Cutarwa complete by ayshercool - Chapter 61
Cutarwa complete by ayshercool Chapter 61: Cutarwa complete by ayshercool Chapter 61. Ummi ta ce "Waye ya ce miki bama faɗa? Babu wata soyayya da za ayi…
3,325 words
Ummi ta ce "Waye ya ce miki bama faɗa? Babu wata soyayya da za ayi zaman aure ace babu saɓani, sai dai danganta da yadda aka gina soyayyar, idan har ta gaskiya ce kuma an fahimci juna, ko saɓani yazo za a warware cikin sauƙi. Ni kaina MD ba dan yana sona ba, kuma mutum ne mai fahimta ba da laifukan da na yi masa a kwanakin nan wani zancen ake yi ba wannan ba, shiyasa ko mun samu saɓani nake duba alkhairnsa bana taɓa yi masa hukunci da laifin da ya yi mini".
Noor ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ni wallahi soyayyar da ba a faɗa nake so, idan muka yi faɗa kuka zan yi"
Ummi tayi dariya ta ce "Sai ki tafi littafi ko film, ko kuma tatsuniya, a nan zaki samu wadda ba a faɗan. Bari na shiga daga ciki"
Noor ta yi shiru tana ta zancen zuci, ita har ga Allah ta fi son ayi ta soyayya babu faɗa.
Ummi daga yin wanka ta ji sanyin Ac, ta kwanta ta hau bacci a ɗakinta. Noor ta zage tana ta gyara gidan, ta iya aiki sosai da sosai saboda zama da ummi.
Ta gama aikin ta shiga ta yi wanka ta saka wata ƴar doguwar riga da ɗan kwali, ta dawo falo tana shan lemo mai sanyi. Ba ta daɗe da zama ba a ka buga ƙofar falon.
Ta tashi ba tare da tambayar waye ba, ta buɗe ƙofar, kallonsa ta tsaya tana yi tana murmushi, hannunsa ɗauke da manyan kulolin abinci, ta ce "Sai yanzu ko? To koma mun yafe" alama yayi mata da ido, ya tura ƙofar hajiya ta gani a bayansa.
Da sauri noor ta nutsu, ta durƙusa tana gaishe ta, saboda ta shaidata, ta karɓi kayan hannunta suka ƙarasa cikin falon.
Hajiya ta ce wa noor "Kamar na so na gane ki"
Salim ya ce "Ƙanwar ummi ce" ya kalli ummi ya ce "Ga hajiya, in faɗa mata me ki ka ce a kan ta?"
Noor ta kalleshi da sauri tana zare ido, ta girgiza masa kai.
Hajiya ta kalleshi ta kalleta, ta ce "Laifi na yi mata?"
Yayi murmushi ya ce "Hotonki ta gani a wayata, ta ce na sanki, na ce eh ƴar uwammu ce ke, wai ranar bikin su raihan tana ta kallonki, wai kwalliyar ki tayi kyau, gashi kin iya turanci, kina magana kina turanci, har gwada maganarta ki ka yi ko ba ayi ba?"
Noor tamkar ta nutse a wurin nan, ta sunkuyar da kai tana hararsa ta ƙasan ido.
Hajiya ta yi dariya ta ce "To ai da sauƙi tun da ba laifi na yi mata ba, ina ummin ne?" Duk da noor ta san ummi bacci take yi, ta tashi da sauri ta ce "bari na kirawo ta" har noor ta bar falon kallonta yake yi yana dariya.
Hajiya ta ce "Wai ya aka yi har ku ka saba haka ne?"
Ya gyara zamansa ya ce "Ina ganinta a nan gidan, sai kuma lokacin da aka samu matsalar nan na su raihan, da na je gidansu ita ta gaya mini. Ta wurinta na din ga samun information ɗin da na samu ummi a can garinsu. She's very funny ne kawai tana bani dariya.
Hajiya ma ta yi murmushi, noor ta dawo falon amma ta laɓe ta bayan labule ta ce "Na duba bacci take yi"
Ta gudu ta koma kitchen, ta haɗa musu ruwa da fruit, amma ta kasa fitowa tana jin kunya, sai a yanzu ta fuskanci hajiya mahaifiyar Salim ce dan suna kama sosai, saɓanin da ya ce mata ƴar uwarsu ce.
Da ƙyar ta dawo falon tana sunkuyar da kai.
Hajiya ta ce "Ya sunanki ne?"
"Mariya, amma ana ce mini noor, maman ummi aka yi wa takwara aka saka mini sunanta"
Hajiya ta ce "Masha Allah noor, kar ki damu da abun da ya faɗa rabu da shi, bari mu tafi ga abinci muka zo wa da ummi, na zo na ƙara duba jikinta"
Noor ta ce "Dan Allah kar ku tafi, bari na tashe ta"
Hajiya ta ce "A'a ba sai kin taso ta ba"
Muryar ummi suka ji tana cewa "Hajiya sannunku da zuwa, wallahi bacci ne ya kwashe ni"
Hajiya suna can suna hira da ummi, Salim ya fita, noor ta bi bayansa.
Yana tsaye yana waya ya ji muryarta ta ce "Allah ya kama ka"
Ya waiwayo ya ce "Da na yi me?"
"Ashe mamanku ce"
Ya ce "A'a ƙanwar Alhaji ce"
Noor ta ce "To wallahi mamanku ce, shi ne ka gaya mata abun da na ce, duk na ji kunya".
Salim ya yi dariya ya ce "Last born"
Ta ce "Ba wata last born, wallahi ka bani kunya sosai"
Yayi dariya yana kallonta, ƴar ƙarama da ita sai baki.
"Ka san me? Babanmu yayi aure fa, ya auri babar su yaya ummi, mamanmu sai fitina take yi a gida, ni kuwa na yi tahowata nan"
Ya ce "Kin kyauta, ba kyau kallon manya idan sun samu saɓani"
Kawai ta saka hannu a aljihun rigarsa, sai ga kwalin sigari.
Ta ce "Ba ka daina ba ko? Ka ce mini fa ka daina"
Ya haɗe rai ya ce "Meyasa ba ki da kunya ne? Dan kin ga ina yi miki dariya har ki ka saka hannu a aljihuna?"
Noor ta ce "To ai ba kuɗi na ɗaukko ba, kuma ka ce mini ka daina"
Hannu ya kai ya karɓa, ya mayar da kayarsa cikin aljihunsa, ya juya ya tafi.
3 MONTHS BACK
Salim ya je gidan raihan, amma maigadi ya sanar masa raihan ya ce duk wanda ya zo ace masa baya nan.
Ya tambayi maigadin dalili, ya ce bai sani ba, amma tun da hajiya bilki ta je, ummi ta tafi tana kuka da kayanta a hannu, amma bai san meyafaru ba.
Tun daga nan jikinsa ya bashi akwai wani abu, da safe neehal za ta fita suka haɗu, ya tambayeta meyafaru a gidan raihan da mami ta je, ta ce masa ba komai, sai da ya zageta sannan ta gaya masa abun da ya faru.
Da azahar ya wuce gidan su ummi dan jin meyafaru, ya haɗu da noor a hanya za ta je makarantar islmaiyya . "Ke!" Yayi maganar yana sauke glass.
Ta tsaya ta ce "Sunana mariya wato noor" tsyaawa yayi yana kallon ta ya ce "Kin gane ni?"
"Eh, na ganeka ɗan uwan su yaya raihan"
"Yauwwa, ummi na gida ne?"
Ta ce "A'a tana gidanta"
Ya buɗe motar ya ce "Ba ta can ki gaya mini gaskiya "
Ta ce "Eh ta zo gida, mamanmu ta ce wai ba zata zauna ba, ba a san fa in da take ba, yaya raihan ya zo ana ta nemanta, sakinta fa yayi".
Salim ya ce "Ina ta tafi yanzu?"
"Gaskiya ba zan gaya maka ba, islamiyya fa zan tafi, kar na makara".
Salim ya ce "Shigo mu tafi na kai ki islamiyyar "
"A'a ni ba zan hau motar wanda ban sani ba"
Ya ce "A'a ai ni kin sanni, yayan raihan ne ni"
Ta ce "Bari na gaya maka dai, duk da ta ce kar na sake na gaya wa kowa, gagarwa ta tafi, can garinmu a jigawa, amma kar ka gayawa yaya raihan, ta ce kar na faɗa, jiya kan ta tafi ta gaya mini".
Salim ya ce "Na gode sosai da ki ka gaya mini, daga gagarwan ina za a yi aje gidan"
Ta wassafa masa komai, kwatancen gidan tun daga tasha, da yake ba ɓoyayye bane ba, ya yi wa noor godiya ya tafi.
A yammacin ya tafi gagarawa, bai jira sai washegari ba, yayi sa'a ya tarar da ummi, kuma ta sanar masa duk abun da ya faru, da shawarar da ta yanke, ta kuma roƙe shi a kan dan Allah kar ya gayawa kowa in da take.
Bayan wata guda, ya haɗu da noor ta je gidan yayar farida, a sharaɗa, shi kuma ya je wurin wani abokinsa.
Suka gaisa, yake bugun cikinta ko an ga ummi, ta ce masa ba a ganta ba, ta nuna masa yadda take cikin damuwa, rashin sanin in da ummi take. Ta saki baki tayi ta bashi labarin zaman da ummi ta yi a gidansu, da yadda ake yi wa ummi gorin ta auri yaro ƙaninta.
Ta ce "Yauwwa ka ce kai yayan yaya raihan ne, amma ba mamanku ɗaya ba ko?"
Ya ce "Eh"
"To wallahi in gaya maka mamansa ce ta saka ya saketa, ba ta sonta wai mummuna ce ta auri yaro, dan Allah ai auren yaro ba haramun bane ko? Kuma ai yaya raihan babba ne yana da gemu fa"
Ya ce "Eh gaskiya ba laifi ba ne, in dai mutum yayi gemu ba yaro bane"
Message ya shigo wayarsa, ta kalli lock screen ɗin sa, da hoton hajiya ne a kai, ta ce "Laa ka san wannan matar?"
Ya amsa da "Eh, ƴar uwanmu ce"
"Innalillahi, ta burgeni lokacin bikinsu yaya ummi, ta iya wanka, gashi ta iya turanci"
Yayi dariya ya ce "Gaskiya ne"
Noor ta ce "Wallahi duk ƙarfin hali nake yi, rashin yaya ummi har kuka nake yi, rayuwarsu tayi ta bani sha'awa da MD ba sa faɗa, amma kawai ya saketa na zata auren saurayi ya fi daɗi, amma na fasa"
"Tsoho zaki aura kenan? Ai shi ma yana sonta ba laifinsa ba ne"
Ta ce "A'a ba tsoho nake so ba, me dai gemu kamar naka, wai dan Allah da ka je gagarawa ba ka ga yaya ummi ba?"
Abun da ta faɗa na farko ya bashi dariya, ya ce "Da na ganta ai da na gaya miki, amma me zaki bani na nemo miki ita?"
Noor ta ce "To ai bani da kuɗi"
Ya ce "Ba kuɗi zaki bani ba, zan gaya miki amma sai na nemo miki ita"
Tun daga ranar suka saba da Salim, lokaci-lokaci ya kan bi unguwarsu, dan ya ganta, saboda yana son surutunta.
A haka ta gane yana shan sigari, tayi ta masa mita, ya ce idan ya nemo mata ummi, zai daina sha.
Haka nan yake jin daɗin mu'amalarsa da ƴar yarinyar da da yayi auren wurin zai haifeta.
CIGABAN LABARI.
Hajiya sun daɗe tare da ummi, kuma ummi ta samu ta ci abincin da hajiya ta kawo mata sosai ta ƙoshi, kuma Allah ya taimaketa ba ta yi amansa ba.
Bayan tafiyar Hajiya, Dr. Ya kira ummi a waya, bayan sun gaisa ya ce "Noor tana gidanki ko?"
Ta ce "Eh kawu"
"Na san ta riga ta gaya miki komai ma, bayan mun zo gidanki mun yi wannan maganar, na yanke shawarar yin abun cikin gaggawa, saboda kar wani abun ya kutso ya hana.
Na kira baban maiduguri, muka yi magana da shi, da na tabattar da ya amince, kawai da muka je jiya, na tafi da sadaki aka ɗaura, dan hatta ƴan gagarawa ba su sani ba, sai da aka ɗaura na san za a iya samun matsala ko daga gare su ko wani ɓangaren. Nan da sati ɗaya idan komai na ta ya zama ready, zan ɗaukkota ta yi miki kwana ɗaya ko biyu sai mu wuce".
Ummi bakinta ya kasa rufuwa, ta ce "Alhamdilillah ala kulli halin, Allah ya cigaba da faranta maka kamar yadda ka ke yi mana kawu, Allah ya saka da alkhairi na gode sosai da sosai"
Dr. Ya ce "Ba komai ummi, yi wa kai ne".
Can Maiduguri kuwa, mariya na zaune ta yi shiru tayi zurfi a tunani, mama ta ce "Mariya, wai menene? Ko abincinki fa baki taɓa ba"
Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Wallahi mama tunani nake kawai"
"Tunanin me?"
"Auren nan mana, ni fa banda baba ya matsa ba zan yi wani aure ba, ido ya mutu kwalli ba zai farfaɗo da shi ba, kuma idan ina tuna wahalar da na sha a hannun iya, ko a mafarki bana fatan sake yin aure"
"Ashsha, mariya ba a fitar da rai da rahamar Ubangiji, kuma ke ba tsohuwa ba, haryanzu da sauranki, babu wanda zai ce kin haifi ummi, gashi albarkaci auren har jirgi zaki hau" ta ƙarasa maganar cikin zolaya.
Mariya dai ta rausayar da kai ta ce "Wallahi mama ba na ƙaunar abun da zai sake haɗa ni da iya, auren nan ya sake mayar da ni jikin su"
Mama ta girgiza mata kai ta ce "Akwai banbanci, tsakanin Bashir da Yahaya, Kuma ai ba wuri ɗaya zaku zauna ba" mama tayi ta lallaɓata tana kwantar mata da hankali.
Can gidan dr. Kuwa Farida kamar za ta kama dr. Ta daka, saboda azabar kishi da bala'i, sai dai fafur ya mayar da ita kamar mahaukaciya ya ƙi saurarenta.
Yanzu da safe Abdul ya kawo kai zai shigo falo, ya ji yo muryarta tana ta ɓaɓatu, tare da amfani da kausasan malamai wurin ci masa mutunci.
Dr. Ya fito ya fice, ba tare da ya ce mata uffan ba, Kausar na ta ba ta haƙuri, Abdul ya shigo rai a ɓace ya kalli farida ya ce "Maama wannan abun da ki ke yi ba mutuncinki bane ba, duk maƙwabta na jinki, wannan zubar mana da mutunci ki ke yi"
"Haba yaya Abdul, ka san menene kishiya kuwa? Kuma kishiya da mahaukaciya ku baku san komai a kan wannan lamarin ba"
Farida ta ce "Rabu da shi, baƙin ciki ya kasheni, sai su ci duniya da tsinke da ubansa, bands butulci da zalunci irin na ɗan Adam, duk halaccin da na yi masa ya rasa da mai zai saka mini sai wannan rashin mutuncin, maimakon ya auro cikakkiyar mace da zan yi kishin na gaske da ita, sai ya ƙare a mahaukaciya, ai da ƴar tata ya aura shi ne ƙarshen soyayya"
Abdul ya ce "Koma wa ya auro, hakan dai zaki yi maama, wallahi Abba ba ma bin sa bashi, shi ne yake bin mu, menene bai yi mana ba na kulawa a rayuwar nan, shekara sama da ashirin yana ƙarar da ƙarfin sa saboda mu, kuma lokaci ɗaya duk sai mu haɗu mu goya miki baya mu rabu da shi? Bamu yi masa adalci ba, kuma wataƙila da baki kori ummi ba, da bai ce zai ƙara auren ba".
Muguwar ashariyar da ta luluƙa masa ya sanya shi waro ido, ba shiri ya fice ya bar su da kausar.
Ta kalli kausari ta ce "Ki shirya ki je gidan ta, ki dawo mini da ƴa ta, idan ta ƙi ki ci uban noor ɗin, tun da ba mahaukaciyar uwarta ce ta haifeta ba, sannan ki tabattar kin ci mata mutunci da sai ta zubar da hawaye"
Kausar ta ce "Zan yi, amma dan Allah ki kwantar da hankalinki, kin ga fa yadda ki ke haki" gaba ɗaya farida sai ta fi kama da mahaukaciyar tuburan.
Noor kuwa ta miƙe abun ta a gidan ummi, ummi ta fara samun sauƙin wasu abubuwan saboda noor, ita take bata kuɗin motar zuwa makaranta boko da islamiyya. Ummi ta ce mata yakamata ta biya gida, su gaisa da su farida, amma ta ce ita ba ta son ta je gidan ta tarar da su Abba suna faɗa.
Ɓangaren mami ma abubuwa sun yi mata zafi sosai, dan haryanzu Alhaji fushi yake yi da ita, ga ɓangaren su safiyya sun hura mata wuta, dan zuba ido suke yi, a danƙaro musu kayan lefe.
Sai dai zancen nema yake yi ya shiririce, dan Alhaji ma ya ce kar ta sake yi masa maganar auren raihan, shi na fari da ya yi masa, shi ne hurumin sa.
Kuma sanin halinta ya sanya yayi mata gargaɗi na gaske, a kan gidan da raihan ya saya wa ummi.
Kausar kuwa da ta je gidan ummi, hankali kwance ta tarar da su har da raihan suna kallo, babu abun da ya dame su.
Sai duk ta kasa sakewa ta yi rashin mutuncin da ta ƙullo, duba da yadda raihan yake muzurai.
Hankali kwance ummi ta karɓeta, ta karrama ta.
Ta ce "Dama maama ce ta ce noor ta koma gida"
Raihan ya ce "Saboda me?"
"Haka dai ta ce"
Raihan ya ce "To ai ni mun yi magana da dr. Ya ce tayi zamanta, ta din ga zuwa makaranta daga nan, amma noor kin ji abun da mamanki ta ce"
Noor ta tura baki ta ce "Ni na tambayi Abba ya ce na zauna, zan koma amma ba yau ba" juyin duniya, noor ta ce ba in da za ta je, ita fa maama ba son ta take yi ba, dan kullum cikin yi mata faɗa take da zaginta.
GAGARWA.
"Kai auwalu, daga kai har Alhassan kun kashe zuciyarku, kalli yadda rana ta take, sai baccin asara ka ke yi ba zaka tashi ba?" Tayi maganar tana dukan ƙofar ɗakinsa.
Amma ya ƙi tashi, ta gama ɓaɓatunta yayi burus da ita, ta ƙyale shi, ta koma sashinta, ta ɗebi ruwa tana alwala.
Ta ɗago za ta tashi, ta ji an yi ball da ita gaba, ta dungura.
Cikin tangaɗi da maye, ya ce "Ke banzar tsohuwa, ban gaya miki babu ruwanki da ni ba? Ko in tashi ko kar in tashi ban hana ki shiga harkata ba"
Iya da ƙyar ta motsa, wani irin jiri ya din ga ɗibar ta, taga gari yana jujjuya mata.
Kan ta ankara, ya sake surarta yayi jifa da ita kamar tsummokara.
Ta kurma uban ihu, amma ba kowa, ya din ga jifa da ita, tun tana ihu, ta koma kakari, jini ya fara zuba daga hancinta.
Ya sake surarta yana tangaɗi ya nufi wawakekiyar rijiyar da ke tsakar gidan.
Ayshercool
PAID ADVERT!.
Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku
Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi Man garan gashi Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921
*TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*
BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.
CUTARWA!
AYSHERCOOL
(BRIGHT PENS)
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
47
PAID ADVERT
*Hajiya ina zaki? Saurin me ki ke yi haka? Ɗan bani aron mintuna biyu kacal, na gaya miki albishir ɗin da na zo miki da shi. Shin ko kin san sirrin sheƙin fatar ummi, da ya sanya ta kama zuciyar MD raihan ta hana shi sukuni? Kai ba ma skin care ba, har da sirrin gyaran gashi, ina masu fama da amosani, karyewar gashi ko kuma sanƙo, jan gashi ne da ke? Ko taurin gashi kamar soson ƙarfe. Idan matsalar ki budurwar fata, tare da rashin glowing, Annur skin scrub da hair bliss sun shirya tsaf domin magance muku kukanku, me ku ke jira ku tuntuɓe su a kan lambar wayar su dan ƙarin bayani 07045971194 ko 08140450950*
47
Gadan-gadan ya nufi rijiyar yana tangaɗi.
Amaryar kawu Ilyasu ta ƙwala ihu da salati, bayan ta shigo daga cefane.
Bai kai ga rijiyar ba, ya sake yin jifa da ita. Ta tafi da gudu tana kiran sunan iya, sai dai jini sai zuba yake daga hancinta.