Dan karuwa Complete na zahra muhammad surbajo - Chapter 5
Dan karuwa Complete na zahra muhammad surbajo Chapter 5: Dan karuwa Complete na zahra muhammad surbajo Chapter 5. Yana fitowa ya hangesu,da dan saurinsa ya…
2,377 words
Yana fitowa ya hangesu,da dan saurinsa ya isa garesu suka rungumeshi cike da murnar ganinsa.
Nana da sabrina ne kawai basu zo tarbarshi ba.
Hamra ko bace mata yayi yasa bata ganshi ba,ba haka tasoba amman tarasa abunyi haka tabi yan gidansu itama ta wuce gida.
Sultan ma haka suka dunguma zuwa gida kowa na cike dajin dadi.
Gidan uncle dinshi ya sauka.
Nan yay wanka ya sauya kaya sannan yayi zaman cin abinci,bayan ya gama
Suka taba hira da mutanen gidan kadan,sannan ya mike yacewa matar hydar wacce yake kiranta,mummy.
"Mummy zanje na duba umma,abanj key."
Da sauri tasa najwa ta dauko masa ta bashi.sannan suka fice shida su najwa din dan sui masa jagora.
Suna isa gidan yayi parking.masu gadi nata zubewa suna kwasar gaisuwa har ya shige cikin gidan.
Zaune nana take,kan kujera yayinda sabrina ke kwance akan kafarta sanye cikin kayan bacci riga mara hannu sa gajeren wando wanda ko cinyarta be gama rufewa ba.
Muje zuwa
Surbajo for life.🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 *DAN KARUWA* 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*writen by zahra surbajo*
*page 24*
Kallo sultan yabita dashi,na mamakin girmanta.
Kauda kai yayi ya nemi guri ya zauna,sannan ya duka yagaida umman tashi cike da girmamawa.
"Idonka kenan sultan,haba kai har se an fada maka baka kyauta ba,taya mutum ze zauna akasar da ba tashi ba sannan ba tare da iyaliba,kayiwa kanka fada fa sultan"
Murmushi yayi ya sosa keya,sannan yace.
"Umma zanyi ne kinsan komai lokacine ki tayani da addua"
Harara tabishi dashi alamun ya raina mata wayo shide be kara mgn ba.
Sabrina ko ido take binsu dashi bata da alamun sakkowa ta gaisheshi.
Wanda hakan sosai ya bata masa rai yaji yarinyar sam bata masa ba,ji yayi zuciyarshi na mishi zafi.
Mikewa yayi yayiwa umman sallama yafice daga gidan yanufi gidan sarki.
Bangarenshi ya wuce,yana shiga daki ya haye kan gadonshi se huci yake shi kadai.
Sosai yaji tsanar sabrina acikin ranshi.dan shi mutum ne me shegen son girma.
Bacci ne yayi awon gaba dashi be farkaba se gab da magrib,da sauri ya fada toilet yayi wanka ya daura alwala ya fito ya kintsa cikin kayanshi da suka dace da kirar jikinshi.
Masallaci yaje yasamu jam'i sannan suka wuce falon hydar tare dashi.
Hirar yaushe gamo suka shigayi,kamin hydar yafara mgn cikin kulawa.
"My boy,kullum kara girma kake,shekarunka karuwa suke ba raguwa ba,yakamata babba kamarka ka ajiye iyali,hankalinmu be kwanciya, zamanka a can batare da iyali ba"
Murmushi sultan yayi yakara rusunawa sannan yace.
"Insha Allahu daddy zan nemo matar auren,inyaso kan na tafi se a daura auren mutafi tare."
Sosai batun nashi ya faranta ran hydar yashiga sa mishi albarka.
***********
Wasa wasa yanzu sultan kimani watanni uku kenan da dawowarshi,kuma tun da ya dawo sannu bata taba shiga tsakaninshi da sabrina ba,
A wannan lokacin sun shaku sosai da hamra wacce ta rikide ta zama budurwarshi,
Sosai yake sonta dan yanason mace me wayewa.kuma hamra na dashi dede gwargwado.
Soyayya suke me tsabta,inda takai kowa na gidan su hamra yasan da sultan haka shima gidansu ansan da ita.
Abokanshi da suke nace masa jin ya dawo yasa suka bibiyeshi.
Safwan kawai yakeba fuska dan yasan halinshi kuma ya iya zama dashi.
Sultan ganin sun fuskanci juna da hamra ne yasa ya shaida mata ta fadi agudansy ze turo iyayenshi.
Bayan hamra ta sanar agidansu se aka bashi dama.
Ba bata lokaci ya tura iyayen nashi,
Bayan sun nemamasa aurenta,iyayenta suka shaidamusu cewa zasuyi bincike akanshi kamin atsaida ranar auren.
Kudin gaisuwa suka bada sannan suka tafi da zummar in an gama binciken zaa kirasu.
Hamra diyace ga mininstan tsaro,Alh habu dogon karfe,so gidansu babban gidane itama.
Mahaifin hamra baza mutane yayi su binciko masa waye sultan.
Cinkin sati biyu shaidun komai suka bayyana,inda daga karshe de suka bashi final result da cewa.
"Ranka ya dade DAN KARUWANE FA, bashi da wata tarbiyya duba da wacece mahaifiyarshi,kasani ma ko can gurin yawonta ta samoshi,batun gaskiya bedace da hamra ba".
Ran mahaifin hamra in yayi dubu ya baci kasancewarshi me saurin fushi.
Kwalawa hamra kira yayi ya zayyane mata komai gameda sultan.
Sosai taji ta tsaneshi,kuka ta fashe dashi na bata lokacin kulashi da tayi.
Janta mahaifinta yayi se gidan su sultan .
Ranar jummaa ne duka suna harabar gidan azaune.
Fahad ya dauko nana sun kawowa hydar ziyara gidanshi,
Su sabrina kuma suna gefe ita da su najwa suma suna tasu hirar,hydar kuma yana tare da iyayenshi ana tsara yadda bikinshi ze kasance.
Turo kofar da akayi da karfine yasa duka suka maida hankalinsu gurin.
Hamrace tafe ita da mahaifinta cikin fushi.
Da sauri sultan ya mike ya isa gurinsu,yana tambayarsu lafiya de ko.
Muryar mahaifin hamrane ya katseshi.
"Dalla can munafuki kaida iyayen naka Allah ya tona muku asiri. Kunzo zakumin angulu dakan zabo,ashe kai din Dan karuwane!!!!! Dan karuwa ko taya ze kasance me tarbiyya"
Runtse ido sultan yayi,da karfi jikinshi na rawa.
Nana zamewa tayi ta zauna jagwab,wasu zafafan hawaye nabin idonta.
Fahad ko mutuwar tsaye yayi ya kasa magana.
Hamrace ta amshi maganar da cewa.
"So kake in aureka nima asamu karuwar acikin yayana to aniyarka ta bika Allah ya tona ma asiri wlh nafi karfin zama sirikar Karuwa,mata ga DAN KARUWA!!!!never wlh"
Tasss taji an dauketa da mari mw shiga jiki wanda seda taga wuta sabida hasken marin.
Da sauri takai dubanta kan wanda ta maretan.
SABRINA ce rike da kugu tana huci.
Cikin fushi hamra tace.
"Ke yar gidan uban waye da zaki mareni?"
Dauketa tayi da wani marin sannan tace.
"Gimbiya Sabrina ce agabanki ba sako ba,ke har kin isa keda wannan me dattin hular ku shigo mana gida kuci mana mutunci,wlh kunyi kadan,daga ke har uban naki duk shegen daya fasa Allah ya tsinewa uwarshi albarka,"
Daga hannu baban hamra yayi ze tsinke sabrina da mari,da sauri ta rike hannu,tace cikin fushi.
"Hattade dattijo,nasan darajar furfura shiyasa ban kwasheka da mari ba atun farkon shigowarka,amman wlh ka kuskura ka tabani senasa karnukan gidannnan sun farauceka,marasa mutunci kawai ku fice mana agida."
Hamra gaba daya tsorom sabrina ne yakamata yasa batayi yunkurin ramawa ba.
Kowa binta yake da ido cike da mamakin masifar tata wacce ba wanda yasan ta iya.
Baban hamra ganin take taken sabrina gab take da kifeshi da marine yasa ya wurga musu kudin gaisuwarsu yaja hannun yarsa suka fice cike da alwashin se ya dauki mataki.
Muje zuwa
.surbajo for life.🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 *DAN KARUWA* 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*writen by zahra surbajo*
*page 25*
Kowa bin sabrina da ido yake,an rasa me magana acikinsu.
Da gudu ta juya zuwa gurin Nana ta fada jikinta tana kuka tana fadin.
"Umma kice karya sukeyi,su dena ce miki karuwa ke ba ita bace su dena umma in suna fadi wlh zan iya mutuwa"tasake rushewa da kuka.
Rungumeta Nana tayi cikin matsanancin kuka itama.
Fahad ne ya mike ya usa gurinsu a hankali ya zare sabrina daga jikin nana ya ka ma nanar suka wuce gurin motarsu,kai tsaye ya zauna mazaunin direba,yajasu suka bar gidan zuwa nasu.
Hydar kasa cewa komai yayi ya wuce cikin dakinshi.
Matarshi tabishi abaya domin kwantar masa da hankali.
Sabrina kuka take iya karfinta,dan sosai ranta ya baci.
Jiki a sanyaye sultan ya isa gurinta yace cikin taushin murya.
"Kiyi shuru kaddarace kuma tana kan kowa,"
Afusace ta dago tana dubansa tace.
"Kaddara a ina,kode mugun son zuciyarka,taya zaka kwaso karuwa amatsayin matar aurenka,in kana dadironka kayi iya waje mana,taya zaka sa azo har gida azagar mana iyaye.to wlh ni ba ruwana duk wata yar kutumar uban karuwa data.... "
Tasss taji an dauketa da mari.
Agigice take kallonshi ranshi abace yace yana nunata da yatsa.
"Zaki iya zagin komai na kyaleki amman bazan taba bari ki zagi karuwa ba,karuwa nada matukar amfani arayuwata,ki iya bakinki"
A wulakance tabishi da kallo sannan tace
"Can ta matse maka in kai kana da alaka da karuwai mu bamu dashi kuma inde zagin karuwane agidannan yanzu na fara.kuma komai akaiwa shamuwa watan bakwai ne yaja mata"
Tana kaiwa nan ta juya cikin gida da gudu tana kuka.
**************
Nana ko amota in banda kuka ba abinda takeyi,kuka take kamar ranta ze fita,fahad nata rarrashinta har suka isa gida.
Ranar basuyi baccin kirkiba sabida bakin cikin da suke ciki da shi suka kwana.
*********
Mahaifin hamra ko suna fita hukumar yan sanda yay waya yabada umarnin azo akama mishi sabrina.
Yan sanda jin gidan sarki zasu kamota,yasa suka san dole se anbasu warranty na kamo tan daga sama wato ig.
Koda ya tuntubi saman se yasamu safwan abokin hydar shine ig din hakade safwan yay ta bashi hakuri ya hakura.
Maganar ta wuce.
***********
Wasa wasa seda acikin shekara guda sultan ya nemi auren mata uku yana kin yiwuwa sakamakon kalmar dan karuwa dake batawa.
Abun yaki ci yaki cinyewa wanda sanadin hakan yasanya sultan kamuwa da ciwon hawan jini.
Ga wata matsananciyar shaawa dake damunshi yarasa yadda zeyi da rayuwarshi.
Daga karshe de hakura yayi da neman auren ya fara tunanin komawa gurin aykinshi.
Sabrina ma na shiga tashin hankali mara misaltuwa sakamakon halin da familyn su suka tsinci kansu,ranta na matukar kuna gameda lamarin.
Kullum burinta ta nemo.mafita ga batun adena musu gorin.
Hankalin sabrina me taba tashi irin nayau ba bayan da wasu makwabtansu duka shigo har gida suka cimusu mutunci kan yar gidan tace ita sultan takeso wanda shi ko sanin da zamanta ma beyi ba.
Iyayensu basa son daukar mataki ne,gudun kar magar ta gama bazuwa agari yasa suke barin duk wanda yaci musu mutunci badan yafi karfinsu ba.
Sabrina kulle kanta tayi adaki tana kuka gamida tunanin mafita.
Zuwacan kamar wacce aka zabura ta mike da sauri tayi falon mahaifinta inda suke zaune shida fahad suna jimamin matsalar.
Muje zuwa
Surbajo for life
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 *DAN KARUWA* 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Writen by zahra surbajo*
*don Allah ina barar adduaarku kan Allah ya yayemin abinda ke damuna.👏*
*26*
Ganinta kawai sukayi ta fado falon ba ko sallama.
Bin ta da ido sukayi cike da mamaki dan sun san ba halinta bane yin hakan.
Durkusawa tayi gaban hydar tana kuka tace.
"Abba tunda duk auren da ya prince ze nemo se an samu matsala har takai da ana zuwa har gida ana cimana mutunci ana tozarta mu ni na amince adauramin aure dashi.wlh duk tsanani zan zauna dashi"ta karasa maganar cikin kuka me tsuma zuciya.
Ba hydar ba hatta fahad jin maganar yayi kamar amafarki.
Sosai batun nata ya faranta ransu,dan ko kadan su basuyi wannan tunaninba.
Dago fuskarta hydar yayi yasa hannu ya goge mata hawayen dake idonta yace.
"My little princess kin tabbatar zaki iya zama dashi?"
"Na tabbatar Abba"ta bashi amsa.
"To tashi kije Allah yay miki Albarka"
Mikewa tayi ta fice afalon zuciyarta fess ji take kamar ta sauke wani kaya.
Fahad ko da hydar sunma rasa ta ina zasu fara dan gaba daya sabrina tasa su cikin shaukin farinciki mara misaltuwa.
Seda suka natsu sannan suka fara shawara gameda maganar.
"Yaya ni aganina mu nemi sultan muji ta bakinshi kar yaga kamar anmasa shigar sauri"cewar hydar.
"Ba wani jin ta bakinshi da zamuyi shi ya haifemu ko mu muka haifeshi,dolene yayi biyayya ga duk abinda muka zartar masa tunda de yarinya tayi tunanin ciremu acikin damuwa"cewar fahad.
"To shikenan yaya hakan zaayi yanzu semu tsaida lokacin bikin"
"Ranar jummaa me zuwannnan zaa daura auren,dan ranar monday daze wuce su tafi tare,sauran shagalin mata su fara shiryawa"cewar fahad hankali kwance.
**********
Duka family sun samu labarin auren Sabrina da Sultan.kowa yayi naam da auren.
Sabanin shi uban gayyar da sam abun be masa ba,shi aganinshi kawai gani ake yaki auruwa ne yasa akai musu hadin gida da yar kucakar yarinyar daya tsana.
Shiyasa duk wani shaani na bikin shi ba ruwanshi,abokinsa ake tuntuba .
Yau alhamis yau ne aka ajiye domin dinner.
Duk yadda sultan yaso daya rushe maganar zuwa dinner taki rusuwa.
Domin angayyato manyan mutane wanda shi be isa ya rusa ba.
Dole yayi wanka ya shiya awata gezner white colour tasha ayki da golding zare.
Takalmin kafarshi golding agogo da hula ma duk golding.
Sosai yayi kyau acikin kayan turare ya fesa ya nemi gefen gadonshi ya zauna,yana bin kayan da amarya zata sa da ido,wanda aka ajiye akan gadonshi,shi ya rasa dalilin kawosu bangarensa inde ba so ake abata ransa ba meyasa bazaa kai mata dakinta ba.
Yana tsaka da wannan tunani ne yajiyo sallamarta a falonshi.
Ji yayi kamar ya shaketa in yafita falon dan bakin ciki amman ya ya iya dole ya daure.
Amsa sallamar yayi ciki ciki,sannan yabata damar shigowa cikin dakin.
Turo kofar tayi ta shigo, bakinta dauke da sallama.
Kyan da tayi ya firgita sultan,dan angama mata kwalliya kenan aka turota tasa kayanta wanda aka kawosu tare da nashi.
Dubanshi tayi taga ya kauda kai daga kallonta,sema wani cika da batsewa da yakeyi.
Murmushin karfin hali tayi sannan ta taka cike da kirsa ta isa gabanshi.
Tsugunawa tayi agabanshi ta shagwaggwabe fuska ta dora hannayenta duka akan cinyarsa tace cikin shagwaba.
"Ya prince kaga mummy ko,kunshin da nace ayimin ta hana tasa ayimin wannan jagwalgwalon,yanzu dom Allah wannan yayi kyau kenan"
Yanayin da ta ajiye hannun nata akan cinyar tashi seda tsigar jikinshi ta tashi.
A hankali yabi zanen kunshin da kallo wanda yay matukar daukar hankalinshi.dakyar ya furta.
"Yayi kyau mana,ay tamiki zabi me kyau"
Wani murmushi ta sakar masa hadi da wasa da idanunta sannan ta mike tsaye tace.
"Nagode ya prince,ance kayana na gurinka suna ina in saka kar muyi latti dan kowa sun wuce mune kawai muka rage"
Da hannu ya nuna mata inda kayan suke dan koya ta motsa baki tana magana jikinshi mutuwa yakeyi.
Muje zuwa
Surbajo for life.
VISIT www.aihausanovels.com.ng For More Novel.
AIHAUSANOVELS is website consists of hausa novels note, the reason of launching this site is to Entetaint, Motivate and Educate our readers.
We provided hausa novels of many type, Such Adventure, love, romance, fiction, non-fiction, mystry, fantasy, action e.t.c from hausa Authors
We provided a new and old novels both softcopy and hardcopy from our Author with thier permission.
AIHAUSANOVELS shafin yanar gizo ne wanda yake ɗauke da littattafan hausa, dalilin bude wannan shafin shine domin Kayatar masu karatu da kuma ilimantar da su.
Mun samar da littattafan hausa na nau'uka daban-daban, kama daga littafin, soyayya, tatsuniya, almara, Hikayoyi, gyara kayanki (yadda mata zasu kula da kansu a gidan mijinsu) da dai sauransu, daga Marubutan hausa.