Kenza eBookz

Diddigar kaya complete - Chapter 4

Diddigar kaya complete - Chapter 4

Diddigar kaya complete Chapter 4: Diddigar kaya complete Chapter 4. Ba'a rufa shekara ba Aka sake baiwa Baba prof mata Hussaina daga Wani kauye na jalingo…

3,364 words

Ba'a rufa shekara ba Aka sake baiwa Baba prof mata Hussaina daga Wani kauye na jalingo da ake kira Sunkani, itama Fulani ce ba'a ɓata lokaci ba aka yi bukin nasu, shekaranta ɗaya Mammi kaman yadda Faizan ke kira ta sake haihuwar ɗa namiji Faahim(me ilimi or mai fahimta).

Ammi itama ta sake haihuwar Falaq(Ketowar Alfijir), Anan hankalin Ruqayya ya soma tashi, dama wani irin zama suke yi marar daaɗi da Maa wadda musabbabin abun Ruqayya ce, tunda ta saka kafa gidan ta fahimci nisan dake tsakanin Ibrahim da Sulaiman kaman nisan dake tsakanin sama da ƙasa ne, wai ba haka aka so ba kanin miji yafi miji kyau.

Bata kara shiga tunani ba seda taga irin girmamawar Sulaiman ga Ibrahim kai tsaye zaka iya cewa matsayin mahaifi ya bashi don ko ratar dake tsakaninsu rata ne me girma, randa ta haihu kuwa taga Sulaiman ya ɗauki yarinyar musamman ya kaiwa Ibrahim shi ya mata huɗuba ya sa mata suna alhali ta riga ta faɗawa Sulaiman sunan da take so a sawa yarinyar, ba karamin rikici suka yi ba akan sunan Fadeelah sede Sulaiman ya fi karfinta haka ta bari, sede daga ranar maganan arziki ita da Mammi babu dama chan sama sama ne, se kuma gashi Mammi na jera maza Ita kuma tana jera mata alhali Ibrahim da Sulaiman basu bambanta dukiyar su ba.

Zaman doya da manja ake yi a gidan har Amaryar baba prof itama ta haihu ta samu mace, Falusha(Haske).

Bayan haihuwan Falusha Baba prof yayi tafiya Maiduguri inda ya dawo da Auren Zainab, ba karamin rikici aka yi da Hussaina ba kan ta saduda, Mammi kam fatan alkhairi kawai tayi mishi, a lokacin ma tana da tsohon ciki inda ta haifi Fahad(Damisa) ba'a ɗau lokaci ba Ammi ta sake haihuwan Fadyaa(sadaukarwa).

Hussaina da yaran suke kira Maami ta sake haifan Farrah(Florence nau'in haske), har lokacin zainab bata haihu ba, Baba prof ya karo aure cikin ƴan gudun Hijira Sakinah itama barebari ce usul, a tare suka fara haihuwa da Zainab wacce su Faizan ke kira Umma, ita ta samu Faraj(cure, waraka kenan) yayinda sakina ta samu Farzan(me wayau).

Daga nan dukkansu basu sake haihuwa ba seda aka ɗau lokaci Ammi kuwa ta haifi maza biyu a tsakani Farhan(farin ciki) da Faris (horseman).

A lokacin Baba prof ya kara sashe a gefe da masallaci sbd matasan yaran da suka fara tasowa, Mammi ta sake haihuwar Farida(ta musamman ko lu'ulu'u me daraja) daga nan har yau bata sake haihuwa ba. Bayan nan Sakinah (umma) ta sake haihuwan Farhuddeen(farin cikin addini). Sulaiman ya ƙara aure inda ya auri sumayya ta zo gidan da ƴarta Fatima, sumayya sun haihu tare da Ammi(ruqayya), Ammi ta haifi Fauza (triumphant wato nasara) yayinda sumayya ta haifi fa'iza (Gain, wato samu).

Bayan su Fauxa, sumayya ta kara yara uku Fadiyah(me kyau), Fakiha(fruits) se Faazila(gaskiya) su kenan yaran gidan karan katakap.

Mammi na da huɗu Faizan, Faahim, Fahad da farida. Maami na da biyu Falusha da Farrah. Umma na da guda biyu Faraj da Farhuddeen. Daada na da guda ɗaya Farzan. Gabaɗaya yaran na Baba prof guda 9 ne Allah ya bashi.

Se Alhaji wato Sulaiman. Ammi na da shidda Fadeelah, Falaq, Fadyaa, Farhan, Faris se Fauxa. Aunty Amarya na da huɗu Fa'iza, fadhiya,Fakiha da Faazila. Gaɓadaya yaranshi 10.

Gidan na da wani irin dokoki ne wadda duk tsari na addini ne, yaran kuwa akwai matukar shakuwa, tausayi da kauna irin ta ƴan uwantaka a tsakaninsu Baba prof baya wasa da tarbiyar su ko na miskala zarratin, duk kuma abunda ze shimfiɗa hannu bibbiyu Alhaji ke karɓa.

Ya ƙara samun wani girma ne a unguwan sbd yadda baya banbance ƴaƴanshi da na dangin shi Dukda ba komai yake da iko akai ba sede fa ya san duka yaran don dole a islamiyya ɗinshi zasu yi karatu kuma shi da kanshi yake koyar dasu sbd dumbin falala dake cikin koyarwa da yara addini babban sadaqatul jariya ce wacce bata gushewa har se me wannan ilimi ya gushe idan kuma akwai wadda ya koya daga wurin ɗaya haka ze yi ta gudana har illa ma shaa Allah.

Wannan al'ada itace zaɓarwa yara abokan zama masu nagarta, kawai ze kira ka a waya akan Zaku yi baƙo ze zo wurin wacce kaza, ko kuma wane kaza na gidan ka yaje wurin wacce kaza na gidan wane, a haka ya Haɗa wani irin bond me girma tsakanin kaɓilarsu ta barebari da suke nan unguwar, kuma duk zaɓin shi suna alfahari dashi sbd baya taɓa zaɓin banza.

Mata da mazan gidanshi kan yi karatu har matakin degree ma idan har maneminki be fito ba, sbd ya san muhimmancin karatu ya kuma san karatu wani makami ne da zaka barwa yaro wadda ba ze taɓa tagayyara ba hakan ne dalilin da ya sa ko maneminki ya fito baki fara makarantar gaba da jami'a ba dole akwai yarjejeniyar ci gaban karatun ki don gudun halin rayuwa.

Faizan pilot ne wato matuƙin jirgi wadda aka fi sani da Captain Faizan matashi me jini a jika, kyaun fuska da na hali, ilimi both Islamic and western, his father's favorite, the first born to the house of F, har yau Allah be yi yayi aure ba kaman ba Baba prof ne ya haife shi ba.

Fadeelah tana auren wani businessman suna zama a Australia with kids.

Faahim Navy ne, an aura mishi Fadyaa suna da ƴaƴa biyu. Auren da saida aka kai ruwa rana da Ammi ta saduda.

Falaq har yau bata yi aure ba sbd rashin lafiya da take fama dashi.

Fahad na aiki da inland revenue with a wife and a kid.

Farida tayi aure some months ago with a costume officer suna zaune Lagos.

Falusha and Farrah duk tare aka yi aurensu su biyun duk suna yola suna auren ma'aikatan Gomnati.

Faraj, Farhan da Farzan duk suna final year of their studies a Apti American University mabanbantan courses.

Farhuddeen da Faris suna SS3

Fatima na SS2

Fauxa da fa'iza na SS1

Fadhiya js1, Fakiha pri5 and Faazila pri3.

Tou readers ya kuka ji GIDAN F? A tunaninku duk wani haɗin kai da kaunar juna da zaman lumana dake wakana a wannan gida me cike da addini me ɗaurewa ne har abada? Sheɗan ze iya barin ɗaurewar wannan haɗin kan da kaunar kuwa? Akwai wasu abubuwan da ban sa cikin tarihin gidan ba a hankali a hankali Zaku fahimta in shaa Allah, mu je zuwa🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️.

DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya zuwa wannan layin 09039206763 Ko ki tura katin waya ta layin na sama tare da shedar biya ta what'sapp. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰

Karku sake a baku labari.

🖤Gureenjoh🖤

DIDDIGAR ƘAYA (Mai Wuyar Tsincewa)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN. (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* And Now.. *Diddigar ƙaya... Paid*

*Shafi Na Shidda*

*PAID BOOK*

ƊANƊANO

**WANNAN SHAFI SADAUKARWA CE GAREKI MRSJMOON GWANATA KUMA SHUGABATA🥰❤️**

"Wa'alaikumussalam warahmatullah sannu da zuwa Mammi" Cewar Fauxa tana me sakin murmushi.

Jaddah ma sannu Da zuwa ta mata, Seda ta amsa na Jaddah kan tace "Fauxa ke kam ba zan amsa ba, riƙe kayan ki"

Dariya suka yi duka tace "yi hakuri maa in shaa Allahu zan zo"

Tace "na gaji da ji, ke kam gidan mu kaman wadda aka yiwa farraku dashi idan ba'a compound ba ko nan sashen Jaddah ba'a ganinki Sam?"

Dariya kawai take yi, wlh ita tana rasa dalilin da yasa take kasa shiga sashen na Baba prof, duk matanshi ma dama banda gaisuwa Mammi ce kawai take sakewa sossai, tana son matan ba tare da ta san dalili ba.

"Ina yini Jaddah? Fatan mun sameku lafiya?"

Cike da so Jaddah ta amsa mata, duk cikin surukanta babu mafi soyuwa a gareta irin Aisha, matar ta dabance cikin mata, tana da kawaici sossai gata da fara'a bazaka taɓa ganinta bata murmushi ba, tana da son mutane da jan kowa a jiki bata damuwa da kai nata ne ko ba nata ba, tana da kirki fiye da zato, duk cikin matan na Baba prof babu me shiga kitchen da kanshi yayiwa Jaddah girki na musamman ya kuma tako ya kawo ya zauna suyi hira sossai irin Mammi.

Dukda tana yawan fama da matsanancin ciwon kafa se ta kwana biyu uku ma bata iya tafiya idan ciwon ya tasar mata amma hakan be sa tayi kasa a gwiwa wurin kula da mijinta da surukanta ba, kuma ita da kanta take taya baba prof kula da mahaifiyar tashi mace ce da a duk lokacin da mijinta ze shigo da wani abu a Leda bazata taɓa karɓa ba se ta tambayeshi ina na Jaddah? Idan har ya manta ko be saya ba sbd ganin ta girma da abun ko wani abu haka zata sa ya koma ya sayo, tana da wani ƙima na daban a zuciyar mutanen gidan musamman mijinta da surukuwarta.

"Aisha ya ciwon kafan? Fatan kin ji daaɗin maganin nan na Gamborun gala?"

Tana murmushi tace "wlh na ji daaɗinshi sossai Jaddah, kafa yayi sauƙi sosai"

Jaddah tace "Toh Allah ya qara afuwa"

Suka amsa da Ameen.

Chan cikin hiransu Jaddah tace "ni kam Aisha kina ji daga wurin wannan Miskilin nawa kuwa? Kwana biyu be kirani ba fa"

Maa tace tana murmushi "eh Jaddah, ya ce min ze shiga ƙasar da bashi da simcard ɗinta idan har ze fi kwana biyu to ze saya Sim ɗin sbd mu ji lafiyar shi idan kuma ba ze wuce hakan ba in ya bar ƙasar in shaa Allah ze ƙira"

Jaddah tayi tsaki tace "ba ga irin ta ba, mutum ne kullum a sama kaman tsuntsu fisabilillahi idan ya zo nan fa ya zube Sima simai se ki dauka kamfanin mtn ne, wani idan ya manta na wace kasa ce kuma be da lokacin gwadawa sede kiji katttt ya karya ta"

Mammi na dariya zata yi magana kenan Fauxa ta miƙe Tsam tayi ɗakin Jaddah fuskanta babu yabo babu fallasa, da idanu duk suka bita Seda ta shige kan Jaddah ta zabga tagumi cikin jimami.

Mammi tace "Jaddah Dan Allah ki dena sa damuwa a ranki sbd yaran nan kar kije wani ciwo ya kama ki, har yanzu dukkansu yara ne in Shaa Allah gaba ko ance su yi baza su yi ba"

Jaddah tace "se yaushe kenan Aisha? Karki manta Faizan ya baiwa Talatin da biyar baya wannan ta fi sha shida amma ace se gaba? Wani gaban kuma bayan wannan? Wlh Allah ya gani babu abunda ke ci min tuwo a ƙwarya irin tsananin rashin jituwar yaran nan, har tsoro irin ƙin da suke yiwa juna yake bani kwata kwata ɗaya baze taɓa bada fuska ayi maganan ɗaya a gabanshi ba?"

Mammi tace "ni na fi ganin laifin shi babban kwabon nasu ai, na yi faɗa har na gaji amma ya kasa fahimtata"

Jaddah tace "ya Allah ka kawo mana karshen wannan abun nasu"

Mammi ta amsa da Ameen suka kama wani hiran kuma se dab magrib kowa yayi alwala suka tafi masallaci a tare.

Bayan kwana biyu

Tunda ta tsefe kanta bata yi kitso ba gashi har yau Sunday, barta dae da neman tsokananta wadda bata rabo dashi, ita da fa'iza ce tafe suna hira sbd duk gidan babu wacce suke shiri kuma suke ƙaunar juna kaman fa'iza babu wacce kuma ta tsana irin Fatima in ka cire Faizan.

Abun nata kaman jinnu, tana son fa'iza sbd haƙurin ta ta kan yi hakuri da duk wani halinta tana yawan kare ta, in kaga sun yi faɗa to akan Fatima ne, Fatima na son nuna mata uwarsu ɗaya da fa'iza ita kuma ta tsani hakan, idan kuma fa'iza tace mata kar ta biyewa Fatima su yi ai jinin dake yawo a jikinta shine yake yawo a nata jikin tunda uba suka Haɗa se ta ce ai fa'iza ta goyi bayan Fatima alhali Agola take a gidan Anan zasu yi faɗa su Rabu Toh Fauxa da zuciya se ayi kwana biyu bata huce ba hakan yasa shirin su da fa'izan yake yawan ja baya.

Sashen Jaddah suka shiga tana zaune tana jan chasbi Fauxa ta zube kan kujera tace "Jaddah wainar fulawa nake son ci na manja da yaji me tafarnuwa"

Jaddah tace "se ki ci ai, ni kam ban yi tunanin akwai fulawa a gidan nan ba"

Fa'iza tace "kash! Ya kenan Fauxa gashi namu ma babu ya kare"

Mikewa Fauxa tayi tace "mu je wurin Mammi mu yi, dama wlh tun jiya ban je na gaisheta da ciwon kafan nan nata da ya tashi ba"

Ficewa suka yi Jaddah bata ce komai ba har suka fice, ko da suka isa a ɗaki suka sameta kwance a ƙasa an shimfiɗa mata bargo me taushi da pillows, ƴar yayarta da zata ɗan girme su da take hannun ta tun bayan auren farida ita ke taimaka mata tunda bata karatu.

Sashukan nan basu da maraba da sashen su Fauxa, se na kitchen da akwai cikin kowanni sashe saɓanin nasu, se kuma na yawan ɗakuna wadda nan kofa biyu ke fuskantan biyu, na Mammi ne na farko wadda babban parlor ne sossai da kitchen da ɗakuna biyu, hakan ne kuma a kowanni ɗaki, sannan akwai kitchen na waje da kowacce me girki a sashen take girki ranan girkin ta, tsakar gidansu bishiyar cashew ce me ni'imtacciyar inuwa.

"Fauxa yau ke ce a sashen namu? Lallai za'a yi ruwa da kankara"

Fauxa na murmushi ta zube kasa tace "sannu Mammi ina yini? Ya kafa?"

Mammi tace "Alhamdulillah Fauxa da sauki sossai har ɗazu ma na taka zuwa toilet"

Fauxa tace "Allah ubangiji ya ƙara sauki"

Da Ameen ta amsa, fai'za ma ta gaisheta.

Fauxa tace "Mammikina da fulawa? Wainar fulawa nake son yi bamu da fulawa haka Jaddah ma" Ta karashe tana karya wuya

Mammi tace "Ah Kice abunda ya kawo ki kenan ba zuwa na musamman da kike cewa ba"

Tana dariya tace "Allah ba haka bane dama nayi niyyar zuwa"

Mammi tace "ba za'a rasa fulawan nan ba ku duba a kitchen na cikin nan se kuyi, dama akwai yaji da Zuwaira(kanwar ta) ta kawo min ma jiya da alama ze yi daaɗi"

Cikin jin daaɗi Fauxa ta mike, fa'iza ta bi bayanta suka yi kitchen.

Anan suka kwaɓa suka fara suya se suka fara na manja sbd yadda Fauxa ta hanata sakat Seda suka yi me yawa se suka koma man gyaɗa sbd shi fa'iza ke so, suna cikin yi se Fa'iza tace "ni bani manjan ma in yi mixing kaɗan yadda ze bada wani dandano me armashi"

Fauxa tace "Wallahi bazan bayar ba ka jimin wayau, kowa ya ci da plain abunda yake so"

Musu suka fara, fa'iza ta kai hannu da niyyar fusgan manjan Fauxa ta ɓalle da gudu daidai kofar kitchen ɗin taji taci wani uban karo da wani broad chest me yanayi da rock, gabaɗaya manjan ya zube a jikin kayan mutumin.

A hankali na kai idanuna bisa mutumin da aka kwararawa manjan Masha Allah, kyakyawar matashi ne me tsawo sossai a kamannin fuska zaka iya cewa kaman an tsaga kara da Fauxa, banbancin nasu kaɗan ne shi ɗin fari ne Kal saɓanin Fauxa, haka idanunshi wasu irin Ash ne me walƙiya..

Ko kaɗan bashi da rama wani irin tsayayyen namiji ne da yake da jikin every woman dream, daga ka ganshi zaka san cewa ma'abocin workouts ne, yana da dogon hanci sak irin nata da lips wadda suke iri daya da nata kaman an shafa musu cherries yadda suke kyalli, yana da gashin saje gyararre me kyau wadda har zuwa gemu amma be cika yawa ba, a gyare tsab baƙi sidiƙ se shining yake yi wadda ya kara fitar da ainihin kalar farin fatar shi, daga yatsunshi na hannu zuwa na kafa dogaye ne a gyare suke tsab gwanin burgewa, yana da wani irin kwarjini da farin jini sede fa ma'abocin tsare gida ne, Miskilin bugawa a jarida ne sannan yana da murɗaɗɗen hali da zama dashi se ka shirya.

Sanye yake da Fararen kaya Kal Kal Jean da shirt designers kafafunshi sanye da Dior lufas masu kyau, kamshinshi a take ya baza lungu da sako na kitchen ɗin, kyawawan idanunshi na kafe kan inda manja ya zube a Rigan nashi kan a hankali cikin tsantsar natsuwa ya ɗago birkitattun idanunsa dake cike da kwarjini irin na cikakkun maza ya zuba mata.

Wani irin faɗuwar gaba ne ya risketa ga tsoro da ya kusa sumar da ita, cikin da na sanin fara sha'awar wainar fulawa da ta yi a yau ta fara ja da baya, wannan baƙin azzalumin yanzu se ya mata abunda se ta gwammaci kiɗa da karatu, ita kanta fa'iza dake tsaye jikin gas a take ta saukar da pan ɗin sede ta kasa kashe gas ɗin se rawan tsoro jikinta ya ɗauka.

Kokari yake yayi controlling ɓacin ranshi sede ganin ko sannu bare yi haƙuri ta kasa ce mai yasa ya ɗaga kafafunshi ya fara takawa zuwa gareta, a duniya ya tsani ganin yarinyar halayen ta, neman tsokananta, rashin jinta, rashin kunyarta duk ya tsana bata yi mishi don babu fuskan yi ɗin sede ya kan tsinkaya tana yiwa wasu, sannu be taɓa Haɗa su ba tana karama in har zata zo kusa dashi se ya mata mugunta tun tana zuwa har ta dena hakan ya dasa mata tsoron shi, Sam baya zama a inda take sbd hakan itama ta koyi kin zama a inda yake, idan kana son ganin ɓacin ranshi ka ce suna kama yanzu se ku samu matsala, ya kan yi mamakin yadda kowa a gidan complain ɗinshi baya wuce Fauziyya har iyayensu maza, shi yana ganin iskancinta wuri ya samu bata sami me saita ta bane, hakan ya sa ya buga Mata tambarin annoba don shi da annoba yake kiranta.

Ganin da gaske nufanta yake ga fuskanshi babu ɗigon rahama yasa tayi kokarin gudu, taku ɗaya yayi ya saka mata ƙafa hantsilawa tayi zata faɗi, garin neman abunda zata dafe don gujewa kaiwa ƙasa ta ɗaura hannunta na dama bisa kan gas ɗin da yake kunne, ba wutan bane karafunan da suka riga suka jima da ɗaukan zafi sossai ne suka aika mata da wani irin raɗaɗin azaba zuwa kwakwalwanta har bata san sadda ta saki wani ƙaran azaba ba tana rike hannun.

Wani mugun murmushi da ko haƙorin shi be bayyana ba ya saki kan ya juya ya fice daga kitchen ɗin, da gudu Fa'iza ta kashe gas ɗin kan tayi kanta ta kama hannunta a tsorace tana kallon fuskanta yadda hawaye ke ambaliya kaɗai zaka gani ka san tana cikin wani hali ga zufa dake aikin tsatsafo mata.

"Sannu Fauxa! Sannu"

Mammi ce jin ihun Fauxa yasa ta lallaɓa ta fito a hankali ta nufe su tana cewa "Subhanallah me ya same ta? Konewa tayi?"

Cikin kuka Fauza tace "mammi wannan azzalumin ne ya saka min hannu akan karafunan gas, Wayyoooo hannuna!"

A hankali Mammi tace "FAIZAN!" Don shi kaɗai Fauxa ke cewa Azzalumi. Da sauri Mammi ta cewa Fauxa "ɗauko akamu yi sauri gashi a chan in saka mata kar ya tashi"

A hankali ta karasa gareta ta ɗaga ta tare da riƙe hannun har ya tashi gabaɗaya tafin na hannunta yayi wani kalar bororo, wani irin tausayinta ne ya rufe Maa sbd ta san zafin wuta ba daaɗi amma se ta saɓawa Faizan, ashe kaddarar ƙone wa ya kawo ta sashen nata da ta jima tana mita akan rashin zuwan nata, da kuwa ta san Faizan ma ze zo yau da bata ma bari sun yi wainar anan ba, wani irin abu ne haka?

Akamun fa'iza ta kawo ta kwaɓa ta saka mata har lokacin kuka take, tayi tayi ta ci wainar da saura kaɗan ma su kammala ta ƙi tace ta koshi, cikin rashin jin daaɗi Mammi ke bin ta da ido har ta fice se ta saka fa'iza juye wainar a flask ta bita dashi su je su ci a gida don ta tabbatar ko sashen Jaddah Fauxa bazata kara zuwa ba se an tabbatar mata da baya gari.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull