Kenza eBookz

Dingishin kwado Book 3 & 4 complete - Chapter 33

Dingishin kwado Book 3 & 4 complete - Chapter 33

Dingishin kwado Book 3 & 4 complete Chapter 33: Dingishin kwado Book 3 & 4 complete Chapter 33. Saddiqa ce kawai ta tafi, mijinta ya zo ya d'auke ta.…

3,944 words

Saddiqa ce kawai ta tafi, mijinta ya zo ya d'auke ta. Salaha Hamida Abida Anisa kwanan zaune suka yi. Hira soaai suka yi mai sanya nishadi. Washegari suna karyawa abida ta d'auke su a motarta suka rankaya gidan Bilki. A farfajiyar gidan suka tarar da oga Asad cikin kakinsa. Yana ganinsu ya juya da sauri ya koma ciki. Da azama Bilki ta gan shi ya dawo. Ya saka hannu ya dauki baba K'arami. Ya kalleta ya ce "Yi maza ki kawo mini na hannunki". Ba sukuni ta ce ", Lafiya kuwa?" Ya ce "Ki dai biyo ni da shi yanzun nan". Ta saba yaro ta bishi. Ya karbe shi ya kwantar da shi kusa da d'anuwansa akan doguwar kujera. Ya kalleta ya ce "Da Hamida da Ansari ba zasu gansu ba sai sun biya kudin ganinsu, tunda Basu komai ba laifina ya hana Su zo su ya ya'yansu.. Na ga su Hamida sun zo shiyasa na dawo dan na boyesu." Save Restricted Content Bot, [Nov 7, 2025 at 19:19] Bilki ta murmusa tare da fad'in "Amma dai an yi mubaya'a a gaban Baba. Kai ka fara aminta tunda kai ka fara d'ora hannunka akan na Baba. " Ya ce "Hakane to d'auke daya mu sauka". Ya saba Baba Babba a kafaɗarsa, ya fara fita, ta bishi a baya tana d'auke da Baba K'arami. Daidai lokacin sun shigo cikin falon. Asad ya bawa Hamida na hannunsa, Bilki kuma ta mik'awa Salaha na hannunta. Hamida ta zubawa yaron ido tana ganin fuskar oga akan fuskar yaron. Haka kawai ta tsinci kanta da jin kunyar Bilki da oga Asad na rashin zuwanta ganin yaran. Amma haka ta matse ta waske. Suka gaishe shi ya amsa sannan ya fice. Daidai lokacin da junior ya fito daga wajen Alti don jiya da suka zo tare da Salaha kin bin ta ya yi saboda Farha da Noor. Ya zubawa Hamida ido. Sai kuma ya kalli Abida ya ce "Ammi kamar Maman Kano". Abida ta ce "Ai kuwa ita ce junior". Gaban Hamida ya yanke ya faɗi da ta ga junior. Ba buk'atar a fad'a mata dan Sulaiman ne don kammaninsu guda. Kunya ta rufar mata fiye da kunyar rashin zuwa ganin twins. Inama lokacin haihuwarsa ta yarda sun taho tare da Bilki? Shi ya santa amma ita bata san shi ba. Murya ba amo ta ce "Zo a ina kasan ni?" Ya je kusa da ita ya ce "Ammi tana nuna mini pics dinki ta ce "Ke ce maman Kano ce kuma sister din Dadyce kuma sister dinta ce". Hamida ta ji tamkar ya doka mata guduma. Ta yi dif ta kasa magana. A ranta kuma fadi take yi wato Abida tana nunawa d'anta su tunda dan yaro irin haka duk ya gane su. Ta kasa cigaba da yi masa magana tsabagen an kashe ta da kunya. Save Restricted Content Bot, [Nov 10, 2025 at 09:41] *Dingishin kwado* *Surayya Dee* 08032773332.

*Bojuwa herbs* *Oder your kayan mata for women of class* *Our products are healthy and original*. *Tested and trusted*. *Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta ki*. *A zo a saka order din ciccibin garari ko kazar sababi don ko zaki gode mini domin saiwowin da nake amfani da Su na yi imanin ba kowa zai iya zuba kudi ya sarosu ba*. *Duk wadda ta ci ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi* *Just DM for your order @08033773332*. Sai kuma ya koma kusa da Abida yana fad'in "Zan biki ammi". Abida ta ce "Tare zamu tafi, Dady ma ya dawo". Ya ce "To yau zamu tafi gidanmu ne?" Ta girgiza kai ta ce "A a". Ya ce "Ya ce fa yana dawowa". Tace "Idan mun je Sai ka tambaye shi". Alti ta shigo musu da kayan motsa baki. Ta zauna ana hira mai dad'i tamkar komai bai faru ba.

Sai yamma Salaha da Abida suka tafi suka bar Hamida zata kwana, gobe Abida zata dawo ta dauke ta. Bayan sun tafi Alti ma ta kauce ta basu guri. Hamida ta ce "Maigado ikon Allah yawa ne da shi. Allah dai ya yi Yaya Asad Sai ya aure ki. Ni dai yanzu na huce da kowa, na yi taubayan nasuha. Ki bi mijinki, nima yanzu zan gyra kurakuran da na rayu akansu. Tunda Allah yasa baba ya yafi kowa to duk wanda Zan faɗawa ya ji to muma mu yafe keta da warakin da suka gwada mana saboda babu idon ubanmu. Yadda ya yafewa uwarmu haka nake son Duk mu yafe masa gorin da ya janyo mana. Maigidan nan ma na yafe masa Har cikin zuciyata. Shiyasa na zo masa kwana." Bilki ta murmusa tare da fad'in "Oh ba ni kika zo wa ba kenan?" Da azama ta ce "A a gunsa na zo, kafin na tafi zan dawo na ki zuwan". Bilki ta sake murmusawa har cikin ranta ta sake samun gamsuwar rikicin gidansu ya k'are. Don bangrensu Hamida da Ansari ne masu kafiyar masifa kuma suna da tasiri a cikinsu. Idan har yadda ta sauko haka Ansari ya sauko ya karbi sulhu to tabbas babu saurin rikici don Abida ta yi rauni. Yaya Usman kuma Baba zai danne shi tunda suma sune kaffafu a nasu b'angaren.

A farfajiyar suka tarar da Sulaiman yana zaune. Ansari ya fita da motarsa. Salaha ta wuce bayan ta ce "Yaya Sule wai ina tsaraba ta ne?" Ya murmusa ya ce "Salaha ai ba haka tsakaninmu mu bar wannan batun kawai.". Ta wuce tana fad'in "To shikenan, an bar shi". Abida da junior suka nufi inda yake. A hankali ta ce "Yaya Dr Baban junior kwana biyu". Ya d'auke kai ya ce "Kwana goma ma". Ta yi dariya kad'an ba ta ce komai ba. Junior ya ísa kusa da shi ya ce "Dady ka dawo, yaushe zamu tafi gidanmu to?" Ya yi masa murmushi ya ce "Ammi zaka tambaya. Ita ta dawo da ku nan, bansan sadda zata mayar da ku gidanmu ba". Zuciyarta ta harba. Murya ba amo ta ce "Ina ne gidan, a wacce unguwa ne?" Ya kalleta tare da mamakin yadda take ganin zai zauna a Abuja. Tsakaninsa da Abuja ya shigo ya yi uzzirin da ya kawo shi ya juya. A yanzu ma don Baba ne kawia ya sanya shi zuwa har da yin kwanaki. Ya d'auke kai ya ce "Junior shiga ka yi alwallah ka zo ka mu tafi masallaci." Ya juyawa kuwa ya tafi yin alawala. Ta ce "yaron nan ya isa a saka shi a makaranta, sa'anin haihuwarsa tuni an saka su, shima ya matsu a saka shi. Don Allah ka cire yaron nan a cikin matsalarmu". Kansa tsaye ya ce "Wai ban ce miki na bar miki shi ba ne?" Gabad'aya ta ji numfashi na neman gagararta zuk'a. Ta jijjiga kai ta ce "Baba ya yafewa kowa dan haka nima za'a iya yafe mini. Baba ya ce wanda ya yi imani da Allah da manzonsa kowa ya huce ya yafewa d'anuwansa ashe kai baka d'auki wannan batun ba?"

Ya ce ban dauka ba tunda suna mini kallon na jingine ki ne saboda na wulakanta baba. Dole su san abin da kika yi don su gane ban raina baba ban kuma wulakanta aure ba". Idonta ya ciko da k'walla. Ta ce "Ka fad'a musu babu damuwa. Amma ka tabbatar ko da ka bar mini junior to dawainiyar da na yi, da wadda na yiwa kaina ban bar maka ba". Save Restricted Content Bot, [Nov 10, 2025 at 09:44] Ya ce "Ke ce kudi suke gabanki, fad'a mini nawa kika kashe?" Ta ce "Bari na d'auko littafin." Ta juya da sauri ya bita da kallon mamaki. Zuciyarta d'aya fa lissafin take yi da gaske. Bata jima ba ta dawo bayan ta ce da junior Dady ya ce ya jira sai ya K'ira shi. Kusa da shi ta zauna ta mik'a masa littafin. Ya karɓa yana bin rubutun daki daki. Ya kalli jimillilar lissafin. Ya dago a kidime ya ce "Wai ke lafiyarki k'alau kuwa?" Ba alamun kaduwa ta ce "lafiya sumul kuwa?" Da mamaki ya ce "Kina nufin kin kashe zunzurutun kud'i har milyan dari uku da sittin Abida?" Da dukkan gaskiyarta ta ce "Wasu ai diyya ne, wasu na kwanakin da na shafe cikin kewa ne, wasu na kuttun da aka dinga kunsa mini ne a inda kake ganin ba a yi maka alfarma an mayar maka da Ni ba, saboda sun haife ni, duk zaman nan na yi ne cikin taka tsantsan da zullimi ga kuma rashin fuska a wajen Baba da Momi saboda sun ba ni umarnin na koma d'akina na taurare.Wasu na yadda bamu da y'ancin yin walwala ne Ni da junior a gidan nan. Wasu na yadda na zama marar daraja ne a gidan yayana. Kuma ba kowa ya janyo mini ba sai kai. Wasu na wahalar raini da tarbiya ne da na yi ni kad'ai ". Ya mike tare da mik'a mata littafin ya ce "To bari sai na fara fashi da makami." Ta karɓa ba tare da ta ce komai ba. Ta juya ta tafi. Shi gabad'aya ma mamakinta ya kashe shi tabbas bai zaci ta kai nan ba duk inda yake zatonya ta kerewa tunaninsa. Yo ko milyan sittin din kai ta ambato mass ai ya yi mamaki bare wannan zunzurutun manyan kuɗaden. To wai me ma zata yi da su ne haka? "Dank'ari". Ya furta a bayyane. Yayin da Abida ta kasa cigaba da jarumta. Kuka take yi sosia a d'akinta. Ta kira Faruku a waya. Cikin kuka ta ce "Yaya Farouku ka yiwa Allah ka shiga tsakanina da Yaya Sulaiman. Ta tsara masa komai da suke tunda suka dawo. Ya rarrashe ta akan ta kara hak'uri. Da iyakacin gaskiyarsa ya ce " Amma ba zan tilasata shi ya zauna da ke akan dole ba. Idan yana sonki zai d'auke ki ne ku tafi. Idan kuma ba ya sonki hakan ba shine k'arshen farinciki ba sai ki yi hak'uri. Tana son ta faɗawa Faruku abin da ta yi masa amma harshenta ya yi mata nauyi.

A daren wannan ranar Faruku ya zo gidan. Kaitsaye d'akin da Sulaiman yake ciki ya nufa. Cikin sa'a shi kad'ai ya tarar da shi Ansari bai dawo ba ya yi nisan kiwo. Da girmamawa Sulaiman ya dinga fad'in "Yaya Faruku sannu da zuwa. Barka da dare, ya ya iyalin?" Ya amsa da walwala sosai tare da zama a gefen gadon. Faruku ya ce "Zamu yi magana. Ka yiwa Allah ka fahimce. Duk runtsi ba zan k'i ka ba. Ba zan bi bayan karya ba". Sulaiman ya ce 'To na kuma gode". Faruk ya ce "Wai ka ce ka bar mata junior?" "Tabbas na fada mata kuma itama ta san ina da hujjar da zan fad'a mata hakan akan yaron" Sulaiman ya fad'a kansa a k'asa. Yaya Faruku ya ce "Yanzu tunda Baba ya yafe mana, ya ce mu yafi juna, ai komai sai ya wuce a tsakaninku mana". A nutse Sulaiman ya ce "Ai saboda matsalata da ita ya sanya ban d'ora dukkan hannuna akan naku ba. Ni yanzu kai da oga nake jira da Usman mu zauna da ita a gaban Baba. Idan aka yi sannan ne zan samu sassauci a zuciyata ". Yaya Faruku ya ce "Ni kam da so nake yi komai ya wuce . Na kashe koma menene dukkanku kowa da inda ya yi kuskure. Dan haka na kashe batun." Nan da nan ya girgiza kai tare da ce wa "A a bai kasu ba gaskiya. Ai tunda a farkon al'amarin aka zuba mata ido ta yi yadda take so, to nafi son a baje maganar a faifai don kowa ya huce gabad'aya. Idan na yadda aka tafi a dukunkune to fa zan rayu ne kuna mini kallon na ci mutunci baba ta hanyar jingine Abida a gabansa. Ni kuma na san ita ta jingine kanta". Yaya Faruku ya zubawa Sulaiman ido yana aiyyana shima kaffaffe ne tabbas. Ya numfasa ya ce "Sulaiman ya kamata ku fuskanci gaskiya fa. Ka janye wannan maganar kasan ba k'aramar magana ba ce idan aka fasata ta ya ya zaka ce ka bar mata yaron da kowa ya ganka ansan kaine ubansa" Save Restricted Content Bot, [Nov 10, 2025 at 09:47] "Yaya na sa ni mana. Ni ban ce mata ba d'ana ba ne ai, na ce na barta mata ne kawai". Faruku ya numfasa ya ce "Yanzu Sulaiman ace sulhun da aka yi jiya bai wanke komai ba?. Tunda ka iso hankalinsa bai kwanta ba, idan ita mace ce bata da hankali sai kuma ka biye ta ku sake tayar masa da hankali gabad'aya?" Yaya Sulaiman ya d'ago idanuwansa ya zubasu kan na yaya Faruku, ya ce "Abida fa har yau din nan bata gama risina ba. Yau ta bani hak'uri gobe ya yi watsi da ni, sannan har ta samu kuzarin ce mini na biyata makudan milyoyin kudi." Faruku ya ce "Ai yarinya ce ka yi hak'uri ". Wani abu ya tokarewa Sulaiman. Abidar ce yarinya?" Ya bude baki zai ce ba wata yarinya Sai ya tuna irin haka ya faɗawa oga Asad akan Bilki. Abida kuwa ai k'anwarta ce. Kan dole ya had'iye raddinsa ya yi shiru. Ya fesar da iskar b'acin rai ya ce "Tsakani fa da Allah an yi mini ba daidai ba Yaya Faruku. Ni fa kawai shiru na yi amma kai ma na jin zafinka akan wannan al'amarin. Me yasa a wanccan lokacin baka motsa mata k'wanjin ta dawo d'akinta ba? Me yasa baka nuna mata girman hakkina a kanta ba? Ban mata komai ba, ita ce ta mini laifuka masu ciwo da wuyar mancewa. Ko ban cin arzikin komai ba a wajenta sai na ci na jini. Amma ta iya tsayawa a gabana tana fad'a min dama ba sona take yi ba, auren cimma manufa ta yi da ni, mafi munin kuskuren da ta yi mini da ta furzar da munana maganganu akan uwata! Ai mami uwartace aurena da ita kuma ya sake kara darajarta a wajen Abida. Amma tsabar tsaurin ido da tink'ahon yadda take so haka ake yi mata, ta zage mini uwa akan idona sannan ta kwashi jiki ta tafi gida, aka kuma bata mafaka, bayan ta sha magani don ta cire ciki bisa hijjar bata son had'a zuri'a da uwata. Sai kuma Allah ya nuna mata iko ta haife shi ". Ganin da ya yi Sulaiman ya kai kololuwar fusata ya sanya ya sanyaya murya ya ce "Da kasan dalilin da yasa aka barta ta zauna din da ka gane ba mafaka muka bata ba, aurenku muka bawa kariya. A lokacin cikinta k'aramine ya zo ya fara kokarin faduwa ga jininta ya hau. Ta kuma ce idan aka tilasta mata ta koma hankali ba zai taba kwanciya ba. Ga likita ya ce tana buk'atar nutsuwar zuciyata saboda cikin jikinta ya zauna sosai , mu kuma muka tsareta tare da bawa cikin kariya. Ga Sulaiman nan tamkar ka yi kaki ne, lamarin mata ba'a biye su yanzun nan sai su yi abin da zasu jefa kansu cikin *Fargar Jaji (Janafty)*. Yanzu tunda kai ne babba kuma namiji ka yi hakuri komai ya wuce dan Allah Sulaiman ka ga dai yadda hankalin Baba ya fara kwanciya dan Allah kada ku tayar masa da hankali. Yaya Sulaiman ya numfasa ya ce "Wai yanzu so ake yi na je na tare ta na bata hak'uri ta dawo ta zauna da ni?" Cikin rarrashi Yaya Faruku ya ce "Maganar zaman da za'a yi zaka janye, sai ka sake daurewa ka d'auke ta zuwa gidanka shike nan maganar ta wuce, ina tabbatar maka Abida ta yi laushi Sulaiman ". Sulaiman ya ce "ka yi hakuri amma ba zan dauke ta da kaina na mayar da ita ba. Yadda ta fito da kanta, da kanta zata koma matuk'ar tana son zama da ni". Da hanzari Yaya Faruku ya ce "To ina ne gidan da zaku zauna ni sai na kaita da kaina inace shike nan?" Murya ba amo ya ce "Inda ta baro, Funtua zata zauna! Yaya Faruku ya yi shiru yana jin matuk'ar basu bi Sulaiman a hankali ba rikici ne zai sake barkewa a tsakaninsu bayan wanda aka yi akan Ladi farm. Ya riga ya gane Sulaiman bai fahimci da kyakkwar manufa suka bari Abida ta zauna a gida ba. Don haka zai iya yin komai tunda yana ganin basu yi masa kara ba. Tunda y'anuwansa ma sun kalubalance su da rashin yi masa adalci. Ya nisa ya ce "Aikinta fa Sulaiman? Inace kai ma kana shiga specialist Hospital na nan Abuja". Ya murmusa ya ce "Ko ina zan iya aiki ai Yaya Faruku ba ni da matsala akan hakan". Yaya Faruku ya ce "To ku zauna a gidana na Gwarinfa kafin zuwa lokacin da zaku koma Funtua. Ai yanzu gyaran da yake gidan ba kad'an bane tunda ya dade a rufe". Save Restricted Content Bot, [Nov 10, 2025 at 09:50] Gaskiya fa Yaya Funtua zata tafi, ni na riga na saka an gyara gidan gabad'aya dan haka ta koma can ta zauna, da amarya zan zauna a nan. "Sulaiman! Yaya Faruku ya k'ira shi da muryar gargadi. Bai amsa ba amma ya sha mur. Ya ce "So kake Baba ya sake rafkewa ko? Idan an bata maka ba zaka yi hakuri ba? Hankalin mace da na namiji ba daya bane ai." Ya za'a yi da sha'anin mata dole sai hakuri. " Sualiman da sauri ya ce "Yaya Faruku idan hakurin ba zai zama akwai wulakanci a cikinsa ko cutarwa ba. Amma Wallahi ta daina yaudarar kanta da ce wa zan nemi sulhu da ita." Da azama Yaya Faruku din shi ma ya ce "Dama tunda ita ta fara tsokanar ai ba zaka bata hak'uri ba. Amma idan ta k'ira wayarka ko ta yi maka message ka dinga amsawa. Tabbas ta yi laifi, Kuma ko Ni nan Sai na Mata ba dad'i, ka yi hak'uri, amma kaima hukuncin da ka d'auka ya yi tsair6da yawa shine ya bani kuzarin sake baka hak'uri akan ka bata dama ta gyara kuskuren ta." Ya ce "Gaskiya ka yi hak'uri mu zauna da ni da ita da ku. Idan ba haka ba zuciyoyi ba zasu huce ba". Faruku ya rasa yadda zai yi da shi. Ya ce "To ai shike nan ku da Babanku ni kam na gaji gaskiya! Ya sassauta ya ce "Dan Allah yaya Faruku ka fahimce ni, ina son a huce ne gabad'aya." Ya ce "Na fahimce ka da dukkan zuciyata." Washegari sassafe Sulaiman ya kai Ansari airport ya tafi Maiduguri. An rabu lafiya da shi, ya kuma karbu sulhu da yafiya da dukkan zuciyarsa. Save Restricted Content Bot, [Nov 11, 2025 at 13:19] *Dingishin kwado* *Surayya Dee* 08032773332.

*Bojuwa herbs* *Oder your kayan mata for women of class* *Our products are healthy and original*. *Tested and trusted*. *Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta ki*. *A zo a saka order din ciccibin garari ko kazar sababi don ko zaki gode mini domin saiwowin da nake amfani da Su na yi imanin ba kowa zai iya zuba kudi ya sarosu ba*. *Duk wadda ta ci ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi* *Just DM for your order @08033773332*.

Karfe sha d'ayan safiya duk suna hallare gaban Baba. Oga Asad, Yaya Faruku, Usman, Sulaiman da Abida. Cikin nutsuwa Sulaiman ya rattabo irin halin tsaka mai wuyar da ya shiga a lokacin ake danbarwar Ladi farm. Zullimi da rud'anin da ya shiga bai samu sassauci da rarrashi daga Abida ba. Haka ya zama desperate gida da waje ba nutsuwa a tare da shi. Duk irin rarrashi da kwantar da kan da ya dinga yi mata bai saka ta samar masa da nutsuwar da ta dace da halin da yake ciki ba. Zaman wurinsu ma ta daina yi barci zai kawo ta shima yana shiga dakinta zata rufe k'ofar. Ana idar da sallar asuba zata sake ficewa. Duk ya yi hak'uri akan hakan tunda yasan MAMI ta yi ba daidai ba. Ya dago kansa ya ce "Sai kuma ta kasa gane irin hak'uri da taka tsantsan din da nake yi don kada komai ya sake k'wacewa. Ta tsaya a gabana ta zagi MAMI irin zagin tsamar nama da babu tarbiya da mutunci a cikinsa. Ganin idona na ga maganin lalata ciki a bakinta wanda hakan ya sanya jini ya balle mata. Duk izgilin da ta yi mini na zagin uwata hakan na kwashe ta zuwa asibiti da kaina duk da zuciyata na ingiza ni na mata dukan kawo wuka sai ta yi jinyar da hujjar. Amma saboda kai Baba sai ban yi hakan ba. Duk hidimar asibitin ni na yi alhalin nasan ita ta janyo ciwon da kanta. A hakan na daure nake ta zarya. Sai kuma na ji daga asibiti ta taho Abuja. Zuciyata daya na gamsu akan nasan zaku korota tunda ban sake ta ba, ban yi mata komai ba. Sai kawai na ga an barta, a yiwa Allah a duba wannan batun ya ya zan ji ne a zuciyata?Dole na zaci dukkanku da kuke da iko da ita kun gamsu na yi laifin da ya cancanci na rasa y'anci akan aurena. Shiyasa ban zo ba. Zagin mami kuma da ta yi ban sake ta ba. Billahillazi lah illah ha illah huwa nauyinka na ji Baba. Don kuwa babu macen da zata yi mini hakan a duniya na cigaba da zama da ita". Hawaye ya k'wace masa. Daga oga Asad har Faruku jikin kowa ya yi sanyin. Hatta Usman da yake da ra'ayi irin nata jikinsa ya mutu tub'us. Usman ya fara cewa "Lallai ta yi ƙaton laifin da yake da ciwon gaske ". Baba kuwa ya ce "A a lallai Abida ta kerewa tunanina Ai ba matar zama ba ce. Ni kaina ba zan zauna da mai zagin iyaye ba don mace ta gari ba zata yi wannan jahilcin ba". Abida ta rushe da kukan tashin hankali. Cikin kuka ta ce "A yiwa Allah a yi mini hak'uri a kuma fahimce ni. Ba kowacce mace ce zata iya tsallake halin da nake ciki ba. Ace uwar miji da mijin da y'anuwansa sun dunkule suna k'alubalantar uban mace da zalunci har a maka shi a kotu? Dan Allah a duba da kyau. Amma na janye kalamaina, na bada hak'uri kuma ni bansan ma sadda na fad'a ba. Wallahi jinnul Ashiq ne da suka hana ni aure suke shafata lokaci zuwa lokaci." Tausayinta ya kama oga Asad yasan jiki ta ji shiyasa ta jinginawa jinnu alhakin laifin da ta yi. Faruku ya ce "Ai kad'an ma kike ganin tunda ke jununki kaifin harshe". Baba ya ce "Yanzu na gane kana da hujjojinka masu k'arfi. Kuma na gode da ka ga girmama ni amma fa ka sani kana da dama da y'anci a cikin aurenka. Ni dai ka wanku tas a zuciyata. Idan kana sonta a haka zaka iya danne laifinta ka yi mata adalci to hakan nake so. Idan ba zaka iya ba to kada ka yi mata rokon da zaka zalunci kanka Allah ya kama ka da laifinta to ka sahale mata kuma ba zan ga laifinka ba". Abida ta fashe da kuka tana fad'in "A duba nadamata Baba. A duba shekarun da na shafe a rataye alhalin Annabi ya ja kunnen maza akan kada su bar mata a rataye su ba sakakku ba, su ba masu aure ba. A duba zaman goyon ciki da raino da na yi, a duba bak'incikin zura mini ido da kuka yi kai da momi. Gaskiya Baba ka yi mini adalci ". Save Restricted Content Bot, [Nov 11, 2025 at 13:22] Usman ya mike ya yi kanta yana fad'in Baban kike ce wa ya yi miki adalci? You are very stupid!

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull