Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul - Chapter 8
Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 8: Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 8. _TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
4,485 words
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 90165991
Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
*_14_*
.........Wannan dare darene na tarihin da har abadan Iffah bazata taɓa mantawa da shi ba. Badan wani abu ya faru bayan wanda ya faruba, wanda ya farunne bazai taɓa zama shiɗaɗɗe a zuciyarta ba. Kwana ɗaya tak ta kasance cikin ɗimuwa da tsananin kewar ahalinta. Wanda ta riga ta gama sallamawa ta rabu dasu kenan har gaban abada. Sai dai bayan mutuwarta suzo jana'izarta batare da ko kan gawarta an barsu matsawa ba. Sam babu wani barci koda ɓarawo da yaci galabar ɗaukarta a wannan dare. Hakama abincin da aka biyo bayanta da shi na buɗa bakin azumin da tace batacisa ba. Kuka taci ta ƙoshi har kusan rabawar dare kafin ta miƙe zuwa bayi tayo alwala ta nutsu gaba ɗayanta gaban UBANGIJIN talikai maji roƙon bayinsa. Duk da tsananin tsoro da take a ciki na kasancewa ita kaɗai a katafaren sashen haka ta dinga jarumtar son dannewa a zahiri. Sai dai duk ƙanƙantar motsi yakan saka zuciyarta harbawa da tunanin anzo kashetane. Tana idar da sallar asubahi barci yafa ce ya shirya, dan duk yanda take faman turesa da son ƙin yinsa sai da yakaita ƙasa, dole takai kwance kan lafiyayyen kafet ɗin dake gaban gadon kafin ƙiftawar ido ta fara sauke numfashi....
Barci sosai Iffah tasha na tsahon lokaci mai tsayi da har sai da aka tadata ta fahimci hakan. Ƙyawawan idanunta dake cike da barci ta buɗe da ƙyar akan matar dake tsaye a gabanta kanta a rissine. Babbar mace ce mai shekaru sosai, sai dai shigarta ta tabbatar da cewa ita ɗin bakomai bace sai hadima a masarautar. Amma kuma da alama hadima ce mai babban muƙami da matsayi.... “Barka da safiya ya Zawjata-almilki”. Ta katse tunanin Iffah ta hanyar gaisheta. Yunƙurawa tai ta tashi zaune idonta na a kanta, kanta ta gyaɗa da faɗin, “Mama ina kwana”. Dan shekarun girma na matar ya wuce ta zauna saita gaisheta. Sosai ta ga ruɗewa da kiɗima a idanun matar. Cikin yin waige-waige na tsoron kar wani yaji ta zube ƙasa da rawar harshe. “Ranki ya daɗe na roƙeki dan ALLAH wannan sunan yabar fita a bakinki. Kece uwa a garemu, ke kika cancanta mu kira da sunan bani ƙasƙantacciyar baiwa mai miki hidima ba. Sunana shine Diwa, zaki iya kiran Ama (baiwa), ni shugabar hadimai masu kula da tsaftar sashen Malikat ce. An kawo miki abin karin kumallone tare da wanda zasu shiryaki da hadiman da zasu kasance masu hidima a gareki”. Idanu kawai Iffah ta tsura mata cike da tausayawa. Sai dai komai bata iya cewa ba ta kauda idanunta zuciyarta na ƙuna na raɗaɗin ƙasƙancin da su talakawan ruman ke fuskanta a ƙarƙashin waɗannan masarautu. Hadima Diwa miƙewa tai da sauri ta fita. Mintuna kaɗan sai gata ta dawo tare da wasu mata guda biyu. “Ranki ya daɗe, waɗannan matan sune zasu shiryaki a yanzu”. Yanzun ma iyakarta ɗago ido ta kallesu kawai, sai dai batayi musu ba wajen basu damar fara aikinsu. Amma a zuciyarta ta cigaba da yin addu'a sakamakon harbawa da ƙirjinta keyi da sauri-sauri tamkar mai tsoron tunkarar wani abu. Tsaf suka kwance kitson dake kanta, dogon gashinta da mafi yawan ƴan ƙasar ta Ruman keda ya bayyana. “ALLAH ya ƙara miƙi tsahon rai da lafiya, wannan lokacine na wanka”. Komai Iffah batace musu ba ta miƙe, dan tanabin huɗubar Kaka ne daki-daki. Da zata shiga bayi dakatar da su tai daga ƙoƙarin binta da suke. Hadima Diwa dake gurfane gefe tai saurin faɗin, “Ranki ya daɗe ki basu dama dan ALLAH, dan zasu nuna miki yanda zaki amfani da kayan wankan da aka shirya dominki a ciki, su kuma gyara miki kai kawai su fito”. “Karki damu zanyi da kaina”. Ta faɗa tana mai shigewa kafin ma ta sake cewa wani abu, sai dai bakinta ɗauke yake da addu'a. Wani irin harbawa zuciyarta tayi, tareda sarawar kai lokacin da take sanya ƙafa cikin toilet ɗin sai kace ba dashi tai amfani ba da asubahi, yanzu kuma da su Diwa suka shikago sun gyarasa da ajiye kayan wankan da suka shigo da shi tare da matan, hannu takai saman kanta tana karanto addu'a bayan ta shiga toilet da tayi sannan ta ƙarasa shiga. Shi kansa bayin abin kallone a yanzu fiye da ɗazun, dan yanzu an ƙawatashine da wasu irin fure da candles ta gefen jakuzzie ɗin. Sai wasu nau'inkan ruwan turare da aka ajiye domin tai amfani da shi, sam zuciyarta taƙi aminta da hakan, atake ta dinga ɗaga tasoshin da suke a ciki tana maidasu gefe guda ta hau wankanta tana mai zubda hawayen tausayin kanta dana iyayenta da batasan halin da suke ba a yanzun suma....
Koda ta fito da tunanin samun matan data bari sai taci karo da akasin haka. Domin kuwa wayam ɗakin babu kowa, sai ƙamshi mai daɗi na turaren wuta da aka ajiye ke tashi. Numfashi ta sauke a hankali, badan samun nutsuwa na abinda ke gudana ba. Sai dan samun sassaucin nauyin da zuciyarta tai mata. Kusan mintuna biyar da fitowarta ta gagara tsinana komai, hasalima bata san ta ina zata fara ba. Knocking ƙofar da neman izinin shigowa ya sakata ɗaga idanunta manya takai dubanta, kafin ta bada izinin shigowa tana mai janye idanun nata. Hadima Diwa ta shigo sallama kanta a ƙasa, tun'a bakin ƙofa ta zube bisa gwiyawunta. Cike da tsantseni irin na tsakanin yaro da uban gidansa murya cike da rauni tace, “Ya Zawjata-almilki! Yanzu lokacine na shiryawarki da taimakon waɗan nan mata”. Ta ƙare maganar da nuna bayanta. Iffah dake saurarenta tare da zuba mata ido kallonta ta kai bayan nata, kamar zatai magana sai kuma ta fasa. Tai ɗan shiru na wasu sakanni tamkar mai tunani kafin taja numfashi. “Ai zan iya shirya kaina su barshi kawai”. Ƙasa Diwa ta sake yi da kanta da sake gurfana ƙasa sosai. “Ki gafarceni ya Zawjata-almilki. An basu umarnine, saɓawa kuma a garesu tamkar bijirewa ne?”. Tsantsar tausayinsu da takaici mai gimtse maƙoshi ya sake baibaye Iffah, ta nisa tare da haɗiye abinda ya tokare ƙirjinta tana mai jin-jina kai wa hadima Diwa kawai. Tamkar ƙyaftawar ido matan suka shigo su biyu. Suma dai kallonsu kawai Iffah take cike da tausaya wa. dan cike da girmamawa a gareta suka zube gwiyawunsu a ƙasa domin gaisuwa a gareta kasancewar bana ɗazun bane. “Dan ALLAH ku miƙe”. Ta faɗa cikin wani irin yanayi daya saka matan ɗan ɗagowa suka dubeta. Su ɗin ababen tausayine, amma sai sukaji itace suke tausayi fiye da kansu. Umarninta sukabi duk suka miƙe ɗin, suna maiji da kallonta da matuƙar girma a idanunsu duk da ƙanƙantar ta, dan kuwa itace mafi ƙarancin girma a cikin Zawjata-almilki da aka kawo daular ruman.
Sun mata shiri irin na Zawjata-almilki data isa a kirata da wannan sunan. Dan ƙwalliyar tata ta dace da halittar ƙyaƙyƙyawar surar jikinta da ƙyawunta. Ta cancanci a kirata Malikat Fareedah bayan Zawjata-almilki duk da ƙanƙantar shekarunta. Saboda duk da damuwar dake shimfiɗe a ƙyaƙyƙyawar fuskarta hakan bai hana bayyanar fitar kwalliyar ƙawata kwarjininta da cikar haiba ba. Su kansu hadiman dake zagaye da ita sai faman satar kallonta suke. Bawai dan tafi duk sauran Zawjata-almilki da suka shuɗe ƙyawu ba, kawai natan ya matuƙar ƙayatar dasu ne batare da sun san dalili ba. Ita a karan kanta kallon kanta take dajin tamkar ba ita ɗin bace, bawai dan ƙyale-ƙyalen gold da diamonds da aka ƙawata adon jikin nata da shi ba. Hasalima sune abu na farko da takejin tsantsenin gani a jikinta. Hadima Diwa data sake neman izinin shigowa ta shigo a gabanta ta sake zubewa tana mai satar kallonta itama. Cikin jinjina girma irin na UBANGIJI mai halittar abinda yaso a yanda yaso ta isar da saƙonta kamar haka.... “Ya Zawjata-almilki! Yanzu shine lokacin karin kumallonki”. Iffah da takurar ta fara gundurarta ta saurin tarar numfashinta, “Bana buƙatar cin komai nikam Mama”. Tamkar hadima Diwa zatai kuka, muryarta har rawa take wajen faɗin, “Ki gafarceni ranki ya daɗe. Wannan suna bai dace da niba, jinsa a harshenki zai tabbatar da hukunci mai tsanani a gareni. Hakama rashin cin abincinki a yanzu”. (Ya rabba). Iffah ta ambata a zuciyarta cike da takaici dajin sake tsanar Tajwar Eshaan dama duk mai faɗa aji na masarautar. Bata sake magana ba ta miƙe suka fito da hadima Diwa. Dan matan da suka mata kwalliya tuni sun fice su. Babu kowa a ƙaramin falon da Diwa tai mata jagora, inda aka shirya abinci kala-kala kai kace su goma zasu cisa. Ita a rantama tunani tai ko tare da Tajwar Eshaan ɗinne ma. Sai da taga har takai zaune Diwa na ƙoƙarin fara haɗa mata abincin ta tabbatar domin ita kawai akayi kenan. Komai batace ba, har Diwa ta gama buɗe abincin duka alamar taga wanda take buƙata kenan. Komai kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta, da ga ƙarshe ta nuna mata dafaffiyar madara kaɗai. Diwa tai jimm kamar mai tunani, sai kuma ta saci kallon Iffah ɗin tai saurin maida kanta ƙasa. Iffah da duk ke kallonta ta ƙasan ido ta cigaba da nazarinta harta kammala zuba mata madarar. Gabanta tazo ta ajiye, harta yunƙura zata miƙe ta dakatar da ita. “Bani zan sha ba ai mama naki ne”. A wani irin matuƙar hargitse Diwa ta ɗago tana duban ta, jikinta har wani karkarwa yake. “R....ran...ki ya daɗe w...w..wan nan ai ba hurumina bane”. Iffah data kafeta da idanu ko ƙyaftawa batayi ta janyesu a hankali tana mai miƙewa abinta batare da tace komai ba. Da sauri Diwa ta ƙara gurfana a gabanta tana hurwa. “Ranki ya daɗe dan ALLAH karkice bazakici komai ba, dan komai anan umarnine”. Bata zauna ɗin ba, ba kuma tace komai ba. Sai ma ɗakin da suka fito data nufa zuciyarta cike da nauyi. Batafi zaman mintuna biyarba wasu mata da batako musu kallo biyu ba suka iso da wata hamshaƙiyar riga mai kamar alƙyabba daga Malikat. Tare da umarnin tafiya da ita. Batai musu ba, dan a nata tunanin Malikat Bushirat suke nufi, sai dai zuciyarta ta kasa nutsuwa. Addu'a ta shiga ambato a zuciyarta har suka kammala saka mata ƙawatacciyar rigar alƙyabar mai tsananin ado da ɗaukar idanu, zasu kunna mata turaren wuta da suka shigo da shi a burner tai saurin dakatar da su. Kallon juna sukai, kafin ɗaya tai saurin faɗin cikin ƙanƙan da kai, “Ya Zawjata-almilki wannan umarnine daga Malikat”. Yamutsa fuska Iffah tai tana mai kallonta, kallo irin na wannan bata san wacece autar Babiy ba ta ɗauke kai. A karon farko tun shigowarta gidan tai magana da harshen ƙarfin zuciya ta ajiye rauninta a gefe. “Ni kuma wannan umarnina ne bana buƙata. Sai kumuje umarni na gaba”. Babu wanda a cikinsu baiji yayi sumar wucin gadi ba. Sai dai wani irin kwarjininta da jin shakkarta ya gama ɗarsuwa a zukatansu lokaci guda.. Iffah dake jin jininta na wani irin tsitstsinkewa ta sake dubansu da niyyar magana, tamkar wadda aka jefa da narkakken ƙarfe taji yafff! A ƙirjinta. Da sauri ta dafe ƙirjin tana mai rumtse idanunta. Rawar da jikinta ya farayi ya sata zubewa ƙasa tana mai ƙoƙarin ambaton sunan ALLAH, amma hakan ya gagara, dan tamkar an naɗe zuciyartane da harshenta a lokaci guda......
Har rige-rigen fita hadiman nan sukeyi jikinsu na matuƙar rawa. Diwa dake zaune a falo tana jiran fitowarsu ta miƙe da sauri tana tambayar lafiya? Babu wanda ya saurareta a cikinsu suka fice. Hankalintane ya tashi, tai kamar zata bisu sai kuma ta fasa ta nufi ɗakin da Iffah take. Wani irin mugun bugawa ƙirjinta yay damm. Innalillahi..... ta shiga ambata dayin kan Iffah dake ta faman juye-juye a ƙasa, cikin ƙanƙanin lokaci ta jiƙe sharkaf da zufa tamkar an watsa mata ruwa koma an tsamota a ciki. Harta kusa kai hannu kanta sai kuma taja baya da sauri cikin tsoro. Ina bai kamataba, matsayinta na hadima hanunta ya taɓa Zawjata-almilki. A daburce tai waje da nufin isar da saƙo ga Malikat Bushirat duk da bata da tabbacin samun iso cikin sauƙi........✍
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 90165991
Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
*_16_*
........Cikin ƙanƙanin lokaci labarin abinda ke faruwa da Zawjata-almilki ta uku ya gama gauraye daular ruman. A take ko'ina yay tsit sai ƙus-ƙus da maganar ido kawai. Sauran Zawjata-almilki kuwa guda biyu dake gidan dama kafin kawo Iffah tuni sun sake shiga tsantsar tashin hankalin da yafi wanda suke ciki. Su dai dama rayuwa suke cikin jiran tsammanin isowar mutuwarsu. Ko lokacin da aka sanar musu sake ɗaura auren Tajwar da wata matar tsantsar tausayin kansune kawai ya baibayesu, yanzu kam jin halin da matar da aka kawo jiya take ciki ya tabbatar musu suma mutuwarsu tunkarosu take sakeyi kenan.......
Duk wata tuhumar data dace akan hadima Jaza da sauran hadimai biyu da sukaje ɗakin Iffah suma da aka gano anyi amma sunƙi faɗar gaskiyar wanda ya sakasu, sai cewa suke Diwa ce. Yayinda Diwa ke rantsuwa da ALLAH tana kuka akan ƙarya suke mata ita bata san komai ba. Iya jigatuwa sun jigatu har takai numfashi da ƙyar sukeyi saboda azabartawar da ake musu. Sanin rayuwarsu akafi buƙata a yanzu sama da mutuwarsu yasa hadiman kurkukun dake a cikin daular ruman tsagaita musu. Amintaccen hadimin Malikat Bushirat ya koma ya sanar mata halin da ake ciki. Shiru kamar bazatace komaiba. Sai kuma ta dubi Jasrah da har yanzu ke tare da ita ta ɗauke kanta. Jasrah data fahimci mi ƴar uwar tata ke nufi takai dubanta ga hadimin. “Ghazi! A cigaba da tsaurara musu tsaro har zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu”. “ALLAH ya ƙara miki lafiya an gama”. Ya faɗa da tsantsar girmamawa yana mai rissinawa da gyara takobin hanunsa ya fice.......
*_ZAWJATA-ALMILKI_*
Tun Iffah na iya motsa jikinta da furta kalmar bakinta har hakan ya gagara numfashinta ya fara neman barin jikinta. Ga dai masu magani mata rufe a kanta mazan na daga waje suna haɗo duk abinda ya dace amma babu alamar wani canji sai ma ƙwaɓewa da komai ke nemanyi. Tun ana ƙirga awannin iya shawo kan matsalar har komai ya fara firgita kowa. Daular ruman tayi tsitt babu mai ƙwaƙwaran motsi a cikinta. Sautin fitar kiran salla ma dan ya zama dolene. Koda aka idar da salla ma sake komawa zaman jigum-jigum akayi domin kuwa abinda bai taɓa faruwa a tarihin masarautar bane ya faru. Tajwar Eshaan bai fito sallar zuhur ba yau. Hakama da la'asar. Magrib ma ta shiga babu wanda yaji motsinsa. Zuwa lokacin kuma akan Iffah an zubama sarautar ALLAH idone wadda ta girma ta ɗaukaka. Dan kuwa tana a shimfiɗene jiki duk ya ɗashe tamkar wadda ta ƙone gurin yay ja kafin ya tashi. Kaɗan-kaɗan numfashinta ke fita wanda shine kawai ya tabbatar da tana a raye bata mutu ba. Masu magani kowa yayi iya iyawarsa sun koma gefe ana jiran ikon ALLAH kuma. Ana idar da sallar la'asar Malikat Bushirat ta bada izinin maida Iffah sashenta.....
Kamar yanda Malikat Bushirat ta bada umarni an maida Iffah sashenta, a kuma cikin ɗakin barcinta da babu wani mahaluki daya taɓa shiga bayan Tajwar Eshaan da Jasrah. Hakan ya bama dukkan hadiman sashen mamaki da tabbatar da lallai wannan Zawjata-almilki ɗin tana da wata daraja ta musamman ga Malikat. Dan kaf Zawjata-almilki da suka rasa rayuwukansu a gidan babu wanda ya iya ganin makamancin damuwar Malikat Bushirat irin ta yau. Ƙarin tabbaci har hawaye sai da ta share na tsagwaron tausayin Iffah. Lallai halin da Iffah ke ciki ta cancanci duk mai imani ya zubda mata hawaye, dan sauran Zawjata-almilki na baya mutuwarsu kawai akeji bayan kaisu turakarsa. Amma ita ko kaitanma ba'ayiba, a kwana ɗaya tak da tai a gidan batare da an kammala gagarumin taron bikin da aka shirya ba dominta gata a halin da gara mutuwa da shi... Bayan idar da sallar isha'i Malikat Bushirat na hakimce a katafaren falonta na uku Malikat Ashwaq ta iso da tawagar hadimanta duba Iffah. Malikat Ashwaq itace mace ta farko ga marigayi Tajwar Haysam ibn Abdull-majeed. Hamshaƙiyar mace ce data isa take kuma amsa suna Malikat. A ƙa'idar Daular ruman matar data haifi yarima mai jiran gado a cikin matan sarkice kawai ake kira da Malikat. Mafi yawanci kuma ana samu ne daga matan farko. Sai dai ga Tajwar Haysam hakan bata faru ba. Dan matarsa ta farko Ameera Ashwaq bata taɓa haihuwa ba kamar sauran matansa, tadai taɓa ɓarin ciki na wata huɗu daga shi kuma bata ƙara ba. A zahiri mace ce isashiya mai baza mulkin da yafi na kowace mace a gidan bayan malikat Bushirat, amma kuma bata da damuwa sam. Ƙaryarka kace ga wani mugun halinta na zahiri saboda tasan kanta. Rana ɗaya aka ɗaura aurenta dana Malikat Bushirat matsayin Zawjata-almilki. Amma itace uwargida. Duk da mulkinta Malikat Bushirat ta fita, ta kuma fita zafi da nuna kishi a zahiri dan sam ita bata da haƙuri, hakan yasa ake matuƙar jin tsoronta fiye da kowace Zawjata-almilki, dan Malikat Bushirat ba kanwar lasa bace ƙwarai da gaske, sai dai mace ce mai son ƙyautatama wanda yay mata da na ƙasa da ita, hakan ya taimaka mata samun soyayyar hadiman gidan. Haihuwar Miran (Yarima) mai jiran gado Eshaan tasa dole sunan Malikat ya koma kan Malikat Bushirat. Wato Sarauniya Bushirat kenan. Amma duk da haka sai Mahaifiyar Tajwar Haysam mai suna Malikat Haseena ta bada umarnin cigaba da kiran Ashwaq da suna Malikat Ashwaq. Hakan ya ƙona ran Malikat Bushirat, sai dai babu yanda zatayi. Amma ta sake tsananta kishin da takema Malikat Ashwaq ɗin fiye da da, yayinda ita kuma Malikat Ashwaq ke nuna tamkar babu komai a zahiri, amma a baɗini hummm.... Koda ta shigo Malikat Bushirat bata nuna tasan da shigowar tata ba. Sai dai ta ɗagama hadimanta yatsu biyu da ya sakasu rige-rigen fara barin falon. Zaune Malikat Ashwaq takai bisa ɗaya daga cikin kujerun falon tanama nata hadiman nuni dasu fita suma. Da sauri suma duk suka fice aka barsu su biyu kawai. A hankali Malikat Ashwaq ta ɗan sakin murmushi daya danne zafin yarfin da Malikat Bushirat ɗin tai mata, ita ta fara gaisheta da tambayar ya mai jiki?. A daƙile Malikat Bishirat da tai kamar zata basar ta amsa mata cike da isa. Nanma Malikat Ashwaq dai murmushi kawai tayi da haɗiye ɓacin ranta. Sosai ta nuna tausayi akan Iffah ta kuma mata doguwar addu'a da bada shawarar mizai hana a kira likita ma ya duba ta ko wani abune daban da wanda ake tunani. Karan farko Malikat Bushirat ta ɗakko manyan idanunta tai mata kallon tsakkiyar ido. Cikin yamutsa fuska taja numfashi da fesarwa, “Haihuwar magajin Daular ruman daga tsatson Malikat Bushirat rubutacciyar ƙaddara ce da duk yaƙi da gwagwarmayar masu son daƙile hakan. A baya basuci nasara ba, Taya suke tunanin samunta a yanzu kan _Saifulmulk_ ɗi na?. Kamar yanda aka haifesa daga matsayin gudan jinin Shahan-shan, Tajwar Haysam ibn Abdul-majeed. Shima haka za'a samar da Ɗa daga gudan jininsa da izinin UBANGIJI masu lissafi su fara...” Muƙutt Malikat Ashwaq ta haɗiye yawun dake neman kufce mata, a zahiri kuwa murmushi ta saki da ɗan girgiza kanta. Batare da tace komai ba tai yunƙurin miƙewa domin barin ɗakin tana mai ƙoƙarin danne zuciyarta dake yunƙurowa. Har tayi taku biyu sai kuma ta tsaya, batare data juyi ba ta saki murmushi. “Idan dai har Eshaan ya kasance gudan jinin Shahan-shan ne babu gauraye, muma irin wannan fatanne a bakunanmu garesa kasancewarmu uwaye a wajensa. Fatan alkairi da samuwar lafiya ga Zawjata-almilki.....” Har tsakkiyar kai kalaman ƙarshe na Malikat Ashwaq suka daki zuciyar Malikat Bushirat, sai dai kafin ta samu wani damar fassarasu sallamar Ameera Danish-Ara da suka kusan kiciɓus da Malikat Ashwaq ya dakatar da ita. Itace mata ta uku ga Tajwar Haysam. itama da tata tawagar hadiman. Kallon juna sukai da Malikat Ashwaq, Ameera Danish-Ara ta saki wani malalacin murmushi a kaikaice. Sai kuma ta matso cikin girmamawa ta gaishe da Malikat Ashwaq ɗin datai mata kallo guda ta ɗauke kanta. Amsa mata tai cike da ƙasaita, kafin ta matsa ta bata hanya ta shige, itama ta fice tawagarta biye da ita.
Saɓanin Malikat Ashwaq ita ta samu tarba daga malikat Bushirat. Dan duk da take mata itama ga Tajwar kuma Malikat Bushirat kishiya a gareta hakan bai hanata risinawa ta gaidata ba da matuƙar girmamawa tana mai tambayar jikin Iffah. Malikat Bushirat dake kishingiɗe har yanzu a yanda Malikat Ashwaq ta barta ta amsa mata da sassauci mai haɗe da jimami. Cike da makirci Ameera Danish-Ara ke nuna tsantsar tausayin Iffah tana mai yin ALLAH wadai ga duk mai hannu akan waɗan nan al'amura. Malikat Bushirat taɗan jinjina kai irin na ƙasaitattun mata da yamutsa fuska kaɗan, a saman lips ta furta, “Nagode”. A kaikaice Amera Danish-Ara ta ɗan saƙi murmushi tare da harararta ta ƙasan ido. A zahiri kuwa zamanta ta gyara tare da risinar da kanta. “Wannan abunda ya shafemune ai gaba ɗaya ranki ya daɗe. Domin Zaki ɗammu ne, fatammu dai ALLAH ya warware waɗannan al'amura cikin sauƙi”. Har cikin zuciya Malikat Bushirat taji daɗin kalaman Amera Danish-Ara, dan haka a lips ta amsa da “amin” tana mai sauke ajiyar zuciya, dan bata cika samun damuwa da ita a gidanba tunma sunada ƙuruciya. Amera Danish-Ara mace ce mai tsananin kissa da ba lallai a lokaci guda ka iya gano wacece ita ba. Duk da kasancewar ita Zawjata-almilki ce a daular ruman zakasha mamakin irin girman da take bama Malikat Ashwaq da Malikat Bushirat a gidan a zahiri tunda ta shigo. Kai hatta da Amera Haifah dake amarya kuma ƙarama a cikinsu ita bata taɓa bari saɓani ya shiga tsakaninsu ba a zahiri. Wannan halin nata yasa sanda surukarsu Malikat Haseena ke da lafiyar ƙafa take sonta da janta a jiki fiye da su Malikat Bushirat. Wani lokacin har kwatance take musu da halin Amera Danish-Ara ɗin wai suyi koyi ta fisu dattako. A yanzu haka da take zaune babu lafiyar ƙafa Ameera Danish-Ara ɗin tafi kowa sintirin zuwa dubata da mata hidima a zahirance, duk da itama Malikat Bushirat na kamantawa sai dai babu ruwanta da sai wani ya gani yace tayi. Shiru falon ya ɗauka na wasu mintuna, Amera Danish-Ara na son taga Iffah babu fuska ga Malikat Bushirat, dole ta miƙe cikin ƴan kame-kame tana tambayar ko Amera Haifah tazo kuwa?. Kallon ƙasan ido Malikat Bushirat tai mata tana ƙara tsuke fuska, dan ita duk yanda take da zafi babu wanda zaice ga ranar data zauna maganar wani a cikinsu koda da su Jasrah ne kuwa. A ganinta idan tai hakan sunma isa kenan a wajenta. Murmushin yaƙe Amera Danish-Ara tayi cike da basarwa. Sai dai ƙasƙantaccen kallon da Malikat Bushirat tai mata ya matuƙar sokar mata zuciya. Taɗan risina da faɗin, “Na barki lafiya ranki ya daɗe”. Kai kawai Malikat Bushirat ta jinjina mata batare data ko ɗago ba. Amera Danish-Ara ta cije baki da ficewa hadimanta dake jiranta daga falo na biyu suka take mata baya.
Sam Amera Danish-Ara bata gaban Malikat Bushirat, kalaman Malikat Ashwaq ne keta faman mata kaikawo a zuciya musamman na ƙarshe. (Fatan alkairi da samuwar lafiya ga Zawjata-almilki) waɗan kalamai bakwai a cikin tarin kalaman Malikat Ashwaq sunfi komi tsayawa Malikat Bushirat a zuciya. Dan kuwa tana fassarasu ne da wani abu daban ne. Haka manyan mutanen masarautar suka cigaba da shigowa duba Iffah daga sassa daban-daban na gidan. wasu iyaye ne, wasu yayu, wasu ƴaƴa harma da kakanni maza da mata duk da basu samun damar shiga ciki iyakarsu wajen Malikat Bushirat. Bata damu kanta ba sai da dare yaja. Koda hadimanta suka dawo sallamarsu tai dan tafi buƙatar kaɗaici a yanzu saboda son ƙara tunani akan kalaman Malikat Ashwaq da suka gagara haɗiyuwa a gareta. Da kuma nazartar kowa daya shigo sashen nata domin duba Iffah. Tun tana a zaune har takai ta miƙe tsaye hannayenta goye da bayanta tana faman kaikawo tamkar mai safa da marwa..........✍
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 90165991
Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA