Damuwata complete novel - Chapter 1
Damuwata complete novel Chapter 1: Damuwata complete novel Chapter 1. [10/10, 2:55 PM] 💘: DAMUWATA. (Sanin abin adona) By Mrsjmoon
3,309 words
[10/10, 2:55 PM] 💘: DAMUWATA. (Sanin abin adona) By Mrsjmoon
*EXQUISITE WRITER'S FORUM ( EWF).*
Da sunan Allah mai Rahma mai jin kai. Allahumma salli ala sayyidina Muhammadu wa ala alihi ada-da mafi ilmi salatin da'imatan bi du'a'un Janna. S.A.W.
*Sharhi.*
Labarin (DAMUWATA) hak'k'ina ne ban yarda a juyamin shi ta wani siga ba ko yimin iko da shi ta hanyar had'a document ko makamancin haka sannan ba kyauta ba ne amma da pages masu zuwa domin farin cikinku masoya. Allah ya sa mu amfana da darasoshin da ke cikinsa na khairan, muyi watsi da kishiyar shi Allahumma amin.
*Jimlar littafan marubuciyar:*
Free books.
Mabrukha Ra'ayi Rayuwar Bahijja. A tunanina Ruwan dare.
Paid books.
Bak'on lamari Rashin jituwa Banyi zato ba Rabi'atul Addawiyya Rumasa'u Mutunci Madara ne Doctor Laylah.
*Baki d'aya shafin sadaukarwa ne ga Aunty Maijidda Musa (Aunty Jidda) Allah ya albarkaci rayuwarta tare da zuri'arta biy jahiy Nabiy S A.W.*
Page 01.
Cikin talatainin dare wanda masu iya magana kan kirasa da suna mahutar bawa. Ni kam a gareni kiran shi na yi da lokacin gadin kaina domin zaune na ke a gefen katifana ba komi ke damuna ba sai barci wanda yake d'ibana ina korarsa da k'arfi da yaji domin bazanyi sakaci ya d'auke ni ba ya zamo rayuwata ta shiga garari. Abinda na kasa fahimta a rud'ad'd'en lamarin shi ne saceni ake sonyi ko kuwa b'atamin rayuwa.
'Sai dai b'ata miki rayuwa domin alamu sun nuna hakan.'
Sosa gefen wuyana na yi cikin aminta da amsan da zuciyata ta bani.
"Oh ni Deejah me ke shirin faruwa da ni ne? Waye wannan mutumin dake son dasamin bak'in tabbo mara b'acewa a jiki da ruhi? Ya Allah ga baiwarka Nana Khadijatu ka dubeni duban da batasan ya yake ba sai kai da ka halicceni, d'aukinka ya zamo jagoran yayewar duhun nan da na ke ciki."
Ruwan dake d'iga a bayan hannayena ya ankarad da ni kuka na ke yi mara sauti.
" Hak'ik'a DAMUWATA na dabanne da sauran mutane. Shin wai ahaka zan cigaba da rayuwa ban samun barci?"
Amsan da ban samoshi ba kenan tun soma fuskantan barazanar shigomin d'aki cikin dare har zuwa yanzu da na ke mai-maita shi.
Sake sosa wuyana na yi cike da tausayin kaina.
"A kwanaki biyun nan har na rame, samun barci alamun natsuwa ne dan haka rashinsa dole ya sakawa mutum ciwo, ya Rabbi ka bayyanamin abinda ke cikin duhun nan batare da hankalin Mamana ya tashi ba."
Motsin da na jiyo a bakin k'ofa yasa na zabura na koma bayan k'ofar na manne, jikina na mazari cikin bugawar k'irji, ina jin ana kici kicin bud'e k'ofar, ba jimawa akayi nasarar bud'ewa tare da turota a hankali, na d'auke numfashi ina kallon inuwar mugun sadda ya doshi saman katifana a cikin d'an hasken da ya shigo d'akin ta glob din waje, sam ban tsaya tantance ko waye ba duk da burina kenan gano shed'anin da ke lalibeni idan ina barci wanda na ke kwatar kaina da k'yar.
Ganin ya dage da neman inda na ke sai na silale cikin sand'a na fice daga d'akin zuwa mafakana wato d'akin tumakan Mama, wurin dana gyara tun da yamma dan b'oyewa saboda shigana makewayi ya sakani jin tsoro.
Na tsuguna a cikin dabbobi jikina na cigaba da rawa, damuwa ya kuma lullub'eni, sai lokacin naji dama na tsaya na kunna wutan d'akin naga fuskan mugun.
"A sannu zan gano ko waye insha Allah."
Na furta cikin matse gefen wuyana cikin nauyin idanu alamun kwanciya kawai na ke muradi.
'Deejah zurfin ciki banaki ba ne ki sanarwa Mama kada ya sami nasara akanki ya kaiki ya baro, ki jefa Mamanki cikin damuwa da ke kanki.'
"A'a ba zan iya wannan zancen da Mama ba, ina jin nauyin furta shi ga wanima balle Mamana."
'Zurfin ciki nan sam baiyi ba Deejah.'
"Na san da haka amma to ya zanyi?"
'Ki koreshi domin samun 'yancin furta matsalarki gudun cutuwa.'
Jinjina kai na yi domin na amince da wannan shawarar da zuciyata ta bani.
Na jima tsugune zuwan na ji wani abu mai sanyi na bin k'afana ya sa na mik'e, na kuma jin ya nad'emin dika k'afafun, aikam na daka uban tsalle na fad'a cikin tumakai, atake suka soma ihu sabida na firgitasu, bashiri nayo waje a guje na shige makewayi ina haki, muryan Mama da Baba na jiyo suna salati na fito da gudu a rud'e na rungume Mama ina mai danne kukana kada ya baiyana ta ritsani da tambayoyin dalilin yinsa alhali bani da amsa, sai na matse bakina da hannu d'aya ina lek'en abinda sukagani suke yiwa salati.
Maciji ne k'ato ya nad'e k'aramar tunkiya zare idanu na yi jikina na kuma d'aukan rawa ganin tunkiyar a wurin dana tsugunna d'azun ta ke kwance.
'Wato shi ne abinda d'azun ya nad'emin k'afafu?'
Tuno hakan ya sa na kwalla ihu ina tsalle tamkar macijin ne yazo ya sake nad'eni, a rud'e Mama ta kamani ta soma tofamin addu'a. Tsaki Baba ya ja yasoma fad'a.
"Ga Tunkiyanki nan cikin hatsari kin biyewa wannan sokuwan da batasan komi ba sai janyo miki asara."
"Uwata tafi min dik abinda na mallaka Malam dan haka bai dace ka had'ata da dabba ba domin darajar bil'adam mai girma ne sama da dukkan halittun duniya sannan Uwata kam bazata tab'a janyomin asara ba sai alkhairi, nasha sanar da kai wannan zancen amma ka kasa daina jinginamin ita da kalman k'an-k'anci."
Wani tsakin ya kuma ja tare da cewa "Ai sai ta korar miki macijin in gani tunda tafi ni amfani da daraja."
"Ni da kaina zan koreshi Malam domin lafiyar Uwata yafi nawa muhinmanci a yanzu kuma ni bance tafika amfani ba, dan Allah ka rika fahimtana."
"Ai sai kiyi tunda d'iyar t...
"A kul! Malam ka tsaya daganan kada ka furta abinda zai zamo sanadin rabuwarmu, da fatan ka tuna me na ke nufi?"
"Ke! Hurera kifita idanuna in rufe wallahi akan wannan yarinyar mai bak'i jini zan ci miki mutunci matuk'a."
Ina gani Mama zata sake magana na kulle mata baki ta kalleni na girgiza mata kai. Shiru ta yi ranta amugun b'ace, Baba ya buga babban rigarsa a fusace ya koma d'aki. Da kallo Mama ta raka shi zuwa can ta janye jikinta zuwa cikin dak'in tumakan, na biyo bayanta cikin rik'o hannunta ina cewa "Dawo Mama kada ya illamin ke na shiga uku na lalace."
"Insha Allah bake ba shiga uku Uwata balle lalacewa indai ina numfashi "
"Mama to ki...
Maganar ta mak'alemin ganin babu macijin ba sanmatarshi sai tunkiyan kwance ta mik'e bisa alamu ta mutu.
"Muje ki kwanta zuwa gobe mai cire maciji zaizo a fidda shi a inda ya b'oye."
"Mama ina ya je?"
"Ai dama ba zai tsaya ba tunda yaji motsin mutane."
"Mama kada yazo ya cutar damu muna barci."
"Wanda ya dogara ga Allah to Allah zai bashi kariya batare da saninsa ba, ki dage da mik'a lamuranki gare shi domin shi mai amsa buk'atun bayi ne."
Motsa kai nayi alamun gamsuwa da zancen.
Har d'akina ta kawoni wanda ta kunna fitillar dana kashe ina ganin zata fita na rik'ota bance komi ba kaina sunkuye motsa kai ta yi cikin fitar murmushi ta je ta kulle k'ofa tare da zubawa wurin da aka jijjije da k'arfi ido."
"Waye gwanin lalata miki k'ofa Uwata?"
"Nima ban sani ba Mama."
Na ambata cikin rawar murya.
"Uwata sanarmin da damuwanki."
"Lafiyalau na ke Mama."
"Ban yarda ba maza sanarmin kinsan ina jin dirin Damuwarki a k'irjina ko da baki furtamin ba wanda na tabbata kwanaki biyu nan duk kinyisu cikin damuwa ce musanman cikin dare kamar bakya samun ishashshen barci dubi da yarda kike tashi amakare kuma idanu kumbure."
"Kiyimin addu'a kawai Mama wata k'ila wasi-wasin shed'an ne ke hasko miki ina cikin damuwa."
'Uwata na san zurfin cikin ki dan Allah ki sanarmin da abinda ke damunki inyi maganinsa tun bai girma ba."
"Mama ki amince ina cikin walwalata ba abinda ke damuna."
"To Allah ya sa hakan ne dan nasan zurfin cikinki yafi k'arfinki Uwata, abinda na ke nusar da ke aitaka hakan ba abu mai kyau ba, dan Allah ki gyara kada wata rana ya cutarmin da lafiyarki."
Bance komi ba illa na kuma narkewa a kafad'arta ina lumshe ido alamun jin barci.
"Ina jin b'arayi sun soma harin gidan nan dan ko jiya najiyo motsi kamar ana gudu ko da na fito sai na samu Malam na dubawa, wata k'ila waken suyar da na yi cikonsa sukeyiwa fako."
"Allah ba zai basu sa'ar d'aukan komi ba."
"To Allah ya sa hakan."
"Amin."
"Mama kada ki tafi tsoro nakeji."
Na furta da sauri ganin ta janye jikinta daga nawa.
"Ba zan tafi ba Uwata mu kwanta a nan, Allah ya tsaremu da mugun ji da gani."
"Amin Mamana."
Na amsa cikin k'an-k'ameta domin a zahiri tsoron maciji ya danne bargaban da na ke ciki na azzalimin da ke kawomin hari a cikin gidanmu ba tsoron Allah.
Washe gari bayan na kammala tilawar karatun qur'ani kamar yarda na saba na fito na isa k'ofar Mama dan gaisar da ita domin tunda subahi ta koma d'akinta, sai dai kafin inyi sallama najiyo maganar Baba cikin d'aga harshe.
"Wallahi Hurera duk ranar da kika kuma zuwa d'akin Uwani kika kwana sai na sab'a miki kuma in had'aki da mai sakamako wato Allah."
Banjiyo me Mama ta ce ba sabida muryanta ya yi k'asa.
"Na dai sanar miki in har ina gidan nan ban yafe ba kika kuma kwana da baliga alhalin ga mijinki na buk'atarki dan kuyi aikin lada amma sabida rashin hankali kikayi watsi da shi kika manne a jikin 'yar...
Ban tsaya jiyo k'arshen kalaman Baba ba na bar k'ofar jikina na rawa domin na san k'arshen kalman yafi duk kan kalamansa muni. D'akina na koma na tura k'ofar da ta kusa fad'i k'asa na zauna gefen katifa cike da damuwa hawaye na bin kumatuna.
'Anya Baba shi yayi sanadin kawoni duniya kuwa? Ko dai da gaske ne da Maman su Khamila ke ambatamin 'yar karere? kai ban amince ba kawai salon kishinta ne na fitina ke kaita da yin kalamin wanda ko su Maman Anas bata bari ba.'
"Uwani!."
Najiyo sautin kiran da Baba ya kwallamin da k'arfi, ban samu amsawa ba ya kuma kwad'amin wani kiran da yafi na farkon k'ara, da sauri na fito ina hard'ewa.
"Dan Uwarki ki amsamin kinfi k'arfi?"
"Kayi hak'uri Baba."
"Dalla rufemin baki sokuwa kawai wacce bak'in jini ya k'are akanta ba mashin-shini, ai wallahi sai kin tsufa a gaban Uwarki ba aure tunda ta zab'i b'atamin rai a kanki."
Wani kuka ne ya zomin domin na tsani a hantareni, dik da na nasaba da hantarar Baba hakan baisa ya zamemin jiki ba dan kullum ya tozaratani sai na zubda jirwaye.
"Au ban ci Ubanki ba kikemin kuka sabida Hurera ta gama sangartaki?"
Matsawa gefa na yi da sauri saboda nasan yanzu zai iya kawomin duka.
"Tashi ki wanke wake alale nakeson karyawa da shi yau saura kuma ki tsaya sanyin jikin nan da kika kwaso a can duniya dan Hurera kam ita macece mai zafin jini."
Tashi na yi ina cigaba da kuka mara sauti.
"Uhm ko da ya ke meye gamin kifi da kaska da za...
"Ya isheka haka nan Malam, maza tafi Uwata kije ki kwanta dan ina jiyowa a jikina barcin nan bai isheki ba."
"Mama aiki zanyi in na gama sai in kwanta "
"Na ce ki tafi zanyi masa dik abinda ya keso domin samun ladar aure."
Ban sa ke magana ba na bar wurin amma ba d'aki na koma ba kamar yarda Mama ta umurceni, wake na tafi na d'ebo na jik'a na d'auka na koma can wurin rijiya sabida bana son jin zancen da su Mama zasuyi wanda bana dad'i ba ne kuma nasan duk a kaina ne.
"Wallahi bana son wannan takun sak'ar da sukeyi sabida ni, anya zan gama lafiya kuwa idan har ban kawo k'arshen samun sab'anin mahaifana a kaina ba? Tabbas dole na san abinyi dan kawo k'arshen rashin jituwarsu ta sanadina."
Ina wanke waken sai sabbatu na ke yi cikin muryan kuka domin ta wannan haryar nafi jin dad'in amayar da dukkan DAMUWATA.
**** Malam na sha gayamaka bana son abinda kakeyiwa Uwata, raina na b'aci ainun, wallahi duk in ka tozarta Uwata ji na ke tamkar ni kake tozartawa afakaice saboda baka tashi zaginta sai in munsami sab'ani."
"Au Allah."
"Eh, ina jin zafin abin matuk'a."
"To yanzu kika fara ji kuwa."
"Malam kenan, wallahi Allah kaji rantsuwar d'an musulmi, inda ace igiyar aure nan a hannuna ya ke na rantse da girman Allah da tuni na sallameka na huta da ganin tashin hankalin Uwata ta dalilinka."
"Duk sabida na tab'a Uwani kike yimin wannan kalaman Hurera? Shin ke da Uwani ina ce duka mallakina ne?
"Naka ne amma sai ka gyara mu'amalanka da ita sannan zan amince da kalamanka."
"Ya yi kyau Hurera, zan d'au mataki na k'arshe in Allah yaso."
"Malam tafi ka cigaba da laziminka kafin ka fito na tabbata Uwata ta gama alalen."
Mama ta sauya zancen domin tasan nacin mijinta, sam bai gajiya da ririta zance. Shi kam jifarta kawai ya ke yi da mugun kallo ba tare da ya sake yin magana ba.
Aikam kafin ya furta kalma ta bar masa wurin zuwa d'akin tumakanta ta janyo wacce maciji ya halaka daren jiya ta fito da ita waje ta koma d'akinta ba jima tafito rik'e da mayafi ta dubi Baba da ke tsaye har lokacin na harare-harare ta ce "Zan lek'a gidan Malam Habu mai macizai dan yazo ya ciremana kada ya dawo daga baya ya illatamu."
Bai tanka ba itama bata jira amsawarsa ba ta fice, tana shigewa zaure ya gyad'a kai cikin jan k'wata ya shige d'aki a fusace.
*** Kafin k'arfe Takwas da rabi na kammala dafa Alalen itama Mama ta gama dama kunun tsamiya tana soya fanke saboda Bata cin Alale dan yana b'ata mata ciki. Muna gama karyawa Malam Habu ya iso cikin mintoci goma da shigowarsa ya kama macijin kato da shi, duk tsoro ya maga cikani dan yinin ranar manne da Mama na yi domin Baba ya koma d'ayan gidansa sai na sami sakewa na yi ta zuba mata shagwaba tamkar k'aramar yarinya, ita kuwa ta yi ta biyemin tare da bani labarai masu saka nishad'i.
Ni da Mamana aminan juna ne DAMUWATA na ta ne haka nima damuwarta nawa ce.
A ranar Mama ta sanya aka cire k'ofar d'akina da aka karya aka sanja wani mai k'arfi tare da inganci sannan ta sanya aka soma ginamin k'amin bayi na wanka ta waje wanda za'a shigo da shi cikin d'akina. Da yake ta saki kud'i kafin yamma angama ginin floor da sauran gyaran bayi ya rage wanda suka ce washe gari zasuzo su k'arasa.
Washe suka dawo suka kammla komi bayina k'arami mai kyau dan har da tayis aka sakamin a k'asa da jikin bango tare da yimin cabinet na ajiye kayan wanka. Iya farin ciki nayisa, k'awata Fanta na ta tsalle tare da janyoni wai sai na taka rawa ni kuma ban iya rawa ba sam, Mama na gefe sai dariya ta ke yi mana ganin yarda Fanta ta dage tana ta kwasan rawa wai Mama ta maidani yar gayu, kuma Abin k'arin farin ciki har aka gama aikin nan Baba bai lek'o mu ba, faruwar hakan yafi komi farantamin rai sama da ginin bayin, rashin sanya Babana a ido yafimin kwanciyar hankali da samun natsuwar ruhi dan ko Mama na fahimci tafi sakewa idan bai ziyarcemu ba.
Sanjamin k'ofa ya bani damar samun barci cikin natsuwa batare da fargaban komi ba, damuwata ya zamo tarihi indai akan gadin kaina ne yayin da d'aukakin bil'adam ke samun hutu wato cikin dare. Sannan na lura Mama ta sanya ido a game da shiga da fitar masu kawo mana ziyara musanman 'yan samarin unguwarmu masu shigowa siyan Zob'o da kunun Aya wanda ta ke yinsa duk ranakun Litini da Labara dan takance jiki da jini Uwata dole mu huta tunda Allah ya bamu rufin asiri dai-dai misali. Duk in ta ambaci haka na kanyi murmushi.
Hak'ik'a Mama jarumar uwa ce mai kula da kiyon da Allah ya bata akan 'ya'yansu, shi yasa alfaharina da ita ba mai musaltuwa ba ne, abinda na sani dai ina k'aunar farin cikinta matuk'ar k'auna.
Bayan sati biyu.
Sai murmushi na ke dokawa Mama na gefena tana dura kunun Aya a robobi. Ina lura da kallon da ta ke saukemin na son jin abinda ke sanyani murmushi amma dai bata tofa ba, sai lamarin ya k'ara sakani nishad'i na yi ta doka murmushina tare da motsa kai lokaci zuwa lokaci tamkar mai sauraren wak'a. Ba komi ne ya sanyani farin ciki nan ba sai ganin mun sami sati biyu cif Baba bai zo gidanmu ba wanda muka sami labarin wai ya yi tafiya zuwa maiduguri ta'aziyyar Malaminsa da ya rasu ta bakin babban yayanmu Auwalu.
'Allah yasa ya yi wata biyuma a can mu huta da sababinsa.'
Na ambata cikin raina ina mai cigaba da murza Fulawa wanda zanyi meetpie sabida bikin yayen Haddar alqur'anin aminiyata Fanta da za'a yi ranar Asabar.
"Uwata ko na samu suriki ne?"
Da sauri na kalli Mama ta motsa kai cikin murmushi tare da cewa "Ina burin jin wani yazo sallama da Uwata, ko nima na jiyo k'amshin samun jika na yi ta masu tawai."
Samun kaina na yi da rashin jin dad'i, sai na maida kaina k'asa hawaye na taruwamin domin abu kad'an ke sakani kuka.
"Uwata ka da ki damu komi lokaci ne, wata rana sai labari, wasa na ke yi miki amma ina son sanin abinda kike nazartawa da ya sakaki nishad'i."
Numfashi na sauke cikin rawar murya na soma maganar abinda ke cin raina kullum. "Mama na soma tsorata da lamarin, yanzufa shekaruna ashirin da hud'u zan shiga da biyar watan gobe amma ko da wasa wani namiji bai tab'a cewa yana sona ba hatta da k'awaye in aka cire Fanta ba wacce ke k'awance da ni, hakik'a zuwa yanzu na'amince maganar Baba gaskiya ne ni d'in mai bak'in jini ce na k'arshe."
"Kul! Uwata kada ki sake ambatar haka in baso kike kiyiwa Allah butulci ba, komi ya faru da bawa cikin k'addararsa ne, bawa bai isa ya tsarawa kansa rayuwa ba fa ce wanda da ya haliccesa wanda baya kuskure cikin mulkinsa, jalala da buwayarsa masu fad'i ne wanda sanin hak'ik'aninsu sai shi kad'ai dan haka bai manta da ke ba yana sane da ke in lokacin zuwar mijinki ya yi zaki had'u da abokin rayuwarki batare da zatonmu ba."
"Haka ne Mama amma fa ki duba ki gani Khamila k'anwan bayata ce sosai dan kince na bata shekaru bakwai amma gashi saura watanni bikinta ni kuwa ko wanda zaice ina son ki Kha...
Sai kuma na kasa k'arasawa sabida ni d'in mai yawan jin kunya ce.
"Ina Uwata ta ke?"
"Gani Mamana."
"Maza bani hankalinki."
"To."
"Ina son ki nemi zab'in Allah sai kiga Allah ya kawo miki miji d'aya tamkar da dubu ba yawan damuwa ba domin ba zai k'areki da komi ba sai shiga matsala sannan miji irin na Khamila wake burin d'iyarsa ta auri irinsa? Wanda kowa ya shaida baida halin kirki yawo da wuk'a yakeyi, me za'ayi da makashin mutane da tare hanya ya kwace musu hak'k'insu, insha Allah mijinki sai yazamo alfaharin dangi gabas da yamma kudi da arewa, wanna shi ne addu'ar da na ke yi miki duk in na kai goshina k'asa."
"Ba Amin ba!, har abada ita da samun mijin da kikeyi mata fata wannan a rubuce yake."
A razane muka kalli k'ofar shigowa, bakin Mama na rawa ta ce "Malam!"
"Na'am Hurera."
"Shin kai wani irin Uba ne?"
"Uba kuma?"
Mik'ewa Mama ta yi ta shige d'akinta da sauri batare da ta amsa masa ba, rufa mata baya ya yi yana gyara babban rigarsa cike da fitina.