Dawood complete - Chapter 6
Dawood complete Chapter 6: Dawood complete Chapter 6. Ahankali suka Fara nisa akaratunsu sbd exams ma suke rubutawa kuma zuwa lokacin tuni aka yanke…
4,437 words
Ahankali suka Fara nisa akaratunsu sbd exams ma suke rubutawa kuma zuwa lokacin tuni aka yanke shawarar tsayarda ranar bikinsu danma antsaya jiran dawood din Layla yazo da iyayensa sukuma su dad 'dinsa daya tuntubesu da maganar yaushe zasu koma Nigeria sukace sai next month sbd sukuma anasu tsarin so suke sai su aleeya sungama exams saisuxo ayi komai gabaki 'daya.
Ranar dasuka gama exams washe gari suka wuce Lagos sukuma su mum aranar suka sauka Abuja dawood kuwa sai washe gari zai sauka daga baya su sufyaan zasu biyosa sbd kar saraah tayi zargin wani Abu.
Ranar dasuka dawo tun a airport suke mamaki da tsokanar Bilal ganin yanda lokaci 'daya Yana Shirin zama saurayi Dan harma ya kusa kamosu a tsawo.
Ranar gidan cikin farin ciki da nishadi suke komai sbd gida ya kammale.
Ana saura biyu su mum zasuzo Lagos ammy tabugawa anty Nana tafada mata maganar neman aurensu aleeya daza'azo atsayar da date.
Siyama na zaune Koda ummanta ke waya da ammy taji duk abinda aka fada ta ta6e Baki tana cewa,
Duka dukafa Basu Dade dafara University ba shine za'ayi musu aure.
Numfashi umman tasake kafin tace,
Ba Dole suyi musu auren da wuriba kinaji tace bazaa dauki lokaciba za'ayi sbd aurene za'ayi na yayan billionaires sbd mazajen ko wacce ba'ama qasarnan suke zauneba.
Wani kallo siyama tayiwa umman tana juya zancen cikin ranta kafin tace,
Wai harda ita sadaka yallan ba'a qasarnan zatai aureba.?
Saikuma kiyi tunda ke kin kasa tsaida ruwan Ido ki tsayar gashi harkin gama degree saiki tsaya kiyita kallon anayi.
Wani 'daci ta ha'diye a maqoshinta tareda aje nail polish 'din datake shafawa a hannunta ta miqe tana cewa,
Lokacin komawata gidan yayi.
Harararta umman tayi tace,
Ki tsinci uwar me acan bayan duk buhun wulaqancinda sukai Miki Akan sadaka yallah.
Wani shu'umin murmushi tasaki tareda kallon umman tace,
Kika sani nima idan inacan abban yahadani da 'daya daga cikin yaran rich mutanensa.
Baki umman ta washe tana cewa,
Hakane kumafa...wlh maza shirya gobe kitafi kafin kitafi kisayi 'yan mayukan Nan Masu Dan tsada ki qara fito da kyawunki tunda ba finki akayi ba. #Mamuhgee
Vote Comment. *_DAWOOD_* _wattpad@mamuhgee_
*17* Washe gari motar asuba tabi zuwa Lagos taso shiga jirgi Amma sbd karma ta tambayi ammy kudin ticket kamar yanda tasabab idan zata gudun kar ammy tace tayi zamanta yasa tashiga mota Tunda suka dau hanya ta kwantarda kanta tareda rufe ido cikin ranta tana kissima yanda zata Hana auren Layla auren mijin yadawo kanta.
Lokacinda ya sauka a Abuja taheer ne da kansa ya daukosa daga airport cikeda murna da farin cikin ganin 'dan uwansa suka rungume juna sbd sun Dade Basu ha'du shi taheer baya zama sbd aiki shikuma Bai cika zuwaba tunda su mum suka tarki zama Nigeria.
Koda suka iso gidan anshirya Masa dishes na lunch kala kala cikeda farin ciki mum ta qarasa ta rungumesa atare itadashi sukace,
I missed you my love.
Itakuma tace,
I missed you more mi'amor.
Direct part 'dinsa da aka gyara aka zuba komai yanda akasan yanaso da duk sauran abubuwan amfaninsa duka mum tasiyo tazo dazu tun daga can aka Kai luggages dinsa.
Saida yayi wanka ya kwanta ya huta Yana tashi Nur yafara Kira tana ganin numbers ta Nigeria tasaki wani lallausan murmushi sbd farin ciki da wani irin kwanciyar hankali dataji ya shigeta.
Tana 'dauka taji lokacinda ya sake ajiyar zuciya ahankali tareda Kiran sunanta can qasan maqoshinsa Wanda dagashi har ita Saida tsigar jikinsu ta tashi.
Akasalance tace,
Do you really have to do this Everytime?
Lumshe Ido yayi tareda sake bu'de Baki daqyar yace,
you're my life Nur,,I love you and know all I'm feeling is I can't live a life without you in it, Duk duniya yanxu Kece kawai abinda nake nake tsananin son samu so just tell su ammy su shirya I'm coming tomorrow.
Ajiyar zuciya tasake ahankali tanajin sabuwar qaunarsa da sonsa na qara shigarta murya qasa qasa itama tace,
Thank you.
Qasa qasan Shima daqyar yace,
Tell me how much you love me...
Words can't describe it just keeps one thing in mind har lokacinda numfashina zai bar jikin Kaine ka'dai zaka zauna azuciyata wannan matsayinkane Kuma alqawarine bazai ta6a canxawaba.
Shiru yayi jikinsa na qara mutuwa sbd yazamo cikin jininsa jikinsa yake duk lokacinda muryarta ta sauka cikin kunnuwansa sai dukkanin jikinsa ya mutu saidai dayake dama baida hayaniya ko kazar kazar baza'a ganeba saisu jass kawai dadukasan halin abinsu.
Shiru sukayi dukkaninsu tsawon lokaci can Kuma murya a kasalance yace,
Do you miss Nur.
Murmushi tasaki kafin tace,
No.
Wat"""yafada da sauri tareda tashi daga kwancen zaiyi magana ta rigasa cikin murmushi Mai sauti tace,
Silly"""""""tafada ahankali tareda kashe wayar ta aje fuskarta na qara wanxuwa da murmushin data kasa dainawa.
Aleeya data sata gaba da kallo harda tagumi sai dariya take tana ganin ta kashe ta tashi zaune a tsakiyar gadansu tana leqa fuskar laylar dake nuna tsananin sonda zuciyarta ke Masa tace,
Hmmm anya Layla dawood 'dinnan Bai tafi da fiyeda rabinki ba yabar Mana saura.
Harara ta watsa mata still fuskarta 'daukeda murmushi batareda ta Bata amsaba.
Sake matsowa tayi jikinta ta kwantarda kanta a cinyar Layla din tace,
Layla koda Ni bansamu soyayyar mi'amor ba zan dawwama cikin farin ciki ke kinsamu soyayyar Wanda kikeso tunda bamu taru mun rasaba.
Kallon fuskar aleeyar tayi cikin sanyi Jin yanayin muryarta,, Shafa gashinta dake tsefe tayi itama cikin sanyi dason qarfafa Mata gwiwa tace,
Ina roqon Allah idan har Dole 'dayanmu ne zai samu farin cikin samun soyayyar Wanda yakeso to yazamto Kece sbd Ni zanyi farin ciki naji Dadi idan Kece kike tareda abinda kikeso sbd Ni na 'dandana naji ko haka na tuna zanji Dadi.
Nikuma ina roqo da dafatar dukkanin 'yayana su samu soyayyar wainda suke so har abada.
'dagowa sukai atare sukaga ammy tsaye hawayen da kowaccensu ke riqewa na tunanin halinda zasu shiga idan hakan dasuke tunani takasance suka gangaro musu da sauri ammyn ta qaraso ta rungumesu itama jikinta na mutuwa.
Washe gari Layla ta sanarda ammy zuwan dawood da iyayensa ammy tafadawa Abba shikuma ya bugawa cj ya fada Masa Dan suxo su ha'du da iyayen dawood din layla a tsayar da Rana tare.
Threequarter yasaka black da black shir Mai hadeda hula ya fito ya nufi gurin mum dinsa sbd dad bayanan tunda ya iso Bai gansaba.
Dama tunda yatafi takasa sukuni sbd baici abinciba Kuma gashi batason damuwarsa tanason yasamu isashen hutu kar ciwon Kai na stress yakama Mata shi.
Yana shigowa palon ta aje magazine din hannunta tareda miqa Masa hannu ya qaraso ya zauna kusada ita.
Kallonsa tayi Cikeda kulawa tace,
Bakaci komaiba haryanxu my love.
Kallonta yayi cikeda qaunarta aransa yace,
No mum nasha milkshake banajin yunwa yanxu I want to talk to you and dad abt sumthing serious..
Murmushi tasaki tana kallonsa tace,
Ok kabari sai dad dinka yadawo after dinner we'll talk Amma right now I wanna tell you something,
Zuba Mata lazy eyes dinsa yayi sbd Yana iya hango zumudi da farin ciki akan face dinta da abinda takeson fada.
Well you see my love Akan maganar aurenka ne munason zuwa jibi idan mukaje a tsayar da ranar auren gashi haryanxu bakuga junaba shine nakega why not Kai gobe ka wuce kafin jibi muzo kun...ga ju..na.....
Rawa muryarta tafara da I ina sbd kallon daya tsareta dashi Daqyar tasamu zancen yakai qarshe tace,
Meyasa kake kallona haka.
Lumshe Ido yayi tareda riqo hannunta daya yace,
Sorry I didn't get wat you're saying ne.
Ajiyar zuciya tasaki ta 'dauka zaice yafasa ne tasaki sabon murmushi tace,
Yarinyarda muka za6ar maka nake nufin kaje kuga juna tunda kace kaima ka shirya aure kakeso....
Zame hannunsa yayi daga nata Yana sake kallon fuskarta yaga idan da gaske take.
Ganin Yana qoqarin miqewa yasa tayi saurin riqosa zatai magana ya katseta da cewa,
Bansakaku Nemo min kowaba Koda nayi maganar zanyi aure nafada ne sbd nasamu wadda nakeso Dan haka tun wuri mum kidaina maganar nace zanyi aure Kun Nemo wata.
Murmushin qarfin Hali tasaki cikin sigar lallashi tace,
Come on sweetheart idan kaga yarinyar zaka sota, she's very beautiful, classy,rich and.....
Zare hannunsa yayi tareda barin gurin yakoma part 'dinsa gaba 'daya.
Bayansa tabi da kallo tanajin wani irin zafi na taso Mata duk da split AC kusan guda uku dasuka sanyaya palon.
Komawa tayi ta zauna zuciyarta na tsalle sbd Sarai tunda yace bayaso bayi zaiyi ba itakuma tunda taso wannan auren bamai hanashi sai Allah duk yanda tasan zatayi ayi auren saitayi Amma Kuma batason takura 'danta.
Taheer ne yashigo Ganinta cikin yanayin yasa yaqaraso ya zauna kusada ita tareda Kiran sunanta.
Kallonsa tayi da sauri tareda sakin ajiyar zuciya ta riqo hannunsa tace,
Darling kaga abinda mi'amor ke shirin yimana ko? Wai yanada wadda yakeso baimada lokacin abinda mukeyi.
Numfashi yasauke Dan dama yasan za'ai haka tunda ba'ayiwa dawood 'din gwari gwari ba tun farkon zancen.
Lallashin mum din kawai yayi yace ta kwantarda hankalinta dawood din zai amince idan ta lallashesa tai Masa magana.
Akan haka ta miqe tayi sashen dawood din sbd tunda yafara haka baxata ta6a Bari dad yajiba sai dawood din ya amince sbd dazarar yaji zai bawa dawood din wadda yakeso Koda kuwa basuda kudi sosai.
Tana zuwa a Palo ta tarar dashi zaune idanuwansa a lumshe.
My love""""takirasa ahanakali tareda zama kusadashi.
Tashi zaune yayi tareda zuba Mata idanuwansa Bai ce komaiba.
You see my love wannan yarinyar danake fada maka tafi duk wasu models da...
6acin ransa yayi qoqarin dannewa yace,
Mum tunda kin sawa ranki maganar yarinyar Bari na yanke zancennan, Banasonta ko 'yar gidan waye Kuma baxan auretaba wadda nakeso ita zan aura wai for godsake mum me can you go right now.
Kanada hankali kuwa Ni kake cewa na fita.,ita wannan da kake tada jijiyan wuya akanta 'yar wacece dazata sa kana 'dagamin murya.
Rufe idanuwansa dasuka kada sukai jajir yayi kafin ya bude yace,
Mum ko Yar waye,koba Yar wayeba ita nakeso ita zan aura and thats final idan kikace bazan auretaba then ki shirya tarar abinda zai biyo baya and one more thing kidainama sako maganar auren watacan sbd that will never happen sbd I rather die Dana auri wadda ba Nur ba so please mum mubar wannan maganar.
Baki tasake tana kallonsa zuciyarta na tafarfasa da maganganunsa., Nan take kishin Nur din daya fada ya rufe zuciyarta yanda duk duniya ba abinda 'danta keso da qauna kamarta Amma yau son wata yasa Yana fada Mata mgn, Wata irin tsanar Nur din daya fada ta cika zuciyarta tanaji aranta bazata ta6a barinsa ya auretaba sbd tun yanxu Yana Mata haka akanta idan ya aureta shikenan zai rage sonta koma ya daina sonta.
Girgixa Kai tayi tana cewa, Inaaaa.
'daure fuska tayi cikin 'daga murya tace,
Bazaka auretaba yarinyar danake so ka aura ita zaka aura kodan ciwon sonka dake neman kasheta and thats final sannan duk kafadawa dad dinka wani Abu Akan haka daga lokacin kasa aranka bakada mahaifiya a duniya sbd na yafeka daga lakocin.
Qura Mata idanuwansa dasuka qara rinewa yayi zuciyarsa har wani tsallen 6acin Rai takeyi yace,
Bazan fada Masa ba Amma inanan kan ra'ayina bazan auri kowace bitch ba idanba Nur duk Wanda zai mutu ya da'de Bai mutuba anrufe.
Qarasowa taheer yayi tareda riqe mum cikin taushin murya yace,
Mum Please abar maganar aleeyan tunda yace bayaso kibarshi da wadda yace Yana so Mana.
Lafiyayyan Marin datakeson saukewa dawood tini ta sauke Masa tsantsar 6acin ranta na qara bayyana ta kallesu su duka cikin kausasa harshe tace,
Koyanaso ko bayaso saiya aureta kuma wlh cikinku duk Wanda yafadawa dad 'dinku na ciresa acikin jerin 'yayana and one more thing ka shirya gobema zamu je gidansu aleeya anfasa saka auren nesa kusa za"a sakashi.
A fusace ta juya tabar part din Wani zafi da 6acin Rai yakeji a zuciyarsa ga wata irin tsanar aleeyar dayake Kama kowane lungu da saqo na zuciyarsa sbd wannan shine karo na farko da wani yashiga tsakaninsa da abinda yakeso kuma ko so 'daya mum Bata ta6a 'daga Masa muryaba sai akan hakan harma da Marin taheer Wanda ga dukkanin alamu shitayi niyar saukewa da taheer din baizoba.
Taheer dake cikin takaici da mamakin Marin da'akai Masa yaga yanda Nan take fuskar dawood din tayi jajir abinka da farin mutum ya matso zaiyi Masa magana Amma tuni yayi hanyar bedroom 'dinsa cikin tsananin fushi da 6acin Rai Abu 'daya ya aje aransa shine bazai ta6a auren kawace mace idanba Nur ba. #mamuhgee
VOTE COMMENT. *_DAWOOD_* _wattpad@mamuhgee_
*18* Da daddare Koda Abba yadawo babu Mai walwala acikinsu sai mum din dake qoqarin sakewa Dan kada yagano komai.
Washe gari rikici sosai aka sake tafkawa tsakaninsa da mum sbd ko qofar bedroom dinsa yaqi budewa bare tasamu damar sake maganar..
Yanda yaga dare haka yaga safiya idanuwansa har wani laushi da jemewa sukayi sbd rashin bacci da kwanciyar hankali adare 'daya Tak kasancewar Bai Saba da rashin hutu da isashen bacci Babban abinda ya qara birkicesa gabaki 'daya shine baisan yakai wata irin qololuwa ason Nur 'din ba saiyanxu da mum tafara wannan maganar ta rabasu Wanda tuni yasan abune dazai faru bayan ransa sbd Babu ranar rabuwa da Nur agaresa saita mutuwarsa.
Aranar da daddare Koda yakirata kwanciya yayi tareda rufe idanu cikin sanyi yace,
My love kimini zancen dazaisani bacci inajin damuwa sosai kewarki nakeji please kiban dama gobe naxo naganki I seriously want to see you Angel.
Lumshe ido tayi sbd yanda jikinta yayi sanyi ya mace lokaci 'daya sbd tsananin sanyin data jiyo a muryarsa.
Ka qara hkr har lokacinda su dad 'dinka zasuzo,.
No Angel I can't...inajin zan iya zama komai ne idan narasaki, Meyasa nake sonki haka Nur??? zuciyana zafi yakeyi Sam banada nutsuwa ko sukuni yanxu I'm restless, Haka son yake dama..?I love you Nur..I love you so very very much., Kece rayuwana yanxu I have to get you at any cost Nur.
Jitayi idanuwanta sun ciko da hawaye kalamansa sun sanyayata daqyar cikin tsananin sanyin murya tace,
Ka kwanta kayi bacci Saida safe.
Kashe wayar tayi ta aje tareda rufe idanuwanta.
Washe gari mum sabon tashin hankali akai sosai sbd tuni ya ha'da kayansa zai tafiyarsa Nan hankalin mum 'din yaqara tashi gashi batason rarrashinsa Dan karya canxa mata ra'ayi Kuma tasan dazarar yatafi bazai sake dawowa kusaba qilama sai matarsa dayakeso sunyi aure.
Dafe goshi tayi cikin tsananin damuwa da neman mafita. Wani tunani ne yafado Mata ta 'dauki wayarta ta danna Kiran maska.
Cikeda kulawa ya 'dauka asake yace,
Hello mum.
Cikin sauri sauri da tashin hankali tafara yimasa bayanin abinda ke faruwa ta 'dora da cewa,
Son please do something, call him tell him koma meyene I don't want him to go please my boy kayi wani.
Numfashi yasauke sbd jikinsa dayayi sanyi Jin wannan rikicin dakuma tsananin tausayin halinda dawood zai shiga idan mum tacigaba da dagewa akan rabasa da Nur.. Gyara murya yayi yace,
Mum meyasa kikeson Dole saiya rabu da Nur? they're so much in love with each other mum.
Son please just call him now zamuyi sauran maganar but for now kasan yanda zakayi ka hanasa tafiya.
Ok...yace tareda kashe wayar Yana kallonsu jass dake sauraronsu.
Wayar dawood yakira Amma Bai 'dagaba harsaida yayi Masa kusan Kira uku.
Yana 'dauka yanayin muryarsa yasa jikinsa sanyi a tausashe yace,
Dawood mum called.
Numfashi Mai zafi ya sauke murya a shaqe yace,
I love her maska but I can't do this, Zanyi komai Dan ita Amma wannan karon ta 'dauko babban al'amari sbd I can't live without Nur.
Bazamu so ka rabu da farin cikinba ba but karkayiwa komai garaje kabi mum din ahankali I'm sure zata barka da farin cikinka tana sonka sosai bazata juri damuwarkaba so karkayi fushi.,
Qaramin tsaki yaja cikin 'dan zafi yace,
Zantafi idan ta sauka zan dawo sbd ba yanda za'ayi naje gidan datake son naje.
Kar6an waya sufyaan yayi yace,
You'll have to go dawood sbd idan wancan 'din na sonka zatace ta hakura ka samu wadda kakeso kawai kaje kafada Mata gskia you don't want to get married to her kanada wadda kakeso I think this will work.
Shiru dawood yayi ransa na qara quna sbd har cikin jininsa yakejin tsananin qiyayyar yarinyar ko ganinta bazaiso yayiba ace kamarsa harsaiya tsaya yiwa wata bitch bayani kafin yasamu wadda yakeso Amma it's like he has no other option, Akan Nur zai iya zuwa ko inane yayiwa duk mutanen duniya bayani.
Zubewa yayi bakin gado tareda dafe kansa dake Sara Masa sosai ga wani zafi da zuciyarsa keyi Amma bayason ya qara 6ata lokaci ayau zasu wuce gidansu yarinyar.
Su maska kuwa suna gama waya dashi dukkaninsu sukai tsit suna juya tsananin damuwar da abokinsu yake ciki ayanxu Dan kuwa sune shaidai tsananin son dayakewa Nur din, Tun tasowarsu Basu ta6a ganinsa yaso Abu da tsanani hakaba kamar yanda yakewa Nur.
Ajiyar zuciya jass ya sauke cikin kulawa yace,
This is not good.
maska dake juya zancen aransa yace,
Dole zamuje da wuri yana buqatar wani akusadashi Dole.
Waya sufyaan ya 'daga yafara Kira ayi musu booking tickets na zuwa Nigeria.
Wanka yasakeyi ya shirya cikin qananun Kaya dark blue da facing cap tareda shades black yafito su mum kuwa tuni suka shirya sai washe Baki takeyi tana Nan Nan dashi suka fito gabaki 'daya suka nufi airport.
Lokacinda aka bugo aka sanarda zuwansu tuni su ammy suka hau shirye shiryen tarbon baqi gashi itama Nur dawood yakira yasanar da ita yau zaizo da dad 'dinsa zuwa dare ko gobe da safe idan sun baro gidan abokin dad dinsa.
Musamman mum tasake bugowa tafadawa aleeya suna hanya ba 6ata lokaci cikin farin ciki aleeya ta damu Layla Dole suka fita sukaje wani queens beauty pal&spa.
Gyara na musamman akayo Mata har wani irin qyalli take tayi tayi Layla tayi tace aa sbd dawood bayason hayaniyar kwalliya yafisonta a natural 'dinta.
Koda suka dawo gida qarfe biyu ta 'dan wuce Dan haka sallah kawai sukayi ta canxa kayanta zuwa doguwar Rigar wata Julius Holland dark brown ta 'daure gashinta ta 'daura qaramin vail akanta tareda zura bedroom slippers ta Taya aleeya shiryawa sai farin ciki suke suna fira Nan Bilal ya shigo aleeya ta kallesa da sauri tace,
Little qani sun iso? Kaga brother inlaw 'dinka? He's very handsome right?
Dariya ya bushe da ita kafin ya matso ya zauna kusada ita Yana kallon yanda tayi kyau kamar wata model yace,
Daina rawar jiki sunfasa sai gobe Kuma....
Zaro Ido tayi zatai magana layla tayi saurin Kai Masa duka a kafada tana cewa,
Mode spoiler.
Ajiyar zuciya tasake da qarfi tareda miqewa tabi bayansa da gudu tana cewa,
saidakasa zuciyana tsinkewa Allah saina ragewa coconut head 'din Nan naka girma.
Dakin ammy yayi Yana dariya tabisa Nan ammy taraba rigimar Layla tace,
Allah ammy ya rainamu yaron Nan jifa yanda yatashi saka kwalliyar damuka tsara"""tafada tana gyarawa aleeya gyaran gashinta da sul6insa yasa yafara zarewa daga ribbon.
Sallamar siyama ce tasa dukkaninsu juyawa cikeda mamaki sbd ba Wanda yasakaran ganinta.
Fuska 'daukeda murmushi da farin cikin da baikai zuciba ta qaraso tareda rungume aleeya tana cewa,
Wow cousin you're looking fabulous.
Murmushin yaqe tasaki tace,
Thank you siyama saukar bazata.
Eh wlh naso baku surprise ne, Ammy ina wuni ya nasameku?
Lpia klau siyama, Yasu anty Nana da babanki.
Duk suna gaisheku. Kallon Layla tayi fuska asake tace,
Layla ya gida.
Lafiya qlau""tace tareda miqewa ta fice tana cewa,
Bari naje naqara duba cake 'din da Nana keyi koyayi.
Tana fita aleeya da siyama suka biyo bayanta suna 'dan fira.
Suna bedroom 'dinsu sukaji isowar baqin kusan atare zuciyoyinsu suka buga lokacinda Bilal yashigo yafada musu baqin na Palon Abba.
Fira sukeyi Amma kowa kusan Rabin hankalinsa baya gurin.
Acan palon kuwa taheer ne yashigo taredasu dad dawood kuwa harabar gidan ya tsaya Kiran numbern Layla Amma yakasa samu jiyake kamar zai zauce idan baiji muryarta alokacinba.
Ammy ta gaisa dasu sosai cikin girmama takalli taheer dake gaidata ta amsa a mutumce sbd tunanin shine dawood din kafin sukai palonta da mum.
Nur ce agaba sai aleeya da siyama abayanta suka shigo palon ammy.
Zuciyar mum cikeda farin ciki ta amsa gaisuwarsu tana qara godewa Allah dazai cika Mata burinta.
Nur dake gefen ammy ta kafawa Ido ganin wani irin hutu da kwarjini dake fita a jikinta Nan take taji tana yiwa kanta sha'awar ace sirikarta ce, Tabbas tafi dacewa da dawood 'dinta saidai lokaci ya qure saidai taheer 'dinta.
Ficewa sukai daga 'dakin ammy tace,
Layla kije ki qarasa da dawood din guests palour zaifi sakewa sbd su abban Naga hirar business suke tukuna.
Ok ammy.
Aleeya da siyama bedroom suka koma ita Kuma ta nufi palon Abba Kai tsaye.
Da sallama ta shiga..
A cikin idanuwan taheer idanunta suka Fara sauka tayi saurin sunkuyar dakai numfashinta na fita da sauri.
Gaidasu abban tayi tasanarda abinda yakawota Nan taheer daya Dade da mutuwar zaune miqewa sbd baita6a tunanin Laylar ta zarce yanda take a hoto sosai.
Fitowa sukayi palon yace Mata dawood na harabar gidan.
Shigar dashi palon tayi suna qara gaisawa ta juya tana cewa,
Bari naje na shigo dashi.
Tundaga nesa ta hangosa ya bada baya Yana waya saidai kallo 'daya tayiwa bayansa ta tsaya hakanan taji numfashinta na fita da sauri ta tsaya cak kamar wadda aka tsayar.
Wayarta yaqara Kira cikin sa'a tayi ringing.
Saurin kallon wayar hannunta tayi shikuwa Jin qaran waya bayansa yasashi juyowa.
Wani irin jirine ya 'dibeta tayi saurin juyawa ta shige Palo batareda tabari yaqarasa juyowaba.
Rawa jikinta yakeyi sosai daqyar ta lalubi kujera ta zauna tana qoqarin Jan numfashinta ya tsaya.
Sake shigowa Kiran yayi tana gani ya katse zuwa lokacin ko wayar ta kasa riqewa rawa jikinta keyi sosai arikice ta miqe tayi dakin Nana sbd can ne kawai tasan ba Wanda zai ganta cikin wannan yanayin. #mamuhgee
VOTE COMMENT. [1/8, 8:37 PM] 0mmr Farouk: *_DAWOOD_* _wattpad@mamuhgee_
*19* Kasa zama tayi kodata shiga 'dakin ta tsaya tsakiyar 'dakin tana qoqarin samarwa kanta nutsuwar fahimtar abinda ke tabbatuwa arayuwarsu,
Wasu irin hawayene suka gangaro Mata tana qoqarin danne kukan dakeson biyo bayansu.
Dawood 'dinta shine dawood 'din da aleeyarta keso meyasa takasa fahimta tuntuni daya sanarda ita garinda iyayensa suke.?
Meyasa dawood yaqi fada Mata cewar,
Iyayensa sun nemar Masa Mata...?
Wannen wane irin alamarine ya kusantosu. Rufe Ido tayi tana tsananin Jin zafi azuciyarta, Rawa qafafuwanta suka Fara yimata ta sulale tsakiyar 'dakin hawayenta na tsananta gudu sabuwar doyayyar dawood takeji har cikin jininta, Soyayyar dawood tariga tazamo wani 6ari na jikinta wani irin zafi da nauyi takeji ayanxu data gansa amatsayin na aleeyarts to Yaya aleeya zataji idan taji shine dawood 'dinta.
Girgixa Kai tayi hawayenta na qara gudu cikin rawar murya ahankali tace,
Wlh zafi nakeji sosai cikin zuciyana aleeya bazanso kiji wannan zafinba Bazaki iya juresaba.
Ahankali tafara kuka Mai qaramin sauti har lokacin jikinta Bai daina rawaba.
Tunowa da ammy yasa ta tsayarda kukanta tareda tattaro qarfin Hali tasawa zuciyarta ta share fuskarta tareda miqewa da sauri ta fice tana roqon Allah yasa ammy da dawood basuga junaba.
'dakin ammy ta nufa tana qara qoqarin danne halinda take ciki.
Ammy ce kawai a 'dakin itama wayarta tazo 'dauka takoma palon gurinsu Abba.
Ahankali ta qaraso gaban ammy ta riqo hannunta tareda dawowa bakin gado suka zauna.
Sunkuyar dakai tayi hawayen datake qoqarin dannewa sunason fitowa Amma ta 'daure ta mayar dasu Amma idanuwanta sun jajir.
Sanyi jikin ammy yayi ta qura Mata idanuwa ta lurada yanda jikinta ke 'dan rawa ta riqo hannunta da sauri cikin tsananin fargaba tace,
Layla?
'dagowa tayi takalli ammyn Nan take ammy ta qara shiga ru'dani ganin Jan idanuwanta tace,
Layla meke faruwa?
Ammy tunda na taso cikin quncin rayuwa da talauci na taso, Babu Wanda ya ta6a yimin kallon mutum bare ya bani mutuntawa da darajar da Allah yabawa mutum, Ni Almajirace 'yar bola Mara asali da gata, Ammy duk duniya bayan iyayena dasuka haifeni Babu Wanda nake tsananin so da qaunar farin cikinta irin aleeya sbd itace takalleni amatsayin mutum ta miqamin hannu ta cironi daga qanqantacciyar rayuwar titi da bolan danakeyi Wanda da yanxu na zama wata abar qyamar.,
Ammy har abada ina roqon Allah daya nesantani da abinda zaisa nakawo damuwa a fuskar aleeya.,.....
Sosai jikin ammy yayi sanyi murya a sanyaye tace,
Layla meyasa kike tado da abinda yazamo tarihi?.....
Dr Dawood ne Wanda aleeya zata aura..
Yawu ammy ta ha'diye sbd gudun garajen fahimta tace,
Banganeba Layla sakemin bayani.
Ammy dr dawood shine 'dan abokin Abba dasukazo yanxu.
Mummunan fa'duwa gaban ammy yayi ta lashi busasshen bakinta sai alokacin tasake qurawa layla Ido taqara hango mummunan halinda take ciki tana qoqarin dannewa.
Layla wannan ba abun damuwa bane tunda ba auren aka 'dauraba zanyiwasu abbanku bayani yanxu..
Miqewa tayi laylar ta riqo hannunta tareda dawowa gabanta ta sunkuyar dakai cikeda qarfin Hali tace,
Ammy ke uwace dabakyason kan 'yayanki ya rabu, Kin manta nayi Miki alqawarin toshe duk wata hanya dazata kawo 6araka atsakaninmu, Ammy wannan shine alqawarina dazan cika bazan ta6a Bari hawaye yasauka kan fuskar aleeya ba ta hanyata, Ammy kiyimin alqawarin har abada Bazaki ta6a fadawa kowa wannan maganarba...
Girgixa Kai ammy tayi cikin tsananin tashin hankali da damuwa tace,
Wannan shirme ne kikeyi layla sbd bazai ta6a yiyuwaba, Idan har farin ciki kikesowa aleeya to Bazaki Bari ta auri Wanda baya sonta yanada wadda yakeso wace irin rayuwar aure zatayi da Wanda keson wata mace ba itaba...
Hawaye ta goge da bayan hannu tace,
Ammy shine farin cikinta,shitakeso bazata ta6a iyason waniba bayansa....
Kidaina fadamin haka sbd wannan ba sacrifice bane Layla rayuwarku ce ku uku zata lalace, Kalli halinda kike ciki yanxu, Ji yanda kike qowarin danne quncin dake ranki Amma ina iya ganinsa,
Dawood ke yakeso bazai ta6a son aleeya ba sbd tun farko ba ita yakesoba.
Tsananta hawayenta sukayi tace,
Ammy Koda Baki yardaba na yafe dawood har abada sbd bazan iya cigaba dason abinda aleeya kesoba, Wannan alqawarina ne duk ranarda aleeya taji zancen Nan zan tafi tafiya ta har abada ammy sbd bazan iya hada Ido da itaba nayi tarayya da ita akan abinda takeso nakasa cirewa zuciyata cewa hakan ba laifina bane.
Tsananta tashin hankalin ammy yayi tace,
Layla meyasa zakiyi haka Dan kuwa hakan shine babban kuskuren dazaki tafka wannan ba mafita bace.
Kuka tasake ahankali ammyn tayi saurin rungumeta tana danne nata hawayen sbd Laylan tasakata a tsaka Mai wuya sbd rayuwarsu duka su biyun ne zata lalace garin toshe 6araka za'ayi gaba Mara da'di.
Jin motsin shigowa yasa laylar zamewa ta miqe ta shige toilet 'din ammy.
Siyama dake jinsu tun farko ta gyara tsayuwarta tareda sakin wani shu'umin murmushi tace,