEKARU BIYU!.
Sauri-sauri ta kammala tulin wanke-wanken da ke tsakar gidan, ta warewa kowane sashi kwanukansu ta kai musu. Duk in da ta faki ido ta tsaya, sai ta yi soshe-soshe, dan itakaɗai ta san me take ji.
Guntun omon da ya ragu, da shi ta wanke kayan makarantar bokonta, duk hantsar wandon ta fatattake, sun koɗe sun jeme, ƙafar wandon duk ta ɗage ta tattare, gwiwar duk a farfashe.
Kasancewar lokacin rani ne, rijiyoyi duk sun ƙafe, ta ɗau bokiti ta samo ruwan wanka, ta ɗauki ledar omon da babu komai a ciki, ta faɗa banɗaki wanka, da sosonta na buhu.
Ta daɗe a tsaye tana fargabar ta ina zata fara? Tun safe a makarantar boko take jin fitsari, ta riƙe shi bata yi ba, saboda azabar da take sha.
A hankali ta cire kayan jikinta, ta ware gashin kanta, ta nannaɗe shi ta tufke, ta kawo tsumma da take ɗaure kan da shi, ta ɗaure yadda ba zai jiƙe ba.
Ta cire wandon da yake jikinta, subhanallah, wani irin ragargazajjen wando ne, kusan da shi gara babu, duk roba-robar jiki ta zaro, har da in da aka yi ɗinkin zare da allura a jikin phant ɗin, haka ta rataye shi a jikin ƙofar banɗaki, sai tsami yake mara daɗi.
Ta koma gefe ɗaya, ba tare da ta tsuguna ba, ta fara sakin fitsarin da ya cika mata mara fam, a tunanin ta hakan zai sanya ta kaucewa faruwar abun da take gudu.
Sai dai kash! Tamkar ta zuba ruwan barkono a gabanta, wani irin raɗaɗi da azabar zafi, ya ratsata tun daga kanta har ƙafafuwanta, ta toshe bakinta tana jin zafi kamar ana kekketa mata wurin, ga mararta da ta ƙulle kan fitsarin ya fita.
Ta shafe tsawon lokaci, kan ta motsa, saboda tsananin azaba da wahalar da ta shiga.
A hankali ta motasa, ta tsuguna wani irin ƙarni mai haɗe da wari ya daki hancinta, ta ɗebo ruwan nan da sanyinsa da komai, ta zuba a wurin ta fara wankewa, wani irin ruwa mai ƙarni mara daɗi ya din ga fitowa daga jikinta. Zuba ruwan sanyin da tayi, ta ji tamkar ta zuba karara a wurin, wani irin ƙaiƙayi kamar ta kurma ihu, duk yadda ta so ta daure, ta kasa ta din ga sosawa, ƙurajen da suka feso a gabanta suka yi jawur, tun tana jin daɗin susar sai da ta koma jin zafi, dan da gask take yi iya ƙarfin ta, saboda azabar ƙaiƙayi, sai da ta yi wa kanta rauni, har da jini.
Ta yi shiru ta jingina da jikin bangon banɗakin tana tunanin haka kowa yake yi? Ko ita kaɗai ce take fama da wannan masifar da bala'in, to idan ma haka ne wa zata tambaya?
Da ƙyar ta samu ya lafa, ta zuba ruwa a cikin ledar omon nan, ta zuba a jikinta tayi wanka, sai dai a ƙarshe ta rasa yadda za ta yi ta wanke wandonta, dan babu omo, dan haka ta wanke shi a haka, da zallar ruwa, ta yarfe shi ta mayar shi jikinta a jiƙen, ta fito daga wankan tana tafiya a hankali, tana ɗan buɗe ƙafarta, saboda raɗaɗin da wurin yake yi mata.
Man kaɗanyarta da na'ima ta aiko mata, shi ta shafa abun ta, ta sanya uniform ɗin ta, ƙungun wandon saboda rashin roba, da leda take kama wani sashin ta ɗaure, hakazalika takalminta ma, kasancewar ya mutu dan a tsinke yake, ta samu leda shi ma ta yi masa cunan leda, ta ɗaure shi da shi, ta saka. Haka ta tafi makaranta tana kaffa-kaffa da jikinta, ko yaya ta saki jiki za a iya ganin tsiraicinta, saboda yadda kayanta suka mutu. Ga wannan bala'in da take ciki, na sanyi da yayi mata mugun kamu.
Iya kuwa hankalinsu yana kan bikin Idiris da za ayi, ana ta shirin biki a gidan, shi yaƙi karatun boko yaƙi na islamiyya, ya ce shi aure yake so, Hashim ya kaɗa ya raya, ya ce shi ba zai iya wannan wahalar banzar ba.
Kawu Yahaya ma sai da yayi mitar idiris ɗin nawa yake, da har zai ce zai yi aure me yake da shi? Iya ta goya masa baya, ta ce su haɗu su yi masa aure.
Aka kama masa hayar wani gida mai ɗaki biyu da kitchen da banɗaki, ginin ƙasa ne dai, amma an yi floor, da plastar ƙasa an shafa farar ƙasa.
Wata yarinya ya nema a can gaban unguwarsu, yake ta yi musu sintiri yana son ta, babanta ya ce idan da gaske yake ya fito, shi ne ya zo ya saka Iya a gaba, lallai shi aure yake so, aka je aka nema masa auren ƴar mai suna Hindu.
Kawu yahaya ya ce lokacin auren, yayi dai-dai da lokacin zuwansa umara, ba zai samu zuwa ba sai dai matarsa za ta zo, ya kuma aika musu da gudunmawa mai tsoka.
Albarkacin bikin Idiris, Iya ta sayawa ummi atamfa, da takalmi na kayan fitar biki, ummi duk da ba shiri suke yi da idiris ba, ta ji dadin zai yi aure ya bar gidan ko ta samu ta sarara.
Ana ta shirye shiryen biki, gida ya ɗau harama, ƴan uwa na nesa tuni sun fara zuwa, ummi na ta aiki kamar jaka, ɗan wannan idan yayi kuka a bata rarrashi, ɗan wancan yayi kashi ta wanke, haka dai ba ta da sukuni.