Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul - Chapter 67
Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 67: Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 67. A take suka dunkule waje daya suka zagaye Tajwar…
4,135 words
A take suka dunkule waje daya suka zagaye Tajwar Eshaan ya koma tsakkiya tare dama kansu garkuwa kibiyiyin suka dinga sauka akan saman garkuwar karfen hannayen nasu. Da wanna damar yan kabilar su uwa da ke saman bishiyu da duwatsu fara dirgowa kasa suka zagayesu. Sanda suke janye garkuwar bayan gama saukar kibau din sun gama zagayesu. Ko kadan hakan bai razanasu ba, dan kowa a fusace yake da jin tsanar wadan nan kafirai. Sannan sunyi alkawari duk rintsi bazasu bari a taba musu Shahan-shan din su ba. Tuni sukai wata irin rabewar da kaka duk ya tsara musu. Su kuma gain hakan sai sukai tunanin tsorata sukayi ne suka afka kai tsaye da tunanin korar su. Wannan itace damar farko data basu nasara akan wadan nan mutane, cikin kankanin lokaci kura ta tashi waje ya hargitse. Kabilar uwa sunyi shiri ne irin shirin da wuka ko bindiga bazata ratsasu ba. Yayinda Kaka ya bada shawarar fara tunkararsu da wuka sai sunzo hannu ai amfani da maganin daya tanada wajen karyasu su da karfin yakin nasu. Gurin na cakudewa kam wadanda zasuyi feshin maganin ta sama da ga cikin jirgin sojoji suka fara. Tun anan fa ihu-da-ihu ya hargitse, suka fara kaiwa kasa samarin nan a gille kawunansu. Yayinda kabbara ke tashi da amsa kuwwa a cikin jejin. Cikin abinda bai wuce awa uku ba an gama da kaso biyu da rabi bisa uku a cikinsu. Zuwa yanzu fa hankalin uwa da ke kwasar dariya ya fara tashi. A take ta bada umarni ga wadanda ke zagaye da ita fara aiwatar da shirinsu akan Malikat Bushirat. Dan hakanne plan c dinsu, plan b shine wasu kason mutanensu da ke can masarauta dakko karagar mulkin Shahan-shan..
** MASARAUTA **
Kukan da taci ya haifar mata da matsanancin ciwon kai, duk yanda taso kin kwanciya sai da Malikat Haseenat ta takura mata. Kwanciyar tayi, sai dai bata rufa mintuna ashirin cikakke ba ta tashi a matukar firgice. Hankali tashe Malikat Haseenat da Daneen Ammarah sukai yunkurin riketa amma ta girgiza musu kai. Sun fahimci tabbas akwai matsala, dan haka Daneen Ammarah ta ce, "Mammah barta. Barta kawai akwai matsala ne".
Hankalin Malikat Haseenat tashi ya karayi, dan tuni itama Daneen Ammarah din ta birkice a cikin kankanin lokaci. Dai-dai nan ko Amintacciyar hadimar Malikat Haseenat ta shigo hankali tashe, cikin hakki take sanar musu babu lafiya, ga was irin mutane nan da ba'asan ta inda suka shigo masarautar ba sun zagaye ko ina. Wasu a cikin jami' ai sun fara harbinsu amma ko gezau da alama ma bindigar bata kamasu. Wasu kaso a cikinsu kuma sun nufi fada ne inga karagar mulki take.
Kafin ma takai karshe Iffah ta fice, Daneen Ammarah biye da ita. Gaba daya masarautar ta gama harmutsewa. Tuni kowa ya fara gudun ceton rai.Yayinda jami'an masu karfin hali da Ghazi da wasu a cikin hadimai da samari da aka bari sunata kokarin kai musu hari amma mutanen nan babu alamar razani a tare da su, saima wani irin dariya sukeyi cike da karfin iko na ko gezau. Ai babu wanda yasan ta yaya, ta ina ma, kawai saukar kawunansu aka fara gani bisa kasa. Hankalin Ghazi ya tashi, ganin SARAUNIYA Iffah ce da kanta ba sako ba. Tare da Daneen Ammarah da a yau kowa ya shaida eh lallai ba ita kadai bace itama da nata ifiritan aljanun bisa kai.
Duk wanda ya tunkari Iffah kai kawai take sauke masa ta matukar fita a hayyacinta da canjawar kamanni. Suko hatsabiban wani irin bulbulo wuta suke ta bakunansu suna kokarin tunkarar fada da tuni aka rufo ruf. Masarautar tayi masifar rikicewa, mata da yara kuka kawai suke. Hakama wasu a cikin mazan tuni sun nema wajen buya. Hatta su Miran Jasim da ke a cikin kurkuku sun tabbatar yau gidan babu lafiya kam......
** *
Su uwa na tsaka da zagaye Malikat Bushirat da aka gama jikewa da ruwan tsaffi a tsakkiyar gumaka Tajwar Eshaan ya fado musu. Da wani irin jarumta dokinsa yay haniniya mai razanarwa kawai yay kansu.Daga dokin har shi Tajwar Eshaan din gani sukai sun koma musu wata halitta daban. Yau sai ga uwa tsaye akan kafafunta ta mike da ga kujerar tsafinta cikin matsanancin tashin hankalin gain dokin nan fa babban gunkinsu ya nufa. Kafin tai wani yunkuri yay ma butum-butumin gunkin wani irin duka da dukan karfin kwanjinsa shi da dokinsa sai gashi tarwatse a kasa. Ai ko kashin hannunsa yay wata irin karar masifa da ke tabbatar da yaji ciwo a cikin kashi. Hannun yay kokarin rikowa da dayan Hannunsa dake rike da linzamin dokinsa yaji saukar kakkaifar wuka a cikin damtsen hannun.
"Ya Arrahaman!!"
Ya ambata da dukkan karfin murya dana jiki da ya masa saura. Dan wata irin azabar zafi ce ta ratsasa har cikin kwakwalwa, Dai-dai juyowarsa kan wanda ya sokesa da wukar a dartsen hannun ya sauka kasa. Babiy ne da ya biyo bayansa, dan tun barowar Shahan-shan din a cikinsu ya farga yay azabar biyo bayansa. Bummm!!!! Shima Baby uwa ta sauke masa wani mulmulen ice saman kai, kara ya saki shima cikin ambaton ALLAH ya dafe kansa da jini ya balle, luuuu ya tafi kan dokinsa zai zubo cikin karfin hali Tajwar Eshaan yay wani irin juyi ya tallafosa. Gaba dayansa ya dago ya ajiye saman dokinsa. Kafin ya fisgo sarkar da suka shirya rataye Malikat Bushirat a ciki ya watsata, cikin amincin UBANGIJI ya samu nasarar sarko wuyan uwa da ke kokarin zare wata takobin tsafi da ga jikin wani gunki. Razananninayar karar data fargar da wanda ke waje ta saki, dan sarkar ta tsafi ce, amma cikin amincewar UBANGIJI shi Tajwar Eshaan din sai bata masa komai ba. Duk da da yawansu an musu jina-jina haka suka dinga dannowa dakin dan zuwa yanzu suma sun gama da wanda suke wajen, wadan da suka rage kuma an kamesu an daure bisa umarnin kaka.
Cikin tashin hankali suka nufi Shahan-shan, amma sai ya girgiza musu kai alamar su barsa. Da kansa ya dirgo kasa, su kuma suka kama Baby da babu numfashi tare da shi suka sauke aka fita da dokin Shahan-shan. Shi da kansa ya daure uwa da sarkar nan tare da bama matasan sa umarnin rushe gumakan: a gabanta, rushewar kam suka farayi itako tana kukan bakin ciki da wata irin jijiga a cikin sarkar da ya dauretan.
Shi kam takawa tay a hankali gaban Malikat Bushirat. Hannu ya kai ya yaye jan mayafin da suka. lulluba mata, dai-dai nan ta bude idanunta sai ko a cikin nasa, kallon juna sukai na kusan sakkani goma. Shi ya fara janye nashi da sukai wani irin jazur cikin lumshesu da budewa. Batare da ya yaye farin mayafin dake a kasan jan ba yasa hannayensa biyu ya dauketa duk da yanda hannunsa a haggu da yaji ciwo ga wuka a ciki jini na zuba ke masa azaba da rawa. Wasu irin hawaye ne masu zafi suka shiga rige-rigen sakko mata, dan su kadaine ke aiki a jikin ta, amma su Uwa sun sandarar mata da jiki gaba daya babu abinda ke aiki tare da ita sai kanta da idanun.Duk yanda ta kuresa da ido shi yaki yarda ya kalletan.Cikin sauri masu bada taimakon gaggawa da aka taho dasu cikin sojojin suka nufosa da gadon daukar marasa lafiya. Amma bai daurata ba har sai da yaje ga jirginsu na sojoji da suka sauka. A hankali ya shimfidar da ita, sai da ya tabbatar ya gyara mata mayafin da take ciki dan tsirara take sannan ya dubi matukin jirgin yana lunshe ido. Ya fahimci abinda yake nufi, dan haka ya kame jikinsa tare da salute nashi.
A gaban su kaka ya tsaya ya wani rumtse danunsa da daura hannunsa saman wukar nan dake kafe a jikinsa zai fincike kaka yay saurin dakatar da shi. "A'a ranka ya dade, hakan da zakai matsalane, dan wukar ba wuka bace takai tsaye kamar saura akwai dafi tare da ita. Kawai ka shiga jirgi dan bai kamata ka koma damu ba a doki".
Bai cire din ba, sai dai ya bama kaka amsa da cewar"Tare da ku zan koma Jaddi".
Murmushi kawai kaka yayi shi da Sayeed Tasadduq- Husain, dan yau ne karo na farko da Tajwar Eshaan din ya kira shi da kaka. A dai-dai nan aka fito da Uwar dake daddaure cikin sarka. An tsareta da tambayar ina yaran garin suke amma taki fada, sai ma dariya data sanya musu da cewar, "Bazan fada ba, bazan taba fada muku ba. Dan ku tabbatar karar da mu iyayensu kamar kashe maciji ne baku sare kansa ba hahahahaha!!!!!".
Babu wanda ace da ita komai saboda isowar jiragen sojoji da shugaban sojoji ya bada umarnin a karo, dan yanda suka jigata din nan babu mai karfin iya komawa ta mota ko doki. Ga wasu shimfide babu alamar rai ma tare da su. Wasu kuma sun jigata matuka da ko yatsansu basa iya dagawa ma. Kin fadar inda yaran suke yasa sukai tunanin ko sun dauke su ma daga jejin ne gaba daya yasa shugaban sojoji bada umarnin ana gama kwashe su a sakama garin wuta kawai. Uwa bataji wannan furuci ba, kasancewar an tisa keyarta ita da sauran mutanensu ashirin da daya daba'a kashe ba cikin motar yaki.Hakama sauran mayakan duk an sakasu a jirage su, marasa lafiya sune farkon wucewa domin zuwa a basu taimakon gaggawa. Kaka da Tajwar Eshaan da Sayeed Tasaddug-Husain da shugaban sojoji sune karshe, za'a warema Tajwar Eshaan jirgi ya dakatar dasu.
Tuni sauran sojojin da aka bari suka sakama garin wuta gaba dayansa bayan an tabbatar da babu wani kauye a kusa da su da wutar zata iya shafa. Dan su tsabar bakin hali ma basu yarda yin makwaftaka kota kusa da wasu kauyukan ba. Wannan wuta itace ta dinga wasar kogon dutsen da suka boye aransu zafin ya dinga ashes batare da an san anan din suka boyesu ba.
*
Abinda ya far a cikin masarautar ya sasu iske cikin Dahab City a hargitse. Dan jiragen a inda suka dauke su farkon jejin dole anan suka dakata aka dinga kwasarsu a motoci. Nan din ma cike suka samesa da jama'ar gari ga yan jarida. Jinin da Tajwar Eshaan ya rasa sakamakon sukar wukar da aka masa mai dafi a hannu dama ga kananun raunuka yasa idanunsa har sun fara rinjaya, dan sal da taimakon shugaba sojoji da kaka aka fito da shi aka daura a gadon marasa lafiya zuwa mota Hankalin mutane ya tashi matuka dan sun fahimci Shahan-shan dinsu kenan gariin yanda sojoji suka zagaye gadon, hakama da aka saka shi a motar an zagaye motar da uban tsaron da korna miye ya gitta zal iya zama gawa ne….✍️
DAUDAR GORA Book2 93
……..Cikin masarautar ma a hargitse suka sameta,dan tuni an is da Malikat Bushirat da aka fara tahowa da ita. Ga Iffah da jini ya balle mawa ta yanke jiki ta fadi itama aka shiga da ita ciki har yanzu likitocin da ke kanta basu fito ba. Tashin hankalin hakan yasa ko wanda suka sarewa kawuna ita da Daneen Ammarah bama a janye ba. Ba'a bari kowa ya ga halin da Tajwar Eshaan ke ciki ba aka shige da shi sashensa. Hakama sauran mayakan da sukaji munanan raunika aketa nufar cikin clinic da su duk da kukan da iyayensu keyi ba'a bar kowa matsowa kusa da su ba, wanda sukaji kananan raunuka ne dai aka zube a harabar masarautar suma ana basu taimakon gaggawa na ruwa da magani. Ga magrib ta gabato. Amma burin kowa dai yaji yaya Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdul-majeed Aliy Qutb yake. Yanda suka tada hankalinsu yasa dole sai da Sayeed Fayzul-haq ya fito yay magana da yan jarida akan kowa ya kwantar da hankalinsa Shahan-shan na nan raye, sai dai yana bukatar addu'oin Su...
*WASHE GARI*
Alhamdullah an wayi gari da dadin rai, dan su Babiy duk sun farfado. Hakama Tajwar Eshaan kaka ya saka masa magani an kuma masa na asibiti da dorin karayar sai dai ace Alhamdullah. Itama dai Iffah an samu nasarar tsayar da jinin kuma cikin da aketama damuwar zai iya lalacewar dai yana nan. Malikat Bushirat ce dai idanun nan da kai kawai ke aiki, sai dai duk abinda za' a fada tana ji. ALLAH sarki Jasrah bata gazaba a yi mata hidima. Jama'"ar gari dama na masarautar da basu san komai akan al'amarin nata ba sunata tausayinta da gain Uwa ta tsafeta ne saboda cikar burinta. Was har addu'a suke mata na samun lafiya. Gawarawakin dangin uwa an tattaresu anyi rami acan daji an biznesu, wanda kuma suka rage tare da uwa an zubasu a kurkuku har sai ALLAH ya bama Tajwar Eshaan lafiya.
Tako ina labaran abinda ya faru a kasar ruman dinne ke yawo a duniya, wasu na caccakar Shahan- shan akan abinda akai bai dace ba suma mutanen nada yancin kansu, wasu ko na ganin hakan da akai shine dai-dai. To koma dai yaya ne yan kasar ruman sudai hakan da akai yayi musu. Dan babu wata kasa da zata so rayuwa da masu bakin kafirci irinsu uwa.Masu ganin ba'a musu dai-dai ba ma son zuciya ne kawal.
Lokacin da Iffah ta tartado taci karo da Tajwar Eshaan jikinsa ta fada kawal ta fashe da kuka. Ya rungume kayarsa yana murmushi shima idanun nasa dai sun kada. Sai da tayi mal isarta sannan ta dago, babu zato kawai yaji ta manne lips dinsu a waje guda. Idanu ya zaro itama sai ta zaro nata tare da janyewa tana dariya. Da sauri ya rikota da hanunsa mai lafiyar ya maidota jikinsa yana murmushi.
"Wannan ai mugunta ce a lasama mutum zuma a baki a gudu". Ya fada cikin rada a kunnenta. Dariya ta shigayi a hankali tana boye kanta a cikin jikinsa, da ga haka ya canja wasan a yanda yake bukatar kasancewarsa, duk da kuwa komai da yake na karfin hali ne kawai, dan sam zuciyarsa babu dadi, shi kadai yasan halin da yake ciki akan mahaifiyarsa. Amma yanata kokarin dannewa da gayama ALLAH kukansa.
Lokacin sallar azhar domin sake Kwantan da hankalin mutane ya fita sallar cikin karfin hali duk da hanun nasa an masa dorin karaya ne. Ga yankan wukar nan da yay matukar shiga jikinsa sosai, saukin ma dal anyi maganin dafin. Bayan anyi salla an fito ya dan gana da manema labarai da yasa a tara masa. A nan yay ma al'ummar kasarsa godiva da fatan alkairi bisa kokarinsu da addu'oinsu. Ya kuma sake jaddada Iffah matsayin SARAUNIYARSU har yanzu dan bazai amshi mulki ba sai ya samu lafiya. Babu wanda yay jayayya da wannan al'amari. Sai ma Tajwar na jihohi da manyan kasar dake ta layin zuwa dubashi tako ina, tare da sauran mutanen da suka fita wannan gumurzu. Musamman yan kauyukan nan da Hadimai da wasu a jama'ar gari da suka taimaka musu anhadasu da manyan kyautuka, hakama itama SARAUNIYA Iffah ta bisu su dukansu da manyan kyaututtuka da ya sakasu a farin ciki, dan ita dukansu ta hada har matasanta.
Lokacin da don Malikat Bushirat ke gain bayanin Shahan-shan akan Iffah zata cigaba da rike matsayinsa har sai ya samu lafiya, da lokacin da ake nuna Iffah'r akan karagar mulkin Shahan-shan din randa take zartar da hukuncin kyautukan da ta bama wanda sukaje yakin a matsayin Sarauniya kuka ta dingayi, kuka mai zafi da tsananin kona zuciya. Sosai takejin radadi matuka a cikin kirjinta, ji take inama kafin zuwan wanna ranar ta mutu ta huta. Bayan tasha kukanta ta godema ALLAH ta cema Jasrah a cire mata tvn daga dakin. Jasrah har ta amsa da to Malikat Haseenat ta ce kar a cire. Dan tsaf ta fahimci manufar Malikat Bushirat din. Tana ammakin taurin zuciyar matar nan, ace duk wadan nan abubuwan daka gani basu isheka izna ta saraya ba. Ko dan data haifa ta kasa neman gafararsa ma balle su. Kai ALLAH ya rabamu da irin wanna mummunar zuciyar ta kafuran farko,
Kullum sai Tajwar Eshaan yabi ta barauniyar hanyarsa dubota. Zasuje da safe shi da Iffah da an idar da sallar asuba. Zakuma suje bayan sallar isha' i. Da ga gaisuwa da tambayarta yaya jiki bai iya kara sake cewa komai. Sai ma ita Iffah'r ce kan dan mata addu'a ta tofa mata, duk da dai kaka nata kokarin bada magani ana mata ko za'a dace. Haka zatayi ta kallon Tajwar Eshaan tana hawaye, amma shi daga kallo daya na gaisheta baya sake yarda ya kalleta har yabar dakin kansa a kasa yake.
**.
Bayan kwanaki bakwai abubuwa da yawa sun dai-data, musamman masu kananun raunuka sunji sauki sosai, sai wanda suka jigata ne sosa ke cigaba da karbar magani. Baby ma dai da yake buguwace Alhamdullah jikinsa da sauki, dan haka Tajwar Eshaan yace kawai Daneen Ammarah ta tare haka nan. Duk yanda taso zamewa sai da aka shirya wani dan kwarya-kwaryar walima data kayatar. Dan anyita ne irin ta manyan mata masu aji da ilimi. Zuwa dare aka shirya mika amarya dakinta, Iffah kuwa ta dage sai taje. Sai da aka tuna mata itafa SARAUNIYA ce a yanzu, babu yanda ta iya dole ta hakura, amma tanata ima Mamyn (Daneen Ammarah) tabarar wai shikenan ita haka kowa zai tafi ya barta. Ita an kawota gidansu ita kuma za'a maidata gidansu. Itakam data san hakane kawai kowa yay zamansa gidansu. Dariya sosai Malikat Haseenat da Daneen Waheeda keyi da drama din tasu. Dan wata shakuwace ta musamman ta sake shiga tsakanin Iffah da Mamyn (Daneen Ammarah) taja yarta jikinta sosai da sake tabbatar mata da kaunar da take mata dabance a rayuwa. Haka itama Iffah'r tana kaunar mahaifiyar tata matuka duk da bata rayu da ita ba. Sannan tana kaunar Ummu dinta da Baby. Hanash Akhi kam ai shi na musamman ne gareta da Kakanta abin alfaharinta. Kullum cikin lallabasa take shi da lyyani su dawo cikin masarautar da zama ko zata dan ji saukin kewarsu da tayi. Shi dai ya nuna bazai dawo ba. Amma Tajwar Eshaan ya ce ta kawantar da hankalinta zai dawo mata dasu, Ba karamin farin ciki tayi da hakan ba.Dan shima Babiy an gyara masa gidansu sosai dan bazai iya barinsa ba saboda gidan gonarsa.
Lokacin da za'a wuce da Daneen Ammarah sai gashi tana kuka, ta rungume Malikat Haseenat da Iffah sunata kuka. Da kyar Daneen Waheeda da Malikat Ashwaq suka rabasu aka fita da ita. Yau kuma sai dakin mijinta ban yarta.
Tarbace ta mutuntawa suka samu da ga su Ummu, kowa halayen Ummu na birgesa, dan mace ce data amsa sunanta cikakkiyar mace jaruma abin koyi da nunawa a duniya ga kowa, Yan kawo amarya basu wani jima ba suka wuce abinsu. Lokacin da ango zai shigo Ummu da kanta tayo masa rakkiya cakin amaryarsa. Zata gudu Daneen Ammarah tace saifa ta zauna sunyi hira. Babu yanda Ummu ta iya dole ta zauna. Sai dai hirar ma dai duk akan rayuwarsu ta bayace data shude. Kuruciyar Iffah da su Arfa Daneen Ammarah har kuka tayi, ta jinjinama hakuri irin na Ummu. Ta kumayi alkawarin kyautata zamansu tamkar yan wan juna har abada. Zasu zama aminan juna bawai kishiyoyi ba. Ganin dare yaja da wayo Ummu ta tattare kwanikan da sukaci abinci ta gudu. Dama shi Hanash Akhi yana can masarauta Iffah ta rikesa wai shine amintaccenta, nan ko duk wayone dan taita gain dan uwanta ne. Dan babu wani abu da yake yi sai idan sun dan shiga fada zatai wani zama mai muhimmanci da manyan masarautar ya kasance a gefenta. Hakan sai ya saka mata zaman lafiya da Tajwar Eshaan sarkin kishi, dan tana ambata maganar Hanash Akhi dinne zai kasance amintaccenta harda kyauta sumba aka bata. Wai hakan shine dai-dai.
Ummu na fita Babiy sauka yay kasa gaban Daneen Ammarah ya zabga tagumi ya wani zuba mata idanu. Murmushi tayi da jan mayafin jikinta ta rute fuska cike dajin kunyarsa. Ya lumahe idanu da budewa yana murmushin shima, Kafin ya mike tsaye ya yaye mayafin gaba daya ya kama kafadunta ya mikar da ita ya rungume abinsa. A tare suka dinga sauke ajiyar zuciya, sai kuma hawaye na tsananin kewa da tuna baya.
"ALLAH na gode maka daka maimaitamin wannan rana a rayuwata. Ka gamamin komai UBANGIJINA daka bani mafi tsadar nan a cikin mata matsayin matata"
"Ni zan godema ALLAH da samunka matsayin miji kuma uban yayana Zayyan. Tare da yar uwa jaruma Saliha irin Jumaymah. Yanda kuka sharemin hawayena, da zama silar canja labarin da ban taba tunanin zai canju daga kaddarata ba kuma ALLAH ya share naku hawayen. ALLAH ka hana shaidan shiga tsakaninmu. Nayi alkawarin in har inada rabon sake haihuwa a duniya zan malakama Jumaymah (Ummu) yayan nan har abada".
Cikin rada-rada a kunenta ya furta, "Insha ALLAHU a yau din nan zan dasa kwam Arfa da Fariha gimbiyata." cike da jin kunyar furicin nasa ta wani kankamesa da boye kanta a jikinsa. Wani irin rungumeta tsam-tsam Baby ya sakeyi shima yana dariya, tare da bata sumbata tako ina a jikinta harya sauke akan lips dinta, Jin tsaiwar na neman gagararsu ya dauke abarsa tsamm suka shige daga ciki, dama dai ga Daneen Ammarah yar dum-dum kai kace bata wuce talatin a duniya ba. Jin an rufo kofa harda murza key nayi baya dan wanna fagen na manya-manya ne ba gain kanana irimmu ba 🥱😉😂🚴
* BAYAN WATANNI SHIDA DA FARUWAR YAKI TSAKANIN SU SHAHAN-SHAN DA SU UWA
Kai kawo yaketa famanyi a cikin bedroom din nashi bakinsa dauke da addu'a. Duk ko yanda waya ta motsa sai ya daga da tsammanin su Malikat Haseenat ne. Babu abinda yafi burin ji a wannan gabar kamar ace ALLAH ya sauki Sohaa dinsa dake nakuda tun a daren jiya lafiya. Duk yanda yake da tarin ayyuka a fada ya kasa fita. Su Sayeed Fayzul-haq ma sun hakura da fitowar tasa yau tun sanda labarin nakudar Iffah'r daya iso kunensu. Sai kowa ya koma fatan saukarta lafiya.
Daga wayar da tai dai-dal da bugawar agogo karfe sha biyu dai-dai na raar litinin din ya wani irin sauke ajiyar zuciya da zama cikin kujerarsa a hankali. Murmushi ne mai sanyi ya subuce ma kyakykyawar fuskarsa. A hankali ya motsa lips dinsa ya ambaci "Alhmdullah"., Sai kuma hawaye suka dan ciko idanunsa. Shi Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed Aliy Qutb ne yau ALLAH ya azurta da kyautar yayan har guda biyu mace da namiji daga jikin yar uwarsa kuma matarsa, farin cikinsa Fhareedah bint Zayyan. A take bakin ciki da kuncin dake tare da zuciyarsa a cikin watanni shidan nan yaji ya wani fada masa daga makoshi zuwa cikin ciki. Babban yatsarsa ya kai a idanun nasa a hankali ya dauke hawayen da sake furta. "Abbie an haifo maka jikoki har guda biyu a rana daya, lokaci daya da ga tilon danka. Insha ALLAHU za'a sake haifo maka wasu biyun kamar haka har sau hudu Abbie na. ALLAH ya gafarta maka, ALLAH ya yafe maka kurakuranka kai da Jaddi da ma duk zuri'ata data musulmi baki daya. Kai da Jaddi da Jaddah ne abin AL'FAHARINA ABBIE NA"……✍️
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (94)
*_MAAB LUXURY HOME._* _Duniyar kayan Kitchen da decoration din gida na keta raini. Ina uwar gida da Amarya, Ku ziyarci shagon mu dake No 22 Ahmadu Bello Way, Kano state. Ko kuyi order daga shafin mu na Instagram @maabluxuryhome. Ko Facebook @maabluxuryhome. Ko Ku nememu a lambar waya *08034631010*._
_____________________
.........Cikin ƙanƙanin lokaci zancen haihuwar Iffah ya karaɗe ƙasar ruman baki ɗaya. Tuni farin cikin kowa ya bayyana, tare da addu'oi ga waɗan nan jinjiraye da ga bakin al'umma. Yayinda Tajwar Eshaan daya matsa a kai masa su ke can rungume da kayansa tsam-tsam a jiki. Jinsa yake a yau ɗin kamar wani sabon mutum, final shima dai ya zama Abbie. Ga yaran sun ɗakko kamanninsa sosai musamman ma mace kamar an tsaga kara an karya da shi, gara namijin yafi rinjaya da Iffah shi kuma. Da kansa ya tauna dabino ya basu tare da musu huɗuba. Duk yanda yaso ganin Sohaa ɗin sa hakan bata yuwuba sai bayan la'asar tai barcinta ta huta sannan. Murmushi ta dingayi kanta a sinne saboda irin kallon nan na ƙasa-ƙasa da yake faman binta da shi. Duk sai taji kunya ta lulluɓeta. Har ya ƙaraso gaban gadon bata yarda ta ɗago ɗin ba sai da ya zauna a kusa da ita ya ɗago fuskar tata da kansa. Bai tsaya wata wata ba kawai ya manne lips ɗinsu waje guda. Sai da yayi yanda yake so da ita ya barta dan kansa sannan ya rungumeta yana jero mata daɗaɗan kalamai masu sanyi da ratsa zuciya da bata san yayi nisa a sani ba har irin haka. Jitai kawai idanunta sun cika da ƙwalla. Dan ita kanta bata san adadin ƙaunar da takema wannan bawan ALLAH ba zuwa yanzun. Tana jinsa daban a cikin daban a duniyarta. Shi ɗin na musamman ne a gareta fiye da yanda yake jinsa na musamman...