Kenza eBookz

Dawood complete - Chapter 8

Dawood complete - Chapter 8

Dawood complete Chapter 8: Dawood complete Chapter 8. Shiru mum tayi cikin tunani sbd har abada bazata ta6a Bari 'yayanta su auri wainnan biyun dake…

4,478 words

Shiru mum tayi cikin tunani sbd har abada bazata ta6a Bari 'yayanta su auri wainnan biyun dake gabantaba Dan kuwa data Bari taheer 'dinta ya auri wannan ba gara tabari ya auri Laylanba tayita gana Mata wulaqanci da azaba tasan zata 'dauka akan tasa ya auri wannan da zata iya korota daga gidan wata Rana..

Murmushin Dole tasaki tana cewa,

Shinkenan tunda kince haka na amince zansa ya aureki Amma da sharadin sai bayan aurensu na yanzu Kuma sai kunyi narasar raba 'yayana dasu Kuma ba.....

Sallamar Nanace tasa mum 'din yin shiru tareda sakin yaqe Nana tace,

Ammy na magana.

Ok ganinan muje.

Bin Nana tayi tana watsawa gefensu wani mugun kallon qyama.

Bayanta sukabi da kallo saraah harda qaramin tsaki kafin ta juyo ta kalli siyama up and down tace,

Zan fada Miki gaskia wannan matar qarya take Miki bazata ta6a barin ki auri 'dantaba zatayi amfani dakene kamar yanda take tunanin tanayi Dani batasan Nice zanyi amfani da itaba Dan haka just name any price zan biyaki kifadamin komai gameda yarinyar.

Kallon saraah 'din tayi koba komai maqiyin maqiyinka abokinka ne koba komai mace ' dayace suke Hari kuma dole dama wasu ayukan datake planning Saida cash gashi saraah nadasu Dan haka komai zaizo musu asauqi dan haka ta matsa jikin qofa tasaka key tareda dawowa ta zayyanewa saraah komai ta 'dora da cewa, garaje ba naki bane kibini kiga yanda asannu zamu tarwatsa rayuwarta da duk wani munafukin dake binta idan mun gama dasu saimu koma kan yanda zamu samu mazajen burinmu.

Wani irin murmushin Jin Dadi saraah tasaki tana jinjina shawarar siyama aranta Dan kuwa siyama itace irin mutanen datakeso arayuwarta wainda zasu iyayin komai dansu samu abinda sukeso at long last tasamu qawar dasuke ra'ayi guda.

Zama tayi bakin gadon dakin tana cewa,

Zan nunawa mrs Damien kuskuren data tafka na tunanin zata yaudareni sbd bayan zuwana Nan gidan ayau na fahimci komai wato itakeson dawood ya auri aleeya nikuma tayi amfani Dani gurin rabasa da wadda yakeso hmmm dukkaninsu saisunyi danasanin cin amanata harshi dawood 'din su maska kuwa saina hargitsa rayuwarsu 'daya bayan 'daya Susan wa suka taru suka hainta, Mum kuwa bamu Bari tasan Layla bace sbd zata iya canza ra'ayi idan dataga 'danta na Shirin mutuwa Baqin cikina 'daya Dole zan hkr Ina kallo dawood yafara auren wata kafin Ni.

Cikeda murmushin farin ciki itama siyama ta jawo doguwar Riga ta zura tasamu wadda zata tayata aiwatar da aikinta cikin sauqi.... Hmmmnnnn Layla tashin hankalinki ya qarato kekuma aleeya saikinyi danasanin fifita bare akaina. #mamuhgee #vote #comment. *_DAWOOD_* _wattpad@mamuhgee_

*24* NOT EDITED.

Rama tayi sosai tareda firgicewa duk da tana iya qoqarinta gurin ganin ta danne abunda ke damunta sbd gudun damuwarda aleeya da ammy zasu shiga saidai dauriya kawai takeyi gashi bikin sai qaratowa yakeyi,

nana ce kawai tasan halinda take ciki sbd duk lokacinda taji wani abu na taso mata dakinta take zuwa musamman yanxu da kuka ya daina zuwar mata saidai qirjinta gayi mata wani irin nauyi sosai takeson kukan yazo mata kotasamu sauqin abunda takeji a qirjinta,

biki kuwa kusan dukkanin wani buri na ammy da nasu akan bikin aurensu ya kau sbd kusan dukkaninsu su uku din babu mai wata doguwar walwala sbd kowa da damuwarda yake fama da ita saidai kowa qoqarin 6oyewa dan uwansa yake kada yasashi damuwa.

6angaren siyama da sarah kuwa duniya sabuwa sbd wani aminci dasuka qulla da juna ko yaushe suna tare wani lokacin ma can gidansu mum take kwana gurin sarah koda mum ta tambayesu maganar Nur kai tsaye suka nuna mata tabari sai andaura aurensu dawood tukuna idan ba hakaba sukaiwa NUR wani abu dawood yaji kafin daurin aure zai iya fasawa kenan basu samu yanda sukesoba.

ba wani dogon nazari ta amince da hakan tanaso ayi auren tukuna suci mata uwar NUR itakuma tayi musu korar wulaqanci daga gidanta kenan komai yatafi a yanda takeso, wani irin murmushi tayi ta fice daga room din,

bayanta sukabi da kallo sarah ta dauki ipad dinta tana cigaba da abinda takeyi tace,

wlh saina mayar da rayuwar mrs damien abun kwatance batasan akan danta saina aika kaf zuriarta lahiraba stupid woman.

murmushi siyama tayi batareda tace qalaba sbd so dadama tana mamakin yanda rayuwar sarah takeba samsam batada tarbiya ita haryanxu tama kasa gane musulmace ko muna musulmi sbd bata ta6a ganin tayi sallah ba ga yanayin shigarta wani lokacin ko rufe kanta batayi suke fita shiga ko wace iri yi takeyi dan taga tanada kyawu ne qila.

duk inda hankalin mum yake yatashi daurewa kawai takeyi kullum saita kira maska taji ko sun iso sbd daqyar suka yarda zasuzo tareda dawood din.

yana gama waya da mum ya kalli inda dawood din ke kwance sun daura masa drip daqyar ya yarda sbd ko miqewa yayi jiri ke dibarsa, babban tashin hankalinsu shine ramar dayake tafara basu tsoro gashi yanxu ko aiki baya zuwa koyaje baya zama gashi hakan na neman lalata carier dinsa gaba daya sbd so biyu yana samun matsala gurin aiki danma duka biyun allah ya taimaka tareda jass suke aikin.

ruwan na qarewa yasamu qarfi ajikinsa ya tashi zaune tareda kallonsu da idanuwansa dasuka canxa sosai, sanyi jikinsa yayi ganin yanda komai ya canxa musu rabonda suyi fira suyi dariya tunda yarasa Nur, barinsa gida adamawa yakoma yafi sati biyu yana gararin nemanta harya kwanta ciwo maska yaje yadaukesa suka dawo new jrsey duk iya qoqarinsu na ganin abun bai ta6ashi ba sosai sunyi amma sam babu nasara saima lalacewa dakomai ke qarayi,

washe gari tun kafin su fito yayi wanka ya fice zuwa office dan ganin ya qoqarta sbd ganin yanda rayuwarsu tafara duqushewa sbd tasa,

cikin rashin sa'a yana isa ya tararda wata emergency theatre da farko yaso yaqi shiga sbd sam baya tunanin zai iya saikuma ya daure yashiga yana qoqarin daidaita nutsuwarsa,

sabon tashin hankaline ya riski su maska lokacinda wani dr bk yakirasu ya sanardasu dr dawood yashiga theatre,

arikice hankali tashe suka iso su duka ukun kowanne na addua da fatar kar asamu matsala sbd wannan shine karo na qarshe da idan yaqara samun matsala carier 'dinsa zata lalace gaba 'daya,

cikin sauri jass yaje yayi shirin theatre saidai kafin ya gama aka fitoda dawood akayi emergency dashi sbd yana cikin aiki ya yanke jiki ya fa'di,

sufyaan ne yashiga dubasa cikin gaggawa shida nurses, ruwa da allurai ya daura masa nan take kafin yafa sakawa ayimasa runnin wasu test.

koda ya kar6i results din yaduba zama yayi a kujerar office 'dinsa inda aka dawo da dawood din tareda miqawa jass yana cewa,

sake dubamin.

kar6a yayi yana kallon yanayin face dinsa kafin ya maida kallonsa ga result din,

rashin hutune da damuwa sosai datayi masa yawa sai ciwon qirji abunda ya 'daure kusu kai sosai tareda basu tsoro shine yaushe dawood 'din yafara shan alcohol.

shiru maska idanuwansa sunji jajir dan kuwa baya buri ko fatar wani masoyinsa yafara shan giya sbd illarta shima tazame masa kamar wata qaddarane yakasa daina shanta duk da kuwa yanason yadaina amma yakasa, basu ta6a luraba ko tunanin dawood yafara shaba saidai ga dukkan alamu lafiyarsa da jikinsa basu qar6etaba tunda gashi tafara masa illa da wuri saidai ya tabbatarda duk akan matsakarsa ne rabasa dashanta kuwa zaifi musu sauqine idan suka samu inda Nur take dan haka suka hau shiri kai tsaye dan tahowa saigashi mum takira akan suzo bikin yana qaratowa.

aranar dazasu taho nigeria sosai jikinsa yaso tsanani saidai sufyaan yayi masa wasu allurai na bacci suka taho dashi ahaka.

ranar dazasu iso aranar su mum suka dawo abuja daga adamawa kuma aranar su dad da taheer suka dawo atare,

kallo daya dad yayi masa hankalinsa yayi mummunan tashi nan maska ya kwantar masa da hankali yace bawani abu bane alcohol yakesha a yan kwanakin shine ta tabasa amma daya kwana biyu aba masa allurai yana samun isashen bacci batareda yashataba zai warware insha allah.

tom kawai dad din yace badan hankalinsa ya kwantaba saidan kasancewar yasan su maskan qwararin likitocine dabaida haufi akansu koba komai yasan yanda sukeji da abokin nasu,

mum kuwa duk yanda taso daurewa kasawa tayi ganin cikin qanqanin lokaci yafara canzawa sbd rama da wani 'dan duhu dayayi sannan ace dawood 'dinta nason zama mashayi sbd mace,,danko baa fadaba tasan sbd nur ne,itakam tanason ganin wannan nur 'din yanxu kodan taga abinda yasa danta ke neman illata lafiyarsa akan sonta.

bacci yake sosai sbd allurar da akai masa saidai bazaka kallesa kace baccin hutune yakeyiba sbd fuskarsa data rame zata nuna baccin wahala da dolene yakeyi,

kwanansu 'daya da dawowa kenan amma harlokacin bai farkaba sbd qarfinta, ajiyar zuciya maska ya sauke zuciyarsa ba dadi a karye lokacinda yafama kallon dawood 'din,

jass dake zare masa drip ya kalla yana dafe goshinsa tareda furzar da numfashi mai zafi murya amace yace,

yau zanje adamawa inason ganin matarda mum zata aurawa dawood we need to talk kafin daga baya akwai wanda zan sanya ya nemo mana nur cikin garin na tabbatarda zai nemota duk inda take insha allah kafin nan zanfara biyawa kaduna gurin mamyna.

wani irin sanyi jikin jass yayi yakalli maska cikin sanyin murya yace,

zanbika muje tare inason zan gaisa da mamy nima.

ajiyar zuciya ya sauke ahankali kafin ya girgiza masa kai yace,

kabari idan nadawo zamuje gaba 'dayanmu kamar yanda muka saba zuwa mu gaidata, yanxu dawood na buqatarku atare dashi fiyeda komai,

juyowa yayi yasake qurawa dawood 'din ido saikawai yaji hawaye sun taru a idanuwansa yayi saurin dauke kai tareda kallon jass da jikinsa yaqara sanyi da wata irin murya yace,

jass promise me zaka kulada dawood da sufyaan kafin nadawo,

'daga masa kai yayi kawai batareda yasaniba sbd shima yayi nisa sosai cikin tunani,

rungumesa maska yayi yana cewa,

see you soon.

'daga masa kai yayi ahankali tareda cewa,

safe journey friend.

har mota yarakasa daidai isowar sufyaan daga gidan maska inda dawood yayi zama dama acan suka sauka jass ne kawai atareda dawood anan gidansu mum.

rungume juna sukayi batareda sunyi maganaba tsawon lokaci kafin suka saki juna ya wuce yana qara maimaita musu su kula da dawood sosai karsu bari yacigaba dashan alcohol.

murmushin qarfin hali sufyaan yasaki tareda jinjina kai har maskan ya fice daga gidan cikin motarsa sbd da mota zaiyi tafiyar kaduna daga kaduna zai hau jirgi ya wuce adamawa.

koda ya isa kaduna mamynsa batanan tayi tafiya zuwa wani taron gidan marayu sbd batasan ayau zai baro abuja ba,

bedroom dinta yashiga ya zauna tsawon lokaci kafin ya miqe yafito tareda barwa masu aikinta saqon dayazo mata dashi yafasa kwana ya wuce sbd itama bayau zata dawoba,

airport ya wuce cikin saa yasamu ticket yawuce.

kaida kawo mum keyi cikin tsakiyar bedroom ranta ajagule, saraah dake kwance tana shopping ta cikin waya ta 'dago tana kallonta sbd yanda kaida kawon yafara damunta cikin ko inkula tace,

wani abu nadamunki ne mum?

rai a6ace ta juyo tace,

dama yazaayi narasa damuwa ina tareda mara amfani kamarki.

aje ipad din hannunta tayi tareda daure fuska tana kallon mum din.

yes mana sbd gashican maska yakama hanyar adamawa zai nemo nur dakansa kuma kinsan daya samota wlh babu abinda zai hana aurenta da dawood koba komai nafara gajiya da wannan balain.

shiru sarahh tayi cikin tunanin dole takira siyama duk yanda zaayi ayi kar abari maska yaga nur ko gidanma kar abari ya isa kota halin qaqane. #mamuhgee vote comment. *_DAWOOD_* _wattpad@mamuhgee_

*25* NOT EDITED

koda ya isa adamawa ko hotel 'din dazai kwana bai isaba saida yanufi gidansu aleeya,

bai wani sha wahalaba ya isa gidan saidai cikin rashin sa'a mai gadi yasanar dashi suna lagos acan sukefin zama,

dafe goshinsa yayi cikeda damuwa kafin yayiwa maigadin godia ya wuce,

hotel room yakama yayi salloli tareda ordern ruwan lipton da black coffee sbd hakanan yakejin baya iyacin abinci mai nauyi.

shiru yayi tareda qurawa ruwan lipton din ido wannan shine karo na farko dabaiyi ordern giyaba tun girmansa, yau kuwa sam baya shaawar shanta sbd tunda yaga result din dawood yafara shanta yaji ya tsaneta sbd yasan zataiwa amininsa illa dan haka koda zai hanasa shanta saiya fara raba kansa da shanta wannan alqawarine ya dauka bazai qara shantaba insha allah,

kur6a biyu yayiwa lipton din ya ajiye sbd kwata kwata bayada apatite,

wayarsa ya 'daga yakira wanda yakeson gani yace yazo yasamesa a hotel, cikin qanqanin lokaci wani babban saurayi ya iso yayi knocking room din yabude masa ya shigo,

cikin girmamawa yace,

dr barka da isowa nigeria,

murmushin qarfin hali maskan yasaki tareda cewa,

thank you sambo,aiki zan baka kuma koma meyene inason samun aikina ta kammalu zuwa gobe zan biya ten times na amount din aiki.

washe baki sambo yayi yana kar6ar wayar maskan dayake nuna masa hoton Nur,

bude bluetooth dinsa yayi yatura hoton cikin wayarsa tareda miqawa maska wayarsa yana sake kallon hoton yace,

dr wannan aikin anriga angamasa kafin safe insha allah sbd yau komai dare saina gano komai gameda ita,

daga masa kai kawai yayi tareda miqa masa envelope,

kar6a yayi ya fice yana kiran wanda zaifara tayasa aikin.

washe gari qarfe goma sambo yagama hado masa duk wani tarihi akan nur har asalin inda tayi zaman bara kafin mahaifinta ya rasu da address dinsu na lagos.

lokacinda yakawowa maska bayanin da wasu sabbin hotunanta datake tareda aleeya a instagram,

shiru yayi tareda qurawa hoton ido zuciyarsa cike fal da farin ciki mara misaltuwa sbd yasamowa abokinsa farin cikinsa,

bai tsaya 6ata lokaciba ya harhada ya wuce airport ko takardun bayanan bai kar6a ba ya wuce sbd matsuwar yaje yaga nur da aleeya suyi magana atare,

tunda yakama hanyar airport yake kiransu jass amma babu wanda wayarsa ke shiga,

sukuwa sunacan hankali amatuqar tashe sbd jikin dawood aya rikice musu amai kawai yake shararawa mum tayi kuka har idanuwanta sunfara kumbura amma duk da haka batajin zata bari a 'daga bikin gwara ayi matarsa tayi jinyarsa idanma wata qasar za'a fitar dashi,

ganin yakasa samunsu saiya yanke shawarar kiran numbern nur da sambo yabasa,

qaramin tsaki yasaki lokacinda yaji wayar bata zuwa, shiru yayi tsawon lokaci kafin ya yanke shawarar kiran numbern aleeya yafara fadamata komai ta waya kafin ya iso,

numbernta da duka cikin binciken sambone aka samo yakira,

zaune take bakin gado ta tallafe kanta dake tsananin ciwo tayi zurfi cikin tunani,

ringing din wayar dake kusada itane yasa tadan juyo ahankali takalli wayar tareda lumshe idanuwanta dasukai jajir ahankali tasake ajiyar zuciya tareda dauke kai sbd hoton dawood ne kwance akan screen din wayar ta aleeya,

sake kira akayi ta miqe da sauri tabar 'dakin batareda tasake kallon wayarba.

tana fita siyama dake toilet na fitowa hararar wayar tayi tareda jan qaramin tsaki tana wucewa,

cak ta tsaya tareda dawowa da sauri ta duba numbern kamar wadda sarah ta turo mata ta tsohon 'dan iskan dakeson yiwa aikinsu shishigi,

wayarta taciro da sauri taduba numbern taga tabbas itace kiran nasake shigowa ta 'dauka da sauri tareda daidaita muryarta tace,

hello

ajiyar zuciya yasake ahanakali tareda amsa sallamarta cikin qwarin gwiwa yace,

aleeya madibo please?

ahankali itama tace,

yes waye?

khaleefa maska aboki kuma 'dan uwan dr dawood, inason maganane dake akan keda 'yar uwarki nur sbd samowa kanmu mafita gabaki daya,

wani yawu siyama ta hadiye mai daci na tsanarsa sbd da allah baisa itace tadau wayarba kenan haka zai lalata musu komai, wlh zaiyayi danasanin wannan karanbanin bashibama duk wanda yayi shishigin ha'da wainnan masoyan saiya biya da abinda yafi qarfinsa,

daidaita muryarta tasake yi cikin sanyi tace,

gskia ayanxu banason muyi wannan maganar agida sbd nur batasan nasan komaiba dama ina neman mafita dan haka yanxu saidai muhadu wani guri muyi magana,

shiru yayi nadan lokaci kafin yace,

ok kibani address na.....

aaa kabani address na inda zan sameka ni zanzo.

ok idan na iso lagos zanmiki sendin room no na hotel dinda na sauka.

kashe wayar tayi tareda sakata silent ta tura cikin jakarta sbd karya turo address din wayar bata hannunta,

shiryawa tayi tafito ta nufi 'dakin ammy ta tarardasu kamar koyaushe cikin kwanakin,

layla da zaune tana gyarawa ammy wardrobe amma sam hankalinta na wani guri, aleeya kuwa tana qoqarin gusar da damuwartane ta hanyar qoqarin taya bilal wani aikin a laptop amma itama hankalinta na wani gurin ammy kuwa waya takeyi na kayan datayo order na aurensu itamadai daga sautin muryarta kana iya jiyo sanyi da samuwa aciki,

wani irin 6oyayyen murmushin farin ciki tasaki sbd haka takeson ganin rayuwarsu na sauyawa zuwa qunci,damuwa,baqin ciki yazamo ba abunda yarage musu sai kuka,kuka,kuka.

sulalewa tayi ta fice daga gidan da sauri,

tana fita direct wata shegiyar anguwa ta nufa bata fito mota ba takira waya tareda cewa,

seeya ina gurin kasameni,

tana kashewa bada jimawaba saiga wata baqar blackmaria tayi parking gefen taxi dinda take ciki.

fitowa tayi kai tsaye tashige gaban motar sukabar gurin,

qarfe biyar ya sauka a lagos zuciyarsa har wani bugawa takeyi agajiye ya isa wani babban hotel yakama daki yashige,

saidaya fara tura mata text na numbern dakin kafin ya tube yashige toilet yayo wanka tareda yin odar fruitsalad kawai,

tunda yayi sallah bai tashiba yayita kwararo adduoi da istigifar yana nemarwa amininsa sauqi da mafita agurin allah,

knocking akayi ya miqe ahankali ya bude ganin fuskarda baisanibane yasa ya 'dan 6ata fuska yace,

lafiya?

lumshe ido tayi tareda cewa,

masha allah.

ra6asa tayi ahankali tashige dakin tareda zama afusace ya juyo fuska adaure zauyi magana yaji saukar qarfe atsakiyar kansa ko motsi baiyiba ya zube gurin jini na fita ta hancinsa da kunnensa,

kallon seeya tayi tareda jinjina masa kai kafin suka sawa qofar key tafito da wayarta tadauki hotunansa ta turawa sarah tareda kiranta,

ajiyar zuciya sarah tasauke tace,

yanzu abinda za'ayi zan turo miki dubu dari uku kibawa su seeya da yaransa dubu 'dari da hamsin kiriqe sauran kisiya ticket sbd inason kixo dan yanzu mutuwarsa zata saka sauran maida himmar qarasa abinda yabari,

tsaki siyama taja tace,

wai meyasa bazasu barmu muhuta bane yanzu bayan wannan akwai wasu kuma,,,,koda yake zasu qarasa abinda wannan yabari ne idan basuda masifar kansu, zamu gayyatowa kowannensu masifar dabazata barsa yatsaya kallon ta waniba...

cikin takaici sarah ta katseta da cewa,

suna tsananin qaunar junansu bazasu ta6a barin junansu dan matsalar gabansuba,,,,,,

dariyar takaici siyama tasaki tana cewa,

banda wannan karon kibari kiga yanda kowannensu saiyayi shawa'awar dama shine ya mutu ba maska ba.

dariyar farin ciki sarah tasaki tana cewa,

seeya ya qarasa maskan and make it look like suicide ma'ana kuyi hanging dinsa abun yayi kamar shiya kashe kansa ne sannan ku rubuwa wasiya as shine yabarta cikin wasiyar kusa ya kashe kansane sbd abokinsa dawood.

su seeya ne suka cicci6esa suka daure wuyansa sukayi hanging dinsa daidai lokacin kiran sufyaan yashigo wayarsa suna kallo suka fice suka barta yanata shure shure yana kallon wayar na ringing wasu zafafan hawayene suka gangaro masa ta gefen idonsa ya rufe ahankali.

***** shiru sufyaan yayi da wayar ahannunsa yana kallo kafin ya 'dago yakalli jass dake zaune kusada dawood dinda yayi wani irin fari fat kamar baida jini sai bakinsa daya bushe murya asanyaye yace,

bai daukaba,

lumshe idanu dawood yayi cikin ciwo kafin dayar ya iya cewa,

kasake kiransa inason magana dashi, meyasa zaije adamawa bai jirani natashiba muntafi tare i know he's lonely acan please call him again i want to talk to him. #mamuhgee *_DAWOOD_* _wattpad@mamuhgee_

*26* NOT EDITED.

Dafasa jass yayi cikin sanyin murya yace,

please dont stress your self dawood may b he is praying or sumthing,he will call back wen he saw the missedcall.

girgixa kai yayi yanajin wani rashin sukuni na damun zuciyarsa.

shiru dukkaninsu sukayi tsawon lokaci kawanne zuciyarsa ba dadi,

har tsakar dare babu wanda ya kwanta cikinsu dawood kuwa saida sufyaan ya hada masa da allura sbd dagewa yayi saiyabi bayan maskan ayau.

restrnt na cikin hotel din dayayi order fruitsalad waiter din yadawo kawo masa chanjinsa yana dora hannu zaiyi knocking yaji qofar ta bude,

wani mahaukacin ihu yasaki yana kiran jesus...

arikice wasu roomservice biyu dasuka kawo suka matso qofar dakin ai nan take hankaki yatashi da gudu dayan yaje yakira manager da sauran securities.

hannu manager ya dora akai cikin tashin hankali nan take takira police.

ahankali suka kwanto gawarsa suka shimfide tsakiyar dakin cikin maikatan wasu harda hawayensu duk da basusan dalilinsa na kashe kansaba.

rufesa sukayi daidai lokacinda wayarsa tasake ringing babban officern yakai hannuwansa dake sanye cikin handgloves ya dauka.

sufyan naji andauka yayi saurin tashi zaune cikin qaguwa yace,

maska mey...shiru yayi tareda kallon gefen da dawood yake kwance cikin baccin dole na allura saidai yana tunanin tashinsa kowane lokaci shiyasa ya kalli gefensa.

ganin yanayinsa yasa jass dake zaune ya quresa da ido tasowa danjin abinda ake fada.

rawa yaga jikin sufyaan nayi sosai jiri na neman dibarsa atsorace yace,

what is it?

hawaye yaga suna gangarowa daga idanuwansa tuni yasake rikicewa atsawace yace,

tell me wat is it.

sunkuyar dakai yayi tareda fashewa da wani irin kuka abunda baita6ayiba arayuwarsa aikawai sai jass din shima ya zube gefensa zaisake magana cikin wata irin murya sufyaan yace,

khaleefa haydar maska is gone, our friend our brother has left us he is no more,,innalillahi-wainnalayhirrajiun.

kallon sufyaan jass yake ko qyaftawa bayayi idanuwansa da hancinsa tuni sukai wani ja sosai jikinsa ke wata irin rawa har sufyaan baisan sanda ya rungunesa da sauriba wani sabon kuka na zuwar masa.

kamar daga sama sukaji andafasu sufyaan ne kawai ya dago yana ganin dawood yayi saurin miqewa tsaye yana kollonsa cikeda fargabar halinda zai shiga ciki idan yaji rasuwar maska.

wani ja idanuwansa sukayi bakinsa ya qara bushewa yaji komai saidai jin zuciyarsa yake ta bushe masa kamar dutse babu abunda yakeson gani kawai yanxu banda maska.

daqyar ya bude bakinsa dayayi mugun bushewa yace,

muje maska na buqatarmu yanxu.

sai alokacin kuka mara sauti yazowa jass ya dago yakalli dawood yaga yanda idanuwansa sukayi da yanda jikinsa ke rawa yasan tabbas zaifisu shiga wani halin rashin maska.

sufyaan ne yayi qarfin halin sanarda taheer yakaisu airport, suna isa cikin saa suka samu ticket na jirginda zai tashi zuwa lagos alokacin,

harsuka sauka lagos babu mai iya magana acikinsu kowanne idanuwansa jajir abunka da dukkaninsamu farare.

wayar maska sufyaan yasake kura sukaji sunan hotel din sbd ba'a dauke gawarsaba su ake jira.

tunda suka isa harabar hotel dun jikin dawood ya tsananta rawa sufyaan yayi saurin riqesa.

ALLAHU AKBAR,,shine abinda sufyaan ya furta da wata irin wahalalliyar murya lokacinda yabude gawar maska yatabbarda shi 'dinne ya rasu.

kuka sosai jass yakeyi musammam da aka sanardasu shine ya rataye kansa da kansa.

wani irin murmushi dawood yasaki yana kallon gawar yace,

nasanshi tun tasowana bazai ta6a kashe kansa da kansaba.

matsowa officern yayi ya dafasa cikin jimami yace,

a iya 'dan bincikenmu dole zamuce shine ya kashe kansa.

kai tsaye bayan rubuce rubuce aka basu gawar suka wuce kaduna.

koda mamynsa tayi ido biyu da gawar 'danta yanke jiki tayi ta fadi saida aka hada da dr ta farfado gari naqarasa washewa tuni gidan yafara cika da dangin daddynsa sbd mahaifunsa tuni ya rasu.

wani irin yaji da zafi idanuwan dawood keyi sbd tsananin tashin hankali gashi kukanma yaqi zuwa sai rarraba jajayen iduwansa yake akan gawar yaqi masa ko ina yana kusada gawar jiyake kamar maskan zai tashi sukoma rayuwarsu tada mai cikeda farin ciki jin dadi da qaunar juna.

lokacinda aka gama yiwa gawar komai za'a tafi da ita sai alokacin wani irin kuka nai ciwo yazo masa ya sunkuyar dakai yanayi nan jikin duk wanda ke gurin yaqara sanyi musamman dangin dadynsa dasukafi kowa sanin kirki da kyawawan halayensa sbd shine dauke da nauyin karatun 'yayayensu.

dad dinsa da taheer dasuka biyo jirgi da safe sukazo jana'izar suma sun tausayawa dawood dasu jass matuqa sbd ganin halinda suka shiga na rashin amininsu rabin jikinsu.

kuka dawood yayi sosai harsukaje suka dawo nanma hankalinsu yaqara tashi sbd ganin sunrabufa kenan har abada sun rabu kenan da maska musamman ma jass dayaga yanda ake rufe gawa nan take wani irin tsoro da imani yashigesa sbd yasan wata rana zasubi maska da guda guda suna fitowa maqabarta ya kar6i musulunci yana wani irin kuka a hannun limamin dayayi sallar batareda ma su sufyaan sun saniba sbd shikadai yasan ciwon dayakeji na rashin sanin adduar dazaiyiwa maska kamar yanda yaga su sufyaan sun masa.

suna dawowa dakinsa suka shige sunyi kuka har babu wanda zai iya bawa wani hkr acikinsu musamman ma dawood dake ganin duk akansa komai ke faruwa, meyasa tun farko yafada soyayya, meyasa Nur ta 6ace masa har rayuwarsa ta lalace harma data waindake taredashi, kallonsu sufyaan yayi da jajayen idanuwansa yaga yanda sukai wani kalar tausayi bayason yarasasu ko wani abu suma ya samesu dan haka zaiyi nesa dasu sukoma suci gaba da aikinsu su fuskanci sabuwar rayuwa bayason rayuwarsu ta lalace kamar tashi sbd ya rasa NUR,yarasa MASKA, yarasa SOYAYYAR MUM dinsa sbd baya tunanin akwai so yanxu atsakaninta dashi,ya rasa FARIN CIKI, yama rasa komai tunda ya rasa maska da nur.

bayan angama zaman gaisuwa anwatse saida suka qara kusan sati 'daya suna qara kwantarwa da mammyn maska hankali,

ranar dazasu tafi riqe dawood tayi tanata wani irin kuka, kasa riqe nasa kukan yayi saida sukayi mai isarsu kafin daqyar suka tafi bayan dawood yakira taheer anema masa babban gida a abuja zasudawo da mammyn kusadasu a abuja zasu siye mata sbd shine111 babban abinda zasuyiwa maska bayan ransa.

ranar dasuka dawo gidan kamar gidan zaman gaisuwa sbd ko abincin kirki cikinsu bamai iya ci mum ce keta yawo ranason taga kowa yasake sbd bikin nan batason ace za'a dagasa,

tunda dawood yadawo yarasa sukuni zuci sbd yakasa kankarewa zuciyarsa duk shine sanadi har lokacin jin rasuwar maska yake sabuwa gashi jass ma lafiya na neman gagararsa sbd rashin sabo da wahala gashi mum 'dinsa takirasa akan dad dinsa kwanakin zuciyarsa na tsufa na yawan tashi.

hakanan su dawood suka fara shirin tafiya sidney gurin dubo yanayin jikin dad din jass saidai jass din yace su bari saisun gama settlin komai na dawo da mammyn maska abuja tukuna saisu samesa daga baya.

ana gobe zai tafi saraah tabugawa siyama waya tace duk yanda za'ayi ko nawane zata kashe asamo mata abunda takeso sotake idan jass yasa qafa yatafi har abada bazai iya dawowaba ko yaso dawowar,

gyara tsayuwa siyama tayi daga cikin toilet din datake wayar tace,

me kike ganin zai hanasa dawowa ga aminansa biyu dasuka rage masa?

murmushin mugunta tasaki tace,

bazai iya dawowaba koyaso sbd abunda na shirya masa ko airport din qasar bazai bariba za'a wuce dashi prison daurin rai da rai idanma ba'a kashesaba kenan, kedai kibawa seeya dubu dari biyu komai dare komai asubanci akawomin abunda nace.

dariya siyama tayi tace,

wlh koda masifa kuwa sai saqonnan ya iso hannunki. dariya sukayi suna qarasa qulla muguwar aniyarsu kafin suka kashe ta fito toilet bayan tayi waya sa seeya har tayi masa transfer kudinda saraah ta turo mata.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull