Kenza eBookz

Daudar gora complete - Chapter 20

Daudar gora complete - Chapter 20

Daudar gora complete Chapter 20: Daudar gora complete Chapter 20. ★Sam Iffah dake cikin wani yanayi na tsananin faɗuwar gaba da sanyin gaɓɓai sakamakon…

3,144 words

★Sam Iffah dake cikin wani yanayi na tsananin faɗuwar gaba da sanyin gaɓɓai sakamakon mummunan mafarkin da tai akan su Babiy a barcin zuhur daya figeta bata san mi ake ba saboda bata fita ko'inaba yau iyakarta ɗakinta. Yanzu hakama da aka idar da sallar la'asar tana tsumayen Daneen Ammarah ne kamar yanda ta saba, dan duk yinin yau ma basu haɗu ba tun bayan idar da sallar asuba dai data fita ta gaishesu kamar yanda ta saba ita da Malikat Haseena. Hadimai dai sun kawo abinci tare da saƙon gaisuwa daga Daneen Ammarah ɗin ɗazun da rana akan cewar tana nan tafe. Malikat Haseenah ma kullum da kanta takan zo ta duba ta, kasancewarta tsohuwa mai dattako da iya zama da mutane tuni ta shige zuciyar Iffah itama, dan duk da bata da sakewa da yawan fara'a har dan jan Iffah take da hira. Sallayar datai sallar ta linke har yanzu jikinta a sanyaye ga damuwa fal ranta akan iyayenta, acan ƙasan zuciyarta takeji akwai wani mummunan abu dake sake tunkarota koma ya riga ya iso garetan ta hanyar iyayenta batare data sani ba. Yanayin ɗan zafi da ake ya sata yaye mayafin abayan data naɗe kanta da shi ta ajiye, ɗaurarren dogon baƙin gashinta dake reto a tsakkiya ya bayyana. Abincin da aka shirya mata tun ɗazun da bata ci ba ta nufa, ta bubbuɗe taga komai, batama jin cin komai har yanzun, dan haka ta tsiyayyi madara kawai da shanta tamkar al'adar ƴan ƙasar ne. Tana buƙatar fara canja kayanta zuwa marasa nauyi, dan haka ta ajiye kofin madarar a bedside drawer. Toilet ta fara shiga ta fito sannan ta shirya cikin wata yar yololuwar rigar mara nauyi mai zubin shimi. Iyakar rigar gwiwar ta ne, gata kalar fari da adon jajayen firanni. Ta matuƙar haskata da fidda ƙuruciyarta tamkar ƴar budurwar balarabiya. Turarrukan da Daneen Ammarah ta tule mata ta zaɓa kusan kala uku ta fesama jikinta. Cikin nutsatstsen takunta ta dawo saman gadon tana mai kallon fatar hanunta dake jajir saboda saɓar da tayi. "ALLAH dai ya isana wlhy" ta faɗa cike da halin tsiwarta tana jan bargo ta rufa iya cinyoyinta bayan ta jingina jikinta da fuskar gadon. Littafin da take rubuce-rubucenta na duk abinda ya faru ta ɗauka ta buɗe ko zata ji sassaucin tunane-tunen da zuciyarta ke mata marasa daɗi akan iyayenta, dan sam mafarkin nan yaƙi barin ranta koda na sakan ɗaya... A zahiri rubutun tai shirin fawara, dan yanda ta tsurama littafin ido da riƙe biron da nutsuwa matuƙa zai saka ka hasashen haka. Sai dai sam ko kalma biyu ta kasa rubutawa tamkar ma an mata wankin ƙwaƙwalwa komai ya gudu, hasalima nisan da tai a tunani yasa bibbiyu take ganin rubutun baya da tayi.... Knoking ƙofar da akai ya sata jan numfashi ta fesar, sai kuma taja mayafin dake gefenta ta yane jikinta har saman kanta tare da amsawa da "Yes! Kowaye ya shigo". A ɗarare hadima banou ta shigo, tsananin tsoron Iffah shimfiɗe akan fuskarta ya kasa boyuwa. Daga bakin ƙofar ta zube muryarta na ɗan rawa kamar yanda jikinta ke tsuma. "Amincin ALLAH da lafiya su tabbata ga Zawjata-almilk". Harara Iffah dake kallonta ta zabga mata. "Ina tare da masu lashe kurwar mutane irinku lafiyar zata tabbata a gareni? mtsoww!! Malama faɗi abinda ya kawoki bana son gulma". Ƙasa Banou ta sakeyi da kanta muryarta na rawa, dan harga ALLAH tana shakkar wannan yarinya da ko magana gatsau take yinta babu alamar shakku tattare da ita. "Uhm uhm dama Malikat ce take buƙatar ganinki". Hannu kawai Iffah ta ɗaga mata, dan har cikin rai ta tsani matar nan matuka. Sai da ta miƙe zata buɗe ƙofa sannan tai magana a gadarance. "Ki jirani a ƙofa, saura kuma kafin na fito ki lashe mun hadimai azzalumar bamza". Da rawar jiki data harshe Banou tace, "Hakan bazata faru ba ranki ya daɗe". "Uhm munafuka kamar gaske". Iffah ta faɗa tana sauka a gadon cikin mita......

★Tunda suka shigo ko sau ɗaya Iffah bata iya ɗaga kai ta kalla ko ɗaya a cikinsu ba. Saɓanin su da duk suka zuba mata ido cike da jin ƙaunarta a rayukansu. Cike da nutsuwarta ta karasa garesu, maimakon kujera da duk suke zaune sai ta kai ƙasan lallausan dardumar... "Haba Ibnati tashi ki hau sama mana". Jasrah tai yunƙurin dakatar da ita. Kai Iffah ta girgiza da ɗan murmushi a fuskarta, "A'a nanma ya isa". Cike da sha'awa da jin daɗi duk suke dubanta. Ta juya ta gaishe da Malikat Haseena, da fara'a da kulawa ta amsa mata tana mai sanya mata albarka. Cikin jin daɗi ta juya gasu Malikat Bushirat ta gaidasu suma. Suma da kulawar suka amsa mata, dan duk ƙasaita da jin kan Malikat Bushirat sai ta tsinci kanta da murmushi da sauƙaƙawa akan yarinyar saboda kwarjini da tai mata. Shiru na wasu ƴan sakkani ya biyo baya, kafin Daneen Ammarah ta katse shirun ta hanyar kiran sunan Iffah. Ta amsa mata da girmamawa sai dai bata iya ta ɗago kanta ba. Daneen Ammarah ta sake kiran sunanta da faɗin, "Kinga ɗago ki kallemu". Da ƙyar ta iya dauriyar bin umarninta. Dan duk rashin jin Iffah tana da wani hali na girmama duk mai nuna mata ƙauna koda bai cancanta ga sauran mutane ba. "Ibnati nasan nan zuwa yanzu duk kin sammu ko?". "Eh Mamy". "Amma baki san matsayinmu ba?". Nanma tace "Eh Mamy". "To Alhamdullah yau duk zaki sani. Ina son ki bani dukkan hankalinki nan ki kuma saurare ni yanda ya kamata". Ta jin jina mata kai. "Kamar yanda nasan kikaji Mamma a garemu mahaifiya ce, itace ta haifi Hama (Suruki) ɗin ki, da ni dama wasu biyu da zaki sani anan gaba sai dai ɗaya ya rasu". "ALLAH ya gafarta masa". Ta faɗa cike da rauni. A tare suka amsa mata da Amin. Daneen Ammarah ta ciga da faɗin, "Wannan da kike jin ana kira Malikat Bushirat itace Hamah (Suruka) ɗinki data haifi Shahan-shan na yanzu kuma mijinki da yazo nan jiya......" A razane Iffan ta waro idanu ƙirjinta na wani irin harbawa kamar zai wantsalo. Cikin subutar baki ta ce, "Shahan-shan! Na jiy....." sai kuma tai shiru ta haɗiye sauran maganar saboda tuna a inda take... "Kin sanshi ne kafin jiya?". Malikat Haseena dake nazartarta ta jeho mata tambayar a bazata. Da sauri Iffah da zufa ta jiƙema dukkan jiki, ta girgiza kanta. Kasancewar ta gwanar wayo tai saurin faɗin, "Mamma ina mamaki ne dai, ban zaci ganin Shahan-shan ɗin nada sauƙi kamar haka ba". Kusan a tare suka saki murmushi saboda hango tsantsar ƙuruciya a maganar tata. Sai dai malikat Haseena tsaf ta gama karantar Iffah waskewa tai. Amma kasancewar ta tsohuwa mai dattako sai ta dake itama ta shiga jerin ƴan murmushin.. Daneen Ammarah ta cigaba da faɗin, "Wannan ƙanwa ce ga Malikat Bushirat, Khaalah (Aunt) ga mijinki. Na baki ne a dunƙule iyamu da muke anan saboda muhimmancin abinda zakiji a yanzu". Kai Iffah ta jinjina mata da alamun gamsuwa. Jasrah ta cigaba daga inda Daneen Ammarah ta tsaya. "Ibnati dalilin miki wannan dogon sharhin a kammu shine fara aikinki matsayin Zawjata-almilk a wannan masarauta. Alhamdullah tunda kinji sauƙi zaki koma sashenki kamar sauran Zawjata-almilk guda biyu, sai dai zaki samu horo daga wasu amintattunmu matsayinki na Zawjata-almilk. Mun zaɓeki ne saboda nutsuwarki da tarbiyyarki. Basai mun zaman sharhi akan abinda ya faru ba a baya kasancewar kema ƴar kasa ce kin san komai na dangane da mutuwar matan Shahan-shan da suka gabata." Iffah ta haɗiye kududun baƙin cikin daya tokare mata maƙoshi akan famin rasa ƴan uwanta da tai da ƙyar ta jinjina kanta. Malikat Bushirat ta amshe da cigaba da faɗin, "Ibnati kece zaki zama mutum ta farko a rayuwa da zan nema alfarma a gareta, hakan kuma ta faru ne saboda jinki da nake a cikin raina da kallon da duk muke miki anan matsayin wani haske da insha ALLAH zai haska mana duhun da muke ciki. Muna son ki shiga jikin Saiful-malik domin binciko mana ainahin minene matsalar, saboda dukkan waɗan can matan da aka rasa daga kaisu turakarsa ne ake samun matsalar. Mun miki alƙawarin baki dukkan kariyar da bazamu bari ki cutu ba...." (Kariyar UBANGIJINA zata kasance tare da Ni). Iffah ta ayyana a zuciyarta. Malikat Haseena ce ta cigaba da faɗin, "Zamu fara ne da matakai da hanyoyin dinga haɗuwarku daga nan zuwa wani lokaci, fatanmu ki zama mai saka ido a dukkan wani motsinsa, a karan kansa, da duk wasu wanda zasu mu'amulancesa har a cikin hadimai. Kiyi takan tsantsan, dan mutum ne shi mai wayo matuƙa, sannan mai wahalar sha'ani da fahimta. Ba'a gane mi yake nufi ko minene a ransa akan fuskarsa, kar ki yarda ki bashi wata damar da zai iya zargi a kanki. Fatanmu dai ki zama jaruma a dukkan al'amuransa dama na kowa dake a wannan masarauta, duk abinda kikaci karo da shi ba dai-dai ba kiyi maza ki sanar da ɗaya daga cikinmu". Zantukan nasu ya saka zuciyar Iffah dinga tsalle-tsalle a kan dalilai biyu.......✍️

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 96 09 67 63

Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

*_28_*

........Na farko ji a ranta UBANGIJI ya amsa mata addu'ar ta akan burin data shigo da shi Daular ruman. Na biyu minene dalilin waɗan nan mutane na buɗe mata cikinsu?. Na ƙarshe da yafi kowanne razani da ban mamaki a ƙwaƙwalwarta dama suma sun san shike aikata kisan kenan? Amma suka zaɓi yin shiru saboda ba ƴaƴansu ake halakawa ba kokuwa suma tsoronsa sukeji? A ɗan ƙaramin tunaninta tanaga zasu iya yin amfani da ƙwanji wajen sanin mi Shahan-shan ɗin ke aikatawa musamman Malikat Haseena da Malikat Bushirat. Amma miyasa suka zaɓi yin amfani da ita? Kodai sun gama gane manufarta ne a kansa.....? "Ibnati!". Daneen Ammarah ta katseta daga nisan da tai a tunani ta hanyar kiran sunanta da taɓata. Firgigit kuwa ta kawo ajiyar zuciya. "Karki kasance a dogon nazari, manufarmu ta sakaki a wannan sabgar tana da nasaba ne da dalilai biyu. Na farko juriyarki ta bamu ƙwarin gwiwar kallonki a jaruma. Na biyu jinki wata abu mai muhimmanci da muke fatan nasara ta dalilinta kodan tsallake tarkon masu aikata wannan ɓarna da kika tsallake a harin farko da muke jin shine lagon da aka dinga ɗanawa a farko wajen salwantar da rayukan da suka gabata...." "Mamy nima zata yuwu bana tsallake bane dan nafi ƙarfinsu, maybe na tsallake ne saboda tsayawarku da fatanku akan ganin na tsallake ɗin. Amma tabbas zan iya sadaukarwa, zan kuma iya bin umarninku badan inajin ƙarfina ya kai ba sai dan kun isa ku bani umarni". Su dukansu kalamanta sunyi wani tasiri na musamman a zukatansu tare da ƙawatata a cikin idanunsu. A wani gefen sunyi amanna irinta ɗansu ya dace ya samu tun farko, dan ƙarfin gwiwarta sunyi dai-dai da Zawjata-almilk da akafi buƙata ga kowane Shahan-shan. Sannan Malikat da sukema kansu fata. "ALLAH yay miki albarka". Suka faɗa kusan a tare su duka huɗun. A kan laɓɓanta ta amsa da amin. Sun cigaba da tattaunawar da gaba ɗaya ta saka Iffah cikin ƙagara, ƙagara mai nasaba da shiga ruɗanin wani furici daga Daneen Ammarah. Wai jiya Shahan-shan ne wanda ya ziyarcesu a wannan falon, tana buƙatar samun filin tunani dan zuciyarta da ƙwaƙwalwarta fa gaba ɗaya sun kulle, ruɗani ya gama mamaye duk wani hangenta da dama bai wuce iya tsayin ƙafafunta da shekarunta ba....

★★....

A hankali ta maida ƙofar ta rufe tare da jingina a jikinta ta lumshe ido da sauke numfashi tamkar mai kokawar jawosa. Shin murna zatayi a wannan gaɓar ko kuwa shiga ruɗani?. Idan ance Shahan-shan ne a jiya ta yarda, shi kuma wanda tai gamo da shi a mabanbanta wajeje kafin shigowarta masarauta wanene shi?. Wannan tambaya tafi kowace tambaya girma da girgiza zuciyarta a duk abubuwan dake cin ranta. "Kai nifa nama ruɗe wlhy". Ta faɗa a zahiri tana zamewa cikin sarewa ta zube ƙasa. Ta jima a wajen cikin halin shiru da ambaton hasbinallahu wa ni'imal wakil ko zata samu dai-daiton komawa cikin hankali dan da gaske komai na halittarta mai motsi ya raunana da rauni mafi ban tsoro da shiga ruɗani. Tsahon lokaci ta kwashe a wajen tana kokawa da raunin zuciyarta da rashin ƙarfin gudanar jini. Fahimtar wancan tunanin na buƙatar lokaci ya sata turesa ta maida hankali akan tattaunawarsu da su Malikat. Tabbas wannan shine babban ƙudirinta dayin ƙundunbalar juriya na tunkarar rayuwar da bata da tabbacin tsallakewa. Duk da tasan anfi ƙarfinta, dama duk wani mai ƙarfi da take kallon ƙarfinta ta zaɓi fuskantar mutum mafi girman iko da tsaro domin ɗaukar fansa. A kwanakin da suka gabata na kasancewarta cikin wannan daula ta fara fidda ran samun cikar burinta saboda dalilai masu yawa. Ciki harda rashin samun koda ƙanƙanuwar ƙofar sanin minene ma daular ruman ɗin ta ƙunsa balle Shahan-shan da kansa. Sai gashi a yau cikin sauƙi an buƙaci kaita inda zuciyarta ta fara raya mata zuwansa ba ƙaramin tsalle bane da ba'a da tabbacin fita idan an shiga, aka kuma sanar mata wani yanki na sirrin daular ruman mai girman gaske da ko na ciki basu san da shi ba ƙila. "Anya babu wani abu a ran mutanen nan saɓanin abinda suka faɗa?" bakinta ya furta a zahiri cikin sake dulmiya a ruɗani. (Koda akwaisa yardar ki dasu ce zata baki ilimin sanin hakan) zuciyarta ta faɗa cikin ƙarfafata da ture raunin dake neman rinjayarta.... Knoking ƙofar daya wanzu a dai-dai lokacin ya sata jan numfashi a sauƙaƙe. Da ƙyar ta iya miƙewa daga zaman daɓaron da tayi ta buɗe. Daneen Ammarah ta sakar mata murmushi. Cikin yaƙe ta mayar mata da murtani da matsawa ta bata hanya. Rissinawa hadimar da suke tare tai ta gaisheta, hannu kawai ta ɗaga mata alamar amsawa tana bin ledar hanunta da kallo......

★★.... ★.... ★★.....

Kamar yanda aka sanar da Barrister kai tsaye station ɗin da akace su Babiy suke suka nufa. Kasancewarsa babba kuma sananne basusha wahalar ganin ogan station ɗin ba kai tsaye. Sunyi gaisuwa irin tasu ta manyan ma'aikata, su kai kuma gaisuwar girmama juna da su Kaka. Barrister ya gabatar da kansa, ya kuma gabatar da abinda suke tafe da shi harda hoton su Babiy domin sauƙaƙawa. Jami'in yay shiru yana kallon hotunan kamar mai hasashe, sai kuma ya ɗago ya kalla Barrister "Gaskiya banajin akwai waɗan nan mutanen a wannan station ɗin Barrister". Barrister daya fahimci matsala ce ke neman shigowa yay ɗan murmushi da muskuta zamansa. "Yallaɓai adai sake dubawa, zata iya yuwuwa ko akwaisu ɗin baka da labarin hakan. Amma tabbas suna a wannan station ɗin. A matsayina na Barrister ba nazo nan dan a bani belinsu bane ba, duk da nasan basu da hannu a abinda ake zarginsu. Nazo ne dan na gana da su, sannan a miƙasu kotu saboda nasan dai ita matar data saka aka kawosu nan burinta a kwatar mata hakkin mijinta". "Iya gaskiyata nake faɗa maka Barrister babu waɗan nan mutanen a wannan station ɗin. Amma mizai hana ku sami ita matar na tabbata tunda tare da ita akaje tasan wane station ne". Barrister yay shiru yana kallonsa cike da nazari. Hakama Kaka da Abu Zainab. Kusan minti biyu shiru babu wanda ya motsa, kafin Barrister ya miƙe yana ɗan murmushi ya bashi hannu. Suma su Abu Zainab miƙewar sukai...

Da kallo ya bisu har suka gama ficewa, ya kai hannu kan wayarsa dake saman desk ɗin sa yana wani murmushi. A bugu biyu aka ɗauka wayar daya kira. Sallama kawai yay da faɗin, "Kamar yanda kai hasashe ranka ya daɗe yanzu suka bar office ɗina". Shiru yana sauraren mi'ake faɗa daga can, sai kuma yay murmushi da amsawa da "Angama ranka ya daɗe". Daga haka ya ajiye wayar yana wata ƴar iskar dariya...

Abu Zainab daya kasa fahimtar komai saɓanin Kaka da Barrister dake hangen wani abu dalilin kashedi da akai musu kafin zuwansu nan dama ya katse shirun da motar ta ɗauka ta hanyar nisawa. "Anya kuwa wannan jami'in akwai gaskiya a maganarsa Barrister. Kagafa yanda yake ƙyaf-ƙyaf da idanu kamar tsohon ɗan jari hujja. Nifa wannan al'amari ya fara bani tsoro wlhy". Barrister da zuciyarsa ke kai kawo ya fesar da huci, "Kana tunanin yaƙi faɗa mana gaskiya ne Zakariyya?". "Fuskarsa ta nuna hakan ai Barrister, ko kuwa Kaka?". Kaka da shima dai yake aune-aunensa a rai ya girgiza kansa. "Zata iya yuwuwa gaskiyar ya faɗa, sai dai kumin wani taimako ɗaya dazai warware mana gaskiyar tasa ko saɓaninta, bayan nan zan sanar muku abinda ya faru kafin zuwanmu nan". Barrister da shima abinda ke'a ransa kenan ya ɗan juyo ya kalla kaka ta madubi, "Muna jinka Baba". "Muyi gaggawar isa gidan Dawood". "Shawara mai ƙyau Baba". Barrister ya faɗa yana juya motar hanyar da zata kaisa gidan Abu Moosa.

★★... ★★... ★★...

"Mamy kuma duka wayar da lap-top ɗinne nawa?". Iffah ta faɗa da mamaki. Murmushi Daneen Ammarah tayi, "Ibnati wannan ai ba komai bane ba, sannan ko baki faɗa ba kina buƙatar su tare da ke kodan ki dinga jin motsin gida. Na biyu kuma wannan aikin da zaki fara kowa yasan mai haɗari ne, dolene ki kasance da waya a duk inda kike a masarautar nan. Da zarar Kinga abinda zuciyarki bata kwanta da shi ba a cikin mu huɗun zaki iya kiran kowa ki sanar masa. Lap-top kuwa ni naga ya dace na kawo miki ita domin ɗebe kewa. Amma kiyi taka tsantsan ki kuma kula sosai, dan samun waɗan nan na nufin zaki iya mu'amula da kowa musamman a yanar gizo batare da kin samu tabbacin wanene ɗin ba". "Haka ne Mamy, insha ALLAH zan kiyaye. Nagode sosai ALLAH ya saka da alkairi". "Karki damu kin cancanta ne ai".

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull