Diddigar kaya complete - Chapter 26
Diddigar kaya complete Chapter 26: Diddigar kaya complete Chapter 26. Tuna cabin crew na ranan tayi da irin shigar su se taji hankalinta ya tashi, yanzu fa…
3,362 words
Tuna cabin crew na ranan tayi da irin shigar su se taji hankalinta ya tashi, yanzu fa da su yake yawo duk inda zashi, kuka ta fashe dashi tana jin zafin kishi na huda kirjinta.
Kaman kuwa yaji a jikinshi se ga video Call daga gareshi, ɗagawa tayi bayan ta share hawayenta.
Idanu ya zuba mata na seconds kan ya miƙe zaune yana jefar da pillown hannunshi yace "what happened? Meyasa kika yi kuka?"
Kawai se ta sake sakar mishi kukan. "OMG darling please! Menene? Me ya faru?"
Ganin tana shirin ɗaga mai hankali ne ya saka ta tsagaita kukan tace cikin wata kalar murya. "I miss you 😩 please ka dawo haka..!"
Ajiyar zuciya ya sauke shima cikin kasalalliyar murya yace "kukan duk na kewata ne pretty?"
Kai ta gyaɗa tana sake matso hawaye.. "Ya rabb! I wanna hug you so tide right now...but you are too far I also miss you so bad dear.. amma me aka tanadar min da ake so in dawo?"
Yayi maganan yana kwanciya kan pillow ta saki murmushi tace "Duk abunda kake so"
Yana dage gira yace "really? Duk abunda nake so? U promised? Zaki bani vitamin K, H da L?"
"Me kuma hakan mi carazon?(My heart in Spanish).
"Lalala baki san vitamin K,H da L ba?" Ya faɗa harda kama baki.
Ta gyaɗa kai yace "tohm lemme educate you, vitamin K stands for kiss, H stands for Hug and L stands for love.. Zaki bani?"
Kai ta gyaɗa tace "everything..!"
"Kar fa ki sa in kamo hanya yanzu?" Dariya ta saki yana murmushi yace "soon zaki ganni kinji? Don't cry again please"
Kai ta gyaɗa mai, nan ta sake suka fara labarin gidan suna da kyaun babyn, jin ya kamo zancen saura nata ne yasa ta sallameshi ta gudu.
Washegari a gajiye ta dawo daga school ko abinci bata iya yi ba ta sha tea bayan tayi wanka ta saka light black shirt da iyakarshi cinyarta tare da zubewa kan gado bayan ta yi sallar isha.
Har bacci ya fara shirin daukarta kawai taji tsayuwar mota, da sauri ta miƙe tana leƙa window se ta hangeshi ya fito sanye da kananun kaya baƙaƙe wadda suka mugun amsar farar fatar shi yayi fresh yayi wani irin kyau, da mamaki take Kallonshi har ya ɓace da alama ciki yayi shine ko ya gayamata yana zuwa?
A take farin ciki ya cika fuskar ta, da ɗan gudunta ta buɗe kofa zata nufi sauƙa se suka yi kicibus a parlorn saman, fadawa jikinshi tayi tana murnan ganinshi shima ya rungumeta tsamm yana shakar kamshin ta me daaɗi, daga haka ya nemi zarce mata nan fa tsoro ya bayyana kiri kiri a fuskar ta, janyewa tayi ya tsaya yana kallonta.
"Mu je kayi wanka bari na samo maka abunda zaka ci" Tana shirin wucewa ya dawo da ita jikinshi yace "ke kin ƙoshi?"
Kai ta gyaɗa yace "fine" Yana faɗar haka ya ɗauke ta chadak se ɗakinshi, tana ta zillewa haka ya ribaceta duk da irin tsoratar da tayi ya lallaɓata kuma ya bita a hankali ya cika ta da soyayyarsa me tsayawa a rai, tayi ta mishi raki da shagwaɓa... Wannan dare na daga cikin daren da bazasu taɓa mancewa dashi ba.
Sossai ya buɗe musu wani sabon baabin soyayya, har mancewa da karatu take bare ma da ya ɗan kwana biyu be sake tafiya ba, komai da komai tare suke yi, da yamma su fita koyon tuƙi ana yi ana shan love, a cikin kwanakin duk wadda ze gansu se sun bashi sha'awa, kana ganinsu zaka san akwai tsananin soyayya da shakuwa tsakaninsu.
Kwance take kan doguwar kujera a parlorn tana kallon wani series film yayi sallama ya shigo, da sauri ta miƙe ta tare shi suka rungume juna ya bata peck a kumatu tace "sannu da dawowa Noor"
Yace "yauwa my queen, je bedside ki ɗauko min 50k zan sallami driver ɗin nan tunda my queen hannu ya faɗa"
Tayi murmushi tare da Juyawa ta nufi ɗakinshi ta buɗe se ta sake cin karo da wayanta, a hannu ta ɗauko bayan ta ɗauko kuɗin Dukda ya ga wayan sede be ce komai ba ya karɓi kudin ya sauka.
Bayan ya dawo ya zauna ta kawo mishi ruwa da lemu ya sha, ta dubi wayan tace "Yaaya a bedside ɗinka na ga wayan nan"
Yana kallonta yace "uhmm"
Se ta rasa me zata ce, kawai se ta mike don mayarwa yayi hanzarin riƙo ta yace "you wanna know me nake yi dashi ko?"
Kai ta gyaɗa tana Kallonshi ya janyo ta ta zauna gefen shi yace "bude ki shiga gallery"
Ta buɗe tayi yadda yace Hotunan ta ne masu yawa ciki kasancewar ta me yawan son ɗaukan pics, ta kalleshi ya ɗaga mata gira yace
"su nake kallo a ko da yaushe, ban san taya ba ban san yaushe ba na dae tsinci kaina tsundum cikin ƙaunarki wadda a ko yaushe bani da wani aiki se na kallon hotunanki, na kan yi chargyn wayan musamman don in kallesu, kusan babu wadda ban haddace kalar kayan, tsayuwar da kuma yanayin hoton ba... Believe me I loved you tun kan na san menene so"
Ajiyar zuciya me nauyi ta sauke idanunta cike da hawaye ta rungumeshi tace "our lives are one even though we are in two different bodies, I love you too"
Shima sake shigar da ita jikinshi yayi a hankali tace "sweetheart! Meyasa Zubair yace ka mishi mugunta?" Da sauri ya ɗago ta, tayi hanzarin Kallonshi gabanta na faɗuwa kar fa ya ɗauka da wata manufa ta mishi wannan tambayar..
DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰
Karku sake a baku labari.
🖤Gureenjoh🖤
DƘ
ƘARSHE
"why do you care to know?" Ya tambaya fuskanshi ba cikakken fara'a.
Mikewa tayi tace "am sorry"
Ɗakinshi ta shiga ta Haɗa mishi ruwan wanka ta fito tace "ruwan wankan ka is ready"
Mikewa yayi ya wuce ta ba tare da yace komai ba ya shiga toilet ɗin yayi wanka, ko da ya fito akwai kayanshi marasa nauyi da ta fesa wa turare ta ajiye bisa gadon, dauka yayi ya saka bayan ya shafe jikinshi da mai da turarukan shi, fitowa yayi ya tsaya yana kallonta tana karasa gyara dining ɗin.
Takawa yayi ya rungumeta ta baya a kunnenta ya raɗa mata "I just hate him tun daga sadda na ganki dashi a Abuja, wanchan ganin ya hana mini natsatsen bacci ba tare da na san dalili ba, a sadda na sake ganinku a hotel na ja mishi federal warning amma be daddara ba wai shine har da raba ki da school kina neco at that time ya zo min iya wuya, kuma na san shi dama farin sani sbd miyagun kwayoyi da yake yawan yawo dasu akan kama shi sau da dama a Airport kwana biyu a sake shi, so bayan ya dawo ya tafi Russia, that time nima Ina chan kuma ni zan tuƙo jirgin da ze dawo daga chan zuwa Nijeriya, I clearly saw him with the drugs again.. I then reported him Dukda na so hukunci me tsanani ya hau kanshi sede sun yi anfani da hanya da kuma kuɗi wurin kubutar dashi Dukda ko da ya dawo already you are mine, shiyasa ban kara bi ta kanshi ba"
Kai ta gyaɗa tace "ga abinci"
Bata so Sam ta nuna interest ɗinta kan labarin kar ya ɗauka da wata manufa sanin yadda yake da zafin kishi a kanta, a tare suke cin abincin cikin plate guda, bayan sun gama ta tattare kwanukan.
"Are you OK" Ya tambaya yana janyo ta jikinshi. Kai ta gyaɗa tana ɗan murmushi yace
"menene?" Ta girgiza kai, da yayi insisting se tace Kawo kunnenka kaji yana mika mata ta d'an cije shi kad'an tare da Mikewa ta kwasa da gudu da gudu ya bi ta yana kokarin kamata tana zillewa.
Haka suka ta zagaye tana ta mishi dariya da gwalo daga karshe yayi nasarar kamata suka zube kan kujera yana mata jakulkuli da tambayar wa ya kama tana dariya sossai har da hawaye.
Bayan kwana biyu..
Karfe shidda ta fito lectures ta nufi motarshi ta shiga tana cewa "washhh Allah na, hubby na gaji dayawa"
Yace yana riƙo hannunta "sorry dear, mu je mu sayi abinci sannan mu wuce gida kiyi wanka se in miki tausa"
Murmushi ta saki, suna ƴar hira har suka isa restaurant bata shiga ba shi ya shiga ya fito daga nan suka yi gida.
Da kanshi ya ɗauko plates da spoons da ruwa ganin da gasken gaske ta gaji ɗin, don tunda ta zube kan kujera bata mike ba, Seda ya gama ajiye komai kan ta miƙe zauna buɗe ledar yayi tare da Fiddo takeaway ɗin yana buɗe psoup na kifin tayi hanzarin toshe hancin ta.
Kallonta yayi kan yayi magana ta mike da gudu tayi wurin dining sbd ɗaki ya mata nisa, a take ta fara kwara amai cikinta na murɗawa, a ruɗe ya riƙeta yana mata sannu ruwa ne kawai cikinta don tun safe da ta ci cips bata kara sha'awar komai ba, ta jigata sossai kan ya riƙo ta suka dawo tana kallon kifin ta sake fara kokarin amai cikin muryar kuka tace
"Don Allah yaya ka ɗauke kifin chan bata son gani"
Taimaka mata yayi ta zauna ya karasa ya ɗauke kifin zuwa kitchen yana mamaki.
Hannunta ya riƙe yace "baki da lafiya ne shine baki faɗamin ba? Tun yaushe? Me ke damunki?"
Tace "lafiya ta ƙalau kawai gajiya ce se kuma kifin nan bana son warin"
Yace "wari kuma? Amma I thought kifi da nama na daga cikin abubuwan da kike so?"
Kai ta gyaɗa, yana ta kallonta se kuma yace "wait..! Fauza" Da sauri ta kalleshi, rabon da ya kirata da sunanta tun a yola, tace "Na'am"
"when last kika ga jininki?"
Idanunta na kanshi ta tafi tunani, da sauri ta sanya hannu a kan cikinta tana cewa "could it be possible?"
Yace "sure, When last kika yi period?"
A hankali tace "tun kan in bar nan in tafi yola, satin da ya kamata na fara kuka je kai da Fatima"
Ai da wuri ya tafi ya ɗauko mata hijab ya zo ya kama hannunta suka yi asibiti, bayan dogon gwaje gwaje Jafar ya musu albishir da ciki na tsawon wata uku bata taɓa sani ba se ranar, farin cikin da suka shiga baya misaltuwa barin ma shi da har Seda yayi hawaye, ze kira gida tayi saurin kwashe wayar tana shagwaɓewa.
"Eyyaaa yaya karka gayamusu don Allah"
Yace "Meyasa bayan abun farin ciki ne ya same mu love?"
Tace "Ai to ba zasu san abunda aka yi ba, ni dae bana so" Dariya sossai ya saki, Fauza har yanzu taɓara irin na yara na damunta.
"Fine my baby mama, ba zan faɗa ba"
Daga asibiti yawon neman abunda zata ci suka fara, a wani tsadadden restaurant suka yada zango a gabansu aka ajiye abun gashi yana gasa mata nama tana ci, ta ci sossai kan aka kawo mata milkshake ta jingina da jikinshi.
Kwanciya tayi jikinshi tare da kai mishi cup d'in bakinshi yayi sipping ta dawor dashi nata ta sha tana sake murmushi.
Rayuwa ta sake yi musu daaɗi sossai, a week after suka fara exams ya ɗan yi tafiya bayan ya dawo lokacin ta gama ya shirya musu tafiya, Allah ya sa cikin nata ba wani laulayi me wahalarwa, ƙasar Greece suka tafi suka baje kolin soyayyarsu a chan, sati uku suka yi a chan kan suka wuce Australia se ganinsu Ya fadeela tayi.
Sun matukar burge ta soyayyarsu ya tafi da ita ga wani kyau da kowannensu ya kara da girma alamar hankalinsu kwance yake, daga nan suka wuce wurin Ya fadyaa husna tayi ta murnan ganinsu suma kwana biyu suka musu suka tattara suka dawo sbd hutun ta ya kare.
BAYAN WATA HUƊU
A hankali take sauƙowa daga jirgin sbd yadda cikinta yayi wani mugun girma Dukda kwata kwata wata bakwai kenan, kafafunta da kyar take ɗaga su sanye da wani bubu Abaya me stones ta yafa gyalen, yana rike da jakanta a hannu daya yana rike da ita suka nufi farhan dake ta zabga murmushin ganinsu.
Se kallonta ake sbd Fauza fa ciki be hanata gayunta ba, wani lokacin in su firdausi na tsokanarta ta kan ce ciki ne fa da ita ba hauka ta soma ba, suyi ta mata dariya, shi karan kanshi ya kan yaba kokarin ta Dukda kankantar shekarunta bata taɓa gazawa a kanshi ba daga cimarshi, tsabtarshi da hakkinshi babu abunda ta dena ga karatu.
Gidan cike yake da mutane sbd yaune ake walimar Fa'iza da Faraj se Falaq da itama se yanzu lokacin yayi, a haka suka ratso mutane duk yadda take sunne kai shi kam ko a jikinshi se kara mannata da jikinshi yake har parlorn Jaddah.
Farin ciki ne ya cika ta fall ko a hira basu san da cikin ba se ganin abu kawai suka yi, daga Amminta har mammi ba karamin farin cikin ganinta haka suka yi ba hankali kwance, kar iyayenta mazan su ji labari.
Duk yadda ta ci Burin bukin se gashi ita a zaune tayi komai sbd kafafunta da suka ƙi, har aka sada su da gidajensu jama'a suka watse.
Tana kwance kan gadon Amminta hannunta waya ne tana dubawa taga saƙonshi.
Mikewa tayi zaune ta dubi Ammi tace "Ammi akwai abinci kuwa a sashen nan?"
Ammi tace "eh a kawo miki ne?"
"A'a Yaya za'a Haɗawa faazila ta bini dashi na tabbatar be ci komai ba" seda ta faɗa kuma kunya ya kamata, Ammin murmushi kawai tayi tare da miƙewa ta hado ta ba faazila tuni Fauza kam ta lallaɓa ta wuce.
Tun daga kofa ya tarbeta ya ɗan rungumeta "Sannu baby mama... Allah ya sauke ki lafiya, Allah ya miki albarka".
Kusan kalaman da ta saba ji kenan daga gareshi tunda cikinta ya fara girma "Ameen Daddyn baby thank you"
Zama suka yi yana nuna mata wasu gadajen yara masu kyau sossai wai ta zaɓa order ɗinshi zasu zo wani sati, tace "yanzu duk waenda muka yi ta jida a Abuja be isa ba hubby?"
Yana murmushi yace "ko duka shagunan Abuja muka saye ni dae be min ba... Uhmm na fa ba da aikin ɗakin nan da muka yi magana"
Ɗakin Fatima ne ya sa aka fidda komai za'a gyarawa baby, tayi murmushi kawai se ga faazila da abinci, shi ya karɓa suka ci tare sbd ya Santa idan ba shi yake bata ba bata wani ci me yawa.
Duk yadda ya so tafiyarsu tare haka ya hakura ya barta sbd ya san yanzu tana bukatar babba kusa da ita, sede suna manne a waya.
Watanta ɗaya da sati biyu a gida ranar ta tashi da nakuda me tsanani, yana kwance tun dare yake ta juye juye bayan mafarkin ta da yayi, ya kirata bata yi picking ba.
Hankalinshi gabaɗaya ya tafi yola, haka dae da yaga baccin ba ze yiwu ba ya tashi ya fara nafilfili yana rokar mata sauka lafiya.
Bayan ya dawo sallar asuba ya danna kiran Jaddah, ta ɗaga daga yadda yaji muryarta ya rikice yana tambayar lafiya? Ta sanar mishi Fauza ke labor.
Hmm Allah ne kadai ya kaishi Airport lafiya don ma akwai available flight karfe takwas haka yayi ta safa da marwa a Airport ɗin hankalinshi duk a tashe.
Har ya isa yola ya isa asibitin bata haihu ba, kuma wai ta kwana a haka, ai be jira wani jawabi ba ya banka kofar ya shige, duk ta galabaita kaman jira nakudar ya sake taso mata.
A jikinshi ya sanyata yana mata Adu'a, wani riƙo da ta mishi seda ya runtse idanu be buɗe ba se da kukan jariri ya cika kunnuwanshi, Alhamdulillah! Yake ta nanatawa yana mata sannu a lokaci ɗaya yana shafa kanta.
Wani Sabon nakuda ne ya sake tasar mata, ba bata lokaci ta sake sulbiyo wani babyn.
Shikam Sam hankalinshi na kanta irin wahalar da ta sha se zufa take yi yana share mata.
Mika mishi yaran aka yi bayan an tsaftace su. Ya rungumesu hawaye na zubar mishi..
"Alhamdulillah! Alhamdulillah!!" Lallai Allah me kyauta da ƙari shine yau rungume da ɗan shi ba ma guda ɗaya ba har biyu, wani irin godiya ze yiwa ubangiji? Fitowa yayi dasu su Jaddah kowa farin ciki a take Fa'iza da tun asuba ta iso asibitin ta ɗaukesu hoto ta turawa su ya fadila kowa murna mata ne Duka kaman babansu yayi khaki ya tofar har hasken fatar.
Wani irin so da kauna da Faizan yayi ta nuna mata a asibitin sede ita ta ji kunya shi kam ko a gyalenshi, Kwananta ɗaya aka sallameta, Faizan ya kusa cika parlorn Jaddah da saye saye, duk.abunda aka ce ya dace me jego ta ci se ya je ya sayo, kan saniya har uku ya kawo ga manyan bindi yace ayi ta mata psoup tana sha.
Ranar suna yara suka ci sunan Jaddah da mammi, fa'iza ce ta musu inkiyar Arwa da marwa, me jego ta samu kyaututtuka masu dumbin yawa, ta shiga ta fita a wanka da ado kam masha Allah, shima angon karni ba'a barshi a baya ba suka dinga chanza dressing ana daukar su hotuna take suka baza ko ina latest parents of the month ba, kyautar tsaleliyar mota me rai da motsi Faizan yayi mata da wani set ɗin gold me tsada tukuicin kyautar da ta mishi.
Sanye da doguwar hijabi har ƙasa ta shigo gidan, idan ba ka mata farin sani ba bazaka gane ta ba, tayi baƙi sossai ta rame kaman ba Fatima ba, kai tsaye inda aka yi decorating don taron sunan ta karasa, a gaban Fauziyya kawai ta zube tare da kama kafafunta ta fashe da wani irin kuka da ya ja hankalin mutane masu yawa.
Faizan yayi saurin mikewa yana kallonta, Fauza ta ganeta tayi saurin tare shi ganin ze taɓa ta don rabata da jikinta.
"Fatima???"
Kowa sunan ya maimaita yana kallonta da mamakin yadda ta koma
"Don darajar Allah ku yafemana Fauziyya, ke da Ammi da mammi ku dubi Allah ku yafe mana ko zamu ga da kyau, Don Allah ku yafewa Auntyna ta tafi tana rokar gafararku sede babu halin zuwa nan ɗin..."
"Ta rasu??"
Fa'iza tayi tambayar idanunta duka waje
Kuka me ciwo Fatima ta cigaba da yi wadda ya saka su jin tausayinta.
"Ta rasu Fa'iza, ta ce don Allah in ce kuma ku yafe mata, ku rokar mata Allah gafara, ta kamu da cutar dajin kwakwalwa ba tare da mun sani ba aka mata allura, tayi jinya me tsawo wadda kan ta rasu seda kamannin fuskanta ya sauya, fatar fuskanta da naman haka suke zazzagowa suna zub....." Kuka ne ya kwace mata, fa'iza ma nayi.
Fauza seda ta zub da hawaye jin irin wahalar da Aunty ta sha kan mutuwa lallai wadda yace ruwan wani baze tafasa ba nashi ko zafi baze yi ba, yanzu wa gari ya waya? Arziki, kuɗi babu abunda baya jawowa.. Allah ya tsarremu da son zuciya.
Sun ce sun yafe sauran ita da ubangijinta, Fatima tayi ta godiya ko da Baba prof ya tambayi ina take zaune ita nan ta gaya musu ai Aunty ɓoye iyayenta tayi suna fama da baƙar rayuwa, kilan da ta taimaka musu sun zama wasu abu kan barinta gidan Sulaiman ɗin da sun iya sun Haɗa mata kudin aikin da ya gagara har ta mutu da azabar ciwon cancer.
Ta sheda musu itama zata koma gidan nata mahaifin dama Aunty ne taki sam ta bari su wani shaku sbd burinta a gidan prof ɗin..
Kyauta me yawa suka mata, Faizan dae be ce komai ba, se Kallonshi take da yaranshi rungume kirjinshi tana jin yadda azabar sonshi ke huda zuciyarta sede ya ta iya ba komai kake so kake samu ba.
***
Yau suke gama wanka, ita da su faazila suka fita zagayen arba'in sun zazzaga wuraren en uwa da abokan arziki, sun zo ta wurin gidansu Sakina tayi parking motar ta sauka tana tambayar me gadi mutanen gidan.