Kenza eBookz

Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul - Chapter 65

Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul - Chapter 65

Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 65: Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 65. …..……….Bayan dawowar uwa al'amuran mu sun cigaba da…

4,363 words

…..……….Bayan dawowar uwa al'amuran mu sun cigaba da tafiya, dukan shardanta a cigaba da cikasu, dan dama ko bayan batanan ban fasa ba, dan ina tsoron abinda ta fada akan Saiful-malik ya tabbata. Dan wannan tsoron da son cimma buri ne suka jagoranceni har zuwa wannan lokaci. Ni naita zungurar Haysam akan yin murabus lokacin da Saiful- malik ke cika shekara talatin da uku a duniya, nayi hakanne kuma bisa umarnin uwa. A duk sanda nai maganar yakan yi murmushi ne kawai, amma baya cewa dani komai, Sai hakan ke cimun rai da tunanin baya son ya sauka ya daura Eshaan din ne. Ni kuma abinda nake hange adadin shekarun da Uwa ta tabbatar min zai rasa ransa a dalilin shayin da nake shayar da shi gabatowa suke, ta kuma tabbatar min infa ya mutu ba'a daura Saiful-malik a karagar mulki ba akwai rikici sosai, domin Haysam nada kanne, shekarunsu kuma sunfi zama shekarun hankali da yan kasa zasuyi jayayya da samun rabuwar kai akan magajinsa Eshaan. Na sake takura masa da tada hankalina akan hakan har takai wata rana ya furta min abinda ya girgizani. Ya ce (Bushirat basai kinyi gaggawa akan mutuwata ko rayuwata ba. Idan kaddarar mulkar kasar ruman na rubuce a littafin kaddarar Eshaan sai yayi ko ina raye ko bana raye, abinda na sani kawai ina matukar tausaya masa, ina tausaya masa yaki na cikin gida da waje. Yakin da zai masa matukar wahala musamman kasancewarki ke wa mahaifiya da kika zamto a cikin manyan makiyansa) rai bace nace ban gane ina cikin manyan makiyansa ba? Bai sake cemin komi ba, illa murmushi kawai da ya saba mun. Maganar ta zauna min a rai matuka, har ta kaini da fadama uwa. Itama naga alamar ta girgiza, dan haka take anan ta tabbatar min dole muyi motsin da Haysam fa zai bada mulkin nan sannan mu kaudashi, dan alamominsa na nuni da akwai abinda ya sani game da ni, idan kuma har mukai sakaci wahalarmu ta baya zata zama a banza. Babu wani damuwa a raina na bata goyon baya, dan saima tashin hankali da nakeji akan cewar Haysam yasan wani abu game da ni din, ina tsoron ya fadama mahaifinmu, dan wilhy zai iya tsireni ne kawai kasancewarsa mutum mai zafi da bin dokar addini. Haka akai, ta kawo abinda naita saka masa a madara yana sha har tunaninsa ya karkata a yin murabus, babu zato babu tsammani kawai ya dawo da Eshaan gida, ya kuma tabbatar da zai yi murabus ya daurasa a karagar mulkin Shahan-shan. Kalubalen dana so fuskanta shine Eshaan da kansa, dan yaso bijirewa da cewar shifa baya son mulkin nan, bai taba ma birgesa ba, yafi son rayuwar yanci, yayi abinda yake so a lokacin da yake so, a cikin tarin burukan rayuwarsa ma babu maganar mulki a ciki. Na tashi hankalina Uwa tace na kwantar, ta bani wani turare tace na basa kyauta, in har yay amfani da shi na kwana uku sai ya amince. Hakan ce kuwa ta kasance. dan satin bai shigeba sai gashi da cewar ya amince. Uwa ta kara shiga raina da jin bani da kamarta duk duniya, zata kuma iya sakani komai nayi amma banda sadaukar mata da Eshaan, dan shine abinda nafiso fiye da komai a duniya. Anyi nadin sabon Shahan- shan tare da shagalin bikin aurensa na mata hudu, ko sau daya bai tanka akan auren ba, baice bai son su ba bai kuma ce yana so ba. Ni kuma bam ma damu da tambayarsa ba tunda nasan makomarsu. Kamar yanda uwa ta fada Haysam ya shude, matan Eshaan ma daya bayan daya sun zama labari, an cigaba da auro masa was suma tarihinsu na shudewa, a haka har nazo gab da cikar burina na gama wannan sharadin. Rana tsaka, ina gab da cimma abinda na faro kwatsam yarinyar ta shigo rayuwata. Ba kai tsaye ta shigoba, dan bana jin ma ta sanni ita. Yaki ta shirya, ya ki domin yakar Eshaan saboda rasa yayunta biyu da suka shigo cikin aikina. Itama tanada tunani ne irin na sauran mutanen kasar ruman akan Saiful-malik ne ke halaka matansa. Wanna itace mafarin matsala, dan tunkan ta shigo ita nacema uwa ta kauda min ita, dan ina a gabar da zuciyata ta gama dakewa da bushewa zuwa yanzu, hatta hadiman dake mun ayyuka da sunyi kuskure mafita daya nake hangoma kaina shine kawai na kaudasu, idan na kaudasu matsalata ta kare kenan. Da nayi din sai inga ta kare kuma, dan haka nake kallon kashe duk wanda ya shiga gabana akan cikar burina kawai na kauda san Uwa ta tabbatar min babu kaddarar mutuwar yarinyar a wannan tsakanin, sai dai mu nemo wata hanyar, a cikin neman mafitar ne muka yanke zamowarta a daya da ga cikin matansa, domin a ganinmu idan ta matso gab da mu sai munfi cin nasara a kanta. Sai dai kuma al'amarin bai kasance yanda mukai hangesa ba, dan tunda ta shigo rayuwar gidan komai ya daina yiwuwa a cin sauki. Labarin farko ya canja zuwa wanda bashi muka tsara ba. Dan hatta madarar farko da nake shayar da duk Zawjata-almilk ita kin sha tai, alkyabba da turaren da nake badawa a musu wanka da shi a sako musu tun daga gidansu shima basu akai mata ba, ban hakuraba na bibiyeta da su nan ma taki yarda tai amfani da shi, duk ta inda muka bullo sai ta waske, da ga karshe ma wata rigar da mu bamu san ta ina ta fitoba ce ta sanya, daga haka ta koma sashen Mammah da zama, ita kuma ta kaita sashen Saiful-malik batare da shawarar mu ba bayan mun yanke a yanda zamu mata rakkiya zuwa can. Dan saboda na rabota da sashen Mamma da uwa bata iya zuwa yasa na bada shawarar maidata sashen Saiful-malik ta mana bincike, amma sai Mammah ta canja shirin namu gaba daya. Wannan abu ya konamin rai matuka, ya kuma zafi zuciyata na kasance a bakin ciki. Mairakon nasara komai sai sake tabarbarewa yake, da kyar muka samu cikon ayyukan mu akan Zawjata-almilk data tarar, Itako dai ta kasa tabuwa a garemu a duk ta inda muka bullo. Tun ana yakin sunkuru har komai ya fito fili da fitar da ban san mafari ba da ga gareta, yakin ya koma na kasanni na sanka......" ta rushe da kuka mai karfi. Sai da tayi mai isarta babu wanda yace mata ko kanzil sannan ta cigaba da fadin, "Babban tashin hankali na a yanzu da jagorantar dukkan karfin halin iya maida martanina ga uwa a wannan gabar da komai na tabbatar da ya lalace shine rasa Saiful-malik, ta sake tabbatar min sai sun amshi jininsa matsayin diyyar kin cika shardansu, bana son na rasashi, shine kadai ya kuka ya sarketa ta kasa cigaba. Jasrah ma kuka take iya iyawa, sauran yan uwanta kam tagumi duk sukayi kawai. Hankalin Iffah gaba daya akan Tajwar Eshaan yake, dan tunda ya dukar da kansa da kamo hanunta ya rumtse a cikin nasa har yanzu bai ko yi wani motsin kirki ba, hannun nata kuma na rumtse a nasan duk da azabar da takeji saboda yanda yake matse a cikin nasan haka ta cigaba da daurewa tana mai ambaton addu'oi da duk sukazo bakinta. Fatanta ALLAH ya saukaka masa zuciyarsa, ya bashi juriyar dauka.

Gyaran muryar kaka ne ya katse tunanin kowa. Ya nisa a hankali tare da gyara zamansa. "Lallai kinyi kuskure, kin kuma shiga rigar yaudara irin ta wadda bokaye kanyima bayin ALLAH saboda son zukatanmu da burin gina DUNIYA mai yankewa. Wannan mushirika tai tasiri da tasirin gurbataccen burinki ne da niyyarki ta shigowa wannan gida. Amma karya take bata da alaka da samuwar cikin Shugabamu da kikayi, dan dama sanda ta baki maganin kina tare da shigar cikinsa…....

Babu wanda bai zabura ba, hatta da Malikat Bushirat din kanta. Tajwar Eshaan kam sake kankame hanun Iffah yay cikin nasa tsam-tsam fiye da farko. Kai Kaka ya jinjina musu, "Wanna maganar da nake fada muku haka take, dama akwai cikin. Koda ace babu shi ta bada taimakon magani shi wannan maganin sai dai ya magance matsalar wani ciwo da ya zama sanadin jinkirta samuwar haihuwar bawai ya samar da dan ba. To sai a wannan labarin ma akwai samuwar cikin ma kafin ta shigo cikinsa. Rashin samuwar haihuwa jarabawace ga duk wanda baiyiba, jarabawa kuma mai ciwon gaske da radadi a zuciya, bazaka fahimci haka ba sai in ka kasance daya daga ciki. Ya halatta ka nema magani da ga kowace irin cuta a rayuwa. Sai dai fa akwai matakan da ya kamata mumini yabi wajen neman magani kowane irine balle ma akan neman haihuwa. A duk lokacin da muka rasa haihuwa idanunmu kan rufe da fadi tashin neman mafita ta kowanne yanayi. Burinmu shine kawai mu haihun. Sam babu tunanin maybe ita haihuwar ba alkairi bace a tare damu, a ganinmu kawai mun rasa shine mu nemota ta kowace irin hanya. Duk da abinda UBANGIJI ya baka ya fika sanin dalilin baka shi, idan kuma ya hanaka ya fika sanin dalilin hanaka da yayi. A rayuwa babu abinda yafi karfin addu'a, sadaka, yarda da kaddara mai kyau ko sabaninta. Idan kuma har ta kama saika nema maganin ka zama sani ba a wata gabar. A neman haihuwa wajen bokaye da malaman tsibbu zakaci karo da abu hudu in har ka samu daya da kaje nema. Na farko rasa imaninka da cire yardarka ga UBANGIJI mai badawa da hanawa, dan zaka cigaba da ji a ranka shifa wanna din nan ne ya baka wannan haihuwar (Wa'iyazubillah). Na biyu zata iya yiwuwa dan aljani ma aka samar a cikin naka batare da kasan hakan ba kai tunda kai a kai kanka ai. Na uku wasu matan ko da saninsu, ko bada saninsu ba zata iya yuwuwa bokan yay mata cikin a zahirance ko kuma ta hanyar tsafe-tsafen sa batare da ita tasan hakan ta kasance ba domin shi tsafi gaskiyar mai shine. Idan kuma ALLAH yasa dama ana a kan gabar da ALLAH ya iyakance ne dama haihuwar tata ta kusanto gareta batare data sani ba sai a samu dai-daito da bada maganin nasa haihuwar ta samu amma zuciyarta na tabbatar mata ta sametane daga wannan bokan ko malamin tsubbun……..✍️

Mu hadu in ALLAH ya kaimu Please🚴🚴🚴🚴🚴🚴🚴 hannuna ya gaji😂

DAUDAR GORA Book2 88

."Kamar dai yanda ta kasance a gareki. Ita tana da buri akan wannan masarautar, sai akai sa'a ke ma kinada naki burin da kika kai kanki gareta. Ita kuma sai tai amfani da haka kika zame mata yar aiken isar da sakonta ta yanda babu wanda zai fahimci ruhinta ya sake dawowa wanna masarauta balle ma a zargeta akan dukkan abubuwan da suka faru har a maida hankali. Wanna labarin naki yasa na fahimci maganar mahaifina da ya ce, duk saninka kankanuwar samarwace da ga taskar ALLAH da bata yankewa. Sannan haihuwar ita Fhareedah wani mashine da ga UBANGIJI da zai zama sanadin tarwatsa al'amuranku batare da kun fargaba, shiyyasa ya boyeta a cikin sirrinsa har zuwa ranar da zata dawo gareku cikin karfin ikonsa da zai tabbatar muku babu wani karfi da ke saman nashi. Shirka babbar faduwa ce, ginshikine na gina kaskanci a duniyar bawa dama lahirarsa. A duk lokacin da ka dauki cewar wanin ALLAH a iya baka koda kariyane da ga wani abin tsoratarwa to akwai babbar matsala,dan kuwa shi wanna mushirikin zai bika mataki-mataki ne wajen kaika fie da inda bakai hange ko tsammanin zuwa ba. Kamar dai ke din nan. A matakin farko bukatar haihuwa kikaje mata da shi, sai ta ce miki kada kiyi sallar la'asar. Tayi hakane saboda kasancewarki mai bautar ALLAH, sannan kina jingine da wasu muminai da zasu iya saurin fargar dake kuskurenki kuma ki gyara. Amma data kafa miki wannan tarkon sai ta busar miki da zuciya ta yanda duk yanda za'a kiraki bazakiji wannan kiran ba, ba kuma zaki saurari mai kiran ba koda ace kin jisa. Hanaki bautama UBANGIJI itace allurar farko mai tsananin dafin data sakaki shagaltuwar da bijire mata zai miki wahala koda ace kina so. Shiyyasa maganin ayima kar a fara, tun farko ma yi kokarin yin addu'a da yakar kanka daga son zuciya ko tunanin nema daga wanin ALLAH. Miyasa musulunci ya mana gatan cewa mu tashi mu nemu na kammu? Saboda kare kammu da ga biyayya ga abinda zai iya cutar damu. Dan a mafi yawa ko nace rinjayen dan adam yana son a duk sanda ka nema daga garesa duk sanda wani abu ya taso da zaka iya masa to ya tuna maka wannan taimakon da yay maka wanda zai iya sakaka jin kunyar yimasa abun nan koda ace bai dace ba. Kamar dai cin hanci da rashawa. A duk lokacin da mai bada cin hanci ya mika ga mai karba zai iya aikata aiki komai muninsa koda ace zai iya cutarwa ga rayuwar mal karbar shi kansa ne ma. Dan haka maganin data baki a tun farko ma bashi da alaka da abinda kikaje neman. Ta baki shine domin cutar da abinda ke cikin ki data riga ta tabbatar da akwai. Sai dai ALLAH ya riga ya kaddara babu abinda zata iya yi sai ya zo duniya, dan haka ta tafi mataki na biyu wajen rabaki da mahaifarki gaba daya. Mataki na uku ta rabaki da mijinki, mataki na hudu tai amfani dake wajen gogama rayuwar danki bakin fentin da zai bakantashi ga al'ummar kasar sa da mulkinsa. Lokacin da ake ihun yay murabus badan Iffah ta shayar da shi wannan madarar mai dafin macizai ba da burinta a tsigesan, hakan yana cikin plans dinta da idan wanna baiyi tasiri ba zata tsallaka na gabansa. Da ace taci nasarar kun hada auren wadda taso ta haifi magajinsa da taci nasarar duka wasan. Dan sam wadda take burin ya aura bama mutum bace cikakkiya yar zuri'arsu ce aka raina a anan duk saboda zuwan wannan lokacin. Daga kuma sanda ta samu ciki burinta shine ta kasheki, shima ta kasheshi wanna jinjirin ya amsa suna magaji, da ga haka ta karbe mulkin ta karfin tuwo da ga wanna ahalin. UBANGIJI bai gitta rayuwar Iffah a cikin al'amurran ki da rayuwar danki ba sai dan shi tsarkakakkene mai tarin tsoron ALLAH da kiyaye dokokinsa. Ya gadar da shine da ga kyawawan halayyar mahaifinsa sabanin naki dabi' un. Addu'oin da al'umma ke masa na tasiri a tare da shi tare da yin dubi da tsarkakakkiyar zuciyar kakarsa da tai yaki da yakar mushirikai. Mutuwar mahaifinsa da kakansa tazo ne akan gaba bawai bisa karfin ikonta ba. Da ace ma tayi hakuri zasu musu, tabbas zasu mutu a dai-dai wanna gabar har su matan nasa. Amma a yanzu hakkin ruhinsu duk ya rataya a gareku ke da ita domin harda amincewarki akai komai ba tilastaki tai ba a aikace.Kaiconmu da irin wannan burin duniya, kaiconmu da irin wannan hangen da babu hango iyakar karewarsa, kaiconmu da zuciyar da ke jin hakkin wani ba komai bane komai Kankantarsa komai rashin muhimmancinsa, Wlhy duk abinda akace maka ba naka bane sunansa ba nakan ba. Idan kuma harka taba da son zuciya ko izgili sai ka biyashi a ranar da babu kudi irin madadin a duniya. A ranar da cuniya ce zata taru, a ranar da ake biyan hakki da lada ko zunubi. Dan duk hakkin wanda ka taba zaka biyashi da ladanka, idan baka da lada za'a dibo zunubinsa a lafta maka. Shiyyasa mutane da yawa zasuje lahira da tarin lada a taskokinsu, amma yayin kammala musu hisabi sai su koma basu da korai sai tarin zunubai dan an biya duk wanda suka cima hakki da wanna ladan nasu. Haba yan uwa har wane aiki muka tara da har mukejin cin hakkin wani zai isa mu biyasa har mu sami rarar shigar aljanna da sauran. Wani ma har kaji yana izgilin shi hakkin wani ko ALLAH ya isa bata masa komal a jiki, why da tabon da zatai maka a rayuwarka gara ace a jikinka take tsirowa maybe kaji tsoron ALLAH da wuri ka sauke hakkin. Shi kuma wanda ma ya hadiye bai ce dakai komai ba yafi ban tashin hankali fiye da wanda zai furta maka maybe ka razana ka sauke. Wai miyasa bama tunanin cewar wanda muka cima hakkinsu sune masu nasara akan mu ne? Tabbas masu nasara a kammu, dan sun kasance masu ajiyewa a dauka a kuma biyasu a ranada ake farautar ayyukan cika mizani. Kawai akan son farantama was mu mu tauye kammu mu daga nasarar wasu. Wai a hakan dan wawanci murna mukeyi, farin ciki mukeyi mun karya wane, mun kaskantar da wane, mun maida wane baya, waya fada maka dariya ya kamata kayi ko kiyi?Wlhy kuka, kuka ya kamata ki fara tun kafin ganin anar nasarar mai wanna hakkin da taki faduwar,Wadan nan hakkokin da muke rainawa suke hauhawa su gawurta su zama manyan abubuwan ruguza ayyukanmu. Kamar dai ita, ta fara ne tun a kuruciya, zalinci wancan, tirsasa wancan ana gain yarintace hakan ba komai bane amma sai abin ya cigaba da tasiri a rayuwarta har yay gawurtar da ayanzu ta fado kasan-kasan kafafun wadan da take gain ba komai ba, wanda take ganin murjesu ta taka ko cin hakkokinsu ba komai ba. Gadai shi taji dadin, tayi farin cikin, ta dauki kanta a mai nasarar, amma a karshe itace ta zama mara nasarar, mafi kaskanci.Mafiya masu cin hakki da ruguza rayuwar wasu zamu samu matasane masu tasowa, maybe batai aure ba ko baiyi aure ba, kokuma bata jima da yin auren ba,dan duk wanda, ko wanda ya kai shekaru arba'in a duniya ya zabi take hakkin wani babu babban wawa sama da shi. Amma su wadan nan masu tasowar gani suke abinda sukeyi ba korai bane, yanzu ma aka fara rayuwar. Waya gaya miki koya gaya maka ba komai bane ba. To ko kasa mutum ya gino ya tara kikazo wucewa ko kazo wucewa ka barbaza masa ai hakkine balle abinda ya killace koya nunama duniya abun nan mai muhimmanci ne a garesa koda ace kai baka ganin muhimmancin nasa. Kanada kananan shekaru kana ta daukar hakkin mutane da kake gain bamai muhimmanci ba kana tarawa yana hauhawa a mizanin aikinka yana rusaka, yana rusa rayuwar yayanka masu tasowa, yana rusa cigabanka na duniya dana lahira kai kana shirmen kana nasara akan mai hakkin. Kajifa toshewar basira, shi kana kara masa nasara ne fa, tunda dole-dole ka biyashi a inda babu kudi sai aiki inhar baka biyasa da kudin daya shardanta akan kayan nasa ba. Kamar dai ita a yau, komai yazo mata a gabar da bata da damar neman gafarar wadanda ta zalunta ta cutarma da rayuwa saboda nasararta da neman cikar burinta. Ta rasa a lokacin da su kuma suka samu, wata tayi amfani da ita dornin nasararta ta barta da katon nauyi bisa kai. Kaicon rayuwar da ba'a tuna mutuwa a cikinta. Kaicon rayuwar da ake ginata kamar bazata yanke ba. Kaicon rayuwar da ake daukar hakkin wani kamar ba hakki ba. Kaicon rayuwar da cikar buri ke jagorantar imani da tsoron ALLAH a zuciyar mai shi. Kaicon zuciyar dake bushewa da jin komai tayi dai-daine. Ya ALLAH ka karemu, ka kara tsaremu, ka tsarkake mu, ka kiyaye mu. Ka killace mu, ka karfafa mu, ka jagorance mu bisa tsoronka da tsoron shirka, da tsoron cin hakkin wani komai kankantarsa, ka kyautata neman mu da ga halak, ka karfafa ayyukanmu bisa umarninka da kiyaye saba maka badan halinmu ba. ALLAH ka shiryar da wanda suka kauce, idan ba masu shiryuwa bane UBANGIJINMU mun barka da su kafimu sanin miya dace da su. ALLAH ka rabamu da ruin duniya da kyale-kyalen cikinta. Ya rabbi ka saka DUNIYA a tafukan hannayenmu ka nisantata zama a cikin zukatanmu. Ya rabbi ka wajabta mana tsoronka, ka karfafa imaninmu. Ka yafe mana kura kuranmu, ka bamu ikon kyautatama duk wanda ka hada kaddarar zaman mu a tare ko mu'amularmu, Ya rabbi ka hana mugayen halayenmu cin nasara a kammu, kasa muci nasara akan mugayen halayenrnu da ayyukanmu".

A tare suka dinga amsawa da Amin kowa na sharar hawaye, yayinda Malikat Bushirat ke kuka mai tsananin gunji. Matuka takejin radadi a zuciyarta da azaba a cikin jikinta, So take ta kara cewa wani abu koda ga tilon danta ne da har yanzu bai dago kai a dubi kowa ba balle ita amma ta kasa hakan. Da ga karshema mikewa yay a hankali cikin tangacfin juwa hannunsa cikin na Iffah har yanzu batare daya kalla kowa ba balle cewa wani abu ya jata suka fice. Ta hanyar sirrin da suka fito ta can suka koma hankalin Iffah a tashe da yanda yake tangadì mai bada tabbacin akwai matsala….✍️

DAUDAR GORA Book2 89

...... Suna shiga bedroom din sa ya wani irin rungumeta tsam-tsam a jikinta tamkar zai maidasu su zama abu guda. Yanda Iffah kejin gudun zuciyarsa da bugawarta hankalinta ya tashi matuka. Tayi yunkurin dagowa ta kallesa amma yaki bata koda kankanuwar dama. Sosai numfashinsa ya fara fisga, gashi ya ki sakinta balle ta bashi wani taimako, mutsu-mutsun kwatar kanta take amma ta kasa. Sai kawai ta fashe masa da kuka. Sakinta yay da sauri, sai dai bai yarda sun hada ido ba ya rabata ya wuce. Gaban window yaje ya tsaya kawai ya tsirama harabar masarautar ido. A gurin Iffah ta durkushe ta cigaba da kukanta. Tsahon mintuna goma suna a haka sautin kukanta kawai ke ratsa dakin, shiko yana a inda yake tsayen kamar gunkin da aka dasa domin tarihi. Mikewa tai itama jin jiri ya fara dibar idanunta, dan akwai yunwa tare da ita, rabonta da abinci tun jiya. A bakin gadon ta zauna jagwaf, ta dafe kanta tsahon minti daya kafin ta janye. Ciwo hannayenta ke mata sosai saboda matsar da suka sha a wajensa, har sun dan kumbura dan matsar bata wasa bace. Jin sun mata tsami babu dadi ta shiga murzasu a hankali ko zataji sassauci. Bata san sanda ya baro wajen window din ba, ganinsa kawai tai durkushe gabanta ya kamo hannun nata a cikin nashi. Kallo daya taima fuskarsa tai saurin dukar da kanta, dan idanunsa sun yi masifar firgitata. Sun yi wani irin kadawa jazur irin wanda bata taba gani ba,hakama fuskarsa gaba daya tayi jazur kuma babu alamar yayi kuka, kawai tsabar tashin hankaline ta sauya masa kamanni. Hannayen ya shiga murza mata a hankali, kafin tsahon lokaci kamar wanda aka fisgo furucin da ga halshensa ya ce, "I am sorry".

Da sauri ya dago ta dubesa, ganin yanda ya tsurama tafin hanunta idanunsa masu ban tsoro yasata jin hawaye sun sake cika mata ido. Dayan hanunta ta daura akan habarsa mai cike da lallausan bakin gashi ta dago, cikin dauriya da dakiya ta saka idanunta cikin nasa, muryarta na karkarwa ta furta, "Dan ALLAH kayi kuka koda kadanne Zakina. Kayi kuka! kayi kuka!! kayi kuka!! Zan shanye hawayen a cikina na adanasu cikin manyan SIRRIKANKA da ka bani ajiy....."

Kafin tama kai karshe sai ga hawaye sharrrrr da ga idanunsa kamar an bude fanfo, wani irin murmushi mai tsananin ciwo da kuna ya sakar mata hawayen na kara gudu. Da sauri ta tara hannayenta suka sauka a ciki, kallon tafin hannun nata da hawayen nasa ke sauka yayi, sai ya sake fashewa da kukan, hawayen na cigaba da sauka a cikin tafin hannun nata. Sai da suka taru sosai sannan tasa harshenta ta shiga lashe hawayen tana hadiye tare da fashewa da sabon kukan itama. Kansa ya daura a saman cinyarta yana zaune da ga kasan lallausan carpet din gaban gadon itako tana daga zaune a kan gadon, itama sai ta daura kan nata a kan nasa suka cigaba da kukan a haka zabban tausayi…

Bayan sallar azhar da ya kasa fita saboda zazzabin da ya rufesa mai zafin gaske itama ciwon ciki ya takurama Iffah na jin yunwa, abinka da ba ita kadai ba. Haka ya tashi cikin kakkarwar sanyi ya bata madara ta sha, tana sha ta amayar da ita, a hakan dai ya taimaka mata cikin karfin hali ta gyara jikinta, sake bata madarar yay tasha kadan, shima sai ta takura masa wai sai ya sha dan rabonsa da abincin kirki tun jiya. Kin sha yay ta sanya masa kuka, dole yasha rabin kofi ya kauda kansa, da ga haka suka dunkule waje daya kwance zafin jikinsa na matukar ratsata. Ganin zazzabin baida alamar sauka sai ma karuwar da yake yi yasa Iffah kiran Sayeed Fayzul-haq. Babu bata lokaci suka iso da Doctor Afif da ke matsayin amintaccen likitansa. Doctor Afif din kansa sai da hankalinsa ya tashi gain yanda jinin Shahan-shan din yay wata irin kololuwar hawa, ga bugun zuciyarsa har ya canja. Cikin sauri ya danna masa allurar barci mai matukar karfi dan in har aka cigaba da zama a hakan akwai babbar matsala kam. Da farko kin yarda ma yay ayi allurar sai da Iffah ta sanya masa kuka sannan ya kauda kansa kawai baice komai ba. Sai Sayeed Fayzul-haq ne yay ma Doctor din nuni da yayi aikinsa dan kauda kan nasa a nufin amincewa, Iffah dai na zaune ne kansa a saman cinyarta tanata faman sharar hawaye. Duk da karfin allurar ya jima baiyi barcin ba, dan sai da Iffahr ta hada da tofa masa addu'oi sannan aka dace barcin ya daukesa.

Haka ta cigaba da zama kansa a saman cinyarta har aka kira sallar magrib, kafafunta duk sunyi tsami,da kyar ta gyara masa kansa ya koma kan fillo, sannan ta mike ta gabatar da sallar magrib din. Alkur'ani ta dauka ta shiga raira karatu a nutse tana hawaye, bata ajiye ba har aka kira sallar isha'i nan ma ta gabatar. Ta jima tana addu'oi akan wadan nan al'amura da suka cure musu, tashinta babu jimawa Malikat Haseenat da Daneen Ammarah da Daneen Waheeda da Iftihal sukazo dubashi. Basu shigo ciki ba iyakarsu falo, Iftihal nata yan kalle-kalle dan wanna shine karo a farko a rayuwarta ma data shigo sashen nasa. Iffah na fitowa ta wani dukar da kai dan ita kam tsoranta takeji matuka yanzu. Cike da kauna da tausayi Malikat Haseenat ta rungumeta, kafin ta dagota da fadin, "Hafida-ti kema ai ba lafiyarce da ke ba ma, dan zazzabin ne a jikinki. Kin ma ci abinci. Idanun Iffah cike da hawaye ta girgiza kai da fadin, "Na koshi Jaddah".

Readers Also Read