Dawood complete - Chapter 11
Dawood complete Chapter 11: Dawood complete Chapter 11. wani irin mugun gudu yake yana tsiyayo wasu irin hawayen farin ciki zuciyarsa har wani bugawa…
4,491 words
wani irin mugun gudu yake yana tsiyayo wasu irin hawayen farin ciki zuciyarsa har wani bugawa takeyi da qarfi kamar zata faso qirginsa.
da wani irin mugun gudu da horn yashigo kwanar layin gidan daida lokacinta police biyu suka fito da ita daga gidan nana na biyedasu tana kuka kamar ranta zai fita,
kasa gasgata idanuwansa yayi sai kawai yayi cikinsu aguje da motar yayiwa motarsu wani mugun bugu nan take tafara hayaqi da gudu ya fito ya damqota ya cilla cikin motarsa yayi ribas yabar layin da mugun gudu babban inspectern da mum aguje suka fito cikin tashin hankalin jin qarar bindiga suka tararda tuni motar dawood din tabar layin,
da gudu suka shiga motarsu suka rufa masa baya.
sabon tashin hankali da baqin cikine tasowa mum tadawo cikin gida daidai leqowar sarah tana hada gumi,
kallonta mum tayi dakyau nan take wani zargi yafado mata gabanta yayi mummunan faduwa ta hadiye wani mugun miyau ta nufota tareda bude qofar dakin taga akwatinta da passport tayi saurin kallonta murya na rawa tace,
saraah kece kika kashesa.....
kuka tasake da sauri ta matso tana cewa,
wlh bansan lokacinda na.....
wani mahaukacin mari mum tasakar mata saidata kife ta nunata da yatsa saita kasa magana ta fashe da wani sabon kuka mai qarfi tana cewa,
wane irin balai da masifa ne wannan na jawowa kaina.
kuka tayi sosai harsaida muryarta ta dashe ta miqe daqyar ta fice batareda ta iya cewa qalaba takoma asibiti kukanta na kasa tsayawa.
kodata koma asibiti sabon kuka tasaki aleeya datayi kuka harta fice hayyacinta ita tafara rarrashinta amma sam takasa sbd babban tsoronta na biyu bayan na halunda taheer ke ciki shine makomarta idan CJ yaji itace mafari idan aka gano saraah ce taso kashe taheer.
gudu yakeyi sosai kamar zai tashi babu ruwansa da tudu ko ina fadawa yakeyi gashi police basu bar binsuba gashi sunyi waya anturo musu wasu motocin cike da police sosai suka bude masa wuta amma taqi tsayawa harsunyi nisa da gari sosai sai kawai ya yanka daji cikin rashin sa'a motar ta qwace masa tayita gudu saidata kai gurin wani qaton ice ta dakesa tafara hayaqi,
daqyar ya dago kansa daya bugu harda jini ya fito motar ya bude baya ya cicci6ota sbd tun aqofar gidan ta some batareda taga wanda ya daukotaba,
cicci6arta yayi yakutsa dajin da ita yacigaba da gudu yayi nisa kadan motar takama da wuta sosai daidai isowar police suka tararda takama da wuta nansuka buga suka sanarda wainda ke ciki sun mutu suka juya.
gudu yayi sosai cikin tsakiyar dajin har asuba ga gajiya ga qafafuwansa dasuka fara farfashewa sbd tafita cikin manyan qayoyi, yana kaiwa gurin wani qaton kogi jiri ya dibesa agurin suka zube asume dagashi har ita.
dad qarfe bakwai na safe ya dira a asibitin mum na ganinsa hankalinta yaqara tashi,
cikin saa dr yafito lokacin yakallesu tareda miqawa dad hannu yace,
mu gode allah he is out of danger wuqar bata samesa a cikiba a gefe tasamesa kuma bata shiga irin sosai dinnanba munyi masa aiki mun 'dinki gurin kowane lokaci zai iya farkawa saidai kuma gskia zai dade sosai bai fara miqewa tsayeba sbd akwai jijiyar data ta6u kadan.
ajiyar zuciya suka sauke cikin farin ciki da hamdala nan dad ya juyo ya kalli mum yasake tambayarta yanda abin yafaru,
kallon gefen aleeya tayi ta hadiye wasu yawu daqyar murya na rawa tace,
matarsace ta sokesa nima bansan daliliba yanxu haka ta gudu police sunbita....
isowar police gurin yasayin shiru tana kallon inspectan.
kalllonta yayi cikin jimami yace,
haj saidaifa haquri yarinyar motarsu ta qone qurmus muna tsaye ta cinye babu wanda yafita acikin.......
ganin sukayi aleeya ta yanke jiki ta fadi agurin bata motsi,
juyawar dazatayi sai ganin ammy da bilal tayi kowannensu ya daskare ga dukkan alama ma suma suman ne sukayi atsaye jin abinda inspectr yafada daga isowarsu.
hankali tashe akayi emergency da aleeya ammy ma nan take hawan jininta yatashi akai gaggawar kwantarda ita sbd kartayi kwalapsin, bilal kuwa tsayawa yayi cak gaban gadon ammy idanuwansa jajir jijiyoyin kansa har wani motsi sukeyi tsabar tashin hankali sam kwaqwalwarsa takasa daukar cewa 'yar uwarsa ta tafi tabarsa.
sulalewa mum tayi takoma gida afusace ta banka qofar dakin sarah tareda fusgota ta jehota waje tareda watso mata kayanta tace,
duk wata masifa data afkomin nida yayana kece, nayi baqin ciki da dana sanin kawoki gidana, kin tarwatsa rayuwar yayana, na hana yarona farin ciki ina kallo rayuwarsa ta ta6ar6are sbd ke, yanxu kinzo kinyi qoqarin kashemin taheer inaji ina gani na maqalawa wata sbd kar laifin yashafeni gashi ta rasa ranta ta rasu ta sanadinki amma bazan iya fadaba sbd dole nima saina fuskanci sharia dan haka tun kafin kowa yasani kitashi kibarmin gidana bana buqatar sake ganinki inason gyara abubuwan dana lalata da kaina.
muqewa sarah tayi tana kallon bayan mum din ido a waje, juyawa mum tayi tayi ido biyu da dad tsaye idanuwansada fuskarsa qunshe da tsananin 6acin rai,
mummunan faduwa gabanta yayi wani mugun zufa ya karyo mata tadaga qafa zata matso ya daga mata hannu da ido jajir,
sarah na ganin haka ta sulale takwashi kayanta tabar gidan.
cikin wata irin murya mai tsananin sanyi yace,
faraah kanki kika cuta, dasaka hannunki cikin lalacewar danki, dasaka hannunki cikin mutuwar yar mutane, bazan miki komaiba sbd haryanxu duniya bataimiki darasin daya kamata saidai nizan dauke 'dana mutafiyarmu bazaki sake ganinmuba insha allah dawood ma zan dawo na daukesa sbd yanxu matarsa na buqatarsa na rashin yar uwarta datayi.
matsowa tayi da gudu ta zube gabansa tareda riqo qafafuwansa tasaki wani irin kuka mai qarfi ya zame qafafuwansa ya wuce ya tattaro duk wasu takardu da abubuwan buqatarsa dana taheer yafice tabisa har jikin mita tana kukan tashin hankali amma ko kallonta baiyiba yawuce da gudu yabar gidan.
yana isa asibiti cikin qanqanin lokaci yasaki kudi sosai nan take suka samu flight aka saka taheer suka tafiyarsu bataredama taheer din ya farfadoba. #mamuhgee.
vote and follow pls. _*DAWOOD*_ _wattpad@mamuhgee_
*32* NOT EDITED
bayanta baffa dahiru yabi da kallo yana jinjina alamarin kafin ya nufi dakinsa ya zauna yana sake nazarin alamarin, baifitoba sai maraice yayi alwala shidasu dawood suka wuce masallaci har lokacin sosai dawood yake cikin yanayi na jin zafin abinda laylar ke shirin yi duk da dai yasauki alqawarin kobataso saiya aureta yagaji da wannan azabar datake gana masa arayuwa.
amasallaci bayan sallar magriba baffa yasamu mal liman yayi masa bayani akan rasuwar mijinta dakuma auren dasukeson adaura,
dogon naxari mal liman yayi kafin ya nisa yakalli baffa dasu dawood din yace,
tabbas zata iya aurensa tunda wancan qaninsa din kunce yarasu saidai dole sai bayan tagama takaba...
shiru baffa yayi na seconds kafin ya dago murya a tausashe yace,
eh to babu wani abu na aure daya ta6a shiga tsakaninsu hasalima basuyi rayuwar irinta zaman aureba kuma kafin rasuwarsa yabata sakinta ahannunta.
sake gyada kai mal liman yayi yasake cewa,
eh to zasu iya aure amma idan son samune zaifi subari zuwa gaba kamar......
katsesa sufyaan yayi dafara zayyano masa komai daga farko zuwa qarshe.,
mal liman yayi shiru tareda qurawa dawood ido yana jinjina kai yace,
sannu dauda.
kallonsa kawai dawood yayi da lazy eyes dinsa shidai fatarsa kawai ace zaa daura auren.
tabbas daura musu aure bai haramta ba dama dai nasone subari tayi kwana biyu kamar zaifi amma tunda abun hakane gobe takasance alhamis jibi ranar jumaa insha allah da safe sai a daura auren,allah yasa hakan shine mafi alkhairi arayuwarsu duka.
amin sukace dukkaninsu dawood najin wani sanyi da kasala na shigarsa sbd yasan babban burin rayuwarsa ne zai cika idan NUR dinsa tazamo matarsa, godiya sukai masa sosai kafin suka miqe,
basu koma gidaba saida sukai sallar isha suna komawa suka shige daki duk da zuciyarsa a tsananin takure takedason ganinta amma hakanan ya daure sbd yasan idan ya matse mata zatacene bazatai aurenba gwara yabata space har yasamu adaura auren, yanaji inna halima nayiwa baffa complain taqi fitowa har lokacin kuka takeyi yayi zuru tareda mayarda dukkanin hankalinsa kan qofar dakin datake, sufyaan dake qoqarin sanardashi maganarsu saraah ganin hankalinsa baya jikinsa yasa yabari harsai bayan auren idan hankalinsu yadan kwanta.
da tsakar dare kasa kwanciya yayi sbd yana jiyo ajiyar zuciyarta alamun idanunta biyu sam bayada sukuni na jiki dana zuciya sbd rashin sanin halinda take ciki.
har asuba yana zaune ko gyangyadawa baiyiba sbd ita.,
suna fita sallar asuba itama tafito daqyar sbd ko gani batayi sosai sbd kumburin idanuwanta na kuka,
alwala tayi takoma ta tayarda sallah a zaunema tayi sallar sbd wani irin mugun jiri da zazza6i mai zafi dayake cinta,
tana gamawa ta dunqule gurin tana kakkarwa tareda wani irin wahalallen nishi.
hankalin inna halima ne yafara tashi ganin halinda take nan tazauna jiran dawowarsu baffa basu dawoba saida gari yayi haske sosai.
maganin zazza6i baffa yabayawa innar abata shima bayason matse mata dankarma ta tayarda maganar rashin son auren,
dawood ma ganin zai iya rasa nutsuwarsa yasa sufyaan jansa suka fita bayan gidan,
zama sukayi bakin wani dutsi ya rufe idanuwansa ahankali tareda jinginarda kansa jikin ice zuciyarsa na qara rasa sukunin halinda nur din ke ciki, tabbas NUR itace rayuwarsa,farin cikinsa,baqin cikinsa,qaddararsa dakuma burinsa aduniya.
dafasa sufyaan yayi ahankali tareda tausasa murya yace,
idan andaura auren ya kake tunanin zamu fuskanci su mum?
bude idanuwansa yayi dasukai jajir ya qurawa qasa ido kafin ya dago cikin takaici yace,
idan na aureta she's mine, my responsibility, my future, rayuwar danayi abaya cikin mummunan yanayi yasa na qara daukan wani life lesson so na shirya gyara rayuwana ta hanyar shimfida sabuwar rayuwa dan haka ba ruwana dasu mum or wata aleeya can,am gonna take her somewhere,where we can start a very happy married life sai bayan wani lokaci zamu dawo idan sunga dama su kar6emu idan sunga dama su gujemu.
jinjina kai sufyaan yayi tareda cewa,
ina bayanka lets start a new life afterall jass yakusa cika shakarunsa biyu yafito....
yes saura sati biyu yacikasu inaga wannan wata damace da allah yasake bamu mu shimfida kyakkyawar rayuwa mai tsafta.
murmushi suka saki dukkaninsu sai alokacin yaji dan sauqin abunda yakeji.
suna gurin baffa yazo wucewa gona sufyaan ya miqe yabisa dawood kuwa gida yakoma yashige daki ya kwanta yana kallon sama tareda lumshe idanu yana tunanin abubuwa da dama.
sufyaan kuwa saida sukayi nisa sosai yakalli baffa yace,
baffa inason shiga inda zansamu harkar banki maana wayayyen guri haka.
tsayawa yayi tareda juyowa gefen sufyaan din yace,
mezakayi dabazaka bari sai bayan daura aurenba?
gyara tsayuwarsa yayi yace,
inason nine zanbiya kudin sadakin abokina sbd wannan shine burin maska harya rasu shine yayi alqawarin biyawa dawood sadakin aurensa matuqar da NUR ne ayanxu dabaya raye inason dauke wannan nauyin.
murmushi baffa yayi yace,
to ai dan wannan ba matsala bane ni zan biya....
aa baffa kaine kazamo kamar kawu ga nur kuma kaine zaka bada aurenta baikamata ace sadakinta yafito daga garekaba nine nayi niyya kuma nine zanbiya insha allah.
to tunda kanaso hamisu rakasa kuje gonar mal jamilu kugani idan motar akori kurarsa bata wuce gariba saiku bisa yawuce daku idan zai dawo yadawo daku.
juyawa sukayi suka wuce shima ya qarasa gonarsu dake kusada rafi.
cikin saa suna zuwa suka tararda yadauki kayan miya zai wuce suka fada yawuce dasu atakure bama kamar sufyaan dabai ta6a shiga irin wannan motarba da duk qarfece ba guri mai laushi ko kadan ko gurin zaman duk ya cinye sosai yakecin duwawu amma haka yadaure sukaita gurxawa.
tafiya mai nisa sosai sukayi kamar bazata qareba daqyar suka iso wani dan gari ba laifi yanada cika sosai dakuma abubuwan zamani kamarsu bankuna biyu da yar babbar kasuwa da babbar tashar motoci harda babbar asibitinsu gasu da wuta koina.
bai tsaya bata lokaciba yashiga banki bayan dogon turanci daqyar ya iya cire kudi masu yawa ta slip yafito suka shiga kasuwar daqyar ya iya shigarta aka kaisa wani babban shagon saida kaya daqyar yasamu shaddodin dubu ashirin ashirin yasiya guda biyu agurin aka dinka musu shida dawood ba aiki ba komai kawai babbar riga hudu yace ayi musu ta ishesu tunda ana daurawa zasu wuce.
gasassun kaji dakaton na drinks yasiya da takalmi sai dogayen riguna guda biyu daya siyowa nur. daganan lafiyayyar matarda bataji jikiba golf yayi musu shata tamayardasu da sharadin acan mai motar zai kwana washe gari bayan daurin aure zai fito dasu qauyen abuja zai kaisu.
sai bayan magriba suka iso nan ya miqawa inna halima kayan nur dakuma kajin sai baffa babbar riga daya hamisu daya shima daya sai ango daya.
dawood baiyi wani mamakiba sbd shidai amatse yake da gobe tayi adaura auren su wuce.
lokacinda inna halima takai mata kayan kar6a kawai tayi ta ajiye sbd tuni kuka ya qaurace mata tayi zuru zuru ko iya bude ido sosai batayi.
daren yau dinma daga ita harshi babu wanda yayi bacci uwa uba abinda yake tsananin cinsa shine yinin ranar gaba 'daya basu ga junaba ba qaramar azabtuwa da dauriya yayiba.
ana kiran asuba yasaki wata irin ajiyar zuciya shiya riga kowa fitowa yayi alwala kafin suka fito sukai alwalar suka nufi masallaci baki daya.
kamar koyaushe saida gari yayi haske suka dawo suna shigowa gidan cikin sa'a idanuwansa suka sauka akanta lokacinda take qoqarin aje butar data fito bayi.
sunkuyar dakai tayi daqyar dasashiyar muryarta dake rawa ta fito asanyaye ta gaida baffa dake gaba.
amsawa yayi cikeda farin ciki kafin yq wuce sufyaan dake bayansa fuska asake yace,
gud morning.
'daga masa kai kawai tayi tareda juyawa da sauri zata bar gurin yakasa haquri ya riqo hannunta ta tsaya cak numfashinta na futa da sauri sauri.
matsowa taji yanayi ta janye hannnunta da sauri tareda shigewa daki ta dafe qirjinta sbd bugawar dayake.
kallo yabi qofar dakin da shanyayun idanuwansa dasuka galabaita dasonta kafin ya wuce dakin dasuke shima.
sauran kajin jiya sufyaan yaci shukuwa bakinsa wata irin bushewa yayi yawunsa suka qafe babu abinda ke gabansa dayafi yaga andaura auren, baida wata nutsuwa ko sukuni ayanzu saiyaga nur tazama tasa.
wanka yayi yamayarda kayansa da aka wanke jikinsa wani irin sanyi yayi sosai daqyar sufyaan ya taimaka masa yasaka babbar rigarsa sbd bai iya sakata ba.
koda baffa yafito yace su fito nan jikinta ya tsananta rawa tanason yin kukan amma takasa haka ta rarrafo ta fito ta tsaya gaban baffa ta sunkuyar dakai sbd idanuwanta dasukai jajir zatayi magana dawood dake gefen baffa yadawo gabanta tareda kafeta da lazy eyes dinsa murya amatuqar sanyaye yace,
zakice bakyson adaura miki aure danine sbd kema kinga na zama abun qyama ko?
'dagowa tayi ahankali takallesa sai takasa magana sufyaan na ganin haka yayi saurin cewa,
baffa muje su malam nacan najira .
wucewa sukayi kowanne na gyara babbar rigarsa shikuwa saidaya qara kallon fuskarta dake sunkuye kafin ya wuce.
suna futa ta shige daki tareda qanqame jikinta dake wata irin rawa wace irin masiface zata sameta yau ta auren mijin aleeyarta.
sukam suna isa dama tuni sukawai jamaa ke jira sbd anyi sanarwa daurin auren bayan sallar asuba nan aka fara sufyaan yafito da sadaki naira dubu hamsin nan take aka gabatarda daurin auren aka shafa fatiha. #mamuhgee
vote and follow. *_DAWOOD_* _wattpad@mamuhgee_
*33* NOT EDITED.
wasu irin hawayene suka ciko idanuwansa dasuka qanqance sbd yunwa da wahala dakuma fargaba, kallon mutanen dake miqa masa hannu yake kamar wani wawa sbd tsanananin mamaki da farin cikin daya kasa gasgatawa yau NUR tazama tasa da sauri ya miqe yayiwa allah sujjada yatashi tareda rungume sufyaan daketa faman washe baki farin cikinsa baya misaltuwa.
saida aka gama komai mutane suka watse suka sakeyiwa mal liman da baffa godiya sosai nan sufyaan yayiwa mal liman babbar kyautar kudi sosai sukai masa bankwana suka wuce sbd so suke su isa abuja da wuri,
gida suka nufa ahanya ya zare babbar rigar tareda zuba hannunsa a aljihu murmushi yake saki yana tafiya kwata kwata hankalinsa baya taredasu sufyaan da baffa shi wata duniyar tunanin dayake dabam,
sufyaan na lure dashi yasaki murmushin farin ciki yana girgiza kai tareda cigaba dayiwa baffa bayanin wucewa zasuyi yanxu.
kudinda yatanadar masa tun jiya ya ciro yabasa cikin girmamawa yace,
insha allah dakomai ya gama daidaituwa zasu sake dawowa sukawo gaisuwa.
godiya kawai baffan yayi tareda cewa,
bakomai allah dai yakawo fahimta acikin alamarin cikin sauqi.
amin''''sufyaan yace yana kallon gefen dawood da wani irin annuri ke fita fuskarsa baimasan mesuke cewaba.
suna isa gida cikin tsananin farin ciki inna halima tayi musu allah sanya alkhairi sufyaan ne kawai ya amsa dawood hankalinsa nakan qofar dakin datake yasan kuka takeyi kobaa fadaba.
ko dakuna basu shigaba sukace wucewa zasuyi,
inna halima tashiga dakin datake takalleta taga har lokacin ko wanka batayiba tana zaune yanda take tundazu harlokacin jikinta bai daina rawaba.
dafata inna tayi tareda yimata yar qaramar nasiha ta dagota daqyar suka fito tana fitowa idanuwanta suka sauka cikin nasa ta sunkuyar dakanta tareda dagawa baffa dake mata magana kai.
'yar nasiha baffan yayi mata tareda bawa dawood amanarta suka fito,
motarda sufyaan ya dauko musu tun jiya shata har qofar gidan ta qaraso suka shiga suka wuce hawayenta na saukowa ahankali na fargabar abunda zasuje sutarar.
sufyaan ne agaba itada dawood din abaya tunda tashiga ta juyar dakai gefe tareda rufe idanuwanta ahankali sbd ko jinsa zaune gefenta tsananta bugun zuciyarta yake bare ta iya kallon gefensa.
qura mata idanuwansa dasukayi laushi yayi cikeda wani irin farin ciki shikadai yasan irin rayuwar dayake musu tunanin shimfidawa kafin sudawo sbd bazai ta6a gangancin bari suje gida yanxuba a 6angale masa auren dako kwana daya baiyiba aduniya dan yasan sarai hakan zata iya faruwa takowane 6angare na mum dinsa kona su aleeya.
doguwar tafiya sukayi babu wanda yayi magana acikinsu basu iso abuja ba sai yamma sosai nan sufyaan yayiwa drivern magana kai tsaye ya nufi gidan maska dasu.
lokacinda suka isa gidan sosai taji habkalinta yatashi ta kalli dawood din da sauri ganin yaciro mukullin gidan inda suke aje spares cikin wata flower dake qofar shiga,
daure fuska yayi nantake yakoma dawood dinsa sbd karma tasamu fuskar jeho masa wani zancen,
ganin yanayin fuskarsa yasa ta sunkuyar dakai tareda rufe ido hawayen ciki suka sauko ta share ahankali,
suna shiga sufyaan yayi saurin shigewa bedroom daya yabarsu apalon.
kallonta yayi yaga yanda ta tsaya batada alamar motsawa ya matso ahankali yakamo hannunta yakaita har tsakiyar 'dayan bedroom din ya juyo yafito yakoma wanda sufyaan yake sbd duka gidan is two bedrooms flat ne,
tu6ewa yayi ya kwaso kayan daya cire yaje yazuba dusbin yadawo yashiga wanka,
kwanciya yayi cikin ruwan dumin tareda lumshe idanuwansa yasaki ajiyar zuciya ahankali wani irin kwanciyar hankali na shigarsa,
ya jima acikin toilet din yana dumama jikinsa tareda yin wankan daya jima baiyi irinsaba kafin ya fito daureda towel iya qugunsa.
yana fitowa ya tsaya gaban mirror tareda shiryawa cikin three quater black da black shirt mai hula yayi sallah yana idarwa ya kalli sufyaan daya fito wanka yace zashi gida yadawo.
dayake basu sallami drivern ba sai gobe tukuna saiya shiga motar suka fuce,
nesa da gidansu yasa drivern ya tsaya yajawo hular rigarsa yarufe rabin fuskarsa ya isa qofar gidan ahankali cikin saa babu kowa sai maigadi,
maigadi na ganinsa ya miqe da sauri cikin sauri ya girgiza masa alamar karyayi magana ya matso kusadashi sosai yace,
akwai mutane sosai aciki gidan?
bakowa yallabai alhaji yayi tafiya hajiyama bata dade da fitaba zuwa asibiti can gurin haj aleeya daaka kwantar kwana biyu yanxu sbd rasuwar mai dakin taheer.
wat yace da dan qarfi kafin yayi saurin yin qasa da murya yace,
kana haukane zakace nur ta mutu,,,get lost and karka fadawa kowa nazo komai rintsi.
cikin sauri yashiga gidan direct part din mum yafara zuwa yashiga dakinta yafara duddubawa baiga komai na nur ba yafito yashiga dayan dakin cikin sa'a yaci karo da handbag akan gadon dakin da sauri ya bude yana dubawa cikin saa yaga passport dinta bai tsaya cire komaiba yadauki jakar tareda akwatinta dayagani aje tun dawowarsu bata budesaba yasan ba shakka tatace,
maigadi yabawa yakai masa mota da sauri shikuma ya nufi part dinsa ya dauki passport dinsa dana sufyaan tareda wasu kayansa da laptop da duk wasu mahimman takardunsa da komai nasa mai mahimmanci ya fito.
saidaya qara gargadar maigadi tareda basa wasu kudi masu dan kauri daya tsinto a dakinsa suna barin gurin mum da Nana nadawowa daga asibiti sbd har lokacin anrasa gane kan aleeya ciwo take sosai anyi qarin ruwa da maganguna har anfara gajiya babu wani saiqi sbd ba qaramin bugun zuciyarta da qwaqwalwarta batun rasuwar layla yayiba ga 6angare guda annemi gawarta acikin motar baaganiba.
yana isa gidan yazauna palo tareda kallon sufyaan dake zaune palon yana waya da lndline ta gidan,
waya yake da wanda zaiyi musu komai so suke kamai rintsi gobe su wuce. yana gamawa order daya bayar daga pizza kitchen ta iso ya bude qofa ya karbo tareda ajiye nasu ya miqawa dawood na layla.
kar6a yayi tareda jan akwatinta ya nufi dakin,
knocking yayi ahankali ya tsaya jiran ta bude.
tsawon mintuna bata budeba yasake knocking tareda tura qofar ahankali yashiga tareda turo qofar,
zaune take qasa kan daddumar sallah ta kwantarda kanta bakin gado idanuwanta alumshe.
qura mata ido yayi tsawon mintuna kafin ya qaraso ahankali tareda aje mata abincin gabanta cikin wata irin sanyin murya yace,
kici abinci ga kuma kayanki nan na dauko miki.
bude jajayen idanuwanta tayi takallesa tanason yin magana takasa sai kawai ta miqe ta zauna bakin gadon batareda tasake dagowa ta kallesaba,
kasa hkr yayi ya zauna bakin gadon kusada ita sosai tayi saurin miqewa zuciyarta na bugawa da sauri ya riqo hannunta tareda dawo daita ta fado masa ya zaunar da ita kan qafafunsa ya riqeta gam,
kasa motsi tayi sai kawai hawaye suka 6alle mata tafara fitarda kuka mai qaramin sauti sbd ba qaramin riqoyayi mataba,
jin kukan nata na shigarsa sosai yasa ya sassauta mata riqon tareda dago fuskarta yana kallon hawayenta murya a tausashe yace,
please NUR kukan ya isa haka, tun shekaran jiya kike kuka har yanxu zaki jawa kanki ciwon kai nayi miki alqawarin komai zaizo da sauqi insha allah so please nur kina axabtardani da wannan kukan.
tsananta kukan tayi harda shesheka ya shigarda ita ahankali cikin jikinsa ya rungumeta tareda sakin wata kasalalliyar ajiyar zuciya,
saidatayi kukan har baya fita sai ajiyar zuciya kawai takeyi yana shafa bayanta ahankali alamar rarrashi hartayi shiru kafin ya miqar da ita yaja hannunta har toilet ya hada mata ruwan wanka masu 'dumi ya bude sabon brush yasaka mata toothpst yasaka mata cikin hannu kafin yafito yaja mata qofa,
ahankali ta daga kai takalli fuskarta ta mirror taga yanda kamanninta suka canza sbd kuka kafin tafara brush din ahankali tana qoqarin daidaita kanta da bawa kanta nitsuwa da qarfin hali kafin ta fuskanci aleeya sbd tasan tariga tazamo butulu agun aleeyarta.
wanka tayi sosai kafin ta dauro towel ta fito cikin saa baya dakin yafice.
ko mai bata shafaba ta bude akwatinta ta dauko doguwar riga mara hannu kawai tasaka takoma ta zauna tareda 'daukar ruwa kawai tasha sbd batajin zata iyacin komai.
anayin sallar isha ta miqe tayi ta koma gado ta kwanta tareda rufe idanuwanta ahankali tana tunanin hindasu aleeya suke ciki ayanxu dan tasan sunacan suna nemanta.
cikin daren komai na tafiyarsu ya kammalu suka harhada komai nasu gari na wayewa sukaje gidan mamyn maska sukai mata bankwana tareda yimata bayanin komai tareda aje mata kudade masu yawa dazasu tafi tareda ita suka dawo sbd tace tanason ganin nur,
lokacinda tashiga dakinta da sallama azaune tasameta bakin gado tayi wanka ta canza kaya zuwa doguwar riga black.
tanaganin mamyn ta sunkuyar dakai tareda zamewa qasa ta gaidata cikin sanyin murya.
amsawa tayi tareda sakar mata murmushi tana kallon dawood daya zubawa laylar ido.
fita sukayi ta gyara zama sosai tafara yiwa laylar nasihar yarda da qaddara ta rungumi mijinta sbd aure dai anriga andaura gwara su tsaya su fuskanci yanda zasu gyara gaba da abunda zai biyo baya,
sanyi jikinta yaqara yi duk dadai babu mai karkare butulcin datayiwa aleeya.
lokacinda mamyn zata tafi tabata kyautar yankunnayen zinari da turaren datazo mata dashi kar6a tayi tareda godiya hawaye na zubo mata,
bayan tafiyar mamy lokacin tafiyarsu yayi yashigo dakin ya tsaya daga bakin qofa tareda zuba hannayensa duka biyun cikin aljihun wandonsa yace tafito,
tasowa tayi ahankali tazo gabansa ta tsaya tareda kallonsa ta dauke kai cikin dasashiyar murya tace,
muje gida dan allah karmu tafi koina.....
girgiza mata kai yayi kafin yace,
zamu tafine yanxu sbd kar masu nemanki su kamaki yanxu zuwa gaba idan angano gskiya zamu dawo so please karkice bazakiba i promise to bring you back idan lokacin hakan yayi.
shiya jawo akwatinta tariqo handbag dinta suka fito kamar yanda suka zo daga qauyensu baffa haka suka nufi airport sune abaya sufyaan agaba har suka isa ba 6ata lokaci jirginsu ya daga.
tunda suka shiga jirgi yana riqe riqedq hannunta akai akai yakan juyo ya kalleta har wani irin wahalallen barci data manta rabonta dashi ya dauketa a kafadarsa.
sai dare sosai suka isa direct gidansu suka nufa nan kowa yayi hanyar dakinsa. kasa zama tayi ganin daki daya zata zauna dashi ganin yanda takasa sukuni yasa ya riqo hannunta ya zaunar da ita bakin gado tareda sakar mata wani qayataccen murmushi yana kallon face dinta yace,
sweethrt relax ok,,,ba anan zamuyita zamaba zamu dan kwana biyune anan kafin jass yafito zamu tattara mukoma wani gurin ne acan zamu fara sabuwar rayuwa.
zame hannunta tayi tareda jinjina masa kai ya miqe yashige toilet.
wanka yayo wanda yasaka masa wata irin nutsuwa yafito daureda towel iya qugu ta dauke kai tareda miqewa ta shige toilet dindaya fito. #mamuhgee
vote and comments pls. *_DAWOOD_* _wattpad@mamuhgee_
*34* NOT EDITED
Tsayawa tayi cikin toilet din tana qoqarin saita numfashinta kafin tayi wanka tareda dauro alwala ta fito,
akan daddumar sallah tagansa atsanake ta shirya cikin doguwar riga fara mara nauyi ta zura hijab tazo gefensa ta tayarda sallah.
tana gamawa yasata miqewa sukai nafilar godewa allah daya cika musu burinsu.
sosai yayiwa allah godiya tareda yiwa maska,taheer da jass addua sosai kafin ya miqe yafice dakin.
a palo ya tararda sufyaan tayi musu order abinci yashiga kicin ya dauko qaramin tray da spoons bayan ya dauraye ya jera mata tafeda ruwa da drink mai sanyi ya koma dakin.
zaune take har lokacin kan sallayar saidai idanuwanta dake lumshe.
ajiye tray din yayi tareda zama kusada ita yana sakin wani sahirtaccen murmushi,
bude mata abincin yayi chips ne da kidney souce sai chicken shawarma.
kallon abincin tayi ta kallesa tareda girgiza masa kai ahankali.
shima girgiza mata kai yayi yana smiling harsaida dimple dinsa ya lotsa ya matsoda ita jikinsa sosai ya debo da fork yakai bakinta tareda kafeta da idonsa.
budewa tayi dole ta kar6a yasakar mata qayataccen smile tareda matsoda bakinsa kunnenta cikin rada yace,
thaz my beautiful bride.
wani kallo ta watsa masa ya daga mata gira daya yace,
yes baby...
rasa abinyi tayi sai kawai tayi kamar bata jisaba yaci gaba da bata abincin tanaci,