Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul - Chapter 47
Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 47: Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 47. ........Bai fahimci gagarumar ɓarnar da ya aikata ba…
4,199 words
........Bai fahimci gagarumar ɓarnar da ya aikata ba sai da ya dawo jayyacinsa. Tun-tuni azaba tasa Iffah ta sume masa batare da ya farga ba. Ba ita da dama ya zama dole ta jigatun ba, hatta da shi kansa a jigacen yake kasancewar wannan shine lokaci na farko a tarihin rayuwarsa. A kallo ɗaya zaka fahimci tabbas maza sunyi laushi, laushi bana faɗuwa ko gazawa ba, laushi na jin-jina girman UBANGIJI da godiya a garesa dan shine mai azurta bawa da ni'imomin kala-kala iri-iri daban-daban da kai kanka baka fahimtar girman wannan ni'imar sai randa ta isa gareka. Babu ɗan gata a ma'aurata mace ko namiji sai mafi ƙololuwar iya riƙe kansa da nisanta kansa da ga ZINA har sai randa ALLAH ya azurtaka da halal ɗinka. Ya shaida yau kam ya shaida. Bayan uwa da uba da kakarsa bayajin ya taɓa jin ƙauna da soyayyar wani mai tsananin ƙarfi a zuciyarsa kamar yarinyar nan. Ƙololuwa yake jinta, ƙololuwar da in har akace yay fassara ba lallai masu jinsa su iya yarda ba ko zaman saurarensa har ya kai inda yake buƙatar gamsar da su. Badan kar ace ya bada maza ba da shimafa kukan zai fashe da shi kawai a wannan gaɓar. Da ƙyar ya iya ɗagota yana ɗan bubbuga fuskarta da kiran sunanta cikin sarƙaƙaƙƙiyar muryar sa. A baɗini a birkice yake, amma a zahiri da zaka iya ganinsa a nutse yake komai tamkar ma koman da mai kallo zai kalla komai bai zama komai ba. Iya jijjiga da kiran sunanta da yayi babu alamar rai tare da ita. Ya rumtse ido da ƙarfi tare da kai hannunsa saman goshinsa yana murzawa tsabar baima san miya kamata ace yayi ba. Shifa ɗan gata ne, ɗan hutu ne, ɗan lele ne, tunda ya tashi bai san komai ba sai ai masa cikin bada umarni, a inda ya rayu zagaye yake da masu hidima daban-daban da ko abinci inda zai yiwu tauna masa za'ai a zuba masa a cikinsa. Sai da yay matuƙar yaƙi da iyayensa kafin ya samu wasu damammaki na dogaro da kai dan shi yafi son tsayawa a kan ƙafafunsa koda ace shine mafi zama ƙololuwar gata a wannan rayuwar. Bai taɓa ƙyamatar rayuwar talakansa ba sai ma birgesa da basa tausayi yake. Shiyyasa ya zaɓi shiga cikinsu ta hanyar ɓadda kama, ya kuma ƙir ƙiri wasu hanyoyin tsaya musu a duk lokacin da ya fahimci ana zaluntar su. Bashi da zaɓin da ya wuce sake maidata a jikinsa kawai ya rungume tsam-tsam ya shiga bata wasu irin manya-manyan sumbata masu daraja da ba'aima macen data ɓarar da darajar a wajen marasa daraja. “Kiyi haƙuri, kiyi haƙuri na tuba my Ashna”. Ya faɗa cikin kunnenta yana ɗan hura mata isaka a sautin muryar nan tasa da ta sake disashewa matuƙa cikin maƙoshi kai kace zata iya jinsa. Kamar ko wani siddabaru sai kawai tai wani irin zaburowa da jan numfashi a fisge. Da sauri ya janye hannunsa da ke saman goshi ya dubeta, sai kuma ya sake riƙota da ƙyau cikin jikinsa da take neman kufcewa yana ambaton sunan ALLAH a daburce. Wani irin siririn kuka data sake birkita masa lissafinsa ta sake sakar masa tana ƙanƙamesa da jera masa magiyar roƙon ya barta, ya barta zata mutu, dan a rayuwar Iffah bata taɓa cin karo da azaba makamanciyar ta wannan gaɓa ba. “Am sorry relax, cool down babie” ya faɗa yana ƙara ƙanƙameta cikin jikinsa da tura yatsun hanunsa cikin birkitacciyar sumar kanta da ya gama harmutsawa. Har aka fara kiraye-kirayen sallar asubahi bai daina lallashin da bai san taya zai mata magana mai tsahon da zata fahimcesa ba. Shi gaba ɗaya ma ya wani mance kansa a matsayin Shahan-shan, duk ta gama harmutse masa ɗan sauran lissafin da ya rage masa da rikicinta. Yasan zai fiskanci ma fiye da haka in dai yarinyar nan ce, ba'ace mata kule ba ma tace cas inaga yau shi ya taro fitinarta da karan kansa, ai yasan a darunta ma bata fara komai ba kam dan har yanzu bata gama dawowa a hayyacinta ba ballema ta fara. A hankali yay ƙoƙarin kwantar da ita domin sauka ya samu mafita amma ta ƙanƙamesa ta na sake sakar masa wani sabon kukan da ko muryarta ma ba'a iya ji tsabar yanda ta gama galabaita. Ji yay kawai murmushi mai sanyi ya suɓuce masa, sake riƙota yay yasa a cikin jikinsa yana hura mata iska a kunne cike da soyayya da ƙaunarta da ke neman fallasa kansu a zahirinsa. Ajiyar zuciya ta cigaba da saukewa jikinta na saki kaɗan-kaɗan, da ga haka wani wahallen barci yay awon gaba da ita. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke ya kwantar da ita a hankali sannan ya sauka a gadon. Cikin ƴar sassarfar da a zahiri bazaka taɓa gani ba, dan babu abinda ya canja a salon tafiyarsa ta ƙasaita ya nufi bathroom, ƙarƙashin shower kawai ya shiga, babbar gaba ɗaya ya kunna ma kansa tare da dafe bangon glass ɗin da aka zagaye wajen shower ɗin kamar wani ɗan ɗaki. Duk da sanyin da garin ya ɗauka na hadarin da aka haɗa ya ƙare da isaka da ɗan yayyafi ya baje dana ruwan baya jinsa ma. Cikin ƙanƙanin lokaci ruwan yay masa sharkaf, tattausan yalwataccen gashin kansa duk sun kwanta masa a goshi har wasu na ɗan taɓa saman idonsa saboda ɗan tsayin da suke da shi. (She's my everything. Ta daban acikin daban ƙololuwa!....) Kawai yake iya maimaitawa a zuciyarsa hakwaransa cije da lips ɗinsa kamar zai hudasu kawai ya huta. Sai da ya kwashe kusan mintuna bakwai a ƙarƙashin shower ɗin sannan yasa hannu ya danne makunar yana sauke numfashi a jajjere. Har lokacin hannunsa ɗaya dafe da bangon glass ɗin. Jin atshawa na taso masa sannan ya buɗe idanunsa da sukai wani irin jajir da ƙanƙancewa. Sanin in har ya fita da wannan sanyin a jiki zazzaɓi salamu alaikum ya sashi sake kunna shower ɗin, sai dai yanzu ruwan ɗumi ne saɓanin ɗazun. Sumar kansa ya shiga yamutsawa a kasalance ruwan ɗumin na ratsashi da ƙyau, da ace zai iya kuwwar tattaro hankalin mutanen duniya baki ɗaya zai faɗa musu itace komansa, idan yace komai, komai da komai yake nufi akan komai. Sake jin kiran salla ya sashi ƙarasa komai a gurguje ya fito.. Yana fitowa a kanta ya fara sauke birkitattun idanunsa da launinsu ya zama abin firgitarwa ga mai kallo. Tuni barcin da ya ɗauke ta ya ƙara nisa, barcin da shi a karan kansa yasan na wahala ne kawai. Janyewa yay ya cigaba da takowa cikin ɗakin sannu a hankali kamar mai sanɗa, dan gaba ɗaya jikinsa babu wani ƙarfi kona sisin kwabo. Sai dai jarumtarsa ta ɓoye komai bayan canjawar launin idanunsa baka isa fassara yanayinsa ba. A gurguje ya busar da kansa domin rage laimar cikinsa ya shirya cikin jallabiya mai taushi fara tas, ya ɗaura baƙar alƙyabba irin ta sarakunan Saudiya da mayafi a kansa tare da daɗaɗan ƙamshi kamar ba sallar asubahi zai fita ba. Gaban gadon ya tako a hankali, barcin kam da nauyi ya ɗauketa, sai dai a kallo ɗaya zaka fahimci a matuƙar wahalce takeyinsa, dan sai yamutsa fuskarta da yake ɗan gani a hasken ɗakin da yake dimmm take ga ajiyar zuciya da take ta faman saki a jajjere. Idanunsa ya ɗan lumshe ya sake buɗewa a kanta yana sakin guntun murmushi da jan jikinsa baya a hankali ya fice fara gabatar da salla kafin ya dawo su ɗora daga inda suka tsaya dan yasan sabon daru kam zai fuskanta. Shi kuma ko a yanzu badan yana jin tausayinta ba sake zuwa mata zai a yanda yake jin kansan nan.
★Ana idar da salla ya baro massalin, dan gaba ɗaya hankalinsa na gareta saboda yasan tana matuƙar buƙatarsa kusa da ita da taimakonsa a wannan gaɓar. Yanda ya barta haka ya dawo ya sameta. Yanzun ma baiyi wani motsin da zata farka ba har ya kammala zame kayan jikinsa ya canja da ƙananu. Bathroom ya nufa ya haɗa ruwa na musamman sannan ya dawo gareta. Kai tsaye ya kunna wutar ɗakin da ta haske ko'ina ko allura kuwa ka yarda kaga abunka. A hankali yake bin ɗakin da kallo tamkar yau ne karo na farko da ya fara kasancewa a cikinsa. Ya ɗan saki murmushi yana mai lumshe idanunsa da sake buɗewa. Shi kansa ɗakin ya ƙara zama mai wata irin daraja da kima ta musamman a garesa, dan ya zamar masa ɗaki mafi zama ƙololuwar sirri sama da duk sauran sirrikansa. Dubansa ya kai ga gadon inda Iffah ke ƙudindine sai faman sauke ajiyar zuciya take yi cikin barcin wahalar da take yi. Magiya roƙo neman agajin da ta dinga jera masa na dawo masa daki-daki, da'ace gilashin ɗakin nan ba mai hana fitar sauti bane babu abinda zai hana a daren na jiya gaba ɗaya daular ruman su jiye masa sirrinsa, dan bakinta bai mutu ba sai da ta sume masa. Ya ɗan sake murmusawa da takawa sannu-sannu kamar wanda baya so zuwa gaban gadon ya zauna gefenta. Fuskarta da tai luɓu-luɓu na kukan data sha ya shafa yana kaima lips ɗinta da sukai bushewar wahala sumbata. A firgice ta farka tamkar ɗazun, ta saki wani irin wahallen kuka da jujjuya kanta tana mai jero masa roƙon ya barta, dan ALLAH ya barta karya kasheta bazata iyaba. Yanda take yi ɗin dole ne ya baka tausayi, dan a kallo ɗaya zaka fahimci har yanzu bata cikin hayyacinta. Shi baima san ta ina zai fara ba duk da ya jima da shiryama irin wannan ranar ba tun yau ba, amma a yanda yaje mata shi kansa yasan ya jigata ta, irin jigatawar da da'ace wani ne ya aikata aka kawo masa ƙara sai ya hukunta mutum. Sai gashi shi da kansa ne, shi da kansa ya kasa control ɗin kansa yay ma ƙaramar yarinya kamarta zuwa har uku a dare ɗaya duk da ta kasance tamkar jaririya a hannun uwa garesa. “Shiiii!!” ya faɗa a hankali yatsansa kan lips ɗinta. Riƙeta yay da ƙyau tare da manna mata wata sumbar a goshi kafin ya miƙe cak ya ɗagata zuwa bathroom. Wata gigitacciyar ƙara ta saki jinta a ruwan zafi tana rirriƙesa azaba na ratsata, jikinta sai rawa yake shi kansa har abin ya bashi tsoro. Dole ya shiga cikin ruwan shima ya rungumeta a jikinsa. Kuka take matsananci da ƙoƙarin ganin tabar jikin nasa amma ya hanata damar hakan. Kansa ya dafe yana riƙota jikinsa da ƙyau cike da takaicin kansa, sai dai kuma shima ba laifinsa bane, gaba ɗaya idanunsa ne suka rufe, duk wani haƙurinsa da jarumtar da yake dannewa a tsahon shekaru sai da suka amayar da kansu. Tunfa yana da shekarun da basu haura ashirin ba yake dakon wannan matsalar, taya ma zai iya tuna abinda ya dace yayi a wannan gaɓar, ta yaya, ta yaya ake son ya tuna.......✍️
_🚴🚴🥱Bazaka tunaba kam mai Rumawa._
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 96 09 67 63
Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (45)
........Sai da ya tabbatar ta samu isasshen gashi sannan ya taimaka mata tayi wanka, har lokacin bata daina hawaye ba. Idan kuma ya ɗan motsata da ƙarfi ko yaya ne sai ta saki siririyar ƙara da ƙara ƙarfin kukanta. Babu abinda ya ke iya jera mata sai kalmar “Sorry, I am sorry”. Bai san tunzura mata zuciya kalmar haƙurin nan take sake yi ba. Koda ya saka mata bathrobe shima sai da ya cire kayan jikinsa dan duk sun jiƙe. Yanzu ma cak ya ɗagota zuwa ɗaƙi, ganin lokacin salla ya ƙwace da yawa ya ɗakko mata rigar jallabiyarsa ya saka mata, veil ɗin ta na jiya ya naɗa mata sannan ya saka mata sallaya ya sake ɗakkota da ga kan sofar da take kwance ya ajiye kan sallayar. Ta kasa tsaiwa yanda ya kamata tsabar yanda ƙafafunta kansu sukai mata tsami, sai da ya dinga lallaɓata sannan tai dauriya da ƙyar, lokacin da take kaiwa ruku'u da sujida yana jin yanda kukanta ke ƙara ƙarfi alamar a wahalce take, zaman tahiya kam ta kasa zama da ƙyau. Duk sai hankalinsa ya ƙara tashi, dan ya fahimci lallai akwai matsala. Tana yin sallama ta zame kwance tana rusar kuka da kiran Ummu ta zo ta taimaketa. A gabanta yazo ya durƙuso tare da kamota jikinsa, yanda ya motsatan yasa ta ƙanƙamesa sosai. “Please stop crying babie”. Ya faɗa da wata irin murya mai tsananin sanyi da taushi yana rungumeta da ƙyau idanunsa a lumshe. Duk yanda taso tsaida kukan ta kasa, dan ciwo takeji sosai a jikinta. Ga kanta na mata wani irin ciwo mai azaba shima. Ga zazzaɓi mai zafi sosai. Gaba ɗaya ta birkice kamar ba Iffah'r Babiy mai shegen tsiwar nan da tsaurin ido ba. Dama irinsu bakin ne kawai ba iya jurar wahala sukai ba (lols😆). Bawan ALLAH Shahan-shan gaba ɗaya ta susutashi ya daina gane komai, yanda take kukan jinsa yake har tsakkiyar zuciyarsa dan shi mutum ne mai tausayi tun da can ma. Amma akan fuskar babu alamar wani abu kamancin hakan tattare da shi, yayi masifar dakewa kamar komai ma bai faru ba. Ɗagata yay daga wajen ya kaita saman kujera dan gadon gaba ɗaya ya ɓaci gashi farin bedsheet. Rirriƙesa tai da sauri alamar bazata iya zaman ba, dole ya ɗan kai gaban kujerar durƙushe yana riƙe da ita. “Faɗamin minene ke damunki?”. Yanda ya zuba mata fitinannun idanunsa ba shiri ta shiga ƙoƙarin ganin ta haɗiye kukan, da ƙyar ta iya furta, “Zafi yake wajen, zafi mai azaba kamar sanda k.......” sai kuma ta kasa ƙara sawa ta fashe da kuka. “Stop crying please, bara na duba naga ko kinji ciwo ne”. Da sauri-sauri ta shiga girgiza masa kai tana matse jikinta waje guda da faɗin, “Ni bazaka gammun ba, ka kiramin Ummuna”. Hannunsa ya ɗan kai bisa goshinsa ya murza. Sai kuma ya sake ɗago kan a hankali, har yanzu durƙushe yake gabanta tamkar ba Shahan-shan ba. Cikin ƙara tausasa murya da shima har yanzu bata gama dai-daita ba ya kai hannu saman fuskarta ya tallafo da duk hannayensa, babban yatsansa yasa yana share mata hawaye. “Kiyi haƙuri, ki zaɓi wanda zan kira miki bayan Ummu, dan ko tana a ƙasar nan bazan iya haka gareta ba, bazan so ta ganki a haka ba. Faɗamin wa kike so na kira miki bayan ita? Ammie, Jaddah, ko Mammy, ko Aunty Jasrah? Ko na baki wayar ki zaɓa wanda kike so yazo?”. Kanta ta ɗaga masa hawayen na cigaba da kwaranyowa. “Okay tom bar kukan, Ni bana son ganin hawaye nan suna sake raunani, rauni na kuma yana nufin sake maimaita abinda nai a daren jiya ko kina so a ƙara?..” Har zabura take tana girgiza masa kai wani sabon kuka na taso mata, amma sai tai saurin danne bakinta da hannayenta duka biyu tana ƙoƙarin haɗiyewa. Tausayi ta bashi da dariya, amma sai ya dake abinsa yana yi a cikin rai. Dan da gaske badan kar ya kashe musu yarinya ba babu abinda zai hanashi sake kai mata ziyara. Shi kaɗai yasan mi yake yaƙin dannewa da ga safiya zuwa yanzu, kawai dai abar kaza cikin gashinta. Ɗan kwantar da ita yay da ga zaman karkacewar da tayi, ya miƙe ya ɗauko ɗaya da ga cikin wayoyinsa. Gabanta ya sake zuwa ya dirƙusa ɗin dai maimakon zama da ya saba yi, ita inba a gaban UBANGIJINSA ba yayin bauta masa bata taɓa ganinsa durƙushe haka gaban wani ba. Duk da bawai yayi wani durƙuso bane na ƙasƙanci. Hasalima yanda yay ɗin sai ya ƙawatar irin masoyi a gaban masoyiyyarsa ɗin nan da suke cikin tsananin shauƙi ma juna. Contact ɗinsa ya shiga sannan ya miƙa mata wayar. Karɓa tai tana sake kumbura fuskar nan da tai jazur duk a suntume musamman idanunta. Kalmarsa ta zai ƙara ne ya sata danne hawayen tilas badan ta gaji da kukan ba. Number Mammy ta lalubo, taja wasu sakkani kamar mai tunani ko tsoron kiran sannan tai dialing. Bugu biyu zuwa na uku kuwa aka ɗaga. Da sauri ta rumtse idanunta hawayen da take riƙewa na ɓulɓulowa. Da ga can jin anyi shiru Malikat Haseenat da ta ɗauka wayar kasancewar Daneen Ammarah ta shiga wajenta sanar mata Malikat Bushirat babu lafiya tace ta haɗa mata ruwan wanka shine ta bar wayar gefenta, ita kuma ganin number Tajwar Eshaan yasa ta ɗauka da tunanin ko shima zancen Malikat Bushirat ɗin ne. Amma sai kuma taji anyi shiru ga kuma kamar ana jan ajiyar zuciyar kuka da ake ƙoƙarin dannewa yana son fita. “Assalamu alaikum”. Ta faɗa a nutse cike da dattakonta. Kamar an ƙwalama Iffah farantin silver saman kai da sauri ta ɗauke wayar a kunnenta ta miƙa masa kukan da take dannewa na kufce mata. Bashi da zaɓin amsar wayar shi ya kai nasa kunnen, tunda har aka riga aka ɗaga bashi da hurumin cewa zai yanke sai ya sakata a tashin hankali. Wayar ya kai kunnensa yana mikewa da yin sallama cikin sassanyar muryar nan tasa mai cike da nutsuwa da kame kai. Malikat Haseenat ta lumshe idanu da sakin ajiyar zuciya ta amsa masa. Cikin mamaki yace, “Jaddah ke ce? Ina Mammyn?”. “Tana haɗamin ruwan wanka ne. Ina fatan lafiya dai ko naji kamar ana kuka da farko?”. Ji yay duk yama kasa cewa komai, a karo na farko na rayuwarsa yaji yana jin nauyin kakar tasa. Amma sai ya daure da ƙyar acan ƙasan maƙoshi ya furta, “Fhareedah ce Jaddah. Dama muna buƙatar Mammyn ne anan”. Malikat Haseenat tsohuwar ƙwarai mai ran ƙarfe da cikar kamala. Sai kawai ta saki murmushi batare da ta nuna ma ta fahimcesa ba tace, “Oh to bara ta fito sai a sanar mata”. “Uhum”. Ya faɗa ciki-ciki. Bata sake cewa komai ba itama ta yanke wayar... Nannauyan numfashi ya sauke yana ɗan murza goshinsa. Sai kuma ya kalli Iffah da ta rufe idanu hawaye na cigaba da tsiyaya. Shi kam yama rasa gane kan wannan kuka, amma ya fahimci harda shagwaɓa da ragwantakar tsiya sai shegen tsiwa bakinta babu mai iya kadata a zance. Amma gashi a ɗan tabatan da yay da bai wuce ko ƙwayar zarra da ga abinda ke tattare da shi ba ya sauke take wannan rakin. Lallai ashe akwai aiki gabansa dan ba'a fara komai ba wannan sharar gona ce. (🚴🚴Taɓɗi). Tashi yay ya yaye bedsheet ɗin gadon dan yayi ma kansa alkawarin gyara sirrinsa da kansa. Gudun karma ya barsu a gani closed dinsa ya wuce da su ya adana. Sai kuma yama ga su bar ɗakin kawai, dan haka ya zo ya ɗauketa zuwa ɗakin kusa da wannan ɗin ya rufe wannan...
Cikin abinda baifi mintuna goma ba sai ga kira da ga amintaccensa. Bayan gaisuwa da yay masa cike da tsantsar girmamawa ya nema wa su Daneen Ammarah iso. Duk da yaji mamakin jin kamar su biyu ake nufi kai tsaye ya bada umarnin ya shigo da su room 3. Karo na farko kenan bayan ita da ke matsayin matarsa da wani zai shigo jerin bedrooms ɗin sa na saman nan gaba ɗaya. Dan ko su matansa da duk aka kawo nan suka rasa ransu a hawa na huɗu ake ajiyesu. Iffah ce ta farko da ta taɓa hawowa hawan ƙarshen nan. Ba shi kawai ba, hatta da Iffah da tayo gayyar sai da ta daburce da jin sautin muryar Malikat Haseenat na sallama. Amma jarumin naku sai yay ɗam da fuska daɗa duniya bai aikata komai ba babu alamar ko gezau tattare da shi. Sai dai kasancewar sa mutum mai tsananin kunya sai ya kasa yarda ya haɗa ido da Malikat Haseenat ɗin. Dan ita kaɗai ta shigo Daneen Ammarah na falo ta kasa shigowa. Bata san dalili ba kawai taji bazata iya ba, dan zuwan ma sai da Mammah ta tilasta mata harma yanda ta nuna ya bama Malikat Haseenat ɗin mamaki matuƙa dan kunya ce a bayyane kamar wadda zatai gamo da surukinta. A hankali ta cigaba da gara kekenta cikin ɗakin idanunta na yawo kan Tajwar Eshaan da tun kallo guda da yay mata bai sake ba da Iffah da ke duƙunƙune a gado cikin bargon da ta sashi ya lulluɓa mata saboda rawar sanyi da takeyi. A gaban Iffahn ta dakata, a hankali cikin dattakonta da ƙasaita ta kira sunanta da kai hannu ta janye bargon data lulluɓe har kanta da shi. Ɗan zabura Iffah tayi, sai kuma tai saurin maida kanta tana hawaye. Tausayi yarinyar ta bata, dan duk wanda ya kalleta yasan tana cikin wani halli. Batace komai ba ta juya kallonta ga Tajwar Eshaan da ke ɗan satar kallonsu... “Barka da safiya Jaddah”. Ya faɗa a taƙaice yana wani ƙara fuskewa abinsa. Itama sai tai kamar bata fahimci komai ba ta ce, “Barkan ka dai. Mike damunta haka jikinta zafi zau ga fuska duk ta kumbura idanu sun ɗashe yarinya duk ta fita a hayyacinta”. Wayyo shikam ina ƙasa ya ɓuya ciki ko zai kuɓuta da ga bata amsar da bai ma san ta ina zai fara ba. Amma sai ya dake yana ƙara ɗan kauda kai gefe tsahon sakkani kamar bazaice komai ba. Sai kuma ya motsa lips a hankali a gaɓar da ma ta gama fidda rai da samun amsa. “Ta girma ne”. Kallonsa kawai Malikat Haseenat keyi, da jinjina murɗaɗɗen hali irin nashi mai cike da shegen miskilancin tsiya. Sai kuma ta janye a hankali ta maida kan Iffah dake raira kuka a hankali. “Niger (Sweetheart)” ta kirata a hankali. Da ƙyar Iffah ta iya amsa mata murya a ɗashe. “Daure ki tashi zaune muga”. Kwatanta tashin tai har sau biyu amma ta kasa, sai ma wani wahallen kuka da take saki saboda yanda zafi mai azaba ke ratsata. Ta shiga jujjuya kai da faɗin, “Jaddah bazan iya ba. Zafi kamar zan mutu”. Idanu ya lumshe a hankali. Ji yake kukanta na wani irin sukar masa zuciya. Itama kanta malikat Haseenat ɗin wani irin tausayin Iffah'r ne ke ratsata. Ita tasan ba lalaci bane ko raki kawai. Dan zuri'ar su Tajwar Eshaan ɗin fitinannun mutane ne da indai mace taje hannunsu basa iya mata ta sauƙi. Shiyyasa mafi yawansu basa iya zama da mace ɗaya, sannan suna aure da wuri gudun faɗawa halakar zina duk da akwai bijirarru a cikinsu da kan ringa aikatawar. Amma ita a karan kanta ta daɗe tana mamaki akan Tajwar Eshaan da ya nuna baya buƙatar aure tun a shekaru fara girmansa, hakama yanda ya kai har shekarun da aka masa auren fari na sata jin waswasin ko yana neman matan banza ne ko baida isasshen lafiya. Dan tasan duk wanda ya kasance jinin zuri'ar wannan daula baya iya kauda kai ga mace irin hakan da ya nuna shi.........✍️
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 96 09 67 63
Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (46)