Kenza eBookz

Dingishin kwado Book 3 & 4 complete - Chapter 10

Dingishin kwado Book 3 & 4 complete - Chapter 10

Dingishin kwado Book 3 & 4 complete Chapter 10: Dingishin kwado Book 3 & 4 complete Chapter 10. Tara daidai suka iso gidan, ita da yaran. Hannun Hafcy an…

4,300 words

Tara daidai suka iso gidan, ita da yaran. Hannun Hafcy an nad'e shi da bandage mai yawa. Ga zazzabi ya rufe ta, haka nan ana iya ganin wasu daga shatin kebran da ta sha. Aysha kuwa kuka take yi sosai idanuwanta sun yi luhu luhu. Ganinsu a haka ya yi matuk'ar tayar masa da hankali yayin da zuciyar Bilki take yin lugude sosai. Ba tsoron ya sake ta take yi ba, kawai kada ta wulakanta ta a gabansu ne zulliminta. Ya amsa gaisuwar Haj surayya hankalinsa na kan Hafcy. Ya kasa hakuri ya tashi ya isa inda take ya ji jikinta zafi ainun sannan uban bandejin da yake nade a hannunta ya dungunzuma masa lissafi. A rikice ya ce "Menene, me ya same ki?"

Ta kasa magana illah hawaye da yake sintiri a idanuwanta. Ya juya ga Aysha da take kukan sharb'e yana tambayar me ya same su. Duk sun kasa magana. Yayin da Bilkisu junior da su Amal suka yi tsamo tsamo. Ya kalli Haj Surayya ya ce ". Wai menene, fad'uwa suka yi ko kuwa?" Rai a b'ace a kuma takaice ta ce "Dukan rashin imani aka yi musu babu gaira babu sabar". A zabure ya ce "Duka! Wa ya dake su irin haka?" Da kaudi Laura ta ce ", Anty Maigado ce". Mamaki ya yi matuk'ar kama shi. Ya kalli inda Bilki take zaune ya zuba mata ido tare da son gane da gaske ita ce ta yi hakan ko kuwa sharri za'a k'ulla mata. Take ya gano ita din ce don babu alamun razani ko mamakin da ta shiga akan jawabin Laura. Falon ya yi tsit don kuwa ya rasa ta yadda zai bude baki ya yi magana. Amma ransa ya rub'anya baci. Jin ya yi shiru ya sanya Haj Surayya gyara zama ta ce "Abin da ya sanya na zo takanas shine na ji ba'asin da zata kama manyan y'anmata ta jibga son ranta, ko ita ta haifesu ai ba zata yi musu hakan bare ba d'aya.

Akan me ba za'a k'yalesu su ji da azabar rashin mahaifiyarsu ba? Ban da rabon haihuwa mai kauda wani! Ya za'a yi ace wata mace ce a cikin wannan gidan ba wacce aka yi gwagwarmayar rayuwa da ita ba? Sannan dan rashin adalci sai a mayar da yara marasa galihu a gidan ubansu. To Wallahi ba zamu lamunci duka ba, ko wannan din ma ba zai tafi a banza ba." Baban Bilkisu ya kaurara murya ya ce "Surayya ina ganin ki bar maganar nan a hannuna tunda ina nan nine yafi cancantar na yi hukunci a gidana. Ita matatace su kuma ya'yana ne, dukkansu suna k'arkashin ikona ne dan haka ki bar maganar hannuna zan dauki matakin da ya dace ". Ta hassala don kuwa sai ta ga fishinsa ya ragu sosai. A hassale ta ce "Ni ce nake zaman uwarsu dan haka sai ta fad'a mini dalilin da zata yi musu wannan cin zarafin, ai tasan zafin haihuwa, idan aka kama nata ya'yan aka yi musu irin wannan izayar ai ba yarda zata yi ba". Cikin nutsuwa Bilki ta zuba mata idanuwanta duka biyun ta ce "Dalilin da ya sanya kika zo don ki bi musu kadin zaluncin da na yi musu a matsayinki na k'anwar uwarsu, shine dalilin da ya sanya na gyara musu tarbiyar da ta yi musu k'aranci a matsayina na k'anwar ubansu, idan ban isa dukkansu a matsayin matar tsohonsu ba, to na dakesu ne a matsayina na goggonsu, kuma ina kan bakana ko yanzu suka biyo ni d'akina da nufin su ci mutuncina sai na yi musu dukan da zasu gigice don kuwa gidanmu gidan tarbiya ne dan haka ba zan bari su fita zakka a zuri'armu ba". Bak'inciki ya kama Surayya tamkar ta tashi ta rufe yar iskar yarinyar nan da duka. Yaushe Bilki ta yi bakine? Tana tuna ta da wata sumu sumu da ita. Ta kalli yadda ya yi shiru tamkar ruwa ya cinye shi, uffan ya kasa ce mata duk da yadda ya dinga rawar jikin b'acin rai kafin ya ji itace ta duke su Ta ji tamkar ta ce mata a wanne zumuncin da kuka kai ubansa kotun ne za ki yi ƙafafar zumunta irin haka? Sai dai ta sa ni idan ta fadi hakan shi da ita abin zai juye dan marigayiya Rukayya ta taba fad'a mata har aka yi abin aka gama bai taba buda bakinsa ya fad'a mata ba, bai kuma bata fuskar da suka yi maganar rikicin Ladi farm shi da ita ba, har ta bar duniya. Kan dole ta shanye ta mike ta ce "Dadyn Aysha zan tafi tunda ka ce hukunci na hannunka to dan Allah a kiyaye don ba dan girmanka da mutuncinka ba sai dai a jimu da yarinyar nan a media ko kotu don keta haddin ya isa. Dubi hannun Hafcy. Ace an doki mutum har k'ashinsa ya tsage ai ansan da mugunta a ciki" Ya fesar da iskar b'acin rai ya ce "Allah ya sauwake. Ta yi masa sallama ta tafi Laura ta yi mata rakiya zuwa wajen motarta. Su Aysha suka yi sai da safe suna daga zaune. Ya kalli Bilkisu junior ya ce "Bilkisu ku je ku kwanta". Ta mike Amal da Noor suka bita. Ya kalli Aysha ya ce "Me kuka yi mata ta doke ku?". Aysha ta fashe da kukan bak'in ciki ta ya ya ma zai tambaye su, ita duk zatonta kawai zai yi fad'a na tashin hankali mussaman idan ya ga Hafcy da bandeji da shatin duka. Sai kawai ya tambayi me suka yi? Tabdi jam! Ya tsare gida sosia ya sake maimaita tambayarsa. Cikin nishin ciwo Hafcy ta ba shi labarin Farha ce ta yi mata rashin kunya shine ta bita d'akin Anty Maigado ta doke ta, shine itama ta rufe ta da duka" . Ya juya ga Aysha ya ce "Ke kuma menene sanadin na ki dukan?" Murya a dakushe ta ce"Hafcy na je ceto kada ta kashe ta, ban ankara ba kawai ta zabga minin bulalar da iya k'arfinta har wajen ya fashe ". Ya ce "Idan na fahimta dukkanku a cikin d'akinta ta doke ku, hakane?" Ya yi tambayar hankalinsa yana kan Aysha. Ta kasa amsawa. Ya gyara zama ya ce "Yaune rana ta k'arshe da wata a cikinku zata bi yara d'akin Maigado ta dokesu. Haka nan na haramta muku dukan yaran nan ba Farha kawai ba, dukkan yaran ban yarda ba. Ya zubawa Aysha ido ya ce "Maigado kanwata ce. Ko ban aurenta ba Antinku ce, aurenta da na yi kuma ya sake mayar da ita uwa ta sosai a wajenku. Ban ji dad'in dukan da ta yi muku ba mussaman na Hafcy amma tunda ta ce ta doke kune bisa hujjar ita din kanwata ce to magana ta wuce ba zan iya ce mata komai ba. Dole ku bita, ku girmamata don matata ce.

Duk wacce kuma ta ce zata yi fito na fito da ita to tabbas da ni ta shirya yin tashin hankali ". Dukkansu kuka suke yi tare da hakkake ta doke su a bulus ba wani matakin da zai dauka. Gabad'aya sun gane tsoronta yake ji da gudun zuciyarta. Ba dan haka ba, ba yadda za'a yi a yi musu hakan ya kasa rikicewa ya dauki mummunan mataki. Laura ta yi sakare tana kallonsa tare da jinjina yadda bai d'auki al'amarin da zafi ba. Ta tuna ko momi idan ta daki wani ya dinga yi mata fad'a, yana rarrashin wanda aka doka. Amma yau an yiwa manyan ya'yansa dukan kawo wuka ya kasa motsa k'wanji. Ya kalli Bilki ya ce "A dafa mini shayi a hau mini sama da shi". Ta mike ta yi kicin dan yin abin da ya ce din, ta sa ni kuma sallamarta ya yi. Ta samu k'warin jiki a dalilin bai tsinkata ba, illah girma da ya siya mata. Ta yi imanin zasu shiga taitayinsu. Ta dafa shayin ta fito ta wuce su. Bayan ta tafi ya dinga yi musu nasiha da rarrashi tare kuma da jaddada musu dole su mutuntunta matarsa, bayan haka kuma wannan ne karon k'arshe da za'a taba jikinsu da sunan duka ya yi musu wannan alk'awarin. Sun dan ji dad'in rarrashin da ya yi musu sai dai sun so a gabanta ya yi musu wannan rarrashin tare da alak'awarin ta yi na farko ta yi na k'arshe bayan ya gama cin mutuncinta. Gabad'aya sun dauka zai sake ta tunda uwarsu ma baya kaunar ya ga ta daga musu hannu. Ya raka Hafcy d'akinta ya ce Laura ta kwana da ita. Sannan ya dawo falon ya kashe fitilu da AC ya hau saman Bilki tunda haka siddan ta k'i samansa. Ya same ta daure tawul ta fito daga wanka. Cikin jikinta ya turo sosai. Duk yadda ya tunzura da ita ganin cikinsa a jikinta sai ya tafi da kaso sittin na zafinta da ya ji. Band'aki ya zarce ya yi wanka, ya fito ya ga ta ajiye masa shayi a wajen da ya saba zama ya sha din. Ya saka jallabiya ya fesa body spray ya zauna ya fara shan shayin, yayin da ita tuni ta shirya ta haye gado ta lullube rabin jikinta da duvet. A nutse ya kammala ya kashe fitilar sannan ya tarar da ita. Ya kwanta a bayanta. Tsawon lokaci tana dakon ta ji hannunsa a jikinta amma shiru. Ta ji babu dad'i sai dai ta matse ta k'i yin ko da motsi. Can ta ji ya ce "Maigado". Cikin murya marar amo. "Na'am" ta furta a sanyaye. Ya ce "Zamu yi magana a matsayin yayanki ba mijinki ba". "To" ta fad'a a takaice. "Idan yaran nan sun yi ba daidai ba ki yi kokarin yi musu hukuncin da ba zasu ji ciwo ba. 'Ya'yana ai ya'yanki ne. Sannan bai kamata akan diyarki ki dokesu ba, na sa ni tunda suka zo cikin dakinki sun yi babban laifi, amma tunda akan Farha ne bai kamata ki dau irin wannan hukuncin ba don kuwa zan ji a raina, kin banbanta tsakanin ya'yana da ya'yanki ko na Ansari! Zuciyarta ta harba mussaman da ta ji b'acin ran da yake zuciyarsa ya bayyana har cikin muryarsa.

Gabad'aya jikinta ya mutu. Tsawon lokaci bai ji ta ce komai ba. Ya numfasa ya ce "Yanzu kuma Zan yi magana a matsayin mijinki ba yayanki ba. Kada ki kuma dukansu duk abin da suka yi miki, ki fada mini, nine zan dauki mataki ba ke ba. Ina fatan yaune rana ta k'arshe da za ki d'agawa yaran nan hannu da sunan duka, bana so, bana so, kuma dokar nan har akan d'iyar gold din ta ki Farha! Daga haka ya juya mata baya tare da jan bargo. Ba'a jima ba ta ji saukar numfashinsa tabbacin ya yi barci, hakan da ta ga ni ya tabbatar mata fishi ya yi da ita. Don duk gajiyar da ya kwaso idan ya yi tafiya baya hana ya sauke mata gajiyar sannan ya rungume ta a k'irjinsa su yi barci. Amma yau ba d'aya. Gabad'aya ta ji wani irin al'amari mai kama da nadama ya mamaye ta. Mussaman yadda ya juya mata baya ya yi barcinsa ba tare da ya rungeme ta ba. Wannan abu ya yi mata ciwo. Ta yi tsam da ranta tana nazarin sauyin da ta samu cikin rayuwarta. Ta fara auna banbancin aurenta na farko da wanda take ciki yanzu. A yanzu bata siyan kayan abinci, bata siyan komai ma da kudinta ko da kuwa abin ita kad'ai ya shafa. Bandir bandir din kudi yake ajiye mata masu yawa. Store din gidan duk wani nau'in abinci akwai shii tamkar banza. Kifi da naman rago da na kaji kuwa har yan aikin gidan bai zame musu abin kwadayi ba, haka k'wai. Mafi dad'i da kwanciyar hankali.

A yanzu gangar jikinta bata kewa, bata kwana da ciwon mara, bata kwana tana kukan son a marabci gangar jikinta. A yanzu ana yabon kwalliyarta ana yabon girkinta. Sannan a zahiri yana nuna mata tana da muhimmanci. Wadannan sune abubuwan da ta rasa a gidan aurenta na farko. Ta numfasa tana ayyana a can kishiya ce da ita ba wai ya'yan mijine kishiyoyin ba. A can ba yaron da zai mata sharri ko ya zage ta, haka nan a can ya'yanta sun girma suna sanya ta farinciki babu kuma mai zalintar. Haka nan a can ba a yi mata yarfe ko ba'a. Da ace a can ne ake suburbudurta yadda ake yi mata a nan da ta ce gwara can don duk yadda take hidimar rik'e gidan da aljihunta gara can da masifar ya'yan miji sangartattu irin wadannan. Ta nisa ta sake yin istigifari tare da yiwa Annabi salati ta daga dukkan hannayenta sama ta ce "Ubangiji ka taimake ni akan sha'anin yaran nan, Allah ka kawo mini mafita ka shirye su ka fahimtar da su ba ni da niyyar zaluntarsu, Ubangiji a duba hak'urin da na yi a baya a sassauta mini wannan matsalar. Allah ka mini zabin alheri ka ƙara mini hakuri da juriya. Hawaye ya k'wacewa mata. Ta rufe addu'a da yiwa iyayenta addu'ar samun Rahma. Tana jin k'addarar cikin jikinta ya saka ta auren uban marayu.

Dan Allah waɗanda Baku mini likes a YouTube ba ku daure ku yi, ba saui kun ji ba, dannawa kad'ai za'a yi a fito. Na gode Allah ya saka da alheri. [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: [Sep 18, 2025 at 11:37] *Bojuwa herbs* *Oder your kayan mata for women of class* *Our products are healthy and original*. *Tested and trusted*. *Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta ki*. *Ki zo ki saka order din ciccibin garari ko kazar sababi ki gode mini domin saiwowin da nake amfani da Su na yi imanin ba kowa zai iya zuba kudi ya sarosu ba*. *Duk wadda ta ci ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi* *Just DM for your order @08033773332*.

*DAN ALLAH A MINI LIKES DIN LABARIN NAN A TASHAR LIMAMIN TSAKAR GIDA TA YOUTUBE EPISODE 1-10 KAD'AI ZA'A DANNA MINI DON LABARIN YA KAI GA MATAKIN NASARA*.

Da suka tashi sahur bata wani gane kansa ba. Haka dai ta gabatar tar masa da inibi da kankana hadi da ruwan roba. Ita kuma ta sha kunun gyada. Sassafe ya fice daga d'akinta. Tana zaune har wajen takwas akan sallayarta. Ga mamakinta sai jin tashin motarsa ta yi. Karon farko da ya yi mata hakan tunda ta zo gidansa. Ta jijjiga kai don kuwa a yadda yake son ya'yansa ta dauka ma hukuncin da zai dauka a kanta zai fi haka tsauri. Ta yi shiru tana nazarin yadda jiya ya ƙi yarda Surayya ta taka ta, sannan ya ki yarda ya nuna ta yi laifi a gaban yaran. Hakan ya fahimtar da ita son da yake yi mata ne ya hana shi kuzarin ci mata mutunci bare ya bari a ci mata. Don haka duk abin da zai yi yanzu ba zata ji ciwo ba, tunda ya daura zani a kasuwa. Bai dawo gidan ba sai daf da shan ruwa. Suna idar da salla Isha ta ga sun yi dakunansu, Farha ta matsa kusa da ita ta ce Mahmah ki ba ni kayana Dady ya ce "mu shirya za'a je shopping ". Zuciyarta ta tsinke wato fishin nasa har ya yi tsananin da ba zai mata magana ba?" Ta jijjiga kai tana fad'in tabdi jam a k'asan ranta. Ta yi tamkar ta ce Farha ba zata je ba, sai kuma ta tuna hakan ma laifine. Ta yunk'ura da ƙyar ta hau samanta Farha na biye da ita. Ta dauko mata doguwar rigarta mai kyau ta fesawa rigar turare. Ta watsa mata ruwa sannan ta shirya ta. Ta yi kyau sosai. Ta ce "Mahmah mai zan siyo miki?" Ta murmusa ta ce "Duk abin da kika zabo mini ina so" Ta fita da sauri tana fad'in "Sai mun dawo". Tana zaune a bakin gadonta da yake Farha bata rufo mata kofar d'akin ba. Ta ga wucewarsa zuwa samansa. Ba jimawa ta ga ya sauko ya nufi k'asan da yaran suke. Ta yunk'ura ta bi bayansa. Yana shiga falon itama tana shiga. Ta ga duk yaran sun shirya wani irin k'amshi ya cika falon tunda sun yi amfani da turaruka daban daban. Sosai suka yi kyau. Hafcy ba za'a ce hannunta da ciwo ba ta shirya ta yi fes da ita. Ta ji sha'awar haihuwar y'anmata ya kamata haka nan sai ta ji tausayin anty Rukayya ya dirar mata ta mutu bata ga auren zaratan y'anmatanta ba. Haka Allah ya so. Itama ta ji tausayin al'amarin ina ga ubansu? Da kanta ta fahimci dole ta canja taku akan yaran matuk'ar tana son ta samu kan Babansu. Ya zura hannunsa cikin aljihun rigarsa ya fito da ATM din asusun Zenith. Ya damkawa Hafcy tare da fad'in ki siya komai kike so don ke zasu raka. Ya juya ga Aysha ya bata wani ATM din ya ce "Dukkanku kowacce ta siyo abaya biyu da takalma biyu, sai turare da inner wears. Kada ku wuce hakan". Ta shagwabe fuska don kuwa wanda ya bata takaitattun kudade yake zubawa sabanin na hannun Hafcy na babban asusunsa ne da komai za'a siya ba zai girgiza ba. "Dady amma nima ya kamata ka jingina ni a wanccan ATM din gaskiya". Aysha ta fad'a cikin shagwaba. Ya rausayar da kai ya ce "Yau kam a hannun Hafcy yake ita kad'ai zata rik'e shi ta yi yadda take so. Ban da ita kuwa kowa ya yi hak'uri". Bilki na tsaye tana kallonsu, take ta fahimci ya yiwa Hafcy haka ne don ta huce daga dukan da ta sha. Suka rankaya suka tafi sai lokacin Laura ta fito itama sanye cikin tata Egyptian abaya ta maman asalan da asala. Da wani irin salo ta ce "Sai mun dawo Dady". Wani irin abu mai kama da kishi ya caki Bilki. Yayin da shi kuma ya ce "Ki kula da yaran fa Laura" .

Bai zauna ba sai da ya ji an rufe gate tabbacin sun tafi. Ya zauna yana danna remote ya kamo TRT. Fitacciyar yar jarida Halima Umar Saleh tana bayanin k'alubalen tattalin arziki da nahiyar Africa take fuskanta. Sosai ya nutsu yake saurarra. Ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya. A hankali Bilki ta ja ƙafafuwanta ta isa kujerar da yake zaune mai cin mutum biyu ta zauna daf da shi. Ta saka hannunta ta rik'e nasa a hankali ta ce "Baban Bilkisu how far?" Ba tare da ya kalle ta ba ya ce "Fine". Ta sake jin wani iri da gaske dai fishi yake yi ta dukar masa y'ay'ansa. Ta sake daurewa ta ce "Ka tura yara su siyo abayas din zuwa sallar idi babu ni. To ni da wacce zan je?"

*WANNAN LABARIN NA KUDI NE DUK WACCE TA KARAN BATA BIYA NI HAK'KIN WAHALAR DA NA SHA BA* *ALLAH NE ALKALINA* *WACCE TA SIYA KUMA TA FITAR ALLAH NA GANINTA NA BARTA DA SHI* 2384876855 *SURAYYA IBRAHIM* *ZENITH BANK* *GA MASU SON SAUKE HAK'KI*

Tana rufe baki ya ce "Ki shirya gobe James ya kai ki, Ki siyo". A sanyaye ta ce "James kuma? Ni kai zaka kai ni ". Ta fad'a tana turo baki irin na shagwaba. Ya girgiza kai ya ce "A a ina da ayyukan da zan yi kada ma ki saka rai". Ya fad'a idanuwansa na kan tafkekekiyar allon talabijin din da take girke ƙirar zamani.

Ta ce "Tom shikenan Allah ya kaimu goben ". Bai amsa ba. Ta yunk'ura ta ce "Sai ka hawo". Ba tare da ya kalle ta ba ya ce "Tom". Ta hau samanta, kaitsaye wanka ta shiga ta fito ta tsane jikinta da tawul ta shafa tuararukanta kalakala masu dad'in gaske. Ta sanya wata irin rigar barci mai bayyana komai mai kyaun gaske. Ummu asalan da asala k'arshe ce wajen kawo mana abayoyi da rigunan barci masu tafiya da imanin mazaje. A ranta kuwa ayyanawa take yi duk tsiyarsa yau sai ya huce da fishin da yake yi da ita tun daren jiya. Ta zunduma hijabinta na gunis hijab... Ta shiga kicin dinta na saman nata ta hado masa shayinsa ta shigo masa da shi. Daga nan ta yi sallar isha. Ta Dade tana lazimi akan sallayarta. Sai wajen shadaya saura ta ji motsin dawowarsu. Don haka ta mik'e da hanzari ta sauka ta tarar da shi a inda ta bar shi. Ya dago ya kalle ta don k'amshinta ya cika masa kofofin hancinsa. K'ananun ne suka fara shigowa kowa da ledarsa a hannunsa Amal da Noor da kuma Farha suka nufe ta suna nuna mata abin da suka siyo. Da murmushi ta duba na kowa a cikinsu tare da yaba musu sun iya zabe. Bilkisu ma ta nuna mata. Sababin Aysha da Hafcy da suka nunawa Babansu kawai. Hafcy siyayyar da ta yi tamkar da gayya don kuwa har da zoben gold ta siyo da hadaddun turaruka designers. Ban da dogayen riguna da takalman da ya ce. Ya kalli Laura da ta gefe ya ce "Ke ina na ki kayan?". Ta matsa kusa da shi ta bude ledar ta fito da su ya ga ni. Daga haka ya karbi ATM d'insa ya ce "Oya ku je ku kwanta don ku tashi qiyamul lail". Kowa ta debi kayanta cikin murna suka haye samansu. Suna fad'in "Mun gode Dady". Tuni an kammala labaran TRT. Don haka ya latsa remote ya kashe talabijin din a sanyaye ta ce "Mu ma muje mu kwanta kada mu makara". Bai ce komai ba, ya mike ya rigata tafiya, ta tsaya ya kashe komai sannan ta bishi. Ta tarar ya zauna ya fara shan shayin da ta ajiye masa. Yayin da ta shiga bayi ta yi fitsari ta fito kaitsaye ta haye gado. Sannu a hankali ya gama shan shayinsa ya shiga wanka, ya fito ya shirya, sannan ya kwanta. Mintina goma bata ji ya kai hannunsa ba, ta ji wani irin takaicinsa na kamata. Tsawon lokaci suna kwance kowa na tunanin zuci. Cikinta ya cure ya dunkule waje d'aya sannan sai harbin inda ya dunkule din yake yi sosai. Da azama ta kamo hannunsa na dama ta d'ora akan cikin daidai inda ya dunkule din yake bouncing da k'arfin gaske. Jin yadda cikinta yake yin lugude tamkar ana kokawa a ciki ya sanya jin tausayinta har cikin zuciyarsa ya ratsa shi. Da sauri ya matso gabadaya ya rungumeta ta baya yana fad'in sannu "Maigado, sannu kina jin zafin naushin nan ko?"

A tausashe ta ce "Tun jiya fa har yanzu ban huta ba." Murya na rawa ya ce "To ko asibiti zan kai ki a duba a ga ni, kada ya taba miki kidney ko liver! Ya fad'a da firgici. A shagwabe ta ce "A a da zarar ya samu an zuba masa abin da yake so zai k'yale ni na huta". Murya na rawa ya ce "me yake so to?" Da wata irin murya ta ce "Baku gaisa shekaranjiya, da jiya ba, yau ma ya jika shiru" . Jikinsa na rawa ya hau kai mata kisses masu zafi daga nan kuma suka lula sama jannati. Tsawon lokaci suna dirzar juna kafin su samu nutsuwar da ta dace da su. Da kansa yake mamakin yadda ita bata gajiya da harkar, takaici ya kama shi na yada waninsa ne ya horar da ita da son wannan al'amarin. Matarsa ba mai yawan sha'awa ba ce, bata kuma da juriya a fannin amma Maigado kam ya lura sun yi matching da juna, mai juriya ce duk yadda zai gurje ta bata nuna ta gaji ko ya gundure ta kawai ruwa take feso masa da yake k'ara masa kuzari da gamsuwa. Cikin jikinta bai rage musu komai ba illah k'ara mata zalamarsa da ya yi. Ya dinga jin kishin yadda Sahal ya kwashe shekaru masu yawa yana kwasar ganima da babbar mace irin Bilki alhalin ita din matar manyan maza jarumai ne ba irinsa da yake a lankwashe ba.

Tare suka yi wanka suka kwanta Yana shafa cikin da ya yi luf da alamu suka nuna ya yi barci. Murya ba amo ya ce "Maigado na ji ya baje daga nan". Ta taya shi d'ora nata hannun ta ce "Ya ji ruwan dumi, ya ji lafiyar babansa, ya yi barci". Dariya ta subuce masa ya ce "Maigado bana son sharri fa ke dai ki fad'i gaskiya kina son a jijjiga ki kawai, ba sai kin jinginawa unborn ba" Da murmushi sosai ta ce "Allah Dady shine ga zahiri ka ga ni, yanzu ba ya daina hautsinawa ba?" Ya yi saki gauron numfashi ya ce "Na yarda." Ta karya harshe sosai ta ce "Baban Bilkisu gobe idan an sha ruwa tare zamu fita ka yi askin sallah, nima a wanke mini kaina. Jiya na yi Oder din abayas a wajen Maman asalan da asala mazauniyar Eggypt din nan". Da hanzari ya ce "Tom Allah ya kaimu, zamu je. Amma ban da kin fad'a mini ai har da yaran Sai a siyo musu daga can din". Dad'i ya ratsata waton dama ba wani abin da zai yi? A tausashe ta ce "Yanzu ma tunda bata turo mini ba, sai ta hado da nasun, gobe zan yi magana da ita sai Slsu zabi design din da suke so. Na gode ka ƙara hakuri da ni Allah ya tsare ka daga dukkan sharrin zamani". Dad'i ya ratsa shi ya amsa da fad'in "Ameen Maigadona Allah ya sauke ki lafiya na k'osa na yi tozali da abin da ke cikinki k'warai da gaske. Tun ban gan shi ba ya samu matsayi mai yawa a zuciyata. Ina sonki ina son duk abin da ya shafe ki sarauniyar shaiba! Daga haka ya latsa makunnar wutar. Ya karanta falaki da nasi tare da ayayul kutsiyu ya tofa a hannayensa ya shafe mata jikinta.Wani irin faricinciki ke tunda ga k'asan zuciyarta tare da wani irin shaukin da bata taɓa jinsa akan kowa ba sai akan Baban Bilkisu.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull