Kenza eBookz

Daudar gora complete - Chapter 11

Daudar gora complete - Chapter 11

Daudar gora complete Chapter 11: Daudar gora complete Chapter 11. A dai-dai lokacin da Diwa ke ƙoƙarin son isa gaban Malikat Bushirat ƴan uwa ga Malikat…

2,694 words

A dai-dai lokacin da Diwa ke ƙoƙarin son isa gaban Malikat Bushirat ƴan uwa ga Malikat ɗin na can sun doshi sashen Iffah domin kai kayan al'ada da akema kowace Zawjata-almilki da zata saka kafin a wuce da ita wajen taron buɗar amarya da duk wani babba mai faɗa aji a daular ruman zai halarta, wanda kuma akaf matan Tajwar Eshaan ɗin da suka shuɗe huɗun farko ne kawai akaima wannan bikin sai Iffah a yanzun. Anan zata san kowa, kowa kuma ya santa. Tafe suke tare da rakkiyar hadimai masu ɗauke da wata lafiyayyar rigar alƙyabba mai tsananin ɗaukar hankali da aka ɗinkata ta musamman domin Zawjata-almilki da kuma wannan rana. Sai sauran kayan ado irin na hamshaƙan mata da akayisu da zallar zinare da diamond. Sun ɗanyi mamakin rashin samun kowa a sashen, saboda sanin tunda safe an turo hadimai da zasu mata hidima. Yanayin tsaftar sashen kuma ta tabbatar musu hadiman sunzo. Tunanin ko itace ta sallamesu ya sakasu ture zancen a zukatansu suka bama cikin hadiman umarnin wata ta nema musu iso. Har hadimar ta nufi ɗakin da aka kai Iffah jiya ta tsaya cakk sakamakon wani irin kakari da sukeji tare da ɓarin fashewar abubuwa. Su dukansu dubansu suka maida ga ƙofar, da alamun mamaki ɗaya daga ciki ta sake bama wata hadimar umarnin zuwa ta duba. Minti ɗaya baima cika da shigar hadimar ba ta dawo a guje numfashinta na fita da ƙyar tana nuna ɗakin da faɗin, "Z...Z....Zawjata-almilki!......" A kusan tare suka afka ciki. Su dukansu babu wanda bai firgita da ganin Iffah dake layi hanunta na dama dafe da ƙirjinta tana laluben hanya dana haggu ba. A dalilin laluben ne taketa faman zubda abubuwan da aka ƙawata adon ɗakin da su. Sakamakon hakan kuma duk ta jima hanunta ciwo sai jini yake yi. Da zafin nama ɗaya daga cikin matan nan ta riƙota cikin jikinta suna mai ambaton sunan ALLAH a tare. Ganin yanda ta jiƙe sharaf ga jikinta yayi jajur abinka da fara sai hankalinsu ya ƙara tashi. A fisge Iffah ta damƙo hanun matar ta haɗa da nata takai kirjinta tana fadin, "Ummu wuta, jikina zai babbake Ummu ki sakani a kanƙara dan ALLAH karna ƙone. Zan mutu Babiy wuta tana cin jikina...." Gaba ɗaya kalamanta sake ruɗasu sukayi. Duk sun daburce sunma rasa miya kamata su mata. Dan wadda ke rike da ita har hucin zafin takeji a nata jikin itama. Ƙaramar cikinsu ce tai ƙarfin halin fita da hanzari tana mai musu nunin tana zuwa. Cikin sauri tamkar zata kifa ta nufi sashen Malikat Bushirat. A yanayin data shigo ya saka Malikat ɗaga yatsun hanunta dake ƙawace da jan lalle da adon zabban zinare biyu. Tamkar ƙiftawar ido duk hadiman dake zagaye da ita suka fice. Zaune ta tashi da ƙyau, idanunta akan ƴar uwar tata. Cike da ƙasaita ta ambaci sunanta akan lips "Jasrah!". "Na'am Bari-Hamshira". "Mike faruwa kika shigo kamar an koroki". "Afuwan. Duk abinda kikaga ya koro ɓera daga wuta tofa yafi wutar zafi ne. Wai kin san kafin zuwanmu har an kai mata rigar alƙyabbar buɗar amarya ta saka, akwai babbar matsala Bari-Hamshira, ga yarinyar mutane can a wani mawuyacin hali". "Kamar ya?". Malikat Bushirat ta faɗa tana mai miƙewa zaune sosai da sake ware ƙyawawan manyan idanunta akan Jasrah. "Bari-Hamshira ba lokacin neman ba'asi bane wannan, lokacine na neman hanyar ceto ran yarinyar mutane. In ba hakaba itama zasu kashe mana ita kamar sauran na baya...." Lokaci guda idanun Malikat Bushirat suka kaɗa sukai jazur. A kallo guda zaka fahimci ƙololuwar tashin hankalin daya tsargata. Da ƙyar ta iya ɗaukar wayar landline dake gefenta hanunta na rawa, ƴan danne-danne tayi kafin ta miƙama Jasrah. Da hanzari Jasrah ta amsa. Sanin kowa Malikat zata iya nema a yanzun yasata kai tsaye ambaton sunansa. "Ghazi! A tattaro duk wani mai magani dake a daular ruman dama wajenta yanzu zuwa sashen Zawjata-almilki ta uku". "An gama ranki ya daɗe". Aka faɗa daga can cike da tsantsar girmamawa....

★★_________★★

Ƙarar marin da azabarsa ya saka hadimar zubewa ƙasan lallausan carpet ɗin dake katafaren falon. Sosai jikinta ke tsuma tamkar mazari. Ga hawaye har rige-rigen sauka suke a fuskarta. Kanta ta shiga girgizawa da sake gurfana a gabanta sosai tamkar mai neman gafara... "Ki gafarceni uwar-gijiya. Wlhy nayi iya yina domin ganin mun mata turaren amma ta nuna sam bata aminta ba. Wannan ba irin waɗan can na baya bane, akwai wani sirri mai razani a cikin ƙwayar idanunta da taurin ka...." Saukar wani sabon bahagon marin ya hanata ƙarasawa. Ƙara dafe kuncin tai da hannu bibbiyu. "Ina neman gafara a gareki bisa kuskurena Uwa- gijiya..." hadimar ta faɗa da sauri tana mai ƙoƙarin gumtse kukan dake son kwace mata dan harga ALLAH marin ya shigeta matuƙa. Matar dake harɗe bisa kilisa tana cin inibi cike da ƙasaita irin ta masu isa ta ɗaga idanu kaɗan ta dubi wadda ke tsaye kusa da ita tana faman hura hanci, wanda marin ma itace ta yisa daman. ƙyawawan idanunta ta juya a fuskar amintacciyar hadimar tata, sai kuma ta janyesu ta maida a yanda take tamkar batasan mike faruwa a wajen ba. Cike da girmamawa hadimar ta ranƙwafa. "An gama Uwar-gijiyata. Umarninki wajibine a garemu". Kamar yanda bata motsaba a yayinda hadimar ke kashe fuskar waccan da mari da neman afuwa a yanzu ɗinma haka. Ga hadimar tata hakan ba sabon abune a gareta, dan haka bata damu ba. Sai ma nuna waccan hadimar dake gurfane tana sharar hawaye tai da ɗan yatsa da kakkausan harshe. "Shugabata bata yafiya, bata ɗaukar kuskure koda zaka shekara dubu kana mata hidima kuskurenka ɗaya bazai taɓa fansarka ba". "Innalillahi wa-inna ilaihirraji'un" Hadimar dake a gurfanen ke faɗa cikin rawar jiki, ta sake kaiwa gurfane gaban Uwar-gijiyar tasu tana kuka da hurwa irin ta masu neman afuwa. Amma ko kallo bata ishetaba. Sai ma amintacciyar hadimar nan tata ce ta kora ta waje tana mai sake kaimata mari......

★★......

Cikin ƙanƙanin lokaci duk wasu masu ƙarfin faɗa aji akan magani suka rufu a sashen Iffah da komai ke ƙara rikicewa. Dan takai ƙoƙarin ma yaga kayan jikinta take saboda azabar da takeji a jikin. Matan nan dake matsayin ƙanne ga Malikat Bushirat sai faman zuba mata ruwa mai azabar sanyin da taketa ambata suke suna hawaye amma tamkarma basa zuba matan. Fatarta kam tayi wani irin masifar ja kai kace za'a taɓata ta ɗashe ne da kanta. Dan tayi wani luguf-luguf tamkar an dafa ganda taji wuta. Abin tausayi duk yanda Iffah ke son ambaton sunan ALLAH bisa a zabar da takeji hakan ya gagari harshenta. Sam ƙwaƙwalwarta da zuciyarta ma sunƙi connecting wajen taimaka mata. Sunan Ummu da Babiy kawai take ambata akan su zo su taimaketa zata ƙone......

*_MALIKAT BUSHIRAT_*

Diwa da jikinta ke tsuma kamar mazari ta zube gurfane agaban Malikat Bushirat data saka aka nemota tun kafin a sanar mata dalilin kiran. Gaisuwa ta mika cike da tsantsan da kai. Sai dai daga Jasrah dake faman kai kawo a falon har Malikat babu wanda ya amsa mata. Sai tarar numfashinta da Jasrah tayi tare da jeho mata tambayar data nema sakata sakin fitsari a bujenta. "Bisa umarnin wa kuka aikata, kuma ke da su wanene?" Kanta ta shiga girgizawa jikinta na rawa. "Wlhy ranki ya daɗe bansan komaiba, taya za'a haɗa baki dani a aikata wannan kuskuren. Sam ban san badaga nan aka turasuba, kai tsaye ma suka shiga wajen Zawjata-almilki batare da sun jira na musu iso ba saboda bana kusa. Amma wlhy wlhy banida wani alaƙa ko sani akan wanda ya turasu, hasalima nayi iya ƙoƙarina na ganin na kama ko ɗaya a cikinsu amma hakan ya gagara saboda hankalina ya kasu biyu gashi sai ni kaɗai a wajen". "Ƙarya kike yi? K kina ina suka shigan?". "Na rantse da UBANGIJI mai zartar da mutuwa akan kowa iya gaskyata kenan ALLAH ya baki yawan rai, ina kan tattare abincin da aka shirya mata ne da bata ci ba ma". "Zaki iya gane hadiman?". "Sosai ALLAH ya taimakeki". "Kafin cikar awa biyu muna buƙatar ku anan". "Da ikon ALLAH hakan ce zata tabbata". Hadima Diwa ta faɗa tana miƙewa da rawar ƙafa ta fice. Sai lokacin Malikat Bushirat ta ɗago idonta, dan tunda Diwa ta shigo bata sake motsawa a yanda take ba, duk maganar da sukai da Jasrah ne. "Bari-Hamshira! Karsu kashe yarinyar mutane itama. A daren jiya harna fara murnar ALLAH yasa zuwan wannan yarinya alkairine garemu, ALLAH yasa itace zata zama mana hasken da zai haska duhun dake zagaye da mu saboda ganin rashin tsoro a ƙwayoyin idanunta, Amma yanzu a wani ɓangaren inajin matuƙar tsoron kar muna akan dokin zaton wuta a maƙera ne kamar yanda mutanen gari ke ma Zaki. dan gaskiya a yanzu gaba ɗaya komai neman ƙwacemun yake...." Wani irin rumtse idanu Malikat Bushirat tayi mai nuna alamar jin ɗacin zancen, sai dai kuma a duba na gaskiya ƴar uwarta gaskiya ta faɗa, kuma da itane kawai take iya tattauna irin waɗan nan matsalar tata taji sauƙi a ranta duk da ba ita kaɗai bace ƴar uwarta mafi kusaci. Sai dai Jasrah itace autarsu, ta kuma rayune a hanunta tamkar itace ta haifeta, dan haka tasan bazata taɓa jifan tilon ɗanta da sharri ba domin taji daɗi kamar yanda maƙiyansu keyi. Ita a karan kanta mahaifiyarsa a kullum zuciyarta takan ɗarsa mata kodai gaskiyane da sanin bahagon ɗan nata mai wahalar sha'ani da fahimta ake kashe yaran mutane? Saboda al'amarin akwai matuƙar rikitarwa da ban mamaki a cikinsa, amma a yau tana fatan a wannan gaɓar su samu wani haske.....

★★________________★

Kai tsaye sashensu na hadimai Hadimar nan ta tasa ƙeyarta, sai dai suna gab da shiga ta hango Diwa da wasu hadimai maza masu ƙarfin faɗa aji a cikin dogaran sashen Malikat Bushirat suna tattaro hadimai. Da sauri taja burki tare da damƙo hanun hadimar baya. "K dakata, bana raba ɗayan biyu ku ake nema kuwa". Sake ruɗewa hadimar tayi, jikinta sai faman rawa yake gab-gab abin tausayi. "Shugaba Azwa ki taimakeni". "Na taimakeki ni kuma na tozarta. Kinga Jaza babu wannan maganar, ki ƙarasa garesu zanyi duk abinda ya dace naga kin ƙuɓuta, sai dai ki sani zaki bani wani kaso a cikin dukiyarki. Kiyaye harshenki akan amsa laifin dake kaɗai ya shafa shine tseratar da kanki. Kuskuren ambaton sunana kona uwar-gijiya shine mutuwarki". "Na yarda wlhy, zanma iya mallaka miki komai da nake da su shugaba Azwa". Jajayen haƙwaranta ta washe. Tare da kaɗa kai tamkar ƙadangaruwar data hango mage. "Baki da matsala, hatta ga uwar-gijiya ma zaki iya tsira, dan haka faɗamin inda kike ajiya". Sosai Jaza ta aminta da maganar Azwa. Dan tasan ita ɗin amintacciyace ga uwar-gijiyar tasu. Domin duk wani aikin sharri sune suke mata shi a cikin Daular Ruman. Sai dai bata raba ɗayan biyu akwai ire-irensu da yawa a ƙarkashin ikonta..... "Yauwa ga ɗaya nan a cikinsu". Cewar Diwa data hango Jaza na rabe-raɓe. A take hadiman maza suka tasa ƙeyar Jaza tare da Diwa dake biye da su. Kaf hadiman da abin ya faru a gaban su duk da basu san ainahin abinda ya faru ba tausayin Jaza da sanin ta shiga uku ne keta musu kaikawo a cikin zukata......

*_MALIKAT BUSHIRAT_*

Bayan wasu mintuna da batako nuna alamar tasan da isowar su Diwa ba ta ɗago ƙyawawan idanunta da tsantsar damuwa ta bayyana a cikinsu. Da sauri Diwa da hadima Jaza suka sake risinar da kawunansu jikunansu na tsuma. Kallonsu take tamkar mai neman amsar abinda ke ranta a cikin jikinsu, kusan minti guda da wasu mintuna ta janye a hankali ta maida ga Jasrah, sake janyewa tai ta sake maidawa ga amintaccen hadiminta dake buƙatar umarninta. "Bayan mintuna goma, a tabbatarmin da abinda nake buƙatar ji daga garesu". "An gama Uwa goya marayu". Ya faɗa da tsantsar girmamawa yana mai zabga ma su Diwa shimfiɗeɗiyar bulalar hanunsa a gadon baya. A zabure suka miƙe su duka suna mai sosa bayan nasu kowanne idonsa cike taf da ƙwalla. Ƙeyarsu ya tusa suka fice, Diwa na kuka da rantsuwar bata san komaiba ita..........✍

🤦🏻Nama rasa abin faɗa🙆🏻.

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 90165991

Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

*_16_*

........Cikin ƙanƙanin lokaci labarin abinda ke faruwa da Zawjata-almilki ta uku ya gama gauraye daular ruman. A take ko'ina yay tsit sai ƙus-ƙus da maganar ido kawai. Sauran Zawjata-almilki kuwa guda biyu dake gidan dama kafin kawo Iffah tuni sun sake shiga tsantsar tashin hankalin da yafi wanda suke ciki. Su dai dama rayuwa suke cikin jiran tsammanin isowar mutuwarsu. Ko lokacin da aka sanar musu sake ɗaura auren Tajwar da wata matar tsantsar tausayin kansune kawai ya baibayesu, yanzu kam jin halin da matar da aka kawo jiya take ciki ya tabbatar musu suma mutuwarsu tunkarosu take sakeyi kenan.......

Duk wata tuhumar data dace akan hadima Jaza da sauran hadimai biyu da sukaje ɗakin Iffah suma da aka gano anyi amma sunƙi faɗar gaskiyar wanda ya sakasu, sai cewa suke Diwa ce. Yayinda Diwa ke rantsuwa da ALLAH tana kuka akan ƙarya suke mata ita bata san komai ba. Iya jigatuwa sun jigatu har takai numfashi da ƙyar sukeyi saboda azabartawar da ake musu. Sanin rayuwarsu akafi buƙata a yanzu sama da mutuwarsu yasa hadiman kurkukun dake a cikin daular ruman tsagaita musu. Amintaccen hadimin Malikat Bushirat ya koma ya sanar mata halin da ake ciki. Shiru kamar bazatace komaiba. Sai kuma ta dubi Jasrah da har yanzu ke tare da ita ta ɗauke kanta. Jasrah data fahimci mi ƴar uwar tata ke nufi takai dubanta ga hadimin. "Ghazi! A cigaba da tsaurara musu tsaro har zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu". "ALLAH ya ƙara miki lafiya an gama". Ya faɗa da tsantsar girmamawa yana mai rissinawa da gyara takobin hanunsa ya fice.......

*_ZAWJATA-ALMILKI_*

Tun Iffah na iya motsa jikinta da furta kalmar bakinta har hakan ya gagara numfashinta ya fara neman barin jikinta. Ga dai masu magani mata rufe a kanta mazan na daga waje suna haɗo duk abinda ya dace amma babu alamar wani canji sai ma ƙwaɓewa da komai ke nemanyi. Tun ana ƙirga awannin iya shawo kan matsalar har komai ya fara firgita kowa. Daular ruman tayi tsitt babu mai ƙwaƙwaran motsi a cikinta. Sautin fitar kiran salla ma dan ya zama dolene. Koda aka idar da salla ma sake komawa zaman jigum-jigum akayi domin kuwa abinda bai taɓa faruwa a tarihin masarautar bane ya faru. Tajwar Eshaan bai fito sallar zuhur ba yau. Hakama da la'asar. Magrib ma ta shiga babu wanda yaji motsinsa. Zuwa lokacin kuma akan Iffah an zubama sarautar ALLAH idone wadda ta girma ta ɗaukaka. Dan kuwa tana a shimfiɗene jiki duk ya ɗashe tamkar wadda ta ƙone gurin yay ja kafin ya tashi. Kaɗan-kaɗan numfashinta ke fita wanda shine kawai ya tabbatar da tana a raye bata mutu ba. Masu magani kowa yayi iya iyawarsa sun koma gefe ana jiran ikon ALLAH kuma. Ana idar da sallar la'asar Malikat Bushirat ta bada izinin maida Iffah sashenta.....

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull