Cutarwa complete by ayshercool - Chapter 65
Cutarwa complete by ayshercool Chapter 65: Cutarwa complete by ayshercool Chapter 65. Kamar daga sama raihan ya shigo ya ce "Hajiya ba ni su na gansu"
3,355 words
Kamar daga sama raihan ya shigo ya ce "Hajiya ba ni su na gansu"
Hajiya ta maze kamar babu abun da yake faruwa ta ce "Tun yanzu ka fara nuna wariya, ka tafi wurin matarka ko ɗaukar su ba ka yi ba" cikin washe baki ya ce "Tuba nake, dole in fara zuwa kanta, saboda su an yanka mini mata" yayi maganar ko a jikinsa yana ɗaukar su, wanda hakan ya sake ƙular da mami.
Ya ce "Tubarkallah, Hajiya irin idon ummi ne da su, brown masu kyau masha Allah, yaya ka ga namijin kallesu duk farare. Alhamdilillah" yayi maganar yana kallon Salim.
Farincikin da mariya ta gani a fuskar raihan, sai ya mantar da ita takaicin abun da mami ta yi musu.
Sauran mutanen maiduguri da suka zo ganin gidan mariya, suka cika asibitin. Ana jimawa ma sai ga dr. Ga Alhaji.
Raihan ya din ga sanar da ƴan uwa batun haihuwar.
Tsabar takaicin yadda raihan yake rawar ƙafa, ya sanya ta tashi ta bar asibitin.
Sai da ummi ta yi awa shida tana bacci, sannan nurses suka tasheta, suka ɗagata aka wanke ta, sannan aka bata abinci. Ta saka kaya tayi kyau, kamar ba ita ba, sannan aka turo ta a kan gado aka mayar da ita main ɗakin da take.
Suka din ga murna ganin an fito da ummi ras da ita.
Sai jerawa ummi sannu ake yi, aka miƙo mata yaran dan ta shayar da su, amma ta kasa saboda yadda ido ya yi yawa.
Hajiya tare da Salim suka koma gida, ta yi wanka ta yo girki, suka dawo da Alhaji.
Shi ma Alhaji baki buɗe yake ta murna, yana yi wa jariran addu'a, duk da babu wanda ya gaya masa abun da matarsa ta yi.
Sai dai noor ta gaya wa ummi, abun da mamin ta ce, wanda ba ƙaramin ciwo yayi mata ba, sai dai ta basar saboda tana cikin murnar kyautar da Allah ya bata.
Ummi ta ce "Mama, jikin yaran nan kamar jariran mage, basu da gashi kwata-kwata".
"Me ki ke ci na baka na zuba? Zai fito in sha Allah"
Dr. Ma da daddare ya zo ganin jariran, tare da yi mata sannu.
Kusan kwanaki uku, ana ta shigowa ana fita duba ummi, a kwanaki ukun nan gashi ya cika kan yaran nan fal.
Kwanan ummi biyar, aka sallame su daga asibiti, raihan ya ce bai yadda a ɗauki hoton yaransa ba a saka a waya. Saboda masha Allah kai ba zaka ce ummi ce ta haife su ba, dan sun fi kama da larabawa sosai.
Su Hajiya Aishan bauchi, da sauran jama'arta, duk suna kano, sai da ummi ta yi kwana goma da haihuwa, sannan aka shirya gagarumin taron suna a wani katafaren event center.
Sai ranar suna ƴan gagarawa suka zo, aka ci aka sha, ummi sun samu kyaututtuka sosai da sosai ita da yaran, manyan mutane abokan hulɗar Alhaji Tahir, da abokan aikin Raihan, ban da ƴan uwa da abokan arziki.
Sai dai kan ranar sunan nan, yaran nan sun juye kalar larabawa sosai da sosai, gashi ya cika kansu da girarsu, kuma dukkansu brown eyes ne da su, namijin mai baƙin gashi, macen kuma irin na ummi.
Sai dai sunan da aka sakawa yaran ya yamutsa hazo, dan kuwa raihan sunan ummi ya saka wa macen Salma, namijin ya saka masa Muhammad, wai ya yi wa kansa takwara, ya yi wa Alhajin su, kuma ya yi wa mahaifin Ummi, tun da duk sunansu Muhammad laƙanin ne daban-daban, aka yi musu laƙani da Iman da kuma Ayman.
Ba yadda ummi ba ta yi da raihan ba, a kan ya canzawa macen suna, kar ya janyo mata magana a cikin dangi.
Amma ya ce "Kome mutum zai ce ya ce, son da nake yi miki, dole na yi miki takwara dole duniya ta shaida ina son matata".
Noor ta sha kwalliya, kamar amarya.
Ta je ta saka salim a gaba, sai ya yi mata hotuna da iphone ɗin sa.
Ya gama yi mata hotunan yana nuna mata, sai murmushi take yi, ya kalleta ya ce "Kin yi kyau kamar ranar bikinmu" a razane ta kalleshi ta ce "Bikinmu kuma?"
"Eh mana, ko ba kya so na?"
Ta ɗan sosa kai ta ce "Yarinya ce fa ni"
"Ba kya son tsoho ko?"
Ta girgiza kai ta ce "A'a kai ba tsoho ba ne"
Ya ce "Tsoho ne mana a kan ki, am 37 you are just 15, dama so nake bayan suna in yi wa Alhajinmu magana, amma tun da kin ce haka shikenan, idan kin gama hotunan ki kawo mini wayar"sai kuma ta ji babu daɗi.
Mami kuwa a ranar sunan sai da ta kira raihan, ta ƙare masa zagi da cin mutunci, wai ya ƙare a gidin mace, saboda asara har da saka wa ƴar sa sunanta, bayan uban kuɗin da ya kashe mata ita da yaranta.
Shi dai yayi shiru bai ce komai ba, dan ya san duk abun da ya yi wa ummi bai faɗi ba, kuma ba zai yi hidimar da Alhajinsu yake yi wa iyalinsa ba.
Da daddare ummi ta yi wanka ta saka kaya, Anty maryam ma ta wanke jariran, an samu sun yi bacci saboda sun gaji, sun sha kuka da jagwalgwalon ƴan suna.
Raihan ya shigo yana yi wa ummi murmushi.
"My MD, murmushin me ka ke yi ne?"
"Kallonki kawai yana sani murmushi, amma murmushin na yau na musamman ne, guess what?"
Ta girgiza masa kai ta ce "I have no idea"
Ya kamo hannunta ya danƙa mata mukullin mota ya ce "Gashi in ji Alhaji, ya ce a baki ya riga ni"
Ummi ta waro ido ta ce "MD mota Alhaji ya bani" ta rungume raihan tana murna, ta din ga zuba masa addu'a da shi da Alhaji.
Da gudu ta fita falo, tana nuna wa su mama da ba su riga sun bar gidan ba, aka din ga yi mata murna.
Noor ta ce "Yaya ummi baki ji zuciyata ba, na taya ki murna, amma ina son mu yi magana"
Suka keɓe da noor, ta gaya wa ummi abun da ya faru tsakaninta da Salim.
"Noor meyasa baki da wayo ne? To meye aibun yayan?"
Noor ta ce "To ai ni yarinya ce, kuma ni bana son ayi ta yi mini surutu kamar yadda aka yi miki"
"To sai me? Wataƙila da ina nan a gida ban yi auren ba, ai yanzu ki samu mai sonki tsakani da Allah shi ne. Shi da ake son ya yi auren ma, kin san da manyan ƴan mata nawa aka haɗa shi, duk ya ce ba ya so dan ya ce yana sonki zaki wulaƙanta mini yaya, to kin yi wa kanki"
Noor ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri"
"Kin fi son ki koma gida kina jerawa da kausar kuna faɗa kenan? Ke ba kya son ki ganki kema a gidanki?"
"To ai yanzu ba a gida nake ba, gidan mama zan koma, ni ba zan koma gidanmu ba, maama haushina take ji kamar ba ta son ganina ma"
"A'a ba sonki ne ba ta yi ba, amma dai yaya Salim dai kin yi wa kanki"
"Na shiga uku, yanzu ya zan yi?"
"Ki ɗauki waya ki bashi haƙuri"
Noor ta tura baki ta ta ce "Salon ajina ya zube" ummi ta ƙare mata kallo kawai tayi tsaki ta bar ɗakin.
Ummi na komawa ɗaki ta kira Salim, suka gaisa sannan ta ce "Yaya ka ji Alhaji ya bani mota?"
Yayi murmushi ya ce "Na riga ki sani ai, ina taya ki murna ƙanwata"
"Na gode sosai yaya salim, Allah ya saka muku da mafificin alkhairi"
"Amin ƙanwata, Allah ya raya mana su Iman"
"Amin yaya. Yauwwa noor ta gaya mini shirmen da ta yi maka, abun duk ya dame ta, dan Allah ka rabu da ita, Alhaji ya samu dr. Da maganar".
Yayi murmushi ya ce "Kin je kin takura mata ko? Bana son takura ta, daga baya nake ganin kamar na yi wauta nayi mata tsufa"
"Dan Allah ka bar wannan maganar, tana sonka, duk ta damu fa"
"Amma, kina ganin dr. Zai bani noor kuwa? Kin san ni ina da case"
"A'a yaya me zai hana? Kuma dan kana da case sai a ƙyamace ka? Ai yanzu ka shiryu a kan yadda na sanka a da, dan Allah ka ƙyale shirmen noor yaya"
Yayi murmushi ya ce "Auta danger, shikenan zan yi tunani, a bata lokaci"
"Dan Allah yaya ka ƙyaleta, mun yi magana da ita fa"
"To shikenan, sai da safe"
"Yauwwa yaya, a yi wa su hajiya bangajiya"
Suka yi sallama, ta din ga addu'a, Allah ya tabattar da alkhairi, dan tana fatan noor ta yi aure da wuri, tun kan farida ta ƙwace ta, ta siffantu da miyagun halayenta.
Har dr. Ummi ta kira, ta sanar masa da abun alkhairin da Alhaji ya yi mata.
Ƴan gagarawa sai da suka kwana uku a gidan ummi, da zasu tafi ta haɗa kayan suna ta basu suka tafi da shi.
Ummi ta saka noor a gaba, ta bata waya ta kira Salim.
Sai dai da ya ɗaga wayar ya ji murayarta, bai kashe ba suka gaisa.
"First born"
"Mmmm auta"
"Fushi ka ke da ni ko?"
"Me ki ka yi mini zan yi fushi da ke?"
Ta ɗan sosa kai ta ce "Maganar da muka yi ranar suna".
"Ai ta wuce auta"
"Ba ka so na yanzu?"
Yayi murmushi ya ce "Ke dai ba kya so na, an bar maganar bana son takura miki"
"To yanzu na canza shawara ka yi haƙuri"
"To" ta ɓata rai saboda yadda yake bata amsa a taƙaice da izza.
Ummi ta girgiza mata kai, alamar kar ta yi fushi.
"Yaya Salim"
"Noor"
"Idan muka yi auren zaka bar ni in yi makaranta, ka ga yaya inteesar mijinta hanata yayi daga baya".
"Zan barki in sha Allah"
"A'a rantse da Allah, kar ka canza shawara" yayi mata shiru, ummi ta dafe kai, saboda wautar da noor ɗin ke yi.
Bayan sun gama wayar, ummi ta ce "Eh lallai akwai jan aiki a gabana, noor babban mutum yayi magana ki ce ya rantse? Ke fa baki da kai"
"To ba ki ji yadda yake yi mini magana da gadara ba, da fa ba haka yake yi mini ba"
"Ba aurenki zai yi ba yanzu? Dole yayi miki izza. Ke fa miji ba abun wasa bane ba" ta din ga yi mata faɗa.
Ummi ta ƙara ɗaura aniyar, raba noor da Farida har zuwa lokacin da za a saka auren noor ɗin, saboda kar ta ɗorata a kan mummunar ɗabi'arta na raina miji da yin asiri.
Ummi ta kira Alhaji a waya, ta din ga yi masa godiya, tare da yi masa adduo'i masu daɗi.
Ummi ta tara kuɗi da suturu, da sauran abubuwa.
Farida kuwa tayi watsi da dr., Shi ma yayi watsi da ita ya daina shiga sabgarta kausar ma ta biye mata ba sa kula shi.
Yau yana gidanta, tana ta cika tana batsewa, ta same shi a fall ta tsaya a kansa ta ce "Malam yaushe za ka dawo mini da ƴa ta ne?"
Ya ɗaga kai ya kalleta ya ce "Ke da noor, sai lokacin aurenta, ta bar gidan nan kenan na bawa mariya ita"
"Wallahi ba ka isa ba, ai ba ita ta haifa mini ita ba, da zaka bayar mini da ƴa"
"Ni ban isa na ƙwace miki ƴa ba, halinki da ki ke nuna mata ne, ya sanya ta guje ki ita ma" za ta yi magana wayarta ta fara ringing.
Ta ɗaga wayar ta yi sallama.
"Farida kina ina, ki yi maza ki zo asibitin murtala emergency, Rahama mijinta ya ƙonata da ruwan zafi da ita da ƴar da take goyo"
Farida ta dafe ƙirji ta ce "Ruwan zafi me tayi masa?"
"Wai faɗa suka yi, ta tafi tsakar gida tana girki, ya zageta ta rama, ya fito yayi balla da kurfotin gabanta da tafasasshen ruwa a kai, da garwashin duk ya watse musu a jiki ita da ƴar"
"Innalillahi na shiga uku" tayi jifa da wayar tayi ɗaki tana salati.
Kiran sallar la'asar ake yi dama, dr. Ya fice sallar isha'i, dan bai san me aka ce mata a wayar ba.
Daga sallar isha'i, ya tafi gidan mariya.
Ya tarar ta idar da salla tana zaune ta yi shiru.
"Ya dai, na ganki sai a hankali, ina noor ne?"
"Tana gidan ummi, ai noor ta gujeni saboda sun yi jarirai"
Yayi murmushi ya ce "Noor an kusa girma, Alhaji Tahir ne yayi mini magana, wai su na riƙo Salim yana so, na ce zai sha shiririta"
Mariya ta ce "A'a kar ka ce haka, abu namu ƴa ta wa ɗa na wa, za ta yi hankali in sha Allah kan lokacin"
"Wane lokaci kuma, shekara ɗaya ne kawai fa, tana gama secondary school ne suke so"
Mariya ta yi dariya ta ce "Allah ya sa zamu gani"
Ya ɗan kalleta ya ce "Kamar akwai magana ko?" Ta jinjina masa kai alamar eh.
"To ya aka yi?"
"Dr. Tun muna waccan ƙasar kamar ban kuma al'ada ba fa"
Yayi dariya ya ce "To me ki ke so in ce?"
"Koma meye ka ce mana"
Dr. Yayi dariya ya ce "Maman ummi rigima, kin fi ni sanin meyake faruwa ai"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wai ciki ne da ni?"
Dr. Ya kashingiɗa yana dariya, gaba ɗaya ta ruɗe "Haba dr. Ummi na jego nima a ganni da ciki, na shige su"
"To laifina ne? Ni dai ina so ina murna Allah ya raba lafiya, kowa ya kalle ki fa zai gane kin ƙara haske sosai" gaba ɗaya ta rikice, wai abun kunya ne, shi kuma ya din ga yi mata dariya. Gaba ɗaya ya manta da a gidan farida.
Ummi na ɗaki tana ta yi wa noor nasiha, a kan maganar salim, ta ce mata ita tana son sa amma tsoron auren take yi, ummi tana ta lallaɓata, dan sun yi magana da dr. Kuma ta san zai kira noor ɗin ya tambaye ta.
Anty Maryam ta shigo ɗakin ta ce "Ummi, kin yi baƙuwa, sai wani harare-harare take yi, ban san me aka yi mata ba, amma da alama ƴar uwar mai gidan ce, suna kama da shi"
Ummi ta yi murmushi ta ce "Anty ki ce ta shigo".
Mintuna kaɗan sai ga Maryam ta shigo.
Ummi ta ce "Sannu da zuwa, yanzu ki ke tafe?"
Ta ja tsaki ta zauna.
Noor ta ce "To, ikon Allah"
"Noor kawo mata ruwa da yaran ta gansu"
"Ai fa, an samu abun da ake so, an samu daular da ake kwaɗayi tashin farko an zubo yara biyu, yaran da aka ce babu kalarsu a danginmu"
Ummi ta yi dariya ta ce "Ai abun alfaharinku ne, kun samu iri a dangi. Kuma ƴaƴa biyu sai matar so ba kwaɗayayyi ba, abun alfaharinku ne, ƙaninki akwai himma, ko kuma maybe daga ni ce"
"Ummi ni ki ke gaya wa haka?"
"Ke fa ki ka fara, wai kwaɗayi? Ke in kwaɗayi ne kawai ya kawo ni gidan nan, da ban kai haka a cikinsa ba"
Noor tayi sallama, ummi ta amsa, ta miƙawa maryam yaran, maimakon ta karɓa ta ce "Ba shakka, dole mami ta ce akwai lauje cikin naɗi a wannan yaran, ba zata taɓa karɓar su a matsayin jikokinta ba"
Ummi ta ce "Noor mayar mini da ƴaƴana wurin Anty"Noor na fita ummi ta ce "Kar Allah ya sa ku karɓe su a matsayin jikokin, ku mayar da su in da suka fito, tun da ubansu ya san nasa ne shikenan. Dama ni ban ce ta ƙaunace ni dole ba, tun da ba ku ku ka halicce ni ba. Ni yanzu a duniyar nan da a so ni da a ƙi ni duk uwar ubansu ɗaya. Babu yadda ban yi ba wurin yi wa mami biyayya, da girmamata amma ba ta gani, a gaban uwata saboda rashin ta ido, take cewa wai yara ba na ɗan ta bane, da yake uwata ba zuciya ce a ƙirjinta ba ko? Maryam da zan baki shawara da kun daina jayayya da ikon Allah, ni da raihan ajiyar Allah ne mutu ka raba. Idan ku ka cigaba da takurawa aurena ko kun raba aurena da raihan, zan cigbaa da rayuwar aure da shi ina haihuwa ko da aure ko babu, dan a yanzu ba wani ƙalubale ko abun kunya da ba zan iya fuskanta ba. Zaman gidan raihan, da zazzago ƴaƴa yanzu na fara, idan kin ga dama daga nan ki je wurin mami ki yi mini wani sharrin ke ta shafa da ke da ita"
Maryam ta miƙe ta ce "Ummi, mamin ki ke gaya wa haka?"
"Idan tsoho bai ji kunyar hawa jaki ba, jaki ba zai ji kunyar kayar da shi ba. Na yi iya yi na, na gaji, ba zan cigaba da cusa kaina in da ba a ganin kima ta ba. Kuma wallahi idan kuka cigaba da uzzura mini, hakkina zai fara bibiyarku ai ke ma mace ce, kuma a gidan wani ki ke aure, a sannu kema zaki haɗu da dai-dai ke".
Ta fice ta bar ta a ɗakin a tsaye.
Farida kuwa hankalinta ya tashi, saboda yadda ta je ta tarar da rahama, a asibiti, jikin yarinyar duk ya saɓule, haka na rahama cikinta, fuskarta da ƙafafuwan ta duk sun ƙone ƴan sanda sun kama mijin nata.
Ta din ga kuka tamkar za ta zare.
Ummi kuwa duk da furucin da Maryam tayi mata, ko a jikinta ta miƙe ƙafa ta cigaba da sabgoginta a gidanta.
Hausawa suka ci idan kana da kyau, ka ƙara da wanka, ummi ta san in dai ɓangaren kula da mijinta ne, to tana da kyau ba a magana a ɓangaren kula da raihan. Amma duk da haka, maganar hausawa gaskiya ce, dan haka ba ta yi ƙasa a gwiwa ba, wurin lalubo lambar Amina Gachi, CEO beenad herbal center, mussaman ita da taɓa fama da ciwon sanyi, kuma galibi ciki ya kan tayar da ciwon, dan haka nemi Amina gachi, domin shiryawa koma wa ɗakin mijinta.
(Bari na baku bayani, beenad herbal center, ba iya maganin sanyi suka ƙware ba, suna bayar da magunguna daban-daban dai-dai da matsalolin ku, damun kawo daidaito a gidajen auren ku. Suna da kaya kamar haka; Shedaniyar gumba Gumba mai saying Garin mai kabbara Mai dalalan miyau Wayyo dadi Zumar kwakwa Zumar ridi Zumar dabino Zuma mai ma'ul ijaba Farin jini Gumba kalla kalla da dai sauran su A BEENAD HERBAL suna da turarukan wuta da humrah kalla daban daban sai Wanda kuka zaba Ga kuma maganin slimming Gyaran nono Maganin hips Maganin Kara kiba Da dai sauran su. Kayan mu tested and trusted ne Suna maraba da masu siyan Daya ko sari Suna Nan cikin garin kaduna Kuma suna tura Kaya duk inda kike da yardar Allah
AMINA GACHI 07034404975 CEO BEENAD HERBAL MEDICINE &INCENCE KADUNA Phone no 07034404975.
Da labarin abun da ya faru da rahama ya zo kunnen ummi, hankalinta ya yi mummunar tashi, dan sai da ta yi kuka, dan yadda Abdul ya gaya mata abun babu daɗin ji, ummi ta ce raihan ya bar ta je ta dubata, ya ce ba zata fita ba sai tayi arba'in.
Yaran raihan kamar ana hura su, dan baya wasa wurin kula da su, ummi na cin abinci mai gina jiki, da zai samar mata da ruwan nono, kunu masu kyau da kayan marmari, su kuma yaran ga isashshiyar madara yana saya, kan su yi arba'in suka cika ɓul-ɓul gwanin sha'awa.
Can gagarawa, aka samu wani irin maimakon ruwan sama, kamar da bakin ƙwarya, ga ƙarfi ga kuma iska hakan ya sanya rufin ɗakin iya kwashewa.
Dama dr. Ne ya bayar da kuɗi, a gyara mata ɗakin ta saka aka yi rufi ta karɓe sauran kuɗinta ta cinye, sai ledar ɗaki da ta saka.
Iska ta yaye kwanon, ruwa ya din ga zuba a kanta, ruwa ya jiƙa tsohuwar ƙasar da aka yi ginin ɗakin da ita, ita ma ta zube wani ya danneta, ban da katakon rufi da ya din ga ƙwalo mata a ka.
Gashi itakaɗai take kwana babu kowa a wurinta, dan haka babu wanda ya san abun da ya faru sai washegari.