Kenza eBookz

Cutarwa complete by ayshercool - Chapter 16

Cutarwa complete by ayshercool - Chapter 16

Cutarwa complete by ayshercool Chapter 16: Cutarwa complete by ayshercool Chapter 16. Ya dubeta ya ce"Well, ummi bare ce, amma ko ba komai ƴa ce a wurina,…

3,375 words

Ya dubeta ya ce"Well, ummi bare ce, amma ko ba komai ƴa ce a wurina, idan har ummi za ta bar gidan nan, ki tabattar rahama ma sai ta bar mini gida, dan bani da wata alaƙa da ita, dan ina aurenki ba dole ne na riƙe ki na riƙe ƙanwarki ba, tun da baki san mutunci ba, a gobe in Allah ya kaimu rahama ta bar mini gida na gaya miki".

"Yahaya, ni ka ke gayawa ƙanwata ta bar gidan nan?"

"Tun da ki ka iya kallona ki ka ce, ƴa ta ta bar gidan nan, to rahama ma sai ta bar gidan nan tun da ko ban riƙeta ba, bani da laifi a wurin Allah, ummi kuwa dole ne riƙonta a kaina" ya tashi fuuu ya nufi ɗakin su intisar.

Ummi na zaune a ƙasa rungume da kayanta, tana kallonsu, suna zaune a kan gadonsu, sun sakata a gaba suna ta dariya, saboda yanayin ƙauyanci da yake tare da ita da kuma baƙar fatarta.

Sallamar babansu ce ta sanya su tashi a razane, suka daina dariyar.

"Ina ruwan wankan da na ce a bata?"

Intee ta ce "Anty rahama ba ta haɗa ba"

"Wannan ban isa da ita ba, ku na isa da ku, ki haɗa mata ruwa ki nuna mata yadda ake amfani da toilet ɗin"

Ta jinjina kai, ya juya ya fita dan tafiya masallaci sallar isha'i.

Cikin ƙyama take nunawa ummi banɗakin, ƴar ƙarama da ita, amma ta iya wulaƙanci.

Ta cewa ummi kar ta kuskura ta taɓa musu sosunan wankansu, ta je ta ɗaukkowa ummi sabulun wanki, ta bata wai tayi wankan da shi, ta kuma nuna mata iya in da zata tsaya, tayi wakan.

Ummi ta jinjina mata kai, sai dai ta tsaya tana kallon banɗakin yadda ya ƙawatu.

"Rahama kina ina, wai ni yahaya ya ɗaukkowa ƴa a ƙauye na riƙe, wai idan ba zan riƙe ba kema ki bar masa gida"

Rahama ta kalleta ta ce "In bar gidan nan wai? To me ki ka ce masa".

"Wallahi ba zan riƙe ba, kuma ba in da zaki je, shi ya isa ma, wallahi yayi kaɗan, zai gane kuskurensa".

Rahama ta ce "Anty ke da ki ke neman ƴar aiki? Gashi kin samu a ɓagas, ba dai gida ne ba, ta zauna mana iya ka idan bala'i ya isheta ta gaji ta bar gidan nan, ki rabu da shi, sai dai karki saurara mata wallahi, idan ma sa ido aka turo ta ki ci ubanta, ki rabu da shi kawai"

Ta ce "Kuma fa haka ne rahama, haka za ayi, ɗakin mai aiki kawai zata koma, na samu baiwa zata ci ubanta kuwa, sai ta koma in da ta fito dan ba zan zauna da ita ba wallahi. Nifa gaba ɗaya ban yarda da yarinyar nan ba, lokacin da muka je gaisuwar babanta, ina jin kakarta na ta ce mata kamar mayya, ke kin ganta baƙa ƙirin ƙwayar idonta kamar mage".

Raham ta ce "Idan ma mayyar ce ta ci kanta, dan wallahi mun fi ƙarfinta, to ma ina uwarta da za a kawo miki ita? Gaskiya baban Abdul yana da matsala wallahi".

"Oho masa, sai ta bar mini gida dai wallahi, amma na san yadda zan yi da shi".

Ayshercool 08081012143 *CUTARWA!*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

BRIGHT PENS (FREE BATCH)

(Ku garzaya YouTube channel ɗina na COOL HAUSA NOVELS, KU YI SUBSCRIBING, AN FARA ƊORA LITTAFIN ƘANWAR MAZA NA SAURARO)

P14

Har kawu yahaya ya dawo daga sallar isha'i, suna tattaunawa ita da rahama, suka gama ƙulle-ƙullensu, sannan farida ta baro ɗakin rahama.

Yahaya ya tafi ɗakin yaransa, in da suke ta tsalle-tsalle a ɗakin, ummi kuma na ta gyangyaɗi a zaune a ƙasa.

Suna ganinsa suka tsagaita da tsallen da suke yi, ya kalli babbar ya ce "Ke intee, ku yi squating da kausar a kan gadonki, yaya ummi ta kwana a kan ɗaya gadon.

Turus suka yi suna bin mahaifinsu da kallo, cikin tsawa ya ce "Ba ku ji me na ce ba ne?".

Intee ta ce "To" ya kalli ummi da ta buɗe ido ya ce "Ummana, ga gado nan tashi ki kwanta kin ji"

Ummi ta ce "To na gode"

Ta tashi ta hau gadon nan ta kwanta, wani irin laushi, ga ƙamshin room freshner mai daɗi kayan shimfiɗar suke yi, tun kan ya bar ɗakin bacci ya fara kwasarta.

Inteesar ta kwashe wa da kausar da dariya ta ce "Shikenan bedsheet ɗin ki zai kwashi baƙi, kamar an ciro a buhun gawayi".

Kwaɓe fuska kausar tayi za ta yi kuka, intee ta cigaba da dariya, ganin kausar ta fara kuka ya sanyata cewa "Bari idan abba ya daɗe da tafiya, sai mu tashe ta, ta saukko".

Haka kuwa aka yi, intee har da leƙawa, ta tabattar da ya tafi, sannan ta dawo, ta hau dukan ummi a ƙafa.

Ummi ta buɗe idonta tana kallonsu.

"Saukko mana daga kan gado, kausar zata kwanta"

Kasa magana tayi ta cigaba da bin su da kallo.

"Ki saukko zata kwanta, dan ba zata kwana a gadona ta matseni ba" babu musu ummi ta saukko, ta koma ƙasa ta sake tada kai da kayanta.

Kausar ta watso kayan kan gadon nata, har bedsheet ɗin da komai, wai saboda ummi ta kwanta a kai.

Wajen ƙarfe ɗaya na dare, ummi ta ji ana haurinta da ƙafa, ta tashi firgigit, dan ji tayi kamar a gidan idris za ta buɗe ido ta ganta, dan shi yake yi mata irin wannan wulaƙancin, na haurinta da ƙafa.

"Tashi malama, in nuna miki in da zaki din ga kwana, dan ba zaki kwanar mini a cikin yara ba, ban san irinki ba"

Kai ka ce sokuwa, haka ta tashi, ta ɗaukko jakar kayanta, ta bi bayan farida.

Ɗakin ƴar aiki da yake farkon falon, ta nuna mata ta ce ta shiga a nan zata kwana. Ba ta damu da a yaya ɗakin yake ba, ta je ta kwanta, saboda yanayin jikinta ga rashin lafiya ga gajiyar tafiya, dan haka duk a gajiye take.

Washegari da safe, kowa ya fito falo, rahama ce ta haɗa breakfast, yaran duk sun shirya cikin uniform na makarantar boko.

Abba ya fito ya kallesu ɗaya bayan ɗaya babu ummi, rahama ta gaishe shi ya amsa sama-sama.

Ya kalli farida ya ce "Kawo mini abincina nan"

Haushi ne ya kama ta, yana ganin yadda take fama da ciki, amma ya sakata aiki, bayan ta kai masa kayan abincin ɗaki.

Bayan ta tafi ɗaukkowa, ya kalli intee ya ce "Kirawo mini ummana" intee tayi saroro tana kallon shi.

Ya ce "Ummi nake nufi"

Tunawa tayi da safen nan, ta ji maama da anty rahama suna zancen a ɗakin mai aiki ta kwana, har take gaya musu abun da suka yi mata jiya da daddare suka din ga dariya.

A zaune ta tarar da ummi, ita ummi ɗakin ba ƙaramin kyau yayi mata ba.

Duk da ba wani abu a ciki na burgewa, amma ɗakin ya yi mata kyau.

"Ki zo in ji abba" yarinyar ta faɗa cikin fitsara.

Ummi ta tashi ta bi bayan ta, sai dai farida na ganin ummi kamar taga kashi, ta haɗe rai.

Daga in da suka fito falon, ya fuskanci a in da ummin ta kwana.

Ummi ta durƙusa ƙasa ta ce "Abba ina kwana?"

"Lafiya ƙalau ummana, ya jikin naki, ina fatan baki kwana da zazzaɓin ba?"

Ta ce "Eh da sauƙi".

Ya ce "Masha Allah, baki gaisa da maman naki ba, gata nan sunan ta farida, yara na kiranta maama, kema zaki iya kiranta da hakan, ga ƙanwarta nan anty rahama, ga Abdurrahman Abdul, ga inteesar, ga kausar, sai kuma muna jiran unborn baby da maama zata haifa mana. Abdul, intee, kausar kamar yadda na gaya muku jiya, yayarku ce, duk da kai Abdul ka girmeta, amma ku girmamata, ku zauna lafiya. Ummina duk abun da ki ke buƙata, ki sanar da ni, ko maama gidanku ne ki yi zamanki ki kwantar da hankalinki".

Cikin ladabi ummi ta ce "To Abba" ta kalli farida ta ce "Ina kwana" banza tayi da ummi kamar ba ta ji abun da ta ce ba, ba ta damu ba ta kalli rahama ta ce "Anty ina kwana"

Ba yabo ba fallasa rahama ta amsa mata, abun da farida tayi, ba ƙaramin ƙular da shi tayi ba, bai ce komai ba da kansa ya haɗa wa ummi abun breakfast a abincinsa, ya bata. Wanda hakan ba ƙaramin tunzura farida yayi ba, cikin ƙulewa take tuna masa yara zasu makara a makaranta, amma ya kada baki ya ce "Ƴaƴanki ne ai ki tarar musu abun hawa ya kai su, ƴa ta zan kai asibiti"

Tsit suka yi suna kallonsa, aka rasa mai magana, ya jira ummi ta gama, ya sakata a gaba suka fice.

Sai da ta kusa kuka, abun ka da mai ciki dama ga zuciya a kusa.

"Rahama ki na kallo daga kawo yarinyar nan, ni zai yi wa wannan wulaƙancin, ya fifita bare a kan yaransa".

"Kema anty farida you over react, a gabansa ta gaishe ki, ki ka shareta, ai kisan mummuƙe zaki yi mata".

"Yanzu kwana ɗaya tal a gidan nan ta fara haɗa ni da shi? To wallahi da sake ba zai yiwu ba"

Ran farida yayi matuƙar ɓaci, ta din ga cin alwashi kala-kala na mugunta a kan ummi.

Ya tafi da ita wurin aikinsa, ya kulleta a office ɗin sa, ya je ya gabatar da lectures ɗin da zai yi, wajen ƙarfe sha biyu na rana, ya tafi da ummi kasuwa.

Ya sai heater da nurse ɗin nan ta ce ya saya, ya sai mata phants dozen ɗaya, ya saya mata soso sabulu, brush, manyan jakar omo. Ya saya mata sababbin kaya wasu ready made wasu kuma sai an ɗinka, kasancewar yana da yara mata, kuma shi yake sayen komai na gidan sa, dan haka duk wani abu na ɗawainiyar yara mata ya sani, hatta ɗan kunne sai da ya saiwa ummi, under wear vest duk ya saya mata. Ya ce suje mota ta zauna ta huta, ya ƙarasa sayayyar, wani irin farinciki ummi take ji, saboda kayan nan da aka saya mata, gani take kamar a mafarki, wai duk wannan kayan nata ne, har da su ɗan kunne da ribbon, ga takalmi mai kyau, ta din ga kwarara masa addu'a a cikin zuciyarta.

Wurin masu sayar da kayan ƙamshi yaje, domin haɗa magungunan da aka gaya masa a yi wa ummi.

Sai dai wasu abubuwan duk ya manta yadda aka gaya masa, mai kayan ya tambaye shi, mai zai yi da su, yake gaya masa ai maganin sanyi za a haɗa.

Kasancewar mutumin sana'arsa ce, sai ya haɗa masa komai da yadda ake amfani shi.

(Previous page, na bayar da magungunan in breif, wasu sun biyo ni suna so, yanzu zan rubuta full yadda ake amfani da su) _Kanumfari _Tafarnuwa ƴar kaɗan ba mai yawa ba, saboda idan tafarnuwa ta huda jikin mace, tana sanya warin baki, na jiki har da na al'aura ma, sai dai maganin sanyi ce sosai. _Tumeric (yellown kur-kur) _Namijin goro _Citta mai yatsu _Lemon tsami

Kowanne za a zuba shi in a moderate amount, lemon tsami babba guda ɗaya mai ruwa ya isa, namijin goron ma za a iya daddatsa shi, yana da ɗaci sosai, tafarnuwa one clove, sai citta mai yatsu madaidaiciya guda ɗaya, sai 1 table spoon of tumeric, sai a zuba ruwa kamar 2cups, a dafa su a din ga sha, za a iya zuba zuma, saboda yana da ɗaci, za kuma a iya haɗe su a mazubi guda, a jiƙa su, su jiƙu sosai a din ga tsiyaya ana sha.

Idan wannan bai samu ba, ana iya jiƙa kanumfari, a din ga sha yana maganin sanyi sosai, amma sai an juri sha.

Sai kuma ana samun saiwar zogale, a ɗaurayeta da ɗan gishiri, a tafasa ta da jar kanwa, a din ga sha, salam yake babu ɗaci, amma yana maganin sanyi sosai.

Sai kuma kama ruwa da ruwan magarya da bagaruwa ba da yawa ba kaɗan a haɗa su a tafasa, ana kama ruwa da shi, ganyen magarya yana gyara jikin mace, mussaman bayan gama al'ada, ayi shaving a din ga kama ruwa da shi, kuma a din ga ɗiga farin miski a kan phant, ba a jiki ba, yana kawar da ƙarni ko wani wari mara daɗi, but mark you ba kowane wari ne yake fita a gaban mace na infection ba, akwai bacterias ɗin da suke wurin wanda ba masu cutarwa ba ne ba, suna haifar da wannan ƙarnin wasu lokutan. Galibi na infection ko na ƙazanta ya fita daban mussman idan ya haɗa da ƙaiƙayi ko ƙuraje shi ne na infection.

Shi ma wannan warin, ana iya amfani da apple cider vinegar, ruwa kal da hausa, ana zuba tablespoon ɗin sa biyu, a ruwa cikin kofin shan shayi a din ga sha, yana magance warin gaba.

Sai dai dole a kula da abincin da ake ci, domin cin abinci mai ƙarni, ko wari kamar kifi, albasa ko tafarnuwa suna da tasiri a gumin mu da sauran fluids da muke fitarwa a jikinmu.

Kawu yahaya duk ya haɗowa ummi abubuwan da suka kamata, suna tafe yana sake yi mata bayanin yadda zata yi amfani da su.

Sai azahar suka koma gida, sai dai matar gidan bata nan, da kansa ya bi ummi ɗakin masu aikin, ya dudduba abun da babu ya ce zai sayo mata.

Tamkar yar da ya haifa a cikinsa haka yake jin ummi,kuma haka yake burin ta samu lafiya daga wannan ciwon, dan ya san illarsa da hatsarinsa, dan ya san halinsu maza bakomai suke iya jurewa su kawar wa da kai ba.

Ya nuna mata yadda za ta din ga amfani da heater, da sabon flask ɗin ruwan zafi.

Da kansa ya tafasa magungunan, ya zuba mata a jarka, na kama ruwan ya zuba mata a cikin flask ɗin shayi, ya ɗaukko tsintsiya ya taimaka mata wurin gyara ɗakin saboda an kwana biyu ba a gyara shi ba.

Ya je ɗakinsa ya duba bedsheet ɗin da shi ya saya da kuɗinsa, har da bargo ya kawowa ummi.

Ya bata babban gwangwanin turare a cikin nasa ya ce ta din ga fesawa.

Kallonsa kawai ummi take yi, cikin jin daɗi da annashuwa, yadda ya zage yake ta ɗawainiya da ita, daga jiya zuwa yau, idan ta ce ya bari tayi da kanta, sai ya ce mata ai bata da lafiya, kuma cikin barkwanci ya ce mata albarkar ummansa yake nema.

Haka nan ummi ta din ga murmushi tana yi masa godiya.

Ya ce "Yauwwa ummina, Allah yayi miki albarka, saura makaranta ita ma in sha Allah sati mai kamawa, zaki koma makaranta ki manta da duk abu da ya faru, iyaka dai kar ki sake ki gaya wa wani kin taɓa aure kin ji ko?"

Ta jinjina masa kai ya ce "Good, yi wanka ki yi salla, a cikin kayan nan akwai gurasa ki ci kiyi kwanciyarki ki huta"

Murmushin kawai da ya gani a fuskar ummi, ya sanya shi cikin farinciki, kullum yaje ƙauye sai dai ya tarar da ita cikin kuka, sai kuma Murmushin yaƙe. Hatta yadda zata din ga amfani da banɗaki, sai da ya nuna mata komai.

Fitowa yayi daga ɗakinta, a zuciyarsa yana tawasalli da farincikin da ya saka marainiya yana addu'a Allah ya biya masa buƙatunsa na alkhairi.

Ba yau farida ta fara fita yawonta ba, tun yana faɗa har ya gaji ya daina yi.

Ummi kuwa tun daga kama ruwan da tayi, ta ji daɗin jikinta, ta tsiyayi maganinta ta sha bayan ta ci gurasar nan, ta ɗauki sabon phanta ta canza.

Wani irin daɗi take ji da nishaɗi, ta sake bubbuɗe kayan da ya saya mata tana jin daɗin hakan.

Ko da wasa ba ta yi gangancin fitowa daga ɗakin nan ba, dan ta fuskanci ƴan gidan ba ƙaunar ganinta suke yi ba.

Ana kiran sallar la'asar ta yi salla, ta cigaba da zamanta a ɗakin.

Kamar an watso su, taga farida da rahama a ɗakin, hakan ya sanya ta tashi a razane.

Farida ta ce "Tashi munafuka, ai ba zama ki ka zo yi ba" a zabure ummi ta tashi tana rarraba ido.

"Ba dai kawo ki aka yi leƙen asiri da saka mini ido ba, zaki ci ubanki sai kin bar mini gida da ƙafarki" idonta ya sauka a kan ƙatuwar ghana must go sabuwa fil.

Ta ce "Rahama janyo mini jakar nan ki zazzageta, wato zuwa yayi ya kashe mata kuɗi, wallahi ba zai yiwu ba ya daidaita da ƴaƴana, kar ta san kar ai".

Rahama ta janyo jaka, suka zazzageta, farida har da ashar, farida ta saka farida ta tsitstsince mata kayan, phants ɗin ma duk ta kwashe ta bar mata uku, Allah ya taimaketa, tana da sauran wanda ta zo da su, da na'ima ta saya mata.

Cikin ikon Allah, Allah ya taimaketa basu lura da ƙullin kayan maganin da ke bayan katifar ɗakin ba, heater da flask ɗin kuma suna cikin banɗaki.

Hatta omo da sabulun da ya saya mata, sai da suka kwashe ta bar mata ɗai ɗai.

Sannan ta sake dubanta a wulaƙance ta ce "Ki buɗe kunnenki da kyau ki saurareni, nan gidana ne, abun da na dama shi ake sha, shima kwana biyu na sarara masa ne, amma tun da haka ya zaɓa zan yi maganinku duka. Ki saka a ranki ke ƴar aiki ce kawai a gidan nan. Kullum da yamma idan yara suka taso daga makaranta, zaki wanke musu uniform ki goge musu shi tas, wanke-wanke da duk wani aiki a gidan nan ke zaki din ga yin sa, idan ki ga dama ki gaya masa babu abun da zai iya yi a kai, bari in gaya miki ƙiri-ƙiri idan ki ka sake kiransa da Abba sai kin bar gidan nan, dan bai haife ki ba. Kuma wanki ba na yara kawai ba, kaya ko na waye sai kin wanke a gidan nan, tashi mu je ma ki fara aikin ki daga yanzu. mummunar banza kawai".

Rahama ta kwashe da dariya ta ce "Ni wallahi fuskarta ma dariya take bani, wannan baƙi kamar a dangwala".

"Rabu da ita tashi ki wuce" ummi kaf maganganun su babu wanda ya ɓata wa ummi rai, dan ba yanzu aka fara yi mata ba, ƙwace mata kaya yafi komai ɓata rai. Sai dai wata zuciyar ta ce da kin san zaki samu ne?.

Saboda tsabar mugunta akwai injin wanki a gidan, kuma akwai mai guga, amma farida ta tula wa ummi kayan makarantar su Abdul, na boko da islamiyyar su, kusan kowanne nasa set uku, daga na makarantar boko har na islamiyya.

Ummi ko a jikinta, ta durƙusa ta fara wankin kayan nan. Tas ummi ta wanke su, kasancewar ta riga ta saba da wahala tun a gaban Iya.

Bayan ta gama cike da mugunta, rahama ta ja ta kitchen, ta sakata sassauke kwanukan da sun fi wata shida ba a saukko su an yi amfani da su ba, ta ce ummi ta wanke. Babu ƙyuya ko ƙosawa ummi ta wanke su.

Duk yadda suka wahalar da ummi a yammacin nan har zuwa bayan isha'i, ko da wasa bata nuna musu gazawarta ba.

Kwanaki uku da zuwanta gidan, rashin mutunci da kyara, haka babar su Abdul suke yi mata, da yaranta da ƙanwarta, kuma wasu lokutan a hana ummin abincin.

Sai dai lokaci ɗaya kawun nata ya rage bata wannan kulawar da yake bata da farko, hakan sam bai damu ummin ba, dan gani take duk wahalar da zata sha, ba zata kai ta gidan Iya da idris ba.

Ranar lahadi suka koma ganin likita, sai dai ummi ta ji daɗin amfani da magungunan nan, dan kuwa sosai yayi mata sauƙi ba kamar da ba.

Likita ya dubata, ya rubuta mata magunguna, Allah ya sa kawu yahaya bai yi ƙwauron baki ba, ya sanar masa magungunan da take sha, likitan ya ce ta ajiye su ta gama shan na asibiti, idan suka ƙare ta cigaba da waccan.

Yayi masa godiya suka tafi gida, suna tafe yana rarrashin ummi, yana yi mata nasiha.

Sai da ummi ta yi sati biyu cif a gidan, baban su Abdul ya cewa farida zai kai ummi makarantar su Abdul, amma ta ce ba ta yadda ba, sai dai ya nemi wata mai arha ya kai ummi, dan ba zai dai-daita ta da yaranta ba.

Readers Also Read