Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul - Chapter 31
Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 31: Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 31. Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku…
4,347 words
Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (09)
.........Yanda ya umarcetan haka tayi akan Iffah, dan dole ta kasance a tare da ita har zuwa lokacin da ya bukaci ta kai tare da itan. Komai dake faruwa kuma akan idanunsa ne, sai bayan wucewar Daneen Ammarah da kusan mintuna talatin ya ɗauka Alkur'aninsa ya fito cike da takun nan nasa na izza da ƙasaita ya nufi ɗakin. Zama yay a kujerar da ke gaban gadon shanyayyun idanunsa a kanta, ya mata kallo na wasu mintuna tamkar mai nazari kafin ya fesar da ɗan huci ya ɗauke kansa. Alkur'anin ya buɗe yana mai ƙara tabbatar da nutsuwarsa gaba ɗaya garesa sannan ya fara raira karatu cikin daddaɗar muryarsa da bama kowane harafi hakkinsa cikin ƙwararren larabci yanda ya kamata. Ya ɗauki tsahon lokaci yana karatun, kafin ya tsagaita ya rufe ya ajiye. Kujerar da yake zaunen ya sake matsarwa gab-gab da gadon, tamkar wanda baya so ya kai hanunsa kan bargon ya ɗan yaye kaɗan. Kauda idanunsa yay da ga kallon inda suka sauka ya maida a fuskarta, ɗan bakin tsiwar nan duk ya bushe. Ya ɗan ja wasu sakanni a kallon nata, sai kuma ya kaudar yana sake tsuke fuska ya fara karanto addu'oi yana tofa mata. Haka ya kasance tare da ita har gabannin asubahi, dan sai da katafaren agogon masarautar ya buga cikar ƙarfe uku dai-dai sannan ya bar ɗakin ya koma nasa. Dole ya kai kwance dan shima ba jikin nasa ya gama komawa normal bane, a yanzu hakan ma jiri-jirin da ya fara ji yana rinjayarsa ne ya sakashi haƙura ya dawo nan ɗin.......
★★... WASHE GARI ★★....
Ƙoƙarin rufe system ɗin gabansa yake dai-dai da shigowarta da sallama doctor Afif na take mata baya kasancewar hadimanta basu da hurin biyota har nan. A kallo ɗaya zaka fahimci ɓacin ran da ke shimfiɗe kan ƙyaƙyƙyawar fuskarta. Doctor Afif ya gyara mata kujerar da ke gaban gadon jiyyar Tajwar Eshaan ɗin, sai da ta zauna ya juya ya fice tare da zuge musu ƙofar gilashin duk da wajene da bana shiga kowa da kowa ba. A hankali ya ɗan risinar da idanunsa alamar girmamawarsa gareta, sai kuma ya motsa lips ɗinsa a tausashe ya furta “Amincin ALLAH ya tabbata a gareki ya Ammie-na”. Duk da ɓacin ran da ke zagaye da zuciyarta hakan bai hanata ɗan sakin murmushi ba, ta kai hannunta kan nasa ta riƙo, itama cikin sauƙaƙa harshe da nuna kulawa ta amsa. “Tare da kai Bin Haysam Abdul-majeed. Ya ƙarfin jikinka?”. Suna mafi soyuwa da yakan so ji da ga bakin mahaifiyarsa, sai dai kuma a duk sanda ya jisa da ƙarfin izzar harshenta ya kan saurin gane ɓacin ranta a bayyane. Ganin damuwarta kam shine abu mafi ƙona zuciyarsa dan shi karan kansa bai san irin tarin ƙaunar da yake ma mahaifiyar tasa ba. Kaɗan ya gyara kishingiɗar da yay har lokacin idanunsa na kanta, ya juya yatsunsa da ke riƙe da nata ya maida nasa a ciki, a sannu yake tausa mata gaɓɓansu da kulawa da lallashi batare da ya sake cewa komai ba. Tsahon mintuna suna a haka har ta fara sauke ajiyar zuciya alamar saukar fushin nata. Ganin ta koma kamar yanda yafi buƙatar ganinta ya ɗan sake mata murmushi. “Nafi buƙatar ganin murmushin akan ƙyaƙyƙyawar fuskar Ammie-na a kowace daƙiƙa ta numfashi na. Akasinsa kan ƙona zuciyata fiye da yanda wuta ke narkar da kitse.” Kalamansa koda a taƙaice suke zinarai ne a zuciyarta, shi ɗin yafi hasken diamond walwali da ƙyalli a cikin idanunta a duk sanda take dubansa, ta so abubuwa da yawa kafinsa ciki harda mahaifinsa sai dai shi tamkar shafine dake shafe dukanin fejin sauran fejikan baya a littafin rayuwarta. Kafin ka buɗe a bangonta shine, a shafin farko da shi take shimfiɗa, tsakkiya da ƙarshe shine mafi girma a ababen yabonta da ƙaunarta. Ta sake sakin murmushi zuciyarta na sake risina da ga fushin da ta baro sashenta a ciki. Malikat Bushirat wata irin mace ce da gane halinta sai wanda ya santa, tana da abubuwan ban mamaki ta na da kuma na ban tsoro harma dana ban sha'awa da suka kasance mafi rinjaye a yimata ado. Hamshaƙiyace ta gasken gaske dan ko'a cikin manyan matan dole a kirata *_ZAKANYA UWAR ZAKIN ƘASAR RUMAN_*. A yanzun ma halin dattakon nata ta nuna, ta hanyar shanye dukan tarin abubuwan bakin nata ta cigaba da bama ɗanta magajin mijinta mai amsa suna shugaban sarakunan ƙasarta kulawa har zuwa lokacin data gamsu zata iya magana da shi babu fushi a harshenta. Ta tsatstsaresa da idanunta masu kaifi irin na uwa, yayinda shi nashi ke a rissine gareta risina irin ta ɗa a gaban mahaifiya. “Na kasa gane komai da ga Mammah dangane da al'amarin yarinyar, a sanina ita ke fara hukunta duk wanda ya zaɓi cutar da kai koda da mummunar magana ne, kuma koda ni da na haifeka ce. Amma a wannan lokaci sai ta zaɓi bama mai son kawar da numfashinka kariya batare da fahimtar da ni kaina hujjarta akan hakan ba. Shin taya ake tunanin zan iya haɗa numfashi a ƙarƙashin runfa ɗaya da wadda ta shirya kawarmin da abinda bani da madadinsa ko samin madadinsan ba har abada? Taya ake tunanin zan iya kawaicin barinta da cigaba da kallonta a matsayin Zawgatu al-ibn duk da yunƙurinta na son ganinta ta tarwatsani da tai? Idan har igiyar aurenka da ke kanta ne katangar da ake iya min nuni da ita bango gareta ina son ka rusheta, ka yanketa, yankewa ta har abada ibn Haysam Abdul-majeed. Dan hakan shine kawai zai iya bani nutsuwa na manta da komai”. Da ɗan ƙarfi ya matse idanunsa yana mai sakin numfashi a harɗe, sai dai mai kallo da ido bai isa fassara kamilar fuskarsa ma'abociyar annuri da kwarjini ba hatta ita dake amsa sunan mahaifiya a garesa..... “Yanke hukunci cikin fushi da rashin haƙuri akan bincike ba itace ɗabi'ar shugaba nagartacce ba”. Daneen Ammarah ce dake tsaye mai maganar tana ƙoƙarin shigowa ɗakin, da alama ta ji dukkan kalaman Malikat Bushirat ɗin. Bai motsa ba, hakama bai buɗe idanun nasa ba harta ƙarasa shigowa garesu, sai dai ya sauke wata irin ɓoyayyar bahaguwar ajiyar zuciya acan cikin maƙoshinsa. Jin shiru ya ratsa ɗakin ya sashi buɗe idanun sannu-sannu. Dukansu cikin ɓacin rai suke kallon juna kowa najin ya isa yana kuma da ƙarfin iko akan yaƙin. Abune da babu wanda zai ce ya taɓa gani a tsakaninsu sai a wannan lokaci, ciki kuwa harda shi kansa. Daneen Ammarah ta sake katse yanayin nasu ta hanyar ɗora hannunta a kafaɗar malikat Bushirat da alamu suka nuna ta gama kaiwa maƙura a fusata.. “Úht!”. (sunan data kan kirata da shi wani lokacin) “Ban sanki da garaje ba, ban sanki da kasa fahimta ba, ban sanki da munana zato ba. Ban sanki da dagiya ba. Ina roƙonki ki danne, ki jure, ki zama mai ƙarfafa gwiwar mai ƙarfin da ba ƙarfin akafi son ya gwada ba kai tsaye, saboda amsa sunansa na shugaba. Bazan musa miki sunan Fareedah matsayin mai laifi ba, amma zan so ki kasance a yanda na sanki wajen tabbatar da gaskiya akan kowane ne kafin zartar da hukunci. Muma ba burinmu hana a hukunta ta ba, ko fifitata sama da gudan jininmu kuma shugabanmu ba, so muke kawai abi tsarin da ya dace da dokar shari'a da muke fata bayan ita za'a iya tono waɗan da ma suke aikata ɓarnar baya mai barinma gudan jininmu baƙin fenti da tabo a rayuwarsa da rayuwar mulkinsa. Ki fahimci Mammah ba fifita Fareedah take sama da abinda ta cancanci fuskanta bane, kariya take bata matsayinta na tamkar makamin da zai iya zama zaren da zai jamu ga duk ɓoyayyun masu laifin da muke fatan kamawa a cikin hannayenmu. Shin baki ji a ranki wanda suke aikata ta'asar baya nada nasaba da na yanzu ba? Baki ji a ranki yanke mata hukunci a kallonta ita kaɗai mai laifin tamkar basu ƙwarin gwiwar cigaba da aikatawar bane koda kuwa a yanzu basu da hannu kan abinda yarinyar ta aikata? Shin baki tunawa shi shugaba ne ba mai azaba ba?. Da yawan mutane gani suke sakacinsa da ƙin bama abu muhimmanci koda mai muhimmancin ne halayyarsa, sai dai yanda yake yi shine cikar zama cikakken duk wani shugaba. Shugaba da shanyewa aka sansa koda ɗacin na ƙona makoshinsa, da haɗiyewa aka sansa koda raɗaɗin na azabtar da hanjinsa, da ɓoyewa aka sansa koda girman al'amarin yafi girman zuciyarsa, da nazarta aka sansa koda ƙarfin yafi ƙarfin ɗaukar ƙwaƙwalwarsa. Ba ko yaushe yake ihu ba, ba ko yaushe ake gane ainahinsa ba, ba ko yaushe ake iya karantar zuciyarsa ba koda a ƙwayoyin idanunsa ne.....” ta ɗan ja numfashi ta fesar a hankali da cigaba da faɗin, “Idan har mu a karan kammu zamu kasa fahimtar kammu taya wanɗanda ke zagaye da mu zasu fahimcemu?. Idan har uwa zata iya shanye wa da daurewa akan halayyar ƴaƴanta da duk girman adadinsu bazasu haura ashirin ba mai zaisa shugaba mai mulkin ƙasa baki ɗaya kamar ruman za'a so ganin zahirinsa a dole dan kawai farin cikin wani ɓangare ko munanama wani ɓangare? Tayi laifi an yanke mata hukunci, daga baya gaskiya ta bayyana bata da laifi ko tursasata akayi ko wani dalili da zai iya wanketa koda ace ba shine yay hukuncin ba, to shi ne za'a kalla da tabon gazawa? Wa za'a munana? Wa za'a aibanta? Wa za'a munanama kima da mutunci? Amasar itace shugaban nan dai Umm-Jasrah. Dan ALLAH na roƙeki ki kwantar da hankalinki kar wasu su dinga amfani da fusata fushinki domin cikar nasu burin, ki cigaba da zama a yanda na sanki inba hakaba wasu zasuyi amfani da hannayenki wajen shafama kanki da kanki fentin da babu wani ruwan da zai wankeki ya wanke wanda ake son amfani da soyayyarsa a zuciyarki. Bayan ke uwa ce, kema ɗin shugaba ce.....” Har cikin rai da ɓargo zantukan Daneen Ammarah sun matuƙar ratsata, sai dai basu ruguje kaso ashirin cikin ɗari ɗin matsayin da take kallon Iffah da shi ba har a yanzun, amma taji ta kuma amince zama mai haƙurin bin matakin da ya dace ɗin wajen hukuntata, hakanne kawai zai bata salama kasancewar ta wadda bata ɗaukar ƙiyayya da sauƙi ga duk wanda ya nuna mata, hakama soyayya. (Hakan kuskure ne Malikat Bushirat, karka zafafa ƙiyayya, kar kuma ka zafafa soyayya dan wataran duk zasu iya canja kansu a gurbin juna), sai kuma ƙudirinta na biyu babu gudu babu ja da baya zata tabbatar da shi koda babu yardar kowa a daular ruman har shi kansa Tajwar Eshaan ɗin........✍️
(Nace, “Humm”)
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 96 09 67 63
Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (10)
........Daneen Ammarah da dama sanin fushin malikat Bushirat ɗin kan al'amarin ya sata tada hankalinta ganin an kusanto da Iffah ga Tajwar Eshaan tai ɗan murmushi, tasan kalamanta sunyi tasiri, sai dai ba tasirin da zai iya ruguje abinda take son ganin ta ruguje ɗin ba (Wato ƙiyayyar Iffah a zuciyar Malikat Bushirat a yanzun). Kanta ta ɗan rausayar tare da kallon Tajwar Eshaan da yay kamar babu shi a ɗakin, dan idanunsa ma a lumshe suke kamar wanda barci ya ɗaukesa. Juyawa tai ta fice a binta itama zuciyarta cike da ƙudirin tsayuwar daka domin tabbatar da gaskiya da kuɓutar da yarinyar da takejinta har cikin ƙasan zuciyarta. Idanun ya buɗe kaɗan ya bita da kallo tamkar yanda itama Malikat Bushirat ɗin data gagara iya cewa komai ta bita da kallon..
*_“Hummm!! Bazan iya hakuri ba sai na tofa”_* “Idan nace Humm fa ina nufin Humm da gasken gaske. Idan har Iffah ta rayu yaya kuke tunanin a yanzu salon zamanta zai kasance da uwar mijin nata mai tsananin ƙarfin iko? haka koda an tabbatar da jagororin abinda ya faru ta dalilin nata. Masu karatu akwaifa cakwakiya, dan yanzu salon zai fara a ƙarƙashin abu uku ne, da zaku iya canko min su dana baku babbar ƙyauta😉😁🥱”.
★.... TA-ƘURYA ★.....
“Na daɗe da faɗa miki wannan yarinyar hatsabibiya ce kar ki sakaci da rauninta na kasancewa mai ƙarancin shekaru ko ƙanƙanta sama da ƙarfin ikon ki ta-ƙurya?. A duniyar cikar buri raina abokin karo kuskure ne kuma ganganci ne da kan iya rusa duk wani ginin da aka faro komai tsahon shekarunsa.....” Ta-ƙurya da ke gurfane gaban Uwa cikin jin raɗaɗi a zuciya ta ɗago idanunta da launinsu ya koma jazur, cikin rufewar idon irin na mai ɓacin rai da manta wake a gabansa ta ce, “Mina gaza Uwa?! Minene ban bi ba a dukkanin sharuɗan ki a shekarun nan? Miyasa matsala bata kasance abokiyar gogayya ta ba sai a lokacin da zan girbi shukar dana ɓata tsahon shekaru wajen yimata barruwa? Miyasa? Miyasa?. Na ce miyasa hakan ne?!. Miyasa sai da na yarda na rasa komai domin samun abinda nake kallo komai a gareni sannan zaki hana mini? Ke ce kika ce karna taɓa kokwanto bazaki taɓa barin zubar waɗan nan hawayen da a yanzu suke kwaranya akan fuskanta ba da ga gareni. (Wa'iyazubillah 😭🙏). Miyasa? Miyasa a yanzu sabanin hakan nake gani? Yarinya ƙarama da bata wuce na murjeta da tsinin takalmina ba ta shigo rayuwata da barazanar yin kutse akan nasarata. Idan tafi ƙarfinki ne ki faɗa min danni batafi ƙarfi na ba, babu wata uwa data haifi ƴa ko ɗan dazai zama barazana akan cikar burina, in ko uwar ta haifosa har kuma ya kwatanta zan shafe babin zuri'arsa kaf da babu wani abinda za'a kalla a tuna su kuma. A yanzu kam zanyi yaƙin da hannayena dan bana buƙatar k......” “K!! Ta-ƙurya ki dawo cikin hankalinki, kalleni da ƙyau ki san a gaban wa kike? Uwar mugu nake bata sakarai ba. Banyi lalacewar da ke zaki ci tuwo a kaina ba koda kuwa tuwun na ƙasa ne mai sauƙin wawaso. Idan kuma zaki gwada ga fili ga mai doki”.. Cikin nuna halin ko gezau ta-ƙurya taja tsaki mai tsananin sauti dai-dai lokacin da Uwa ke ɓacewa daga idanunta rai a ɓace. Ta rakata da harara tana mai miƙewa da ga durƙuson da tai. Waya ta fusga cikin tsananin fusata ta hau danne-danne tana kai kawo a katafaren ɗakin...
🙆Tofa al'amarin babba ne tsakanin ta-ƙurya da uwa ta ta😱. Mu dai ƴan kallo ne😜.
★★..... ★.....
Alhamdullah a daren yau likitoci suka sami nasarar dawowar Iffah dake cika kwanaki huɗu hayyacinta, zuwa safiya kam sai dai ace Alhamdullah duk da bawai tana a cikin ƙarfin jikinta bane ko warkewa sarai kamar yanda take a baya. Daneen Ammarah har da kukanta na farin ciki, bata ɓata lokaci ba wajen sanar ma Malikat Haseenat. (Alhamdullah) ta dinga jerawa itama tare da jin nutsuwa na saukar mata, dan tunda yarinyar nan ta tsinta kanta a halin nan hankalinta ya gagara kwanciya. Malikat Bushirat duk da labarin farkawar Iffah ya zo har kunenta ta hanyar doctor Afif batace komai ba hakama bata leƙa dubata ba, sai ma yazam a safiyar ranar har zuwa yamma bata leƙa sashen Tajwar Eshaan ɗin ba gaba ɗaya, ta dai kira waya domin jin cigaban lafiyar jikinsa. Shi ɗin ma dai bai shiga duba Iffahn ba sai yamma duk da kuwa jiyan ma a gaban idonsa ta farfaɗo, Sannan har yanzu jikinsa babu ƙarfi shima, dan da gaske gubar da suka haɗa da dafin macizan ta so masa illa ƙwarai da gaske tunda gashi ma har sai da akai masa aiki dalilin taɓa wani sashe na jikinsa data so tayi saboda ƙarfinta.
Duk da ɗakunan jiyyar tasu na maƙwaftaka da juna a yau bamai iya ganin wani sakamako labulolin da aka zuge suka toshe gilashin da ya raba sun, koda babu labulen gilashin mai ƙarfine da babu mai jin maganar wani koda za'ayi da ƙarfi ne, sai dai zaka iya hango mutum fes. Har zuwa yanzu dai kayan jiyya ne a jikinsa sai dai a kullum yakan canja da wasu sabbi sau fiye da biyu, ya ɗan rame saboda yanda ciwon ya bugesa. Sai hakan ya sake fiddo hasken fatarsa mai launin tar-tar a cikin idanun mai kallo. Cikin jarumtarsa da ƙarfin hali yake tafe doctor Afif biye da shi a baya tare da Sayeed Fayzul-haq dake tsaye da ga bakin ƙofa dan zuwansa kenan. Cikin sauri Sayeed ya danna maɓallin ƙofar gilashin ta zuge kanta a hankali. Baya ya ɗan ja yana mai rissinar da kansa ga shugaban nasa mai matsayin gaske a garesa da bazaya iya musaltuwa ba. Izzarsa da ƙasaita na tattare da shi, dan tamkar itace jinin dake zagayawa a maimakon jininsa, ya ɗan ja iska ya fesar na wasu sakkani kafin ya cigaba da takawa a sannu ya shiga bakinsa ɗauke da sallama can ƙasan maƙoshi. .. Daneen Ammarah da ke zaune a gefenta tana ƙoƙarin bata shayi mai zafin gaske da Doctor ya bada umarnin bata ce ta ɗan waigo najin motsi, numfashi ta ɗan ja ƙaɗan tana mai sauke idanunta a kansa. Sai kuma ta miƙe dai-dai Iffah tana damƙe kofin shayin cikin hannunta duk da zafinsa da takeji sakamakon jin Daneen Ammarah ta ambaci “Abni”. Sosai zuciyarta ke harbawa da ƙarfin gaske, kusan tare da ɗaga sawunsa da saukewa cike da izzar da raunin ciwo bai rageta a gareshi ba sam. A tsumen da fuskarsa take ya tabbatar ma Daneen Ammarah a Shahan-shan ɗin sa ya shigo ba ɗanta ba, dan haka ta ɗan ja gefe a yanayin girmama darajar da ALLAH ya basa. Cikin sauri Sayeed Fayzul-haq ya gyara masa kujera yana mai ja baya kusa da Doctor ya rissinar da kansa. Duk abin nan dake faruwa yana tsaye kaifafan idanunsa masu matuƙar tasiri da tabbatar da girman da ALLAH ya bashi na mulki badan yafi saura ba na a kanta, kallo yake mata irin na ƙasan ido mai hana wanda akema sukuni koda bai san wanda ke masa ba. Sai da ya gaji dan kansa sannan ya kai zaune sannu a hankali ga kujerar da aka gyara masan... Iffah ta kasa sake iya motsi duk da azabar zafin shayin da raɗaɗin da ke ratsa mata hannu, sauƙinta ma ta ɗora shi ne bisa lallausan duvet ɗin da ƙafafunta ke ciki har zuwa cinyarta. So take kawai taji ta ɓata, ɓata irin wanda ta daɗe tana jin labarin masu layar zana nayi, ta kasa tantance ainahin abinda ke razanar da kasancewar sa gareta, shin tsoro ne ko matsananciyar kunyar kai ne?. Inama inama, inama daga halin data tsinci kanta bata sake farkawa ba balle su haɗu, inama an cigaba da barinta ta dawwama a kurkukun da bazata sake ganinsa ya ganta ba har abada. Tabbas har yanzu tana jin zafi, zafi mai haɗe da raɗaɗin rasa ƴan uwanta guda biyu, sai dai saɓanin yanda ta ɗauka abun a da akwai banbanci da yanda take kallonsa a yanzu... Sake maida idanun nasa da ya ɗan kauda daga kanta yayi, sai dai yanzu a kan kofin shayin da take faman damƙa ya sauke su, ya ɗanyi sama da su zuwa ƙirjinta da girman rigar asibitin ta sakaya, sake sama yay zuwa kan fuskarta da ke nuna ainahin yanayinta. Lumshesu yay da sake buɗewa cikin salon shanyesu matuƙa mai son nuna kasala a bayyane, sai dai tsaf ya shanye komai daga kan fuskarsa ya haɗiyema ransa yana mai furzar da iska kaɗan tare da gyaran muryar da ta sakata zabura alamar hakan yazo mata a bazata. Dubansa ya maida ga Daneen Ammarah da itama gyaran muryar tasa ya sakata ɗagawa kamar su doctor, sai dai maimakon shi bakinsa ya ce wani abu sai Sayeed Fayzul-haq ne yay saurin faɗin, “Ranki ya daɗe, adalin shugaba mai musanya sharri da alkairi na miƙo gaisuwar yaya jiki ga Zawjata-almilk. ALLAH ya ƙara mata lafiya da rayuwa mai albarka.” Daneen Ammarah ta ɗan nisa kaɗan da jinjina kanta tana mai gyara tsaiwa. “Zawjata-almilk na godiya da wannan karamci, tana mai fatan alkairi da addu'ar samun lafiya ga Shahan-shan shima”. Iffah da ke saurarensu cikin tsinkewar zuciya ta ɗan ɗago ido kaɗan da niyyar duban sa dan rashin gamsuwa da zancen Sayeed Fayzul-haq a maimakonsa, tasan bazai barta ba, dolene ta samu hukunci dai-dai da laifinta. Sake tsinkewa zuciyarta tai sakamakon shigar idanunta cikin nasa da ke mata kallon ƙasa-ƙasa da ta gagara iya bashi fassara, sai kawai taji jikinta ya fara ƙyarma. Bata san ta ya ba, bata san ya akai ba taji an riƙe kofin shayin hanunta da ke faman tangal-tangal zai kife a jikinta. A raunane, a kuma birkice ta sake ɗago manyan idanunta da ciwo ya sakasu raunana haɗe da kumburowa. Damar sarƙesu ya sake samu cikin shanyayyun nasa masu kaifi, sai kawai ta saki kuka, kuka irin wanda ta jima da son tayi, kuka irin wanda take buƙatar mai lallashi, kuka irin mai nuna tsananin bukatuwar ɗumin mahaifa ko shaƙiƙan ƴan uwa da zasu rungumeka su lallasheka. Cigaba yay da kallonta kawai shima zafin shayin na ratsa masa hannun da har ya fara gumi ga raɗaɗi na shigarsa. Baya son ji dan yana matuƙar sukarsa, sai dai bazai hanata ba dan yafi son tayisa har iya iyawar jin ta gamsu a karan kanta. Takoyi ɗin fiye ma da yanda yake buƙata, dan sai da ta kai har ya fara cije lips ɗinsa a tsakkiyar haƙora. Sai dai ƙasaita, izza da tsananin miskilanci mai samun jagorancin gudanar jinin mulki da ke tare da shi ya hanashi cewa da ita komai, koman da koda kuwa abinda ya shafi laifinta ne harta fara jan numfashi a suƙe mai alamar ƙoƙarin haɗiyewa........✍️
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 96 09 67 63
Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (11)
.........Doctor dai da Sayeed Fayzul-haq kawunansu a ƙasa mamaki na ratsa su, dan ba abinda sukai zaton gani ba kenan musamman idan akai la'akari da laifin Zawjata-almilk ɗin. Daneen Ammarah kam idanunta ta lumshe tana mai sakin murmushi da addu'a mai girma a ƙasan zuciyarta. Duk da tasan gane ainahin abinda ke cikin zuciyar wannan gwarzon nasu abune mai wahala, mutum ne miskili da ya gajesa wajen uwa da uba. Ga zurfin cikin tsiya uwa uba jinin mulki dake yawo a jikinsa. Sai dai hakan baya nufin taƙi son tabbatuwar abinda take fata ɗin.... “Wannan ya huce a canjashi da wani Mamy”. Ya faɗa a can ƙasan maƙoshi yana miƙewa tamkar bashi ne yay maganar ba. Da alama Daneen Ammarah ta fahimci abinda yake nufin, dan kallo ta bisa da shi mai tattare da ɗan murmushi har ya fice Sayeed Fayzul-haq da Doctor suka take masa baya. “Muna godiya da wannan karamci”. Ta faɗa dai-dai zai fice a ɗakin. A yanzun ma Sayeed ne ya amsa mata da tausasawa, yayinda shi ya fice abinsa. Daneen Ammarah ta sake sakin murmushi da zaunawa a gefen Iffah, kofin shayin ta amshe tana ƴar dariya. “Haba Ibnati, irin wannan rawar jiki haka! Ki kwantar da hankalinki insha ALLAHU babu abinda zai faru sai alkairi. Abni adalin shugaba ne mai son kwatanta adalci wa kowa koda kuma maƙiyinsa ne”. Kalmar ƙarshe da ƙarfi ta zabiri Iffah. Sai kawai ta sake fashewa da kuka tana mai jujjuya kanta lips ɗin ta na rawa. “Mamy nayi kuskure, kuskure irin wanda bazan iya yafema kaina b.....” “Ya isa haka”. Daneen Ammarah ta faɗa tana mai ɗora mata yatsa akan baki alamar tai shiru. Shirun kuwa tai sai dai hawayen basu bar zuba ba, ga jikinta na ɗan tsuma har sai da ta rungume ta cike da lallashi..
*_★.. TA-ƘURYA ..★_*