Kenza eBookz

Daudar gora complete - Chapter 23

Daudar gora complete - Chapter 23

Daudar gora complete Chapter 23: Daudar gora complete Chapter 23. Tamkar raƙumi da akala haka Iffah ke tafiya bisa jagorancin Malikat Haseenat. Kasancewar…

3,145 words

Tamkar raƙumi da akala haka Iffah ke tafiya bisa jagorancin Malikat Haseenat. Kasancewar dare ne babu yawaitar hadimai masu hidima. Sai dai masu tsaro tako ina kai kace zasu iya kare ran wanda suke tsaye a dalilinsa daga ziyartar mutuwa. Tsirarun hadiman da suka samu nata zubewa kwasar gaisuwa, Malikat Haseenat ce kawai ke iya jinsu da ganinsu. Iffah dake ta faman sauke ajiyar zuciya da al'ajabin dukiyar dake narke a wannan gini ji take komai ya ƙwace mata. Ta kasa fasalta komai ta kasa auna komai a ma'aunin rinjayen aikin zuciya dana ƙwaƙwalwa.... "Bismillah". Malikat Haseenat ta katse mata ɗimuwar da take ciki ta hanyar nuna mata ɗaya daga cikin kujerun katafaren falon mai cike da abubuwan da bazasu lissafu ba. Da gaske Iffah bazata ma iya tantance yanda akai ƙafarta tazo nan ɗin ba. Komai Malikat Haseenat batace ba, dan ta gama karance ɗimuwar dake jagorantar fitar numfashin Iffah. Amintattun Hadiman dake a falon na uku suka zube gaban Malikat Haseenat kawunansu a ƙasa. Hannu kawai ta iya ɗaga musu. Babu buƙatar sai ta faɗa abinda tazo dan shi, shugaban hadiman dake a wannan falon ya miƙe zuwa ga landline domin isar da saƙon zuwanta... "Tsahon rai da lafiya su tabbata ga Uwa a garemu, shugaban na tsumayen isarku a falon sama". Shiru malikat Haseenat batace komai ba. Yayinda Iffah da zuciyarta ke luguden ke saurarensu cikin juyewar tunaninta da har yanzu bai dawo dai-dai ba. Kusan mintuna uku Malikat Haseenat taima Iffah nuni data miƙe, ita kuma ta birka wheelchair ɗinta suka shiga lifter. Mintuna biyu ne kacal suka iso da su katafaren falon da yafi kowane falo ƙawatuwa a kaf daular ma da sashen kawai ba. Iffah tai ƙoƙarin danne harbawar ƙirjinta sakamakon tozali da wanda ke zaune a falon cikin zama na ƙasaita da izzar masu mulki. Tafiya take tamkar hawainiya saboda tsabar kasala da sanyin gaɓɓai. Zuwa yanzu wannan fuskar bata aljani take fassarata ba, neman ƙarin bayani take a kanta a dalilin ganinta a waje biyu da basu da alaƙa da juna a zahirin rayuwa... Tajwar Eshaan da ke kishingiɗe bisa ƙayataccen kujera mai kama da wani madaidaicin gado gabansa butar shayi ce da ƙaramin kofin da alamu suka nuna yasha ko zai sha, idanunsa ya janye daga kan television da yake kallo ya ɗan waigo garesu. Akan Iffah dake tafiya tamkar hawainiya ya fara saukewa, fuskarta a sakaye take, hanunta dake riƙe da rigar jikinta ne ta ƙasa kawai a bayyane. Janye wa yay ya maida ga Malikat Haseenat. Ta ɗan hararesa da salon kulawa da nuna damuwa. Idanun ya janye a sannu daga kanta itama yana sakin kasaitaccen murmushi.... Harya gama gaisawa da kakar tasa a yanda yake kishingiɗe batare da ya motsa ba Iffah na tsaye ƙyam tamkar an dasata. Malikat Haseenat ta maida kallonta gareta tare da ambatar sunanta. A dake Iffah ta amsa dan tayi alƙawari ma kanta bazata taɓa barin rauninta sake bayyana ga kowa ba a yanzun. Kafinma Malikat ta sake cewa wani abu tai ƙasa a hankali, cikin rashin ƙwarin jiki ta zube ƙasan lallausan carpet ɗin da ko jikin zomo bazai nuna masa laushi ba. Ƙamshi ko ba'a magana dan ko'anan ake shukashi iyaka kenan. "Amincin ALLAH ya tabbata a gareka". Ta faɗa badan har zuciyarta abinda take son faɗar kenan ba. Sai dai kwarjininsa daya mamaye falon da duk girmansa take jinta a matse yaƙi bata damar fitar jin zafinsa dake a ƙasan zuciyarta a zahiri. Kamar a waccan ranar yau ma bai amsa ba, babu ma alamar yajita tattare da shi. Daga cikin hular alkyabbar jikinta ta cije lips ɗinta da masifar ƙarfi tamkar zata hudasu da haƙori..... "Ai ma Zawjata-almilk rakkiya ɗakin da Tajwar zaiyi barci a yau". Furucin Malikat Haseenat ga hadiman dake rakuɓe gefe zube a ƙasa kawunansu rissine tun shugowarsu ya nema sarƙe numfashin Iffah da Tajwar Eshaan a lokaci guda. Babu wanda Malikat Haseenat ta kalla a cikinsu sai ɗaya daga cikin Hadiman ce da suke girki ta miƙe da rawar jiki zuwa inda Iffah take. Dole ta mike dan a furucin Malikat Haseenat babu wasa ko ɗaukar turjiya ga kowannensu.... Shiru falon babu wanda ya sake ƙwaƙwƙwaran motsi har hadimar data raka Iffah iyakar ƙofar ɗakin ta dawo Malikat Haseenat ta sallamesu. Da ga shi sai ita suka rage, dan haka ya kafeta da idanunsa. Kai Malikat Haseenat ta ɗauke gefe tamkar bata gansa ba ko fahimtar kallon. "Anan zata zauna, sai ka zaɓi inda kake buƙatar ta kasance har tsahon sati ɗaya, dan zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu masu mata hidima zasu kasance tare da ita. Na damƙa amanarta a hannunka, ina kuma fatan ta kasance ƙarƙashin kariyar UBANGIJI. Fatan alkairi da shiga sabuwar rayuwa, tare da tayaka murnar sabon aure. Na barku cikin amincin ALLAH". Da alama gushewar numfashi da rikicin wannan tsohuwa ya gama daskarar da jinin Shahan-shan. Dan harta fice a falon ko gashin idonsa bai ƙyafta ba, kai kace wani butun butumine aka dasa a wajen domin tarihi.......

(🤔Tsohuwar nan kuwa na lafiya? Zata kai mana Iffah har ƙuryar Dodon Mayu🥱🤦).

★★... ★★....

Duk da dare ne gaba ɗaya masarautar ta ɗauki ɗumi bisa wannan bahagon hukunci na Malikat Haseenat. Basu da al'amarin yazoma a bazata ba, hatta Malikat Bushirat da Daneen Ammarah da Jasrah da akai zaman da su komai ya musu cak. Abinda suka sani kawai komawar Iffah sashenta, bawai kaita turakar Shahan-shan ba. Miyasa Malikat Haseenat ta canja lissafin a kan kansu suma?. Wannan itace tambayar daketa musu kaikawo su duka.

"Ni kam dai a wannan gaɓar na kasa gane komai wlhy Akia. Shin minene dalilin Mamma nayin haka? Miyasa lissafin ya canja daga yanda muka tsara gaba ɗaya?". Kamar malikat Bushirat bazata tanka har ta kai ta kawo kusan sau uku kafin ta dubi Jasrah mai maganar. "Kaina ya kulle Jasrah". Ta faɗa a takaice da kaiwa zaune bakin gadon ta dafe kanta. "Ya ALLAH! Wlhy zuciyata ta fara kai ni ga hasashen wani abu daban?". Jasrah ta sake faɗa tana dafe nata kan itama.

A ɓangaren Daneen Ammarah ma dai a rikicen take. Sai dai ita nata lissafin yasha banban da nasu Malikat Haseenat. Daga ɗakin taro bedroom ɗin Malikat Haseenat ta wuce zaman jiranta. A zaman da bai wuce mintuna arba'in ba kuwa sai gata. Kallo ɗaya taimata ta ɗauke kai. Hadimar dake biye da ita ta ajiye madarar hanunta da zubewa ƙasa tana gaida Daneen Ammarah. Hannu kawai ta ɗaga mata.... "Na matuƙar gajiya, kwanciya kawai nafi buƙata". Malikat Haseenat ta faɗa tana wulla kekenta hanyar bathroom ɗinta batare data sake kallon Daneen Ammarah ba. Da kallo ta bita cikin shakku da shan jinin jiki. Dan duk da a dunƙule tai magana tana nufin bata bukatarta a ɗakin kenan. Jiki a sanyaye ta miƙe ta fice zuciyarta na faman tsalle-tsalle...

Duk yanda taso kwanciya ta kasa hakan, fargaba da tausayin Iffah ne ke matukar ɗawainiya da ita. Har cikin zuciya bata son rasa yarinyar dan ta matuƙar shiga ranta. Soyayya take mata irin ta ƴa da uwa. Ita kanta har takanyi mamakin yanda takejin Iffah a rai matuƙa, amma tasan wannan ƙaunar daga ALLAH ne kawai. Wayar dake a hannunta ta ƙara rumtsewa, ta gwada kiran Iffah ya kai sau huɗu kenan amma tana fasawa, so take taji lafiyarta ko zata samu ƴar nutsuwa, amma wata zuciya na gargaɗarta da kalmar rashin dacewa....

★★.....

"Mi wannan tsohuwar ke nufi wai shin? Ko itace abin neman mu kamar yanda barbushi ya sanar mana?". Miran Arshaan yaja numfashi ya fesar, kamar bazaice komai ba sai kuma ya kafe Miran Jasim da kallo yana girgiza kai. "Wlhy kaina ya kwance Jasim Akhi. Na kasa gane komai a wannan gaɓar, abinda na sani kawai shine mutuwar yarinyar nan a wannan gaɓar tamkar mutuwar cikar birinmu ce, dan na gama ɗora dukkan hope ɗinmu a kantane. Bai kamata ta mutu a yanzu ba har sai ta ƙarasa mana aikin da muka kwashi tsahon shekaru muna ginawa". "Miye mafita?". Cewar Miran Jasim a firgice, dan zantukan Arshaan ɗin kamar sun zaburar da shi ne abinda ke gabansu. Kai tsaye Miran Arshaan yace, "Ziyartar Barbushi a wannan daren, kafin waccan sankaran matar da ban san amfaninta a tafiyarmu ba tazo ta ishemu da tsarin banza". "Hakan yayi mun, babu amfanin ɓata lokaci kaje kayi shiri". Kai Miran Arshaan ya gyaɗa masa, tare da mikewa ya fice. Da banzan kallo Miran Jasim ya bisa, cikin ƙanƙance idanu da wani shu'umin murmushi a fuskarsa "Ba matar can bace kawai abin banza a cikinmu, har da kai Arshaan, daka gama mun amfani zan kawar da kai, dan ni kaɗai nake son mulkar daular ruman batare da ɗan uba ko ɗaya ba da zai zame min abokin gaba, nasan idan har na barka kaima zaka zamemin maƙiyi dan burinka wannan kujerar ne na sani shashasha"...

(🥱Waɗan nan mutane dai to bara nayi shiru dai🤫)

*_ZAWJATA-ALMILK_*

Duk da akwai wani ɗan ɓurɓushin tsoro a ƙasan zuciyar Iffah ta matuƙar dakewa da addu'a ta shiga ɗakin bayan ta gama ƙarema bangon dogon corridor ɗin da suka biyo kallo, ta jinjina kai cikin jin matuƙar ƙuna da tausayin talakawan ƙasan ruman baki ɗaya. Tayi imanin akwai dubbunan mutane dake barci akan titi cikin yinwa da ƙishirwa da yawa. Amma abin mamaki yau ga bangon ɗakin barcin Shahan-shan yasha ado da zinari matsayin fenti, "Taya ma imani zai zauna a zuciyar mutanen nan har su ɗauka rai wani abun mai daraja?" ta faɗa a zahiri idanunta na cika da ƙwallar baƙin ciki da ƙara jin tsanar Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed..........✍️

(😭Hikenan Iffahr mu an shigo ɗakin mutuwa😱🙆).

Ko miye dalilin Malikat Haseenat na kai Iffah turakar Shahan-shan kai tsaye haka? Miye dalilinta na canja abinda suka tattauna da su Malikat Bushirat? Shin ko dai malikat Haseenat ce T....😱🤫🤭?.

Yaya zata kasance tsakanin Iffah da Shahan-shan ne? Ta wani ɓangaren abinda ke kashe Zawjata-almilk kuna ganin zai ƙyale rayuwar Iffah a wannan dare kuwa?.

Gadai wasu ɓoyayyun maƙiya na sake fitowa. Irinsu Miran Arshaan (mijin Jasrah kuma ƙani ga Tajwar Haysam) da Miran Jasim (shima ƙani ga Tajwar Haysam). Shin wacece wai matar nan da suketa a ambata batare da sunanta ba?.

Hhhh tabbas yanzu ne wasan zai fara. Sai ku shirya ku sake shiri dan sai a yanzu ne muka kalmashe bakin shimfiɗar labarin dake cikin littafin DAUƊAR GORA... Wasan na asali yanzu ne filin yinsa ya kammala. Masoya sai mu antaya kawai😉🥱🏇🏇🏇🏇.

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 96 09 67 63

Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

*_32_*

........Ni'imtaccen ƙamshin dake tashi a katafaren ɗakin ta zuƙa ta fesar da cigaba da bin komai daki-daki. Ɗaki kam ya cika a kirasa ɗaki ga masu arziƙin dake ɗaukar duniya gidan zama. Sai dai ta gama ayyanawa a ranta babu wani ƙyale-ƙyale da zatai sakacin da zai ruɗeta har ya dakatar mata da ƙudirinta data fara taka tsanin nasararsa a yau insha ALLAH. Ta saki kasaitaccen murmushi da ware hannayenta iskar na'urar ac ta busota tare da ƙamshi, idanunta ta lumshe ta buɗe tare da tsuke fuska. Cikin wani kakkausan sauti daya bambanta da nata na baya ta furta. "Yanzu ne za'a fara wasan na gaskiya. Dodon matsafa MATAN ƘWARAI bisa kanka!!"...

(🥱 Iffahn mu irin wannan alwashi haka🤔 kinfa fara bani tsoro😱🏇).

★★...

Tun wucewar Malikat Haseenat ya bar falon shima. Tsaye yake jikin windown ƙaramin falonsa na hutawa da babu mai shigarsa sai shi ɗaya tak da amintacen hadiminsa mai gyarasa. Dan a doka ma hatta matarsa bata da hurumin shiga wannan falon a tsari da ƙa'idar masarautar. Hasken daya ƙawata cikin masarautar ya bashi damar iya ganin abubuwan dake kusa daga inda yake, sai dai kuma a zahiri idanun nasa ne kawai ke kallon zuciyarsa sam ba'a nan take ba. Ya kwashe tsahon lokaci a wajen kafin ya warware hannayensa dake goye a bayansa ya furzar da numfashi. Ƙofar ɗakin barci ƙwaya ɗaya dake a falon ya nufa. Shima tsaf yake tamkar anan yake zaman din-din-din. A maimakon kwanciya anan ɗin ma zaune yakai cikin kujerar dake ajiye a gefe domin hutawa kawai. Tun agogon ɗakin na juya sakanni da mintuna har ya koma awanni yana zaune idanunsa lumshe, ya kwantar da bayansa a makarin kujerar dake ɗan juyawa a hankali. A kallon fuska baka isa gane yanayinsa ba balle ka samu damar masa fassara. Bugawar agogon ɗakin mai nuni da cikar ƙarfe biyu dai-dai ta sakashi buɗe idanunsa da ƙarancin hasken ɗakin ya hana damar iya tantance launinsu a yanzu. Agogon ya tsurama ido tamkar mai lissafa daƙiƙun da suka cigaba da motsawa.....

A ɓangaren Iffah wannan lokaci na dai-dai da kai goshinta ƙasa domin yima UBANGIJI suduja a karo na babu adadi. Tun bayan kammala lissafe-lissafenta da ƙidaye-ƙidaye ta zanzare rigar jikinta, ƙaramin akwatinta ta buɗe babu alamar damuwa tattare da ita ta sauya kayanta zuwa abaya. Daga haka ta nufi bayi bakinta ƙunshe da tarin addu'oin da taketa yi tun shigowarta ɗakin. A karan farko data buɗe fanfo da nufin yin alwala saɓanin zubar ruwa sai taci karo da jan abu tamkar jini. Tabbas taji firgici, amma sai tai yaƙi da rauninta wajen cigaba da addu'a da son daidaita harbawar da zuciyarta keyi da sauri-sauri. Tamkar almara kalar jan ya ɓace a idanunta ainahin ruwa ya maye gurbinsa. Numfashi taja ta fesar zuciyarta na tabbatar mata ta ƙara dakewa. Tsaf ta ɗaura alwalarta kuwa ta miƙe, tana ƙoƙarin gyara ɗan kwalinta taji tamkar an gitta ta bayanta. Anan ɗinma dai zuciyarta ta tsinke, amma sai ta cigaba da ambaton sunan ALLAH ta basar. Bata damu da nan wanin abin salla ba, dan tsaftar dardumar da aka ƙawata ɗakin da ita ya gamsar da ita. Mayafinta ta naɗa tai nagartacciyar tsayuwar salla domin fuskantar UBANGIJIN talikai mai jin kukan wanda ma basu fara kukan ba, mai bada kariya ga wanda ya yarda babu abin dogaro sama da shi... Taja tsahon lokaci a sujidar tana mai zubda hawaye da ƙaskantar da kai ga mai gani a duk inda ka ɓuya. Bayan ta sallame tai zaman karatun Alkur'ani a cikin wayarta dan batajin zata samu Alkur'ani a wannan ɗakin da ƙyaleƙyalen cikinsa ya tabbatar mata zamowa fadar aljanu ba komai bane. Sai da ta gama karance baƙara har zuwa inda suka tsaya a makaranta sannan tai addu'a mai tsawo itama. Sosai taji wata iriyar nutsuwa na ratsa dukkan jikinta, ta sauke ajiyar zuciya da miƙewa. Hankalinta kwance ta haye katafaren lafiyayyen gadon da Shahan-shan ne kawai ya taɓa hawansa a tarihi. Nanma zama tai tai addu'ar barci ya shafe jikinta ta gyara lausasan filos ɗin da aka ƙawata adon gadon da su ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya. Barci mai daɗi ya fara fisgar idanunta a sannu-sannu sai gata tana sauke numfashi.......

★★...... ★★..... ★★.......

Bayan wucewar saurayin da Kaka ya shimfiɗama sha tara na arziƙi gidan yay shiru. Kamar yanda bai cema Iyyani komai ba itama batace ba, tsahon wasu mintuna sannan ya miƙe ya shiga ɗakinsa. Tashi Iyyani tai ta bisa, dan ta fahimci maganarce baya buƙatar ayi sam.. A ɗakin ma baice mata komai ba har tsahon wani lokaci, ganin haka ta katse shirun da faɗin, "A haɗa maka ruwan wanka?". Batare da ya bar abinda yake ba ya jinjina mata kai. Fita tai jiki a sanyaye, babu jimawa ta koma ta sanar masa an haɗa. "ALLAH yay miki albarka". Ya faɗa kamar yanda ya saba. Ta ɗan ji sanyi a ranta, dan haka ta amsa da "Amin tare da kai" cikin sauke ajiyar zuciya....

"Ai bakaci wani abincin kirki ba". Iyyani ta faɗa idonta akan kwanikan gaban Kaka da ya gama cin abincin data kawo masa bayan fitowarsa wanka. Kai ya jinjina mata da sakin murmushi a karan farko tun bayan shigowarsa gidan. "Alhamdulillahi wanda naci ya wadatar dani". Kai kawai ta jinjina masa jikinta na ƙara sanyaya. Duk wanda zai sam mijinta a bayanta yake, ta san murmushin sa ba yana nufin farin ciki bane na tsantsar damuwa ce..... "Yaya jikinta?". Ya katse tunaninta da abinda taketa zumuɗin san ji a bakinsa. "Alhamdulillahi da sauƙi". "ALLAH ya ƙara afuwa. Bara na ganta".

Ummu na zaune shiru ta tsurama waje ɗaya idanu suka shiga. Har suka kai zaune gefenta babu alamar tana san da zuwan nasu. Kaka ya kafa mata idanu na wasu sakanni sai kuma ya kauda kai. Taɓata Iyyani tayi, ta kawo nannauyan numfashi da ɗan zabura na ganinsu a ɗakin dan da gaske bata san da shigowar tasu ba. Kaka ta kalla idanunta na cikowa da ƙwalla, sai kuma ta duƙar da kai ta fara gaishesa. A hankali ya nisa kafin ya amsa a taƙaice kamar yanda tai gaisuwar. "Jumaimah!". Ya kira ainahin sunanta. "Na'am Baba". Ta amsa akan laɓɓanta. "Damuwa ko ƙuntata kai bata sauya ƙaddarar bawa. Juriya da tsantsar jarumta baya hana ƙaddarar zuwa. Haƙilo ko nuna ƙarfin iko baya ture ta a lokacin da aka so. Rauni ko rashin tawwakali bazai dawo maka da abinda dama can ba naka bane ba. Haƙuri shike samar da komai koda kuwa a zahiri yafi ƙarfin ƙarfinka". "Hakane Baba". Ta faɗa cikin rawar murya. Murmushi ya saki da matsawa kusa da ita sosai. Ɗa a gaban iyayensa baya girma koda ace yayi furfura a saman kai. Kaka ya riƙo hanun Ummu cikin nasa, ɗayan kuma ya shafa kanta. "ALLAH yayi miki albarka. Yasa ƙaddarar su ta zama kaffara a garemu baki ɗaya." "Baba mun rasa su suma ko?". Ummu dake dubansa idanu cike da ƙwalla ta faɗa. Murmushin ya sake sakar mata. Sai kuma ya girgiza kansa da kwanto da kanta bisa kafaɗarsa. "Bamu rasa su ba, ba kuma mu fidda rai da samunsu ba". A hankali hawayen da suka kasa fita a idonta tsahon kwanaki suka fara sauka a kafaɗarsa.......

★★.... ★★.... ★★.....

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull