Kenza eBookz

Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul - Chapter 51

Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul - Chapter 51

Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 51: Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 51. "Mammah wai yau ma zakije zaman kotun nan kema? Naga…

4,490 words

"Mammah wai yau ma zakije zaman kotun nan kema? Naga kamar kina jin kafar nan sosai fa?".

Dan murmushin karfin hali Malikat Haseenat ta saki idonta akan Daneen Ammarah mai maganar. "Karki damu ai bawani ciwo take mai yawa ba. Ke dai yi sauri ki bani kunun nan nasha, kin sanshi dan ka'ida ne akan bin lokaci".

Yar dariya Daneen Ammarah tayi kawai, Da ganta itama zaka fahimci tana cikin farin ciki. Daga ita har Malikat Haseenat din tun jiya fuskokinsu sun kasa daina murmushi, da dare kam zama sukai suka ding hirar Iffah. Su kansu sun kasa gane ta yanda akai yarinyar ta shiga ransu matuka har haka, kuma take ma kara shiga a kullum musamman ma ita Daneen Ammarah din da kwanakin nan taketa mafarkai da ta kasa gane kansu……………✍️

DAUDAR GORA

Book two( 53)

Wata shegiyar dariya ya saki idanunsa kan takardar da aka aiko masa ta sake zaman shari'ar yau. Ya kai hannu ya yarce ruwan wankan dake kan goshinsa zuwa fuska. Tun safiyar jiya basa gidan shi da Miran Jasim. Sai yau ne shi yake dawowa Miran Jasim kuma da daddare.

Wayar landline dake gefe gadonsa ya dauka,yay yan danne-danne yana da ga tsayen da yake. Ana dauka ya kwashe da dariya, sai kuma ya kai zaune a bakin gado. "Yaya dai kawun mai sharia kaima an kawo maka takardar ne?".

Wani irin shegen tsaki Miran Jasim yaja da ga can. Ya ce, "Bar wawa dan wahala mana. Shifa gani yake kamar ya wani kai anan. Muje zuwa idan ya isa sake zaman wata shari'ar da ga wannan. Zamuyi maganinsa ne shida shegiyar yarinyar nan mai bakin akkunaye".

Sake kwashewa da dariya Miran Arshaan yayi, tare da fadin, "Ai boka dan gurguzu yayi,tunda muka fita muka dawo masarautar nan babu wani shege da yay magana shima bai isa yinta ba yau".

Dariya suka kwashe da ita a tare kamar wasu mahaukata...

_Tofa, mi Fir 'auna da hamana suka shiryo ne haka🥱😂🚴🚴🚴🚴

Yau kam a tare suka fito zuwa dining room. Amintaccensa ya zube kansa a kasa yana gaishesu cike da girmama. Iffah ce kawai ta amsa masa cikin kulawa. Gogan nata kam lips kawai ya motsa ya wuce abinsa. Da kansa ya ja mata kujera, itama sai ta ja masa tana kallonsa da murmushi. Shi dai bai murmushin ba, amma ya juya idanu cike da salon birgewa. Koda amintaccensa ya taso domin hada masa abinci kamar yanda ya saba dakatar da shi tai. Sai ma ta sallamesa akan yaje idan sun kammala sai ya dawo.

Sai da ta gama bubbude duk kwanikan wajen sannan ta kallesa alamar mi yake so? Kaifafan idanun nan nasa ya zuba mata, sai kuma ya daga yatsarsa manuniya a hankali ya nuna ta.Baki ta tura gaba tana wani kyaf-kyaf da idanu."Ni abinci nace fa". Yanda tai din sai ya bashi dariya. Amma sai ya gimtse abarsa ya dauke kai Itama sai ta tabe baki ta dauke nata kan dan ta fahimci yau kuma yan mislinacin ne da mulki a kansa. Zabar abinda taji tana so a ranta tai kawai ta zuba musu ta ajiye komai gabansa da fadin bismillah. Abincin kawai ya zubama ido yana jinsa wani daban yau din. A da sai daiamintaccensa ya hada masa, yau kuma gashimatarsa ce, abinda ya jima yana mafarki. Rayuwa kenan mai farko da karshe.

A nutse suka fara cin abincin, Iffah na satar kallonsa da jinjina mulki da kasaita. Yanda yake cin abincin ma kansa abin birgewa ne. Suna gab da kammalawa kanta yay wani irin sara mata. Da sauri ta kai hannu ta dafe tana ambaton sunan ALLAH. Kallonta yay shima da mamaki, sai kuma ya riko hanunta da ta dafe kan da shi. Dago idanunta da sukai wani irin jajaja cikin kankanin lokaci tai ta kallesa. Shi har sai da ma yaji tsigar jikinsa ya tashi, amma sai ya dake kasancewar shima akwai nasa abebadan a kansa. Da ido ya mata alamar minene? Dan da gaske yau miskilancin ne a kusa. Ji yake motsa lips din ma yay magana babban aiki ne.

A hankali ta furta, "Kaina ke dan mun ciwo

Tun yaushe?".

Ya fada a fusge. "Da safen nan ne fa. Amma ba wani ya matsa bane karka damu. Dan ALLAH ka barni na fara tafiya kotun nan sai kai kuma ka taho da ga baya".

Idanu kawai ya tsira mata. Ita kuma ta langabe kai gefe alamar roko. Dauke idonsa yay kawai da ga kanta batare da ya ce komai ba. Ya lima yana zargin akwai junnu a jikin yarinyar nan, yanzun ma kuma abinda yake zargin kenan. (Ya arrahaman, komai na yarinyar nan sake sakashi a rudani yake). Sai kuma maganar data fada masan yanzu ta shiga masa kaikawo a rai. Ya barta ta fara yin gaba kafin shi na nufin akwai wani abu kenan. Shikam yaga takansa da wadan nan ahali nashi. Wani abu kenan wani ya sake masa ko kuma dai aljanun nata ne ke neman raina masa hankali. Cikin rashin bama abin muhimmanci ya cigaba da cin abincinsa, sai dai kuma abinda ta fada kuma ya faru a wacan ranar na masa kaikawo. Iffah dake binsa da kallo kamar zatai magana sai kuma ta hadiye kayarta tana sakin nannauyar ajiyar zuciya da jan jikinta baya.

Komai baice mata ba, sai da yaga ta mike. A can kasan makoshi ya furta "Ina zuwa?".

Agogo ta nuna masa. Kallon agogon yay ya dauke ido. Batare da ya sake kallonta ba ya ce ,Kina bukatar masu rakkiya ne?".

"A'a".

Ta bashi amsa a takaice.

'"Amma kin san bazai yuwu kije ke kadai ba. Kije akwai masu jiranki a can kasa".

"Nagode".

Da kallo kawai ya bita ganin yanda ta sauya lokaci guda. Ga fuska ta wani daure tamau babu alamar wasa. Shi sai ma ya fara jin ko dai itace aljanar da kanta.

*Yau kam da alama shari'ar zatai zafi. Dan kotun tacika fie da zaton mai hasashe. Abinda Kuma zai birgeka duk ahalin masarautar ne.Cikin wani irin takun kasaita da izza da ya jawo hankalin duk wanda ke cikin kotun Iffah ta shigo da shi. Ga hadimai na take mata baya. Tayi matukar kyau cikin shigar jikinta, ga wani irin kyawu da fuskarta ta kara sai shining takeyi fiye da hasken tauraruwa zarah. A zahiri ita tafiyarta takeyi normal, amma ga masu kallonta babu abinda suke gani tattare da ita sai tsantsar izza mai ban mamaki. Wani abin birgewa da tai ya kayatar da was a wajen shine kai tsaye inda Malikat Haseenat take ta nufa. Takai kasa cike 17:42 yanzu bayan Tajwar Eshaan da Malikat haseenat sama da ita a duniya.

Shigowar mai gayya mai aiki tasa tunaninsa katsewa…. a take kotun tai tsitt kowa ya mike domin girmamawa. Taku yake cikin tsantsar kasaita da izza data zame masa jinin jiki. Ga wani irin kamshinsa mai kada zuciyar mai shaka na tashi. Yammatan wajen da suka dade da folawa a sonsa tuni zukatansu suka shigar narkewa, duk da babu abinda ake gani bayyane a fuskarsa. Dan ya sakayata hatta da idanunsa saye suke cikin eyeglasses dake nuna blue daga waje. Addu'ar neman tsarin ALLAH da ga duk wani abin cutarwa ya karanto lokacin da yake kaiwa zaune a hadaddiyar kujerar da ke a mallakin zamansa. Ya dan saci kallon sashin da yake tunanin ganinta. Tana a wajen kuwa, sai dai abin mamaki ita sam bama shi din take kallo ba.Ajiyar zuciya ya dan sauke a hankali wadda ko amintaccensa da ke gefensa da masu tsaro guda hudu haggu da damansa basu isa ji ba.

Bayan an tabbatar da kowa ya natsa Sayeed Hanifud-Din ya mike ya dubi jama'a. "Alhamdullahi muna godiya ga ALLAH da ya sake dawo damu zama na uku akan wannan shari'a. A zaman daya gabata wadda ake kara ta amsa laifinta, sai dai ta Bama wannan kotu mai adalci damar bincike mai zurfi akan tushen shugaba na wanna daula. Inda wannan kotu mai adalci ta amshi korafinta har ta bada dama ga masu bincike. Matsala ta ratsa ta yunkurin son halaka Zawjata-almilk da akai, inda dalilin haka aka samu tazarar daga wanna zama har sai da ta samu lafiya. To yanzu dai alhmallh, wanna zama a wanna gabar duka zai ta'allaka ne ga jin bayani da ga bakin shugaban jami'ai da aka danka wanna bincike garesa. Shugaban jami'ai bismillah".

Sai da ya mika gaisuwa ga Shahan-shan cike da girmamawa kafin ya juya ga jama'a. "Assalamu alaikum kamar yanda aka bamu damar bincike a gaban wannan kotu mai adalci mun gudanar. Mun bibiyi tushen samuwar madara da kaita sashen Zawjata-almilk. Inda bincikenmu kuma ya kaimu har ga wanda ya shigo da wannan madara mai dauke da dafin macizai a ciki. Karna cikaku da surutu waka bakin mai ita tafi dadi. Ina rokon alfarmar wannan kotu da ta bani damar gabatar da Dafiq in Ghalib a gabanta".

"An baka".

Cewar Sayeed Hanifud-Din.

Kallon juna Miran Arshaan da Miran Jasim sukai suka saki murmushi. Sai kuma sukai saurin duban wanda jami'ai ke kokarin shigowa dashi kirazansu na wani irin mummunan harbawa.Kokarin mikewa Miran Arshaan yay da sauri Miran Jasim ya danne masa hannu jikinsa na rawa. Iffah da ke kallonsu ta saki murmushi,cikin Sa'a kuwa suka hada do da Miran Jasim.Ido daya ta kashe masa da dauke kanta tana dan wani cizar lips cike da salo.

Dattijo da jami 'ai suka shigo da shi bazai wuce shekaru hamsin da takwas a duniya ba. Cikin nutsuwa ya gurfana gaban Shahan-shan yay gaisuwa, bai o motsa ba da ga zaman kasaitarsa. Dattijo Dafiq in Ghalib ya gyara tsaiwarsa yana fuskantar kotu. Dubansa Sayeed Hanifud-Din yayi ya ce, "Dattijo waye kai?".Cikin dan rawar harshe ya ce, "Dafiq ibn Ghalib. Ni masanine akan macizai. Ina zaune a kauyen Bansh". "Miye alakarka da daular ruman?".

"Alakata da Daula ruman alakace irin ta kowanne dan kasa. Wato fadan shugaban kasata adali".

"Amma duk da haka ka iya bada dafin macizan da za'a cutar da shi?"

"Ko kusa ba haka bane, ko wani naga zai cutar da hadimin wannan daula bama shugabana ba sai inda karfina ya kare ai. Ni dai a ranar daren wata laraba wani bawan ALLAH ya sameni akan shi din jami'in ne na hukumar bincike akan sanin nau'in dabbobi masu dafi.Yazo kuma wajena ne da bukatar samun kalolin dafin macizai zaiyi bincike a kansu. Da farko naso naki, dan nasan dan adam na wannan duniyar ba abin yarda bane. Amma sai ya nuna min katin shaidar aikinsa. Hakan yasa na yarda da shi na dauka na bashi"……….✍️

DAUDAR GORA

Book2 (54)

......."Ko zaka iya gane mutum idan ka sakeganinsa".

"Sosai ma kuwa. Dan akwai ma cctv footage na abinda duk ya faru a tsakaninmu batare da shi ya san inada camara a wajen ba." ya kare maganar yana duban shugaban jami'ai. Ya fahimci mi yake nufi, dan haka ya mike ya mikawa Sayeed Hanifud-Din flash da ke a hannunsa, anan take kuwa aka saka flash jikin lap-top aka kai gaban Tajwar Eshaan, sai ko ga duk abinda ya fada din dalla-dalla.

An shigo da wanda ya amso dafin macizan, wanda ya kasance amintaccen hadimi ne ga Miran Jasim, kowa ya sani kuma a masarautar nan, dan tun yana a matashin saurayi ma yake tare da hadimin, shine ke masa duk wasu ayyuka na sirrinsa dama na mugunta. Ai Miran Jasim baima san yay wata iriyar zaburar tashin hankali ba jikinsa na kakkarwa. Yayinda gaba daya kotun ta dauka yan kananan magana har sai da aka tsawatar. Sayeed Hanifud-Din da shima dai gaba daya jikinsa yay sanyi da al'amarin ganin daga inda ya fito, dan koba'a fada ba komai a bayyane yake. Fuskantar hadimin da gaba daya ya fita hayyacinsa a hannun jami'ai yay. " "Bama bukatar wani kwana ja da ga gareka ko ja' in ja, fadar gaskiyarka na nufin zaka iya samun sassauci, zabar yin taurin kai kuwa ya rage naka. WANENE YA SAKA?". A hankali hadimin ya dago ya dan dubi inda su Miran Jasim suke, idanu suka hada da Miran Arshaan da yake masa kallon kasa-kasa yana wani dan motsa yatsunsa. Ajiyar zuciya ya ja a hankali, kafin ya maida dubansa ga Sayeed Hanifud-Din. Kai tsaye babu wata kwana-kwana ya ce, "Shugabana Miran Jasim ne ya sakani

A take kotun ta dauki wani irin hun karajin Miran Jasim da ya zaburo kan hadimin nasa, sai da jami'ai suka rirrikesa. Yayinda jama'a suka hau salati suma har sai da aka tsawatar. Hadimin ya cigaba da fadin, "Sai dai ni ban san mizaiyi da ita ba, amma a gabana ya zubashi a cikin madara ya bani madarar yace na kai sashen Zawjata-almilk nace daga sashen uwar masu gida. Bani da ikon cemasa a'a, amma navi niyyar kin kaiwa sai dai nasan zai iya sawa a bibiyeni idan nai hakan zai halakani kuma, dan haka na cika umarninsa amma ni duk tunanina ma Zawjata-almilk din zai ba. A ranar nata kokarin ganin samun ganawa da ko amintaccen adalin shugabanmu ne amma hakan bai faruba,da ga karshe ma sai naji wai ashe shine za'a bama madarar ta hanyar Zawjata-almilk ba kamar yanda nai tunanin itace zai bamawa din ba. Kuma zan fadi gaskiya, ba laifin Zawjata-almilk bane ba asiri yay mata kan duk yanda yaso haka zaiyi da ita, daga baya itama zai kasheta.

Duk yanda akaso samun nutsuwar kotun kam hakan ta gagara. Salati kawai kake ji da la'antar Miran Jasim da akeyi. Iffah ta saki wani irin shegen murmushi tana mai kallon Miran Jasim da yay sumar tsaye. Sai kuma ta maida kan Miran Arshaan da gaba daya yay sharkaf da zufa. Wata dariya ta kyalkyale da shi a zuciyarta tana fain (tun banzo kanka ba) a zahiri kam baka isa fassara yanayinta ba.

A bangaren Miran Arshaan kam ya dauka makircinsa ne yay tasiri kan Miran Jasim. Dan kuwa hasalima shiya tura hadimin ya shiga jikinsa duk tsawon wanna shekarun da suke a tare, dan kawai ya san duk wani motsinsa Abinda bai sani ba a yanzu hadimin ba aikinsa yake ba aikin Iffah yake yi, ita kuma ta zabi tattara laifin ga Miran Jasim a karan kanta saboda haka ta tsara binsu daddaya, shi kuma zata cigaba da jansa a kasa har zuwa gabar da take so..

Wata irin daddagewa da fashewa da kuka da Miran Arshaan yay ne ya katse mata tunaninta. Ta zubama drama din tasa ido dan ya wani daddagene ya fashe da kuka yana duban Miran Jasim kai kace dada duniya har zuciyarsa ne. "Jasim! Jasim Akhi mu zakama haka? Kai da kanka zakaci amanar dan uwanmu ka zama jagoran shirya halakashi. Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un.…. Mi kake bukata ne? Miye dan uwanmu bai mana na gata ba a wannan duniyar? Ya rikemu tamkar yanda Abie (Tajwar Abdul-majeed) zai rikemu, amma mu mu kasa rike jininsa daya tilo a duniya da bashi goyon bayan mulkin da ALLAH ya daura masa. Dama na jima ina zargin kana kwadayin mulkin nan ne,ban tabbatar da hakan ba sai randa aka samu kayan tsafin daka saka a kujerar da adalin shugabanmu yake zama, kaki zuwa kuma wajen meeting da ga karshe ma bakin cikin an ganoka ka nema halaka iyalinka" ya sake fashewa da kuka.

Wata irin mahaukaciyar shaka Miran Jasim da jikinsa ya hau kakkarwa ya kaima Miran Arshaan da kyar kuwa aka bangaresa yana fadin sai ya kashe Miran Arshaan din.

Duk da wannan dambarwa mai gayya mai aiki Shahan-shan na zaune ne yana binsu da kallo ta cikin gilashinsa. Shi kansa a wannan gabar sai ya shiga dan rudani, dan a iya bibiyar rayuwar uncle's din nasa da yake yi tun lokacin da ya fara zarginsu a tare suke aikata komai sai dai a sirrance ne kam. Kuma ita kanta Iffah ta sanar masa su biyu ne ai, amma yaya akai hakan ta kasance komai ya juye kan Miran Jasim shi kadai.

Tamkar Sayeed Hanifud-Din kam yasan mike ransa ya ambato sunanta. "Ko Zawiata-almilk nada wani karin bayani akan alakarta da Miran Jasim da har hakan ta kasance tsakaninsu?".

Shiru kamar Iffah bazata motsa ba, sai kuma ta yunkura da kyar fuskarta jage-jage da hawaye. Handkherciff din da Malikat Haseenat ke miko mata ta amsa ta goge fuskar sannan ta fuskanci kotu bayan ta saci kallon Tajwar Eshaan da takeji a jikinta kallonta yake, dan tun dazun takejin kaifafan idanunsa a kanta. Hakama Malikat Bushirat kallonta takeyi. A nutse cikin nuna rauni ta ce, "Ni ban san mizan ce ba, amma abinda na sani kawai bani da wata alaka da shi nikam, hasalima ban sanshi ba a zahirance sai a randa aka nunani gaban dai iyayen wanna gida mai albarka. Kuma ko'a ranar bazan iya cewa ga kamaninsa ba. Sai a randa Zawjata-almilk farko ta rasa ranta ne dai-dai da rasuwa sayeed Khairul-Bashar na nufi sashen mai girma Shahan-shan hankali tashe dan ina son tabbatar da abinda al'umma keta fade akan shine ke kashe matansa. Ina tsaka da dube-dubena akan gawar suka shigo tare da shugaban jami'ai, Ni kuma sai naji tsoro na buya, bayan an fita da gawar ashe shi ya ganni shine ya dawo da baya. Na tsorata amma sai ya ce na nutsu muyi magana, zai rufamin asiri amma yana so muyi aiki tare. Ya dan mun maganganu dai da yawa. A ranar ya kawo min maganganu masu rudarwa, mafi girma a cikinsu nunamin video cewar adalin shugabanmu ne ya halakamin iyayena da tsafin maciji kamar yanda naga alamar saran maciji a jikin Zawjata-almilk da ta rasu, ya kuma sanar min nima na tsira zanyi ba dan haka nima nayi takaina. Nazo mu hada hannu mu yakesa dan baza'a hukuntashi ba. Ni a lokacin maimakon cemasa wani abu ma rudani na shiga da tashin hankali akan iyayena,dan haka bamma gama saurarensa ba, ganin bana a hayyacina ya tashi ya fita. Sai kuma A ranar 9 ga watan 2 dai nanma na samu kiransa misalin karfe takwas a dare. Nayi matukar mamakin hakan, dan bai boyemun ba ya sanar min aiki fa yake son miyi tare kamar yanda ya a waccan ranar amma zai sanar min abu. Ban katsesa ba nace ina saurarensa.Yasanar min magana bazata yiwu ta wayar landline ba, amma ga number dinsa na kirashi direct video call. Har lokacin ban kawo komai a raina ba, duk da dai inajin toro ganin shiga uncle dinsa ne, idan na fadama wani bama za'a yarda dani ba. Dan haka nabi umarninsa na kira din dan bangama sanin yanda akeyi anan din ba. Tun daga wannan ranar ban sake fahimtar komai ba da ga yanda yake bibiyata sai da nakai madara ga adalin shugaban wannan kasa ya sha. Daga nan na fara fahimtar makirci ne musamman yanda ya dage akan sai an kaini kurkuku. Bayan an kainin kuma ya bini har can yana fadamin maganganun banza harda na rashin da'a". Ta fashe da kuka mai cin rai, wanda a yanzu kam da gaske kukan take, dan kalmar KARUWA da Miran Jasim ya ce zai maidata na mata radadi har yanzu a cikin rai.

Dolene yanda Iffah ke bayanin yasa kaji hawaye yazo maka, kuma ko kai waye sai kaji ka yarda da ita. A nan din ma fa rudewa kotun ta sake yi, yayinda Miran Jasim ke hargowar sai ya batar da ita, sai ya shafe babin rayuwarta baki daya ita da Miran Arshaan da sukaci amanarsa. Babuma wanda ke saurarensa sai ALLAH wadai da ake jifansa da shi da tausayin Iffah da gaba daya yau kowa ya fahimci an mata makirçin ashe ,Dama can wasu da yawa tunma a ranar data aikata suke fadin bayin kanta bane, tayi kankanta da aikata laifin ita daya. To sai gashi yau kam komai ya fito filin ALLAH. Kotun tai bala'"in daukar turiri har sai da Tajwar Eshaan da kansa ya tsawatar. Dan danan kowa ya nutsu kotun tai tsitt. Ya dauka tsahon mintuna uku babu alamar zai ce wani abu, kafin ya nisa da kyar cikin maganar nan tasa a fuse kamar wanda akaima dole. Da kyar ya iya danne zafi da radadin da zuciyarsa ke masa kanjin wai uncle dinsa yama matarsa magana ta rashin da'a,amma ta boye masa.

"Alamu da kalaman Jasim in Abdul-majeed Aliy Qutb sun tabbatar da duk abinda aka sanar anan game da shi ya aikata. Sai dai duk da haka wannan kotu mai adalci zata bashi damar sanar damu dalilinsa na aikata duk wannan a zama na gaba. Za'a tsaresa a kurkukun da Zawjata-almilk tai rayuwa har zuwa ranar da kotu zata sake bukatar ganinsa a gabanta. Wannan kotu kuma ta wanke Zawjata-almilk da ga zargi, tare da bada damar kawo bokan da yay sihirin gaban shari'a shima. Tanada damar shigar da kara itama a karan kanta game da amfani da ita da Jasim yayi. Daga karshe ni Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed Aliy Qutb ina shigar da kara nima bisa yunkurin kashe min MATA da akayi har karo biyu ta hanyar yimata allurar guda da jefata cikin ruwa..." da ga haka ya mike anutse cike da salon nan nasa yayinda ya bar jama'ar kotu gaba daya a yanayin mutuwar zuune da kalamansa na karshe. Malikat Haseenat kam murmushi ta saki mai sanyi da kayatarwa, hakama Daneen Ammarah. Yayinda zuciyar Malikat Bushirat ke bugawa da wani irin sauri-sauri a cikin kirjinta dake yin kamar zai bude.

A bangaren Iffah kam idonta akan Miran Jasim ne, a cikin iska ta rubuta *_FINAL_* da yin alamar yanka wuya ta kashe masa ido daya…….✍️

_Mai RUMAN sai kayi takanka kaima to, dan da gaske Iffah kaza zata koma uwar tone-tone🥱_

17:14 DAUDAR GORA.. Book2 (pg55) Il A ..Wani irin fadawa tai saman gado cike da farin ciki tana sakin siririyar dariya. Babu abinda take hangowa sai idanun Miran Jasim da na Malikat Bushirat harma da Miran Arshaan. Tai wani irin juya ta sake juyawa a gadon sai kace tarwada. "Kina lokacinki Fhareedah bint Zayyan". Ta fada a fili tana sake kyalkyalewa da dariyarta kai kace an mata albishir ne da dawowar su Baby kasar ruman. Yanda take ji kam kamar ta tashi tayita taka rawa. Daya da ga cikin burikanta ya cika, ya cika a gabar da ALLAH ya bata abinda baya cikin lissafinta. Tabbas zama mallakin Shahan-shan baya cikin lissafinta. Lissafinta na daukar fansa ne kawai,fansar jinin yan uwanta da bazata iya yafewa ba. Sai dai kuma dukkan labarin ya canja, ya canja da canjawar shigowar su Miran Jasim cikin tattakinta batare data tsaro da su ba. Shigowar Tajwar Eshaan in Haysam Abdul-majeed matsayin wani abu mai daraja a ciki labarinta batare da ta rubuto da hakan ba nan ma. "Ya rabba" ta fada a zahiri tana lumshe idanunta da sukai wani tar-tar na haske fuskarta na kara kawatuwa da murmushi mai kayatarwa.

"Miyasa kika boye min?".

Bata fahimci mi yake nufi ba, dan haka ta idanunta da jan cikinsu ke dan raguwa a hankali ta zuba masa. Bazata iya jurar kallonsa cikin ido ba dan haka ta dauke su ta maida gefe. "Ban san akan mi kake magana ba Sultan".

Sai da ya dan furzar da hucin baci ran da yake ta dannewa, a dan fuse ya furta, "Jasim! Miyasa kika boyen ya sameki a kurkuku da maganar banza?"

Shiru kamar bazatace komai ba, sai kuma ta motsa cikin sauke ajiyar zuciya ta ce, "Kayi hakuri, a lokacin ban san ta yanda zan tunkareka ba. Ban kuma san ta yanda zaka fahimceni ba. Kuma ai ALLAH ya kareni da ga sharrinsa tunda ga shi yau gaskiya tayi halinta".

Shiru baice komai ba, dan zuciyarsa tafasar kishi take har yanzu akan wanna kalmar, tafi komai tsaya masa a zuciya fiye da abinda Miran Jasim din ya aikata masa dan ya jima da sanin dama suna farautar rayuwarsa. Sai maganar rashin fitowar sunan Miran Arshaan shima na masa kaikawo, kamar zai mata magana akan hakan sai kuma dai ya hadiye kayansa da tunanin ko Miran Jasim din ne kawai ya fiddo mata da nasa hali. Amma in bai manta ba ranar a kalamanta ta masa nuni ne da mutane biyu ko yace fiye da daya. Hakan na nufin bayan Jasim din akwai wani kenan. To miyasa ta boye? Bashi baice komal ba ya dal cigaba da kallonta. Kusan minti daya sannan ya motsa da cigaba da don takawa a hankali cike da kasaitar nan tasa. gabanta yaja ya tsaya, tare da zare hannunsa dake cikin aljihun wandon jeans dinsa ya mika mata. Idanunta ta dago ta kalli hannun da ke fari tas da shi, ga jini nata kaikawo a tafin kamar ba namiji ba. Idanunsa ya dan lumshe da budewa a lokaci guda yana gyada mata kai alamar ta daura nata. Kamar mai jin tsoron hakan ta dago natan ta dora a cikin nasan. Sake lumshe idanun yayi kamar wani wanda maganadisu ya taba,batare da ya bude ba ya dagota ta mike tsaye itama. Matsota yay kawai jikinsa ya rungumeta tsam-tsam. Sassanyar ajiyar zuciya ta saki nutsuwa na ratsata, sai kawai ta kankamesa itama tare da kwanciya luff a faffadan kirjinsa tana shakar daddadan kamshin turarensa mai saka zuciyar mai shaka nutsuwa

_Oh oh su Iffah an waye an manta da mu dangi

Mammah duniya abin tsoro ce why, duk da mun jima da sanin Jasim baya kaunar Abni sai yau din da komai ya fito fili ya bani mamaki. Har zuciyata iya abinda nake kallonsa da shi shine nuna adawa kawai ga mulkin tunda shine burinsa. Amma why ban taba kawo zai iya shirya halaka rayuwarsa ba haka. Wace irin rayuwa ce wannan wai dan uwanka jininka ya zabi cutar da kai akan abin duniya mai yankewa. Wai ina mahaifinmu da ya zama sanadin kawomu duniyar ma? A da shine a wannan kujerar, amma ya shude kamar ba'ayisa ba, aka daura dan uwanmu, shima ya shude kamar baiyi ba, idan sukai hakuri shima wataran bashi bane anan din. Bazan boye miki ba Mammah,zuciyata ta fara min sake-sake da kokwanto akan rasuwar Haysam Akhi, haka Zawjata-almilk da muka rasa, anya kuwa hakan baida alaka da su Jasim Akhi ya karba makamancin tayin da muka jima da tsigesa a cikin jininmu?. Dan zuciyata ta fara rabuwa biyu bayan zargin mushirakar can data dade da shudewa a tarihinmu kamar akwai wata mai irin al'amuranta a yau zagaye da wani namu". Malikat Haseenat da ke ta faman jinjina kai taja ajiyar zuciya mai karfi tare da fesar da iska zazzafa da ga bakinta. "Tabbas duniya ta cancanci zama abar toro kam Ammarah, nima kuma kamar ke zuciyata ta fara rawa, ta fara rawa da wannan gabar har inajin ni kaina ban yarda da kaina ba. Tabbas mushirikar can ta shude ita da tarihinta, amma sai zuciyata ta gagara nutsuwa da hakan duk da tsahon shekarun nan da suka shude da kasancewarta.Babu abinda Jasim bazai iya aikatawa ba,musamman idan na kalla irin mugun zaman da mukai da mahaifiyarsa a masarautar nan. Dan haka shima kam yanzu abin tuhuma ne. Sai dai akwai wani furuci da yarinyar nan tayi yafa tsaya mun a rai, tun dazun kuma yake mun kai kaWO….

"Wane furuci kenan Mammah?".

"Furucin bibiyar gawar Zawjata-almilk ta karshe da muka rasa, inda ya zama sanadin haduwarta da Jasim. Lallai ina bukatar ganawa da Zawjata-almilk".

Readers Also Read