Kenza eBookz

Diddigar kaya complete - Chapter 8

Diddigar kaya complete - Chapter 8

Diddigar kaya complete Chapter 8: Diddigar kaya complete Chapter 8. Da sauri ya miƙe tsaye kenan ba gizau idanunshi ke yi ba ita ɗin ce, yace "mammi…

3,325 words

Da sauri ya miƙe tsaye kenan ba gizau idanunshi ke yi ba ita ɗin ce, yace "mammi yarinyar nan ba Gombe ta tafi ba, jiya na ganta da wani a halin maye da shigar banza!"

"Faizan!" Mammi ta kirashi daga jin muryarta ya san ranta ne ya soma ɓaci.

"Faizan don baka son yarinyar nan shine zaka ɗauko hanyar yi mata sharri? Buguwa fa ka ce? Sannan da namiji a hotel?"

Yace "kin san ban taɓa miki ƙarya ba, kuma a kan wannan annobar ba zan fara ba. Ko rantsuwa nayi ba zan yi kaffara ba, zan kira Farhan ya je min makarantar ya bincika don bazamu lamunta ta ɓata mana sunan gida ba, Never!"

Mammi tace "sunanta Fauziyya, kada ka sake ce mata annoba, sannan takarda da tambarin makaranta da kuma stamp da sa hannu ta kawo ni ta fara kawowa kuma tafiyar ba ita kaɗai ba ce, kar in sake jin irin wannan zance daga bakinka, karka manta ƙanwarka ce kuma karka manta tarbiyar gidan da ka fito"

Tana kai nan ta kashe wayan, hannunta har rawa yake, ta san Faizan be taɓa yi mata karya ba, idan ba akwai abunda ya tsana karya ne, sai dae bazata taɓa yardar wa zuciyarta Fauza ya gani a hotel a Abuja ba, kila kama ce kawai.

Har ta gama girki tana nazari, Farhan na shigowa gaisheta bayan sun gaisa tace "Farhan ina so ka je min makarantar yaran nan ka samu vice wadda ya sanya hannu a tafiyar su Fauza ya sake tabbatar maka da tafiyar, sannan ya kira wani a Haɗa ku kaji lafiyarta"

Farhan yace "mammi wani abun kuma ya faru ne? Na san Fauza sarai yadda kike maganan nan kuma kaman kina ɓoye damuwa ne a ƙasan ranki"

Tace "Babu komai Farhan, ka tabbatar kayi duk abunda nace maka"

A ladabce yace "To mammi"

Mikewa yayi ya fice.

***

Yana sauke wayan daga kunnenshi yayi shrugging kafadanshi, a ranshi yana furta 'ina ma ruwana'

Ya gyara kwanciyar shi ya fara bacci gajiya tuni ya mance ma da wata Fauza.

Ita kuwa a ɓangarenta bacci take yi kaman gawa, ko Asuba bata iya ta tashi tayi ba, karfe takwas na safe wani irin amai ya tashe ta, da gudu ta nemi bayi ta fara kwararawa cikinta na Juyawa, saida ta gama tsab tana dafe da kanta dake sarawa kaman zae rabe gida biyu, a hankali ta wanke bakinta kan ta mike tsaye tana kallon bayin da take ɗin.

A hankali Tunanin abubuwan da suka faru jiya suka fara dawo mata.

Wani irin tashin hankali ne ya bijiro mata, jarabar masifarta ta sa har bata gani da kyau, bata san sadda ta lalubo Kalmar "innalillahi wainna ilahi rajiun" ta fara ambata ba.

"He drugged me!" Da sauri ta kai idanunta jikinta, tana taɓawa hankalinta in yayi dubu ya tashi.

Da sauri ta fito daidai lokacin shima yake shigowa, kanta yayi yana furta "Babe kin tash...."

Zazzafar Marin da ta sauke mishi hagu da dama ne ya saka magananshi ɗaukewa. Cikin ihu da masifa tace "Zubair or what so ever, who the hell did you think you are da zaka yi drugging ɗina? U even had the audacity na bani kayan maye?"

Yace "am sorry babe! Am so sorry don't be mad I knew I messed up, but listen...."

"Ba zan yi listening ɗin ba, get the he'll out of my way!"

Ta faɗa da karfi tana nufan waje, hannunta ya riƙo ta juya ta mishi wani wawan tura da saida ya faɗi kan kujerar ɗakin, da sauri ta fice tana danne hawayenta..

Tana fita ta nufi room da aka fara kama musu, abun takaici Bacci ta samu suke yi, toilet ta faɗa ta sakarwa kanta shower kan ta fashe da kuka, abu guda ya saura mata a hanyar da ta ɗauko shima yana zuwa, tunda har ta iya ɗanɗana kalar buguwa watarana zata faɗa zina.

Ta fi mintuna talatin kan ta fito, ta samu Sakina na waya, gata nan sir.

"Yayanki Farhan ne yaje office na vice wai yana son Magana dake"

Abun Dukda ya mata banbarakwai kuma gabanta ya faɗi haka ta sa hannu ta karbi wayan ba tare da tace komai ba.

"Ina kwana ya Farhan!"

Yace "kina lafiya?"

Ta amsa da. "Eh"

Ba wani magana suka saba ba, don haka yace "mammi ne ta matsa a zo a ji lafiyarki"

Tace "Allah sarki! Ina lafiya gobe ma zamu dawo, an fasa sati Ɗayan"

Duk kallonta suke, har ta kashe wayan.

Se a sannan ta fitar da ɓacin ranta "am so so disappointed in u sakina nd rahama, kun san bana shan giya don Zubair ya bani na bugu na san ba laifin ku bane amma taya Zaku fara barin shi ya tafi dani na kwana gado ɗaya dashi? Me kuke tunani?"

Rahama tace "kiyi hakuri muma duk sadda ya tafin daken ba a hayyacinmu muke ba bare mu hana shi tafiya dake"

Sakina tace "to menene ma don ya tafi dake ɗin, ai tunda kika zabi wannan hanyar dolen dole watarana kin sha kayan maye, ita ma abunda kike yiwa gudan dole ne ya sameki so just chill ki sake jiki, ki waye pls"

"tir da wayewar zina da shaye shaye, kun kuwa san azaba da fitinar dake cikin waennan abubuwa?"

Kallon juna sakina da rahama suka yi kan suka washe da dariya, sakina tace "lallai ashe ƴar gidan malamai ce"

Tafiya tayi gaban kayan ta ta fara Haɗawa ba tare da tace komai ba.

"Haɗa kayan me kike? Cewar rahama

"gidanmu zan koma."

"Amma ai sati guda muka ce zamu yi"

"ba zan yin ba".

Tunda ta fara basu amsa a haka sun san in suka cigaba be gameta ba su samu gagarumin matsala se suka kyale ta.

Knocking aka yi, Raham taje ta buɗe, samarin guda uku ne, duk suka janye en matansu suka bar ta ita da Zubair a ɗakin.

Gabanta yaje ya durkusa bisa gwiwowinshi, cikin lalama yace "am very sorry! Na san ban kyauta miki ba amma wallahi ba da wani mugun nufi na baki ba, na zata kina sha a lokacin ne kawai ba kiyi niyyar sha ba shiyasa na baki don na tsokane ki, zuciyata zafi take min ina ganinki cikin wannan yanayi Fauxa, na tuba please"

"leave me alone zubair" Ta faɗa calmly Dukda fuskanta a mugun haɗe yake.

Kanshi ya duƙar daidai kafafunta sai digar ruwa taji.

Da sauri ta ɗago, a take yayi deceiving ɗinta da crocodile tear ɗinshi yace "am sorry please Fauza"

Tace "Abunda ya faru ya riga ya faru"

"Kin yafe min?"

Ya tambaya cikin murmushi da yayi mata kyau, kanta kawai ta mayar kan wayanta, hannu ya sa a aljihu ya ciro wani box me kyau daga idanu zaka san ba karamin kuɗi ya ci ba yace "accept this as my apologies dear"

Ɗagowa ta sake yi ta kare mishi kallo, ba laifi Zubair kyakyawa ne, sai de kallo ɗaya zaka mishi ka san crook ne, ga kuɗi ga iskanci.

Hannu ta sa ta karɓa ta buɗe, kasa ɓoye excitment ɗinta tayi tace "isn't it that necklace..?"

Wadda take kallo jiya har yake cewa ze mata kyau.

Murmushi ya saki ganin ta saki ranta, ta mishi godiya.

Zama yayi a gefenta suna hira jefi jefi, duk yadda suka so su hanata tafiya a washegarin tace ita sam gida zata koma.

Duk abunda take chan Kasar zuciyarta bakin ciki ne fal na kayan maye da ta sha, ga sallar asuba gari ya gama wayewa, se istigrafi take yi haka dae Zubair yayi ta lallaɓata yana yaudararta bata yi wani fushi mai nisa da shi ba..

Washegari da safe da kanshi ya kaisu har Airport ya mata sayayya mai yawa ya hada da kuɗi, duk da ya burgeta, sai de fa bata nuna ba.

Sauri sauri ya shigo Airport ɗin don shi ze tuƙa Max Air ɗin zuwa birnin Yola daga Abuja, gashi ya so yayi letti, a cikin jirgin ya haɗu da sauran crew ɗin da kuma wadda ze taimaka mishi suka gaisa, he supposed to be a mazauninshi tunda har an soma shiga amma se ya tsaya daga bakin kofan, waya yake amsawa lokaci lokaci ya kan ɗaga idanunshin nan ya kalli masu shigowa ɗaya bayan ɗaya.

Gudu gudu suka karaso don ana final announcement ne, Sakina ce a gaba sai Rahama kan ita, loggage ɗinsu bai da nauyi so kowacce na riƙe da nata ne a hannu, Sakina ce ta fara wucewa ta mika ticket ɗinta, aka bata na seat number ɗinta ta shige, rahama ma ta shigo tayi hakan sai Fauza ta sanyo kafafunta cikin jirgin....

*Toh Alhamdulillah! Free pages sun kare saura ni daku da kuka biya paid, na san kaunar da kuke yiwa labarin ne ya saka ku nuna wannan soyayya sai dai har yanzu ina kara jaddadawa ba zan san kuna kaunar littafin ba idan har baku comment, ni karan kaina ba zan ji kwarin gwiwar yi muku typing ɗin ba due to squeezing time kawai nake nake yi don ina aiki, bani da enough time na kaina, sannan typing in kun ga kun samu da rana to shikenan amma ka'ida sai dare in shaa Allah zan din ga yi don nafi samun time between magrib, isha. Looking forward for ur comments and love🥰🙏

DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰

Karku sake a baku labari.

🖤Gureenjoh🖤 DƘ

12

Daidai tana sanyo kafa shi kuma yana Juyawa, an tambayeshi wani code da se ya duba paper ɗin don be riƙe ba, har ta gama ta wuce seat ɗinta chan karshe be dawo ba.

"Ke kinga wani haɗaɗɗen captain da ya tafi da ni? Wlh ya haɗu karshen haduwa ina ma zan samu ko phone number ɗinshi ne" Rahama dake kusa da ita ne ke maganan cikin koɗa kyaun wadda take magana a kai da ita bata sani ba.

Tace "ni ban ga wani captaina ba, kuna da matsala ai ku kam" Ta faɗa jin sakina ma ta karɓa tana taya rahama gulman wadda bata gani ba ita kam.

Har suka sauƙa yola basu daina maganan captain ɗin nan ba, Sakina Dan Tsoho hotel tayi don chan zata karasa satin da tace zatayi a gida, yayinda rahama tayi gida don duk iyayenta basa ƙasar, cab ne ya sauke ta kofar gida ta sauka tare da miƙa mishi kudinshi ta Janyo loggage ɗinta tayi ciki.

Harabar gidan nasu tsabtsab ba kowa ta tabbatar yanzun haka suna school tunda kwata kwata karfe goma ne na safe, sashen jadda tayi direct a parlor ta taddata kan sallaya ta idar da walaha tana tasbihi, da gudu ta zo ta faɗa jikinta tayi shiru tana sauke numfashi.

Ɗago fuskanta Jaddah tayi cikin farin cikin ganinta tace "oyoyo oyoyo! Maraba da mutanen Gombe kune da safen nan?"

Kai kawai ta gyaɗa ta sake mayarwa tayi lamo, Jaddah ta ɗago ta gabaɗaya tana kallonta "lafiyan ki kuwa? Ko baki da lafiya ne kike hawaye?"

Hannu ta sa ta share kwallar tare da karya wuya tace a shagwabe "kewarki nayi Jaddah na"

Dariya Jaddah tayi tace "to ba gashi kin dawo ba? Ba shikenan ba? Oya tashi je kiyi wanka ki sauya kaya bari na sa zaliha ta sama miki abunda zaki ci"

Mikewa tayi ta nufi ɗakinta tana cewa "ya yi yaji pls" Tana shiga ta jefar da Akwatin tare da dogon hijab da daga Airport ta sanyo shi zuwa gidan, ta shige toilet ta sakarwa kanta ruwa tana lumshe idanu, se yanzu take jin wani sukuni na rufe ta, lallai ta zalunci ahalinta tayi fatali da tarbiyar gidansu, tunda ta dawo daidai take jin rashin daaɗi a zuciyarta na abunda ta aikata amma fa wani zuciyar na kwaɗaita mata daaɗin shi.

Bayan ta fito tayi shafe shafenta ta janyo tsarabar da Zubair ya Haɗa ta dashi, chocolates ne daban daban se wasu designers perfume guda biyu se, hoodie ash na kamfanin Fendi.

Boyesu tayi a wardrobe ɗinta kan ta zaro riga ƙarami fari da wando navy blue ta saka, wandon a kaurinta ya tsaya ya kuma matse ta ya fitar da duk wani shape ɗinta, gashinta ta taje ta sake shi, tana shirin kwanciya Call na Zubair na shigowa wayanta, da sauri taje kofa ta rufe da key kan ta dawo ta haye gado tare da shigewa bargo ta amsa.

A hankali suke waya tun bata saki jiki ba har ta sake saboda ya iya hira da sanya dariya ga kalamai, ta shagala sossai se jin bugun kofa tayi da sauri ta ce mai tana zuwa ta kashe wayar tare da boyeta cikin Rigan pillow ta dirka taje ta buɗe kofan.

"Jadda tace ki fito ki ci abinci kar kiyi bacci baki ci ba" Cewar zaliha.

Bayan zaliha ta bi suka fito tare, kan kujera ta zauna bayan ta ɗauki abincin daga cikin tray da zaliha ta shirya ta fara ci, Jaddah na bata labarin irin kewar ta da suka yi gidan yayi shiru sossai a kwana biyu da bata nan.

"Ashe ana kewata amma in ina nan kowa ya buɗe baki Fauxa kaza Fauxa kaza!"

Jadda zata yi magana wayanta ya fara ruri ta duba tace "oh kai kuma se yau ka tuna dani" Ko bata faɗa ba Fauxa ta san waye don haka ta maida kanta kan TV Dukda wa'azi ne gwara ta ji da ta ji zancen da zasu yi.

Bata san ma jaddar ta kashe ba saida taji tana cewa "Fauziyya yi sauri gama ki je ki sharewa Yayanku ɗaki ki wanke mai toilet yadda kwana biyu be zon nan ba na tabbatar yayi kura kuma kin san shi da rashin son datti, yace min ya shigo garin gida ne dae ze ɗauki mintuna masu yawa kan ya karaso akwai abunda ze yi"

Haɗe gabas da yamma tayi kaman zata yi kuka tace "Jaddah ina Fatima da ni zan mishi aikin ɗaki yau? Allah ya kyauta wlh kin dae san kap rayuwata ban taɓa taka kafa ɗakin shi ba haka kawai ba zan fara yau ba..."

"Fitsararriya ajiye abincin nan ki wuce kan in Haɗaki da abincin in take" Cewar baba Alhj da yake shirin shigowa sallamar da ze yi ma be yi ba sbd abunda yaji Fauzar na faɗawa Jaddah.

Da sauri ta miƙe tsaye "ban hanaki saka waennan kayan ba?"

Da sauri ta wuce ɗaki tana tura baki seda ta shiga ta fara kunkuni, kaman zatayi kuka haka ta sanya hijab kato har ƙasa ta fito, ta samu baba Alhj na cewa Jaddah

"Mama ni fa ba tsanar ta nayi ba, halayen ta ne bana so, a yadda Fauziyya ta ɗauko rayuwarta wlh bata so gamawa da duniya lafiya ba, tun da ta sanya kafa ta bar sashena bata sake zuwa ko da gaisheni bane wai dani uban ta zatayi gaba? Har Fauziyya ta bar garin nan bata iya zuwa ta min sallama ba se a bakin mamanta nake ji?"

Kanta ƙasa tace "key!"

Jadda tace "Kin san inda nake ajiyewa ai"

Ɗakin Jaddar ta wuce ta ɗauko ta zo ta fice jin Jaddah na bashi hakuri ta kuma tabbatar mishi da ta tura ta ta mishi sallama saide kila zuwan ne bata yi ba, zata mata faɗa Adu'a da lallashi Fauza ke bukata ba faɗa da duka ba.

Ita kam ta wuce abunta, ita fa a yanzu mahaifin ta bata san wani baabi ta saka shi ba, dukda tana son shi sossai da sossai saide wannan kiyayya da yake nuna mata yasa itama take jin babu ruwanta da shi (Subhanallah).

Direct ɗakin Faizan ta wuce, a hankali ta tura kofan bayan ta murda key ɗin, kamshin room freshner da na turarukanshi ne suka bugeta, inda zata iya jinjina mishi kenan tsabta da kamshi, komai tsab tsab yake a ɗakin Sam babu tarkace kaman ba ɗakin namiji ba.

Gado ne a ɗakin saɓanin sauran ɗakunan samarin gidan dake da katifa, daga gaban gadon akwai set na kujeru se TV manne jikin gini, daga gefe akwai ɗan corridor inda drawer ɗinshi yake se kofar toilet, bedding ta fara cirewa ta chilla cikin kwando wankin dake gefen wardrobe ɗinshi tare da ɗaukan tsintsiya ta fara aikin ɗakin, tana yi tana mita da masifa wlh ba don jadda ba da abunda zata mishi a dakin nan se ya kusa kasheta, sannan itama yanzu tana son lafiyar fatarta inda Allah ya taimake shi kenan.

Tsab ta share ɗakin ta gyara tare da kunna burner ta sa turaren wutar da ta gansu kan dressing mirror ɗinshi masu kamshi irin na asalin Maiduguri, ta kunna Ac take ɗakin ya ɗau kamshi, bayi zata shiga se ta cire hijab ɗinta ta ajiye kan cushion kan ta wuce bayin, komai tsabtsab, wankewa tayi tana yi tana masifa, haka dae ta gama ta nufi fita.

Tana sanyo kai ɗakin shima yana sanyowa, a kan junansu idanunsu suka fara faɗawa, wani irin disgusting look na me kike min a ɗaki ya fara watsa mata, ita kuma se ta so rikicewa don ko yaya Faizan na da wani kwarjini da babba ma se ya ji wani iri in ya zuba mai idanun nashi bare mace karama irin ta.

Bata saba gaishe shi ba don haka bazata fara yau ba, wucewa Tayi ta ɗau hijab ɗinta zata sanya, se lokacin ya tuna abunda ya gani a Abuja don haka kai tsaye hannunta ya fara bi da kallo, kan ya maida idanunshi kan body shape ɗinta da ya bayyana sossai a wandon kaman yadda ya bayyana a wanchan kayan da ya gani, daga karshe ya kai kan gashin kanta daidai lokacin ta gama sa hijab tare da nufan kofa.

Kai tsaye yace "Ke!"

Chak ta tsaya, ya fara takowa gabanta hannunshi zube bisa aljihun wandon shi.

"Ke! Sa gwiwowinki a ƙasa"

Da sauri ta kalleshi kaman zata fashe da kuka tace "Amma me na y...."

Ɓas haka ya buge mata baki da sauri ta dafe bakin yace "kin yi abunda nace ko se na tattaka ki?"

Da sauri tayi kneeling ranta duk ya gama ɓaci wani tsanar shi na sake mamayarta.

Shi bai damu da ita ba don haka be damu da ko ta gaishe shi ko bata gaishe shi ba, clearing thoughts ɗinshi kawai yake son yi.. "Me ya kaiki Abuja?"..

Rassss haka gabanta yayi wani irin mummunan faɗuwa, hannayenta suka soma rawa, bata ɗago ba don tana ɗagowa firgicin idanunta tsab ze bayyana rashin gaskiyarta.

"Don't let me repeat myself... Uban me ya kaiki Abuja? Me kika je yi a Transcorp Hilton?"

Gabaɗaya wani irin zafi ne ya rufe ta kaman an sanya ta cikin Kasar tukuban tsire "A...abu...ja kuma?"

Be yi magana ba, tace da sauri "ni babu abunda ya kaini Abuja, ban je Abuja ba"

Duk yadda ya so ya firgita ta ta faɗi gaskiya be samu nasara ba sbd ta kafe kai da fata ita bata je Abuja ba.

Tsaki me karfi ya ja yace "get out of my sight"

Da sauri ta miƙe tayi kofa ya sake cewa. "Ke!"

Chak ta tsaya, yace "this is the last time da zan ga waennan singallin kafafun naki a ɗakina bana son harka da kazamai kin gane ko?"

Kai ta gyaɗa wani irin takaici na zuwar mata wuya, duk Jaddah ce ta ja mata.

Da sauri ta fice tayi sashen Jaddah kaman zata fashe don fushi da tashin hankali. Taya aka yi Ya Faizan ya ganta a Abuja? Allah ka rufa min asiri. Ta furta tana me shiga parlorn Jaddah har zata wuce jadda tace

"Fauziyya" Dawowa tayi tana amsawa ganin jaddar is serious. "Fauziyya kin san girman iyaye ko? Kin kuma san saɓawa iyaye kaman saɓawa mahallicci ne ko? Sannan kina gani irin yadda mahaifanki basu saɓa mini ba meyasa kike shirin daukar wani hanyar saɓa musu alhali ban koyar dake ba?"

Raurau tayi da idanu tace "me nayi kuma Jaddah?"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull