Kenza eBookz

Dingishin kwado Book 3 & 4 complete - Chapter 2

Dingishin kwado Book 3 & 4 complete - Chapter 2

Dingishin kwado Book 3 & 4 complete Chapter 2: Dingishin kwado Book 3 & 4 complete Chapter 2. Basma ta karɓe da ce wa" Abubuwa da dama sun faru. Aurenta ya…

3,699 words

Basma ta karɓe da ce wa" Abubuwa da dama sun faru. Aurenta ya mutj sannan kuma tana kwance cikin mawuyacin hali ". "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Tun yaushe?" Ya tambaye ta a sukwane .

A sanyaye Basma ta ce "kwanaki sha shida ke nan". "Subhannallah ya furta a takaice". Ya numfasa ya ce "Yanzu a ina take ?" Tana gidanta na unguwar Alkali". Ya ce "Zan zo in sha Allah. Allah ya bata lafiya." Ta amsa da ameen a sanyaye.

Washegari wajen azahar kamar daga sama sai ga yaya Faruku a gidan Bilki. Ganinsa da Bilki ta yi ya sanya kukan da ya kafe mata tunda ta shigo gidan ya k'wace mata. Ta dinga yinsa tamkar zata hadiye zuciyarta. Gabadaya ya rikice ya rasa kalmar da zai yi amfani da ita wajen yi mata magana. Komai ya tsaya masa cak domin ya ganta cikin mawuyacin halin da duk dakiyar zuciyar mutum sai ta motsa. Da ƙyar ya bude baki ya ce "Bilkisu ki yi hak'uri, ki daina irin wannan kukan! Duk abin da ya samu bawa mukaddarine daga Allah. Bawa kuma ba ya wuce k'addararsa."

Bilki ta tsananta kukanta ainun wanda ya sake jagula zuciayar Yaya Farouku. Ya tausasa harshe ya ce "Fad'a mini damuwarki na magance miki ita Maigado"

Ta kasa ba shi amsa saboda kukan da take yi. Sai da ta numfasa don kanta. Cikin kuka ta ce" Ba ni da matsala, ina kukane saboda jiya aka fad'a maka halin da nake ciki, amma yau ka yi asubanci ka bar komai ka taho tunda ga Abuja don ka ga halin da nake ciki. Ko na rasa komai a duniya na tabbatar ba zan rasa ka ba yaya Farouku".

Karon farko da ta bude baki ta yi maganar da bata shafi Farha ba.

Tausayinta ya yi matuk'ar kama shi, don ya fahimci ta yi amannar ta rasa duk wanda yake da muhimmanci a duniyarta. Dawowarta gidanta alamace na ta gamsu ta rasa dukkan muhimman mutane a duniyarta da zata zauna a kafaɗarsu. Ya sunkuyar da kansa idonsa ya cika da k'wallar alhini. A ransa yake fad'in zumuncinsu bai yi lalacewar da Bilki zata yi zaman kanta a shekarunta ko da kuwa babu Baba Babba a duniya ba.

Ya tausasa harshe ya kalle ta da kulawa sosai ya ce "da yau zan juya don ban yi zaton aurenki ya mutu ba. Amma tunda hakane zan kwana kafin su Alti su shirya miki kayanki tare da ke zan tafi". Ba ja in ja ta ce "Na gode sosai na kuma tabbatar zaka yi mini komai a rayuwata, ban tankwabar da kokarinka ba. Amma bana son na kawo maka hargitsi a gidanka. Ka yi hak'uri duk abin da zaka yi mini, ka yi mini ina da ga nan". Tsawon lokaci suna muhawara amma fir Bilki ta kafe ba zata bar Katsina ta gode da k'ok'arinsa. Alti ta kyafta masa ido fahimtar hakan ya sanya ya yi shiru, yayin da Bilki ta runtse idanuwanta a zuwan barci take yi. Daidai lokacin Alawiyya ta kawo masa abinci. Ya zuba ya ci abinsa suna hira jefi jefi da Alti. Ganin haka ya sanya Bilki jan bargo ta lullube jikinta har fuskarta. Da ya kammala ya yi mata magana amma babu amsa kan dole ya hak'ura ya yi musu sallama. [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Alti ta bi shi k'ofar gida ta ce "Yaya Farouku kada fa ka yi fishi da Mahma gabad'aya fa ba a hayyacinta take ba. Sannan ba zata yarda ta bar Katsina ba, ba don komai ba sai don ya'yanta." Ya girgiza kai tare da fad'in "Ko zata mutu kuwa sai ta bar Katsina. Su mata basa tunanin komai da kowa sai ya'yansu? To idan ya'yan suka mutu suka bar ta sai ta fasa rayuwa ke nan? Ko kuwa idan ita ta mutu ya'yan suma mutuwa zasu yi?" Alti ta yi shiru don bata da ta ce wa akan sha'anin, amma itama kam da za'a samu a raba Bilki da garin da tafi son hakan tunda zullimin da take ciki kada mijinta ya ce ya mayar da ita don bata yiwa Bilki fatan komawa hannun wannan mutumin. Ya ce "mu je na sake yi mata sallama ko zata amsa" Suka shiga har d'akin suka tarar har lokacin tana lullube ruf ya kaurara murya ya ce "Maigado! Ta bude fuskarta sannan ta bude idanuwanta ta zuba su akan fuskarsa. Ya numfasa ya ce "Zan je na bincika asibitin da ya dace Ki dinga ganin likita. Gobe da safe ki shirya da wuri zan zo na d'auke ki da Alti zuwa asibitin". Kai ta daga masa tabbacin ta ji. Ya numfasa ya ce "Za ki je ai ko?" Nan ma sake gyada masa kai ta yi alamun zata je din". Daga hakan ya ce "To na tafi sai goben". Ta d'aga masa hannunta na dama alamun bye bye. Ya fita a matuk'ar sanyaye don ba zai yaudari kansa ba. Bilki ta samu matsala. Har mota Alti ta raka shi tana ta yi masa fatan alheri mai yawa.

Tunda ya tafi yake ta nazarin asibitin da zai kai Bilki. Karshe dai ya ya make shawarar ya kaita babbaan asibitin gwamnati don yafi son kwararren likita ya ganta. Sai yamma ya samu nutsuwa bayan abokinsa da yake pharmacist ne a cikin asibitin ya ba shi tabbacin Su zo karfe tara na safe zai had'asu da likitan da zai duba ta.

Washegari kuwa k'arfe takwas a gidan Bilki ta yi masa. Ya tarar Alti na fama da ita ta kurbi ko ruwan shayi ne amma ta k'i. Haka ya ɗebe Su zuwa asibiti. Basu sha wahala ba suka ga likita. Ya yi dube dubensa tare da tambayoyi wanda sau d'aya Bilkisu ta amsa Duk Alti ke ba shi amsa. Ya kalli Farouku ya ce "Depression ne ya shige ta! Don duk alamomin cutar sun bayyana a tare da ita. Zan d'ora ta akan magani sannan a dinga samar Mata da nutsuwa tare da yi mata abubuwan da zai ɗebe mata kewa tare da sanya nishadi." A sanyaye Yaya Farouku ya ce"Za'a kiyaye Dr. Ya mik'a masa hannu suka yi musabaha, ya yi godiya sannan suka tafi. Mota ya bude musu suka shiga, shi kuma ya wuce ya siyo magungunan sannan ya yiwa abokinsa godiya. Tunda suka hau titi ya tausasa harshe ya dinga yi mata nasiha da muhimmancin yarda da k'addara. Ba zato suka ji ta ce '"Na gode sosai Yaya Faruku. Zuwan da ka yi Katsina don ni ya tabbatar mini ina da sauran gatana". Idanuwansa suka cika da k'walla amma ya sanya jarumta bai bari sun zuba ba. Da suka isa gidan ya ce "Maigado ki daure ki ci abinci don na tabbatar kin ji dad'in zuwana da gaske." Ta yi k'asa da kanta. Ya ce "A zubo miki?" A hankali ta ce "Eh." Da azama Alti ta zubo mata kunun gyada da ta yi mata tun dare ya zuba a flask amma bata sha ba. Ta karba ta kafa kai ta shanye nan da nan ta mik'a mata kofin. Dad'i ya kamasu sosai. Alti ta ce "To ke fa? Rashin cin abincin ma ai jinya ce babba." Ya numfasa ya ce "Bilki ina son na tafi da ke Abuja kuma tare da Alti zamu tafi ta cigaba da kulawa da ke ". Nan da nan idanuwanta suka cika da k'walla ta dinga girgiza kai tabbacin ba zata bi shi ba kenan. Ganin zata sake rikice wa ya sanya ya ce "To Shi ke nan ki zauna a nan din amma ki dinga shan maganinki akan kari. Idan lokacin komawa asibitin ya yi zan dawo da kaina na mayar da ke". Murya ba amo ta ce"Ubangiji ya fini yaba maka Yaya Farouku ". [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Sai ta yi kamar ta fad'awa yaya Farouk batun motar da ya ce zai siya mata, tunda ya saka ta bayar da tata, har Anisa ta k'ira ta yi masa godiya. Sai kuma ta fasa tare da tunanin bai manta ba. Rannan wajen karfe d'ayan dare ta tashi ta yi fitsari, ta fito a band'aki sai ta ga wayarta na haske. Sai da ta kwanta sannan ya dauki wayar ganin wasu lambobi a jere iri d'aya ta gane layine na mussaman. Ta ajiye bata dauka ba. Kafin ta yi tunanin waye mai layin, k'iran ya sake faɗowa wayarta. Ta saka hannu ta amsa tare da kangawa a kunnenta. Murya ba amo ta yi sallama. Ya amsa ba alamun barci a muryarsa. Gabanta ya buga Yaya Asad zai bugo mata waya da tsakar dare?"

Kafin ta samu amsar tambayarta. Ta ji cikin wata irin ya ce "Maigado na tashe ki ko?" A sanyaye ta ce"Ba komai". Ya numfasa ya ce "Ya yanayin aikin ba kya samun matsala ko?" "Ba wata matsala". Ta ba shi amsa a takaice. "Ya ce "Ma sha Allah! Dama zan tambaye ki ne wacce irin mota kiki so , don bana so ki dinga tahowa a taxi ba idan an tashi tunda na ga Abida ke kai ki da safe ko?" "Eh ita ce, amma mun yi magana da Yaya Farouku zai siya mini. Ka bar ta na gode". Ya sake tausasa harshe ya ce "Ga shi kuma na yi niyyar yi miki alheri Maigado. Shike nan sai ki had'a biyu, ko ki ce masa ya siya miki wani abin amma mota kam ni zan siya miki". Abin alheri ya yi mata amma ko kusa bata ji dad'in alherin ba. Don kuwa ta tabbatar akwai abin da zai biyo ba. A takaice ta ce"To na gode, Sai da safe ". Ya sake yin k'asa da muryar ya ce "Ko za ki daure na turo miki hotunan motocin ta what'sapp ki zaba so nake a kawo miki da wuri " Har cikin zuciyarta sai da ji nishin da ya yi kunne a kunnenta. A kidime ta ce "To" tare da katse kiran zuciyarta na bugawa sosai. A fili ta furta "Duk masifarka bana sonka, ba namijin da zan sake sa shi a zuciyata idan ba Yaya Farouku ba." [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Tsabar kidimar da ta shiga ya sanya bata bude what'sapp din ba. Sai da ta ga yana k'iranta ta what'sapp din sannan ta katse ta duba. A zabure ta tashi ta zauna ganin motocin gararin da ya turo mata da zasu lashe millions of naira wai ta zabi wacce take so. Ta murtsuke idanuwanta sosai dan ta sake gasgata ita Bilki ake yiwa tayin ta zabi guda cikin wadannan motocin? Ta tabbatar dai ba gizo ba ne . Sai ta rubuta masa wadannan duk sun yi mini yawa. Waɗanda basu kai wannan ba ta isa. Ya ce "Amma tunda ba rokona kika yi ba, bai kamata na ce ga yadda nake so, ke kuma ki ce yadda kike so za'a yi ba ko?" "Hakane" Ta fad'a a takaice domin ta ji tamkar ya ji haushi ne. "Kawai ki zabi kalar da kike so". Ya fad'a cikin sigar umarni. Maimakon ta yi masa voice irin yadda yake yi sai ta sake rubuta masa "Farar". "Yauwa Maigadona! Na gode miki sosai Allah ya saka da alheri". Tana mamakin jin godiyar da yake yi tamkar ba shine ya kamata ta yi masa godiyar ba. Ta jijjiga kai tana fad'in komai ma kake nufi ba yiwuwa zai yi ba dan ba kunyar wadda zaisa na k'wari kaina. "Wai Maigadona! Ta furta a bayyane. Ta juya tana gyarawa Farha kwanciya. Ta saki tsaki tare da fad'in "Ko ta ina na zama tasa?" K'ira ya sake fadowa wayarta. Ta rasa yadda zata yi haka ta dauka akan dole. "Maigado kin yi barcine?" "A a Farha na gyara ta kwanta kan hannunta ". "Sannu da kokari to" Ta share tamkar bata ji ba. Ya nisa ya ce "Maigado barci kike ji ne?" Murya ba amo ta ce "um" "To bari na k'yale ki haka nan, zamu yi magana da safe. Stay blessed". Yana gama faɗin haka ya kashe wayarsa ta bi wayar da kallo cikin sake mamakin sabbin hallayar da yaya Asad ya tsiro da shi zuwa gare ta, sai take jin wani bambaraƙwai wai namiji da suna Hajara. Ita fa ba yarinya ba ce ta san manufarsa akanta kuma sai dai ya yi haƙuri ba zata taɓa sonsa ba, ba ruwanta da kuɗinsa balle muƙaminsa ya je wani waje ya nemo matar aure dan kuwa ita bai mata ba.

Tunda ga ranar yaya Asad kullum da daddare sai ya kirata yana kashe mata murya, tare da hilatarta. Ita dariya ma yake ba ta ɗauka yake yi ba ta gane manufarsa ba nan ko kallon shi kawai take yi tana dai biye mishi sama sama domin ta ga iya gudun ruwansa, har zuwa ranar da zai furta manufarsa ita kuma a lokacin za ta taka masa burki ta faɗa masa gaskiyan cewa ba ta son shi daga nan sai ya kama kan shi da ita.

Haka Bilki ta cigaba da gudanar da kyakyawan rayuwarta a gidan Baba Babba ba ta da matsalar komai, gata da wani irin tattali ake nuna mata kamar su lashe ta, ihum kawai za ta ce a taso mata ana tambayanta ko tana son wani abu, ta samu kwanciyar hankali ta fara mai da jikinta kamar ba Maigadon da Sahal ya sukurkutawa rayuwa ba. Ta dawo cikin natsuwarta sai da ta ɗan sauya, wasu sabbin daɓi'u ta fito da su na abu kaɗan ne yanzu yake ɓata mata rai nan da nan za ta ruɗe ta fara faɗa daga nan sai kuka saboda cutar da ta yi na depression shi ya sa yanzu kowa ke lallaɓa ta, har Abida duk tsiyataku ta ta daina yi mata, kaffa kaffa take da ita sosai, zama suke yi su yi hira na tsawon lokaci suna dariya har da shewa, sannan su kan raba dare a ɗakunan juna suna hira. Ana cikin haka ne irin zuwa ɗakinta da Abida take yi suna hira, ranar ma sun daɗe suna ta hira har wajen sha biyun dare Yaya Asad yana ta k'iranta a waya ta ƙi ɗauka Allah ya taimake ta, ta sanya wayar a silent da Abida ta lura da ta yi mata ɗan biki. Suna cikin hirar Abida ta zama serious. Tace "Maigado zamu yi magana muhimiya! Amma amanatul amana". Bilki ta fara dariya tana tuna yarintarsu da lokacin da Abida ta ke siyar da jarida, idan kuma ba na kuɗi ba ne sai ta ce Amana ne. "To Abida idan kuma subutar baki yasa na faɗa ma wani fa. A ranar lahira ta ci ni gudan jini ya faɗo?" Suka kwashe da dariya har suna tafawa suna tuna lokacin yarintarsu da abubuwan da suka faru. "Kai ba abin da ya fi ƙuruciya daɗi Abida."; Bilki ta faɗa tana ɗan share ƙwalla daga gefen idanuwanta.

"Kamar jiya ta dawo. Kowa ya fi more lokacinsa a lokacin yarinta."

Bilki ta ce "haka ne kam suna tuno yaya Munnira suna cikin tsananin kewarta. [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Ta fad'a da alamun rashin sukuni. Nan da nan Abida ta bata rai ta ce "Wallahi tunda na shirya sai mun je, ke ba dama a yi miki abin arziki sai kin gwasale mutum?" A sanyaye Bilki ta mik'e ta ce "To jiramu mu shirya". Don tasan tunda Abida ta rantse to idan har bata kubutar da ita daga yin kaffara ba sai sun yi rikici mai tsananin gaske. Ita kuma a yanzu da suka shirya bata son su sake b'atawa da Abida.

Farha ta fara shiryawa cikin wani leshi Mai kyau Wanda aka yi masa kawataccen dinkin da ya sake fito da ainihin kyaunsa. Kai gaskiya telan d take bawa dinkin Amrah ta k'ware wajen iya d'inkunan yara.() Ta fesa mata turare, sannan ta ce ta je falo wajen junior ta jirata. Tunda suka dawo Abuja fir Farha ta ki sakewa da Abida. Duk da ko ina ta yi sai junior ya bita shi kam yana sonta tamkar yadda take son Yaya Farouk. Ita ma cikin Egyptian abaya din ta Maman asalan da asala ta shirya () Ta kalli fatarta a madubi yadda farinta ya sake bayyana ga shi fatarta ta yi taushi ainun. Tunda matar Yaya Asad ta rasa rayuwarta a dalilin canja surar halitta da canja launin fata Bilki ta yi matuk'ar tsorata. Ta tsaya a iya mayukanta na oriflame da Aisha Lame ta zaba mata tun shekaru biyu da suka shud'e. Ta kuma gasgata ingancin products din oriflame. Babban abin da yasa ta likewa Aisha Lame saboda yadda ta nakalci rabe raben fatar dan adam tamkar wata shararriyar likitar fata. Ta shafa hoda ta gogo man lebe a bakinta. Sai ta feshe jikinta da turarenta mai dad'in gaske. Ta same su a falo tare da Momi. Suka yi mata sallama sannan suka fice tare da y'ayansu. A motar Abida suka fice. Bilki a gaba yaran a baya yayin da Abida take tuki. Kaitsaye millenium Park suka je. Suka dan yi chilling da hotuna. Sannan Bilki ta yanka cake tare da taimakon Farha. Wani hoton da Abida ta d'auki Bilki ya yi matuk'ar yin kyau Ta saka shi a status ta yi caption da cewa" Happy Birthday Maigado."

"Haka Mai gadon ta fita?" Yaya Asad ya yi tagging hoton yana tambayar Abida. Sai ya ga kamar kyan da ta yi, kamar kowa a wajen ita yake kallo. Kishi ya ji ya turniƙe shi from no where. Ganinta a status din Abida duk sai ta sukurkuta shi ya ji ba zai iya sake wani dogon jira ba, yana son ya mallaki maigado cikin gaggawa kafin soyayyarta ta yi masa illa. Abida ko da ta ga maganarsa sai ta tura masa emojin dariya. "Haka muka fita dai." Sai ta tura masa wanda suka ɗauka tare da Balki itama abayan ne a jikinta amma na ta ɓaka ce.

"Lalle zan zo na samu Baba Babba. Ya sake muku da yawa." Haka ya ce mata ta bi shi da dariya. Abida tana mamakinsa to menene abun da bai kyautu ba a tare da su? Ranar sai dare suka koma gida washe gari dalleliyar motar ƙirar Toyata da Yaya Asad ya siya mata ta iso gida tunda Abida ta ƙyalla ido ta ga motar nan ta buga tsalle ta ce itama ba ta yarda ba sai an siya mata irinta. "Tab lalle ne ma Yaya Asad ɗin nan, tunda Bilki da dawo gidan nan ya manta da ni. Wallahi nima sai ya siya mini wacce tafi ta Bilki tsada." Ta fad'a tana kumfar bakin ya yi son kai, tana shinshino wani abune a ransa game da Maigado.

Momi ta gaji da mitar Abida ta saka baki da cewa ita ba tana da mota ba, ya siya mata kwanaki baya.

"Ai itama Bilkin tana da mota. In adalci ne ya siya mana gabaɗaya mana." Abida ta fad'a tamkar ta fashe da kuka. Baba Babba ya dinga dariya yana fad'in" Abida rigima." Duk da haka ba ta haƙura ba sai da ta bi Bilki har ɗaki ta tsare ta da tambayoyi.

"Bilki me yasa yaya Asad ya siya miki wannan motar? "To ni ina zan sani, ki kira shi ki tambaye shi mana" Bilki ta bata amsa tana cunno mata baki. Abida ta yi jim kafin ta ce" Baku da gaskiya daga ke har shi. Kuma idan bai siyo mini tawa ba. Billahillazi abin da ya faru a 2022 zai sake maimaituwa a wannan shekarar da muke ciki." "Ya dade bai faru ba Abida ".

Bilki ta bata amsa cikin murya marar amo.

"Haka kika ce ko Maigado? Da ni kike zancen, Allah sai na fasa kwan ai tuni na harbo jirginsa." [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: "Bilki to be sincire magana nake so mu yi dake, amma heart to heart." Abida ta faɗa tana mai kallon Bilki a tsanake itama ganin haka yasa ta gyara zama tana sauraranta da dukkan nutsuwarta. "Bilki ki ji tausayina! Ki duba halin da na ke ciki don Allah ba na ba ki tausayi?" Ta faɗa tana mai nuna kanta muryarta har ya fara karyewa tana shirin ta fara kuka. Abida mai taurin taurin zuciya amma yanzu rayuwa ta sanya duk ta yi laushi.

"Abida ina tausayin ki mana. Amma me ya faru ne?"

Bilki ta faɗa itama cikin damuwa ganin sauyawar Abida lokaci ɗaya.

"Dube ni fa Balki. Magana ta gaskiya ki ji tausayina ki faɗa mini in da Ya Sulaiman yake in kin sani. Ki duba shekaru uku ba kwana uku bane, ba sati uku bane haka nan ba wata uku ba ne, don girman Allah ki faɗa mini in dai kin san inda yake Bilki.". Abida ta faɗa cikin karyewar zuciya. Bilki ta yi tsam tana kallonta cikin wani yanayi na tausayin Abida tare da madaukakin mamakin yadda take cikin alhini da kewar Yaya Sulaiman. A sanyaye ta ce "Wallahi Abida na rantse miki da Allah tun ranar da Yaya Sulaiman ya bar gida ban ƙara ji daga gare shi ba. "

Ta faɗa tana mai kallon Abida da ta yi tsuru kawai tana kallon Bilki. "Ki yarda da ni. Wallahi da na sa ni da zan faɗa miki." "Na yarda da ke Bilki. Shike nan mu bar maganar. Ba sai an ji ba" Kawai sai ta fashe da kuka har da gunji, jikin Bilki ya yi sanyi k'alau itama bata san ta fara hawaye ba sai da ta ji danshi a saman kumatun ta. Tare suka zauna suka sha kukansu, ita Abida tana kukan gararin rashin mijinta ita kuma Bilki tana yin na rashin Yayanta da tausayin Abida. Tasan kuma danne abin take yi a ranta dan kada a fahimci fargar jajin da take ciki. Ranar ma tare suka kwana bayan sun gama kukan su nan Abida ta bingire ta fara barci sai da asuba ta farka.

Haka rayuwa ta cigaba da garawa Bilki ta hak'ura da dukkan zuciyarta mussaman da fahimci ya'yanta basa cikin mawuyacin hali sai kewarta da suke yi. Kullum ne sai sun yi waya sau biyu sau uku. Domin tana ganin yadda take shiga farinciki in ta ga Ya Faruku ko ta ji ana mganarsa har gobe Maigado ba ta daina son Ya Faruku ba, kamar yadda shima tana da tabbacin bai daina son ta ha amma dai a yanzu ne ta kasa gane yanayin shi tun da yadda yi ma Balki wani kulawa ta musamman.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull