Duba min baya fakon biri - Chapter 30
Duba min baya fakon biri Chapter 30: Duba min baya fakon biri Chapter 30. Zaune take a falon tana katatun littafin da take kai a Islamiyansu yayi sallama…
3,344 words
Zaune take a falon tana katatun littafin da take kai a Islamiyansu yayi sallama ya shigo falon nata ta dago daga karatun tana amsa mashi. Kallo daya tayi mai ta fahinci akwai matsala koda bai fadi ba tasan akwai matsala a wani bangare hakan yasa ta rufe littafin da take duba din ta fuskanceshi. Zaune yakai har tsawon wani dan lokaci kafin ya dago yace zancen hafiz ne dai yake damuna don ban fahinci me yake nufi da yar mutanen dake gidanshi zaune ba da muka tauye. Dazun ina shago ta bugo min tana fada min cewa hutunsu ya kare tana son ta koma karatun ta watau hakan ke nan yana nufin bai waya da ita tun tafiyansa ? Dan murmushi mum ta sake a fuskanta kafin tace ai kaima ka sani Alh ban tsamanin cewa hafiz nada number mama a wayarshi. Kuma hafiz bai yarda ya karbi auren mama ba kamar yadda kake zaton ka shawo kansa daga baya har ya yarda ya amince nina sani saidai sanin baida amfani a gareni . Tunda banda power din da zan dauki mataki alokacin da nasan haka din wayar yarinyar nan samira dake hannun mama din a cikinsa mukaga irin yankar kaunar da yai mata ranan da kuka kaita kuka fita. Mikewa ta tashi tayi ta dauko wayanta data tura ta kunna mashi yayi shiru yana sauraren rashin mutuncin da yake shuka min a lokacin har lokacin da aka fara nocking kofa ya fita da dan hiran mu dasu Anty da suka shigo take fadin har yanzu kukan rabuwa da mum nakeyi ne ? Nisawa daddy yayi kafin ya dago kai ya kallo mum da idanuwansa da sukai ja jajir dasu yace lalai yaron nan yakai dan banza yana ganin banda sauran amfani a garesa yanzu ko ? Tunda nagama masa wahala ya girma yana ganin yanzu kafansa shi sun kama kasa sakaiyan da zai mun ke nan kafin ta kiraka ni ta fara kira ai mum ta katse mashi magana don luran da tayi ya fara fita hankalinshi lokacin. Cikin hikima ta fara canza zancen da fadin tana kirana ta fada min wai tana jin tsoron fadama shine nace dole saika sani ai wanan yasa ta kiraka. Alhamdullahi ai tunda ita yarinyar bata bijire muna ba har yanzu tasan a karkashin iyayye take tana kuma biyayya ka kyaleshi kawai shida kansa zaizo ya gane cewa yayi kuskure abinda yakeyi a yanzu. Yin shirun ka shi zaidaga masu hankali zasu shiga tashin hankali don basu san me shirun ka yake nufi dasu ba amma idan kai magana abinda suke nema ke nan dama rayuka sukai ga baci a yanzu ka kyalesu kawai ka saka masu ido zaifi. Illa iyaka ita mama mu saka ido akan al,amuranta a bata kula yadda ya dace ta yadda damuwan hakan bazai dameta ba ni shawarana ke nan . Ya shafo kai yana fadin neman maganane nina sani kuma da hadin bakin uwarsa yake hakan duk abinda hafiz keyi malka tana da labari don hakan shawaran ki ya kawo min mafita a cikin zancen nan yanzu ya mike ya fito daga dakin nata . Ranan monday da safe bayan na shirya naji horn direban dake kaimu school ne yazo daukata shiya kaini makaranta a ranan da aka tashi kuma yazo ya daukeni . Anty nafisa bata san da cewa nashigo ba don bamu hadu ba ban kuma nemeta ba don banba office dinta ba har na dawo gida don a yanzu ko waya bamayi da ita tunda aka kawoni gidan dan uwanta halakar mu ya danyi rauni tsakanin mu. Bansan dalilin hakan ba amma tun lokacin buki ta fito da wasu abubuwa gareni mum tace a shareta kawai nikan badon mum ba gaskiya da bansan ya rayuwana zai kasance ba a cikinsu. Hankalina kwance nake karatuna ban sakawa zuciyana komai ba inci mai kyau insha maikyau ba abinda ya dameni saboda kurciya har mantawa nake da nayi aure a lokacin don wauta. Sai wata ranane malam isah ya daukoni zamu dawo gida muka hade da ita a daidai get tabi motan da kallo don sanin motar gidansuce wanan . Sai lokacin ta ganni ciki zaune a baya malam Isah yana jana zai mayar dani gida mamakine ya rufeta a lokacin tabimu da kallo har muka bace mata. Malam isah din ke fadin ga hjy Nafisa can ko mu tsaya ne nace a,a mu wuce kawai illa iyaka ya danyi mata horn ta mayar masa itama muka tafi. Mamaki tayi sosai har takai inda zata kafin ta dauki waya ta kira mummy tana tambaya dama ashe yarinyat nan tana zuwa makarantane mummy yanzu naga malam isah ya daukota zai mayar da ita gida. Wace yarinya ke nan mummy ta sake tambayanta tace Zeey mana ta nan gidan matar hafiz ta fada kai tsaye sai uwar tace kika ganta ina tace school mana mummy na dauka aitamooiu n dainane yanzu don auren nan. Kima daina zancen nan don Allah bari nakira hafiz din inji sai yar ta katseta da fadin to meye mummy idan taje school tunda dama tana karatunta ba sai a barta tayi ta zuwa ba. Wai meyasa ke baki gane abinda ake nufine baby wanan fa anyi hakanne da wani manufa sai yanzu nake gane nufin dan iskan yaron nan me dadin bakin tsiya da har ya bada shawara kan taje karatu zaifi. Watau ita tayi karatu su mairo ko suna gida zaune wai suna aure ba damuwansu bane su kinga abinda nake sha fada maki ke nan baby amma kin kasa fahintana dake ke nan suke son jayayya a gidan nan tunda hjy kubrah bata da diya mace sai wanan yarinyar. Haba mummy ni kuma Zainab fa har yaushe zainab zata iya kaini balle su tsaya kwatantawa dani don Allah sai dai idan suna da wata manufa dai ta daban akan karatun nata dai. Shiko hafiz din data kirashi bai dauki waya a lokacin ba sai data masa da dare ya dauki wayan suka gaisa ta fara fadin kai ka umurci yarinyar nan da tafita zuwa school ? Wace yarinya ke nan mum ya tambaya tace matarka mana zeey dazun baby ke fada min ta ganta malam isah driver ya daukota daga makaranta. Mummy akan zancen yarinyar nan kika kirani don Allah kibar kirana kanta mummy don banson ai min zancen wanan yar iska don nabarwa daddy ita shida ya matsa sai anyi auren nan to anyi din ban bashi kunya ba sai su zauna da ita din mugani. Wai dama har yanzu tana gidan a matsayinane kota koma gida tace kai hafiz ka natsu ka saurareni kaji me zan fada maka akanta. Don na rarasheka ka yarda ka aureta hakan ba yana nufin ka fita zancenta yadda kayi din nan gaba daya bane don akan zancen nan na tabbatar da Alh zai iya saba muna gaba dayan mu daku. Koma yayane akala ka dan kula da ita a matsayin matarka kana dan zuwa baka share haka ba har ana neman kwasan wata baka leko ba me hakan da kayi yake nufi ke nan ? Gaskiya mummy i can't ban taba jin wani feeling akan yarinyar nan ba kwata kwata wallahi mum banko son in ganta a rayuwana wallahi kai kadakata da wanan shirmen ka saurareni kaji me zan fada ma. Nan dai ta koma lurar dashi abinda ya dace yayi har ya fahinceta don a yanzu ta fahinci Daddy ya juya mata baya itama duk da bata san dalilin hakan ba saidai ta fahinci akan zancen dan natane da yake ganin bakinsu daya ya kawo sauyin nan tsakaninsu. Don yanzu iyakan daddy da ita ina kwana ya amsa mata a daure ko kuma inta kawo abinci daga part dinta zai zauna ya danci wani lokacin wani lokacin kuma ko kallon abincin baiyi zai barshi a wajen. Bata saba da irin wanan rayuwan ba sai abin yazamo mata sabon ak,amari don hakane tayi shawaran cewa dole sai tasa dan nata ya natsu kafin ta fahinci inda Alh ya dosa da ita. Bawai tana nufin ya zauna dani dole bane a,a suyi nasu irin takon suma su nunawa Alh din ai suna tare dashi da hakane zata fahinci me yake nufi da canzawabshi. Duk da dai bai sake mata magana ba akan dan nata amma tasan shirun shi a yanzuma din maganane bawai ya kyale zancen bane akan a tafi a haka hakan na nufin shima da nasa shirin akansu ke nan. Anty nafisa bata dadara ba saida ta dauki waya ta kirani bayan sjn gama waya da mummy tana fadin sis ashe kina shigowa school shine baki taba nemana ba sai yau dana ganku din nan ? Ina zuwa anty iyakaya department din mune kada nayi wani laifi kuma ace ina yawo donshine ban zuwa ko ina idan nashigo amma kiyi hakkuri don Allah na fada a karshe. A,a aiba komai nafahince ki amma ki sani dake da hafiz din dukkan ku kanne nane don kinzo waje na bashi zaisa a jefiki da wani zargi ba sai dai idan dama kina da wani manufa akaina. Na danyi murmushi na sake fadin anty kiyi hakkuri ba haka bane na fada maki gaskiya kawai don ki fahinceni bayaga school a yanzu babu inda nake zuwa kuma. Gidan na bude nashiga ina sauke ajiyan zuciya tare da zama ina bin ko ina na gidan da kallo kafin in sauke ajiyan zuciya ina lumshe idona na fada bayan kujera na fara tunane. Wayana dake aje gefena dana aje yake dan haske alaman kira yana shigo min a lokacin na dauka ina kallo number kasar wajece Canada na gani a rubuce. Na sake maimaita sunan garin har kiran ya tsunke ban daga ba don ina tsoro banda kowa dake kasan waje da zai kirani nayi tunane a zuciyana lokaci guda. Saiga kiran ya kara shigowa again nayi karfin hali na dauka na kara a kunnena ba tare da nayi magana ba sai naji muryanshi yana fadin. Keda wullakanci ana kiran waya kina share mutane me kike daukan kankine wai ko kin dauka kina da wani matsayin da za,a kirakine wai ? Muryanshine ba tare da sallama ba yatareni da fadin hakan daga daukan wayana kafin ya koma fadin ke ina kika fita kikaje ba tare da sanina ba ? Wai waye hakane don Allah kamar ba musulmi ba daga daukan waya sai bakar magana kamar mara hankali to wrong number naja tsuki na kashe waya kai tsaye. Ina jin yana fadin kika kuskura kika kashe min waya wallahi dip na kashe wayan ga baki daya ina jan tsuki nace wawa dab giya kawai kafin in koma fadin. Lalai mum tayi gaskiya da takece min na kula da Anty Nafisa don yanzu a matsayin yar miji take a gurina watau dan ganin nan da tayi min har ta buga masa waya kai lalai mutum abin tsorone duniya. Wasu zafafan hawayene suka zo min lokaci guda suna sintiri a fuskana har sai yaushe wanan zai fahinci iyayyenmune na tambayi kaina ina runtse idanuwana a cikin takaici. Wanan kila ya kora tsiyar nasane yake son ya karanto min hauka daga kawai fita zuwa school inba abin dan giya ba zaka kirani kana zagina. Na dade zaune a wajen kafin na mike zuwa dakina na sauya kayan jikina zuwa na shan iskan gida banso yin girki ba amma dole nayi saboda maigadina tun lokacin da yace min shi bakone daga kauye yazo neman abinci kano ya samu gadi nake tausayinsa. Dadina guda shine Allah baiyini da yawan magana ba don haka ban fadawa kowa abinda ya faru ba balle a ban shawaran na dakata da karatuna dana kwallafawa rai. Don hakane washegari na shirya na nufi school duk da zancen ya tsaya min a raina ni kadai nake hade abina tunda banda abokin shawara a lokacin. Ina nan zaune da yake ina fashin sallah naji sallama a gefena na dago ina amsawa watace tsaye a gefena take fadin ko zan iya zama ni bakuwace a department din nan bansan kowa ba asalima dai ni ba yar gari bace transfer akai muna muka dawo kano daga Lagos. Zaki iya zama mana na fada ina kawar da kaina gefe daya takai zaune tana bissimillah sai hakan ya burgeni amma ban dago na kara kallonta ba duk da kamshinta dake shiga hancina a wajen. Itama din karatunta takeyi hankali kwance har lecturan da zai dauke mu ya shigo ajin muka mayar da hankalin mu ga abinda yake koya muna din. Ya dade kafin ya fita lokacin ta juyo ta kalleni tana fadin gaskiya ban fahinceshi sosai ba da zan samu karin bayani zanso ni dai banyi magana ba sai kokarin bin abinda ya koya muna nakeyi. Tana kokarin jana da hira duk da basar da ita din da nayi a lokacin bai hana taci gaba da magana ba dani sai amsa da nake bata a takaice take fadin in taso muje wajen motarta mu karya don lokacin break yayi. Sai lokacin na dan dago ina fadin nagode ban tare da yunwa saida na karya na fito ke dai yar uwa naga kamar baki natsu dani ba niko kaf ajin nan dake hankalina ya kwanta. Nagode na fada tace kinsan komai gamon jinine na hango natsuwa a tare dakene sunana hauwa Garba daga Niger state muke aiki ya kawo mu garin nan duk da mijina uwarshi yar garin nan ne ita. Sai lokacin nayi dan murmushi a fuskana ina dagowa nace surname din mu daya dake ashe nima zainab Garba katsina nake bearing a takarduna. Tace shike nan mun zama sisters dake ashe shine mafarin sakewana da wanan bakuwar da yanzu take dan sakani magana koda ban son ba kuwa. Don irin mutanen nan ne masu son asani nan halinmu yasha bamban da ita amma ba laifi tana da son naci ga karatu ga yadda na fahinta idan an koyar bata gane ba zatayi ta nacin da sai ta gane kome ake nufi wanda nima ina kara fahinta ga hakan.
ZAINAB IDRIS MAKAWA [3/1, 07:51] +234 706 511 1949: *_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
PAGE 13
Waya ta sameshi yana yi. Dogon wando ne fari qal a jikinsa da singlet fara itama,sai ya ajjiye wayar yana duban tanja data tsaya nesa da falon
"Mainasara bibi ce take kira"
"d'accord" ya amsa can qasa da muryarsa me sanyi.
Ko daya baiyi niyyan shiga sassan bibi din ba,ya sanyama ransa ma sai tayi cigiyarsa kafin ta sake ganinsa,saboda yana ganin cewa suna da tagomashi wajen lalacewar ginin da ya fara yiwa rayuwar sultana. Saidai kuma bibi din ta wuce ta kirashi yaqi zuwa,don haka ya sauke qafafunshi dake saman table qasa yana ajjiye wayarsa saman kujerar ya wuce zuwa bedroom dinsa.
Kaftan abaya budaddiya ya zura navy blue,kalar data fidda sigar kyawunsa matuqa,haskensa ya fito sosai,ainihin zallar hasken cikakken ba'abzine.
Kamar yadda yake dabi'arsa hannayensa zube a aljihun kaftan abaya din yana qissima abubuwa da dama cikin ranshi. Iskar bayan azahar tana kadawa kadan kadan me cakude da sanyi maras tasiri. Ire iren wannan yanayin suna masa dadi sosai kasancewarsa mutum ras son zafi ko kadan. Hatta da sutura ba kowacce yake sanyawa ba saboda baison abinda zai takura jikinsa.
Da nutsatstiyar sallamarsa ya shiga parlor din bibi. Ta amsa masa tana karantar nazarinsa sanda yake basarwa ba tare daya kalli fuskarta ba,daya daga cikin alamun fushinsa kenan.
"Samu waje ka zauna" bibi ta bashi umarni kai tsaye,ita dinma yau fuskarta ba'a sake take kamar yadda ta saba ba.
Kaman bazai zauna din ba sai kuma ya matsa sofa din gefanta ya zauna a kai bayan dukka wadanda ke zirga zirga a falon sun kau,don basu waje.
"Aliyyu" bibi ta kirashi da sunansa na asali kai tsaye. Sexy eyes dinsa ya daga ya kalli Bibi sannan ya motsa bakinsa
"Kada kace komai maina,mamaki kurum yanzu kake bani" ta fadi tana qare masa kallo tamkar tanason hange meye abinda ya canza a tattare dashi da ya sauya launin mu'amalarsa da sultanan tashi
"Gaba daya ka canza maina,kamar ba kai ba,ka tashi daga mainan sultana ka koma aliyyu haidar,ka tashi daga frèren sulty ka koma wani abu na daban,kana neman zamewa yarinya kamar wani dodo,kamar ba kaine ka raineta da hannunka ba?,kamar ba kaine kaci kashi da fitsarinta ba?,kamar ba kaine kake hana idanunka bacci saboda sultana na kuka ko tana rigima ko bata da lafiya ba,dukka ina wannan kulawar?,tsakaninka da ita yanzu sai kyara sai hantara sai tsangwama,sama da tsangwamar da kakewa kowa cikin gidan nan" bibi ta qarashe fada tana sauke maganganun nata hade da fitar sirrin numfashi,da alama daga qasan zuciyarta maganganun suke fita
"Me yasa bibi?" Ya jefa mata tambayar,idanunta kadan ta qanqance tana dubansa alamun neman ba'asin tambayar da yayi matan
"Me yasa bibi zaku barta ta sangarce bayan kowa cikin gidan nan tarbiyya bai daya ake musu,waye tafi cikin yaran gidan nan bibi?,sai abinda sultana ke so?,sai abinda ya kwanta mata a rai yayi kuma dai dai da raayinta?,bibi wannan ba soyayya bace sam ba qauna bace,ita din diya macace,gidan wani zataje,baki tsoron ta tashi a haka taje masa da dabi'ar da bazai iya ba a dawo muku gida da ita?,wala'alla ni din bana kusa da ku,kune zaku fini jin ciwon hakan,kuma kafin ni na gani ku zaku fara gani kune zaku fara karbar sakamakon"
"Auzubillah......haidar me kake cewa haka?" Bibi ta fada fuskarta na nuna girman da zancan yayi mata. Ba komai saman fuskarsa kaman ma baisan me dame ya cewa bibin ba ya dage dukka girarshi biyu
"Oui(yes)"
"Dukka maza ne zasu iya daukan halin banzanta?"
"Subhanallahi,da gaske ka sauya maina,ka canza,na tabbatar frèren sultana bazai taba fadin haka a kanta ba......to bari kaji,kai din yaro ne da har yanzu bai wuce shekara ashirin da biyar zuwa da shida ba,a dukka matakan tarbiyya banjin kasan wani abu me yawa,bata haka ake yiwa yaro tarbiyya ba,tsanani da matsi basa kintsa yaro ko kadan,ka sanyawa sultana zafi da yawa,kana amfani da irin zafinka na halitta,ita diya mace kwata kwata bata buqatar zafafawar namiji,bare kuma yaran mata da yanzun suke tasawa tarbiyyarsu nada matuqar sulbi da santsi,don Allah maina.....banajin dadin canzawarka kwata kwata,ka koma frère din sultanansa na baya".
Idanunsa ya lumshe sannan kuma ya budesu, muryarsa a lanqwashe yace
"Bibi na fiki jin rashin dadin dabi'un sultana,na kuma taras da ku ba masu goyon baya na ba wajen maidata hanya,bazan canza ba indai sultana ba zata canza ba,dole ta koma kamar kowanne yaro dake gidan nan" kai bibi ta gyada,tun ba yau ba tasan irin nasa halin. Yana da tarin kafiya da taurin kai akan dukkan abinda ya sanya a gaba ko ya furta zai aikata. Fadin zaiyi abu yana da wuyar ji daga bakinsa,amma muddin ya furta din to babu sauyi,komai dadi komai wuya.
Sake gyara goyon school bag dinta tayi dake bayanta,tana jin kamar ta fada dakin ta rufe yaa maina da duka,ai ita batasan haka yayi nisa wajen qinta ba,batasan haka zuciyarsa tayi zurfi wajen son quntata mata ba,lallai Allah baya bacci da har kunnuwanta suka jiye mata komai. Indai yana tunanin iya tsare gidansa,daci da baqin ransa,fada da hararraminsa zai bashi abinda yakeson yaga ta koma din to tabbas zata tabbatar masa ita din ba tsoronsa takeyi ba,kuma bai isa tabuka komai ba
"Sultana kibi a hankali,kinfi kowa sanin waye frère" wani sashe na zuciyarta ya gaya mata sanda take qissima da irin salon da zata shiga falon
"Idan garwashi ne shi ni wuta ce" ta baiwa kanta da kanta dama zuciyar dake gargadinta amsa,bata kuma sake tsayawa sauraron kowacce shawara daga zuciyarta ba ta sanya kai falon da waqar data zame mata madadin sallama.
Idanunta saman fuskarsa tana nazarin furucinsa daya bayan daya,dai dai sanda siririyar muryarta dake cike da tsiwa ta isa ga kunnuwansu tana rera waqar ado isa gwanja
_Allah ka aika munafukinmu qarshen nesa,tafiyar qasa koda lafiya ko babu,kaishi garin da ko kuyanga babu,barshi a can da arziqi ko babu,ni nasha tabara nasha yasin,kuma nasha rigakafin alatsine_ . Sai ta juya zuwa waqar wani mawaqin qasarsu ta nijer
_Munafuki Alla kasheshi,koda safe koda rana ko ma dare ne_
Tana maganar ne kanta yana kallon lobby na dakunansu tana kuma nufar can,tamkar batasan da zaman mutane a wajen ba.