Cutarwa complete by ayshercool - Chapter 9
Cutarwa complete by ayshercool Chapter 9: Cutarwa complete by ayshercool Chapter 9. Karo na farko da iyalan su mariya suka ji mahaifinsu yayi wa wani ɗan…
3,351 words
Karo na farko da iyalan su mariya suka ji mahaifinsu yayi wa wani ɗan adam Allah ya isa, wanda sai da ya zubar da hawaye, yana matuƙar tausaya wa mariya, dan haka bai gaza ba, ya sake tashin yaya magaji, tare da Maryam, ya ce su je su bawa uwar mijin mariya haƙuri, ko sau ɗaya ta bayar da ummi, ta zo ta kwana biyu tare da mariya, ko a samu hankalinta ya kwanta.
Yaya magaji ya ce "Baba, ka san matar nan ba zata bayar da yarinyar nan ba, sai dai a tafi da mariyar, ta je ta ganta mu dawo"
Maryam ta ce "A hakan zamu tafi da ita? Ba zai yiwu ba ai, kana kallon abun da take yi, ai salon ta sake jin daɗi ne, dan matar nan ba mutunci ne da ita ba, kuma muddin aka bawa mariya ummi, ba zata bari a sake rabata da ita ba, a ganina kawai mu mayar da hankali a kan nema mata lafiya"
Yaya magaji ya ce "Duk da haka, zan jarraba zuwa, duk da na san ba zamu wanyeta ƙalau ba, amma zan jarraba zuwa na ga yarinyar ma daga nan, Allah sarki ummi, na san yanzu ta yi wayo sosai.
"Zata shekara goma zuwa sha ɗaya fa yanzu, ai ta zama budurwa"
Suka bar maganar a kan cewa, yaya magaji zai je ya gano ummi, idan ya ga fuska ya sako zancen tahowa da ummi.
Ummi ta daina zuwa ɗakin iya idan ba dole ba, saboda gudun kar ace ta yi wani abun, kullum cikin itace nan da buhhunan hatsi take kwana. Tsabar daka kuwa hannunta duk yayi kanta, yayi ta ɗurar ruwa yana fashewa, saboda tana da taushin fata sosai.
Tana tafe tana yada hannu, saboda gajiya ga rana, yunwa da ƙishirwa duk sun addabeta, mutumin da ta hango a ƙofar gidan su ne tare da kawu Ilyasu, ya sanya ta tafiya a hankali, ta ƙarasa ƙofar gidan.
Shi ma ƙuri yayi da ido, yana kallonta, ta ƙarasa ta durƙusa ta ce masa "Ina wuni?"
Jiki a sanyaye ya amsa ya ce "Ummi kin gane ni?" Ta jinjina masa kai alamar eh.
"To waye ni?"
Maimakon ta bashi amsa sai ta ce "Ina mama?"
"Haryanzu baki manta da ita ba?"
Da sauri Ummi ta sake kallonsa ta ce "Da ita ku ka zo?"
"A'a, na zo dai neman alfarmar na tafi da ke na kai ki wurinta, amma sun ƙi yarda"
Kawu Ilyasu ya wani haɗa rai, cikin haushi kamar tsohon kare ya ce "Ke! Tashi ki wuce ki shiga cikin gida"
Ƙafafuwanta suka yi mata sanyi, ta ji tamkar ba zasu iya ɗaukarta ba"
"Ba zaki tashi ba?" Ya sake yi mata tsawa. Cikin rawar jiki ta tashi, yaya magaji ya kamo hannunta ya danƙa mata kuɗi, yana riƙe da hannunta ya kalli Kawu Ilyasu ya ce "Da ku da mahaifiyarku, ku shirya amsar da zaku bawa Allah, kalli wai wannan ƴar ɗan uwanku ce dan abun kunya, kalli kayan makarantar da suke jikinta, kalli ƙafafuwanta. Kun ce idan na tafi da ita babu ku babu ita, ku ba dangin mahaifinta bane ba, duk in da aka je aka dawo, da dangin uba ake ado, kuma ba zan cigaba da jayayya da ku ba, muna raba abun faɗa, Allah zai zama gatan marainiya"
"Ummi ki kula da kanki kin ji ko? Ki yi ta yi wa mamanki addu'a, hankalinta yana kan ki, Allah ya yi miki albarka".
"Wai ba zan sake ganinta ba?"
"Zaki sake in sha Allah, Allah ya shiga lamarin ki"
Rirriƙe hannunsa tayi tana kuka, tana yi masa magiyar ya tafi da ita.
Da ƙarfin tsiya kawu Ilyasu, ya fizgi hannunta, ya angizata zuwa cikin gida.
Tana kuka suka ƙarasa shashinsu, sai dai da munanan kalaman iya ta fara cin karo, tana ɗaga murya tana cewa "Ni dai azo a nema mini magani, a rabani da wannan dangin maitar da jaraba, sun kashe mini ɗa suna bibiyata saboda ƴar su na hannuna, ba dole mariya ta haukace ba, ai kaɗan ta gani, hauka bata ma fara shi ba, tun shekarun baya da na karɓi ƴar ba ta yi haukan ba sai yanzu, Allah ya ƙara tuburata, yadda ta rabani da ɗa na babu ita babu sukunin duniya!!".
Bright pens fans group, da sauran masoya ummin Iya, ina ganin sharhinku, ina godiya sosai da sosai 🙏🙏🙏
Ayshercool 08081012143 *CUTARWA!*
BRIGHT PENS (FREE BATCH)
arewabooks ayshercool7724 Watpad ayshercool7724 Subscribe my YouTube channel https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
P7
A guje mama ta koma tsakar gida, tana ƙwalawa malam kira, a kan ya zo ya ga abun da mariya take yi. Suka dawo a tare, ya tarar da yadda jikinta yake ta rawa tana jijjiga, ya fita da sauri, aka nemo maƙwabcin su, kasancewar yana da abun hawa, aka saka mariya a mota suka tafi asibiti.
Can kuma hashim ne ya fito zai fita titi, ya hango yara sun yi dandazo, har zai wuce ya hango ƙafar ummi, ya ƙarasa da sauri, ya tarar da ita a kwance, yara sun yage mata hajjabi, ta sanya hannayenta biyu ta rufe kanta, sai kuka take yi.
Wani irin baƙin ciki ya turnuƙe masa zuciya, ya rasa dalilin da ya sanya yara suka tsani ummi haka, kodayeke iyayensu suka gani suna yi, da sun tsawatar musu da tarbiyantar da su a kan girmama halittar ɗan Adam komai muninta, da ba su yi mata wani abun ba.
Kai tsaye ya je ya tarwatsa yaran, yayi nasarar kama auwwalu, ya din ga kifa masa mari, yana ball da shi, yayi masa dukan tsiya, sannan ya ɗaukko ummi ya shiga da ita gida.
Gaban iya ne ya faɗi ganin yadda ya shigo da ummi, ta miƙe tana faɗin lafiya?.
"Wallahi auwwalu ne ya tara yara, suka cire mata hijjabi suka yi ta dukanta a waje"
"Saboda iskanci, me tayi masa?"
"Oho masa"
"Kema uban waye ya ce ki fita?" Tayi maganar tana kallon ummi, da take ta zirarar da hawaye.
Ya ce "Dan Allah iya ki yi haƙuri, a jigace take, jikinta zafi rau da zazzaɓi"
Ya karkaɗe mata ƙasar nan, ya samu ruwa ya din ga shashshafa mata a jikinta, ya kaita ɗakin gwaggo ya kwantar da ita.
Iya kuwa mita take tana "Na rasa wannan baƙin jini na yarinyar nan, ƴa sai ka ce mujiya, ƴan uwanki yara ma gudunki suke yi, kodayeke ai dole a guje ki, wannan munin gaba ɗaya kalarki ba irin ta mutane ba" Hashim bai kula iya ba ya fice, saboda haushinta da yake ji, dan ya fara tsinkewa da lamarin son zuciyarta, gashi babu wanda zai iya tarar ta ya gaya mata gaskiya kowa tsoronta yake ji.
Duk yadda likitoci suka yi ƙoƙarin ceto ran mariya da yaronta, Allah bai yi ba, yaron ya zo babu rai, kuma alamu sun nuna ya kwan biyu da mutuwa a cikin ta, saboda yadda fatarsa ta fara marmasowa.
Sai dai har kusan kwana biyu da haihuwar ta, an kasa samo kanta yadda yakamata, da magani ya sake ta sai jini ya sake hawa.
Sai suka shafe sati uku a asibiti, sannan aka sallame su, suka koma gida, sai dai abu idan ba ya zama dole ba, ba ta magana.
Tunani kawai take yi, ko ta saci jiki ba a sani ba ta je ganin ummi, amma ta tuna wulaƙancin da iya ta yi wa yayyenta, ta san muddin ta je, ba abun da zai sauya, kuma hakan tamkar watsawa mahaifinsu da yayyenta ƙasa a ido ne.
Ummi ba wanda yake kula da bata magani, sai idan magaji ya shigo sashin Iya, ya sanya ta a gaba ta sha, duk da iya ta ƙwace kuɗin da kawunsu ya bawa ummi, da kuɗinsa ya saya mata yadin uniform, ya canza mata nata da suka yayyage suka yi mata kaɗan. Ummi ta ji daɗi sosai da sosai, ga sabuwar jakarta dan haka cike da ƙwarin gwiwa take zuwa makaranta. Kafin kwana bakwai, tuni kan ummi ya cika da gashi, kamar ba ayi mata aski ba, kalar wanda ya fita kalar sa ne dai yake sake fitowa a kanta, ba baƙi ne wuluk ba.
Duk wannan murnar da take yi na komawa makaranta, da tarin ƙoƙarin da ummi take da shi, ya zama a banza, saboda ko tambaya aka yi a aji, ba ta iya bayar da amsa, saboda gudun cin zarafi da tsokana da ƴan uwanta ɗalibai za su yi mata, koma malaman da kansu.
Wujiga-wujiga ta dawo daga makaranta, saboda azabar yunwa, koko ne kawai a cikin ta, shima tun sha ɗaya da tayi fitsari, take jin kamar an sace mata kayan ciki saboda yunwa.
Da ƙyar ta ƙarasa gida, tana zuwa iya ta ɗora mata kai niƙa, haka ta kuma kwasar rana, ta kai wa iya niƙan ta dawo, a wannan wahalen da take, wannan ya ja ya aika, wancan ya ja aika, har lokacin shiga makarantar allo yayi.
Iya ta rage mata abincin rana, bai fi loma uku ba, a loma ɗaya da kaɗan ta cinye, ta tashi ta tafi makarantar allo.
Naima ce ta hangota tana share hawaye da hijjabinta, ta ƙarasa in da take ta ce "Ummi, ya aka yi ki ka makara? Kuma kukan me ki ke yi?".
Cikin kuka ta ce "Malam babba ne ya dake ni, na makara"
"To meyasa ki ka makara?"
"Iya ce ta aike ni"
"Shegiyar mata, mai zuciyar kafirai" Naima ta faɗa a ƙule, ummi kuma ta kalli fuskar naima tana mamakin yadda take zagin babba kamar iya.
Ta ja hannunta ajinsu, ta ɗaukko wani ɗan kwano ta bata abinci, aikuwa hannu baka hannu ƙwarya ummi take danna abincin.
Na'ima ta dubi ummi ta ce "Ya jikin amma dai kin warke ko?" Ummi ta ɗaga mata kai alamar eh.
"Gashin ya fara fitowa?"
Ummi ta saka hannu ɗaya ta buɗe mata kan, Na'ima ta rufe mata ta ce "Masha Allah, ya fara fitowa, kin wanke kayanki na makarantar boko?"
"A'a yaya magaji ya saya mini sabon uniform na makarantar boko" ta faɗa cike da jin daɗi.
Na'ima ta ce "Alhamdilillah, Allah ya saka masa da alkhairi, na bayar a ɗinka miki atamfar bikina"
Ummi ta kalleta ta ce "Biki, aure kenan?"
Na'ima ta ce "Eh, aure zan yi ko in tafi da ke gidana?"
"Eh yaya Na'ima zan biki dan Allah"
Na'ima ta ciro ɗan ƙaramin tsumma a jakarta da ruwa a jarka, ta bawa ummi ta sha, sannan ta shiga goge mata hannu ta ce "Zan so ace za a bani ke na tafi da ke ummi, sai dai hakan ba zai yiwu ba, ki je aji idan an tashi ki jirani mu tafi tare, zamu je gidan mansura, an kawo mata takalma daga Kano, idan da wanda zai yi miki, sai na saya miki na biki"
Ummi ta ce"Ba zaki tafi da ni ba?"
"Ki yi haƙuri ummi, ba zai yiwu ba"
"Kema tafiya zaki yi ki bar ni? Mama ma ta tafi taƙi dawowa"
Na'ima ta yi ajiyar zuciya ta ce "Maza je ki ajinku, ga malam can ya tafi" ta miƙar da ummi tsaye, ummi ta tafi ajinsu.
Naja da take ƙawar na'ima, ta ce "Ke dai ki na son yarinyar nan naima, gashi kin saka mata ran tafiya da ita"
Na'ima da hawaye ya taru a idonta ta ce "Wallahi naja ina tausayin ummi sosai, wallahi da za a bani ita zan ɗauke ta, kakarta matsiyaciyar tsohuwa ce, ai babarta uwar ɗakina ce, mun yi mutunci sosai, baban ummi ya rasu, ta koma garinsu, Kakarta ta ƙwacw ta take azabtar da ita, ko a lahira na ganni gani g matar nan na san ban yi kyakkyawan ƙarshe ba" Duk da a ƙufule Na'ima tayi maganar, bai hana naja dariya ba, saboda maganar ta ta ƙarshe ta bata dariya.
Bayan tashi daga makaranta, tare suka tafi da ummi, hannunta cikin nata suna tafe tana yi wa ummi hira, tana bugun cikinta, dan jin zaman da take yi, sai dai abun babu daɗi mussman da ta gaya mata abun da su auwwalu suka yi mata, da aka yi mata aski. Na'ima ta ce "Bakomai Allah ya isanki wallahi, duk wanda yayi nagari kansa,. Ki yi ta haƙuri kin ji ummi, duk tsanani duk yunwar da ki ke ji, kar ki bari wani a mazan gidan ku, manya ko yara, su kai ki wani wuri, su saka hannu a jikinki, kin ji ko?" Maimakon ummi ta amsa sai ta ɗaga kai tana kallon na'ima.
Cikin sauri na'ima ta tsaya ta ce "Suna yi miki wasan banza ko?"
Ummi ta girgiza kai ta ce "A'a"
"Ki gaya mini gaskiya, suna taɓa ki ko?"
Ummi ta girgiza kai ta ce "A'a"
"Duk wanda ya saka hannu a cikin jikinki, kar ki yadda kar ki tsaya, ki yi masa ihu ki gudu kin ji ko" ta jinjina mata kai alamar eh.
"Ko bayan na tafi, idan kina jin yunwa, ki je gidanmu wurin babarmu ta baki abinci"
Da haka suka ƙarasa gidan mai takalmi, aka yi sa'a aka samu dai-dai ƙafar ummi.
Na'ima ta ce "Zan ajiye a wurina, ranar bikina in yi miki kwalliya ko?"
Ummi ta ɗaga kai tana murmushi, daga nan suka ƙarasa gida.
Ummi ta shiga gida hannunta riƙe da wani kara tana wasa da shi "Ke!" Idris ya kwaɗa mata kira a wulaƙance.
Ta juyo tana kallon sa.
"Zo ki sayo mini sukari a kanti" yayi maganar yana watso mata kuɗi.
Ta durƙusa ta ɗauka, ta je ta sayo masa, sai dai ta din ga tuna gargaɗin Na'ima na hanata zuwa ɗakin su idris.
Ta nemi wuri ta zauna a ƙofar shiga wurin, ya gaji da jiranta ya fito.
"Dan ubanki ina aiken da na yi miki?"
Da sauri ta miƙe tana nuna masa sukarin.
"Ba zaki shigo ki kawo mini ba saboda baki da mutunci, sai ki nemi wuri ki zauna?"
Tayi shiru tana kallon sa, "Ba zaki kawo mini ba" ya sake yi mata maganar cikin tsawa.
Ta ƙarasa in da yake cikin jin tsoro, sai dai ya ya haɗa da hannunta, ya ja ta cikin ɗakin.
Kuka ta fara yi masa iya ƙarfin ta, yau ya samu damar da rabonsa da ita an daɗe, amma ta nuna masa tayi wayo yanzu, dan haka ta din ga yi masa kuka da ƙarfi, kamar yadda Na'ima ta gama gaya mata ɗazu.
Wawan marin da ya kifa mata ne, ya tafi da ji da ganinta na wani ɗan lokaci, ta dafe kuncinta jikinta na wata irin tsuma, tana karkarwa.
Wata sharɓeɓiyar wuƙa ya nuna mata ya ce "Ki ka cigaba da yi mini kuka, sai na yanka wuyanki" kallonsa take yi, kallo mai cike da tsoro da tsana, ya ajiye wuƙar tare da sanya hannayensa cikin rigarta, rigar da bakomai a ciki sai teɓa dan wannan dai ba nono bane.
Ba ta karaya ba, ta fara kokowar cire hannayensa daga jikinta, tana kuka mai cin rai, iya ƙarfin ta.
Bankaɗo ƙofar ɗakin aka yi, hakan ya razana shi, dan bai yi zaton zuwan wani a dai-dai wannan lokacin ba.
"Idris meye haka?" Hashim yayi maganar yana kallon sa.
"Kamar yaya meye haka, abun da ka gani" a fusace ya ƙarasa ya hankaɗe idiris, ya janye ummi, ya kalli idiris ya ce "Wani irin banza ne kai, ba zaka girma ba a rayuwarka, da me yarinyar nan za ta ji ne?"
Wani uban tsaki idiris yayi, ya ce "Ka daina shiga sabgata ba ruwanka da ni".
"an shiga sabgar taka, wallahi idan baka rabu da yarinyar nan ba, sai na ɗauki mummunan mataki a kan ka"
"To ka ɗauka mana kar ka fasa" ya sake jan tsaki ya fice.
Cikin ƙunar ran yadda ƙaninsa ya raina shi, duk saboda iya na goya masa baya, ya kalli ummi ya share mata hawaye, ya fito da ita daga ɗakin, shaidar yastun idiris kwance a kan baƙar fuskarta, da har idonta yayi taruwar jini.
Ya zubawa ummi ido, da haryanzu jikinta yake tsuma, ga wata irin nannauyar ajiyar zuciya da take yi, har a lokacin a tsaorace take, kuma hawayenta ya ƙi tsayawa.
"Ummi" ya kira sunanta, sai dai bata amsa ba, ta sake fashewa da kuka.
Wani irin tausayinta ya ratsa zuciyarsa, ya din ga share mata hawayen, ya riƙe hannunta suka nufi sashin iya, tana ta dakan fura tana waƙe-waƙe.
Tana ganinsu tare ta hau bala'in tun ɗazu take neman ummi, zata aiketa amma daga zuwa makaranta ta zauna.
Magaji ya ce "Iya"
"Ya aka yi"
"Dan Allah idan ba za a iya riƙon yarinyar nan ba, a mayar wa da uwarta ita, idiris fa na kama yana neman haike mata a ɗakinmu, wace irin rayuwa ce wannan, kalli yadda ya mare ta, haba dan Allah"
Iya ta dafe ƙirji ta ce "Shi idiris ɗin? Ita uban me ya kaita in da yake, me ya kaita ɗakin ku, ai ita ta kai kanta, amma shima zai zo ya same ni, da ni yake zancen. Kai kuma sai ka ce ba ɗan uwanka ba, ka ke ɗaga murya tona masa asiri zaka yi?"
"Iya to zuba masa ido za ayi, idan abun da ba a so ya faru fa?"
"Ba abun da zai faru sai alkhairi, jeka zai zo ya same ni, ke kuma canza kayan ki zo ki kai dusar nan gidan lami, ta bawa dabbobina"
Hashim ya ce "Ni bani dusar na kai, kalli yadda take a razane"
"Ba wani a razane, da a razane take ai da ba ta kai kanta ba, yarinya ƙanƙanuwarta da ita, ta san ta je wurin namiji"
"Haba iya, me ummin ta sani da zaki faɗi wannan mummunar maganar a kanta?"
Iya ta ce "Zaka zo ka kai mini dusar ko ta ɗauka ta kai mini?"
Ya ƙarasa ya ɗauki dusar ya fita, zuciyarsa kamar ta tarwatse, tausayin yarinyar na damunsa sosai da sosai.
Kwanaki biyu tsakanin abun da ya faru, sannan idiris ya shigo sashin Iya.
Iya ta dube shi ta ce "Idris, kashedi zan yi maka a kan yarinyar nan, kar ka kuskura ka sake saka yarinyar nan a loko kana lalubeta, wallahi idan ka sake wani abu ya afku ba zan rufa maka asiri ba, kuma ba zaka janyo mini masifa ba, kai gashi ba sana'a ba balle ace ayi maka aure, in huta. Ina yi maka kashedi, wallahi wani abu ya faru ba zan saurara maka ba, na gaya maka"
Cikin fushi ya ce "Me kuma na yi, magaji ne ya zo ya ce na yi mata wani abu?"
"A'a ni banga magaji ba, bai gaya mini komai ba, fuskanta kawai na yi"
Ficewa yayi ba tare da ya sake magana ba.
Rashin samun biyan buƙatar sa a jikin ummi, ya sanya ya ji ya ƙara tsanar yarinyar, ko son ganinta ba ya yi, ita kanta ummi, har fargaba take yi a aike ta, saboda bayan iya ta yi masa wannan faɗan, sai da ya zane ta, saboda a zaton sa ita ta gaya wa Iya.
Duk wannan cin kashin da ake yi wa yarinyar, daga ƴan uwan ubanta da suke ciki ɗaya, da wanda uba suka haɗa da matayen su, babu wanda ya taɓa shawartar iya a kan sassautawa ummi azabtarwar da ake yi mata, tamkar ƴar tsintuwar da ta faɗo daga sama.
Azumi saura wata biyu, aka yi bikin na'ima, ta yi kuka sosai, ciki har da na rabuwa da ummi, dan har cikin zuciyarta take jin rabuwa da ummi.
Mariya kuwa tun ƴan uwanta na ta tata, suna rarrashin ta, suna bata haƙuri, har suka zubawa sarautar Allah ido suka ƙyaleta, ta riga dai ta kamu da larurar hawan jini, a hankali kuma ciwon damuwa ya fara addabar ta, kullum tana ɗaki, daga bacci, kuka sai shiru. Yaya ɗan lami ya fara tunanin ko ta koma makaranta, amma yanayin da take ciki, ya tabbatar masa da ko an mayar da ita makarantar ba za ta iya mayar da hankali ba. Dama labarin haihuwar ta ta ko su iya ba a gayawa ba, dan gaba ɗaya sun fuskanci sabgar Iya babu Allah a cikinta.
Yaya ɗan lami kuwa da suka ga mariya taƙi sakin ranta, ya ƙare mata cin mutunci, tare da tabbatar mata da muddin ta je wurin su Iya babu su babu ita, ƴa ce idan ta girma da kanta za ta neme ta.