Kenza eBookz

Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul - Chapter 40

Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul - Chapter 40

Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 40: Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 40. Ta ɗauki tsawon mintunan da zuciyarta ke faɗa mata…

4,394 words

Ta ɗauki tsawon mintunan da zuciyarta ke faɗa mata ƙilama ya gaji ya fita, sai dai wani sashe na gargaɗinta. Jin an fara kiran sallar azhar ta sauke ajiyar zuciya, ta san dai tabbas dolene ya fita ai yanzu. Alwala tayi, kai tsaye ta fito tana ayyanama ranta ta saka ma ƙofar key kawai. Da sauri taja birki ganinsa zaune a harɗe cikin zaman ƙasaitar nan tasa a saman kujerar ɗakin, sai kuma ta juya da sauri zata koma dan yayi wani ɗam-ɗam da fuska. “Zaki sha mamaki idan kika koma”. Kamar zata fasa ihu ta dubesa, sai kuma ta ɗauke kanta ƙwalla na cika idonta. (Shikenan Iffah kekam sai abinda ALLAH yayi, gaki dama ba uwa ba uba miya rage kuma? Kawai yasa a tsireki) a zuciyarta take sambatun tana cigaba da takowa sum-suma batare data yarda ta sake kallonsa ba. Miƙewa yay shima fuskar nan babu alamar fara'a, idonsa a kanta. A gabanta ya tsaya mayen ƙamshin turarensa na cigaba da addabarta, ga mamakin yanda yake abubuwa kamar ba Shahan-shan ɗin nan nasu da suke hange da ga nesa ba mai shegen isa da izza na ƙara bata mamaki da ɗaukar komai tamkar wani mafarki. Jinsa a kusa da ita sai kawai ta rumtse idanunta da ƙarfi tana jiran abinda zai biyo baya. “Na tafi?”. Ya faɗa a hankali yana wani shanye idanunsa ƙasa-ƙasa a kanta. Da wani irin sauri ta buɗe idanunta da ɗagowa ta kallesa tana sakin nannauyar ajiyar zuciya saboda shock da furicin nasa ya sakata. Sai kuma ta kaudar da kan gefe dan salon kallon nan nasa birkita ta yake. Muryarta can ƙasa-ƙasa ta jinjina masa kai. “Magana nake so”. Ya faɗa a fisge kamar wanda akaima tilas. Tsabar yanda take jin kusancin nasu kamar zata shiɗe a hankali ta ce, “Uhhm”. Ɗan sake matsawa yay gareta dab har tana iya jin saukar numfashinsa a kan fuskarta. Jin saukar yatsunsa kan haɓarta ruf ta rufe idanunta da ƙoƙarin riƙe rawar da jikinta ke neman farayi. Ya ɗan lumshe idanunsa dake yawo akan fuskar tata yana ƙoƙarin shanye murmushin dake taso masa. A bazata kawai taji saukar lallausan lips ɗinsa saman goshinta ya manna mata sumba mai lafiya da har sai da ta saki wata ajiyar zuciya mai ƙarfi. Batare da ya sake cewa komai ba ya ja da baya ya juya ya bar ɗakin fuskarsa shimfiɗe da murmushin da duk sonshi da basar da shi hakan ya gagara. A ransa rayawa yake (Damisar takarda ga tsoro ga ban tsoro) Da kallo ta bishi har ya fice, ta sauke ajiyar zuciya da kaiwa zaune jagwab kamar wadda tasha gudu ta gaji, sai faman matse jikinta take waje guda amma yaƙi daina tsumar dole ta kai kwance na wani ɗan lokaci, badan taji ƙarfi ba dai ta miƙe tai sallar ganin lokaci zai shige....

Duk yanda yaso dai-daita kansa hakan ya gagara. Tabbas ya yarda SO wani abune mai matuƙar kaifi. Duk yanda kaso ɓoyeshi da ƙin son bayyanashi hakan gagara yake. Duk matsayinka, duk girman shekarunka, sai ya kaika ƙasa. Shi shaida ne akan hakan, tunda gashi yana gani akan kansa. Gaba ɗaya idan yana a gaban mitsitsiyar yarinyar nan manta shi ɗin wanene ya ke da matsayinsa. Ya rasa wannan abu haka mai kama da kamar wata almara. A gurguje ya canja shiga da ɗaura alwala ya fita masallaci. Ya wani tsume kamar bashi ba, dan a Shahan-shan ɗin sa ya fita mai tsananin ƙasaita da izzar nan ga miskilancin tsiya. Bayan idar da salla bai shigo ba ya zarce fada, umarnin isar da saƙon tattaro masa wasu a cikin manyan masarautar ya bada. Cikin ƙanƙanin lokaci duk wanda sunansa ya fito a zaman saƙo ya riskesa. Kafin cikar wasu mintuna duk sun hallara. Duk da kasancewar yana a cikin fadar a wani matsakaicin falonsa yake zaune ba cikin ainahin fada inda karagar mulki take ba. Da ga shi sai amintaccen hadiminsa na amana da ako ina ka gansa shima zaka ganshi, idan ka cire ɗakin barcinsa kawai. Suma ɗin yana shiga kai abinda ake buƙata da kuma gyarawa. A zahiri zaka ɗauka hankalinsa kan television ɗin da ke aiki a falon suke, dan manyan kaifafan idanunsa na kanta ne. A gabansa ƙyaƙyƙyawar butar shayi ce irin ta hamshaƙan sarakai kalar golden mai tsananin ɗaukar idon mai kallo. Dan har wasu irin fararen stones aka jera jikinta da ya sake ƙayatar da ita. Sai dai hankalin nasa sam ba'a nan ɗin yake ba. Gaba ɗaya a tunanin zantukan Iffah ne na ɗazu. Dan shauƙin da yake ciki bawai ya mantar da shi bane ba. Ya dai tattarasu ne ya ajiye gefe domin basu nasu lokaci. Sallama Sayeed Fayzul-haq ta saka amintaccen Ghazi ɗinsa da ke gefensa tsaye ko gajiya bayayi amsawa. Sai kuma ya nufi ƙofar domin duba wanene. Shi dai bai motsa a yanda yake ba, kai kace ma bai san abinda ake ba. Minti ɗaya da wasu sakanni amintaccen nasa ya dawo, a gabansa ya zube murya cike da tsantsar girmamawa yace, “Kariyar UBANGIJI ta cigaba da kasancewa zagaye da adalin shugabanmu. Sayeed Fayzul-haq ne ke isar da saƙon kammalawar kasancewar kowa”. Shiru babu alamar zai tanka har kusan mintuna biyu, sai ka rantse baima jisa ba. Sai da ya mula dan kansa ya motsa lips da ƙyar. “Zasu iya shigowa”. “Umarninka shine abin jiran kowa”. Hadimin ya faɗa yana rissinar da kai sannan ya miƙe da sauri. Cikin abinda bai fi minti uku ba dattijai masu cikakkiyar kamala da nutsuwa suka dinga shigowa ɗaya bayan ɗaya a nutse. Duk wanda ya shigo sai ya miƙa gaisuwa kafin ya wuce ya zauna. Sayeed Fayzul-haq ne ƙarshe hannunsa ɗauke da ledar da aka zuba kayan surkullen nan. A gaban Tajwar Eshaan ɗin ya kai ya ajiye yana ɗan matsar da ƙyaƙyƙywar butar shayin nan kaɗan. Leda ɗin ya buɗe sannan ya ja da baya shima ya zauna. Yanzun ma sharewa yay tsahon wasu mintuna kamar bashine yasa a tarasu ba, kowa kuwa a cikinsu ya zubama ledar ido musamman Miran Arshaan da jikinsa har tsuma yake, sai dai yana ta faman taushe kansa. Tajwar Eshaan da ke nazartar kowa ta ƙasan ido ya motsa lips ɗinsa da ƙyar yana mai buɗe idanunsa masu saka mara gaskiya tsuma tar-tar a kansu da ƙyau. “Bana bukatar sanin wanda ya ajiye su balle dalilin ajiye sun. Sai dai zan gargaɗi mai ajiyewar da abu uku. Eshaan a koda yaushe yana zagaye ne a cikin kariyar UBANGIJINSA insha ALLAHU. A komai na ina amfani da zuciya ne fiye da ƙwanji na da ƙwaƙwalwa. A kuma duk sanda maƙiyi ya sokeni ta baya sunansa matsoraci a wajena, jarumi gaba-da-gaba yake zuwa filin daga in har ya cika sunansa jarumi. Saboda haka, idan har ya shirya na bashi tabbaci ɗan Haysam bin Abdul-majeed Aliy Qutb a shirye yake shima”. A take falon gaba ɗaya ya ɗauka kalmar neman afuwa da fatan hucewar zuciya ga Shahan-shan. A baɗini kam baka jin komai sai bugun zuciyoyi, yayinda ake ma juna ƴar kallon kallo, dan ba ƙaramin ratsasu kausasan kalaman Tajwar Eshaan ɗin suke ba, duk da a zahiri shi ya yisu ne cikin sanyin nan nasa mai amon nutsuwa da cikakkiyar ƙasaitar tabbatar da shi ɗin wanene. Ƙananun maganganu ne suka nema fara tashi kowa na ƙoƙarin son ganin ya kare kansa. Yi yay kamar bama jinsu ya ke ba, sai da Sayeed Fayzul-haq ya fargar da su sannan falon yay tsitt. Wani ɗan ƙyamusashen tsoho da suke kira Sayeed Tasadduq-Husain da fuskarsa ke nuna alamun ɓacin rai ya dubesu cikin ɗacin murya, a karo na farko da tun shigowarsa falon yay magana. Shima ɗin kamar Uncle ya ke a wajen Tajwar Eshaan, mutum ne mai tsananin tsage gaskiya a duk yanda tazo shiyyasa bai cika farin jini a wajen su ba, alokuta da dama idan yaga an dabaibaye rayuwar Tajwar Eshaan da yawa yakan nuna ɓacin ransa har ya faffaɗi maganganu masu ɗaci, to a yau ɗin ma tin ganin waɗan nan kayan sirkullen ɗazun ya nuna takaicinsa, hasalima shine ya ingiza Sayeed Fayzul-haq kan Tajwar Eshaan ya tarasu ayi maganar kar a wani rufe, gara wanda ya ajiye abubuwan ya san an san ya ajiye ɗin.........✍️

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 96 09 67 63

Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (30)

..........“Ƙoƙarin kare kai bashi zai fidda kowanne mu ba, duk da bazai yiwu ace dukanmu anan ne muka aikata ɗin ba, sai dai dole duk ma wanda ya aikata a cikinmun yake dai. Shin wace irin rayuwa ce muke son ta cigaba da yaɗuwa a wannan zuri'ar tamu ne bayan kasancewar mu jini ɗaya?. Shin mi muke nema wanda UBANGIJI baiyi mana shi ba? Mi muke buƙata da ga siffofin shugaba na gari da ALLAH bai azurta bawan ALLAHn nan da shi ba da a kullum muke son nuna bore da hukuncin ALLAH? Ni na rasa gane mi duk mai ƙoƙarin assasa fitine-finen nan ke buƙata ba ko san zuwa. Shin mulkin yake so ne? Ko kuwa rayuwar wannan bawan ALLAH da'a kullum alkairinsa ke zagaye da mu..” takaici ya saka hawaye ziraro masa. Handkherciff yasa ya share tare da sake dubansu ya cigaba da faɗin, “Shike nan babu mai hana koma waye yin yanda ya ke so, sai dai ya sani a duk randa yazo hanunmu wlhy ko shi waye a cikinmu sai yayi dana sani da nadamar kasancewarsa cikin zuri'ar mu. Sannan tarihi zai masa tanadin da bazai taɓa goge sunansa ba a matsayin azzalumi mai fuska biyu a cikin zuri'ar mu. Wannan faɗan ba nashi bane namu ne, dan mu nan da mu akeyi ba da shi ba, dan haka duk wanda ya shirya bismillah muma mun shirya”. A zahirance duk nuna goyon baya a kan maganarsa sukai, sai dai a ransu ji suke kamar su shaƙo wuyan Sayeed Tasadduq-Husain ɗin. Yasan da hakan, shiyyasa ko kallo babu wanda ya ishesa a cikinsu, ya kuma ci dubu sai ceto. Miran Arshaan da gaba ɗaya ya ke jin kamar ya danne Sayeed Tasadduq-Husain a wajen ya masa yankan rago ya taushi zuciyarsa da ƙyar, dan wannan wata dama ce a garesa, rashin ganin Miran Jasim a wajen yay masa da ɗi, dan haka ya miƙe cike da dakewa da tsan-tsar iya makirci shima ya fuskancesu ya zuba kausasan kalamai, da ga ƙarshe ya rufe da faɗin, “In ma tsoro da kunya sun hana duk ma wanda ya aikata ɗin zuwa nan batare da mun farga ba to na tabbata akwai mabiyansa da irinsa anan ɗin, sai su isar da saƙonmu na tabbatar da duk randa mutum yazo hanunmu sai ya yabama aya zaƙinta a wannan masarauta kamar yanda Sayeed Tasadduq-Husain ya faɗa”. Kalamansa kam tabbas sun saka wasu fara hasaso abinda yake son dama ai hasashen, sai dai babu wanda ya furta a zahirance aka cigaba da tattaunawa.

Ya ɗauka tsahon lokaci da su a falon suna tattaunawar, dan suna fitowa da ga zaman ma masallaci suka zarce sallar la'asar. Bayan an idar ya koma sashensa. Bai nema Iffah ba yanzun kam. Dan yana buƙatar ɗan hutawa saboda yau zai ɗanyi fitar dare ta sirri zuwa cikin gari. Sai dai koda ya shiga ɗakin ma sai yaji baida buƙatar kwanciyar saboda ransa a matuƙar ɓace ya ke har yanzun. Tashi yay ya canja kayansa cikin wasu fararen wando da riga tas na kamfanin *Nike* da sukai masa matuƙar ƙyau duk da ya sane badan kwalliya ba. Takalma ya ɗaura a ƙafarsa baƙaƙe ya ɗauka p-cap a hannu ya fito cikin takun nan nasa mai tabbatar da shi ɗinne dai ko da ga nesa. Cikin sauri amintaccensa ya miƙe ƙansa rissine, ba sai yace masa ga abinda yake buƙata ba, kai tsaye ya fahimci inda suka dosa. Kafin ya ƙaraso gareshi yay saurin ɗaga waya yay kiran sarkin barga. Ana ɗagawa yay saurin bashi umarnin shirya dokin amana da kowa ya san in ba shi ba Shahan-shan ɗin baya hawan kowanne doki a gidan. Wayar ya katse dan dai-dai da isowar Tajwar Eshaan ɗin, ganin ya nufi elevator batare da ko kallon inda yake yayi ba shima ya zabura. Cikin sauri ya danna floor 1 bayan ƙofar ta maida kanta ta zuge. Suna fitowa da ga lift ɗin ɓoyayyar hanyar da zata fiddasu batare da ko hadiman ƙasan sungansu ba ya nufa, amintaccensa biye da shi. A wani ƙaton fili suka fito, an gyara wajen da wani irin farin yashi mai matuƙar ɗaukar idon mai kallo da birgewa. Kasancewar ruwan saman da aka sha sai wajen ya sake bada wani yanayi mai matuƙar daɗi ga sassanyar iskar da bishiyoyin da aka ƙawata wajen na dabino na bayarwa. Da ga ɗan nesa da su Sarkin barga ke riƙe da ƙyaƙyƙyawan farin dokin da shi da kansa ya raɗa ma abinsa suna da ƙyautar ALLAH. Kamar yanda ɗabi'ar dokin take suna fitowa yay wata irin haniniya da girgiza kai kace ƙamshin Tajwar Eshaan ɗin yake ji ya shaida kasancewar sa a waje. Da wani irin gudun bajinta ya nufosu, yana isowa gabansa yay wata irin ƙwafutar ƙasa yay girgiza da haniniya, har gashin saman kansa zuwa wuya na wani tarwatsewa da haɗe kansa waje guda. A hankali Tajwar Eshaan ya lumshe idanunsa yana sakin sassanyan murmushi da mutane kan jima basu gani tare da shi ba sannan ya kai hannu ya shafi fuskar dokin yana masa magana ƙasa-ƙasa da ko Sarkin barga da amintaccen hadiminsa dake tsaye gefe kawuna a risine basa iya jinsa. Cikin wani irin salon da ke tabbatar da ƙwarewarsa a iya sarrafa dokin ya damƙi linzamin sa cikin action mai matuƙar ɗaukar hankali da bajinta ya ɗane saman sa. Cikin tabbatar da ƙwarewar da dokin ya samu a hanunsa yay wata irin haniniya da ƙwafutar ƙasa ya ɗiba hanya tamkar a filin polo. Rere suka fara ɗan gaske da sauran dokunan huɗu da aka sakakarma linzami batare da kowa a kansu ba. Duk wanda ya ga yanda yake sarrafa dokin basai an faɗaba ya san shi ɗin ƙwarren ɗan wasan polo ne kuma jarumin gaske. Dan cikin ƙanƙanin lokaci yay ma sauran dokunan da babu kowa ɗin fintinkau, har ya sake dawowa ya koma sannan su suka iso. Kaida gani kasan yana nishaɗi da wasan matuƙa. Sosai su sarkin barga ke murmushi da jinjina jarumta irin ta gwarzon Sarkin nasu. Ko'a cikin dubu shi ɗin na dabanne da kai tsaye za'a nuna a shaida. Dan suna da tabbacin da a lokacin yaƙi ne yazo babu abinda zai hana ya zama babban jarumin da tararsa a filin daga abin tsoro ne. Ya ɗauka tsahon lokaci yana wasan dokin har sai da yaji ya gamsu jininsa ya tashi fiye ma da yanda yake buƙata sannan yaja linzamin dokin ya dire bisa ƙasa cike da bajinta yana sauke numfashi ɗaya-ɗaya. Da sauri amintaccensa ya matsa garesa hannunsa ɗauke da ƙyaƙyƙyawan tray mai ɗauke da gorar ruwa da glass cup. Goran ruwan ya ɗauka batare da ya haɗa da cup ɗin ba, ya ɓalle murfin ya kai bakinsa. Yasha kusan fin rabi sannan ya juyo ya juye sauran akan fuskar dokin nasa yana ɗan murmushi. Haniniya dokin yayi mai nuni da isharar jin daɗin kasancewarsa da adalin ubangidan nasa. Shima sai ya kai hannu ya share masa ruwan yana murmushi. Ƙaramin towel Sarkin barga ya miƙo masa da sauri, bai musaba ya amsa ya goge hannunsa da wuyansa sannan ya kai shi ga fuskar dokin shima ya share masa ruwan da ƙyau. Yanda yake ma dokin da kansa dolene ka tabbatar akwai matuƙar shaƙuwa a tsakaninsu mai birgewa da ƙayatarwa. (Ko dabba ma ta san me bata kulawa da nuna ƙauna kenan☺️😘)

★★...... ★.... ★...

Karo na biyu kenan da ta sake dawowa ɗakin ta samesa yana kai kawo rai a ɓace. So take taji miye damuwarsa, sai dai tana matuƙar shakkar hakan. Dan mijin nasu wani irin bahagon mutum ne da sam baida daɗin zama. Su dake tare da shine kuma kawai suka san hakan. Amma ga al'ummar masarautar kowa yabonsa yake, shiyyasa a lokuta da yawa idan suka kai ƙararsa ga Shahan-shan tun ma zamanin Tajwar Haysam sai kiga ana ganin laifinsu na gajen haƙuri da rashin godiyar UBANGIJI. Hayaƙin Shishar da ya bulbule ɗakin da shi ta ɗan saka hannu ta kore, dan shi kansa ma da ƙyar take iya hangosa. Ƙundunbalar shiga tayi dan so take ta sanar masa kiran da aka aiko ana masa da ga Shahan-shan, amma tsoro takeji ganin yanayin da yake ciki. Muryarta na ɗan rawa ta risina da ga tsakkiyar ɗakin tana shaƙar hayaƙin madadin iska da ƙyar. “Barka da wannan lokaci Abu Husam”. Cak ya tsaya da ga zuƙar Shishar, yay wani masifar bulbulo hayaƙin bakinsa da ya sake turniƙe ɗakin zuciyarsa na wani irin kumburowa da takaicin wace ƴar ƙunar baƙin waken ce a matan nasa data manta da dokarsa. Sai da hayaƙin ya lafa sannan ya iya ganinta da ƙyau, e ai ya sani sai ita ɗin, dan babu mai yawan shiga masa hanci kamarta. Tsawa ya daka mata yana miƙewa a fusace. “Buhaysah! Ban ce bana buƙatar ganin wani a sashe na ba da ga nan har sai idan nine na nema mutum?!!”. A ɗan firgice ta zabura baya, sai kuma ta shiga girgiza masa kai jikinta na ƙyarma. “Hakane, amma Ka gafarce ni Abu Husam, wlhy bada son raina na karya maka doka ba. Saƙone da ga Shahan-shan ana buƙatar ganinka. Naga kada kai laifi ne shiyyas....” “Tasss!!” Kakejin saukar wani lafiyayyen mari akan ƙyaƙyƙyawar fuskar ta. Dan mace ce zankaɗeɗiyar gaske dirarriya. Duk da shekaru sunja gareta ƙyawunta a bayyane yake gata ƴar gayu. Ba yau ta saba shan mari a wajensa ba, amma sai na yau ɗin yay mata ciwo fiye da ko yaushe. A hankali ta ɗaga jajayen idanunta ta kallesa, fuskarta na nuna alamar ɓacin rai, abune kuma da bai taɓa gani da ga gareta ba. “Abu Husam minene laifina anan da har na cancanci mari dan ALLAH?”.. “Ƙari kike buƙata kenan?”. Ya faɗa a zafafe da sake yunƙurowa zai sauke mata wani duk da jin wani shakkarta a yau ɗin da yaji ta shigesa.. Abin mamaki da firgici ga Miran Jasim, sai ga Buhaysah kam ta riƙe hannunsa caraf.........✍️

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 96 09 67 63

Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (31)

..........Abune da bai taɓa faruwa ba a tsakaninsu, a tsahon shekarun da suka kwashe tare na aure talatin da ɗaya cif. Cikin ido take dubansa da wani irin kallo mai gigita zuciya “Jasim tsahon shekaru talatin da ɗaya kenan nake zaune a ƙarƙashin mulkin mallakarka. Nayi juriyar nayi kawaicin amma na fahimci kai ɗin gafalalle ne da baya gane komai a rayuwarsa sai son zuciyarsa. A da dai na haƙurce maka na shanye, amma a yanzu zan tabbatar maka dai-dai nake da kai asararre kawai da ya girma bai san ya girma ba!”. Ta yarfar da hannunsa gefe da wulla masa wani irin mugun kallo ta juya zata fice. Wata irin zabura yay da ga sumar wucin gadin mamakinta daya riskesa, ya wani shaƙo wuyan rigarta ta baya ya fizgita jikinsa na rawa. Kiyyyyy rigar ta shiga kecewa, hakan yasata yin gaba. Tsabar shi cikakken mugune yasa ƙafa ya taɗeta. Mummunar buguwar da ta sakata ƙwalla wahalalliyar ƙara tai a ƙasan wajen. Cikin rufewar idanu yasa ƙafar ya taka mata gadon baya sai ga ƙashi na bada sauti. A guje suka dinga rige-rigen shigowa dan ƙarar tata ta matuƙar ratsa kunnuwansu. Basu kaɗai ba hatta da hadiman dake musu hidima a sashen babu wanda zai ce baiji ƙarar baiwar ALLAHr nan ba. Ganinsu baisa ya dakata da dukanta ba. Cikin wata iriyar fusata babban ɗansa da itace mahaifiyarsa Husam yay wani irin kukan kura ya hankaɗashi baya sai da ya daki bango. Baiyi wata-wata ba kuma ya damƙi wuyan rigarsa ya shaƙeshi dan shima yaron tsageran kanshi ne. Kaf halin Miran Jasim ɗin ya kwaso, sai dai duk da haka yana bala'i bala'in son mahaifinsa. Ya jima da ciwon dukanta da mahaifinsa keyi duk da bata taɓa fitowa fili ta sanar masa ba. Tun yana yaro ko shatin yatsu ya gani a fuskarta ya tabbaya sai tace bakomai ko bigewa tayi. Sai bayan ya girama ne ya fahimci mahaifinsa ne ke marinta kamar yanda suma sauran matansa biyu ba tsira sukai ba. Rawa jikin sauran matan nasa ya shigayi, sun rasa ma wa zasu bama ɗauki, shi da Husam ya shaƙe ko Buhaysah da ke kwance tana madoɗowar azaba. Gwara kansa da bango da Husam yayi yana ƙaraji ya sa matan yin kansa da sauri suna kuka da roƙon Husam ɗin ya sakesa. Amma ina yaron nan ƙara gwara kan Miran Jasim yake yana kai masa naushi kamar ba mahaifinsa ba. Ga wani irin ƙarajin ɓacin rai yanayi mai haɗe da kuka. Sukam al'amarin nan yafi ƙarfinsu, hankali tashe suka shiga neman number Miran Arshaan amma ba'a daga ba. Har kira uku babu alamar za'a amsa dole suka maida akalar kiran ga Daneen Ammarah domin ta sanar da Mammah da Sayeed Fayzul-haq kasancewar sun san yana ɗan jin shakkarsu, dan daga Malikat Haseenat ɗin har Sayeed Fayzul-haq ɗin basa ɗaukar raini ko wasa a garesu dama masarautar kowa yasan haka. Wayar ta riski Sayeed ne lokacin da yake fitowa daga sashen Tajwar Eshaan bayan masa rakkiya daga sallar la'asar da suka idar. Itama Daneen Ammarah lokacin tana ƙoƙarin tashi da ga abin salla. Hankali tashe duk suka nufi sashen Miran Jasim ɗin har da Malikat Haseenat ɗin da aka saka a mota, dai-dai da shima Miran Arshaan ya nufi can dan shima yayi mamakin rashin ganinsa wajen tattaunawar da akayi duk da yasan dai ransa a ɓace yake matuƙa. Dan tun jin Tajwar Eshaan bai fito fada ba da safe ransu ke'a jagule. Yanzu kuma a wannan zaman ashe ma akansu ne akayisa duk da dai shi Tajwar Eshaan ɗin bai fito fili ya ambaci suna ba, amma duk da wannan sanin da yay akan Miran Jasim ɗin ya zaɓi yimasa zamba cikin aminci dan a ganinsa lokaci yayi da shima zai dakata da ga rakkiyar Miran Jasim ɗin ya fara yaƙin kansa...

Da ƙayar aka ɓanɓare Husam da ga shaƙar da yay ma Miran Jasim, yaraf ya zube ƙasa hannunsa kan maƙoshinsa yana kakari. Idanunsa sunyi ruƙu-ruƙu tsabar yanda yaji shaƙar nan, ga kansa daya fashe saboda ƙuma masan daya dinga yi sai jini yake yi. A gefe ga Buhaysah da ke kukan wahala Husam ya je ya rungumeta yana kuka da alama dai yaji mata ciwo a baya koma ya karya ta ne oho. Malikat Haseenat da ta ɗan girgiza kanta da duban Sayeed. A matuƙar ruɗe Sayeed Fayzul-haq ya jinjina mata kai. Waya ya ciro yay kiran clinic ya bada umarnin a kawo ambulance ƙofar sashen Miran Jasim ɗin.....

A gaggauce aka miƙa Miran Jasim da Buhaysah asibiti. Husam kuma Malikat Haseenat tasa Daneen Ammarah su wuce da shi sashenta, yaron sai kuka yake mai matuƙar cin rai da zai baka tausayi, dan duk wanda ya kalla mahaifiyarsa yasan akwai babbar matsala a bayan nan nata da mahaifinsa ya taka Jigum-jigum sauran matansa da yara suka zauna. Kowa ka gani cikin damuwa. Dan wannan abun kunya ne da in har ya fita koda a cikin masarautar ne bazasu taɓa jin daɗi ba. Mijinsu mugu ne, dan ba yau ya fara kai hannunsa kansu ba, sai dai in ka cire Tajwar Haysam da Malikat Haseenat da mahaifiyarsa Ameera Banafsha kafin ta mutu babu wanda yasan hakan. Ko ƴayansu Husam ɗinne kawai ya sani sai mai bi masa Faida data zama babbar budurwa, inda ma ALLAH ya bata miji da tuni tai aure. Koda yake ba mijin ta rasa ba, taƙi sauraren samarin ne saboda mutuwar son Tajwar Eshaan da takeyi tun dawowarsa ƙasar ruman. Hatta da mutuwar matansa bai taɓa saka Faida jin zata iya daina son sa ba. Randa ya bayyana fuskarsa ba ƙaramin hauka tayi ba, duk da kuwa itama ɗin ƙyaƙyƙyawa ce sosai, sai dai shi kuma baima san tanayi ba..

Readers Also Read